Showing 126001 words to 129000 words out of 270738 words

Chapter 43 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

tunzurashi wasu lokutan " Haka dai muka gama cin abincinmu, tana bani labari.
Bari inje in sami Yaya Hamma ina zuwa. Ki dinga lura da Dada."
Mi?ewa nayi na fice daga Wakin. A takure a wani benci na hango Yaya Hamma yana saye da wata koriyar suwaita ya tuttura hannayenshi duka biyu a ajjihun rigar. Yana hangoni ya mi?e.
Mu?u_mu?un sanyi akeyi musamman a wajennan, cikin dake akwai numfarfashi da yawa sanyin bai kai na wajen ba.
Isowa nayi inda yake da sallama a bakina.
"Ameen wa'alaikis salam babbar mace, ina mai farin cikin sake yin tozali dake a lokacin da banyi zato ba balle tsammani. Dan mafarkaina a kanki nuna mun suke yi kamar kin barni har abadane Wauke da nauyin da babu wata mace da zata iya sauke mun face ke. Barka da shigowa najeriya" idanu muka ?urama juna.
Wallahi soyayya duniya ne, jina nake tamkar akan yaya Hamma na soma soyayya a kab rayuwa. Son da nake yi mishi a yanzu ya doke son da nayi ma Burodami Debisi. Kazalika ya doke son da nayi ma Gwadabe. Illahirin jikina amsa sa?on soyayyar Yaya Hamma yake yi wanda yake isarmun ta cikin fararen idanunshi. ( Iyabo yau bake ba bacci dan su Khadija maidoki , m Farida Ammar, ummu nabeeha, maman yasser, maman Twins, Uwal matasa da sauransu sun isheki. Mamanmu Hajara Aliyu dai bansan ko zata yi muku uziri ba) A tarihi ansan Fulani da jarumta wajen nuna soyayyarsu ga mace, hakanne yasa kafin saurayi ya samu matar aure dole saiya fito filin shaWi ya nuna jarumtarshi kafin ya samu abokiyar rayuwa. Matansu kuma sunfi son jarumi ba lusari ba, jarumin da zai fito filin daga ya nuna bajintarshi.
"A ina al?awarin da kikai mun ya kwana. Ina fatan babu wanda kika mallakama zuchiyarki?" Idanu na lumshe bansan sanda nace dashi.
Babu wanda na bashi damar samun gurbi a zuchiyata Yaya Hamma. Na kasance mai girmamaka fiye da tunaninka." Wajen zama ya nuna mun da hannunshi. Dariya nayi mishi na zauna, shima ya zauna muna fuskantar juna.
"Bani labarin tafiya, da fatan kunci nasarar samun abinda aka fita nema ko?"
Alhamdulillah abinda akaje nema an samo. Da ba dan na shigo na tarar da Dada babu yadda take ba, dama da maganar siyan gida zan yi. In Wauketa daga cikin wahalar da take ciki. To Allah Allah ya yanke mata wahalarta, sai dai muyi fatan Allah ya bata lafiya "
"Ameen. Ba dai sayen gida ba, sai dai sayen fili ko? Yuguda yana harkar gini koshi zai gina mata Wan Wakin da zata yi rayuwarta, da Wakin du Cubu. Yusufu shi yana can gidan yana kiwo shi Baffa bazai bari ya dawo hannun Dada ba." Dubanshi nayi nace.
Filin yana iya kaiwa nawa Yaya Hamma? Dan da so samune so nake kafin a sallami Dada an gama komai sai ta tare a gidanta in Allah ya tashi kafaWarta, dan nasan ba zata amince ta bar mahaifarta ba". Dariya yayi mun yace.
" Tab ai mutuwace kaWai zata iya raba Dada da JaSSi lamba In akwai kuWi a hannunki filaye akwaisu, me gari zan samu ya nuna mun filayen dake ?asa sai mu siya yasa hannu a baki takaddarki, filin baya wahala har masu saye ake nema. Ko filin dubu talatin ya isa a fitar da Wakuna uku da tsakar gida da banWaki" Abinka da ?auye ni kuma a lokacin akwai kuWi a jikina sai nace.
To a nema mun guda biyu a waje daban daban Yaya Hamma zan siya" Kallona yayi yace.
"Me zaki yi da biyun?" Nima shi nake kallo nace.
Inaso zan ginane in ajjiye a matsayin kadara kudun kar kuWin su lalace" Sai yayi murmushi ya fuskanceni da kyau yace.
