Showing 195001 words to 198000 words out of 270738 words

Chapter 66 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

ROMO ?ANYE

BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI
LITTAFI NA UKU (15)

"Ba aure yayo da kuWinshi ba, abinda yayi ragowa ya cinye shi da amaryarshi ba? Wai ko so kike in dan?a mishi ragamar dukiyata ne, sai yadda yayi da'ita?"
Tabalbalin ta dinga faWa ta inda take shiga ba tanan take Sullowaba. Ni dai dana gama cin sakwara saina mi?e.
Bari in shiga ciki in Wauro alwala inzo in yi sallah"
Ciki na shiga na kama ruwa nai alwala. Sai kawai ma nayi sallata tunda yaran suna ciki sai murnar ganina suke yi. Fitowa nayi shago na tarar da wata mata suna maganar filaye da Uwani.
"Kinga filin yayi sau?i manyane dubu Wari_Wari aketa yankawa wallahi nan da shekara biyar wajannan cika zaiyi sosai. Shi yasa nace bari in sanar miki ko kina da bu?ata ?anina ne suke yanka wajan" Cewar wannan Mata kenan. Uwani tace.
"To zan duba kuWaWen wajena, ko kuma zuwa karshen mako akwai dashi da zan Wauka kuma da kauri ko guda biyu ne sai in siya in haWe ai" Ai sai nayi carab nace.
In babu matsala Uwani nima ai sai in siya tunda na siyar da shanuna kiwon ya?i sai ciwo suke yi" Baki Uwani ta ri?e cike da mamaki. Numfashi ta sauke tace.
"To babu damuwa Halima da daddare zamu zo in Bellon ya dawo sai muyi magana ?awata zata siya. Wannan ?awatace tun muna yara tare muka je saudiyya da'ita. Zan siya sai a bamu kusa da juna"
Da wannan matar tai mana sallama akan sai ta ganmu zuwa daren.
"Wai kiwon ma Hama ta hanaki kiyi sabida bata son kiyi arziki? Hmmm kingani ko Iyabo kinsan muguntar mutumin ?auye kuwa? Yanzu da ba dan kina da wannan gidan ba da haka kuWin zasu haWu su galgance jibi asarori da kika tabka. Ni da ace iyakar karayar jarine da yanzu na Woraki da yardar Allah. To ba'a siyan komai ne a hannunki ba?in asiri mitsiyaciyar tayi miki na ba?in jini. To ince dai bata da labarin gidan da kike dashi ko?"
Bata da labari, ko shi Hamma bai jima da sani ba. Hatta su Dada babu wanda yasan ina da gidannan. Wannan kuWin dabbobinne ma Dada tace in samu in mallaki kadara. To Uwani kina ganin ko in siyar da Wan kunne da sarkar da Saleem ya bani da wanda na siya a siya mun gida a sake zuba ?an haya. Amman ke me kika gani. Inata ajjiye dasu su ba kawo mun kuWi suke yi ba, ko babu komai hayar zatai mun amfani zan dinga karSar kuWina ina magance ?an matsalolina. Amman meye shawararki?" Uwani tayi jim tace.
"Magana ta domin Allah in kin tawo dasu ai gara a haWa a siyar dukka, mu haWa da ?an kuWaWen dake jikinki, shima wannan gidan a siyar sai a sai babba ko da gidan samane, me Wakuna da yawa. Kinga duk shekara zaki samu kuWaWe masu kauri a hannunki, zakita jalautawa. A ?auye in kinsa zinare ma waya sani babu. Ai gara ace ?asa gareki itace babbar kadarar da babu asara a cikinta, yaranki ma sai su gada duk da dai fulanin gadon shanayen wahala ake bar musu"
Mun jima muna tattsunawa. Dab magriba Uwani ta kulle shagonta muka shiga ciki.
Tuwo ta tu?a mana dama tayi miyarta ta Wanyen karkashi yaji Wanyan kifi tun safe, ga yajin daddawa mai daWi da take siyarwa, ga man shanu shima soyayye da take siyarwa. Uwani fa ?a?as ta zama ?ar kasuwa. Bayan munyi Sallah muka ci tuwonmu munata hira, sai naji rabi da kwatan matsalata kamar ta kau. Sai da mu kai Isha Uwani ta Webi kayan jajirai muka tafi gidan kishiyarta barka.
Gidan duk ya fice a hayyacinshi yayi biji, biji.
Da Sallama muka shiga Wakin. Jaririyar sai kuka take canyarawa. Ashe ba kowa ne a Wakin, ko ina uwar oho sai wan jaririyar yana zaune da ?aton ciki sai gyangyaWi yake yi.
