Showing 93001 words to 96000 words out of 270738 words

Chapter 32 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

da daddare haka Gwadabe, ai daka raba tafiyar biyu." Cewar Auwala dake karSama Gwadabe jakarshi. Sai da ya zauna daSas a ?asa yace.
"Kai dai bari. Allah ya iso damu lafiya. Da fatan na sameku lafiya?" A tare suka waiwaya inda Mammada ke bacci yanata gwarti. Dariya suka saki su biyun.
"Wannan matarshi ta shiga uku da wannan gwarti nashi" Cewar Auwala yana dariya. Gwadabe yace.
"Kai kuma taka matar ta shiga uku da shegen cin abinci ba" Harararshi Auwala yayi.
"Au to taka matar dame ta shiga uku, ko kai goma kake ba tara ba?" Dariya ya saka yace.
"Ga gajarta ga tumbi" Dariya suka saka. Gwadabe dai ya mi?e ya samu ya watsa ruwa yazo ya rama sallolinshi.
"Ga abinci Hadiza ta ajjiye maka. Tazo shashennan yayi sau talatin, gorin matan malam ne yasa ta ha?ura, sai ta kawo abincin na ajjiye maka. Ammanfa tare zamu ci ato" Kai Gwadabe ya girgiza kawai. Ya jawo tiran silvern da kwanakin silven ke kai. Kwano na farko dafa dukan shinkafar manja ce da bushasshen kifi. ?ayan ?aramin kwanon kuma farfesun kazar Hausa ne, sai zoSo cikin kofi me murfi na silver. Tunda ya buWe abincin yaji yana wani irin ?amshin spices na musamman. Da ya saka a bakinshi ji yayi tunda yake bai taSa cin abinci mai daWi da ?amshin wannan ba. Yaci abincinnan da yawa, ragowar Auwala ya janye kwanon dan dole.
"Auwala Hadiza ce tayi wannan girkin amman?" Saida ya yagi naman kaza kana yace.
"Itace. Hadiza ba baya ba wajen iya dahuwa, damma bakaci miyar tuwonta ba. Lokacin da take gidan tsohon mijinta ina yawan kai mata ziyara kasanni da son sanwa" Kai Gwadabe ya gyaWa yace.
"Amman mijinta ya tabka babbar asara daya saketa."
"Inji wa? Ko kai Hadiza tayi ma irin abinda tayi a gidan mijinta sakine zai tabbata a garete. Kai bata da daWi fa wajen kishi. Kishinta na hauka ne. Kai dai kabi a hankali. Kuma Allah ne ya jarabceta shi yasa ma ta faWo hannunka a lokacin da kai kuma tuni ka amshi soyayyar wata. Wallahi ba ?aramin so Hadiza take yi maka ba da har ta amince da kishiya tun kafin aure ma" Gwadabe yayi shiru yana jinjina lamarin, tare da auna maganganun Auwala a ma'aunin hankali. Tsoronshi Allah tsoronshi tashin hankalin da zaije ya taSa zumuncinsu. Kuma gashi ya kasance namiji mai son walwala da dauwakammen farin ciki a gidanshi.
Amman yaci alwashin yin bakin ?o?arinshi na ganin bai kunna kishin Hadiza ba a cikin zamantakwar tasu. Yanata tunanin irin zaman da zaiyi dasu su biyun. Da waWannan tunanin gari ya waye haske ya maye gurbin duhu. Nan samarin gidan suka soma layin yin wanka domin fita nema. Masu goge baki nayi, masu goge takalmi nayi. Gwadabe yana zaune a dakali yana jiran fitowar su Auwala. Sai ga Hadiza ta ratso hannunta rike da babban tire. ?urama takunta kallo Gwadabe yayi. A tsanake take yin komanta babu bankaure balle hayaniya. Saida ta kusan zuwa inda yake sai ya mi?e ya karSeta Sadi?u ya ja tsaki yace.
"Aikin banza harara a duhu" Da Hadiza da Gwadabe duk suka waigo suka dubi Sadi?u dake shirin ficewa a shashen.
"Allah ya shirya. Barka da isowa Dijena" Murmushi tayi kawai ta dubeshi tace.
"Ya hanya, ya ka baro kowa da kowa?" Fitowar Auwala ce ta katse amsar da Gwadabe yaso yaba Hadiza. Tiran kayan karin ya karSe.
"Ina kwana Yaya?" Hadiza ta faWa tana haWiye dariyarta.
