Showing 42001 words to 45000 words out of 197828 words

Chapter 15 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9290

da sauri. Surayyerh ta ce "Kaya ne, na kawowa ƙanwata Halisa ta fara amfani da su kafin mu tafi da ita" Dada ta kasa cewa komai domin tana ganin tafiya da Halisa wani wajan ba ƙaramin babban ƙibi bane a rayuwarta, kuma ba zata jure kalar rayuwar da suke ba, Halisa tana da saurin baki bata da haƙuri wani lokacin kana yi mata take maka zafin rai gareta. Surry ta ce "Anjima Dr zai zo, zuwa anjima ko da safe zamu zo mu tafi da Halisa ɗin, akwai wani Sani mai p.o.s a wajan shi zaki dinga karɓar kuɗin aikin Halisa na duk shekara, zan baki number waya koda kina buƙatar jin muryar yarinyar ki sai ki bawa mai p.o.s ɗin ya kira, gaba ɗaya aikin shekara biyu zatai...." Da sauri jikin Danejo na rawa ta ce "Wallahi ba inda zani, ba zan biko ba taimakon da ku kaiwa Dadata Allah ya saka ni dai ba zani ba daman wayo nayi muku dan ku kai Dadata asibitin burni...




Pay before you read.... IDAN BA KE it's paid book 500. Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616.... Don Allah kada a fitar😒😂.




SARAUTAR MARUBUTA"Subuhanallah yi haƙuri bata kula ba" Surry ta faɗa da sauri tana kama hannun Halisa ba tare data bari ta buɗe liƙab ɗin ba. Ita dai Halisa kallon Yaa Sheikh take kamar idanunta zai faɗo ta cikin liƙab ɗin.
Yaa Sheikh ya ratsa ta gefen Halisa zai shige tayi saurin shan gabansa tana kwace hannunta, duk da ta tsorata da yanayin shi amma bai hanata ƙara binsa da idanu ba da ƙarfi ta ce.
"Laa Wallahi shi ne, Balarabe ashe zan sake ganinka?" Dam! Zuciyar Surry ta buga, Umar-khan zai magana Abba Hakimi ya girgiza masa kawai alamar yai shiru.
A wannan karan ba Yaa Sheikh bai kalli yarinyar dake gabansa ba, sai ƙara ɗauke idanu yake gefe guda, ganin yadda ya yi mata ya sanya Halisa ta saka hannu ta cire liƙab ɗin tare da matsawa gaban Yaa Sheikh ta ce "Baka gane ni ba? Nasan ka gane ni ni ce fa Halisa Danejo Rome ka manta ni?
Ina kaje bana ganinka?" Tarin makami da ya yiwa Saif-wazir yawa ya sanya ya hangame baki, anya yarinyar nan ba aljana bace ko kuma wacce Aljanu suka shafa?.
Khalil Ahmad Sarki ya juya da sauri ya kalli El-bashir dake can gefe ɗaya yana waya, ya ƙara juyawa ya kalli Halisa wacce ɗan ƙaramin bakinta ke motsawa tana yiwa Yaa Sheikh rantsuwar Wallahi ya gane ta yana sani yaƙi kulata. Ahmad Sarki da har yanzu yake kallon Danejo sai ya juya ya kalli El-bashir makami kamannin su na rikita masa lissafi musamman da yaji muryar Danejo wacce take iri ɗaya data El-bashir sak! Sai dai ita ɗin macace saɓanin El-bashir da yake namiji. "The wonder never ends" Khalil ya furta a fili na dafe kansa.
Danejo ta ce "Yanzu baka gane ni ba, nice fa? har ka taɓa bani mangoro?" Yaa Sheikh ya ware fararen idanunsa sosai tare da sauke ganinsa akan zagayayyiyar fuskar ta, kai tsaye ƙwayar idanunsa ta shiga cikin nata. Danejo ta haɗiye sauran maganar sbd idanun Yaa Sheikh da sukai mata kaifi, a kallo ɗaya da ya yi mata ya saka mata shakkar shi, tsoro da kuma ganin girman shi. A hankali ya zame hannun yana mai barin wajan Danejo ta bisa da idanu..
"Kin san shi ne?" Danejo ta kalli Saif-wazir kamar zatai magana sai kuma ta murguɗa masa baki Surry ta kama hannun ta suka shige cikin gidan su Zahrah.