Uwani tayi haka zata Wauko jaririyar a gado mai rumfa. Uwar jaririyar ta shigo da gudu ta riga Uwani Waukarta. Har tana sauke ajjiyar zuchiya.
Wai ashe haka kishi, da kishiya yake?.
"Tunda naji kukan yayi yawa nace ko wani abunne mugu ya sameta ashe kune. Sannunku da zuwa"
Ta ?arashe zancan tana dariya.
Uwani ta dubeni, ta dubi kishiyar tata tace.
"Mune mugayen da muka kusanceta kenan shi yasa take irin wannan kukan? Yayi kyau baki da laifi"
"Lahh wallahi Innar Zainab ni ba haka nake nufi ba kar ki juya mun maganata dan Allah" Uwani zata kuma magana na taSata ta baya. Wannan karon nako ci sa'a sai tayi shiru muka zauna. Ta bamu jaririya ta?i ta ?an?ameta, daga ?arshe saita cusama yarinyar mama. Wani shafaffen yan?wanannen mama.
Hafizu ne yayo sallama ya shigo. Ganinmu ne yasa ya washe bakinshi.
"Iyabo ashe kun shigo. Ke basu jaririyar ki kawo musu abinci."
"Tayi bacci ma" Ta faWa. Uwani tayi dariya tace.
"Kinga kwantar da'ita in tayi bacci. Abinci kuma ki bar abinki. Iyabo Jeka lo ( muje)"
Mi?ewa nayi, ledar dake hannun Uwani saita mi?a ma Hafizu tace.
"Ga gumama asa ma takwarata" Ya amsa yanata godiya. Mu dai nan muka fito muka barsu, ya suka ?are oho musu.
Wai Uwani yadda kishiyarki ta Waukeki kenan ba?ar muguwa? Kinji furucinta wai me yasa kishiyoyin kusan halayyarsu gudane, sai WaiWaiku da suka rabauta?"
"Rabu da matsiyaciya. Ba?in ciki nan take Hafizu na aiki a ?ar?ashina, da kuWina ake ciyar da'ita. Da bini_bini zata biyoshi har shago wai tazo ganinshi. Tasa na sallameshi da ?yar na dawo dashi, da sharaWin matarshi karta kuma zuwa nemanshi. Ko gidan biki ko suna haka na ma?ota dana shiga sai ta sha jinin jikinta. Ni nafi ?arfinta da ba dan haka ba wannan ?ar ?auyan juyanu zata yi kamar waina. Shakkarta fa shi kanshi Hafizun yake yi, damma yasan ba kyau ba daWi ni Win, shima da tsiyar zai tatamun ta su rijalu."
Washe gari
Sassafe muka wuce asibitin murtala, bayan bin dogon layin awo. Bata fa sauya zani ba, magana guda Wayace. Bani da ciki su basu ga komai ba.
Hankali saiya tashi fiye dana ko yaushe. Danni abinda nasa a raina shine a Adamawa akasi aka samu, bana jin asibitocin Kano indai dan ?warewa ne. Munbi asibitin kudi huWu a ranar wallahi zancan Wayane.
Kafin yamma idanuna ya faWa na yi wata rama ta fatat Waya.
"Iyabo gobe zamu buga sammako zuwa lahadin makoli wajen mai maganin dana faWa miki. Muje da izinin Allah zamu dace, kuma a dage da adda'a "
Kayya Uwani, ni ina ganin mu ha?ura da zuwa wani gidan magani. A asibiti ba'a gani ba sai a wajen mai maganin hausa ne za'a gani? Allah yana ji yana gani shi zai bani mafita." Uwani ta dafani tace.
"Bazan hanaki kuka ba. Wallahi nima dauriyace tasa ban zubar da hawaye ba. Amman fa Iyabo kowa yasai rariya yasan zata zubda ruwa. Ni dake a asibiti muka ga dun?ule magani a cikin abinci. Amman idanki ya rufe Hamma kawai. Alhalin ya kamata ace ki duba waye abokiyar zamanki shima yana da mahimmanci.
