Showing 165001 words to 168000 words out of 270738 words

Chapter 56 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

wajen Babala ba"
Da haka sukai sallama zuwa gidan Zul?i. A harabar tabkeken gidan nashi suka zauna a wasu fararen kujeru me gadi ya shiga sanar mishi da zuwan na Bara'u. Bara'u ba ba?on gidan bane an saba ganinshi hatta ?an sandan dake tsare lafiyar Zul?i sun sanshi.
"Rigiji gabji lallai Zul?i yafa samu duniya ji gida ma malam, ji ma'aikata da masu tsaro, ga motoci har uku."
"Bafa kaga komai ba Gwadabe bari dai mu shiga cikin falon ka gani"
Me gadine ya ?araso inda suke yace.
"Hajiyar gidan tace a muku iso zuwa falonshi. Bacci ya tashi yanzu wanka yake yi zai zo ya sameku inya fito"
Tiryan_tiryan suka bishi har zuwa masau?in ba?inshi inda anan yake zantawa da ba?inshi irin masu unguwa, mai gari, da hakimai, da dakatai"
Masu aikin girki suka kawo kulolin abinci da filas na shan shayi da kofuna. Gwadabe sai karema falon kallo yake yi. Yana mamakin wai wannan gidan na Zul?i ne" zamansu baifi da minti talatinba sai gashi ya shigo yana saye da shadda wagambari Winkin tazarce. Baki ya buWe ya nuna Gwadabe da yatsanshi yace.
"Gwadabe yau kaine a gidana, to yaushe ma ka shigo garin?" Da sauri Gwadabe ya mi?e suka tafa da Zul?i suna dariya gami da farin cikin ganin juna yaushe gamo.
"Ranka shi daWe ashe rai kanga rai?" Zul?i yayi dariya suka zazzauna yace.
"Bara'u kaji Wan iska waini yake kira da ranka shidaWe. Ni Gwadabe kaida kake tare mun faWa nine ranka ya daWen?" Dariya suka saka Bara'u yace.
"Ai Zul?i ba zaka canja ba. Wai kai baka mantuwane dan Allah?"
"Ba komai ake mancewa ba Bara'u. Gwadabe ai mutumne harda Sari kai ka sani da sauran abokanmu da muka taso tare. Gwadabe wanne aiki kake yi? Bara'u dai ya tsokatamun matanka biyu kuna zaune a nijar gidan Baba Magaji wan Babala" Gwadabe yace.
"Hakane matana biyu. Sana'a anata buga_buga inayin ha?on zinare. Ina tallar magungunan karfin maza na gargajiya dana bature. Kaga irinsu"
Gwadabe yasa hannu a ajjihu ya Wauko wani ?ullin magani guda biyu, dana bature sacet Waya. Baki Zul?i ya buWe yace.
"Kusun uwa tafi da gidanka kenan. Gwadabe kaine ka zama mai siyar da maganin maza?" Sunfi minti koma sunata ?yal?yala dariya kamar waWanda suka ga wawan zama. Gwadabe yace.
"Wannan in ka zuba a tuwo kaci yajinnan Zul?i ko kakai shekara saba'in saika dawo Wanyen jini a wannan ranar, da miyar yau?i ake ci. Wannan kuma na baturene shayin maza ne. Ka juye a kofin shayinka ka shanye ranar ba'a magana. Gana dattin mara, amman shi yana sa gudawa sassafe kafin aci komai ake dafawa a shanye da tu?arshi. Ka jarraba amfani dashi zaka samomun kostoma" Bil ha??i Gwadabe yake musu bayani. Su kuma sai kwashewa da dariya suke yi.
"Ikon Allah kenan. Gwadabe zan jarraba in naga kyanshi niko zan haWaka da manyan mutane"
"Yauwa ni dama abinda nake son ji kenan. Ya batun iyali Zul?i, kuma wai ina katafi yawon duniya ne?"
"Iyali sunanan an tara. Na jima da yin aure yaranmu shida da matar dana aura a bariki ?ar garin bayalsa ce, tana da yare. Sai bayan na hau kujerar mulki saina auri yarinyar ?anwar Babarmu, sun matsa ni bama sonta nake yi ba, dan Jenifa ta taimakeni sosai a rayuwa. Can Bayalsa na yada zango. Dakone kwasar shara, kwata. Gwadabe babu sana'ar da bamba har Allah yasa na auri Jenifa to mahaifinta Wan siyasane babba. A wajenshi na koyi harkar siyasa shi ya wanke mun kai yace ai zan iya komawa ?auyanmu in shiga takarar chiyaman tunda ina da takaddar gama sakandare. Shine ?ashin bayana, Rabo kuma chiyaman daya sauka saiya tsayar dani na zama Wan jam'iyyarsu kaji abu kamar wasa ko?" Kai duk sukaita jijjigawa, dan shima Bara'u yaune yake jin wannan labari" Gwadabe yace.
