Showing 117001 words to 120000 words out of 270738 words

Chapter 40 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

ma lokaci yayi @ zee Musa collection taxo muku da hanya Mai sauki domin ga number =???=???=???08029882667 =؃??#? samun damar mallakar duk abunda kakyeeda bukata. Cikin sauki ta hanyi Yi muku adashin gata =؃??#? idan matsalarki rashin sabbin plates Akwai
1, zubi duk sati 2k sati 10 kwasar kayan 20k =؃? Akwai zubi duk sati 2k sati 20 kwasar kayan 40k har zuwa duk yanda mutum yakyee bukata zamu turo maka da kayanmu idan lokacin kwasarka yayi da yarda Allah kazabi duk abunda kakyee bukata da yarda Allah to mekakyee kikyee jira ki tintibene domin jin yarda raguwar tsarukan sukyee insha Allah idan Kuma kyee ma,aikaciyace to kyeemafa =؃? Akwai kayan Yara yankanti
Akwai takalman da jakunkuna da mayafai
Da sauran kayan amfani kyeedai maxa ki hanzarta kafin mu Fara zubi
Insha Allah zamu Fara zubi a farkon( sabon watan August ) Allah yadafa mana nagodee sossai zee Musa takuce =؃??p? ga number din da zaa iya damuna =؃??#?=???=??? 08029882667




IYABO:.
Lalubo lambar Yaya Hamma nayi a wayar Faty na danna kira. Nan take zuchiyata ta shiga harbawa fafafat, ina jiyo motsin sonshi a zuchiyata. ( M Farida Ana magana )Sau uku ina gwadawa number bata ma shiga, kamar ma layin a ?asa yake baya cikin waya. haka dole na ha?ura, na bari zuwa wayewar gari, in sake jarabawa ko Allah zaisa in dace.
Bacci a ranar lafiyayye muka samu mai nutsuwa. Bayan munyi sallar asuba ma bacci muka sake komawa ba mu muka tashi daga baccinnan ba sai azahar, ni dai akwai gajiya marar adadi tattare dani, haka ma Uwani. Faty kuma dama ita Wabi'ar baccinta kenan. Alwala muka Wauro bayan duk munyi wanka. Kayan jikinmu muka mayar dan kayanmu na cikin mots ba'a sakko dashi ba.
Ina sallah Salim ya shigo, abinci ya kawo mana da burosai na goge baki da makilin. Kafin in idar ya fice. Ina idarwa ya sake shigowa da wata zungureriyar leda sha?e da dogayen riguna da takalma harda agogo, da tarkacen kayan kwalliyan mata harda turare. Ya mi?o mini, nasa hannu na karSa ina mai mishi godiya. Sai cewa yayi dani da harshen larabci.
"Ki shirya zan gabatar dake a wajen dangina. Kakata ma tana nan sai su ganki" Na dubeshi, sai yayi mun murmushi.
"Tuni labarinki duk ya karaWe familyna. Na faWa miki sonki nake yi da aure ba da shashsnci ba. Tun rabuwar dake zuchiyata bata huta ba wajen begenki da mafarkin mallakarki" Ya sake faWa. sai na gyaWa kaina nace mishi.
I am coming ( ina zuwa) shiga uwar Waki nayi na tarar da Faty tana waya. Uwani a falo na barota.
Faty wai ashe da gaske salim yake yi aurena yake so yayi? Kinga fa kaya ya bani wai in saka mu sauka ?asa zamu gaisa da iyayenshi. Sai ta zare wayar a kunnenta tace.
"Kwarai kuwa. Komai a rayuwa yana da sanadinshi. Da kina Najeriya babu dalilin da zaisa ku haWu da Salim har ya soki, tunda baisan hanyar Najeriya ba."
Faty akwai Matsala ne akwai Wan uwana da mu kai al?awai dashi kafin in baro ?asata" BuWar bakin Uwani wacce shigowarta kenan sai tace.
