Showing 147001 words to 150000 words out of 197828 words

Chapter 50 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9298

a kallo ɗayan da ya yi mata ya fahimci da gaske zuciyarta tai mugun kamowa da ciwo wanda ba a son irin shi
"Ya jiki?" Maganar da tai silar faɗuwar Zahrah daga kan gadon ya yi saurin saka hannu ya taro ta, ta juya sukai idanu biyu wata ajjiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke hawaye wani na korar wani, tayi saurin cire drip da jinin da ake ƙara mata, tare da fisge na'urar Oxygen ɗin dake aiki a Jikinta, babu ƙwari a Jikinta amma haka ta miƙe tana zuwa ta faɗa jikinsa ta rungume shi tana sakin wani irin kuka wanda yake nuni da ka tausaya mini ka taimaki rayuwata.
Sanin cewa zuciyarta a yanzu matacciya ce, abu kaɗan za ai mata ta lalace yasa ya ɗan daidaita ya shafa kanta kaɗan ba tare da ya ce
Komai ba, muryarta a hankali ta ce "Ka taimaki rayuwata ka aureni Malam, ka tausaya mini zuciyata babu daɗi kamar zan mutu" wani irin kuka take gwanin tausayi ya janyeta daga jikinsa tare da zaunar da ita saman gadon ta ce
"Saboda Allah, da soyayyar da ka kewa Annabi Muhammad s.a.w" ya kalleta da kyau yana nazartar yanayin kafin ya ce.
"Na amince, zan aureki"
Ta saki murmushi while hawaye na zuba ta ce
"Na gode Allah ya saka da alheri Ubangiji ya ƙara girma" Ya jinjina kai sukai shiru ta kalle shi ta ce "Nasan takura maka akai, ko tausaya mini kayi ba dan kana so na ba ko?" Ya nuna mata pillow ya ce
"Huta, barci" ta ce
"Nayi barci har na gaji, yanzu bani da wani damuwa daman kai ne damuwata" sai yaji tausayinta, sai yanzu ne yake gane cewa duk wanda yake hauka akan SO! To kawai a rabu da shi, so babban abu ne da kan iya tarwatsa zuciyar mutum murus ya lalata masa rayuwa ya ɗauke masa farin ciki yanzu ya shaida haka.
"Matarka? zata amince dani, na maka al'ƙawarin ba zan taɓa janta da faɗa ba ko tayi zan haƙura domin tayi mini komai datai mini halarci har ta amince ka aureni, wlh idan ni ce ita ba zan iya barinka ba, balle ka auri wata ina maka son da Ubangiji kaɗai ya sani kuma shi ne zai zama shaida, kana da kima kwarjini tarin da haiba wacce ba kowa zai iya Fuskantarka da wani shirme, nasan zaka zauna sani bisa takura kayi haƙuri,kai mini adalci ba laifina bane"
Ya girgiza mata kai a taushashe cike da kulawa ya ce
"Ba takura, ki nutsu zamu zauna gida ɗaya tare"
tai murmushi tana ɗan riƙe ƙirjinta. Ya taimaka mata ta kwanta ta ce
"Kada ka tafi don Allah"
Ya jinjina kai yana tsaye kanta tana kallon shi tare riƙe hannunsa har barci ya ɗauke ta.
Fita ya yi, zuwa office ɗin Dr. Dr ya ce "Ko iyayenta basu san tana ɗauke da Cancer ba, wanda kuma munyi scanning yaci ƙarfinta abu ne mai wahala ta tsallake wata biyar a raye a duniya" Yaa Sheikh ya ce "Subuhanallah!" Dr ya ce "Yana da kyau ta ƙare watanni biyar ɗin nan da farin ciki, kada ita kanta tasan cewa akwai Cancer Jikinta hakan zai ƙara taimakawa wajan murmurewar Jikinta"
"Ba wani aiki?" Dr ya ce
"For now babu, domin taje ƙarshe sai dai fatan samun sauƙi wajan Ubangiji" ya miƙe yana godiya. Daga nan sukai sallama Yaa Sheikh ya nufi Rugar Bello a hanya ya kira Abba Hakimi sukai magana mai ɗan tsayi kana ya kira Ummul daga nan ya ajjiye wayar.
