Showing 12001 words to 15000 words out of 270738 words

Chapter 5 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

da Laila da mu ka yi. Iyabo kar ki yarda shaiWan ya rinjayi zuchiyarki. Ki tuna Gwadabe ne naki wanda kikai mishi Al?awarin mutuwace kaWai zata iya gibtawa a tsakaninki dashi, ki rufa mun asiri ki zauna a Wakinki"
Shiru yayi yana jiran abunda zance.
Gwadabe a gaskiya bazan iya zama da Laila a Waki Waya ba. Bayan tana Wakin mijinta ma bata dena turo maka da sa?onnin ?auna ba. To ka sani in ba baka san na san sabida kai Laila ta kaso aurenta ba, to na sani. Dan haka bazan zauna da kishiyata Waki Waya ta gama gane mun sirrina ba, in aurenta zaka yi basai an turota yimun c.i.d ba."
Yanda nake maganar ina haki yafi komai Waga ma Gwadabe hankali ?uri yayi mun da idanu yasan tabbas naje ma?ura dan tsakaninmu yi nayi ne, bari na bari. Kafin ya tuno lafazin da zai rarrasheni dashi akayo kiran wayarshi, ya zaro a aljihu. Oga Lurwanu naga an rubuta, shine ogan Gwadabe wanda yake ma karen mota. Da sauri ya Waga, murya a sanyaye yace.
"Oga Lurwanu yanzu na shigo Kanon, zan tawo yanzu in sha Allah, an gama lodinne?"
Daga cikin wayar Oga Lurwanu yace.
"Ka hanzarta Gwadabe, an yi rabin lodi, ana gamawa zaku kama hanyar Ikko da izinin Allah. Karen motarka yana nan tare dani tuntuni."
"To Oga Lurwanu abinda zan barma iyali fa? Wallahi Wari ukune a jikina da zanyi kuWin motar zuwa inda kuke. Kuma a gidan babu komai. Kasan lamarin sai godiya"
Oga Lurwanu yace.
"Wannan babu wata matsala. Kai dai ka tawo Win. Ko yaro ka ba sa?o ya ajjiyema Iyalan. Kai muke bu?ata yanzu"
A haka su kai sallama da juna. Yana sauke wayar a kunnenshi ya dubeni. Hawaye nake ta faman sharewa.
"Iyabo gashi bani da lokaci a halin yanzu. Kina jina da Oga Lurwanu. Abinda zance miki shine ki tausayama masoyinki ki yi zamanki a Wakin ki, ki toshe kunnuwanki, ki Wauke idanuwanki daga gani ko jin komai. Dana dawo zan nema mana mafita, amman in sha Allah Laila ba zata zauna tare damu ba. Ki kuma kwantar da hankalinki Laila ba zata taSa samun gurbi a zuchiyata ba. Ba zata iya ruWata da komai ba, a gabana ta yi wasan ?asanta. Ni naki ne ke kaWai Iyabo. Nasan kishi ke nu?ur?usar zuchiyarki. Kinga hanya zan hau, taya hankalina zai kwanta in na barki kika koma gida. Sannan ke kan ki in kin koma gidan wani sabon damuwarce kika jefa mu a ciki. In ci albarkacin soyayya haba tauntsun soyayya"
Duk wannan kalaman cikin sigar so gami da rarrashi yake yinsu. Gabaki Waya sai jikina ya mace mus. Ance tsakanin mata da miji sai Allah. Duk da ina jin bazan iya zama da Laila ba. Amman ya kamata in ma mijina uziri tunda shima umarni aka bashi, kuma bazan so akan faranta mun ya saSama wacce tai sababin zuwanshi duniyar ba. Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace.
Kana da girman daraja a guna. Kaje Allah ya tsare maka hanya. Ya kareka da sharrin ?arfe da sharrin hanya. Allah yasa sai dai ka ajjiye motar da hannunka ba dai ta ajjiyeka ba. Allah yasa a soma a sa'a, Allah yasa ?arshen wahalarmu ne yazo. Ka kular mun da kan ka Gwadabe, dan akwai tarin tulin maganganu marasa daWin ji a kan ku direbobin manyan motoci, sunan masu sana'ar tu?in manyan motoci yayi ?auri, sun san sirrin ajjiye daduro ni bana zarginka amman ina tunatar dakai jin tsoron rabbissama wati wal ardi. Kar ka zama daga cikin irinsu dan Allah, duk da a ko wacce sana'a akwai nagari, akwai na banza." Murmushi yayi ya rungumeni dani da ?aton cikina yace.
