Showing 87001 words to 90000 words out of 270738 words

Chapter 30 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

da irin abincin da za'a dafa. Cikin sarewa nace.
Wai Mama dukka aikinnan ke kike yinsu ke kaWai?" Murmushi tayi tace.
"Shekarata biyar cib a gidannan ina aikin bauta. Ciwon baya, ciwon ?afa da ciwon sanyi duk sun kashe mun jiki. Aiki zaki zage kiyi KAN JIKI KAN ?ARFI dan basa son saiSi sai yanzu su koreki." Ajjiyar zuchiya na sauke, na shiga ruWu da tashin hankali sosai. Nayi dana sanin baro ?asata nace
Kuma tsawon awa nawa kike Wauka kafin ki kammala aikinnan har ki samu ki huta?" Dariya sosai wannan karon tambayata ta bata.
Mrs Bukhari


*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*

NAMA YA DAHU...
ROMO ?ANYE
BOOK 2

8
"Iyabo. Abunda nake so dake shine ki kwantar da hankalinki sosai kiyi aikin ki yadda ya kamata. Kije ki soma wanke bayan gidun falon ?asa dana nuna miki. Kiyi amfani da duk man wanke bayan gida dana nuna miki. In kin gama sai in koya miki yadda zaki yi shara da injin." Jikina a mace na gangaro ?asa. Da wani gansamemen Balarabe naci karo a falo. Yana ganina sai yace dani.
"Shayi" Yana mun halama da hannu da sha" Take na gyaWa mishi kai na jiya kitchen Win. Tea spices Takarofi ta nuna mini na dafa na kai mishi yana zaune akan kujera. Nan na shiga aikina. Sai da na wanke bayan gidu takwas, tun daga bango har ?asa. Ina fitowa na soma shara da injin Win shara, kafin in gama bayana ya ?age dan azaba. Wani ruwan fesawa Takarofi ta bani da tsumma, haka na dinga bin bangon gidan ina fesawa ina gogewa yana ?yalli. Na goge TV, TV stand, daining table da gilasan dake saman shi. Ina cikin haka na duba agogon falon naga lokacin sallah har ya gota. Gashi banyi wanke_wanke ba, ban Waura girki ba. Da sauri na koma Waki, Takarofi ta tare ni da cewa.
"Lafiya na ganki afujajan?"
Sallah zanyi" Agogo ta kalla, ta dawo da kallonta gareni tace.
"Kin Waura girkin rana ne Iyaba?"
A'a" Na bata amsa.
"Iyabo muje kitchen ki samu ki Waura girki tukunna, ko a kitchen Win sai ki yi sallah. Ni kuma zan taimaka miki da wanke_wanken. ?arfe biyar yaran gidan suke dawowa daga makaranta baki gyara musu Wakunansu ba,. Akan yarannan za'a iya korarki." Ni dai binta nayi zuwa kitchen Win. Sai da na tsayar da sanwar shinkafa kaza tsab sannan nayi alwala na shinfiWa Wankwalina na gabatar da sallah. Illahirin jikina babu inda baya yi mini ciwo. Amman haka na tashi ni ina gyaran kitchen Takarofi na wanke_wanke. Har dai girkin ya nuna aka juye a wata babbar kula ta silver, na jera komai a teburi. Kana na wuce Wakin yara, a hargitse kaca_kaca ina hawaye ina aikinnan. Sai da na gyara Wakin yara uku, ko wanne da bayan gida. Ina gamawa na faWa Wakin matar gidan na gyara, Wakin mijinma ni na gyara. Bayan sallar magriba kuma muka fita ta bayan gidan da tulin wankin ja'amar gidan, Takarofi na koya mun yanda zanyi amfani da injin wankin. Hannuna tsabaragen gajiya rawa suke yi. A wajen wankin na samu nayi sallar magriba, a wajen naci abinci. Bamu muka gama wanki ba sai dab isha. Ga girkin dare zan Waura, ga wanke_wanken abincin rana, falonma yaran gidan da samarin gidan duk sun lalata. Haka na kuma gyarawa na Waura girki kitchen Win nayi isha na jejjera kayan abinci a daining yaran gidan da matar gidan suna falon suna kallon wani shiri a talavijin. Ina shiga nayi sallar isha ai sai zazzaSi ya rabkeni, ko ina rawa yake yi a jikina abinci ma kasa ci nayi, Idanuna sai hawaye suke fitarwa
"Iyabo ?arfe tara tayi kije ki sama yaran gidan kayan bacci, samarin gidan kuma ki fito musu da kayayyakin baccin, ki kunna ma ko wanne Waki turaren wuta. Ga guga fa baki yi ba, ya kamata ki gama a darennan gobe ki tashi da aikin jerawa" Ai sai na rushe da kuka..
