Showing 21001 words to 24000 words out of 197828 words
Chapter 8 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
halittar da tsaraicin jikinsa, yana tsarkake jikinsa domin sirrinsa ne, amma yau da wanda ya dace da wanda bai dace ko wanne tom and jerry gani yake abin ya yi masa zafi ainun. Dalilin daya sanya ya amsa laifin kenan ba tare daya shirya hakan ba.
Mother na komawa gida ta samu Fattoumah na zaune ita ɗaya a Parlour da sauri Fattoumah ta ce "Mother ina Yaa Lee? Ba zai dawo ba?" Murmushi mother ta yi tana ɓoye damuwar ranta ta ce "Ya dawo mana Manana, yan gidan Abba Hakimi where's your sisters?" Da hannu ta nuna mata part ɗinsu, Mother ya kama hannunta suka shiga ciki. Yaran duk suna zaune sanye da hijabi sunyi shiru bayan sunci kuka sun ƙoshi, cikin faɗa ta ce "Maimoon, Zeefa what's this? Kuna da hankali zaku shigo ɗaki kuyita kuka kamar anyi mutuwa, Depression kuke son ya kamaku ko mene?" Gaba ɗaya suka miƙe tsaye jikinsu na rawa za su yi magana ta ɗaga musu hannu ta ce "Ku fita a nan wajan, maza aje a kunna kallo ayi" fita gaba ɗaya sukai jiki babu ƙwari mother ta bisu da kallo tausayin su na kamata tasan duk sanadin Aliyu Haydar suka shiga wannan damuwar. Kuma ita idan har ƴar halak ce ba zata sake zuwa wajan Father ba akan maganar Sheikh Aliyu ɗin ba.
Tana fitowa daga cikin bedroom ɗin upstairs ta haura zuwa nata bedroom ɗin wayarta ta ɗauka ta shiga kiran Barrister Zainab akan gobe zasu shiga Court sun daɗe suna waya kafin ta kira Yaya Halima anan ta kwantar mata da hankali ta ce ita ma ta nan zuwa dan sunyi nisa ne. Har Mother ta miƙe da sauri kuma ta koma ta zauna domin gaba ɗaya ta manta da batun Jadda cikin sauri ta danna numberta wayar ta jima tana ringing kafin a ɗaga a fusace akace "Allah dai yai gutsi gutsi da duk wanda yake addabata wannan masifar har ina, ba lallai mutum yaga Annabi ba" A hankali Mother ta ce "Jadda ni ce Maryam" Jadda ta ce "Wata abace Maryam kuma? daga wacce duniya mena haɗa dake?" Shiru Mother can kuma ta ce "Mahaifiyar Sheikh Aliyu" Jadda ta zabga salati da duk ƙarfinta ta ce "Yanzu Maryam cewa nayi ban gane ki ba? Masifar gaisuwa ce bana so, Ina shi Aliyu yana can Madina ɗin ne?" Mother ta ce "Baki san meke faruwa da shi ba?" Jadda dake kishin giɗe tayi saurin Miƙewa zaune tana faɗin "Allah ya isa, dake Maryam da shi Aliyu Allah dai ya isa wani abu ne ya samu Sheikh bani da labari?" Kafin Mother tai mgn father ya ƙwace wayar tare da kashewa baki ɗaya ya kalli Mother ya ce. "Yanzu Barrister akan wannan maganar zaki haɗani da Mahaifiyata? Su kike ta tsine mini tunda kin san bakinta ba shi da tsarki wajan sakin magana da kwasa ta" banza tai masa ba tare da ta ce komai ba, yana ƙoƙarin sake magana ta miƙe tsaye tana faɗin "Idan ka gama ka ajjiye mini wayata, I have something to do with my phone" tana faɗa ta shige toilet domin zuciyarta a kusa dake da shi. da idanu ya bita kana ya ajjiye wayar yana mmkin halin mata a wasu lokutan.