"Kamar yadda kika faranta mun raina, Allah ya faranta miki kema. Mala'ikun Allah ku shaida na Waga ?afafuna domin Iyabo matata ta shiga Aljanna" Dariya mu ka saka dukanmu.
Ka hanzarta jiranka akeyi dai kar ka shagaltu"
"Wallahi kuwa. To ni zan tafi, zan aiko da Wan kayan abinci da kuWin da zaki ri?e a hannunki. Ki kula da kanki da abinda yake cikin ki. Da zaran kin soma jin na?uda ki sanar ma Bose, nima ki yi gaggawar sanarmun, Bara'u sai ya zo ya tsaya. Ballema ina ro?on Allah yasa sai ina nan zaki haihu. Sannan ki kula sosai, Laila Sarauniyace ta bugawa a jarida, ko Sera bai kaita iya sata ba, kuma bai fita dabarun iya sace abuba, har hannu take sawa a wandon jeans na maza a kasuwa ta yashesu, gidan biki ko suna kuwa sata take yi tamkar tana bacci dan sauki. In zaki je gidan aiki ki kulle uwar Wakin ki kar ki sake ki bar mana ?ofa a buWe. Dan komai Wauka take yi" Sumbatata yayi a baki, tare da ri?o hannayena muka mi?e tsaye a tare.
To in sha Allah zan kiyaye, Allah ya tsare. Mu je in rakaka" Tare muka fito zuwa falo. Laila na tsaye a gaban hoton aurenmu dake manne a falon. Na ci lace da gwaggwaro. Gwadabe ya sha rigar asheke da hular ashoke kai ka rantse beyerabe ne shima. Jin motsinmu ne yasa ta zauna a kujera mafi kusa da'ita.
"Fita zaka yi ne Yaya Gwadabe?" Ta furta da zazza?ar murya ba irin tawa ba, dan muryata tana da Wan girma gami da kauri.
"E tafiya zanyi ma. Ni sai na dawo. Iyabo ki koma ki kwanta ki huta zuwa azahar kya tashi ki yi wanka ki yi salla." Kafin in ce wani abun muka jiyo sallamar Uwani Tabalbalin ?awata tun ta ?uruciya, ?awarda banda madadinta.
"A maraba lale Tabalbalin kece a tafe? Ai kuwa kinci sa'a dawowar ?awar taki kenan daga ?auye" Cewar Gwadabe daya tari Uwani da fara'a sosai. Cikin dariya tace.
"Gwadabe na Iyabo ikon Allah tsuntsun soyayyar daya tashi daga kan Debisi sai ya hau kan ?an hausawa. Fita zaka yi ne?"
Dariya muka saka dukkanmu, wannan suna ya?i fita a bakunan waWanda suka san gwagwarmayar da muka sha kafin aurenmu.
"Wallahi tafiya zan yi ma zuwa Ikko. Ya yaran, ina Hafizu Oga ba?" Dariya mu ka yi duka.
"Hafizu na baroshi a majalisarsu"
A wajen mu kai sallama da Gwadabe ya fita, mu kuma muka koma uwar Waki ni da Tabalbalin.
"Ashe tafiya kuka yi Iyabo. Kaddai bikin ?anwar mijinnan naki marar kunyar nan, wacce ta watsa mun miya a zani lokacin sunan Toye kuka je?" Zama na yi a bakin gado. Na yi shiru kawai dan batun zaman Laila na ci mun tuwo a ?warya. Zama Uwani Tabalbalin ta yi a kusa dani tace.
"Akwai wata matsalar ne Iyabo? Nasan ai ba zata wuce irin wula?ancin da dangin Gwadabe suke yi miki ba ko. Balle kunje ?auye an shiga taron biki"
Wallahi da shine ma da sau?i Uwani. Ai kinsan Laila tsohuwar budurwar Gwadabe, ?ar uwarshinnan wacce kwanakin baya muka samu saSani?" Kai ta gyaWa tace.
"Na ji na ji. Wacce take turo da sa?on batsa tana gidan wani ko, ai kece banza da baki zaune ?ar banza ba. Halan wani abun tayi miki a cikin taro?"
Itafa ?awata. Ana baki kina karSa Tabalbalin"
Bata labarin abinda ya faru nayi kab ina share hawaye.
