Showing 63001 words to 66000 words out of 270738 words

Chapter 22 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

rashin iya zaman rugarnan kuma. Zan iya ko dan Dada, da ?annena. Bana jin komai na dangane da kewar birni, ko ?yale_?yalen dake cikinta. Ni babu abinda a halin yanzu yake burgeni. Nafi samun nutsuwa a haka" Ashe ni na kasheshi da namaki ban sani ba. Sai da na juyo naga bakinshi a hangame yana kallona, da halama ya Wan jima yana kallon nawa
"Saudiyya fa kika ce zaki je neman kuWi Iyabo?" Ya faWa a ?agauce da son jin amsata.
E Saudiyya da izinin Allah, Lokaci kawai zamu jira."
" Da izinin wa zaki tafi Iyabo, me yasa Kano bata isheki neman kuWi ba har sai kin dangana da ?asa mai tsarki, sannan me yasa baki yi tunanin Aure, ko komawa makaranta wanda nasan yana daga cikin burukanki na rrayuwa ba?" Ya sake jejjero mun wannan tambayoyi cikin Sacin rai a wannan karon. Baki na tsuke bance mishi komai ba. Tsawa ya daka mun wacce tasa ?an hanjina kaWawa.
"Ba dake nake yi ba kin mun banza ba?"
To ni kam Burodami me zance maka? A halin yanzu babu wani karatu, ko aure a gabana. Rayuwar mahaifiyata kawai nake dubawa, da mafarkin samar mata da sau?in rayuwa. Ka dai taya ni da adda'a zaifi. Dan babu makawa zanyi tafiyarnan. In kaga banje ba Allah ne baiyi ba. Kayi ha?uri kar kace na bijire maka"
Sai yayi shiru na wasu da?i?u kana yace.
"Amman ba kya ganin in kika tsallake ?asarki Najeriya, kika tafi wata ?asar neman kudi. Ba kya ganin wasu zasu yi miki kallon da bai dace ba? Ballantana kinga ke bazawarace kina da ?a?a. Acan kuma baki san hannun waWanda zaki faWa ba"
Hannu na gari zan faWa da izinin Allah. Kuma wama zai san na tafi Burodami Debisi?. Kaga Dada tana cikin halin da ya kamata a taimaka mata. Kuma ni bazan wuce shekara uku ba zan dawo. Kafin in dawo amman sai na tabbatar da na samu dukkan abunda naje nema." Ajjiyar zuchiya ya sauke, yayi shiru yana kallona, ni kuma nayi ?asa da kaina.
"To batun aurenmu sai kin dawo za'ayi kenan. Ko kuwa zaki amince a Waura kafin ki tafi? Dan ni harna sanarma Baffa Musa sababin zuwan nawa. Yayi murna matu?a da jin hakan" Wani kallo nayi mishi, wanda ko a mafarki banyi tunanin akwai ranar da zata zo da zan yi mishi wannan kallo ba.
Aure a tsakaninnu babu shi har gaba da abada. Har gobe nice Iyabo mai ?ibarnan, wannan wacce sai da ka kwanta jinyar ?iyayyarta. In ma mafarki kake yi ka farka" Ina dasa aya sai kawai na mi?e hawaye fal Idanuna. Takalmaa nake shirin sawa yayi maza ya mi?e shina.
"Iyabo"
Ya kirani da sauri. Cak na tsaya. Ban tafi ba, ban kuma juyo ba. Ina jiyo takunshi har izuwa daf dani.
"Nasan kina sona Iyabo kar ki soma yaudarar zuchiyarki. A rashinane kika auri Gwadabe. Iyabo zan baki farin ciki irin wanda mafarki da hasashe ba zasu iya hasko miki ba. Duk duniya ba wanda zai soki sama dani, sai dai ya biyo bayana." Hawayena na share, tare da lumshe idanuna, zuchiyata kuwa sai aikin turiri take. Da ?yar na haWiyi miyau nace.