Gari na waye Barrister Zainab ta zo suka fita zuwa State C.i.d ita da Mother abin mamaki gaba ɗaya ƴan jaridu sun cika gidan Redio, da t.v kowa yana jiran a fito da Sheikh Aliyu Haydar Aliyu. Cikin nutsuwa Barrister Zainab dake driving ta kalli mutanan ta ce "Am still wondering ta ya ya zan can nan ya shiga kunnuwan Al'umma" Murmushin taƙaici kawai Mother ta yi wai duk akan Innocent son ɗinta ake wannan tururuwar kamar wanda ya kashe mutum?. "Allah ya kyauta, mutane akwai su da son gulma musamman ƴan jarida wallahi" I.d card ɗinta wanda ke nuna ita cikakkiyar lawyer ce mai zaman kanta ta nuna kana aka basu damar shiga, tun kafin Barrister Zainab ta yi parking idanun Mother ya sauka akan Sheikh wanda aka fito dashi cikin wata ƙatuwar sarƙa tare da wasu manyan ƴan fashi, wani abu ya tsaya mata wanda bata taɓa jin irinsa ba, ko hawaye ta kasa a wannan lokacin. Da sauri ta fita haka ma Barrister Zainab ɗin, ana ƙoƙarin saka Sheikh Aliyu cikin mota wata mota ta shigo da gudu cikin haraba wajan hakan ya sa duk suka daka ta. Wani babban jami'in tsaro ne tare da Abba Hakimi suka fito daga cikin motar sai wata matashiyar budurwa wacce Fuskarta ta kumbura sosai sbd kuka. I.G ya kalli jami'an tsaron cikin tsawa ya ce "Maza a cire sarƙar nan, a bawa Sheikh Aliyu Haydar Aliyu kayansa ya saka, He's Innocent ya fita daga jikin zargi, Wannan matar ita ce wacce ta shirya komai, she's the reason behind, She is the one who harmed Aliyu"
Gaba ɗaya kallon budurwar sukai wacce take kuka kamar ranta zai fita. A karo na farko Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ya ɗago idanunshi tare da sauke su akan budurwar wani irin lallausan murmushi ya sauke wanda ya kusan ɗauke hankali jama'a tare da basu mamaki, hatta Mother tai mamakin ganin murmushi a fuskar Aliyun. Cikin ƙaramin lokaci aka sakawa Sheikh wata jallabiya mai kama da Alkyabba tare da wani farin hirami nan da nan kamalarsa ta fito haibarsa ta cika Idanun kowa. I.G ya bada umarnin a kama budurwa Sheikh ya yi gyara murya yana tafiya a nutse cike da kamala tsayawa yai daidai inda budurwar take, for the first time a tsayin rayuwarsa daya tsaya gaban mace kana ya juya ya kalli I.G sanin cewa ba zai iya taɓa jikin I.G ba yasa ya kama hannun Abba Hakimi ya riƙe da kyau yana runtse idanunshi, ƙafarsa ya ɗaga ya buga a ƙasa cikin In-ina ya ce "Aahhhh ahhha abarta, dooo.. do.. domin ba ba ba....ba a faɗa da Aljani.
Not Edited
08119237616
🫰🏽kai tsaye ga mai buƙatar littafin.*🌈 IDAN BA KE 🌈*
*_Arewabooks@Nimcyluv_*
11.....
Abba Hakima ya kalli Sheikh a nutse yana mai sakin murmushi shi ma, tare da juyawa ya kalli budurwar wacce taƙi yarda ta kalli inda Sheikh ɗin yake, tun daga sama zuwa ƙasa Abba Hakimi ya ƙare mata kallo kafin ya ce "A'uzu bi wajhillahil karim, Wabi kalimaatil lahillati la yujawizuhunna barran wala fajiran, wabi asma'illahil husna kulliha, ma alimtu minha wa malam a'alam min sharri ma yanzilu minas sama'i, wa zara'a fil'ardhi, wa min sharri ma yakhruju minha, wa min fitnatillaili wan nahari, wa min ɗawariƙil laili wan nahari, illa ɗariƙan yadruƙu bikhairin ya Rahamanu. Wa min sharri kulli dàabbatin Rabbi akhizun bi nasiyatuha inna Rabbi ala siraɗin mustaƙim" jikin budurwar ne ya fara rawa sosai, tsoran Abba Hakimi da Sheikh Aliyu Haydar Aliyu suka cika mata zuciya, bata son su cutar da ita tunda ita bata zo da nufin hakan ba, kuma daman Ubangiji ya ɗora mata tsoran Sheikh ɗin tun ba yanzu ba, tana jin girma da nauyinsa tare da shakkar sa kwarjininsa yafi komai dagula mata lissafi. Idan ka ɗauke Abba Hakimi, No one understands the words of Sheikh Aliyu.
"No!!!"