Halisa na zaune tana azkar Idanunta ya kumbura sbd kwana tayi tana kuka sai dab da Subhi barci ya ɗauke ta, kasancewar ta saba ta shi yin Sallah ya sa bata makara ba
Ta miƙe da ƙyar tana dafe kanta Idanunta na lumshewa sbd barci ga wani irin matsanancin feelings dake damunta ta rasa yadda zatai da rayuwarta, harta mata tsayin lokacin data ɗauka ba tare da Yaa Sheikh ba, she miss his torch, his kiss, his body his everything daya shafe shi amma zafin ranta ya kasa bari ta yarda tai kewar, tana ƙoƙarin kwanciya mother ta buɗe ƙofa ta shigo lokacin wasu masallatan nata sallah ta ce "Barka da safiya Mother" bata amsa ba ta ce "Kije, ki haɗa mana breakfast, ga wanke-wanken ma da mopping" a raunace ta ce "Ina maid ɗin? Bana jin daɗi" ta ce "Allah ya sauwaƙa mai aiki kuma mun sallameta ke zaki koma yin komai"
Kamar zatai kuka ta ce
"Bari gari ya yi haske to"
"Yanzu na ce, kafin Abba Hakimi su tafi kai kuɗin Auren Zahrah" kamar an caka mata wuƙa a zuciya haka taji hawaye ya sakko mata, mother tai waje. Ita kaɗai ta dinga kuka babu mai rarrashi
wayarta ta ɗauka da niyyar yiwa Maimoon ko Dr A'isha magana a online sai taga anyi mata magana da prvt number, kamar ba zata shiga ba sai kuma ta buɗe abin data gani ya yi mugun tayar mata da hankali ta dafe cikinta da sauri wanda ya murɗa fitsari ya taho mata, tai downloading picture ɗin Yaa Sheikh ta gani rungome da Zahrah a ɗakin asibiti a ƙasa kuma aka ce. "Mun gode sosai Halisa da shirmanki ya bawa ƙawata damar samun cikar burinta, yanzu Yaa Sheikh na Zahrah ne har abada ki fara kokawar neman mijinki domin yanzu wutsiyyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, ke da Yaa Sheikh har abada.....," Bata ƙarasa karantawa ba ta nemi ganinta ta rasa ta kuma kasa fahimtar komai ta fasa wata ƙara tana faɗin.."Wallahi ƙarya ki ke, baki isa ki auri abin da na fiso a duniya ba, dole ki rasa kamar yadda ki ka rasa" gabaɗaya Jikinta rawa yake har ya gaza ɗaukan ƙafafuwanta ta sulale ƙasa tare da yin zaman ƴan bori.
Wani irin kuka take mai tarwatsa zuciya da sanya mutum cikin damuwa, duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata, hannunta na rawa ta ɗauki wayarta tare da kiran Dr A'isha. Ringing ɗin farko aka ɗauki wayar tare da faɗin.
"Hello!"
Halisa ta ce "Adda A'isha na shiga uku, ba zan iya ba" Dr A'isha tai murmushi tana kallon ɗaya wayar hannunta kafin ta fita daga inda take ciki, ta nemi bakin gado ta zauna ta ce
"Shiga uku dame Halisa?" Cikin shassheƙar kuka murya bata fita sosai ta ce
"Da gaske Abbana aure zai yi wallahi, kuma Zahrah zai aura ba zan iya jurewa ba, ina jin kamar zuciyata zatai bindiga" Dr A'isha ta kaɗa ƙafa ta ce
"Meye abin damuwa? You need a divorce paper, and you got it, I think you will be happy". Halisa ta dafe ƙirji ta ce "I love my husband, ina son mijina kin san ban tsane shi ba, ba kuma zan iya barin wata ta aure shi ba, yanzu ya zan?"
Dr A'isha ta runtse idanunta tana jin kamar wuta Halisa ta watsa mata a ƙirji da ta ce _She loves her husband_ ta kasa cewa Halisa komai ta shiga dannar zuciyarta sbd zafin da tayi..
"Na zama shasha, na rasa meke damuna" Dr A'isha ta ce "It's over, kin yi sake when all is gone, yanzu sai da kibi hanyar da zaki hana Yaa Sheikh ya auri Zahrah, idan ba haka ba kina kallo zai haɗa shimfiɗa da ita"
Ta sauke numfashi ta ce
"Kin san saki uku ya yi miki, ke da Yaa Sheikh har abada domin rama abin da ya yi miki, shi ne hana shi auren Zahrah"
Halisa ta goge idanunta ta ce "Bana jin Abbana zai mini saki har uku, kuma anƙi faɗa mini saki nawa ya yi mini"
"Kira ki tambaye shi mana?" Ta girgiza kamar Dr A'isha na gabanta.