Iyabonnance dai wannan mai ?ibar da ka?i aurenta sabida wannan halitta tata. Ba canjawa nayi ba. Duk da nasan na zabge rabi da kwatan ?ibata, a sanadiyyar halin yau da gobe Ka sani kibata zata iya nunkuwa da kaso sama da hamsin akan na da wanda ka guje ni dominta. Debisi ina mugun girmamaka ne ma yasa harna tsaya saurarenka. Amman da ba dan haka ba ko kusa dani baka isa kazo ba. Maganar soyayya ko aure babu ita, dalilin da yasa ka barni ina budurwa. Dalilin ne dai yasa na barka bayan na zama bazawara" Ina dasa aya nayi shigewata cikin gidan. Duk a tsakar gida na tarar dasu, amman banda Daso.
"Adda Jabu Yaya Debisi ya kawo miki wata ?atuwar leda, tana wajen Adda Daso. Muma duk yayo mana tsaraba mai yawa" ?an murmushi na ?a?aro nace.
Ayya. Ai Burodami Debisi ba daga nan ba ta wajen kyauta. BoWWo ku taso muje gidanki, dan acan nake son mu tattauna kamar yadda na faWa miki ina da Magana da zamu tattauna daku. Ina zuwa bari in samu Daso in sanar mata" A cikin bukkarmu na sameta tayi tagumi sai aikin tunani take faman yi, dan bata san ma na shigo ba har sai da nazo daf da'ita. Ta Wago fararen idanunta ta zuba mun su. Akwai damuwa sosai a tattare da'ita, wanda a tunanina baya rasa nasaba da kewar tsohon mijinta marigayi.
Daso wai me ke damunki ne, ni tunda na dawo na ganki wani sukuku. Ko duk rashin lafiyar Dada ne?" Na jefeta da tambaya, tare da kafeta da idanu domin karantar yanayinta.
"Ba komai abubbuwane sukai ma zuchiyata nauyi Jabu. Amman zamu tattauna zuwa dare" kai na gyaWa mata kawai.
To ni zanje gidan ?oWWo akwai maganar da zamu yi dasu duka" Kur ta mun da idanunta kamar mai karantar wani abun a fuskata, sai kuma ta ja numfashi tace.
"Bari in zo muje, inaso dama inje wajen Hama, in yaso in kun gana tattaunawar sai ki same ni a Wakinta"
Hakan ko akayi, a hanya ne take labartamun Debisi ya kawo mun wata ?atuwar leda, ta adana mun ita. Ni dai kai kawai na gyaWa. Mun ci tafiya sosai kafin muka iso gidan. Matan gidan duk suna tsakar gida anata tuwon dare, wasu kuma suna wanke ?oren tallar nononsu, Yafendnmu bata nan bata dawo daga can gidan Baffa Musa ba. Daso ta ya da burki a ?ofar bukkar Hama, tana zaune tana tu?in tuwon masara, masararnan fara tas gwanin ban sha'awa. Da dariya da haba_haba muka kaisa da Hama kafin muka shige bukkar BoWWo. Bayan kowa ya nemi waje ya zauna, sai na yi gyaran murya na soma da cewa."
Dukkanku kun fini sanin irin halin da Dada take ciki a gidan aurenta. Da irin matsalolin duka, da tsangwamar da Baffa yake yi mata. Ku yi ha?uri Baffa mahaifinku ne, amman nasan ku kan ku kunsan yana zaluntar Dada. A shekaru irin na Dada ai yaci ace ko da an daketa a baya, a yanzu a barta ta huta ko dan kaifin idanunku. Ga yawon talla, duk rauni da da gajiyar dake jikinta tana talle. Amman anan naga ku kamar talla wani abune na dole." BoWWo ta tari numfashina da cewa.
"Talla tana cikin sharaWin aurenmu mu kam. Domin da kuWin nononnan zaki Wauke nauyin ci da sha na gidanki, harma ki yi ma kan ki sutura da dukkan bu?atu. Su kuma maza aka barsu da kiwo. Sai dai wasu matanma suna fita kiwon su dawo lafiya. Dukan da Baffa yake ma Dada ni shine damuwata. Anan Wakin mun sha zama domin tattauna wannan matsalar, rashin mafita ke sa mu yi ha?uri kawai. Amman zukatanmu na sosuwa ainun, hakan ya zabtare kima da darajar Baffa ta Uba a garemu. Domin mun fi son Dada sama dashi sai dubu babu haWi"
To ni dai ina da shawara, so nake zan tafi saudiyya neman kuWi. In na tara kuWi zan dawo, inaso Baffa ya saki Dada ne kawai. Ni kuma zan Wauketa harda su Yusufu in sai mata gid, ta zauna ta ci moriyar haihuwa ko wanke_wanke ni zan dinga yi mata ko da nayi aure. Amman meye shawararku kune ?an uwana?" BoWWo tace.