Sheikh Aliyu Haydar ya furta a nutse yana riƙe hannun Abba Hakimi wanda bakinsa ya kasa yin shiru da addu'ar da yake, dalilin hakan yasa budurwar ta nemi birkicewa wanda kuma daga Abba Hakimi sai Sheikh ɗin ne kawai suke ganin hakan. Shiru ya yi da addu'ar yana kallonta kafin ya juya ya kalli Sheikh fuskarsa ɗauke da annuri irin na cikakkun dadtawan nan ya ce. "Yaushe Aliyu ya samu abokai haka bani da labari" a wannan karan Sheikh bai murmushi ba sai rirriƙe hannun Abba Hakimi da ya yi yana lumshe idanunsa tare da buɗewa alamar "Bai san yadda akai hakan ya faru ba" riƙe hannu Sheikh ɗin kai tsaye Abba Hakimi ya yi domin kai tsaye ya fahimci karatun idanun na Sheikh.
I.G dake tsaye shi da Barrister Maryam yana bata haƙuri ya ce.
"I'm sorry, action was taken without investigation, we were wrong" kasa riƙe kanta mother ta yi cikin losing control ta ce. "You have defamed Sheikh's name, all those who respect him have now stopped, Sbd Kuskuren ku my son is innocent na riga dana faɗa muku, but you refused to understand me" Bar Zainab ta numfasa cikin rashin jin daɗi ta ce "Everything that has happened has already happened, kawai a kira ƴan Jaridu a shaida masa Sheikh bashi da laifi, sharri ake masa bai san komai ba a wanke sunan shi daga ɓacin da ya yi" cikin martabawa da nuna rashin daɗin abin da duk ya faru I.G ya ce.
"Aikinmu ne hakan, za muyi abin da ya dace muma ba zamu so sunan Sheikh ya lalace ba yana da girma da daraja a idanun ba" Mother gaba ɗaya haushin duk wasu jami'an tsaron take ji hakan yasa cikin sauri ta juya zuwa inda Abba Hakimi da Sheikh suke tsaye, idan ka gansu zaka ɗauka da gaske Hakimi shi ne ya haifi Sheikh sbd tsananin haibar dake maƙale a jikin ko wanne kusan duk halin Hakimi Sheikh ya kwashe shi tas.
Kallonsu ta yi cike da son ko wanne wanda ke rinjayar zuciyarta ta ce "Thank you Abba Hakimi" murmushi kawai ya yi bai ce mata komai ba, tana ƙoƙarin sake magana ya yi saurin barin wajan zuwa cikin motar da Umar-khan ya buɗe masa baya.
Tsaye Sheikh yana bin mahaifiyar tasa da kallo ganin tai shiru ya waro mata manyan Idanun shi yana son cewa wani abu amma ya ja bakinsa ya yi shiru a hankali ta ce "zaka bini ko Abban naka za kabi?" Bakinsa ya motsa yana rufe idanu tare da fara buga ƙafa yana riƙe jikinsa da kyau cikin In-ina ya ce "Zazzzza... zan zan zanje gida wajan fa... fa.. father ina soooo son ganinsa"
haushi ne ya kama Mother ganin duk abin da ake Sheikh yana maƙale da son mahaifinsa. "Father baya gari, kaje wajan Hakimi ka huta da kyau gobe sai kazo mu tattauna, ina tunanin za a haƙura da zuwa Madina haka" girgiza mata kai ya yi bai ce komai ba ya juya ganin har lokacin Abba Hakimi na zaune bayan motar, yanzu zuwa shima ya shiga baya Ishaq-hakim ya jasu. daga nan Bar Zainab gidanta ta shige hakan yasa Umar-khan ɗaukan Mother a ɗaya daga cikin motocin Sheikh suka nufi gida, Saif-Wazir kuma ya tsaya domin magana da ƴan jarida.
Suna tafe a hanya Sheikh na yiwa Abba Hakimi hira cikin nutsuwa duk da In-ina yake amma Hakimi na fahimtar komai da Sheikh ke faɗa, a duk maganganun Sheikh ba za kaji kalmar MACE ta fito daga bakinsa ba, balle har ya ware wata musamman yana magana a ganta, Murmushi kawai Hakimi yake Ubangiji ne shaidar son da ya kewa Sheikh a jinin jikinsa yake.
A haka suka ƙarasa haɗaɗɗan gidan Abba Hakimi dake Dawaki roud, gida ne irin na sarauta mai kyan tsari da fasali ko'ina ma'aikata ne , motar na tsayawa Sheikh ya fito ƙwayar idanunsa na nuna gajiyar da yake ciki.