Saif yai dariya son ran shi ya ce "Akwai rigima Yaa Sheikh za ai raino" Khalil Ahmad Sarki ya daki kafaɗar Saif ya ce.
"I couldn't understand, wai wace yarinyar nan? Na ruɗe fa" Saif ya ce "wato abinne gaba ɗaya is complicated, muje mu zauna" Ya juya zuwa ga Abba Hakimi wanda ke sauraran su ya ce "Abba ita ce ƴar fillon da nake baka labari"
Abba Hakimi ya jinjina kai cikin nutsuwa ya ce "Ikon Allah ya kamata mu zauna, Umar-khan maza kira mini Barrister Maryam a waya" Umar-khan ya ce "To Abba" Abba Hakimi ya yi gaba Saif-wazir ya bi bayan shi, Umar-khan ya tsaya kiran Mother a waya.
Khalil Ahmad Sarki ya nufi inda El-bashir yake tsaye ya zuba hannun shi cikin aljihun wandon shi ɗaya hannun yana shafa sumar kansa.
"Kaga abin da na gani kowa El-bashir?" El-bashir ya juya zuwa ga yayan nashi kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce "A'a duk an cika waje da ihu me zan gani haba kun zama kamar wasu mata" Khalil ya ce "let's keep a joke a side wata na gani mai mugun kama da kai" El-bashir ya nuna kansa yana fiddo idanu waje ya ce "Ni kaga me kama dani?" El-bashir ya tambaya yana gyara tsaiwar shi. Khalil Ahmad Sarki ya ce "Ai kamannin har sun ɓaci hatta beauty point da gashin girarka daya rabe biyu, hatta muryarku iri ɗaya ne El-bashir na girgiza" a karo na farko El-bashir ya yi murmushi kawai yana girgiza kansa ba tare da ya ce komai ba, hakan ya fusata Khalil ya ce "Ya ina magana akan abu mai muhimmaci kana dariya?" El-bashir ya jingina jikin mota baka iya gane yanayin shi ya ce "Me zance Abu Juwairah? Kawai kun haɗu da aljana banda haka ina za a samu wata mai kama dani? ni ba ƙanwa ba ni ba ƴa ba, Please mu bar wannan maganar" Khalil zai magana wayarsa ta shiga ringing ganin matarsa ce Oum Juwairah ya sanya yabar wajan yana amsa sallamar ta.
Tunda suka shiga ɗakin Danejo bata kalli inda Zahrah ke zaune ba, kanta a ƙasa ta haɗe fuska sosai. Zahrah gabanta ya faɗi ganin yadda cikin kwana biyu Halisa Danejo ta sauya kamar ba ƴar fillo ba, fatar ta na ƙyalli ko'ina na jikin fes yake duguwar rigar da Surry ta bata ta saka mai purple ta amshi jikinta sosai.
Surry ta ce "kina ta kallon ƴar fillo kamar baki san taba lokaci na shigewa" Zahrah ta sauke numfashi ta ce "Kada dai ki mata matsayin mai aikatau zaki cikin gudana ƴar fillo" Danejo ta ɗago kai ta kalli Zahrah cikin sautin siririyar muryar ta ta ce "Ban manta ba, sunana Halisa Danejo Rome ba ƴar fillo ba" Zahrah taja tsaki ta ce "Ji banza ina cewa a cikin ruga muka ɗakko ki? Banda warin shanu dana Kindirmo me kike? Har kece za kice wai ke ba ƴar fillo bace?" Danejo ta shiga kallon Zahrah zuciyarta na jin zafin maganganun data faɗa mata idanunta har ya cika da ruwan hawaye saboda ba zata iya mayarwa da Zahrah magana ba bisa umarnin Dadarta.
Surry taja gefe guda tana murmushi jin daɗi ba tare da kowa ya lura ba, ita kanta baza taso tun yanzu Halisa ta fara mayarwa da Zahrah magana ba. Cikin sauri ta ce "Zahrah dama shiryawa ki kai yanzu 1:30 ance 2:00 daidai jirgi zai tashi" Zahrah ta miƙe ta ce "Ina son haɗuwa da Deen wlh kwana biyu bana iya barci Surayyerh abin cikina masifa yasa mini ba zan iya jurewa ba idan ban samu abin da nake ba dole naje naga Deen" a fili Surry ta ce.