"Hadiza lafiya. Gwadabe zo da hanzari mu karya mu fice aikine damu sosai"
"To Dijena kije, in muka dawo saimu samu mu tattauna, in kuma baki tsarabarki. Amman naji daWin yin tozali dake, kuma na yaba da abincin da kika girka mun" Farin ciki fal zuchiyar Hadiza tace.
"To godiya nake yi. Nima yanzu wajen aiki zan tafi, in ka dawo ma tattauna ?ila bakasan ina fita aiki ba. Sai kun dawo Allah ya tsare" Juyawa tayi ta kama hanya. Gwadabe kuma ya shiga ciki, suka gama karyawa tsab, aka fita nema. Basu suka dawo ba sai bayan isha yau sunyi dare. Suna dawowa Mammada yayi wanka ya tafi zance. Auwala kuma ya shiga cikin gida ya karSo musu abincinsu. Bayan sun gama ci, Gwadabe yayi wanka sai ya tura yaro yai mishi kiran Hadiza. Bata fi minti goma ba sai gata. Yana hangota ya mi?e tsaye.
"Yau dai muje waje mu Wan zazzaga muna tafe muna zanca Uwar gida sarautar mata" Gwadabe shi ya soma fita Hadiza tabi bayanshi, sai da suka fita waje ne suka jera.
"Soma bani labari. Da safe kince zaki tafi aiki. Dama kina zuwa aikine bansani ba?" Murmushi tayi
"Na fahimci abun ya tsaya maka. Dan in ba haka ba ba hirar daya kamata mu soma ba kenan. Amman tunda ita ka zaSa Shikenan zaka ji. Dama tun ina gidan tsohon mijina ni madam ce ( malamar makaranta) Ina koyar da yara ?an primary school, fannin arabiya, nike Waukarsu Qur'ani da wasu littattafai biyu. to bayan aurena ya mutu ne, sai malam yaje da kanshi ya nemi alfarmar a bani hutu in kammala iddata. To ranar monday na ci gaba da koyarwa. Kaji abinda kake son ji" Kai ya jinjina yace.
"Ashe tare da Madam nake ban sani ba? Kinga in mu kai Aure zaki dinga koyar dani karatu in sha Allah. Yayi kyau ni bazan hanaki aikinki ba, dan Shafa ma tana aiki a Najeriya, kuma wanta ya ro?eni akan in akayi auren zata nemi aiki anan inta samu to." Lokaci Waya annurin dake kan fuskar Hadiza ya gushe. Shiru ya biyo baya, sai tafiya suke yi a hankali. Hardai shi Gwadabe ya kawar da shirun ta hanyar jefo mata tambaya"
"Yaushe su Malam zasu dawo ne?" A ta?aice ta bashi amsar.
"Babu wanda yasan ranar dawowar tasu" Shiru ya ?ara biyo baya, wani Wan dakali Gwadabe ya gani sai ya dubi Hadiza yace.
"Zauna ki huta sarauniyar mata, takawarki Lafiya. Kinsan bana son ki wahala" Dole dai sai da ya dawo mata da farin cikinta, ta hanyar furta mata kalamai. Zama tayi tana dariya.
"To Hadiza nima inaso zuwa gobe in soma sana'ar dafa magunguna na gargajiya. Wanda ya shafi na basir, maganin rana, da shawara, zan dinga ajjiyewa a wajen aikinmu. Sai ki taya ni da adda'a, in Allah ya taimakemu sai kika sana'ar ta karSeni" Sun jima suna taSa hira, daga bisani kuma suka koma gida, shi yayi shashensu, itama tayi nasu shashen.
Kwana Gwadabe huWu da dawowa, Baba Fhatsima suka dawo suma da daddare. A washe gari Malam ya tattare kan iyalinshi harda na gidan auren. Bayan Baba Fhatsima ta rarrabawa kowa tsabarshi, Malam ya soma magana.
"Ma?asudin wannan taron dai shine zaman lafiya da haWin kai. Ni da kaina na ro?eku da ku daure ku haWe kawunanku, ko dan haWin kan ?a?anku. A ko da yaushe a cikin fargaba da damuwar rashin haWin kan iyalaina nake kwana in tashi, lamarin da ya kusan haifarmun da ciwon zicciya. To a wannan karon duk macen data nuna taurin kai, ko ta hana yaran Wakinta yin biyayya a kan dokikina to magana domin Allah zan sallameta. A yanzu in ganku kayukanku a haWe shine babban abinda ke gabana." Take aka shiga ?us?us a falon. Malam yayi shiru yana kallonsu kafin ya ci gaba da cewa.