Uwani da ba dan in na koma gidanmu tamkar na tozarta aurena bane, da wallahi kafin Gwadabe ya dawo na bar gidannan."
"A'a kar ma ki soma. Dan in ma kika je Iya Debisi sai ta kusan illataki banda kwakwazon da za tai ta yi miki, ma?otanku ma sai sun ji meke faruwa. Amman gaskiya kar ki kuskure ki yarda kici gaba da zama da'ita Waki Waya maganar gaskiya. Ba zata zo har Waki ta iskanta miki miji ba. Amman ko da wasa kar ki sake ki bar Wakin ki, yo kin bata dama ta kwace miki miji cikin sau?i kenan ma. Nifa dani Gwadabe yake Aure da tuni na seta kan ?an uwanshi. Ki kwantar da hankalinki tunda Gwadabe yace zai samo muku mafita kema kinsan bazai barki haka ba. Ya kika baro Sakina da mijintannan nata mai barkwanci Bara'u?"
Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Suna lafiya lau Uwani, ya Hafizu da yaran?" Shiru tayi na Wan lokaci tace.
"Iyabo yau haka muka wayi gari ko lomar da zamu kai bakinmu babu wallahi. Yaran sai turasu gidan Hajiyata nayi nasan ko ba komai ba zasu rasa abinci ba, tunda Hajiya na yin Wanwaken saidawa. To mu Win bamu ci komai ba, ga ni da ciki na wata uku ban baki labari ba, wallahi bansan ina da cikin ba. Ga hayarmu ya ?are gobe mai gidan zata zo karSar kuWinta, ko ficika bamu ajjiyeba, babu wanda muka ba ajjiya. To shine na sha maganin zubar da ciki cikin ya zube yau Winnan, Iyabo bazan iyaba, Hafizu bashi da zuchiyar nema. Ni rayuwarma ta isheni Iyabo, Talauci masifane ?an uwanka ma sai su gujeka su ?i taimakonka" Kuka ta fashe dashi kawai. Ban hanata rera kukan ba, domin kusan ni na fita sanin zafi da raWaWin talauci da wayar gari babu abinda za'a saka a ciki. Tunda Hafizu da yana da rufin asirinshi direban ?aramar motane yana lodin Kano to Gomber, da Bauchi. Motarshi ce tayi haWari ta yi rugu_rugu. Har yanzu bai samu wata motar ba. Shi kuma ya Waurama kanshi girman kan neman wata sana'ar. Daga haka ya Sige da zaman kashe wando. Shi yasa rayuwar ta Waure musu. Amman ni dama a haka na shigo gidan Gwadabe na sameshi. Dama bashi da cikakkiyar sana'a duk abinda ya fita ya samu yi yake yi kawai. Numfashi na ja kana nace.
Kiyi ha?uri Uwani da sauyin rayuwa. Mu yi ta yi musu addu'a babu dare ba rana. Ubangiji rabbissama wata wal ardi zai bamu mafita, zamu ji daWi a gaba komai lokaci ne. Tashi mu je mu hura wuta, ga Wan abinci mun samo daga ?auye, ko fara ce in dafa mana, ina da yaji, mai ne babu dai." Tire na Wakko na zuba shinkafa ?ar hausa Gongoni biyar, Uwani ta karSa ta fita. Kurfot Wina na zaro a ?ar?ashin gado da ?ullin gawayin hamsin a kai, nima na fito tsakar gidan. Wuta na hura da leda, Uwani na zaune a kujera tana tsintar shinkafa tace.
"Ji gidan shiru kamar ba shi bane mai tarin hayaniya da bataliya ba" Yatsana nasa a leSena nai mata nuni da tai shiru sabida Laila. Dole mu ka zama kuramen dole. Tashi nayi na Wakko tukunya na buWe randata dake bakin ?ofa cike da ruwa na zuba ruwan a tukunya, na Waura a wuta. Ruwan na tafasa Uwani ta wanke shinkafar ta zuba. Alwala muka Waura dukkanmu muka shiga Wakin. Da sauri Laila ta ajjiye kwanon samira dake ajjiye a gefe guda. Kallonta nayi itama ta kalleni. Kai na girgiza na nufi hanyar shiga ciki.
"Am Iyabo a ina zan ajjiye fantimotaina naga kamar basu dace su zauna a falo ba" Kallonta nayi na ?ara.