"Yaya kake fama da Jama'a amma?" Sakkowa yayi yace.
"A zuba abinci muna ci ina baku labarin wahalar dake cikin kujerar mulki." Dariya su ka yi. Sunsan Zul?i tun yana yaro da zaran rana ta take lokacin cin abinci yayi ake nemanshi a rasa.
Bara'u ya bude kular abincin ya juye masar dake ciki dukka a faranti, ya kwarara miyar masar akan masar ya yaryaWa musu man shanu isasahe. Duk yayi muku komai suka tsoma hannu, saida Zul?i ya kai noma biyar kyawawa kana yace.
"Kujerar mulki bata da daWi Gwadabe sam. Hakkin al'ummar yankunku akanka kai shugaba ya rataya. Kowa jira yake kahau ya kawo maka bu?atarshi, kuma fa dole yake nufin wannan bu?atar ka biya mishi. Yanzu tafiyar da nayi akan yadda za'a samun hannu a takaddar tallafama manoma da taki ne. Satina fin nawa ina sunturi, masu ruwa da tsakin sun?i sa hannun." Ya dinga basu labaran yadda abubbuwan suke tafiya, da yadda ha?i?anin siyasa take. Sunfa jima suna hira a wannan gida basu ankara ba suka soma jiyo kiran sallar azahar. A banWakin falon su kai Alwala sun fito harabar gidan Zul?i ya shiga ya kira yaranshi maza uku suka wuce masallacin dake manne a jikin gidan ta waje.
A cike masallacin yake sosai kundai san jama'armu basai an karashe ba. A cikin masallacin Sai ga ?afa da kafaWun Gwadabe manne dana Yaya Hambali. Duk su biyun basu lura da hakan ba har saida gwadabe ya kalli ?afar ya gane wannan ai kafar Yaya Hambali ce. Da sauri ya Wago ya kalleshi a lokacin har an yi kabbara. Idanu suka haWa wani irin kallon tsana Hambali yake jefo ma Gwadabe idanunnan nashi cike dam da farin kwalli kamar yadda ya saba, a yanzu ma yafi rambaWawa sabida ya samu wadata. hannu yasa ya jawo wani saurayi daga sahun gaba ya sashi a gurbinshi, shi Win ya koma sahun gaba. A sanyaye Gwadabe ya Waga hannu yace.
"Allahu Akbar" Jikinshi sai rawa yake yi dai, haka gabanshi yake ta faWuwa har aka idar da sallar. Kallon saurayin dake kusa dashi yayi sai yaga Ashe Nazifi ne babban yaron yaya Hambalin. Sauke kai kawai Gwadabe yayi baya ma so ya kallesu zuchiyarshi ta idasa karyewa.
Shi dai yana gefe a zaune Zul?i yanata gaggaisawa da jama'a. Ya jima sosai kafin ya samu kanshi ya ?araso inda su Bara'u suke jiranshi. Gwadabe yana ganin yadda Yaya Hambali yake ta girmama Zul?i. Yayi ?iba ya sake kyau na musamman, fatarshi ta murje shi da Zul?i suka saje. A gaban idonshi suka fita shi da Nazifi.
"Kuyi ha?uri na barku. Haka muke fama da jama'a, kuma dole kabi dasu inba haka ba sai zagi da cin mutunci. Kuzo muje can gidansu Baba mu gaishesu*
Dunguma suka yi gidansu Zul?i aka gaggaisa akai zumunci. To su dai a gidan suka rabu dashi akan sai Gwadabe ya kawo matanshi sun gaisa.
Suna tafe suna tattauna abinda ya faru a masallaci sai gasu a ?ofar gidansu. Babala na daga ta cikin ?ofar gidan, Yaya Halima da Yaya Hambali suna daga ta waje. Gabaki Waya sai guiwowinshi suka sake ya tsaya cak shi bai jeba shi bai wuce ba. Kallon kallone ya shiga tsakaninshi da Babala na wasu sakanni. Ganin Babala ta ?urama waje Waya idone yaja hankalinsu Hambali suka juya. Daidai lokacin da Bara'u yake jayeshi.
