Showing 81001 words to 84000 words out of 270738 words

Chapter 28 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

ya sake ya mi?a ma Inusa hannu suka gaisa.
"Ciwo kayi ne Gwadabe, kai kaga yanda duk ka faWa kuwa?" Kai Gwadabe ya sosa kana yace.
"Sha'anin rayuwa ce kawai Yaya Inusa. Yau da gobe bata bar komai ba, a dai samu a adda'a" Girgiza kai yayi cikin tausayawa yace.
"Allah ya rufa asiri. Zamu yi magana da Hambali muga me ya dace a taimaka maka dashi" BuWar bakin Yaya Hambali yace.
"Da za a taimaka mishi da bama zaka ganshi a haka ba. A lokacin da naso in taimaka mishi ai ?i yayi. Inusa in dai kanaso zumuncinmu yaci gaba, to kar ka sake ka taimaki Gwadabe da sisin kwabo" Sai wani huci yake yi, yana hura hanci. Yaci jar shadda dinkin tazarce, idanunshi cike dam da farin kwalli. Murmushi Gwadabe yayi kawai ya wucesu.
Tafiya kawai yake yi, amman baya ma iya ganin gabanshi. Tunanin shi kuwa shine.
Anya Babala itace ta tsugunna ta haifeshi kuwa? Anya su Yaya Hambali ?an uwanshi ne su kuwa? Sai dai yana tuna yanda suka taso cike da kulawar Yaya Hambali, ya kuma haWe kawunansu duka, cikin soyayya yake musu komai. Har wanka yayi musu da hannunshi. Gashi da yawan taimako, hakannema yasa gashi duk ya jaye ?an uwan nashi, kuma dukkansu da bazarshi suke taka rawa. Daga sanda ya Auri Iyabo zuwa yanzu yana ganin ?iyayya. Sun kwana basu ci abinci ba, yaje wajen ?an uwanshi ya bisu kab aka rasa wanda zai taimaka musu. Hawayene yaji suna zuba a idanunshi shaa. Da sauri ya goge yana dariya kamar mahaukaci.
Ko da yayi salllama a gidan Bara'u, Sakina ce ta fito. Tayi mamakin ganin irin ramar da Gwadabe yayi. Bayan sun gaisa ne take cewa.
"Gashi yana gona. Amman bari insa Shehu yayo kiranshi. Ka shigo daga tsakar gida"
"Nagode Sakina" A sanyaye ya shiga tsakar gidan. Ya zauna akan taburmar daya samu a shimfiWe a baranda yayi saroro dashi.
Ruwa Sakina ta kawo mishi, sai da yasha sannan yace.
"Ina yaran ke kaWaice a gidan?"
"Sun tafi makarantar allo dake yau babu boko. ?an kuci_kucin kuma Baban ya tafi dasu gona. Ya wajen su Baba Magaji?" ?an murmusawa yayi kafin yace.
"Kowa yana lafiya, sannu fa da Wawainiya Sakina allahu ya bar zumunci" Dariya tayi ta mi?e abinti taci gaba da kaye_kayenta har Bara'u yayo sallama ya shigo. Ganin Gwadabe ne yasa yayi Dariya, sai dai ya girgiza da yanayin daya ganshi a ciki, musamman ba?i da ramar da yayi. Ga wani rawani daya tuntuma a kanshi irin na buzaye.
"Ba?in buzu gallah mu ka yi a gidan namu, Gwadabe maraba lale" Zama yayi suka tafa. Sakina ta dure musu Wumemen dambu yaji rama da man shanu.
"Fara cin abinci tukunna mu sha labari" Sai da Gwadabe ya ?oshi ya sha ruwa kana yace.
"Na sameku Lafiya ya Wawainiya?"
"Lafiya lau, Wawainiya ai yiwa kaine Gwadabe. Ya bayan rabuwa?" ?an sauke kai ?asa yayi yana wasa da yatsun ?afarshi yace.
"Sai alkhairi Bara'u. Ya gona?" Dariya yayi yace.
"Gona lafiya lau, sai godiyar Allah. Lafiya irin wannan ramar haka Gwadabe, ciwo kayi mu bamu sani ba ko me?" Bara'u ya faWa cikin kulawa. Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke kana yace.
"Wallahi babu ciwo yau ce kawai Bara'u. Ga ciwon damuwar rabuwa da iyali lokaci guda shima yana damuna ainun. Kuma sana'ar tamu tana da wahalar gaske" Ajjiyar zuchiya Bara'u shima yayi.