"Akwai dai wanda kika Wafa sonshi a ranki dai banza. Yanzu haka yama mance dake. Babu mamaki in mutumin ?auyene kije ki iskeshi da mata huWu ma, kinga babu wajen zamanki a gidanshi ai. Yanzu kamar wannan bawan Allah yaji sonki kina neman kisa ?afa kiyi fatali da damarki. Wai Iyabo a ?auyen ?ayayau Winnan kike so kiyi rayuwa, kina Waukar tallar nono aka? Ke sha'awar rayuwar kenan kike yi. Koko sabida fari, gashi da tsawon Hamma ke ruWarki? Duk da dai nasan ba hakan bane tunda Salim ya kere Hamma a komai. Amman dai Iyabo Allah ya wadaran wannan zuchiyar taki ta gaban ?irjinki" Ta ?arashe zancan ta tana hararata
Turus nayi ina kallo da sauraren Uwani da take ta balbalin faWa kamar Uwata. Faty ce ta katse hirar da cewa.
"Yanzu dai ki shirya kije ki dawo mayi magana. Uwani mu karya kafin ta dawo"
Ni dai a tsorace du nake. Doguwar ba?ar riga na saka mai shegen kyau, da takalmina ba?i mai tsini, na yane kaina da mayafin rigar tare da feshe jikina da wani turare mai ruwa ja. A tsaye a inda na barshi na sameshi. Ba sai mutuminku ya nemi lalacewa dan kallona ba. Ni kuma sai kunya ta kamani a raina sai nake ayyana.
Wannan kallo da yake yi mun kallon yaudarace kawai, su da suke da haske da kyau, matansu Allah ya basu diri da cikar ?irji. To ni meye a jikina na kallo da har za'a shagala in ba Saka_Sakan mazaunai ba?
Ashe shi yasan dalilin, tare da larabawa masu auren Sa?a?en fata, da turawa masu auren ba?a?e su bar kyawawan fararen matansu. Haka muka gangara a jere muka tadda ahalin gidan a daining table babba suna cin abinci. Da ganina wata tsohuwa ta iso inda muke ta ri?o hannuna har gaban daining Win. Zaunar dani tayi a kujerar kusa da wani tsoho. Shima Salim ya samu waje ya zauna.
Jikina yana Sari na gaishesu da larabcina irin nami na ?an koyo. Da soyayya gami da fara a suka amsa mun.
Ya dinga nuna mun ?an uwanshi, yayye da ?annenshi. Ga mahaifiyarshi da mahaifinshi, sai kakarshi da mijinta, sai kuma Yarshi Sarla da mijinta Umaid. Ni dai duk ina zaune a mugun takure, su kuma sai jana da hira suke yi. Mahaifiyarshi ta tambayeni asalina.
Ban Soye mata komai ba kama daga yarena, izuwa aure da nayi a baya da adadin yarana.
Duk da haka sun yi na'am dani. Abu guda dana fahimta da larabawa ko basason abu. Muddin yaransu ya nuna Yana so, to suma zasu koyi son wannan abun. Suna da son yara, su kuma yaran sai suke Amfani da hakan wajen tursasama iyayen son ra'ayinsu da yarda dashi.
Gurasa da nono aka zuba mun sai shayi, a kunyace na Wan cakala Salim yace in tashi ya mayar dani. Sai mahaifiyarshi tace ba za'a yi haka ba. Ya Waukemu daga Wakinshi ya dawo damu wani Waki dake kusa da nata, Wakin ?anwarshi dake karatu a landan. Haka kuwa akayi, Wakin yafi nashi kyau da kuma yalwa.
"Ku shirya zuwa dare sai mu fita daku kuyi siyayya, ku ga gari kuma." Cewar Salim bayan mun samu keSewa nake sanar mishi ni Najeriya muke son komawa, zaman bautar da muke yi ya ishemu. Anan yai mana al?awarin zaiyi mana cuku_cukun visar da zamu koma, zaima biya mana, amman in mishi al?awarin zan bashi damar kafa soyayyarshi a zuchiyata dan shi da gaske aurena yake son yi.
Tuni na amince mishi da hakan magana ta domin Allah ba har cikin zuchiyata ba amma.
Da daddare ya fita damu zuwa wani super maket babban gaske na suturu masu tsada da masu arha duk gasu nan. Mu ka dai tsittsinci abinda ba a rasa ba haka. Ya biya komai muka sake nausawa zuwa zagayen cikin gari.
Ni dai banyi ?umun b????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
aki ba nace mishi ni kam inason yin Umara. Ranar juma'a yai al?awarin zai kaimu da izinin Allah. Ai kuwa hakan akayi. Daga umara muka shiga kasuwar DOGON GIDA dake Makka. Anan muka ga dandazon maza da mata na Najeriya iri iri. Ga gumama a zube a ?asa, ga sababbi, zannuwan gadone, takalma. Komai da komai dai.