Jin tayi shiru ya sa Dr A'isha ta ce "Ko ki je inda yake" sai a lokacin ta ce
"Ya yi tafiya"
"Zuwa ina? Yaushe zai dawo?" Cewar Dr A'isha.
A raunace wasu hawayen na biyu mata zuwa saman kuncinta ta ce
"Ban sani ba, bani da labarin yaushe zai dawo"
Dr A'isha tayi murmushi Idanunta akan mijinta wanda ya shigo daga masallaci kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai.
A hankali ta ce "Ask Abba Hakimi, you'll get the information Catch you later" tai hanging up na kiran. Idanunta kan waya
Abubakar ya ce
"Sweetheart waya da Subhi yau babu ko azkar?" Ta yi masa kai ka ɗauka bada ita yake ba.
Ya ƙara cewa "Dr na"
"Abubakar" ya buɗe baki da hanci yana kallonta ɗauke da mamakin yadda ta kira sunan na shi babu ko risinawa ta ce "Dr kin san me ki ke cewa?" Ta ɗago idanunta fes akan shi ta ce.
"Nasan kana da labarin ban taɓa yin hauka ba ko?" Ya jinjina mata kai ya ce "Elxty, The way you called my name surprised me"
"To, Allahamdulillah tunda sunanka ne Abubakar ɗin" ya ce
"Meke damunki ne Dr?"
Idanunta ya sauya kala ta ce "Kai ne damuwata Abubakar, domin ka hana ni abin da nake buƙata tsayin shekaru bayan a koda yaushe ina iya mutuwa,ko kafi so na mutum ban bar masu yi mini addu'a ba? Burinka kenan nasan cewa kai ne baka haihuwa fa"
Da damuwa ya ce
"Ina tauhidinki ya tafi A'isha? Ni zan baki haihuwa?" Ta ce
"In a capital letters YES! ka duba Halisa matar malam, shekaru nawa na mata? Gabaɗaya yaushe sukai aure amma yanzu cike ne da ita haihuwa take shirin yi, ni kuma ina zaune a tutar babu"
Ya kai hannu zai riƙe ta domin wallahi gani yake kamar wacce Aljanu suka shafa ko wacce kwakwalwarta ta taɓo
"Ras nake Abubakar, ina son faɗa maka cewa na gaji ne kawai I'm tired"
"Tired of what, Dr?"
A fusace cike da kallon wulaƙanci ta ce
"Your married, na gaji, na gaji, na gaji wallahi ka sake ni, naje na auri wanda zuciyata ta rayu da son shi, daman aurenka is my destiny i know tun ba yau ba"
Ya dafe kai ya ce
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, ni ki ke faɗawa haka Dr? Kin san abin da kalamanki zasu iya jefani? Kin san tasirunsu cikin zuciyata, kin san son da nake miki,
Kada kiyi amfani da jarabtar da muka tsinci kanmu ki cutar da rayuwata, haihuwa da rashinta daga Allah suke, ta yiwu yaran ba alheri bane a garemu shi ya sa Ubangiji bai azurtamu da su ba, shi da kan shi yana cewa yana jin tsananin kunyar wanda bai azurta su da haihuwa ba, ki riƙe ƙaddara ki kuma yarda da ita shi ne cikar imaninki"
"Shut up your mouth Abubakar Tijjani Asase, ka haifeni ne? ko malami ka zama da zaka zauna kana faɗa mini Allah ya ce Annabi ya ce, tunaninki ni daƙiƙiyya ce ko? Lemme repeat myself I'm tired I need my divorce paper immediately!"
"Wallahi Allah, ba zan sake ki ba, sbd ina son ki IDAN BA KE ki ɗauka rayuwata ta zo ƙarshe ne, ki sani matata ce ke igiyar aurena ke yawo akan ki, da alama baki son rabauta da aljanna ki koma wajan ɗan uwanki Yaa Sheikh ya yi miki darasin dake cikin aure A'isha"
Yana kawowa nan ya fice daga cikin bedroom ɗin zuciyar shi babu daɗi.