Haba kasheni za'ayi da aiki. Wannan aiki sai kace jaka" Kafin in rufe baki naji wata murya daga ?ofar Wakinmu ana ambaton Sheika( ma'ana tsohuwa) A zabure Takarofi ta mi?e.
"Taso Iyabo kinji daure" Da ?yar na bi bayanta naje nayi duk abinda ya dace na dawo. Ina zaune sai guga nake yi. Zuchiyata kuma ta lula tunanin Yaya Hamma, da irin yadda muka rabu muna masu begen junanmu. Idanu na lumshe ina fata da burin in zama mata a gareshi. Sai da na gama gugar nan tsab nayi wanka na kwanta. Abinci ma na kasa ci sam. Ina kwanciya wannan yarinya da Takarofi tace itama ?ar aiki ce sai gata ta shigo. Bata jin Hausa bata jin turanci sai yaren Senegal. ?ar senegal ce, sai gaisuwar kurame mu kai ma juna. Cikin bacci naji ana dukan kafaWata, zabura nayi na zauna. ?irjina sai bugawa yake yi dana ga namiji a tsaye a kaina. Murmushi yayi mun yace mun.
"Uridu an ashbu shayi ( zan sha shayi) Da Wata muryarshi mai za?in gaske. Na fahimci me yake cewa ta dalilin shayi daya ambata. A gajiye tulus na haura kitchen Win sama na je na dafo mishi shayin na kawo mishi yana zaune a falo. Ina harhaWe hanya tsabar bacci da gajiya haka na isa Waki na faWa gado ban sake sanin inda nake ba, sai da muka jiyo kiran Sallah.
"Iyabo maza yarannan kije ki musu wanka su saka kayan makaranta. In kika Waura abincin karyawa sai kiyi Sallah " Bani da zaSi haka dole na gabatar da abinda Takarofi ta faWa mini. A kitchen ma nayi sallah abina. Zuwa shida da rabi na gama jera komai a daining. Har matar gidan, da me gidan sun fito. Cikin harshen turanci na gaishesu, suka amsa mun da
"Sabahul Noor" Na juya na barsu nan. Da duku_duku na soma bi Wakuna ina jera musu kayansu a durowa. ?arfe Takwas batai musu a gidanba, masu zuwa aiki sun tafi, ?an makaranta ma haka. Tunda na shiga aiki banfa zauna ba sai ?arfe biyun rana na kammala komai da komai, sai guga data rage mun kawai. Itama ina idar da Sallah na shiga aiki. Yau babu abincin rana, sai na dare, na dai dafa ma yara ?an makaranta Taliya me kifi. Na cire musu kayan makaranta, nayi musu wanka, sai suka kwanta bacci. Ragowar abincin safe naci, farfesun kaza ne da dankalin turawa, sai dafaffiyar madara.
"Dake da ?warinki kinga har kin gama aikin ki ?arfe huWun yamma. Aikin yayi sauri sosai. Ina mayar da numfashi nace.
Amma Mama azabar tayi yawa. Wannan aikin ai dole ya illata jikin mutum, bautar tayi yawa. Ace in ka tsaya a tsaye tun duku_dukun asuba ba kai zaka zauna ba sai huWun yamma. Shima biyar nayi zaka tashi ka shiga hada_hadar girkin dare. Ba kai zaka samu kanka ba sai kusan sha Wayan dare." Takarofi tace.