"Doka ta farko shine, dole ko wanne yaro a cikin gidannan da safe yabi Wakunan matana kab ya gaishesu wajibine wannan, duk wanda ya saSa zai gamu da abinda baiyi zato ba balle tsammani. Kuma tun yanzu inaso yarana in cakuWesu a Waki ba kamar yanzu da suke a wawware ba. Ina nufin Mammada zai koma ?akin su Sadi?u, shi Sadi?u ya koma gadon Mammada, Sabitu kuma ya koma cikin su Zailani, shi zailani ya koma Wakin su Safiyanu. Haka dai nakeso ya canja, domin su soma sabawa da juna tun kafin su yi aure. Sannan a yarana kab, da matan nawa duk me son wani abu daga gareni ga Tasi'u na Waura mishi duk nauyin. Wanda yasa girman kai sai ya ha?ura. Shine magajina, Babban wa uba, dole a bashi matsayinshi" Baba asshi ce ta mi?e tare da cewa.
"Malam inada..."
"Dakata Asshi. Wannan ba malam Win da kika sani a shekara talatin baya bane. Ki zauna ban ba kowa izinin magana ba, asalima bana bu?atar maganar kowa. Duk matar da taji ba zata iya bin dokikin gidana ba, ?ofata a buWe take" Jin irin yadda Malam yake faWa sai kowa ya shiga taitayinshi. Malam ya dinga tsaro yanda yakeso ayi. Abinda ya kamata ace tun sanda yara suna ?anana ya kamata ayi, shi malam sai yanzu akeyi. Kuma wannan ya farune a bisa yanda Malam ya kasa zama tsayayye a gidanshi. Ya sake ko wacce mace inta shiga da irin abinda take shigowa dashi. Shi kuma ya kasa taka burki a gidan nashi. A haka gidan ya cika da yara, a lokacin da yaran suke ?an?ana babu irin rikicin da ba'ayi a gidan. Uwargidan Malam ce kaWai mace mai ha?uri da kawaici. Itake ke iya kawar da kanta in matan malam nayi ma yaranta hukunci, kuma mafi akasarin hukuncin na son zuchiyane. Babu irin hawala da makircin da Baba Fhatsima bata gani ba a wajen Baba Asshi ba. Dan har takai ta kawo malam ko ?ofar Wakinta baya iya kallo in ba ranar kwananta bane. Ta baza mulki tayi abinda takeso. Sai da malam ya sake auro mace ne Baba Fhatsima ta samu sassauci a gidan, domin kishi an kasafta gida biyu a lokacin. Malam kuma duk matar daya auro saita kasance itace ta gaban goshi a wajenshi, harma baya iya Soyewa, hatta cefanan ranar girkinta dabanne kawai. Ire_iren waWannan halayyar ta maza ta rushe haWin kai da zaman lafiyar haula da dama.
MRS BUKHARI


*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
Domin neman ?arin bayani
07082649563 whats app number kira 07036028230
NAMA YA DAHU...
ROMO ?ANYE
BOOK 2
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

10
Haka sabuwar rayuwar gidan Malam taci gaba da kasancewa. Yaran basu da wani zaSi face su bi umarnin mahaifinsu. Yayin da daga bayan fage iyayensu mata ke musu huWubar tsiya, tare da cusa musu tsanar Baba Fhatsima da yaran Wakinta. Ko gaishe da Baba Fhatsima suka je yi, cikin wula?anci da rashin girma suke gaisheta. Itako Baba asshi ko kallon inda Baba Fhatsima take bata yi, ?ar gaisuwarma sun dena, domin tunaninta shine Baba Fhatsima ta murWa kambunta ta sake ?wace gida a karo na biyu. Dan in ranar kwananta ne Malam ya dinga sunturi kenan a tsakar gidan. Itama in kwananta ne, zata shige turaka ta nitsu ta yi gyara na musamman a kunna turaren wuta. Da yamma taci adonta da kaya masu tsada tayi tafiyarta turaka. Wannan sauyi na Malam da Baba Fhatsima ya tsayama matan gidan daram a zuchiyarsu. Yayin da wasu suka soma sake sabon salon kula da malam, su Baba Asshi kuma bata da aiki sai ya da habaici a tsakar gida. Kuma taci alwashin ba zata taSa tambayar Tasi'u kuWi ko yai mata wani abun ba. Itama tana ?a Jamilu, kuma dai dai gwargwado shima yana samu, saidai Allah yayi shi da shegiyar rowa, dan ko matarshi Siyama da ?yar take SamSararshi.