"Da hakan zai faru wallahi Adda sai mun fi kowa farin cikin faruwar hakan. Ni da Amaduyal mu muka san irin wuya da dukan da Baffa ya dinga yi ma Dada. Har Waureta yake yi a jikin gadonta ya daketa ciki da waje." Anan suka sake fayyace mun halin da Dada take ciki a gidan aurenta. Kuma duk suka bani haWin kai akan suma sun amince a saki Dada. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, duk yawan shanayen Dada dake hannun Baffa bazai yarda ya bayar ba. Ni kuma a wannan lokacin sakin kawai nake bu?ata ba shanayen banza ba. Sai da mu kai sallar isha a gidan. A Wakin Yafendo muka haWu mu ka ci abinci anata hira, maza kuma suna waje suna shan iska.
"Cubu je ki kira Hamma a waje ya raka su Daso guda, kuma sai ku kama hanya tunda ga Yusufu sai yai muku jagora" fitar Cubu ke da wuya sai gata Yaya Hamma na biye da'ita.
"Dada gani" Ya faWa da murya mai kauri. Yarinyarshi dake hannun uwarshi sai Waga mishi hannayenta take yi halamar ya dauketa Hama ta mi?a mishi yarinyar ya ratayeta a kafaWarshi.
"Su Daso zaka raka gida tunda dare yayi ." ?an murmushi yayi kawai kafin yace.
"To Dada su sameni a waje sai mu je. " A tsaye ya Wan yi ma ?ar tashi wasa ya mi?a ta hannun uwarta ya fita. Muma mu kai ma Yafendo sallama muka fito, suma su Yusufu suka nufi hanyar komawa gida.
Shiru_shiru mukaita tafiyar. Duk cikin mu ukun kowa da abinda ke azalzalar zuchiyarshi. Abun mamaki har muka isa gida ba wanda yayi ko tari.
A ?ofar gidan muka haWu da Jatau da Burodami Debisi sun kafa sun tsare suna jiranmu.
"" ?ar halak ta ?i ambato ka ganta ma. Jabu mun fi mintu talatin muna jiranki anan wajen" Hannu Yaya Hamma ya mi?a musu suka gaggaisa, sai naga ya kuma haWe ranshi. Ni da Daso dai muna tsaye, Allah cikin ikonshi sai ga Manga shima ya tawo taWi shi da abokinshi. Yaya Hamma ne yai ma Daso jan ido ta je wajensu.
"Jabu ki je ki saurareshi, ni zan jiraki a wancan wajen itaciyar, inason mu yi magana ne" Yaya Hamma ya faWa a sanyaye.
To Yaya Hamma" Iyakar abinda na faWa kenan. Burodami Debisi yaima Hamma godiya, ni dai na bi bayanshi dai muka matsa gefe haka.
MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI CE


Ina mi?a sa?on gaisuwa ga masoyana.
Sister Khadija maidoki ina godiya.
NAMA YA DAHU..
ROMO ?ANYE
LITTAFI NA BIYU




2


*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*










"Gimbiya Iyabo sai wahalar da zuchiyata sonki yake ta yi. Ni na Wauka dake zan koma Kano a matsayin matata fa, ashe abun ba haka bane. Ki tausayama masoyinki ki tsamoni daga cikin halin da kika sanyani, kaina bisa wuya, banda tuno baya. Kuma nayi imanin su Iyaa da Burodami kokodeen zasu yi alfahari da aurenmu Iyabo "
Duk wannan maganar yana yinta ne cikin kyakkyawan lafazi mai taushi. Maganganunshi babu inda basa ratsawa a jikina. Sai dai kash ya makaro, dan banga abinda zai iya cemun in yarda dashi ba.
Ina Mai baka hakuri ka fitar dani a zuchiyarka dan Allah. Nayi imanin a rashin samun yadda kake so a wajen matarka soja ne yasa kake son ni ka aureni" Da sauri ya fuskanceni sosai cikin kidima yace.