"Ka daure kayi ?o?arin cinye jarabawarka Gwadabe"
"Daya daure da kar ya daure duk Waya. Tsiniwace a kanshi ai inya tako mana gida. Tuni muka tsame matsiyaci a cikin zuriyarmu. Karka sake matanka ko wata banzar tsarabarka ta shigo gidannan. Dan naga Sakina na zagaye da iyalanka" Cewar Yaya Hambali kenan, cikin ihu da Waga murya yake maganar tashi. Kuka Gwadabe ya fashe dashi Bara'u ya jashi suka koma gida babu ma kowa a gidan a tsakar gida suka zauna jigum_jiugm sunata jimantawa juna. Har akayi kiran sallar la'asar babu wanda yace da wani uffan har suka fito daga masallaci. A gindin bishiyar mangwaro suka zauna akan kututture.
"Gwadabe kayi ha?uri ka ?ara. Uwa ba abun wasa bace, ka kiyayi Babala karka cuci kanka taima baki. Tunda bata son ganinka ni kam in dan ta mune karka sake kawo mana ziyararma wallahi mu mun yafe Gwadabe ka zauna zamu dinga zuwa duk ?arshen shekara "
Gaga_gaga haka wunin ya kasance musu. Sai yamma suka samu shiga gidansu Shafa a tsakar gida suke a zube Abba sai kuka yake yi sabida zafi. Shafa tun rana take sa ran zuwan Gwadabe abincin rana ma data girka ma su Hadiza saida ta Webar mishi ta adana da taga har an Waura sanwar dare bai shigo bane ta cinye abincin.
Gaggaisawa akayo da matan gida, Shafa ta mi?o mishi Abba dake ta raraka kuka
"Kukan zafinne haka? Ga ?uraje duk sun feso mishi, me kike shafa mishi to?" Gwadabe ya tambayi Shafa.
"Hodar moju nake barbaWa mishi, bari in Wakko a kuma shafa mishi" Ta tashi taje ta Wakko hodar Gwadabe da kanshi ya shafe jikin yaron da hodar, baifi minti huWu ba yayi baccinshi a jikin Baban. Matan gidan sai suka tashi suka koma zaure dan cikin Waki gaskiya baya shiguwa. Tuwo Shafa ta kawo musu suka taSa dan sun san su Sakina ma suna can suna jiransu da abinci.
"Gwadabe dama ranar da muka zone saina shiga gida wajen Babala. To gaskiya abinda ya faru ya mugun Waure mun kai. Yadda Babala taci mutuncinmu, har Abba bata ?yale ba dan ashe an faWa mata sunan Baba yaci. Wai bata yafe ba da kasa sunan Baba.
"Ya'isa Shafa. Kuma kar in kuma jin bakinki akan wannan maganar.
To fa wata sabuwa su Babala manya.
MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI.
NAMA YA DAHU...
ROMO ?ANYE

BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI
LITTAFI NA UKU (8)

IYABO

Zuchiyata sai naji tana wani irin fusga. Labarin da BaWWo take bani ya jijjigani tsoro ya sake shigata sosai, ni dai har muka isa inda zamu hau acaSa ya fitar damu jere bonyo bance komai ba. A lokacin kawai na riga da nayi saranda na yarda Hama ta ruguzamun rayuwata. Muna isowa jere muka soma cin karo da matan ?auyanmu masu nono. Nan ?an gulmammakinmu na mata ya soma tashi, har a bayan akori kura wata ?awar Hama saida ta kasa ha?uri ta tambayi BaWWo.
"BaWWo hatsari yayarki tayi ne naga fuskarta a kumbure idonta ya tara jini ba?i ga bakinta a fashe?" ?agowa nayi na dubeta, na dawo da kallon nawa zuwa ga BaWWo.
"Zamewa tayi a bayan gida shine taji mummunan rauni asibiti ma zamu je"
"Asibiti a cikin ?auyannan ana zuwa asibiti dama?"
Ni dai takaina nake yi, dan ni a lokacin wallahi ji nake kamar kaina zai faWo, ga wasu jijiyoyi da suka WaWWaure a kaina sai nake jina wani iri haka. banma dawo hayyacina ba har saida naji motarmu ta kawo kan iyaka mun iso Girei.
Da ?yar na sakko jiki duk ciwo, ko ina yayi tsami ga ciwon baya ya far mun. Mun jima a titi kafin muka samu bus Win da zata shiga gari. Wayata na zaro a jakata na kunna a lokacin rawar Wari ma nake yi. Muna shigowa Adamawa kafin ma mu sauka na danna kiran wayar Uwani. Nako taki sa'a ringi biyu ta Wauka.