"In kina jin maganata A'a ba zaki siya ba. In kadara kike so ki sai shanu ko awaki ki ba Amaduyal ko Yusufu su dinga kaWasu jeji suna miki kiwonsu. Yanzu zaki zama Hajiya. Fili ko gida a ?auye irin namu bashi da wata daraja. Abin kiwonki kuwa kullum daraja suke sake yi, kuma ko da yaushe kika matsu zaki siyar da abunki ki karSi kuWinki ba tare da wani ma yasan halin da kike ciki ba" Jinjina kai nayi, na kuma yi na,am da wannan shawarar. Shirune ya biyo baya na wasu lokuta. Ko wanne cikinmu da abinda yake juya tunaninshi.
"Jabu" Naji ya ambaci sunana da wata iriyar muryar data tayar da tsigar jikina, wata kasalace ta sakko mun da ?yar na samu zarafin amsawa a hankali.
"Yanzu in Wan ?auye kamata yace zai aure ki kina ?ar birni kuma Hajiya zaki bashi dama ya aureki?"
Wayyo Allah daWi inji Sarawon takanWa a raina nace anzo wajen. A fili kuma nace.
Me zai hana in aureshi matsawar yayi mun? Zaman birni, da zuwa Saudiyya ba hujja bace da zan ri?e wacce zata nesantani da abinda nake so ba." Shiru yayi yana nazari can sai ya furta.
"Ina sonki Jabu. Tun lokacin da labarin mutuwar aurenki yazo kunnena naji kin kwanta mun a raina. Tsoro da fargaba su suka hanani fasa wannan sirrin. Amman abun mamaki labarin sonki da nake yi ya karaWe JaSSi. Jabu zaki iya aurena kiyi rayuwa dani kamar yadda matanmu suke rayuwa damu, zaki girmamani ki yi mun biyayya kamar yadda matanmu ke yi?" I
danuna na lumshe sanyi da nitsuwa suka ratsa zuchiyata da dukkan rassan jikina. Allah kawai nake ambato a zuchiyata.
Yaya Hamma tabbas nima ina sonka, mu ba ?ananan yara bane munsan menene so, haka munsan ?iyayyar itama. Amman me yasa baka sanar dani kana sona ba a lokacin da zan tafi Saudiyya ba?" Dariya yayi, ya dam?e hannunshi halamar yana cikin farin ciki.
"Wauta, da tsoron kar in faWa miki zumuncin da muke yi ya lalace, ni baki soni ba, kuma zumunci dani ma ki ?iyi. Amman ko a filin jirgi naso sanar dake kwarjini ki Kai mun. Amman na sanarma da Dada ?udurina kuma tasama abun albarka tayi farin ciki, babu mamaki ?ila sunyi maganar da Dadarmu amman bata ce mun komaiba kasancewar akwai kunya mai tsanani a tsakaninmu"
To naji. Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi. Amman wani hanzari ba gudu ba. Bazan Soye maka ba, zanyi maka dukkannin irin biyayyar da ba kai zato ba. Amman bazan iya Waukar tallar nono ba gaskiyar magana. Amman inaso zan dinga kasuwancin kaya tsakankanin ?auyannan, zuwa cikin gari, dan nayi sarin kayayyaki iri_iri. Amman batun tallar Nono babu shi, ka amince ko kana da ja?" Duk wannan maganar kaina a ?asa nake yi mai. Ya jima bai bani amsaba yana nazari can sai naji ya nisa yace.
"To Shikenan. Indai tallar nonone bakya so, to ba zaki Wauki tallar nono ba Jabu. Zanyi iyakacin ?o?arina na ganin na fahimtar da duk wanda zai kawo tsokaci.
Babu damuwa in Allah ya yarda, fatanmu Allah yaba Dada lafiya yasa albarka a cikin lamarin. Yau abinda ya tsaya mun cak zai barni in huta." Dariya nayi cikin zolaya nace.
Menene ya tsaya maka?"
Ya bani amsa da cewa.
"Baki ga na rame ba? Ai tunaninki ne kawai yaketa Wawainiya dani. Ko wajen aiki naje tunaninki baya barina inyi sukuni. Musamman in ina cikin daji da shanu, nafi ware lokaci na musamman ina hango irin rayuwar farin ciki da soyayyar da zamu gudanar a cikin Wakinmu. Jabu zansa ki mance duk rayuwarki ta baya nayi miki al?awari.'