To a ina kike ganin ya dace ki ajjiyesu in ba falon ba?" Na bata amsa cikin danne fishi, dan ji nake wallahi kamar in dira a wuyanta.
"A uwar Waki mana, taya zan ajjiye kayana a falo?" Ta faWa a gadarance irin ta dangi miji dan halinsu ne wannan kam. Cikin cusa haushi nayi dariya nace.
Haba Laila, ai uwar Wakina mallakinane tafi ?arfinki, iyakar taki a falo take. Uwani mu shiga ko?" Na yi shigewata ciki na bar Laila tana surutai ni bansan ma me take cewa ba. Abinci na zuba mana a tire. Na zuba na Laila a kwanon silver, na zuba ma Toye nashi. Wani ?aramin kwano na jawo a ?asan gado, ragowar manjan miya ne a ciki nama mance dashi na tsiyayama Laila da Toye ragowar na ajjiye a gaban uwani danta soma cin abincinta ma gaya abunta. Falo na fita da zummar in ba Laila abincinta na tarar bata cikin falon. Ajjiye mata nayi a inda na barta. Na jawo hannun Toye yanata wasanshi muka shiga ciki na zaunar dashi. Kabbarar Sallah nayi. Ina cikin sallah muka jiyo sallamar namiji. Uwani ce ta fita dan dubawa. Sai da na idar sai gata da leda mai zane, da kuma ba?ar leda da kuWi dubu biyu.
"Sa?one Gwadabe ya aiko miki. Gwadabe akwaishi da ?o?ari akan komai ma, gaskiya ki sake gode ma Allah. Gwadabe ya ri?e miki amanar ?aunarki. Iyabo kar ki kuskura wannan mai idanu a tsakar kan ta rabaki da mijinki."
Tabalbalin sai na dage da tsaiwar dare. Domin tsorona bansan da wanne irin shiri tazo ba. Nasan kyanta, ko farinta, da kyan durinta bazai taSar ruWar Gwadabe ba. Na yarda da irin son da yake yi mun. Kuma na yarda yana ganin kyauna a hakan da nake, ko babu komai yakan yabeni ya kurantani. Kuma yasan da'itan ya tsallaketa ya auroni. Ni dai da sallar dare zan dage kar su je su nemar mun miji ta hanyar asiri. Uwani ina cikin damuwa sosai wallahi. Ke dai mu ci abinci kinji.
Muna hirarmu muna cin abinci, anan na ba uwani labarin abinda ya faru a cikin gidannan ranar da zamu je Takai, da kuWin hayar da zamu soma biya. Uwani tayi mamaki ainun ta jinjina irin ?iyayyar da dangin Gwadabe suke yi mun. Sai bayan la'asar Uwani ta shiga haramar tafiya. Shinkafa da taliya, da kayan miya, da Wanyen kifi, manja, maggin da Gwadabe ya aiko yaro ya kawo duk sai dana Wibar mata, na bata Wari biyar. Bata tafi ba sai da ta Woramun miyar tumatur a gawayi, da kanta ta le?a ta kai mun ni?an ma?ota. Sai da na rufe uwar Wakina sannan na rakota. Mun fito mun samu Laila tana cin gurasa da lemun koka kola, abincin dana ajjiye mata kuma ta tureshi gefe guda, ?ar ?aramar rediyo ta kunna tana jin wa?at barmani choje, wa?ar gwarne ikon Allah. Tana yi tana karkaWa kafaWarta. Wucewa muka yi jiki duk a sanyaye. A sanyaye mu kai sallama da Uwani tana sake jan kunnena kar in kuskura in bar gidana sabida wata. Ko dana dawo ban shiga falon ba, a tsakar gida na zauna ina tsintar shinkafa ina sha?ar iskar ?anci. Dan da masu gidan na nan, da ananan ana zubar mun da habaici, gami da maganganun cin fuska marasa daWin saurare. A ta?aice dai ko dana gama girkin dare na sake zuba ma Laila a wajen ta sake bar mun. Ta fita ta siyo tea da biredi. Ni ko tunda na janye yarona na shige ciki nasa sakata, ban sake sanin halin da Laila take ciki ba.
Misalin ?arfe goman dare sai ga kiran Gwadabe ya shigo wayata. Cike da zumuWi da kewa na Wauka. Daman a zaune nake dan tunda cikina ya tsufa ban fiye samun baccin dare ba. Allah sarki Gwadabe da yana nan da yanzu yana matsa mun ?afafuna.