"Wallahi baki da tunani Zahrah ganin Deen a halin yanzu bai dace ba kuma nasan abin da zaku aikata" a zuciyarta kuma ta ce "Well-done Zahrah ban fatan ki daina bibiyar maza tun yanzu" Zahrah ta ɗauki hijabi tare da juyawa ta kalli Surry ta ce "Meye sunan abin da kika bawa yarinyar nan ta saka bani" Surry ta amshi liƙab ɗin hannun Danejo wacce ta haɗe rai sosai taƙi yarda ta ƙara kallon inda Zahrah take.
Cikin sauri ta gama shiryawa babu mai cewa Zahrah ce ta nufi ƙofar baya akan nan da 20 minutes zata dawo.
Tana fita Surry ta kalli Halisa ta ce "Kina ji ƙanwata, Kinga wannan mutumin da kika ganu har kika ruɗe kina cewa Balarabe?" Halisa dai kallon Surry take kafin Surry ta ce "To shi ne mijin Zahrah, ina so ki nutsu ki fahimta Kinga daga can kano Madina zaku shige, kina wanka sau biyu ko sau uku a rana, haka ma brush da saka kaya masu kyau...." Ta ci-gaba da faɗa mata komai na yadda zata gyara jikinta da tsafta ta ɗora da faɗin "Kin fara Al'ada ne?" Danejo ta girgiza kai. Surry ta ce "stop raising your head, magana zaki" ta ce "Ni ban san wani Al'ada ba" Surry ta zare ido sai ba tace komai ba, ta shiga lodar kayan shafawa ta sakawa cikin jakar Halisa tare da faɗin.
"Kada ki kuskura ta gani ko da wasa, idan ta gani ma ki san me za kice kar ki ambaci sunana"
Abba Hakimi ganin maganar mai muhimmanci ce ya tattara ya barta zuwa lokacin da za su koma gida ayi a gaban kowa, duk family su san matsayin yarinyar.
Yaa Sheikh yana kwance saman gadon hotel ɗin da suka sauka idanunsa rufe kamar mai tunani daga shi sai farar Jallabiya ko barcin ya kasa, har lokacin bai bawa auren muhimmanci ba, balle ya sakawa ran shi nauyi wata ƴar mace ya hau kan shi, iya auren daya san da gaske an ɗaura kuma matarsa ce bisa tsarin addinin Musulunci, na ƴar fillo kam yama mance da shi at all baya tunanin shi.
Ya miƙe a hankali zuwa bathroom tare da sakarwa kansa shower ya jima kafin ya fito ɗaure da bathrobe a jikinsa, cikin sauri ya shirya cikin wani kyakkyawar Voyel mai manyan zane maroon colour ya ɗora farar Alkyabba ya wani irin sahihin kyau kamar Prince Hamdan bin Mohammed.
Ya fito cikin parlourn ɗakin ƙamshin Roja ya cika ko'ina a wajan wanda ya jawo hankalin Khalil dake waya da Oum Juwairah ya ɗago kai bai san lokacin da ya ce "Masha Allah" duk rashin tsaurin idon mutum ba zai iya tsayawa gaban Yaa Sheikh ya yi ba, Ilhamar da Ubangiji ya bashi ta musamman ce, a kallo ɗaya yake dagula lissafin mutum. Yaa Sheikh da jikinsa ya bashi kallon shi ake ya ɗago kai suka haɗa idanu da Khalil ya kafe shi da ido alamar lafiya? Wannan kallon fa? Khalil ya shafa kai sbd Kunya ya ce "Muje ko?" Yaa Sheikh yana gaba Khalil na bayan shi, cikin nutsuwa yake tafiya har suka ƙarasu wani room a ƙofar room ɗin suka ci karo da wani saurayi rungome da mace wacce take rusa masa kuka kamar ranta zai fita. Yaa Sheikh ya ɗauke ido da sauri a ransa ya ce "Asstagafirullah Yaa Allah" Khalil kuma ya taɓe baki a haka suka fitar zuwa reception na hotel ɗin daidai nan kuma Mai martaba da abokin nasa El-bashir suka fito suma, haka Abba Hakimi da nasa abokan Umar-khan, Ishaq-Hakim, Saif-wazir. Father daman yana can ba Alhj Farouk mahaifin amarya. Jirginsu Yaa Sheikh daban na Amarya da ƴan uwanta da suka yanki tickets daban.
A airport suka haɗu baki ɗaya har lokacin Zahrah bata taho ba, Danejo tunda idanunta ya sauka akan jirgi ta gigice tsoro ya kamata.