Matan katsina, Sokoto, zamfara, Maiduguri me yasa zaki ga in akaji dasu za'a haWa kishi sai kiga an tashi hankali? Sabida waWannan garuruwa dana lissafa sunyi ?aurin suna wajen kassara kishiya, da mugun dumi suke Waukar sha'anin kishi. ( Kuyi ha?uri ba duka ake nufi ba, mafi yawancin ?an garuruwan da aka ambata haka suke. Amman akwai da dama waWanda ba haka suke ba. Kar a mance labarin na gaske ne ba ?ir?irarshi akayi ba)
Iyabo mun kama laya a cikin fulonki, muka so ni da BaWWo a nuna ma uwar mijinku. Amman kika ?i waike kaza ke kaza kar aurenta ya mutu. Ba gara aurenta ya mutu ba akan ta tarwatsa rayuwarki. Zuchiyar bafulatani fa tauri gareta basa jin kira. Yanzu jibi a cikin dare dubu Wari da Wayan data saki, baki mutu ba al?iyamarki ta tsaya. Ga ciki yana motsi, yana girma amman ba ciki bane"
Kukana ne ya sake tsananta, ina ganin meye laifi danna zaSi in rayu da sanyin idaniyata. Soyayyar da nake ma yaya Hamma ta wuce gaban kwatance, dan ko mayyace Hama bazai sa in janye aurenshi ba.
Ganin kukana yayi yawa ga dare ya raba Uwani taita rarrashina.
A daren ranar bacci banba, ni innaji cikina yayi motsi sai tsoro, dan bansan dame nake rayuwa a ciki ba.
Washe gari ni ko wanka banyi ba muka wuce, da ?yar da suWin goshi Uwani tasa nasha kokko da ?osai biyu muka wuce.
Motar Karamar hukumar warawa muka shiga, daga warawa muka hau akori kura zuwa ?auyan Lahadin makoli. Daga lahadin makolinma saida mu ka yi tafiyar Wari bibbiyu a AcaSa. Tafiyar Wari biyu a ?auye bafa ?aramar tafiya bace. Sai gamu a wata bukka da mata masu ciki zuzzube a ?asa. Wasu cikinsu ya kusan haihuwa, wasu kuma cikin kamar dai nawa, wasu ma cikin bai kai nawa ba.
Layi Uwani ta kama mana, muka samu mu kai azahar, ta siya mana Wanwake da mai da yaji. Ni bakina ma Waci yake yi da ?yar dana sa Wanwaken a bakina na haWiye.
Uwani dan Allah ki rabu dani da abinci. Ki barni inji da damuwata" Murmushi tayi tace.
"Ki yarda da Ubangijin daya kuSutar dake daga hannun larabawannan da suka nemi ranmu. Ki kuma yarda da ubangijin daya taimakeki kika auri Gwadabe a lokacin da duk wanda ya kalli ala?ar cewa yake bazai yiwu ba. Ki yarda da ubangijin daya ?adarta miki auren Hamma har kika shiga wannan halin. Ki yarda zaki samu taimako daga gareshi. Iyabo nasanki da tawakkali da Waukar komai ba komai ba. Amman naga wannan lamarin kin Waukeshi da matu?ar zafi. Kici abinci kar ki kashe kanki"
Wallahi maganganun Uwani sai suka wanke mun kai. Wani tawakkali ya sakko mun. Murmushi nayi nasa hannu na karSi Wanwaken na cinye tas na sha ruwa. Na dubeta nayi murmushi. Itama murmusawa tayi. A haka har layi yazo kanmu. Mu huWu muka shiga masu ciki, sai Uwani ta biyar. Ta farkon itace ta soma bayaninta, wanda ya gigita tunanina.
"Malam shekarata uku Wauke da wannan cikin. Ni ban haihu ba, ni ban huta ba Malam. Naje wajen masu magani iri daban_daban amman ba'a dace ba Malam. Kishiyata ce ta biyun taimun baki a lokacin da mijinmu yake rawar ?afar na samu ciki yana saka ran haifa mishi namiji. Shine tace, in dai tana doron ?asa ban isa na haife cikinnan ba. Shekaru uku kenan har mijin ma ya gaji ya sakeni, ina gida da ciki"
Take zufa ta wankeni, jikina ya shiga Sari. Malaminne ya soma magana da cewa.
"Kwantar da cikin akayi bazai yi gaba ba bazaiyi baya ba. Amman kin kawo kukanki gidan mutuwa
Akwai aljanin da zamu sa ya tayar miki da cikin. Zaki kawo ba?in ra?umi, da ba?in bunsuru, da Sakar tunkiya, da ba?ar mage. Wannan shine ladan aikin"
Zumbur na mi?e ina ha?i, tari ya kamani na nufi hanyar waje. Uwani ta biyoni tana ri?eni muka fita.
Uwani dama kina ta'amali da bokaye ban sani ba muke ta abota?" Na tambayeta raina a Sace hankalina a tashe.
Ita kanta a cikin rudu tace.
