Showing 36001 words to 39000 words out of 270738 words

Chapter 13 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

biyun zaki yi ki dawo, kuma zaki iya kare mutuncinki a matsayinki na matar aure, bahaushiya ?ar Najeriya, najeriyarma Arewa?"
"To Iyabo ina kyautata zaton hakan. Ke kinga mata aure masu tafiya kuwa? Wallahi sun fi ?an matan yawa, harda dattijai fa baki gani ba. Kuma ba ta Sarauniyar hanya zamu bi ba, ta hazo zamu keta " Shiru nayi ina Wan nazari. Kafin ince da'ita wani abun sai ga Gwadabe ya shigo akan kekenshi. Wannan dalilin yasa dole muka katse hirar tamu. Uwani tai mana sallama ta tafi.
Tun daga ranar na soma ba Gwadabe ruwan addu'o'in nan safe da yamma, haka kullum sai na goge mishi jikinshi da ruwan maganin. Allah al Hakim cikin kwana na tara da rana kawai sai ?afar Gwadabe ta motsa kamar da wasa.
"Iyabo ?afata na motsawa" Na ji ya faWa cikin zabari. Kafin ma in ?araso inda yake harya mi?e tsaye.
Suddajar godiya ga mahalicci mu ka yi a tare. Muna Wagowa Gwadabe ya rungumeni tsam a jikinshi yana shafar bayana, tare da sama rayuwata albarka.
"Iyabo kinga ikon Allah ko? Ha?i?a na sake tsinkewa da lamarin Ubangiji Allah. Allah na gode maka daka bani lafiya. Ya Allah dukkanmin mai ruwa da tsaki akan wannan rashin tafiyar tawa ya Allah ka nuna mishi iyakarshi" Ni kuma sai amsawa da ameen nake yi. Ko yara da suka shigo suka ga Abbansu akan ?afafunshi sai suka shiga murna harda tsalle. Rungumesu yayi dukkansu. Farin ciki da jin daWi bazai misaltuba, bazai rubutu ba balle har mai karatu ya fahimta" Bara'u shine mutum na farko daya samu labarin warakar Gwadabe. Ni kuma ta Sangarena Uwani na soma sanarma, kafin na sanar da gida. Na le?a tsakar gida duk suna tsakar gidan ko wacce tana aikin girki nace.
Ku ta ya mu murna Allah ya ba Gwadabe lafiya, ciwo ya warke"
"Warkewa fa kika ce Iyabo?"
Cewar Gude, kafin in bata amsa Gwadabe ya fito tsakar gidan. Ai sai suka ri?e bakinsu.
"Allah ya bani lafiya haka tace. Gani akan ?afafuna. Godiya ta tabbata ga Allah" Yana faWar haka ya koma ciki ri?e da ?an biyu. A masallaci abun sha'awa Gwadabe yayo sallar magriba, bashi ya shigo gida ba sai bayan isha sabida mutane sun baibayeshi ana mishi barka. Hatta su Baban Nazifi a masallaci suka haWu da Gwadabe, kamar yadda ya labarta mun sun yi mamakin ganinshi akan ?afafunshi. ?afa mai daWi yau sai ga Gwadabe a bayan gida yana yin wanka da kanshi, Allah abun godiya ne
A daren ranar Gwadabe yasha labarai sosai. Hira mu kai ta zabgawa muna murna da farin ciki. Furucin Babala yananan Wamfare a zuchiyata ya zame mun ciwo. Na yi alkawarin washe gari zamana a gidan Gwadabe yazo ?arshe kenan. Har yayi bacci idanuna biyu ina tunanin inda zan nufa in na bar gidan Gwadabe. Wata zuchiyar tace mun.
"Ga mahaifiyarki da kike ganin kamar tana da wani ciwo a zuchiyarta me zai hana ki koma hannunta da zama. Tunda yanzu kin mallaki hankalinki?" Idanuna na lumshe wasu siraran hawaye suka gangaro kumatuna. Na jima ina karanta wasi?ar jaki kafin na daure na taso na fito falo na Waura alwala na soma Sallah. Bani na tsagaita da sallar ba har sai da naji kiran sallar farko tukunna. Takun fitowar Gwadabe na jiyo. ?ura ma ?ofar Wakin idanu nayi. Shine ya fito yana saye da jallabiyya fara. Idanu ya ?uramun yana sakarmun murmushi me kyau da tsayawa a rai. Take zuchiyata ta sake yin rauni ainun. Ruwan hawaye suka Sallo daga idanuna zuwa kumatuttukana. Tsugunnowa Gwadabe yayi a gabana, ya shiga share mun hawayen nawa. Abun mamaki ruwan hawayen sam sun ?i ?arewa.
"Iyabo na yi tunanin hawayen farin cikin ganina akan ?afafuwana kike yi ai. Amman na fahimci akwai ciwo mai raWaWi dake damun ruhinki. FaWa mun menene matsalar? Naso in kwanta dake daren jiya, ko dan kewar juna da muka yi, amman na rasa gane dalilin da yasa kika kasa bani kan ki, mu raya daren da yake cike dam da farin ciki. Daren da babu daren da zai iya tureshi a ?wa?walenmu" Kuka na fashe dashi mai gunji, na rasa yanda zan yi da raina. Zugi zuchiyata take ta tayi mun.
