Showing 51001 words to 54000 words out of 197828 words

Chapter 18 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9295

yi ba, ya fahimci hakanne ta madubin motar.
Kanta a ƙasa idanunta ya yi masifar jaaa jikinta na ɗan rawa a hankali, saukar sautin ƙira'ar daya cika motar har ya kawo zuwa kunnenta yasa ta sauke numfashi mai ƙarfi jikinta ya saki kafin su ƙarasa barci ya ɗauke ta sai ajjiyar zuciya take saukewa.
Bayan magrib Mother na zaune a parlour ita da Jadda. Jadda ta kaɗa ƙafa ta ce "Amma dai Allah ya isa, an munafurce ni ko waye kuma yaje shi da Allah, shi yasa yadda zai yi dashi danni ba zan iya komai ba" "lafiya dai Jadda?" A fusace Jadda ta ce "Ina batun lafiya Maryam? Ashe haka aka haɗawa Uwar matar can lefe hadda na Allah ya isa fa? Ni dai babu ruwana na kusa zare hannuna daga al'amarin Aliyu ko na ɗaga masa nonon kawai tun da nayi niyya" Mother tai murmushi kawai tana jiran zuwan Maimoon.
Zahrah ta ƙarasu parlourn sanye da ƙaton hijabi irin ta Allah ɗin nan nace, ta zauna tana faɗin "Sannu da hutawa Mother" a taƙaice ta ce "Yawwa" ta juya kan Jadda wacce ta haɗe rai sosai ta ce "Barka da gida" Jadda tai mitsi mitsi da idanu ta ce "Allah ya isa, Allah ya isa wallahi ban yafe ba" Jadda ta faɗa tana kallon Mother tare da fashewa da kuka ta ce "To me nayi mata da zata gaishe ni? Sbd Allah ina ruwanta dani ko nace ina buƙatar gaisuwarta" Zahrah bata ƙara bi takan Jadda ba ta kalli Mother tana sunkuyar da kanta ƙasa ta ce "Daman zan mayar da Yarinyar nan ne gida" Mother ta kalli Maimoon dake shigowa tana faɗin "Wacce yarinya?" Zahrah cike da nuna cewa tafi kowa iya ladabi ta ce "Ƴar fillo, zan tura ta gida" Jadda ta miƙe ta ce "Wannan farar yarinyar kyakkyawa mai zubin labarawa kamar ita tai kanta? Idan kin isa Allah ya tsine" Mother tai murmushi ta ce "Me ya sa?" Zahrah tai ƙasa da kai ta ce "Daman Mimi tace na dawo da ita gida, da ƙyar aka yarda aka bani ita kuma tana karatu" Mother ta karkaɗa ƙafa ba tare da ta ce komai ba ta danna wayarta babu jimawa aka ɗaga wayar ta ce "Umar-khan, kayi waya da mutananku na can Madina, a fara nemawa Halisa gurbin karatu a matakin ajin farko na secondary" gaban Zahrah ya faɗi, ganin how smart she had. Bayan gama wayar Mother ta ce "kada ki damu Zahrah, I'll talk to your mom, ki fara shirye-shiryen tafiya" ta miƙe tana faɗin "Na gode Mother" da sauri ta shige part ɗinta.
Tana zuwa ta rufe ƙofa tare da cire hijabin jikinta inners ne kawai a jikinta cikin faɗa ta ɗaga wayarta ta ce "haba Deen wai kai wanne irin maye ne?" Deen dake cikin wayar ya ce "Muna vedio call kika tafi kin barni cikin wani hali Beb" cikin ɗaga murya ta ce "Jarbabbe duk kai ka koya mini jaraba kwana nake bana barci, nifa batun tafiya da yarinyar nan ne na fasa,ina hangowa kai na matsala gaba ɗaya ji nake kamar wani abu zai faru idan na tafi da ita" Deen ya numfasa ta wayar yana faɗin.
"Ya kukai kuma me kike so ayi?" Ta faɗa masa duk yadda sukai da Mother ya ce "Uhm Sirikarki Educated ce kuma Barrister, ta fiki tunani da hankali idan kina wannan haukan da wuri za a gano shirinmu, dole ki yafe ɗan cikin ki a gidan Yaa Sheikh, shi ne zai bamu damar cimma burinmu ya zama dole ki samu kusanci dashi ina nufin ki samu mu'amalar aure da shi, hakan shi ne hanyar farko, ai ana haihuwa bakwaini ki san duk yadda kikai kina zuwa Madina ku samu daidaito Zahrah, kece madafin cimma burina na faɗa miki irin cin amana da zaluntar da akai mini" ta sauke numfashi tare da ta ce.