"Toh Allah ya kawo maka mafita. Ai rashin iyali ga wanda yasan daWinsu babban tashin hankali ne. Sannan ya haWema har da yanayin can ?asar kasan baka sababa. Amman ya batun aurenka da Shafa da Hadiza?"
"To Bara'u ni fa gani nake yi in ha?ura da Shafa kawai. Bana jin motsin san su sam a raina. Ganin girman waWanda suka mun kyautarsu kawai nake ji. Ka ganni sai in yi sati biyu ban ri?e nera biyar tawa ba. Da haka ne zan auri mata biyu? Atampa biyu kawai na iya ajjiyewa da sunan kayan akwati fa. Duk da Tamu zai taimaka mun, amman dole inma Hadiza" Shiru Bara'u yayi yana nazarin maganar Gwadabe, domin maganarshi abun dubawace.
"To Gwadabe maganarka gaskiya ce domin Allah. Amman dole a nemi maslaha, kasan Tamu ba lallai yaji daWi ba. Shafa kuma ta gama sa ranta da kai. A gidansu duk ansan da maganar aurenku fa. Ni ina ganin ka daure dai ka auresu du biyun. Sai a tura bikin ita Shafa zuwa nan da ko shekara ne. In yaso ita Hadizan sai ka soma aurenta. Ko yaya kake gani?" Kai Gwadabe ya gyaWa kafin yace.
"To hakanma gaskiya ne. Nima abinda du ya dameni kenan. Kaga kuwa in da za a Waga Win zuwa lokacin da ka ambata Win da abun zaiyi kyau. Muna sa rai abubbuwa zasu warware da izinin Allah. Dan sana'ar tamu in Allah ya dafa ma mutum yana samun arziki. Da ace ina da wasu jari ma a hannuna da abun sana'a zan dinga tafiya dashi ina Wan siyarwa haka. A samu Wan na kashewa." Bara'u yace .
"Ga shawara kana ganin in kana siyar da magungunan gargajiya ba zaka samu ciniki ba? Da sai ka jaraba ai, ko maganin dattin ciki, da maganin basir, da Wan na warware gaSoSi da sai ka dinga dafawa kana ?ullawa a leda kana tafiya dashi. Kuma fa akwai riba." Shiru Gwadabe yayi yana nazari kafin yace.
"Wannan ma shawarace Bara'u. Sai in jarraba, in zan tafi zan tafi da wasu sa?e sa?in in sha Allah"
"Sai kaga Yaya Hambali ya gyare gida ko?" Yayi maganar yana dariya" Gwadabe yace.
"Gida yayi kyau sosai Bara'u, sai haska gari yake yi."
"Hmmm ai Yaya Hambali in faWa maka harkace ta buWe mishi. Wani bawan Allah ne ya bashi kwangilar dabino, da jar dawa ko buhu nawa yakai yana siya. Kai duk inda dabino da jar dawa suke Yaya Hambali siye su yake yi ya kaima mutuminnan. Shi yasa bashi da aiki sai zuwa ?auyuka ?auyuka neman jar dawa Ance gidanshi na kano ya rushe ya maisheshi bene. Kuma ya sai gonakai shimfiWa_shimfiWa a bayan gidan gonar mai gari baka ga girmansu ba, wai yanaso bana yayi noman jar dawa ne." Gwadabe ya taya Wan uwan nashi murna sosai. Har cikin ranshi yaji farin ciki, yasan ko babu komai Babala zata huta.
"Ni na mance sai kazo kaga Auta a gida miji ya sakota uwar miji ta hanata zaman lafiya " Cikin mamaki Gwadabe yace.
"Autan aka saka Bara'u?" Baki Bara'u ya saki yace.
"Wai baka ganta a gidan ba, ko dai baka tsaya kayi hira da Babala bane?"
"Hmmm Bara'u kenan" Nan ya kwashe duk irin cin kashin da Babala da Yaya Hambali su ka yi mishi. Ya Waura da cewa.
"Zuchiyata dab take da bugawa. Dame zanji Bara'u . Batun mutuwar auren Auta kuma duk Babala ce ta sa aka sakota, ta hanani zama da Iyabo, gashi uwar miji ta hana Auta zaman aure. Lokuta da dama iyayenmu suna kusa kurai" Tsit Bara'u yayi, idanunshi suka rine da kyar yace.