Gwadabe cike ruhina yake dam da farin cikin samun warakarka. Gefen zuchiyata kuma cike da fargabar yanda rayuwata zata koma bayan rabuwarmu. Gwadabe ya zama dole mu rabu, muddin muna son juna so na gaskiya. Mu Wauka rabuwarmu itama ?addarace. Har abada sonka zaita wanzuwa a cikin rayuwata, kullum sake halittar sabo za'ayi. Ta yiwu rabuwarmu ka iya kawo ?arshen numfashina, ko ya zama silar kamuwa da wani ciwon da zai ta cin naman jikina har sai ya kaini ga kushewa. Amman Gwadabe na sani har duniya ta naWe ba zaka manta da gudunmawar dana ba rayuwarka ba....." Tashi nayi ina shirin shigewa uwar Waki domin soma shirya kayana. Gwadabe kuwa duk illahirin jikinshi rawa kawai yake yi mun. Cikin kaurin murya irin ta cikar mazantaka yace.
"Iyabo..." A maimakon in tsaya sai na shige ciki da gudu na saka sakata. A jikin ?ofar na jinjina ina jawo numfashi daga cikin huhuna da ?yar.
Iyabo ki buWe ?ofarnan dan Allah na ro?e ki kar ki sa zuchiyata ta buga." Ya faWa hakan a mugun raunace, tsabar Sarin da jikina yake yi ma na kasa ko da motsawa, jin za'a shiga Masallacine yasa ya fita dole, ina jiyo rufo mana ?ofar falo da yayi. Sai da na haWa ?an tsunmokaraina a ?aramin akwati, na ajjiye gyalena a saman akwatin kafin na tada kabbarar sallah. A lokacin ?an biyu sun tashi daga bacci. Ina idarwa saina gyara zama na soma azkar, ina yi ina kallon yarana. Toye yana tsakankanin ?an biyu yana wasa dasu. Sai dariyarsu suke yi. Yara kenan su basu da matsalar komai. Iyaka su yi bacci su tashi su ci abinci.
Ku sakko ku je ku yi alwala ku yi salla, na faWa musu da yaren yarbanci. Dukkansu sai da suka rungumeni kafin na buWe musu ?ofa suka fita. Ai sai na kife a dadduma na shiga rera wani irin kuka na tashin hankali. Inayin kukan nan ban mance da ambaton Allah ba. Jin hucin mutum nayi a gefe na, Gwadabe ne nasan babu makawa. Ri?o hannuna yayi gam, ya rarrasheni ya kasa, yayi magana wallahi ya kasa. Duk dauriya da irin shanye abu na Gwadabe yau zuchiyarshi a tsinke take. Shima hawayen yake fitarwa a gidanunshi. Mun fi minti goma a haka, yara dai ban sake jiyo Wuriyarsu ba ma. Sai can Gwadabe yayi ajjiyar zuchiya kana yace.
"Iyabo yanzu me kike so in yi, ina al?awarin da muka Waukarma kawunanmu zai kwana, babu rabuwa a tsarin da muka tsaroma rayuwar gidan aurenmu...."
Dakata Gwadabe, kar so ya rufe maka idanu, ka kai rayuwarka ga halaka. Wallahi zaman mu babu alkhairi, kuma ba zamu taSa ganin haske ba. Tunda Babala ko da yaushe a cikin zubar da hawaye take. Ta yiwu bijerema iyayenmu da mu ka yi ne ya jefa mu a cikin halin da muka shisshiga a baya. SiraWi nawa muka tsallake Gwadabe? Ka tsayar da zuchiyarka kul sona ya ruWeka, uwa tafi gaban a tsaya ana jayayya da'ita wallahi. Dukkanmu ba zamu so yaranmu su yi mana taurin kan da mu ka yi ma namu iyayen ba, Gwadabe mun zuba taurin kai sosai da sosai. Allah ya jarabcemu da talauci sosai da sosai sakamakon fishin iyaye da muke ciki. Ka daure ka sake ni kawai in tafi" Cikin dashasshiyar murya yace.
"Ko dai har yanzu da ragowar soyayyar Debisi a zuchiyarki ne Iyabo? Ni fa bazan iya rayuwa babu ke ba. Da maraici kike so yaranmu su taso ne?" Cikin jin haushi, gami da tausayinshi a haWe na dubeshi. Nayi mishi uziri dan tabbas a cikin tsaka mai wuyar fita yake, dole nice dai zan lallaSashi ya sauwa?e mun.