Halisa tunda suka gama waya da Dr A'isha take zube a ƙasa tana auna maganganunta, Hawayen fuskarta yaƙi tsayawa.
Ta miƙe da ƙyar jiki a sanyaye ta nufi Main parlour sanye da hijabi
Kitchen ta nufa aikin data tarar dai da gabanta ya faɗi, ta ta shi akan wahala aiki koma ba sabon abu bane wajanta, tun a rugar Rome.
Zata kunce nagge duk yawansu ta tafi kiwo, ta tatsi nono ta tafi talla ta dawo tayi aikin gidan, amma ƴan watannin da tayi tare da Abbanta Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu
Ya sangarta ta, ya bata farin ciki, ya bata tarbiyya, ya kula da ita bata aikin fari dana baƙi sai ɗaukan darasin zazzafar soyayyar shi
da karatun da yake mata,
ita kanta bata san ya take jin kanta ba, ta manta ita ce Halisa Danejo Rome. Ta dawo amsa sunan Halisa Sheikh Aliyu haydar Aliyu, yanzu kuma data dawo Princess shi ne za a haɗata da aiki har haka wanda ta mance yadda ake yin shi.
Lallai aure rahama ne, cikar ƙimar mace gidan mijinta. "Mena aikatawa kai na ni Danejo?"
Ta yi ta surutu ita ɗaya taci kuka ta ƙoshi she just missed, amma me?
Shi ne abin da bata sani ba, tana buƙatar Mentoring kanta a cushe yake. A hankali ta fara wanke-wanken ta gama tas, kana ta gyara kitchen ɗin.
Kasancewar an gyara wanke ta saka a inji malkaɗe ta malkaɗa. Gefe guda ta kunna gas ta ɗora ruwan kunnun shinkafa. Ruwa ta zuba cikin pot ɗin ta kawo kwakwa wacce ta goga ta zuba cikin ruwan, kafin ruwan ya rafasa ta koma wajan kullin ƙosan ta haɗa shi. Ta ɗora kasko ta zuba mai daidai yadda zai sha kan ƙosan, ta zuba albasa cikin man ta barshi ya yi zafi sosai.
Daidai lokacin ruwan data zuba ya tafaso tare da kwakwa, ta kawo haɗin kullin shinkafar tare da muciya a nutse take zubawa tana damawa har ya yi kauri yadda take so. Ganin bata gama ba ya sanya ta rage gudun gas ɗin man data ɗora, tana gama haɗa kunnun shinkafar ta juye a wani babban flas. Ta goge wajan daya ɓaci ta ajjiye flas ɗin gefe.
Ta dawo kan man data ɗora, ta haɗa ƙosan wanda ya sha kayan ƙamshi da ƙwai da tafarnuwa.
Is taking long kafin ta gama soya ƙosan, ta ɗauki paper ta saka ƙasan flas sbd gudun gumi ya lalata shi,ta juye tas ta ƙara ɗaukan wata paper ɗin ta rufe saman shi. Ta ajjiye gefe guda.
Ta ta fasa tea da ginger da tafarnuwa da sauran kyan ƙamshi da barkono kaɗan. Shi ma ta juye cikin mug ta goge wajan tas, tana gamawa ta koma Main parlour ta share tai mopping ta kunna boner ta saka turare mai ƙamshi sosai ta fesa air-con.
Nan da nan parlourn ya ɗauki ƙamshi, a lokacin gabaɗaya Jikinta ciwo yake da ƙyar take buɗe ido ga damuwar zuciya, ga feelings ɗin dake damunta har tsoro abin ke bata, nan da nan za ta jita a jiƙe. Ta shirya breakfast ɗin lokacin goma saura minti biyar cif. Mother ta fito cikin wata green ɗin atamfa ciganvi ɗinkin doguwar riga. Tausayin Halisa ya kamata amma ta share ta ce "Sai yanzu ki ka gama?" Kallon mother kawai tayi ta kasa cewa komai, ta ɗaga ƙafa da ƙyar ta nufi bedroom ɗinta. ko hijabin Jikinta bata cire ba ta kwanta kan gado tare da jan pillow ta rungome, ta rufe idanu sai suffar Yaa Sheikh ta dinga zama kamar magic a Idanunta, ta tuna rungumar da ya yi mata ta ƙarshe sai ta matse ƙafa da ƙyar barci ya ɗauke ta.