"Wannan aikin shi ya fiye miki alkhairi. Duk yarinyar da bata zaune a gidan aiki, to yawon ta zubas take yi a gari. Kinga kuwa ai zaman gidan aikin ya fiye mata ko?. Sannan inaso in ja kunnenki in gargaWeki. Kinga gidannan akwai Samari har su shida majiya ?arfi. Kibi a hankali dasu, a kullum in zaki shiga Wakunansu ki yi adda'ar neman tsari Allah ya kareki daga sharrinsu. Dan suna shigo da matan banza cikin gidannan. Naga kuma ke yarinya ce, ki tsare darajarki tunda ba abinda ya kawoki ba kenan." Shiru nayi ina nazarin kalamanta hankalina ya tashi ainun, lallai ina cikik tsaka mai wuyar fita. Wannan ai shi ake kira gidan tara. Girman gidan na soma hasasowa, da yanda nake marar ?anci a cikin gidan. Taya zan ?waci kaina daga wannan sharri. Ni kaWai a gida sai samari garada, shin in ihu nayi wazai kawo mun Wauki ma?" Na shiga tsaka mai wuyar fita. Tunanina sai ya koma gida Najeriya. Bani da wani buri daya wuce in koma ?asata in ci gaba da rayuwa a cikin ?anci" Wannan tsoro da fargaba sai suka samu muhallin zama daram a tattare dani. A ranar dana cikata kwana bakwai a ranar Takarofi na tayata ta haWe kayanta tsab. Matar gidan tai mata goma sha tara na arziki. Ni dai ina kuka muka rabu da Takarofi. Damuwa da fargaba sai suka aureni. Na wuni ina bauta, da daddare kuma tsoro ya hanani bacci. ?ayan shashen na zuchiyata bashi da aiki sai begen Yaya Hamma. A duk dare da rana tunaninshi ne ke Wan bani wani nutsuwa da samar min da guntun farin ciki. A baya na faWa muku ni zuchiyata bata iya son abuba sam. Soyayyar Yaya Hamma muhalli sosai ta samu a zuchiyata. Dana tuno siririyar fuskarshi mai Wauke da fararen idanu take Sai inji ba?in ciki ya yaye mun. Amman fa son Yaya Hamma bai taSa matsayi da darajar Gwadabe a zuchiyata da rayuwata ba. Kawai dai ina ?o?arin binne sonshi ne in fuskanci al?iblar da take daidai. Ko da zamu dawo aure misali da Gwadabe, dole sai na auri wani namijin kafin hakan ta faru. Balle bana fatan Abinda zai sa in sake kai kaina inda basu san matsayina da kimata ba." Haka dai lokaci yai ta tafiya, tunani a ko da yaushe shine abokin hirana. Dan ni da Malika bama iya hira sai dai maganar kurame kawai, kuma in ta tafi Sangaren da take aiki bata shigowa Wakin baccinmu sai goman dare. A mugun gajiye take shigowa, to a haka ne muke Wan taSa hirar da bata wuce ta minti biyar ba.
Wasa_wasa watana uku a gidan aiki. Duk wata wahalar aiki, da hawa da sauka ta zame mun jiki. Kullum a cikin ciwon baya dana ?irji nake. Abinci wannan bani da lokacin da zan cishi a cikin nutsuwa, in aiki ya caSe mun ma sai in wuni banci komai ba. Gashi a cikin kwana biyunnan kullum sai Khalifa ya shigo Wakinmu da daddare. Sai ya taSa jikina a kullum in zai tasheni daga bacci. Dana soma bacci sai inji mutum a kaina. Shayi dai shayi dai. Da yana zama a falo ne in dafa in kawo mishi. Amman yanzu sai yayi komawarshi Wakinshi dole inna dafa in shiga in kai mishi. Kullum da mace a gadonshi, babu ranar dana taSa shiga banga mace a Wakinshi ba. Wataran tun daga ?ofa zanci karo da rigar mama da Wan diras a ?asa. Haka zan ajjiye in juya. Irin kallon da yake bina dashi shi yafi komai birkita lissafina. Dalilin da ya soma sani rama kenan.
Yau tun safe na tashi da faWuwar gaba da ?unci. Ko dana shiga kitchen Wora abinci sai na yi zaman dirshan na saki kuka. A mugun takure rayuwata take, zuchiyata babu daWi kaWaici na neman haukatani. Baka da wanda zaka yi magana kaji daWi. Baka da lambar ?an uwanka balle kaji muryarshi ko zaka ji sanyi. Akwai number Burodami Debisi, amman Uwani ta haWa a kayanta ta tafi dashi. Daga kaina naji ance.