"It's ok Deen, na maka al'ƙawarin ƙwato maka hakƙin ka, ina son ka, burina ka tsaya dani banda wata macen" ya yi murmushi ta wayar ya ce.
"Zahrah kenan, kina so na kullum kike cewa, amma son da kikewa Yaa Sheikh yafi son da ki ke mini, duk da hakan me ya sa kika amince zaki cutar da shi bayan kina son shi?".
Zahrah ta ce "kada ka damu wannan sirri na ne, sunna or later zaka sani, Yaa Sheikh manufa ne, kai kuma makami ko wanne nada amfani, amma dole muyi wani abu akan Halisa" ya ja tsaki a ran shi sam bai ga abin damuwa akan wata Halisa ba.
"A kashe ta? Ko kuma a haukata ta?". Zahrah ta ce "Hauka kuma, zan yi tunani akan haka, muje vedio call na nuna maka wani abu mai yaji" dry ya yi ya ce "Zahrah bana son ganin wannan shafaffen ƙirjin naki, wanda yake kwance har ciki serious tun kafin Yaa Sheikh yasan wace ke ya kamata ki nemi magani" maganar Deen ta daki zuciyar Zahrah ta kashe wayar rai ɓace.
Khalil ya ce "Mother daman zuwa nayi nai miki sallama, yanzu zamu tafi airport" ta ce "To sai yaushe kuma" ya shafa kai ya ce "Ina tunanin sai bikin Maimoon ko idan matar Yaa Sheikh ta haihu".


"Ikon Allah daga aure sai haihuwa, Maimoon kam ai da sauran ta" ya ƙara shafa kai idanunsa akan Maimoon dake tura masa baki.
"To Allah ya tsare, a gaida Oum Juwairah" ya miƙe yana faɗin "za taji ai tana gidan Abba Hakimi" kafin Mother tai magana idanun Khalil ya sauka akan yatsun Halisa da mmkin yake kallon Zoben dake maƙale a yatsar zai magana El ya ce "Zan tafi ni dai" ya ce "kafi jirgin sama tashi" Halisa ta kalli El suka haɗa idanu sun jima suna kallon juna kafin tai ƙasa da kanta, tun jiya da suka je visa ta daina walwala taƙi kula kowa surutun ya rago sosai.
El-bashir ya fita Khalil ya ce "Ƴar tsuhuwa Maimunatu zo ki kaiwa Matar Yaa Sheikh gift ɗinta" ta miƙe kafin ta ƙarasa yayi waje, tana zuwa corridor taji an jawota zuwa jikin mutum, a tsorace ta buɗe baki zatai ihu Khalil ya yi saurin rufe bakin ya ce "Haba Amaryata yaushe za mu yi auren ne?" Ta ce "Allah ya sauwaƙe na auri me mata ni ban so" ya ce "Ni kuma na miki al'ƙawarin wallahi sai kin aureni na haɗa mata biyu a cikin masarauta" tai masa shiru, tun Maimoon na ƙarama yake mutuwar son yarinyar. Ya ɗan ƙara matseta a jikinsa daidai kunnanta ya ce "I love you" yana faɗin hakan ya saketa yana damƙa wani box ya ce "For our In-law, and this na ki ne" ya ƙara damƙa mata wani box ɗin ya juya da sauri tare da ficewa.
Washegari gari da safe Yaa Sheikh ne yake fitowa a hankali daga part ɗin sa, yana sanye da jallabiya fara tas ƙafarsa sanye cikin slippers, hannunsa goye a bayansa ya ɗan tsaya a parlourn sbd shiru da yaji juyawa ya yi idanunsa ya sauka akanta tana ƙawance akan duguwar kujera ta kifa kanta a hannunta kamar mai barci, jar rigar dake jikinta ta ƙara fidda tsarin jikinta, madaidaitan hips ɗinta sun bayyana a fili ya ɗauke idanu yana ya mutsa fuska, remote ya ɗauka tare da kunna karatun Alkur'ani ya danna ƙara ya cika gidan. A firgice Halisa ta miƙe tsaye jikinta duk rawa yake, jajayen idanun da kusan kwana biyu suka ƙi dawowa dade ta buɗe su akan Yaa Sheikh dake zaune akan kujera yana ɗan jan gemunsa. Ba tare da ta ce komai ba sbd kanta dake juyawa da sauri ta nufi hanyar da zata fitar da ita daga cikin parlourn wacce kai tsaye kuma zata kaita har waje bakin hanya, Allah Allah take ta fita sbd karatun dake gigita mata lissafi kamar zai fasa kanta.