Bai tsaya jiran Abba ba, kai tsaye ya nufi part ɗinsa wanda yake cikin gidan Abba Hakimin wanka ya yi da ruwa mai zafi yana gamawa ya fito ɗaure da babban towel idanunshi na janye wa barci na cin ƙarfinsa ya ɗauki wani tsadaddan lotion, Shea body butter ya shiga shafawa saman fatarsa a kasalance, Engage Cologne Spray ya fesa a fatarsa sbd ɗauke zafin da ya keji yana gamawa ya miƙe zuwa clothes ɗinsa ya ɗauki wani trousers mara nauyi ya saka ko riga bai saka ba, ya cilla mint bakinsa ya kwanta saman bed yana lulluɓe jikinsa da bargo, ganin rana ce ya sa ya kunna A.c tare da rufe idanunshi cike da fatan barci ya ɗauke shi.
Washegari gari tun da Sheikh ya farka bai koma barci ba, har ya fita sallar Subhi sai da gari ya yi haske wajan 6:30 ya dawo gida jikinsa duk ciwo yake masa sbd rashin gym da bai ba, wanka ya ƙara yi ya shirya cikin Scabal wool suit white colour sai red ɗin necktie. Sai Diamond Rolex daya maƙala a hannunsa, yau a Yaa Lee ya fito ba a Sheikh ba, domin kusan siffa biyu gare shi, idan zashi bank shigar suit yake duk abin da ya danganci addini ajjiye shi yake a gefe amma yana zuciyar shi, idan kuma ya sanya Alkyabba da rawani yana matsayin Sheikh a wannan lokacin ne ba Yaa Lee ba. Wayarsa ya ɗauka jacket ɗin sa a hannu cikin nutsuwa ya fita zuwa main parlour.
Ƙamshin ROJA shi ne ya fara kaiwa su Abba Hakimi ziraya yana zaune da jallabiya gefensa kuma Ishaq-hakim ne da Saif-Wazir shirya zasu shi wajan aiki, sai Momi A'isha tana zubawa Abba Hakimi Shayi mai zafi. "Mrng Yaa Lee" jinjina kai ya yi idanunshi akan Abba Hakimi ya furta. "B...bar bar barka da safi fifi fiya".
"Ya ka kwana? da ciwon kan?" Rufe ido ya yi tare da buɗewa alamar "Allahamdulillah" Momi A'isha ta amsa gaisuwar Sheikh ɗin wacce ya yi mata ita cikin In-ina, tea ta haɗa masa mai zafi ta zuba 2spoon na honey ta juya kaɗan tare da bashi. Amsa ya yi a kame yake shan tea ɗin yana sauraran maganar Abba Hakimi da yake ce masa "komawa Madina ba yanzu ba, kada ya fara tunanin hakan" sanin ba zai iya ja da maganar Abba Hakimin ba yasa ya miƙe yana ajjiye cup ɗin hannunsa, Ishaq-hakim da Saif-Wazir suka miƙe tare da bin bayansa, wata farar mota ya shiga mai Sheikh no 5 yana shiga driver ya ja. Ishaq-hakim da Saif-Wazir kowa ya shiga motarsa suka nufi S.A.H BANK.
tun kafin ya Ƙarasa cikin bank ɗin wanda ya kasance mallakinsa ma'aikatan bakin Sheikh Aliyu Haydar bank suka shiga mutuwarsu ƙwarai. miƙewa ake ana gaida shi hannu kawai yake ɗaga musu har ya shige wani baban office. Wunin ranar Sheik cikin duba files and Ducoments yake.
3:30 yana ƙoƙarin barin Office ɗin saƙon father ya sauka Wayarsa. Da fararen idanunsa yake bin message ɗin da kallo yana mamakin yanzu kuma kiran gaggawar mene?. Da wannan tunanin ya shiga mota Driver ya ja suka nufi unguwar su Sheikh.
Tun a harabar gidan ya san akwai matsala domin kai tsaye idanunshi ya sauka akan motar Abba Hakimi data Yaya Halima sai ta Uncle Haroon.
Ƙamshin turarensa ya bayyana zuwansa, Mother dake zaune saman Kujera yana kaɗa ƙafa ta kalle shi kafin ta ɗauke kai, Uncle Haroon ma kallon Sheikh ɗin ya yi, a kame ya ƙarasa kusa da Abba Hakimi ya zauna yana ɗauke idanunshi daga kan jama'ar daya rasa meeting ɗin me ake.