Billa babu ko sofanen son Debisi a zuchiyata. Mutumin daya gujeni sabida halittar ?ibar da Allah ya hore mun, to shin me zan yi dashi a cikin rayuwata. Ka sake ni kawai, domin cika umarnin Babala da cika alkawarin da nayi mata. Ce mata nayi a ranar daka samu lafiya ko kwana da igiyoyin aurenka bana kumawa" Mun fi awa guda muna tataSurza tsakanina da Gwadabe. Muna cikin haka, Allah da ikonshi muka jiyo sallamar Babala a cikin falo, tana tambayar Toye ko muna ciki ne" Jijjunanmu a mace muka fita falon, ita da Baban Nazifi ne, sai Yaya Harisu. Gurfana nayi a gabansu cikin rawar baki na gaishesu, babu wanda yayi yin?urin amsawa.
"Rana bata ?arya sai dai uwar Wiya taji kunya. Gwadabe yau zan yi bacci harda munshari sabida wannan jikar oduduwan zata bar gidannan, igiyoyin aurenka zasu sauka a kanta. Kuma bari kaji danginta ne su kai ma Agumu ( sammu) ba kowa ba, domin ba ?aunarka suke yi ba. Wajen malamai har biyar muka je, duk maganar Waya ce dai. Maza saketa ta kama gabanta yanzu_yanzu. Ko wallahi in tsine maka"
Idanuna na runtse bakina, harshena suna kakkarwa kunnena na baza ina jiran kalmar saki. Kamar saukar aradu naji ya furta.
"Na sake ta saki Waya Babala" Wani wuji_wuji naji yana dibata, take mashashshara ta saukar mun. Ajjiyar zuchiya Babala ta sauke kana tace.
"Cikace mata ya zama uku Wan albarka"
Na sake ta saki biyu, in aka haWa dana baya dana yi uku kenan." Ya faWa muryarshi a mugun dashe kamar wanda aka sha?e. Mi?ewa nayi tsam, duk da jirin da nake gani, amman bazan iya jure shaa?ar numfashin Gwadabe ba. Uwar Waki na shiga, Toye da ?an biyu suna katifa suna wasansu. Ganina yasa Toye cewa..
"Mama kinga Kahinde yana dukan Taiwo ko, bayan itace yayarshi" Sai da na zari jakata kana nace.
Kahinde ka dena dukanta, yayarka ce. Kai kuma Toye ka kula sosai da maraicin ?annenka. Zan yi wata ?ar tafiyar da bansan yaushe zan dawo ba" Duk da yaron yana da ?arancin shekaru amman sai naga yayi jigum kamar mai tunani. Kayukansu na shafa tare da saka musu albarka, na fito daga Wakin a sanyaye, har na kai bakin ?ofar fita na jiyo muryar Babala tana cewa.
"Yaran wa kika barma, wa kike tunanin zai ri?e yaran yarbawannan? Maza koma ki kwasosu..."
"A'a Babala yara kam zan rayu dasu, ni yafi dacewa in kula dasu tunda dana aurota iyayenta ita gayanta suka bani, kiyi ha?uri dan girman Allah " Gwadabe ya katseta da hanzari. Kai nasa nayi ficewata daga Wakin. Matan gidan duk suna tsakar gida da yaran gidan, suna hangoni ko wacce ta sau abunda take yi kallo ya koma sama wai shawo ya Wau giwa. Ni ko murtuke fuskata nayi sosai ta yanda ba wacce zata iya samun fuskar tambayata, nayi ficewata zazzaSin dake jikina sai tsananta yake yi. Ko da na shiga Bus Win unguwarmu na kifa kaina a bayan kujerar dake gabanku ban Wago ba har sai da muka iso. Duk wannan abun babu ko Wigon hawayen daya sake zubo mun tunda kunnuwana suka saurari kalmar saki. Ko gidanmu ma bansan ya akayi na iso ba, ganina kawai nayi a ?ofar shagon Iyaa.
" Ahh ahhh ahh Iyabo kini o ti sele? ( Me ke faruwa )" Iyaa ta faWa cikin kwakwazo da kuzuzuta lamarin. Kafin in mata amsa sai ga Iyaa Kokodeen ta fito daga cikin gida, itama ganina ne yasa ta nufo ni.
"Iyabo lafiya da sassafe haka harda jaka a hannunki?" Jin haka yasa Iyaa fitowa a kidime zaninta na suSucewa.
"Ahhh ahhh ya sake ta ba? Ai dama mu munsan zaki dawo, ba ri?e aure suke yi ba saki ko da yaushe, da laifi ba laifi saki. Kinga abunda muke guje miki tun ba'aje ko ina ba har ya faru. Da yarenki kika aura da kin samu kwanciyar hankali. Ai sai ki shigo mu ci gaba da zama kafin Allah ya Sullo miki da wani. In ce dai babu wani ragowar igiyar da tai saura? Dan wallahi kin bar komawa wannan auren, an yi na farko, gana ?arshe yayi." Duk wannan maganar cikin yare take yi, tana yi tana buga cinya tare da tafa hannaye. Jiyo muryar ta ne ya tilastama su Iyaa Beji fitowa da sauri. Suna fitowa ni kuma na shige cikin shagon Iyaa na Sulle cikin gida abuna. Ina shiga Wakin Iyaa na tarar da Yemisi a kwance a ?aramin gadonmu a kwance da dukkan halamu itama a gida ta kwana. Zama nayi a ?asa jiSur. Zaman nawa ke da wuya sai ga su Iyaa sun shigo da duk matan gidan, suka tutsiyeni kan sai na faWi silar mutuwar auren. Daga masu cewa gwara da aka rabu, sai masu cewa zasu je su Webo yaransu su girma a cikin yaren mahaifiyarsu. Ni dai suka sak sani a tsaka mai wuya.