"Wallahi bazan iya ba. Baki san irin azabtuwar da ruhina da gangar jikina suke yi bane shi yasa. Ki dena tunanin dan ban samu yadda nake so a wajen Yemisi bane na dawo gareki. Iyabo ina sonki"
?an guntun murmushine ya sufce mun ba tare da na shirya ma hakan ba.
Zaka iya, tunda har na iya cire sonka a zuchiyata. Na rungumi soyayyar Gwadabe har kuma ya samu matsayin da babu wani Wa namiji da zan iya bashi wannan matsayin. Kaga kuwa zaka iya, dan a baya sonka ya rufe mun idanu ta yadda bana ji bana gani. Ido da addini ka?i fur a haWa mu aure. Kaje ka auri sojar matarka siririya irin samburin matan da suke burgeka. Na ro?eka ka barni in auri namijin da yasan darajar ?iba irin Gwadabe. Wanda zai dinga kammamani yana kuranta kyauna"
Baki na tsuke nayi kicin_kicin. Daya isheni ma da magiya sai kawai na fashe mishi da kuka. Da ?yar ya rarrasheni nayi shiru.
"Shikenan Iyabo, zan sake baki lokaci. Ni gobe zan koma asubanci zanyi. Amman fa ki sani zan jiraki kije ki dawo sai muyi auren"
Allah ya tsare ka gaishe mun da kowa da kowa. Banda matarka Yemisi, dan nayi imani batasan wajena ka tawo ba" Bai iya ce mun komai ba na yi tafiyata na barshi a wajen. Yaya Hamma kuma yana daga can gefe can gaba da inda su Daso suke tsaye. Dole ta gabansu zan wuce, hakan yasa saida na tsaya aka gaggaisa kana na Isa wajen Yaya Hamma Daso ta bini da idanu kawai. Zama nayi a gefen itacen da yake zaune, muka ?urama juna idanu ?ur kamar zamu haWiye junanmu. Idanunshi jawur harda kwantaccen hawaye marar yawa a cikin idanun nashi. Lumshe idanu yayi, yaja wani numfashi marar fassara a gareni, yai amfani da murya mai salon taushi da sanyi tarara wajen cewa.
"Me yasaki kuka, kuma me Debisi yake nema a wajenki ne Jabu, na fahimci akwai babban sababin daya kawoshi rugarnan?" ?ireni da idanu yayi.
Nima ajjiyar zuchiyar na sauke. Na fayyace mishi ?udurin Burodami Debisi a kaina. Na tsokata mishi Wan labari akan cewar iyaye a baya sun haWamu aure amman sai ya nuna baya ra'ayina. Amman na Soye mishi dalilin shi na ?in nawa. Murmushi naga yayi har yanayin fuskarshi sai da ta sake. Gyara zama yayi yace.
"To cika mun al?awarina da kika Waukarmun akan kina dawowa zaki sanar dani dalilin zuwanki birni"
Dariya na kwashe dashi, shima dariyar yake yi. Kwashe labari nayi na bashi. Da kuma dalilin da yasa zan tafi Win. Tashi Waya ya birkice har yana tsugunnawa akan guiwowinsa a gabana. Idanunshi suka cika fal da hawayen da suka kasa gangarowa.
"Na ro?eki kar ki tafi Jabu ki barni. Shekara uku ban saki a idanuna ba, ai abune wanda ka iya kwantar dani. Ni zan siyar da saniyata in baki kudin a hannunki ki siya ma Dada gida, kiyi sana'arki da sauran kuWin ki yi haquri ki janye wannan tafiyar dake shirin rabamu. In kuma ni kike so in mata duk abinda kike so a shirye nake. Yafendo uwatace, ina jin motsin sonta da tausayinta a raina. Jabu na ro?e?i kar kiyi nisa damu, rayuka da yawane zasu jikkata"
Mamaki ya kamani, to me Yaya Hamma yake nufi da wadannan kalami nashi? Ni ba yarinya bace na lura sarai tun zuwana yana ra'ayina. Amman ban tabbatarba sai jiya dana ga kishin Debisi ?arara a idanunshi. Wannan kalamai nashi na yanzu sun ?ara tabbatarmun Yaya Hamma rainon sona yake yi. Kuma na fahimci Daso na tsantsar sonshi, Yafendo ma ta sani kuma tana fatan faruwar hakan. A duk sanda Yaya Hamma zai zo gida, sai Yafendona ta ala?anta zuwan da Daso. Gashi matarshi ?awarmu ce, mutuniyar kirki ma??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i son jama'a.