"Kaga Amarya ?ar gaban goshi, shalelen Hamma, yau an fito birni kenan?" Idanuna na lumshe hawaye suka zubo mun da ?yar na Wan saisaita nutsuwata nace.
Uwani ki ro?i Hafizu dan Allah ya barki kizo. Wallahi ina cikin matsala, abubbuwa da yawa sun faru yanzu haka mun shigo garine BaWWo zata kaini asibiti, zaiyi wuya su sakeni in koma gida ma yau." Sai na fashe mata da kuka duk na tashi hankalin Uwani.
"Shikenan Iyabo. Yanzu zan shiryo in tawo, zamu dinga waya har in iso. Kiyi ha?uri koma menene zanzo zamu samu mafita in sha Allah "
Wayar na datse ina share hawayena wasu na zubowa.
Ni hama zata sama wari a jiki, ta rabani da Hammana, to dama shi kishin haka yake, ko kuma a ?auyen haka suke nasu kishin na azaba? Ya Allah ka Wauke mun wannan lalurar warin da aka Wauramun Allah ka bi mun kadina" Idanu na runtse zafin idon daya tara jini har tsa?iyar kwanyata babu shiri na buWe. Motarmu ta sauke mu a bakin tasha, acaSa muka tare zuwa bakin asibiti. Muna bakin asibitin Uwani ta kirani motarsu ta baro kano.
Mu kuma muka shiga ciki, BaWWo ta zauna mun a layi ni kuma na buWe fayil na yanki kati. Akwai layi bana wasaba haka mukaita bi. Saida wata mace tazo wucewa ta ganmu a layi ta dubi idona tace.
"Likitan idanu kuke son gani, dan naga idanunki suna ciwo sai ruwa kuma suke zubarwa?" Nace da'ita.
E likitan ido nazo gani"
"To ku biyoni, nan ba Sangaren masu lalurar idanu bane. Kuzo muje" Haka duk uban layinnan da muka bi ya tashi a tutar babu. A baya mukaita binta har Sangaren masu lalurar idanun. To mun kuma yi latti, da ?yar wannan matar dai ta samu a layi dan taga idanun ya matsa mun. Mune har bayan azahar bamu shiga Wakin ganin likita ba, sai wajajen uku saura aka kirayi sunana. Baddo na barma jakata da wayata na shiga ofishin likitan idon. Izinin zama ya bani, ya Wago ya dubi idon da kyau kana yace.
"Me ya sameki, dukanki akayine, ko me ga idon yanata zubar da ruwa?"
FaWuwa nayi a banWaki shine na faWi idona da bakina suka daki gini" Girgiza kai yayi yace.
"Ashsha, Allah ya kiyaye gaba. Ga gado zo ki kwanta inason duba lafiyar idanun"
Bayan na hau gadon sai yaga jikina na wani irin Sari, ni kaina Sarin da jikin nawa yake yi saiya tsoratani. Ba shiri ya taSa jikina yayi wani irin mugun zafi, ni dai nasan inajin gadon dana kwanta yana juyi dani. Daga haka ban sake sanin abinda ke faruwa ba.
Ban sake samun kaina ba sai farkawa nayi naga ledar ?arin ruwa a hannuna. BaWWo na zaune a ?asa, Uwani na zaune a kan gadon da nake sun ?ura mun idanu.
"Ta farka BaWWo. maza jeki ki kirawo likita. Iyabo sannu yaya jikin?'
Uwani har kin iso ashe?" Da faWar haka saita soma share hawaye, murmushi nayi nace.
Ki dena kuka, tawa jarabawar ta wannan auren kishiyace Uwani. Wai yau nice a gadon asibiti, namijin da nafi sonshi fiye da kowa shi ya dokeni, banda wari da matarshi ta saka mun. Jarabawar da girma Uwani. Amman akwai Allah "
Shiru Uwani tayi ta kasa cemun uffan. Niko wani tawakkaline naji ya shigeni ainun, lammurana suna ga Allah.
"Tun jiya muke asibitinnan Hamma baizo ba, matar tashi ma bata zo ba ko le?e. Surukarki dai ta zo jiya sai wajajen magriba ma tabar asibitin. Dada kuma basu san halin da kike ciki ba,haka Baffa Musa, saidai Amaduyal ya sani. Kinga shi ya kawo mana abinci jiya, da safennanma shi ya kawo mana. Iyabo na tausaya miki. Amman wallahi kinsan Allah saina rama dukan da Hamma yayi miki a jikin figaggiyar matsiyaciyar matarshi?. ?ar iska ke da zaki zage ki ci ubanshi ko da asiri da kin matseshi gobe bazai tunkaroki da duka ba. Jibi yadda ya nakasaki fa Iyabo . Taya zan tsaya wani Wan ?auye jahili yaimun irin wannan dukan, wallahi ko ya fi karfina da cizo, da yakushi saina kwaci kaina, in haWa da hauka."