Nan Faty ta dinga kutsawa damu. Siyan kaya muka dingayi. Ni da Uwani mune harda ma?ala ha?ori makka bibiyu a bakunanmu.
Adai ta?aice mun kaso kuWi masu yawa, daga haka muka koma Jidda, nanma suna da babbar kasuwa Faty ta kaimu, ni har dilar zanin gado, da kayan mata dogayen riguna da takalma na siya za a Wauro mun a jirgin kaya. ?angaren kayan kitchen hatta plate da cokali saida na siya, na sai manyan kuloli kala biyu, masu filas na shayi. Uwani kuma dila biyu na zannuwan gado da dilar Kayan sawan yara ta siya. Daddumai, da carbi, bagaruwa, dabino, ruwan zamzam kuwa sunfi komai yawa a tsarabarmu. Naima Dada tata tsarabar, naima Iyaa Debisi nata daban, naima Yaya Hamma nashi daban shima. Su BoWWo kuma saina isa Najeriya zansan mai Zan cire musu dai, ragowar kuWaWen muka canjasu zuwa kuWinmu na Najeriya.. Duk wannan siye_siyen da taimakon Salim, da taimakon mahaifiyarshi danta bani kuWi a gaskiya masu kauri. Suna da wani irin karamcin da a Wan kwanakinmu a gidan Salim harya soma samun gurbin zama a zuchiyata. Kwananmu takwas a gidansu Salim Allah ya kawo lokacin dawowarmu Najeriya, mahaifiyarshi da danginshi su kai mana goma sha tara na arziki, har zoben gwal yarshi Sarla ta bani Wan ?arami na ma?alashi a hannuna. Duk tarin kayayyakinmu mun Waure zasu tawo a jirgin kaya wanda akace bazai wuce wata Waya ba zai iso. Sai ?an akwati da jakunnanan kaya, da jakar hannu kawai muka ri?e. Har filin jirgi Faty ta rakamu, Salim shima yana wajen tare da Yarshi. Sai sake jaddadamun yake yi akan in ri?e mishi al?awari, sannan zai biyo adireshin gidanmu na Kano dana bashi yazo a kawoshi har ?auyanmu nanda sati biyu in ya rage abubbuwan dake gabanshi. Sarla itama sai sake ro?ona take yi akan kar in yaudaran mata Wan uwanta. Zai zo da kanshi neman aurena. Ni dai duk sai jikina yayi sanyi tuSis, har na soma kokonton wanda zan Wauka da wanda zan ajjiye. ( To masu karatu wannan zaSi ayi daku. Ku wa kuke ganin ya cancanta Iyabo ta Wauka Hamma ko Salim?)
"To Faty Allah ya sada fuskokinmu da Alkhairi. Zamu dinga waya in sha Allah.
Da haka mu kai sallama da juna. Muna hawayen farin cikin komawarmu ?asarmu Najeriya. Faty tana kukan sabo, Salim da Sarla suna cikin alhini da fargabar kar in yaudaresu. Da misalin ?arfe Taran safiyar ranar laraba jirginmu ya tashi daga king Abdulaziz Airport jidda. Tafiyar awa biyar da minti hamsin da biyar ce ta sauke mu a Airport na Legos Murtala Muhammad.
Kai tsaye daga Airport muka wuce tasha. Wata sassanyar iskar ?anci na kaWamu zuchiyoyinmu cike da farin ciki marar adadin kwatance. Tiket muka siya, motarmu sai ?arfe biyar na yamma zata tashi tafiyar ta dare ce. Masallaci muka samu mu kai Sallah.
Uwani muje mu nemi abinci mu ci yinwa kamar zata kasheni" Na faWa ina ri?e cikina.
Wani Wan ?aramin gidan cin abinci muka shiga. Abinda suke siyarwa tuwon eba da miyar ganye, sai sakwara da miyar egusi. Sakwarar muka siya da nama gunduna_gunduma. Muka ci mu kai ?at, kana muka koma masallaci, mun bar motar da zamu shiga anata lodin kaya. Bayan la'asar muka shisshiga mota kowa ya zauna a muhallin zamanshi.
Gaga_gaga sai gamu a Kano ta dabo tumbin giwa ko da me kazo an fika da misalin ?arfe shiddan Asuba, garin da duhunshi a lokacin. A tasha muka sallaci asuba.