"Hakane Gwadabe kayi ha?uri. Ni kaina Yaya Hambali babu irin cin mutuncin da bai yi mini ba akan sai dai in cire Toye daga boko. Dana faWa mishi gaskiya kuma yace na zageshi. Gwadabe Babala har gidanmu taje ta kai ?arana" Sun jima sosai suna tattaunawa. Da rana saiga ?an makaranta. Toye ya girma abinshi, bai mance da mahaifinshi ba. Har iyabo Toye saida ya tambayi Gwadabe. Zuchiyar Gwadabe sai tayi sanyi jin yaron bai mance shi ba. Sai da daddare Gwadabe ya samu damar yin waya da Hadiza da Shafa.Kwanan Gwadabe biyu a Takai, amman zaman duk ya gundureshi sabida irin hantara da munanan furucin Babala a kanshi. Bayan ya huta sai kuma yabi dangi da gaisuwa gida_gida. Kwananshi Takwas yayi sallama dasu. Dashi da Bara'u suka dunguma Habuja wajen Tamu domin su yi mishi bayani akan batun Waga biki.
Bayan sunci abinci sun huta. Ya ga ?an biyu ya basu ?ar tsarabar da yayo musu da yaran Tamu, ganin yanda yaranshi su kai kyau da gani ana kulawa dasu, dan kayan jikinsu ma mai tsada ne. RaWa yaima Bara'u a kunne yace
"Maganar Waga bikinnan a barta Bara'u. Kunya duk ta lulluSeni wallahi, jibi hidimar da yaketa yi da yara fa" Kai Bara'u ya gyaWa halamar hakane. Fitowar Shafa itace ta dakatar da Tamu da magana dan tambayarsu yake yi gulmar me suke yi. Jus ta dire musu tasha ado tayi kyau tana ta ?amshin turare me daWi. Kanta a ?asa ta gaishesu. Bara'u yace.
"Ja ira yau mu ake jin kunya Shafa? Lallai kin girma" Murmushi kawai tayi mishi. Gwadabe sai kallonta yake yi yana murmushi. Tamu ne ya mi?e tsaye tare da cewa.."
"Kafin su gama Bara'u tawo mu shiga kaga gari. Ai kwana zaku yi dai ko? Dan nasa Shafa ta gyara muku shago an sa katifa ma" Bara'u ya mi?e tsaye yace.
"Kwana zamu yi kai bama Waya ba, dan wallahi ni kam saina huta. Kai kaji falonnan wani sanyin fanka kuwa?' Tafawa su kayi tare da ficewa. Fitarsu ce yasa hankalin Gwadabe dawowa gareta, itama saita gyara zamanta. Idanu ya ?ura mata ita kuma sai sinne kanta take yi kunya ta isheta. Shi kuma yau ne ya samu damar kallonta tsab. Yarinyace gaskiya, tana da madaidaicin kyau, da matsakaicin tsayi, bata da diri a kallon da yayi mata a tsaye, amman ?irjinta a cike yake masha Allah.
"Gani a gabanki amman kin kasa cewa dani komai. Ke da kika ce kinata mafarkin zuwan wannan ranar. Sai naga kin kasa cewa komai " Sake sunne kanta tayi ?asa. Yawan kunyarta sai ya zama silar burgeshi, kunya tana yima Wiya mace kyau, tana zama wani ado na musamman gareta. Murmushi yayi kawai tare da girgiza kai. Shafa tayi mishi ?arama sosai shi yama rasa taya zasu yi wannan zance. Da dai taga shirun yayi yawa sai yace.
"To a Wago fuskar mana in Wan kalla" ?agowa tayi ta Wan kalleshi, shima ya kalleta, tayi saurin kawar da kanta tare da cewa.
"Barka da isowa, ya ka baro mutanen Takai?" Sai da ya yi Dariya sosai kana yace.
"Suna lafiya, ya karatu ya aikin kuma duk anayi ko?"
"Anayi Alhamdulillah"
"To Allah yayi jagora. Sannu da Wawainiya da ?an biyu. Ayashe ta sanar dani irin hidimar da kike yi dasu. Tamu kuma ya bani labarin irin sha?uwar dake a tsakaninku. Kina son zaki tafi dasu ne in mu ka yi aure?" ?asa tayi da kanta tana wasa da yatsunta tace.
"E inaso in tafi dasu, sabida zasu yi maraicina, kuma nima zanyi kewarsu da yawa. Gashi ba ?asa Waya ba balle ince zan dinga sawa a kawo mana su hutu. To Amman Yaya Tamu yace babu wanda zai rabashi da su" Dariya Gwadabe yayi. Dariyar yadda take magana muryarta na rawa kamar tana gaban dodo."