Idanu na lumshe kafin in buWe likita ya iso shi da BaWWo.
"Sannu Jabu. Yaya yanayin jikin naki kike jinshi?"
Ko ina ciwo yake yi mun. Kaina kuma yana matsanancin ciwo, ga wata jijiya da tai tsaye ta saman idon ciwo take yi mini"
"Ki nane idonki mai lafiyar marar lafiyar ki barshi a buWe"
Umarninshi nabi, amman me koda na toshe idona mai lafiyar na bar marar lafiyar a buWe dishi_dishi kawai nake gani"
"Kina iya tantance kalar kayan jikina?"
A'a gaskiya ba?i nake gani babu kala" Sai naji kuka na shirin kamani.
"To to Shikenan sake hannunki, ki biyoni zamu je Wakin gwaji, domin musan a wanne mataki ciwon yake. Karin ruwan dake hannuna ya cire mun" Uwanice ta taimakamun na sakko akan gado.
"Baddo ki zauna ki jiramu, zan rakata" Cewar Uwani kenan. Tare da'ita muka shiga cikin Wakin gwajin. Abubuwa mataki_mataki akaita bi. Har Abcd aka nuna mun a allo akace in karanta, in ban iya karatunba in ina ganinsu da kyau in sanar. Aka sakamun tabarau a idona, asa wannan a cire wannan, harda tocila saida aka haskamun idona likita sai tambayoyi kawai yake yi mun ina bashi amsa.
"To Shikenan zaku iya komawa. ?ila zamu sallameta zuwa anjima ko kuma gobe da safe" Jijjunanmu a mace murus muka dawo Wakin jinyar. Muka tarar da Yafendo ta zo."
"Jabu sannu da jiki"
Yauwa Yafendo sannu da zuwa, ai da kin yi zamanki"
Na zauna akan gadon kaina a ?asa.
"Ban isa in zauna ba, wallahi jiya ko baccin kirki ya kasa zuwarmun." Uwani tace.
"Haura ki kwanta Iyabo sabida yanayin jiki"
Sai data taimaka mun na kwanta, suka gaisa da Yafendo, ta tambayesu yanayin jikin.
"To kusan dai zamu ce ido kam ya samu matsala, dan inuwa take gani dashi. Yanzu haka daga Wakin gwaji muke. Sai dai muce Allah ya bata lafiya ya bata ha?uri dan matsalar idanu tana daga cikin manyan matsaloli kusan zamu iya kiranta mutuwar tsaye. Sannan fa Yafendo har yau Hamma ko matarshi babu wanda ya le?o asibitinnan. Ni cewa nayi sun san Iyabo bata da lafiya kuwa?" Salati Yafendo ta saki tana tafa hannaye.
"Uwani kina nufin Hamma baizo ya duba jikin Jabu ba?" Uwani tayi ?ar dariya tace.
"Baizo ba wallahi, kinga dai tun jiya nake asibitinnan"
Shiru Yafendo tayi ta kasa cewa komai harna tsawon muntuna masu dama. Har wata ma'aikaciyar jinya tazo ta mayar mun da ?arin ruwa, aka diga mun magani a idona. Har zuwa lokacin Yafendo bata ce komai ba."
"Jabu, cuta ce an riga an cutar dake tunda kome za'ayi a matsayin Waukar fansa ba zai goge wannan lulurar data sameki ba.
Amman ki sani wannan yaron bashi da laifi yi mishi akayi. Ita kuma Hama zan Wauki mummunan mataki a kanta matakin da hatta iyayenta bazai musu daWi ba. Dan Allah kiyi ha?uri kuma a rufe wannan sirrin bana so Daso, da Baffa Musa, da su A'i suji. Mu ha?a daku mu burne. Shi kanshi Hamman a hakan zaiga fishina da Sacin raina. Ina zuwa zanje wajen aikinsu in sameshi"
Nayi juyin duniya Yafendo ta bari karta je wajen aikin su Yaya Hamma, ko saurarena batai ba ta fice a cikin fishi tea Uwani ta haWamun.
"Tashi ki sa wani abun a cikinki. Ai gara ki bari taje Win. Duk da ana zargin farra?u akayi musu, baya nufin za'a zuba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login