"Maaza?" ( Menene) Ina Wagowa muka haWa ido da Khalifa. Ganin hawaye a fuskata caSe _caSe yasa shi saurin mi?i hannunshi yana son ya share mun. Da mugun sauri na mi?e na fita da gudu a kitchen Win. Baya na fita naje na saka wanki a injin jikina har rawa yake yi mini. Dana dawo kitchen Win na tarar baya ciki. Ajjiyar zuchiya na sauke, kana naci gaba da aikina. Sai na sake tsananta adda'a nice kullum cikin tsaiwar dare ina ro?on Allah ya tsare mun mutumcina, Allah kar yaba kowa damar iya tunkarata dai dai da maganar iskanci. Kullum cikin kuka da mi?a lammurana ga Allah. Khalifa bai daina shigowa Wakinmu tsakar dare ba. Sai dai kullum zai shigo ya same ni ko ina sallah, ko da carbi a hannuna dai.
Wasa_wasa lokacin sai tafiya yake yi. Yau da gobe rayuwa sai garawa take yi. Kamar wasa yau wata na shida cib a gidan aiki. Yau na tashi da farin ciki marar misaltuwa. Uwar Wakina ta f??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????aWamun tun jiya akan in shirya zanje ( Ijaza) Ma'ana zan tafi hutu can Riyahd. Tun safe na gama aiyukana tsab. Misalin ?arfe Takwas na Safiya muka kama hanya, harda Khalifa ni dashi muna bayan mota, Uwar Wakina da mijinta suna gaban mota. Zuchiyata a cike take dam fa farin ciki da Waukin son tozali da Uwani. Ko ba komai mayi hira muji daWi ai. Tafiya mu ka yi sosai, ni sai yau ne naga nisan wajan sosai. Muna isa bakin kofar gidan na gane gidanne. Khalifa ne ya mi?o mun wata takadda a cikin gidan saka wasi?a. Yaimun nuna da idanunshi akan in karSa. Hannu nasa na amsa ni dai jikina bai bani ba. Tare da ?unshin kayana dama nake. Sallama nayi da uwar Wakina anan take shaidamun nan da sati guda zata aiko khalifa ya dawo dani.
Cikin zumuWi nake ta haura benen, sai dai bayana wani irin ri?ewa yake yi tamkar bayan tsohuwar data gaji da duniya. Ina yi ina hutawa harna ?araso hawanmu. ?akin da Hajiya Babba take na soma shiga. Naje na sameta da ba?in wasu Larabawa da nake tunanin masu Waukar ?an aiki ne. A wula?ance ta amsa gaisuwata, abun ya dake ni sosai, domin wula?anci ba abin so bane.
"Ke kika matsa musu kina son kizo hutu ko? Dan uwar Wakin ki ta kawo ?ararki har sau biyu. Tace baki da aiki sai kuka. Dukanki suke yi, ko wani abun yaran gidan suke miki? Gashi naga kin lalace har kinfi kyau sanda kika tawo daga Najeriya" Duk wannan maganganun cikin Waga murya da harara take yinsu. Ajjiyar zuchiya na sauke tare da cewa.
Ina zaune tace in shirya zanje Ijaza, ni ba ro?o ba. Maganar kuka kuma damuwa da kaWaici ne suke sani kokawa, ai bawa ba'a iya rabashi da kuka. Imma na farin ciki, ko kishiyar hakan"
"To uwar tsari. To zan kirata inji Allah yasa ba sallamarki tayi ba. Kin samu gidan mutanen kirki, duk cikin ?an uwanki da kuka tawo daga Najeriya albashinki yafi nasu tsoka. Wata huWu ya rage miki ki gama biyan kamfani kuWinsu, daga haka kuWi zasu dinga zuwa hannunki ya rage naki kisan yanda zakiyi dasu." Jin wannan daddaWan labarin ya sani a farin ciki dan haka da murna na fita a Wakin zuwa Waya daga cikin Wakunan. Ina buWewa naga Hadiza na kwance tana hutawa. Ganina yasa ta washe bakinta.
"?ar halak kin ?i ambato. Ko awa guda Uwani bata yi da yin maganarki ba sai gaki" Zama nayi a katifar dake kusa da tata.