Mun daWe sosai muna musayar kalaman ?aunaa dan nima ba'a barni a baya ba. Zagewa nayi na dinga zaro mishi zaren maganganun ?auna mai sanya nutsuwa da annashuwa. Daga ?arshe ya rakoni har ?ofar Wakin majinyata muka rabu kamar ba zamu rabu ba tsabaragen shau?in juna.
Na tarar da BaWWo tayi baccinta ta du?un?une da bargo. Dada ma sai baccinta take yi. Majinyatan Wakin kusan rabinsu duk sunyi bacci. Dada na zuba ma idanu ina mata sdda'ar Allah ya tashi kafaWarta taga aurena da Hamma. Ina ro?on Allah ya bata tsawon ran da zata goya Wana da zan haifama Yaya Hamma a bayanta.
A wannan daren in banda shau?i babu abinda ke Wibana. Tunanina yayi zurfi ya kaini har zuwa tsufana a gidan Yaya Hamma yaranmu suma sun girma, wai gamunan har a tsufan Yaya Hamma bai dena alfahari dani ba.
"Baiwar Allah " Naji wata mata ta ambaci sunana ashe ma'aikaciyar jinyace har ?arfe biyu tayi tazo sake ma Dada ruwan dake Waure a hannunta. Matsa mata nayi tayi aikinta, Dada dai bata farka ba, nima a haka bacci ya kwasheni zuwa asuba duk akayi waje damu, za'ayi shara a yi mopping kana a sake ma marasa lafiya zanin gado. A wannan rumfar muka haWu da Sumayya bayan munyi Sallah muka gaggaisa ssi take cemun.
"Bari inje in Waura girki kafin masu shara su gama gyaran Wakin jinya.
Girki kuma Sumayya, anan kuke girki?"
Sai tayi dariya tace.
"Anan nake yi. Gudun Waurama mutane wahala kinsan nace miki mun jima sosai a asibitin shiyasa. Bazai yiwu ace kullum sai an kawo muku abinci ba" Ksi na gyaWa maganarta gaskiya ne. Bakin ?ofar Wakin jinyar muks koma, muns zama Yaya Hamma yana ?arasowa.
Ina kwana Yaya Hamma?" Na faWa a ladabce fiye ma da na da. Shima ya amsani a mutunce fiye da jiya. Suka gaisa da BaWWo.
"Yaya jikin Dadan, ta farka kuwa?"
BaWWo ce ta bashi amsa"
"A's bata farka ba tukunna dai. Amman sunce zata farka yau"
Shirune ya biyo baya kowanne da abinda yake lissafawa a zuchiyarshi. ?arfe takwas daidai aka bads izinin masu kula da masu jinya zasu iya komawa. Tare muka shiga ciki mu uku. Dakta muka gani a tsaye a kan Dada yana dubata, wani irin amai take yi kamar zata amayar da duka hanjinta, harda jini_jini a cikin aman. Ba shiri wannan Dakta ya kira wasu ma'aikatan kiwon lafiya mata suka kawo gadon tura marasa lafiya aka Waura Dads.
"Zamu shiga da'ita Wakin tiyata da gaggawa, ku biyoni maza"
A gaggauce Dakta yayi maganarshi gabaki Waya hankalinmu ya tashi ganin halin da Dada take ciki. A bakin Wakin tiyata muka tsaya, Dakta yaima wata mace magana, shi ya shige da Dada ita kuma tace ni in biyota. Binta nayi ta bani takaddar sanya hannu da kuWin aikin a rubuce. Ta nuna mun windon da zan kai takaddar in biya, inna biya in dawo mata dashi.
Nafi awa biyu anata cuku_cuku na biya duk abinda ake bu?ata na dawo na tarar da su Yaya Hamma a bakin Wakin tiyatar sunyi jigum. Ga wasu iyalanma munzo mun tarar dasu jigum_jigum da halama wani nasu suma suke jira a fito dashi. Kamar awa guda da zamanmu aka buWe kofar Wakin tiyatar aka tu?o wata dattijuwar mace. Wannan iyalan suka bi bayan gadon suna hamdala. Da idanu na bisu ina fatan muma a fito da Dada lafiya cikin nasara.
"Jabu bari in fita daga harabar asibitin kar su Baffa suzo su tarar Dada bata Wakin jinya. Zan dinga le?owa."
Kai kawai na iya gyaWawas, ya wuce nabi bayanshi da idanu har saida ya Sace. Hawayen daya gangaro a kumatuna nayi saurin sharewa.