"Ki buWe baki kiyi magana mana kin ma mutane shiru"
Babu abunda ya haWa ni dashi.mahaifiyarshi ce ta bashi umarnin ya sake ni. Igiyoyin auren sun ?are duka" na faWa a sanyaye. Da hanzari Yemisi ta tashi zaune zumbur kamar wacce aka tsikara. Idanu muka haWa, dan na riga na gane manufarta na wannan zabura haka. Iyaa ce ta katse mun kallon Yemisi da nake yi dafe da kirjinta.
"Sai da kika gama mishi jinya tas ba, iyayen nashi ba ke suka bari da Wawainiyarshi ba? Kika kaWar da kayan Wakin ki tas komai ya ?are a nemo lafiyarshi, to ga sakamako kin gani. Wanne irin bijere mana ne baki yi akan Gwadabe ba, amman shi gashi ya nuna miki yafi son uwarshi sama dake" Cewar Iyaa da take magana a tsawace. Iyaa Kokodeen ce tace.
"Ahh ki barta haka ta ji da zafi gami da raWaWin mutuwar aure, daga baya ayi wacce za'ayi." Da Waya da Waya suka watse Wakin ya rage daga Iyaa sai ni da Yemisi. Da ?yar Yemisi ta amsa gaisuwata har tana hararata. Ni abunda yake damuna shine a gabana da ta kwantar da hankalinta ma ?ila wannan itace gamuwata da'ita ta ?arshe daga ita har mijinta. Dan a wannan karon garin Kano ta yi mun zafi ainun, na fi son in je rugar mahaifiyata in zauna a cikin danginta da ?annena nima. Ina cikin zancen zuchi sai ga sallamar Debisi ya shigo. Irin kallon daya watso mun da dukkan halamu Iyaa ta labarta mishi abinda ya faru dani. Kaina a ?asa na gaisheshi cike da ladabi.
"Lafiya lau Iyabo. Sai kuma naji mummunan labari marar daWin sauraro?" ?an murmushi kawai nayi kaina a ?asa.
"To Allah yasa hakan shine a'ala gareku baki Waya. Allah ya fito muku da waWanda za su yi dai dai da rayuwarku. Kar ki saka damuwa a ranki. Shi aure rai gareshi nasan kin sani" Duk wannan maganar da yayi yana tsaye a kaina yake yi. Shigowar Burodami kokodeen, da Anty Mulka, da iyaa, da iyaa Debisi, da duk masu ruwa da tsaki na gidanmu ne yasa Burodami Debisi ya nemi waje ya zauna. Alfa Kulle shine ya shigo a ?arshe, Wa yake ga mahaifina, ?ani ga Iyaa Debisi cikinsu Waya. Kuma ya kasance shine mai ?arfin faWe aji a family kasancewar shi kaWai ne namiji da yai ragowa. Gidanshi yana jikin namu gidan. Amman iyalinshi suna Ibadan da zama, sai dai duk shekara yana kai musu ziyara. Burodami kokodeen ne ya buWe taron da adda'a kafin Alfa Kulle ya tambayeni cikin yaren yarbanci.
"Meye silar rabuwarki da mai gidanki?" Murya na rawa na labarta mishi a ta?aice, sai Iyaa tayi carab tace.
"Dama tun auren a difane fa take a gidan auren. Dangin miji kullum cikin ?yamatarta suke suna aibanta mata yarenmu. Buradomi Kulle meye kai baka zaunar da yarinyar nan ka faWa mata ba, ba ?afa tasa tashure ba, sabida ganin ba mu muka tsugunna muka haifeta ba, ?asa ta rufe ma Toye idanu. Cikinmu nan babu mai son wannan auren " Alfa Kulle yace.
"Ta faru ai ta ?are. Ba shikenan ba auren ya ?are kan kat ba. Sai. Ki zauna zuwa lokacin da Allah zai Sullo miki da wani mijin.
Inason in koma Rugar mahaifiyata can inda kowanta yake. Dan Allah kar ku hanani wallahi bazan iya zaman Kano ba" Ina jiyo ajjiyar zuchiya da Yemisi ta sauke mai ?arfi. Iyaa kuma ta dire akan ban fa isa in bar hannunta ba. Sai da kowa dake wajen ya sa baki kafin ta amince sai zubar da hawaye take yi. Burodami Debisi kuwa ya kasa cewa komai. Zahiri bai ji daWin amince mun da kowa yayi akan komawata ruga ba.
"Zuwa yaushe kike son tafiya Iyabo?" Burodami kokodeen ya tambaya. A sanyaye nace.
Zuwa gobe in Allah ya kaimu" A haka dai taron ya watse, duk yanda Burodami Debisi yaso keSancewa dani Matarshi ta hana shi wannan ?ofar.
MRS BUKHARI