"Zan mishi magana in lokacin yayi. Dan inason in haWe kan yarana. Toye dake wajen Bara'u ma zan Waukeshi in yaso sai in ba yayarki tayi ri?onshi. Zanfi samun nutsuwa" Da sauri ta Wago tace.
"Wacece Yayata kuma?" Kallonta yayi yana nazarinta, a muryarta yaji kishi. Sai ya basar yace.
"Hadiza nake nufi ?ar uwata wacce zan haWaku" A sanyaye tace.
"Ka yanke hukuncin soma aurenta kafin ni kenan? Bayan ni aka soma baka kafin ita" jin furucinta da rawar muryarta sai yasa yaji kunya. Ba shiri yace.
"Ko Waya Allah shine masanin wacece zata zama fari, in Allah yaso sai kiga rana Waya an Waura auren. Nace yayarki ne sabida Hadiza ta girmeki sosai. Bazawarace yaranta biyu" ?an boyayyen ajjiyar zuchiya ta sauke. A haka hirar taci gaba da gudana. Tsarabarta ya mi?a mata, ya mi?o mata agogon da Hadiza ta bayar a kawo mata. Har a fuskarta taji daWin kyautar Hadiza sosai. Mi?ewa Gwadabe yayi tsaye yace da'ita zashi masallaci an soma kiran sallar la'asar.
Haka dai Gwadabe suka kwana biyu a gidan Tamu. Sunga karramawa sosai. Ranar juma'a ya kama hanyar nijer, Bara'u kuma ya kama hanyar Takai.


IYABO.
Tsarki ya tabbata ga Allah mai kowa mai komai. Sarkin dake da iko a kan kowa da komai.
Muna zazzaune mata da maza sai shigowa suke ta faman yi. Fuskokin al'ummar cikin wannan jirgi mafiya yawansu cike take da annuri. Barinma ire_irenmu da bamu taSa tunanin samun irin wannan damar ba ko a mafarki.
Wata na'urace muka ciyo tana magana da turanci akan kowa ya Waura belt Winshi ya gyara zama zuwa minti sha biyar jirgi zai tashi. Ma'aikatan dake ciki???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n jirgin sun taimaka mana ainun. Dan daga ni har Uwani bamu iya saka wannan bel na jikin kujera ba. Mintunan da wannan na'ura na cika jirgi ya soma tafiya da tayoyinshi a cikin filin girji. A hankali _a hankali har jirgi ya tashi sama. Sai da ya tsayu a sama kana na dawo cikin hayyacina dan juwa naji inaji harda hararwa. Wasu tsofaffi ma harda ihu dan tsoro.
Taga na kalla na ganni a cikin gajimare. Gurun da Yaya Hamma ya bani na sake matsewa a hannuna na lumshe idanuna, abubbuwa ne suka haWemun. Murna da kuma alhinin barin Dada. Da kuma damuwa da fargabar rashin furta mun kalmar soyayya da Yaya Hamma bai yi ba. Ta wani Sangaren gani nake yi na rasa shima, musamman inna tuno da irin soyayyar da Daso take gwada mai. Bani da masaniyar sanda zuchiyata ta kamu da soyayyar Yaya Hamma. Ada nayi tunanin damuwa da lamarina shi ya haifarma da zuchiyata sha?uwa dashi. Ayau rabuwarmu na sake samun ya?inin motsin sone a ?irjina bana sha?uwa ba. Kuma a yaune na tabbatar da soyayyar da Yaya Hamma ya ke yi mini. Iska na furzar daga bakina. Idanu na sake lumshewa.
Allah sarki Gwadabe yanzu inaji ina gani ni Iyabo na rasaka, dole in yi aure in hayayyafa da wani Wa namiji bayanka. Ji nayi Uwani ta balbalin ta dafani. Juyowa nayi na dubeta, murmushi tayi mun, nima shi na mayar mata.
"Iyabo, ko Hamma bai faWa ba tsananin sonki yake yi sosai. Ki duba har kwalla sai da ya zubar, banda irin Wawainiya da kulawar da yaita baki. Ya kamata ki kwantar da hankalinki dan nasan zuchiyarki bata iya kamuwa da soyayya ba. Sannan ki bari ki samu nutsuwa kiyi tunani akan wannan soyayyar. Ki sani dai Hamma a ruga yake rayuwa ba'a birni ba, nifa banga dalilin ma da zaki yi sake har zuchiyarki ta kamu da sonshi ba kema. Na fa yaba ma ?o?arinshi gaya, amman baima dace batun wani so ko aure ya Sullo ba"
Mrs Bukhari


*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
NAMA YA DAHU...