Awa Waya awa biyu muna dai zaune. Yaya Hamma na le?owa yana dubamu. Su Baffa Musa ma sun iso, da su Daso harda Hama. Amman su suna can wajen Wakin jinya suna jira. Baffa Musa ne kawai yazo ya dubamu. Ni a lokacin babu abinda nake yi sai kuka kawai. Awan Dada uku a Wakin tiyata Allah cikin ikonshi aka fito da'ita a gadon marasa lafiya. Muna biye da gadon ni da BaWWo mum ri?e hannun junanmu gam. Su Daso suna zaune a tabarma muka wuce ciki. Anyi sallama a Wakin sosai muma mun samu an mayar da Dada gado.
"Mun mata aiki cikin nasara yanzu jini zamu ?ara mata. Sai zuwa gobe zata samu farkawa. Tana farkawa kuyi maza ku kira Dakta, kar a bata komai taci. Allah ya ?ara sau?i"
Ameen mungode Dakta" Na amsashi. Ina zaune a kujera na tusa Dada a gaba sai hawaye nake zubarwa, zuchiyata tana Waci. A cikin wannan yanayin su Baffa Musa suka shigo suka riskeni BaWWo sai baki take bani.
Daso ta matso kusa daf dani ta ri?e mun kafaWa, mutum baida kama.
"Kiyi ha?uri Jabu. Ayi ma Dada adda'a Allah yasa anyi tiyatar a sa'a, Allah ya tashi kafaWunta."
Ameen Daso mungode, sannunku da ?o?ari" Baffa ma yace.
"Ayi ha?uri, ciwon uwa akwai Waga hankali. Kuma duk mai rai mamacine, in Daso shan ruwanta bai ?are ba ko ciwon da take ciki yafi wannan zata tashi. In kwananta kuma ya ?are tana gaWa tsabar lafiya saita faWi ta mutu, ayi ha?uri" Kai na gyaWa ma Baffa kawai. Hama cikin dakewa kamar ba itace wannan mai fara,arba tace.
"Sannu Jabu. BaWWo Allah ya ba Dada lafiya"
Ameen hama mungode sosai. Haihuwa kikayine?"
Dan na ganta da sabon goyo Wanye sharab. BaWWo ce tace.
"Haihuwa tayi gobe za'ayi suna. An samu mace"
Allah sarki Allah ya raya mana su." Na faWa a sanyaye. Yaya Hamma yace.
"Ki bata jaririyar ta ganta mana Hama" Da fullanci yayi Maganar, saida ta mayar mishi da amsa kafin ta sakko yarinyar ta mi?a ma Daso, ita kuma Daso ta mi?o mun. Bismillah nayi na amshi yarinyar a tsumman goyo, yarinyar na ?arnin nono. Zanin goyon na warin hammata . Dan hammatar Hama cike ma?il take da gashi har wani ja yayi da wani dattin fari.Yarinyar fara sol, ga gashi duk ya lulluSe goshinta da gefen kunnenta. Yarinyar takai minti biyar a hannuna na mi?a ma Daso ita.
Allah ya raya mana" Daso ce ta amsa, Hama kuwa bakinta ko motsawa baiyi ba.
"Jabu ga abinci mun kawo muku. Da yamma matar Amaduyal zata kawo na dare. Dadanmu tace zata zo da rana inta gama tallan Nono "
Da hanzari BaWWo ta buWe ledar abincin. Tuwon masarane da miyar kuka da nama a ciki. Ta zuba nata ta zauna ta soma ci. Ni kuma na haWe musu kan kwanukan jiya nasa musu a leda.
"To mu kam zamu tafi. Ni na bari ana dafa mun Nono"
Cewar Daso. Godiya muka yi musu. Baffa Musa yace shima kiwo zai tafi dan haka zai koma. Ya zaro dubu biyar ya bani yace in ri?e a hannuna.
"Nima zanje in dawo Jabu. Ba jimawa zanyi ba"
Cewar Yaya Hamma. Ledar kwanukan abincin jiya na mi?a mishi. Mu kai musu sallama suka fita. Ajjiyar zuchiya na sauke na zuba tuwonnan da nama yanka biyu. Babu maggi acikin miyar sai gishiri haka na tuttura na kora da ruwa yinwa nake ji sosai. Tea na haWa kofi Waya na kwantar da wannan tuwo.
Yaya Hamma baifi Awa uku ba ya dawo, ya dawo ya tarar an Waurama Dada ?arin jini. Mu kuma har munje munyi sallar azahar mun dawo muna zaune muna Wan hira ya shigo. Sannu da zuwa mu ka yi mishi. Wanka yayo dan har kaya ya sake da suwaita da hular sanyi duk ya canja.