Yaa Sheikh da Abba Hakimi da kuma Mai martaba Ahmad Sarki tare da Father duk suna Vip. Sauran kuma suna nrml waje. Jirginsu ne ya fara tashi babu jimawa Zahrah ta ƙarasu wajan ta sha kwalliya cikin wata lafaya mai kyau da tsada. Tofa kallon ya dawo kan Danejo ta rantse da abin da zai kashe ta ba zata shiga jirgin ba kuka sosai. Wasu nayi mata dry. Da ƙyar Surry ta lallaɓata gudun abin da zai je ya dawo ta zauna kusa da ita.
Danejo ta ƙanƙame jikinta wanda yake rawa hawaye na zubuwa daga cikin idanunta ta ce "Na lalashe Dadata na kaɗe, na bushe shikenan zai a shige sama dani" Surry ta ce "ki nutsu Halisa babu abin da zai sameki kinji ko?" Ita dai kuka take when the plane will take off numfashinta ya tsaya cak Surry ta shiga girgizata tana amsar ruwa tare da yayyafa mata da ƙyar ta dawo daidai ta fara yunƙurin amai yaƙi zuba, lokaci guda ta fita hayyacinta jirgin yana wullawa sama ta fara wata uwar ƙara tana faɗin "Na mutu, Wallahi na mutu.."


Misalin 4:45 manyan motocin da suka ɗakko dangin amarya daga airport suka shiga parking a harabar gidan Mother. Wasu ƴan uwan Zahrah da yayar mahaifiyarta da ƙanwar mahaifiyarta sune suka kamo Zahrah da aka rufe mata fuska zuwa cikin gidan sauran friends suka bi bayansu. A parlour akai musu masauƙi su gaisa da dangin miji kafin a basu masauki. Jadda dake zaune ta ce "Wai ina matar Gadangar ne sai wasu yamutsastsun fuskoki nake gani?" Ladidi ta ce "Gata nan Zahrah buɗe fuskarki ai miki bayanin dangin miji" Mother dai na zaune hankalinta na can waje guda sai kaɗa ƙafa take.
Dr A'isha ma na zaune taci uban kwalliya kana ganinta kasan ba talauci inda take, Yaya Halima ma haka, sai Momi tare da ƴan uwan father, da matar Uncle Haroon.
"A meye haka? Alsulhu khair buɗe fuskar uban kowa ya gani"
"Ai Hajiya kin san amare da kunya" Jadda ta ce "kaji masifa ko? Waye sa dake wace ke? daga gidan wa zuwa ina?" Ladidi tai shiru amma Jadda ta fara ƙular da ita.
"Muhammadur Rasulullah s.a.w wannan ai uwa aka aura Aliyu ba mata ba? Gidan ubawa Aliyu zai kai ɗirkekiyyar matar nan ni kai na ta kusa haifata yau na shiga uku da gaske wannan ce matar Malam ɗin?" Jadda ta faɗa bayan ta saka hannu ta buɗe fuskar Zahrah. Surry na gefe tana danne dariyar dake ranta.
"Maryam zo kiga abin al'ajabi yoo Allah na tuba ko ke ai kinfi matar malam kyan gani? Allah sarki Gadanga an haɗaka da uwar mata" sai kuma ta fashe da kuka sosai ta ce "Innalillahi ashe har gashin doki take saka zunubi babba" ta saka hannu ta kama hannun Zahrah ta ce "Wanne tsinannen abu ne wannan kuma?" Ta faɗa tana duba farcen hannun Zahrah.
"Haba Hajiya wannan abun duk na mene? Ya daga kawo yarinyar sai cin mutunci?" Jadda ta miƙe ta nufi kan me maganar ta dungure mata kai ta ce "Algunguma ai duk duniya an gama cutar Malam an haɗa shi da arniyya" "Arniyya wacce ira kuma Hajiya?" Ladidi ta faɗa rai ɓace. Jadda ta kunce ɗan kwalin kanta tare dacin ɗamara ta ce "Arniyya ƙatuwa ma, mene bambancin su? ga tafkeken zunubi ba tausayi ba komai aka cirewa doki gashin shi aka saka mata, gata narkekiyya mai idanu a tsakar kai, gashi ta wani ɗashe kamar mace mai shigar sabon ciki Innalillahi masifa ta saukarwa Malam" gaban Zahrah ya faɗi tai saurin rufe fuskarta.