Uwani gidanki kika nufa ko gidan Hajiya?"
"Gidan Hajiya dai zanje, in yaso shi Hafizun yazo ya sameni a gidan, zan aika Habu ya nemoshi"
Mota muka shiga har zuwa bakin layinmu. Muna sauka sai gamu ga Lekan da abokinshi suna atisaye. A guje Lekan ya karaso.
"Ahh Antimi Iyabo. Okaabo" Farin cikine ya lulluSeni marar adadi.
Jakunkunanmu suka kinkima, abokin Lekan yabi Uwani, ni kuma Lekan ya bini.
A kofar gida muka samu Iyaa Debisi tana shara, ga shago harta buWe. ?agowar da zata yi muka haWa idanu. Saina fashe da kukan farin ciki dan ada na fitar da ran sake sanyasu ga idanuna. Iyaa ai saita soma wannan kwakwazo data saba, kafin kwabo jama'ar gidanmu duk suka firfito ciki harda yemisi da titsetsen cikinta a gaba, ko me take yi a gida duku_duku ohon mata dai. Iyaa Kokodeen ce ta ja hannuna zuwa cikin gida Wakin Iyaa. Nan aka shiga gaisawa da tambayar bayan rabuwa. Sai cewa suke yi nayi kyau na yi haske, amman na rame. Ni dai sai dariyar ya?e. Ruwan wanka Lekan ya kaimun, na shiga na gargasa jikina. Kafin in fito nazo na tarar da kwanukan abinci har daga ma?ota. Sannan matan unguwa har sun soma cika gidan anzo yimun sannu da zuwa. Na zama kamar watan ramadan, kowa sha'awata yake yi ha?orina na maka har biyu ma?ale a bakina sunata she?i, na fahimci hakan ya ?aramun kwarjini sosai.
Ni dai sai ya?e baki nake yi, amman ta ciki na ciki. Amala naci na ?oshi na sha ba?in bunu. Kwanciya nayi dan in Wan huta, dan a niyyata gobe in Allah ya nuna mana zan kama hanyar ?auyanmu, suma in gansu su ganni, sannan inga ajiyata dana ajjiye.( Ma?iyan Hamma ya jiki? >?#?) Bani na farka ba sai azahar, Burodami Debisi da Burodi Kokodeen suna Wakin, ga yemisi a gefe ana musu sulhun da aka saba. Burodi Debisi muna haWa idanu yayi mun murmushin da ada in banyi mafarkin irinshi daga gareshi ba yau, nayi gobe dan tsananin yadda nake mafarkin in zama matarshi. Sai gashi kash yanzu idanunshi a kulle suke akan sona. Yayinda nima idanuna suka makance akan son Yaya Hamma.
"Iyabo kece kika sake wani kyau da kwarjini haka? Kai maraba lale da shigowa ?asarmu me albarka." Kaina na sunkuyar dan bazan iya juran irin muguwar hararar da yemisi ke watso mun ba.
Kafin in gaishesu Yemisi tace.
"Dama a wannan karon ke kike barazanar kashe mun aurena sai gashi kuma kin dawo gida. Dan Allah in aurenshi kikeso kiyi me yasa tun farko ba kui aurenba, me yasa zaki Wauke tunanin mijina daga gareni"
" Mama Iyare Yemisi ( Kinci uwaki Yemisi)" Iyaa ta zageta, dama dai jira take yi sai ta sau kuka kawai. Ni kuma so nake in yaSa mata maganar da zata sake ingizata amman saina gaishe da Burodami Debisi, da Burodami Kokodeen, Kokodeen yace.
"Tunda kika tafi ba'a waya dake. Iyaa har ramewa tayi sabida tunanin ko kina lafiya. Hakama Dada da wani dogon Wan uwanku Hamma. Dan duk sanda Dada zata zo tare suke zuwa, suna yawan zuwa in banda kwana biyunnan da basu zo ba muke tunanin ko ba lafiya ba.. Gabana ya yanke ya faWi ras jin an ambaci ba lafiya ba.
Yanayin aikine, kuma ni bama waya a hannuna shiyasa. Gobe sassafe nake so dama in wuce Jeren." Burodami Debisi yace.
"Ki zauna ki huta mana kafin ki tafi" Iyaa tace.