"Wallahi Allah bansan boka bane. Kinsan Allah da girma yake Iyabo wajannan wata ma?ociyatace ta taSa zuwa, tana neman maganin haihuwa, ita ta kwatanta mun. Barni da Balbalin kema kin sani harkar shirka bana ciki. Mu maza mu bar wajannan danni gabana ma faWuwa yake yi"
Ba shiri mka bar wajen, a ciki na baro takalmina warin ?afar hagu.
Bamu muka koma gida ba sai wajajen sha Wayan dare wallahi, gajiya, yinwa duk mun kwaso. Ni babbar damuwata bansan ko Allah zai amshi sallolinmu ba. Duk da shine masanin gaibu, munje wajenne ba tare da ilimin boka bane.
Ni dai a zarge na rama sallolina.
Uwani Allah yana gani zan koma gida muita adda,a da izinin Allah zai mun mafita. Bazan sake zuwa asibiti ko wani maganin gargajiya ba. Lokaci zaiyi halinsa, Allah zai nuna ma Hama ikonshi nayi wannan imanin Allah zai dubeni."
Kwanana goma cib a garin Kano. Kwana huWu a gidan Uwani, kwana shidda a gidanmu.
A kwanaki gomannan na siyar da zinaraina, Uwani ta sai gidana dake jikin nata muka gagganWa kuWin aka siya mun gidan sama mai Wakuna goma sha biyar, da shaguna huWu. Burodami Kokodeen da Burodami Debisi, da Uwani sune suka zama shaiduna, muka biya aka gyara takaddu da cike_ciken abinda ya dace, na kamo hanya na dawo, gida na hannun Uwani da Burodami Debisi su zasu saka haya su amshi kuWin hayar.
?an canjinan da suka ragemun, na siyo kayan aune, aune, da busassun kayan miya, da maggi dun?ule da fari, da dai abinda duk nasan ina bu?ata. Iyaa Debisi ma tayi mun tsarabar doya, garin alba, garin amala, bushasshiyar gandane. Burodami Debisi shi kuma shinkafa da wake ya aunarmun mai yawa, ya kawo nama akaimun miyar stew soyayya mara ruwa ?aramar robar fenti.
Uwani kuma kayan miya ta siya da yawa aka ni?o ta tafasamun ta duramun a jarka aka zuba mai a saman, yana daWewa sosai bai lalace ba. Banda tarkacen su yajin daddawane, jan yaji ne. Tsaraba dai rigi_rigi na koma da'ita. A tasha na samu Yaya Hamma a tsaye kamar yadda ya saba yana jiran dawowata.
Da magriba matan gidan duk suna tsakar gida anata aikace_aikace sai gamu mun shigo da sallamata. Ga yara na bina da kaya rigi_rigi. Yaya Hamma shima yana ri?e da wasu kayan.
Hmm kunsan me? Da muka gaisa da matan gida saina nufi Sarayin Yafendo na yada zango acan. Yaya Hamma kuma ya wuce masallaci, dan anata kiraye,kirayen Sallah.
Bayan na rama sallolina BaWWo ta kawo mun tuwo naci. Sai Yafendo take faWamun mummunan abinda ya afku bayan kwana uku da tafiyata.
"Jabu ai bayan tafiyarki da kwana uku gobara ta tashi a lungunku. Da Wakin Safiya, da ?akin Fatu ?arama da naki. ?urmus suka yi babu abinda aka Wauka. Gobarar daga Wakin Fatu ?arama ta tashi, anyi ruwa mamako saita shiga da gaushi Wakin. Ashe ya kama zanin gadonta ita bata sani ba, cikin dare sai wuta ta tashi.
Murmusawa nayi idona na hawayen da suke shirin makanta ganina nace.
Allah yasa sa da abinda ya tare" Yafendo ta girgiza kai tace.
"Ameen. Bayin Allah duk sun kakkawo taimako anata kan karSa kinsan mutanen ?auye da haWin kai.
Zamu kwana tare dake anan har zuwa a gyara miki Wakin naki. Su Safiya duk suna gidansu."
To Shikenan Yafendo mun gode.
Shigowar Yaya Hamma yasa Yafendo ta fice ta bamu waje.
Zama yayi yana fuskantata, ni kuma inata share hawayen da nayi yin duniya ya?i tsaiwa, da kanshi yake hankaWo kanshi.
Kallon tausayi yake yi mun, mai cike da tsantsar so.