Uwani tazo kenan yaushe?" Na tambayeta.
"Ai inajin zata kwana biyar haka. Tama kusan komawaa da rabon zaku gana ne, ni gobe ma zan koma" Gaisawa mu kai da juna.
"Iyabo wannan rama haka. Kaddai kema a cikin tsaka mai wuyar fita kamar ni kike?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Hadiza a tsaka mai wuya nake. Ni fa a gidan aikin da nake ko baccin kirki banayi, sabida bargaba, ga aiki kamar zan mutu, bayana da ?irjina ciwo suke yi" Hadiza ta share hawayenta tace.
"Talauci da neman na rufa ma kai asirine ya kawo ni wannan ?asa. Akwai wata ?ar ma?otanmu bazawarace bayan ta baro gidan mijinta sai ta tawo Saudiyya aiki. Iyabo a cikin shekaru biyu kacal iyayenta suka sauya, mahaifinta har mota yake ja, gashi ta gyara musu gidansu. To shine mahaifiyata ta matsa mun akan nima in tafi, haka na bar mata yaron da nake goyo na tawo. A gidanma nike aikatau ina lura da marayun ?a?ana da iyayena. Sai gashi a gidan aiki saurayin gidan har wu?a yake nuna mun, akan sai na bashi haWin kai. To bani da zaSi dole haka na bashi haWin kai yake biyan bu?atarshi dani dan dole. Gashi ni bansan hanya ba bare in gudo. Iyabo na dawo Ijaza sai nake sanarma Hajiya Babba halin da nake ciki akan a sake mun gidan aiki. Hmm kar ki so ganin zagin tsaman naman da tayi mun. Da ?yar ta yarda akan za'a sake mun gidan aiki. Ni gobe zan kama wani aikin." Kukane da tausayinmu gabaki Waya yake shirin cin ?arfina. Ha?i?a na tausaya ma Hadiza matu?a gaya. Dan kawai kana aiki a ?ar?ashinsu sai su nemi tilasta maka akan abinda sun san haramcinshi. Taya yaron gida zai hakkema mai aikin gidansu, dan kawai ta tawo ?asar da ba tata ba, tana neman guminta?
Ya Allah ka dubi bayanka ka kawo mana Wauki. Allah kasan zuchiyarmu ba iskanci ya kawo mu wannan ?asa ba, neman kuWi ne ya kawo mu ya Allah ka karemu da karewarka.
Hadiza na tausaya mana duka. Ni kaina ayau ba sai gobe ba zan faWa ma Hajiya Babba inason sake gidan aiki. Tun kafin Khalifa ya samu nasarar keta rigar mutuncina. Yaron gidan da nake aiki ne yake kawo mun hari. Kullum bashi da aiki sai kawo kala_kalan ?an mata" Hadiza ta share hawayenta tace.
"Gara mu sake gidan aiki. Ko Allah zai sa mu yi dace da irin gidan da Maryam ta samu. Baki ga Maryam ba yadda tayi kyau ba. Gashi da zata tawo Ijaza sababbin abayoyi aka sai mata gwanin sha'awa" ?an murmushin tausayinmu na kuma yi.
Uwani ina suka je ne?"
"Hmm sun tafi mi?e ?afa da ganin gari ita da su Maryam. Uwani ma baki ga ramar da tayi ba, juyin duniya ta?i faWin matsalarta sai kuka ba dare ba rana" Ana cikin haka p'a ta rako wasu mata su huWu, ?an ?asata najeriya biyu, sai ?an nijer suma su biyu.
"Iyabo ijaza kika zo yaushe banga shigowarki ba?" ?an murmushi nayi na mi?e muka fita da p.a
Yanzu zuwana p.a Hajiya Babba ta sallami ba?inta kuwa?"
"E sun tafi yanzu haka ma Airport take son tafiya zata Webo ba?in Najeriya. Ince dai ba cewa zakiyi a sake miki gidan aiki ba, dan abinda Hajiya Babba ta tsana kenan." Kai na girgiza tare da cewa.
Gidan aiki kam zan canja, domin samun tseratar da mutuncina. Ni bazawarace ina da yara har uku, ga iyaye da ?an uwa. Ai bazan so in Webo musu abun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login