"Jabu anfa samu gidan siyarwa. Abokinane zaiyi aure shine yayi gini. To auren yasha ruwa sakamakon wuta da uwargidanshi ta buWe. To shi yace da zai samu mai siyan gidan shi ko nawane daya siyar. Gidan babbane Wakuna biyarne, sai madafi da banWaki. To me kika gani?"
To Yaya Hamma in kana ganin babu wata matsala ai ni dama nafison in siya gida ba fili ba. Nawa kuWin gidan?"
"To da na nuna mishi ke zaki siya, yace mu kawo dubu sittin da bakwai. Amman yayi sau?i sosai ni dai nace sittin zamu biya. In yayi miki ki ?irgo kuWo yanzu sai in koma in bashi, gobe zaki ganshi ya ?aro shanu."
Jakata na zuge na ?irgi kuWinnan cas na ba Yaya Hamma.
"To saina dawo bazan jima ba" Yasa kai ya fice murmushi nayi na cikar burina, hatta wahalar da nasha domin tara kuWin da zan sa Dada murmushi ya zama tarihi.
Wajajen ?arfe biyar na yamma saiga Amaduyal da matarshi, da Jatau da Hari. Sun tawo dubiya.
"Amaduyal sai yanzu?" Na tambayeshi, shida ya dace sassafe ace ya tawo. Matar tashi ma sai yanzune taga damar zuwa, surukarta bata da lafiya"
"Baffane ya ri?eni Adda, kuma tun duku_duku yasani a gaba muka tafi kiwo. Kari kuma sai nace tayi abinci ta jirani muna dawowa sai mu tawo. Kiyi ha?uri Adda amman wallahi jiya ga Kari ko rintsawa banyiba. Tunanin halin da Dada take ciki ya dabaibayeni"
Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace.
To Shikenan Allah ya kyauta. Kaje ka dubo du Cubu kuwa, a wanne hali suke?"
"Naje, suna cikin damuwa sosai. Baffa dsi yana ?arfafasu, a bakinsu naji labarin anyi ma Dada tiyata"
Hari ta katse mana zancanmu ta hanyar gaisuwa. Jatau yace.
"Amaryarmu Yaya jikin Dada?' ?an dariya nayi mishi kawai. Hari sai zolaya take faman yi.
"Jabu wannan matar Amaduyalce sunanta Kari. Kari wannan itace yar Amaduyal"
Matsowa Kari tayi ta tsugunna muka gaisa tare da tambayar me jiki.
Jiki da sau?i Kari muna jiran farkawarta tukunna."
Sai Wa su Kari su kai magriba sannan suka Wau haramar tafiya gida. Nera dubu goma Amaduyal ya zaro ya bani. Jatau kuma ya bani nera dubu biyar. Sallama dasu suka tafi.
A hanyata ta dawowa daga sallar isha na hango Yaya Hamma daga nesa yana tafe kici_kici da manyan ledoji a hannayenshi. A gaskiya Yaya Hamma mai ?o?arine sosai. Tunda muka zo asibitinnan yake ta faman hidima damu, da ajjihunshi, da jikinshi, da lokacinshi baki Waya.
Bayan munyi sati guda a asibiti Jikin Dada ya soma yin sau?i duk da har zuwa wannan lokacin bat gane suwaye a kanta. Yaya Hamma ya koma bakin aikinshi a asibiti yake kwana ko za'a bu?aci wani abun, da sassafe saiya shirya ya wuce wajen aikinshi dama a cikin birni yake aikin.
Ni da BaWWo nakanje gida, in huta in yo mana girki sai in dawo, itama takanje ta wuni a gida ta dawo. Miyar stew nayi mana mai yawa sai muke siyan farar shinkafa dafaffiya a bakin asibiti, ko kuma mu sai biredi mu dangwala da miya tunda bama rabo da ruwan zafi, dan abincin da ake kawowa gashi ga kamarshi miya ce kamar an wanke kan mahaukaciya.
Anan zan dakata sai mu tara gobe in Allah ya nuna mana.

Assallamu alaikum mutanan kirki Ina Miko gaisuwa daftn alheri=?O??#? samun damar mallakar duk abunda kakyeeda bukata. Cikin sauki ta hanyi Yi muku adashin gata =؃??#? idan matsalarki rashin sabbin plates


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login