Kayi ha?uri ka tashi dan Allah yaya Hamma mu yi magana ta fahimta dan Allah " A tsugunne a gabana Daso ta iso ta sameshi. Numfashi ta ja tare da saurin yin turus, ganinta ne yasa ya tashi ya zauna.
"Ki shiga gida Daso, ban gama magana da'ita ba. In muka gama zan rakota, ina bu?atarta tare dani"
Fuu ta wuce har tana haWawa da gudu. Tausayinta ya kamani, dan babu son da ya kai son maso wani ciwo, zafi ne dashi kamar zafin fitar rai daga gangar jiki.
Mun fi awa Waya da rabi muna tababa tsakanina da yaya Hamma akan tafiyata. Bamu cimma matsaya ba Baffa ya fito ya korani ciki dan gaskiya dare yayi har ?afa ta Wauke magiya kawai Yaya Hamma yake yi tare da tambayata shanu nawa zai siyar ya bani kuWin.
Ko da na shiga bukkarmu a zaune ?i?am na samu Daso ta kurama aci bal_bal idanunta. Ledar gabanta ta turo gabana ina tsaye.
"Ga sa?onki na wajen Wan uwanki" Murya ba daWi ta yi maganar. Ledar na Wauka na zauna. A hankali na zazzaro kayan dake ciki. Kayan tea na gani, da macline da brosh, sai mayafai biyu, takalmi biyu da atampa Waya leshi Waya, sai zungureriyar wasi?ar da bani da niyyar karantawa. Biyu na raba kayannan cib na ba Daso, kayan tea Win kuma na ajjiye mana.
"Ki ri?e abunki ni bana so"
Wai Daso na yi miki laifine kike fushi dani. In akwai matsala ki sanar mun mana?" Na jefeta da tambayar ina Waga murya dan ta mugun Sata mun raina ainun.
"Hmmm"
Shine iyakar abinda tace dani. Kayana na kwashe na mayar ko da na Wane gado na kwanta Amman me? Sai bacci yace bani bashi. Tunanin Dada ya cakuWe mun da tunanin furucin Yaya Hamma na Wazu, da irin yanda duk ya kiWime. Hasko mun da hoton Gwadabe da zuchiyata tayi sai hawaye ya soma tsiyayomun masu zafin gaske. Babala ta zalunci zukatanmu data ?i amincewa mu rayu a tare. Nasan duk inda Gwadabe yake kuwa yana can zuchiyarshi a batse da kewata. A tsakanin ni da Daso babu wanda ya runta
Washe gari sassafe ni da Hari muka gama duk aikin gida. Ina gama karyawa nai ma Yafendo sallamar ni zani gidan Baffa Musa.
Acan na tarar mijin Dada yazo Waukarta, kuma abun haushin harta fito daga Waki ma suna tsakar gida. Da ?yar na danne zuchiyata na bashi girmanshi albarkacin uwata da yake aure. Shi kuwa banza ya ba ajiyata, in kun tanka ya tanka. Har a kan fuskar Dada banga tayi farin cikin zuwan mijinta ba, fuskarta ma cike take da tsoro. Amman haka ya tusata a gaba suka tafi, ni ko da kuka na fice a gidan na dawo gida. Na tarar da su Yafendo sai dafa madara suke yi, taga na shigo da kuka kamar karamar yarinya dai.
"Jabu lafiya kaddai Adda Daso mutuwa tayi?" Ganin yanda duk suka ruWe suka yo kaina yasa na yi musu bayanin dalilin kukana. Yafendo da Hari ne su kaita rarrashina dai haka.
Gaga_gaga haka rayuwa tai ta tafiya. Ko wacce rana kafin faWuwarta sai hawayena ya zuba. Dada jikinta ya warware har ta soma fita tallar Nono. Sabida tsananin tausayinta yasa nake binta wajen sana'ar nonon nata. Sai tayi zamanta a gefen rumfa. Ni kuma ni zan zuba Nono in kai, in je in kwaso ?worena. Munayin hakan ina


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login