Wajan azahar barcinta ya yi nisa taji kamar ana motsi a ɗakinta, ta kasa buɗe ido sama-sama kuma wani ƙamshi ke ratsa hancinta yana sauka har ƙasan zuciyarta, ƙamshin da ba zata taɓa manta irin shi ba, idan tai kamar zata farka sai a hura mata iska taji an rungometa tsam a ƙirji, ɗumi na rasata. Ta saki jiki cikin magagin barci ta ce
"Abbana" aka shafa kanta ana manna mata baki a wuyanta tare da sakar mata wasu lafiyayyun kisses cikin wata murya mai rauni da shauƙi aka ce
"Madadin Abbanki ne" baki ya kai da niyyar kissing nata ta buɗe ido da sauri tana cewa
"Modibbo!" Ɓat! Kamar gilmawar walƙiyya ya ɓaci daga cikin bedroom ɗin sai ƙamshin turaren Roja daya bari, cike da zullumi ta miƙe tana kunna hasken ɗakin, abin mamakin bai huce yadda ta ganta naked babu kaya ta juya zuwa kan bed taga kayanta ya she zube a ƙasa.
Ta shiga tattaɓa Jikinta da sauri ta ɗauki hijabi ta saka har ƙasa ta saka wani skert tai waje da gudu tana sakin ajjiyar zuciya,sam bata lura da tarin mutanan da suke parlourn ba, kai tsaye tai wajan mother ta ce.
"Abbana ya zo?" Mother tai mata kallon baki da hankali ta ce "Waye kuma Abba?" Halisa tai shiru. "Oh! Tsohun mijinki Yaa Sheikh wai?" Ta ɗaga kai da sauri ita burinta ta ji ya zo ɗin.
Mother ta ce "Ikon Allah ko shirman naki har kwakwalwarki ya taɓa ne Halisa? Banda haka ina za muga Yaa Sheikh yanzu bayan ya yi tafiya kuma ha yanzu zai dawo ba" Halisa ta ce.
"Na ganshi yanzu a bedroom ɗina, na tabbatar shi ne, naji ƙamshin turaren shi har na ce masa Abbana sai kuma ya gudu"
Mother ta ce "Ah, ta tabbata kin zauce tsanar shi ce tasa ki ka fara mafarki da shi?" Ta tura baki ta ce "Koma mene ai Abbana ne, ko ya sakeni ai baby zan haifa masa" Umma A'isha ta ce
"Haka ne, kuma babyn mai sunan Ummul da Mother" Halisa ta taɓa rai ta ce "Ai na rasa Mother farin ciki take da Abba ya sakeni" Mother ta ƙara sawa ranta cewa Halisa akwai wauta da ƙuruciya a kanta tana son mijinta sosai abu ne kawai ke yawo a kanta.
"To ai ni ke nake tayawa murna, farin cikin ki shi ne nawa fa" ta juya kan Umma A'isha ta ce
"Ke kaɗai zaki faɗa mini gasky, amma wallahi Modibbo na gani" Ummul dake zaune ita da hajja da Dada da kuma Fulani Atine, da Fulani Balaraba sai Dr A'isha da Yaya Halima da Maimoon da Zeefa. Ummul ta kalli Halisa ta ce "Arɗo ki ka gani, anya ta ya ya?" Ta faɗa tana son tabbatar da abin da take zargi ta ce "Da gaske Ummul naji ƙamshin shi" Ummul a ranta ta ce "Wato ya tuna da layyar zanar shi kenan? Yanzu mata a suffa mai wahalar ganewa" a fili ta ce.
"Ki nutsu, gizau ne da saka abu a rai"
"Ba kiga kayan lefen Zahrah ba ne?" Sai a lokacin Halisa ta lura da wasu mayan set ɗin akwatuna har set biyar different colours ta dinga kallon kayan, abin ka da wacce ke shirin kaɗan ga damuwa da tai mata yawa, kowa ya juya mata baya, ga rashin cin abinci. Ta runtse idanu bata fahimci baya tayi zata faɗi ba sai taji an kamata an zaunar tare da bata ruwa ta gane cewa suman wani lokacin tayi, kanta a ƙasa ta dinga goge hawaye a takaice. Daga ƙarshe ta miƙe tare da barin wajan.
Tana barin wajan Ummul ta ce "Mai ya sa kuke son wahalar da ita, why not a faɗa mata Gasky she's still his wife, look at her condition ba ita ɗaya bace, don't think

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login