3064127935
Buhari Ibrahim Ladan
First bank

Sanya nera 500 Winki kuWin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan.
Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun
Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. ?ar?ashin Amila Foundation gidauniyar da muka buWe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya.

WaWanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ?ANYE)
300 kacal zasu iya kuWin karatu
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm



NAMA YA DAHU...
ROMO ?ANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

LAMBA TA SHA ?AYA (11)

*ASSALAMU ALAIKUM MASOYAN IYABO MUNA MI?A SA?ON GAISUWARMU A GAREKU. IYABO TACE IN SANAR DAKU TANA GODIYA DA KUKA TAYA TA JIN ZAFIN RABUWARTA DA GWADABE. TANA MI?A ?UMBUN GAISUWA GAREKU*

*(Na sha ?orafi akan in yi ha?uri inyi har asabar da lahadi. To duba da irin son da kuke nuna ma labarin ?orafinku ya karSu a yanzu. Amman da zaran free page ya ?are zaku dinga samun posting ne daga monday zuwa alhamis kaWai, juma'a asabar lahadi na hutune. Kuyi mun afuwa kunsan bana wasa da yin posting ina da lalurar idanune shi yasa. Amman zaku samo readmore masu yawa in sha Allah nagode)*




Duk yanda Burodami Debisi yaso ni da shi mu samu keSewa Yemisi ta kulle wannan ?ofar a tsakaninmu. Ta cikin idanunshi nake iya karanto labaran dake cikin zuchiyarshi. A haka na wuni cur a waje Waya tamkar mutum mutumi. Ma?otanmu da ?an uwanmu yarbawa su kai ta shigowa jajanta ma Iyaa. Da ?yar cikin tursasawa da lallami Burodami Debisi yasa na sa lomar abinci a bakina. Har zuwa wannan lokacin hawaye bai zubo mun ba fa, face ruhina dake gasuwa, ha?i?a kuka rahamane.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login