ROMO ?ANYE
BOOK 2

7
Ajjiyar zuchiya na sauke.
Uwani duk abinda kika faWa gaskiya ne akan Yaya Hamma. Amman a jikina gani nake yi tunda bai furta mun kalmar soyayya ba har mu kai bankwana, to bazai furta mun ba. Kar ki manta kasarfa zamu bari, tunda muka shigo garin Kano ya dace ya fallasamun asirin zuchiyarshi ko?" Dariya Uwani tayi mun.
"Iyabo manya. Maganarki haka take. Amman in kin lura Hamma ba?auyene cikakke, babu wayewa a tattare dashi. Ni nafi tunanin ya rasa ta yanda zai furta miki kalmar so ne. Amman a shawarce kar ki bari zuchiyarki tayi zurfi a soyayyar Hamma. Kar mu dawo kiga saSanin abinda kike tunani azo a samu matsala. Shekara uku ba kwana uku bane. Kuma ?ila mu wuce tsawon wannan shekarun." Haka mu kaita tattauna zantuka ni da Uwani. Dare ya ratsa sararin samaniya sosai. Ma'aikatan cikin jirginne suka soma rabon ruwa da lemo, da soyayyen cincin, da naman kaza. Sai shillawa muke cikin gajimare. Awannmu 6 da minti ashirin muka ji jirginmu ya sauka. Dukkanmu muka cika da murna a tunaninmu mun iso Makka ne ashe ba haka bane, itofiya muka iso. Hajiya Salamatu ta sanar damu zamu kwana a Airport zuwa gobe jirginmu da zai ?arasa damu saudiyya zai zo. Ta Waura da cewa.
"Ni daga nan shine iyakata daku. In kuka sauka a Makka Hajiya Mangala zata turo duk a Wauke ku. Allah ya ba da sa'ar abinda aka fito nema." Daga nan muka Wunguma inda zamu kwana. Anan muka rarrama sallolin da ake binmu a filin Allah. Washe gari duku_duku jirgin da zai mayar da Hajiya Salamatu zuwa Najeriya ya tashi dasu, cike da fasinjojin Najeriya. Mu kuwa a gantale ga ba?ar yinwa haka mu kai ta zama a wannan fili. Gashi cikinmu babu wacce take da kuWi, ruwa ma sai da mu ka ro?a aka bamu, shima wasu basu samu ba. Sai kusan magriba aka sanar mana jirginmu yazo. A madadin Makka, sai akace ai dama Riyahd za'a kaimu. Haka aka Wuramu a jirgi. Daga itofiya zuwa Riyahd Awa 2 da minti hamsin da huWu ne ya kaimu. Aka sauke mu a filin jirgin. King khalid international airport. Tun daga sakkowarmu jikina ya mutu. Bani kaWaiba duk tawagarmu jikinsu duk a mugun mace. Bayan mun je Wakin Waukar jaka, daga nan aka nuna mana ?ofar fita, duk muka fito yu. Titine shimfiWaWWe, sai tsirarin motoci masu shige da fice jefi, jefi. Ga wutacen lantarki masu haske kamar rana. Dan ko allurarkace ta faWi zaka ganta kamar ba dare ba. Wata farar Hajiya ce ta nufomu tana murmushi, tasha gwala_gwalai ha?orin makka har guda shidda ne reras a bakinta. Da isowarta sai muka ji tayi Hausa raWau.
"Kune mutanen Hajiya Salamatu kano to jidda?" Kusan dukkanmu muka haWa bakin wajen amsa mata da.
"E mune Hajiya" Dariya tayi tace.
"Masha Allah komai yayi kalas. Yalla ga mota bus ku shiga muje" mota muka shisshiga kowa ya zauna, iyakar galabaita dai munyi. Yinwa kuwa ba a maganarta.
"Uwani nifa jikina ya mutu tunda akace Riyahd za a kawo mu. Domin ba haka mu ka yi da Hajiya Salamatu ba." BuWar bakin Uwani tace.
"Karma kiji komai Iyabo da Makka da Riyahd duk abu Waya ne. Kuma ?ila tana nufin a makka za a sama mana aikin wanke_wanken tunda mu ba zama mu ka zo yi ba." Sai data faWi haka sai na Wanji sanyi. Duk da dai zuchiyata a cike take da tsoro ainun.
Tafiya kuwa tun anayin ta marmari, har abun yazo ya gunduremu, tun cikin dare muke sharara gudu bamu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login