Amincin Allah ya tabbata a gareka gwarzon gwaraza. Barka da hanya, da fatan kana cikin aminci?"
Murmushi yayi mun yace.
"Barka sa dare sarauniyar zuchiyar Gwadabe, da fatan kina cikin Wakinki na sunna cikin aminci ko?" Farin ciki ne ya lulluSeni bansan sanda na lumshe idanuna ba.
Ina lafiya, sai kewarka dake nu?ur?usar zuchiyata. Ya hanya fa?"
"Ba daWi hanya. Kin ganmu a Tafa mun tsaya cin abinci da Sallah. Shine nace bari in ji lafiyarki. Ina Toye?"
Gashi nan yayi bacci.
"To masha Allah babu dai wata matsala da Laila ta baki ko?" Baki na taSe kafin nace.
Babu wata matsala a halin yanzu. Amman abincin rana dana dare dana bata duk bata ci ba. Fita tayi ta sai abunda ranta yake so" FaWa ya soma yi akan karma in ?ara saka mata abincin in nayi tunda abun iskanci ne. Ni dai nace.
Ba za'ayi haka ba. Ai da duk take_takenta so take in ?i zuba mata a kafa mun hujjar na hanata abinci ita da gidan Wan uwanta. Kai dai ka yi tunanin nemo mana mafita kawai. Dan wallahi Allah bazan zauna da gansamemiyar bazawara kamar Laila ba." Dariya Gwadabe ya dinga yi mun yana tsokanata kan na fiye kishi. Nima da dariyar na bishi kawai. A haka mu kai sallama dashi. Bacci bai zo ma idanuna ba, ?arfe sha Wayan dare na Waura alwala a cikin bahun babba. Na raba dare ina neman tsarin Allah ga dukkan masu son cutar dani da mijina, da masu son ganin bayan auren. Na ro?i Allah yai mun katangar ?arfe da Laila ya karemu da dukkan sharrin data kwaso. Gwadabe kuwa alkhairi duniya dana lahira na ro?ar mishi. Sai zaman lafiya, da jin daWi wanda bana gajiyawa wajen sake ro?a mana, kusan duk addu'o'in maimaicine ba dare ba rana. Sai dai yau na ?arama adda'ar tsawo da wasu salon ro?on. Sai wajajen jefin assalatu bacci ya kwasheni ina daga zaune. Amman ana kiran sallar farko na buWe idanuna. Yin?urawa nayi na tashi na buWe ?ofata na fito da bahun Wina na fice. Laila na saman doguwar kujera tana bacci saye da wandon bacci iyakarshi guiwa, rigar wandan mai shara_ shara ne har kan mamanta ina iya ganowa. Gabana ya doka da ?arfi, kifiyar kishi ta soki tsokar jikina. Kai kawai na girgiza domin nasan tabbas dama a rina. Laila da kyan sufa da launin fata take son Jaye Gwadabe daga gareni. Dan tana da kyau tubarkalla masha Allah. Kuma ko a ?auyen ita idanta a buWe yake tar. Fita nayi na kama ruwa, na Waura alwala na koma Wakin. Dai _dai da farkawar Laila tana tsaye tana mi?a. Na ?arema wandon baccinta kallo shima shara_sharenne ina hango zaratan cinyoyinta farare luwai_luwai dasu.
Ya kamata ki sani cewar nan Wakin matar wanki ce, ba Wakin aurenki ba. Wannan shigar a Wakin mijinki kaWai ya dace ki yita ba anan ba. Zan iya lamuntar komai, banda shigar banza mai nuna tsaraici, ki kiyaye sosai"
Hararata Laila tayi tare da yin shewa tace.
"Ashe ana tsoron iya inji ?a?an maiya. Babu rami me ya kawo rami Iyabo? Ashema baki yarda da nagartarki ba a matsayinki na mace ba."
Murmushi nayi mata kawai domin bani da lokacin misayar yawu da'ita.
Bayan na idar da sallah na yi azkar da adda'a, na jima sosai ina tunanin yanda ?arshen zaman Laila a cikin Wakina zai kasance. Ta yaya, kuma ya za'ayi tabar Wakinnan alhalin Babalace ta bata umarnin zama, kuma dani da Gwadabe duk a ?ar?ashin ikonta muke. Wata zuchiyar tace.
"Ai matsawar ba barin gidan kikayi ba Iyabo. To tabbas Laila babu inda zata fita


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login