"Tun da Allah ya kawo shi sai aji ta bakinsa, amma Sheikh ya shige lokacin da za a yi masa auren dole, a baya ba ai masa ba balle yanzu?" Yaya Halima ta furta cike da jin haushin father. Shi ma father da zuciyarsa ke kusa ya ce.
"Bashi da amfani, domin ba zai faɗi abin da kowa ke buƙata ba, na daɗe da sanin cewa Aliyu shi ne ƙaddarata, shi da yake namiji wanda ya kamata ya tsaya kan dukiyata amma ya kasa hakan, duk mutanan da suke buƙatar contract daka gareni idan har suka ji yadda Aliyu ke banzar maganar shi suke contract In-inar Aliyu ta ja mini asara mai yawan gaske, don haka ni bashi da amfani a gareni" sai a yanzu suka fahimci rashin jituwar da babu tsakanin father da Aliyu cikin ladabi Abba Hakimi ya ce "Baka yarda Ubangiji ya ɗorawa Aliyu wannan larurar ba? kenan baka alfahari da Aliyun matsayin ɗa?" Cikin sauri Father ya ce "Aliyu bai taɓa yi mini rana ba, to akan me zan yi alfahari da shi? Idan yana so mu shirya dole ya daina wannan In-inar ko kuma ya yi aure cikin satin nan"
"Aliyu akwai wacce ka ke so ne?" Sai a lokacin Sheikh ya kalli Uncle Haroon yana runtse idanunshi zufa na yanko masa a ƙoƙarin shi na ganin ya yi magana babu In-ina amma ina ba zai iya ba ƙaddarar shi ce hakan.
Cikin fitar hayyaci yana rirriƙe jikinsa da kyau tare da buga ƙasa da hannun kujera ya ce "ba...ba ba bana son son kowa uncle.. ba ba bazan iyyyya zama dadda da mace ba" shiru duk sukai baƙin ciki ne kuma ya hana mother magana. Father ya ce "Ok good a Sbd haka ka shirya zama da Zahrah ƴar gidan babban aminina, cikin satin nan za a yi aurenku kai da Zahran babu fashi" miƙewa Mother ta yi cikin faɗa ta ce "Wallahi Aliyu kayi kaɗan ka saka Sheik ya auri wannan Yarinyar da ban amince da tarbiyyar ta ba, me Sheikh zai da ita? Yarinyar da take kusan sa'ar shi kaɗan ne babu ta girme shi ba? duk shekarun da Aliyu ya yi babu aure sai kuma ya ƙare wajan tsohuwa, ban amince ba kuma ban yarda ba, ka bawa Aliyu duk wacce kaga dama amma ban da Zahrah" murmushi father ya yi ya ce "Idan har ni ne uban Aliyu ba wani ba? Ya zama dole ya auri Zahrah idan kuma bani ne mahaifinsa ba sai ki bashi wacce kikai niyya Barrister Maryam" hawaye ya cika Idanun Mother ta ce "Oh yanzu kuma sheganta Aliyu zaka fara bayan zarafinsa da ka ke ci akan larurarsa?" Banza father ya yi mata. Uncle Haroon ya numfasa ya ce "Engineer Aliyu Wannan bai kamata ba, idan kana so Aliyu ya yi aure,Let him choose the woman he wants to marry himself, ka sassauta yanayin da ka keji game da Aliyun" Father ya ce "Abu ɗaya ne zai kawo Shira tsakanina da Aliyun shi ne auren shi da Zahrah idan bai amince ba yaje na zare hannuna daga Lamarinsa kuma ya zare sunana a matsayin Uba" Dakawa Father tsawa Uncle Haroon yai ya ce "Wai Aliyu wanne irin banzar magana ce kake haka? Ni da kai na zan iya samawa Aliyu matar aure, ka daina ganin kai ne ubansa ni ma uba ne a wajansa, ga kuma babban Uba hakimi duk mun isa mu tsayawa Aliyu, ka daɗe baka cire hannunka ba, kuma wallahi ka sake na rabaka da Aliyu ka rabu dashi kenan har abada" Girgiza kai Abba Hakimi ya yi ya ce "Ba za a yi haka ba Haroon, haƙƙin Aliyu ne samawa Sheikh