"Gara taje, ina tunanin Daso ko babu lafiya fa. Wannan karon sun jima basu shigo ba . Gobe ta kama hanya kawai. Ki yi sallah sai mu tattaka mu je gidansu Uwani kafin Hajiyarta ta rigamu zuwa aji kunya"
To Iyaa" Ina faWar haka na mi?e na fice Wauke da buroshi da makilin dake jakata. Bakina na goge na Wauro alwala na shigo. Dabino da bagaruwa da na jefo a jaka da ruwan zamzam na ?ananun fararen roba na ciro ?ullin nasu Iyaa na ajjiye mata.
Ga wannan Iyaa, kayanmu suna jirgin kaya. Ba zasu wuce wata guda ba, dan munyi sare_sare sosai ne"
Nan Iyaa ta soma rawa tana shi mun albarka. Ai kuwa wannan dabino sai Iyaa ta shiga aikin kididdibashi ana kasabta harda ma?ota ma. Da haka suka ci gaba da shari'ar Yemisi dake gabansu, Iyaa ta lallaSata tasa Debisi ya bata kuWin cefane akan da yamma zata koma. Ina Idar da Sallah na saka doguwar jallabiya irin ba?in larabawannan ni da Iyaa muka kama hanyar gidansu Uwani. A hanya ne take sanar mini cewar sunje dubo Yarana dai aka tabbatar musu wai yaran suna Abuja wajen Matar abokin Gwadaben. Ajjiyar zuchiya na sauke nasan ko babu komai zasu samu ilimi. Allah shine masani idaniyata cike take da son ganin ?a?ana. Amman nasan ?ila yarannan sai sun girma a kwatanta musu inda nake rayuwa su neme ni. Ina musu fatan samun nasara da dacewa akan dukkan abinda aka Waurasu akai. Inma karatu, inma sana'a domin dogaro da kai. Daga su hai mahaifin nasu ina musu adda'ar samun Waukaka. Har a ka'aba na yi musu wannan adda'ar na jaddada. Da tulin tunani da misalai muka shiga gidansu Uwani dake cike. ?annenta duk sun cika gidan, da yaran kawunta dake aure da yaransu.
"Ahh Toyosi yau kune a tafe. Sai kika ga ba?in larabawa sun sauka" Cewar Hajiyan Uwani. Musa wanta yana zaune yana cin bagaruwa Yace.
"Kaga Hajiyoyin ?annenmu Makka kiran Allah, kun sha aikin Hajji da umara har kun gaji, ga sallar juma'a a masallacin ma'aiki arrasul S A W." Na kalli Uwani dake daga cikin Waki Hafizu da yaranta suna ma?ale da'ita. Ido ta kashe mun, ni kuma nayi dariyar da mu kaWai muka san fassararta. Ai kuwa Musa ya saki ihu.
"Ihuhu jibi ha?orin makka yadda yake ?yalli a bakunanku. Dan Allah ko umara ku biya mana da ramadana dai mu je"
Ni dai sai Dariya nake yi. Hajiya na gaisar na shige Wakin da Uwani take. Iyaa kuma suka shige Wakin Hajiya.
"Iyabo barkanku da dawowa ba?in larabawa" Zama nayi yaran duk suka rufeni. Safwan na Wauka ya girma sosai.
Hafizu ina yini mun sameku lafiya?"
"Lafiya lau sai alkhairi. Kin ganni nafi awa nawa ina lallaSa ?ar rigimarnan amman ha?ona ya?i kai ga ci" Yaran na kalla nace.
Amira kama hannunsu, ga Wari biyu kuje ku siyi wara kuci ko? Kafin kayanmu su ?araso yarana na siya muku kaya masu kyau da tsada.
Harda Hafizu a washe baki. Suna fita saina dawo da hankalina kan Hafizu.
Ina saurarenka"
"Iyabo kinsan kun tafi kun barni akan baifi wata Waya nima yayi mun ragowa in tafi Canada ba. An samamun aikin da bamu san wanne iri bane. To ko bayan tafiyarku saida muka fi wata huWu kafinma muka tafi. Tsaiwa kwatanta azaba da wahalar da matasa ?an cirani suke sha a ?asashen waje Sata bakine Iyabo, abun duk gidogace ruWune. Shekarata biyu a daddafe na dawo da kuWin da bai taka kara ya karyaba, banda jinyar jiki dana sha. Dawowata ke da wuya ina zuwa ?auyenmu sai mahaifiyata take


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login