Tasi'u ya dage sai gini aketa faman yi, abunka da kuWi gininnan bai jima ba aka kasheshi, har an soma buga rabta. Ta wani Sangare harya gama siyen kayan gado, da kujerun ?annenshi mata, sauran tarkacen kitchen iyayensu mata ne zasu yi musu. Ya kuma riga ya sallami Baba Fhatsima da ishasshen kuWin kayan kitchen Win Hadiza, da kuWaWen gudanar da harkar sha'anin bikin al'ada. A ranar da yaba Baba Fhatsima kuWinne tace.
"Su mat???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?an Babanka ka basu kuWin da zasu gabatar da sha'anin bikin al'adar ne, kasan fa ana kashe kuWi musamman ga su da zasu aurar da maza. Kuma jibi ma za'aje kan goron mazan gidan. Jibi kuma Malam zai tafi Takai yaje ya sanar musu da lokacin biki" Tasi'u yace da Baba Fhatsima.
"Baba ban ba ko wacce daga cikin su ko sisi ba. Sabida a tunanina tunda auren maza zasu yi su yaran zasu bama iyayen kuWin komai. Yarannan ba ganinki suke da gashi ba"
"Hatta Malam basa ganinshi da gashi. Kai dai kai musu domin Allah domin kuma uwayenka ne. Hatta Amaryar malam nasan zata yi nata taron, da anko duk zata yi naga sai fitarwa akeyi kashi_kashi. Itama ka bata abinda zata yi hidimarta dashi. Allah yayi albarka" Shiru yayi can ya girgiza kai yace.
"Babu komai za'ayi musu kamar yadda kika ce, in sha Allah. Naga yaronnan Gwadabe yayi ?o?ari wajen haWa akwatunan bikin. Sune can ko? Badi'a ta faWamun yasa kaya masu tsada ba laifi, ta yi goshi a matsayinta na Bazawara " Baba Fhatsima tayi dariya.
"Yayi ?o?ari babu shakka, Allah ya fiddamu kunya. Dan Allah ya buWe musu kwanakin baya sosai. Kaga zinarin da suka tono yana da nauyi ainun. Shi ya taimaki harsu Auwala suka ?arashe haWa akwatunan nasu. Kuma sana'ar magani da yake yi matan gidannan na dariya suna tsokanar Hadiza wai taci baya. Sana'ar na taimaka mishi, ana siyen magungunan nashi sosai. Naga har almajiran malam siye suke yi. Kaga akwatin kishiyar Hadizan ma, komai iri Waya ya zuba har kala. Shine ma take ta ?orafi ?asanta da rashin hankali. Da abokinshi ma ya Wauke mishi akwatin ita waccan Win, da dai ya samu halin yine yace zaiyi abinshi" Jawo mishi akwatunan tayi gabanshi, komai na ciki bai bambanta ba, girman takalmi, Wan kamfai, rigar Mama shine kawai na Waya ya zarce na Waya. Dariya Yaya Tasi'u yayi.
"Hadiza daru ba. To na ?ara mata ko kala biyar ne" Baba Fhatsima tayi dariya itama tace.
"Rabu da'ita. Ta haWa kaya famtimoti Babba, kuma duk ta Winka abinta. Ga malam yayi musu kayan fitar biki. Ai kasanta da kishi, kullum cikin faWa nake mata. Jibi Babarku Altine tana hanya zata zo ita da Balaraba ?ar wajenta. Kuma inajin sai an gama bikinnan zasu koma."
Altine ?anwa take ga Baba Fhatsima. Mace mai kirki da son zumunci. Sai dai ba'a wanyewa lafiya tsakaninta da matan malam. Dan bata barin ko ta kwana. Balaraba kuma Wiyarta ce, wacce da akaso ayi musu haWin gida da Tasi'u. Amman a lokacin Tasi'u ya riga ya soma soyayya da matarshi Badi'a. Sai Balaraba ta auri saurayinta dama tana da saurayinta iyayene suka so ayi haWin gida kawai. Yanzu kuma Allah yayi ma mijin nata rasuwa ya barta da yara bakwai.
"Allah sarki. Mama altine jibi ana hanya? To a Sarayina zasu sauka gaskiya wannan karon ?waceta zanyi." Haka dai akaita hidimar biki ta ko wanne Sangare, gidan a kacame yake ko da yaushe.