"Kiyi ha?uri Jabu. Haka Allah ya ?adarto mana. Daga wannan sai mu faWa wannan. Aikin gadin dana samu ma ya kuSuce mun. Matar gidan tasa an Wakko Wan uwan mijin a ?auye an bashi aikin. Shanun da nake gadara dasu duk sun soma ciwo, yanzu haka Yuguda ya tafi dasu asibitin dabbobi. Annobar bace ta samu shanun. WaWanda shanayensu basu kama ciwo ba, duk sun tafi ciranin dole, dan gujema annobar. To mu kam kusan rabin shanunmu ciwon ya kamasu, jikinsu duk kuraje. KaWan daga ciki da basu fi ashirin ba Jumare ya tafi cirani dasu.
Kiyi ha?uri zan sai miki kayan Waki gwargwadon halina."
A'a Yaya Hamma. A halin yanzu bata kayan Waki ake ba. Mu yi adda'ar Allah ya kawo sau?in wannan annoba data samu shanun kawai. Babu komai zamuita lallaSawa"
Jigum_jigum muka yi. Kunsan dai bafulatani da Shanu. Baffa Musa ma ance yana kwance babu yadda yake a dalilin shanayenshi wajen bakwai sun mutu. An siyar da kusan goma. Jikin nashi yayi tsananin tsananta. Haka a daren muka je dubashi baya gane ma wanda yake kanshi. Mu dai gamu jigum_jigum su Dada sai sharar hawaye suke yi. Domin shi suke gani a makwafin uba a garesu.
Wannan kenan. Su Yafendo ne suka yanke shawarar data tashi hankalina cewar asubar fari Yaya Hamma ya kora shanun Baffa Musa ya tafi wannan cirani dasu.
Ai kuwa hakan akayi, a gidan Baffa Musa dukka muka kwana. Washe gari sassafe gun_gun matasa da magidanta suka haWe kawunansu suka Wau hanyar dokar daji, su kansu basusan a ina zasu samu garin da zasu yada zango su kafa tantinsu ba. Har waje nabi Hamma ina kuka. Ku dubi kunya irinta bafulatanin mutum amman gam Yaya Hamma ya ri?e hannayena yace.
Har abada soyayyarki ta dabance a zuchiyata bazan mance da halaccinki a gareni ba. Jabu ki tayani da adda'a ba zan fi shekara Waya ba ko dan inzo inga abinda kika haifa zan dawo. Bazan mutu ba har sai Allah ya sake ara mana lokacin da zamu sake shinfiWa sabuwar rayuwa. Yara goma sha biyu zaki haifamun dukka maza in sha Allah."
Ina kuka ina murmushi mu kai sallama yabi ayarin gungun fulani da gungun shanaye, suna tafe suna wa?ar fullanci ta nuna jarumtarsu.
A ranar nayi kuka sosai. Sun tafi babu jimawa dan ko awa uku ba'aiba da tafiyarsu Allah ya Wauki ram Baffa Musa sanadiyyar mutuwar shanunshi fulani da shanu ba dama ne.
A wannan shekarar anyi asarar dukiya anyi asarar rayuka sosai. Dan wasu da kansu suka kashe kansu, wasu kuma zuchiya suka haWiye suka mutu.
Haka akaita zubar da gawawwakin dabbobi abin tausayi.
Wasu wannan ne yai silar karayar arzikinsu ciki harda Mijin Cubu, da mai Nagge mahaifinsu BaWWo, danshi kab shanunshi wayar gari akayi asa tarar sun mutu. Sai ya zama kamar wani zautacce_zautacce haka.

BAYAN WATA UKU
Ina zaune a Wakina da wuta taci aka gyaramun na buga tagumi ina tunanin ko Allah zai sa mu sake ganawa da Yaya Hamma sai Allah. Ga cikina ya girma watanshi kusan takwas da kwana goma sha Waya. Yayi girma sosai, kullum fargabata yaya zanyi mu rabu da wannan ciki nake. ?ila shine ajalina dan inaji a raina kamar ?arshen rabuwata da yaya Hamma kenan. Yafendo ce ta le?o.
Na Wago na dubeta.
"Jabu kina zaune kina faman aikin tunanin kina da juna biyu? Maza fito ki sha iska ga magani na dafa miki kisha"
Da dabara na tashi, dan cikin ya girma sosai. A ?ofar Wakinta ta shinfiWamun tabarma na zauna ina haki. Maganin za?i ta bani cikin kofi na kafa kai na shanye, kasancewar ba magani mai Waci bane. Ta ajjiyemun lafiyayyen Nono yaji dambu shi kaWai nake iya sha, bana gajiya. Sai in sha sau nawa. Gashi nonon ma wuya yake yi kasancewar babu shanun yanzu. Su BaWWo ma sai kwalba da madara suke ma ?ar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login