Dr A'isha ta fashe da dry wacce tun ɗazo take danne ta. Yaya Halima girgiza kai kawai take kafin ta ce "Kuyi haƙuri don Allah muke ga masauƙi can" Mother hankalinta na kan Danejo wacce take ɗan ɗaga liƙab ɗin fuskarta tana leƙewa da sun haɗa idanu da mother sai ta mayar ta rufe.
Babu wanda Jadda bata ciwa mutumcin ba kafin su bar wajan. Mamaki ya kama Ladidi ganin uwar mijin ta Zahrah ci kanku ba ta ce ba. Kwanan su biyu suka koma Yola aka bar Zahrah tare da Halisa.
Yaa Sheikh ne durƙushe a gaban Abba Hakimi da Uncle Haroon sai Uncle Bashir ga Mother da Yaya Halima da kuma Momi matar Abba Hakimi. "Ina magana kayi shiru Aliyu?" Abba Hakimi ya faɗa cikin sassauta murya. Yaa Sheikh ya ɗago kan idanunsa ya sauka akan yarinyar da ake nuna masa, ya ƙara duban Halisa da kyau sai yanzu yai mata cikakken kalo ya mai da idanunsa kan Abba Hakimi ya ce.
"Wace? kamar ban waye ta ba?" Uncle Haroon yai murmushi yana jinjina halin Yaa Sheikh. Abba Hakimi ya ce "Amma kasan Rugar Bello? Ka kuma san Arɗon rugar ka gane abin ya faru,ka kuma shaida zoben hannunta?" Yaa Sheikh ya ɗan kallin kyakkyawan hannun Danejo wanda yake maƙale da zoben da yake so har ransa nan take ransa ya ɓaci, a lokacin ya tuna everything ya shanye mmkin kamannin da yake gani a fuskar yarinyar, shi kam a rayuwa ko zai so mace ai banda ƴar cikinsa wannan gwaliliyyar yarinyar bata shige raino ba, ita za a kalla ace wai matarsa? Shi kam ya zai yi da mata biyu ba?. Yai shiru yaƙi bada damar da za a karanci halin da zuciyarsa ke ciki. Uncle Bashir ya ce "Da alama ya fahimta" Abba Hakimi ya ce "Halisa maza je aikyan yayar taki kada taga kin daɗe" ta miƙe da sauri domin daman a takure take Yaa Sheikh duk ya firgitar da ita. Abba Hakimi ya ce.
"Ba wasa muka zauna yi ba, jibi zaka shige Madina kafin nan kana son yarinyar nan ko baka son ta?" Yaa Sheikh yai shiru ya kasa fahimtar abin da suke nufi dashi, shi kam duk ranar da ya ce yana son mace ai sai ya yi azumin kaffara shi ya sa har abada ba zai taɓa cewa yana son wata ba.
Ya girgiza kai a hankali "Baka son ta?" Cewar Uncle Haroon. Bai kalli Uncle Haroon ba ya kalli Abba Hakimi. Abba Hakimi ya gyara zama yana sakin murmushi ya ce "Ka shirya sakinta? baka san me gobe zata haifar ba?" Yaa Sheikh ya riƙe hannunsa da kyau yana girgiza kansa harshen shi na harɗewa ya ɗan motsa ƙafarsa ɗaya cikin In-ina ya ce "Ha...hhh...har... Har abada ba ba ba zan zan so ta ba"


_IDAN BA KE it's paid book ₦500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616..... Isn't free if you read for free🤷🏾‍♀️_Yaa Sheikh ya faɗi hakan kai tsaye. Abba Hakimi ya ce "To kafin nan muyi wata game mana, idan kaci ni kuma nayi al'ƙawarin raba aurenku har abada, ka zauna kai ɗaya da ita Zahrah tunda ba a son Ƴar fillo" Mother ta juya ta kalli Yaa Sheikh kafin ta ce.
"Yanzu meye laifin yarinyar? ba tafi wacce aka haɗaka da ita ba? to a karo na farko zan faɗa maka zama da wannan babu fashi a wajanka Aliyu" Uncle Haroon ya ce "A'a Barrister labarin aure baza kici haka ba, ana yin aure dan farin ciki da kwanciyar hankali,idan ba yajin yarinyar a ran shi bai kamata a takura masa wajan zama da ita ba, zai iya amincewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login