Washe Gari akaje kan goron Samarin gidan tare da kai fantimoti. An tsayar da biki wata biyu cib. Ranar a gidan ba'ai girki ba, abincinan da aka tawo dashi daga kan goro ya isa har ma?ota sunci shi a wadace Washe gari Malam da Jamilu suka kama hanyar Takai a motar Jamilun, tare da akwatin Shafa wanda daga nan za'a kai nan gidansu Shafa dake Takai Win.


TAKAI TA KAWO TA SABA DA SAUKAR BA?I
Babala tana zaune a tsakar gida, ta jiyo yaran gida na yima Baba Magaji sannu da zuwa. Sai taga akwatuna Bara'u na shigowa dasu.
"Kai Bara'u waWannan famtimotan fa shi Yaya Magaji shine ya tawo dasu?" Murmushi Bara'u yayi yace.
"E dashi suka tawo. Kinganshi ma ya shigo" Yana kaiwa nan ya fice. Yaya Halima da Goggo Iyatu suka fito daga Waki ri?e da haSa har Yaya Magaji da Jamilu suka ?araso.
"Maraba lale da zuwa, Jamilu yau kaine a cikin gidannan iko sai Allah. Wasa gaske Gwadabe naso ya dawo da tsohon zumunci" Cewar Babala data haWe ranta tayi kicin_kicin.
"Baba ku shigo daga ciki, kunsha hanya, ga magriba tayi." Cewar Yaya Halima kenan.
"A'a Uwata bamu ruwa a buta kinji magriba ake kira, in muka yo Sallah mazo a tattauna a tsanake. Hambali bai ?araso bane, na kirashi shi da Harisu nace duk mu haWu anan." Goggo Iyatu tace.
"Yanzu fitarsu masallaci kuka iso" Ruwa aka basu a buta su kai alwala tare da tafiya masallaci. Tare suka dawo dasu Yaya Hambali. Abinci aka dire musu. Baba Magaji da ya kai loma bakinshi bayan an gaggaisa sai ya soma jawabi.
"Wannan fantimotin auren Gwadabe ne, da Shafa ?anwar abokinshi Tamu, ?a?an mirgayi Hamisun Dogo. Da daddarennan nake son za'a kai kayan tare da sadaki baki Waya. Wannan dalilinne yasa nace Hambali da Harisu su tawo dan su jagoranci komai tunda sune manya."
"Kaga ni Yaya ban gane me kake nufi ba. Au jita_jitar da muke ta ji a gari akan Shafa Gwadabe zai aura ashe da gaskene itan zai aura. Ina batun Hadiza ?ar Fhatsima?"
"Du su biyun zai aura kuma rana Waya da izinin Allah " Dariya Yaya Hambali ya saka.
"Ikon Allah waina kwance ya faWi. In banda talaka da nemo wa kai jarfa ina Gwadabe ina mata har biyu Baba. A duba lamarinnan fa, kar a siyar da akuya ta dawo tana cin danga. Dan Gwadabe ba mai ?ashin ma arziki bane shi tun fil azal, duk abinda yaronnan ya taSa sai ya lalace. Yanda Allah yaimun wannan sutura bana jin zan iya shiga wata hidimar Gwadabe, ko dan gudun kar jarfar dake bibiyarshi ta shafeni." Jim Baba Magaji yayi, yana kallon Yaya Hambali da maWaukakin mamaki. Yaya Harisu yace.
"Ni kaina bazan iya saka hannu a duk wata hidimar Gwadabe ba. Yaron dake tafiya da bakin uwa" Jamilu ya buWe bakinshi dan mamaki. Goggo Iyatu kuwa sai sharar hawaye take yi.
"Ohh Yaya Laila ce dai baka ?aunar Gwadabe ya aura. Amman gashi ka jona mishi ?arka kai. Yarinyata ta ?i zaman aure, yanzu haka tana gida an sake sakota, bayan mijin yayi mata kafirin duka."
"Hmmm ni kam nama rasa ta cewa wallahi. Yaya Gwadabe kaima Wanka ne. Kai kaWai gayyane zaka iya zartar da komai. Gidansu Shafa ka sani. Allah ya sanya alkairi shine kaWai abinda zance. Amman Gwadabe ai ya nuna mun bai haifu a cikina ba. Tunda ni ina matsayin uwarshi sai dai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login