Tana zuwa daidai inda yake zata gilma ta shige ya sanya farin hannunsa mai laushi ya damƙota tare da dawo da ita baya...


Paid book
It's 500
Via 08119237616Dawo da ita baya ya yi tare da zaunar da ita a ƙasa wajan ƙafafuwansa, yana mai sakin hannunta da sauri. Tamkar wacce take gane abin da shirun nasa yake nufi haka ta zauna waje guda taƙi yarda ta ɗago kanta kamar yadda yasu sbd ya fahimci abin da yake tunani.
Yasan har abada indai tana cikin wannan yanayin to ba zata taɓa kallon cikin ƙwayar idanun shi ba, sai dai idan marasa kunya ne suke tattare da ita.. hannunsa daya riƙe nata ya dunƙule waje guda a haka Mother ta fito sanye da duguwar riga ganin Yaa Sheikh a main parlour da sassafe ya bata mamaki, idanunta akan shi kana ta zame zuwa kan Halisa dake zaune kusa da ƙafar shi ta dama. Da mmki tana zama ta ce "lafiya dai Haydar? fitowa da safiya, Halisa fa?" Ta tambaya tana kallon Halisa elxty yadda Yaa Sheikh yake abu lokacin yana yaro haka yanzu Halisa tayi. Ya buɗe idanun shi yana ajjiye carbin hannunsa cikin kamilalliyyar muryarsa ya ce. "Mun tashi lafiya Mother?" Ta saki murmushi tana faɗin "Allahamdulillah Haydar, Halisa fa?" Ya ƙara ware idanu yana kwaɓe fuska alamar tambayar batai masa ba, kamar zai share ya numfasa kaɗan ya ce.
"Wafa?" Mother ta ce "Meya fito da Halisa da wannan safiyar kuma gata kusa dakai kamar bata da lafiya?" Ya jima yana tunanin amsar da zai bawa Mother baya ƙarya baya kuma faɗin abin da bashi da tabbacin sai ya yi shiru Mother ta miƙe tsaye tana faɗin.
"Black tea ko? Bari na kawo maka,ka jira ina son magana dakai" ya jinjina kai. Mother na tafiya ya juya kansa zuwa inda Halisa take zaune a hankali ya miƙa tattausan farin hannunsa mai taushi ya ɗora saman goshinta.
Zabura tayi zata gudu ya riƙe kan da kyau, sosai yaji kanta ya ɗauki zafi yana harbawa. Ya jima riƙe da kan yana ɗan murza babban yatsar shi a tsakiyar goshinta kafin yaji taja duguwar ajjiyar zuciya tare buɗe idanu.
Ya zame hannun shi daga kan, itama ta kasa kallon shi ta kuma kasa motsawa.
Kamar wacce aka tsikara haka ta miƙe jiri na ɗaukanta ta nufi part ɗin su Maimoon domin anan ne take kwana yanzu. Barin ta parlourn ya yi daidai da dawowar Mother daga kitchen, bayan ta zauna tare da tsiyayawa Yaa Sheikh black tea ɗin tare da 2 spoon na honey yana tiriri ta miƙa masa.
A nutse yake sha ganin ya kusa shanyewa ta kalle shi ta ce "You need more? with chips or kunnu?" Ya jinjina kai alamar "Eh" kitchen ta shiga not too long ta dawo ɗauke da tray, Spoon ɗin ya ɗauka ya fara cakar chips yana taunawa a hankali, haka kawai jikin shi ya bashi ana kallon shi gently ya ɗago kai da sauri ta koma ciki tana dafe ƙirji, ya girgiza kai domin idanunsa sun riga da sun ganta tuni.
Mamakin cin abincin na Yaa Sheikh yau ya kama Mother tana zaune tasan ko tayi magana ba zai fahimta ba, sai da ya goge baki da tissue kana ya zaro Aswaq daga cikin aljihu ya fara yi.
"Ina son yin magana da kai ta fahimta Aliyu" ya maida hankali sosai akan Mother ta gyara zama ta ce.
"Halisa bata da kowa, bata da wanda kareta ya kuma ja ragamar rayuwar ta, ko da baka san yaya akai tazo gidan nan ba, amma ka tuna cewa matar kace, ban damu da kai mata kallon mata ba, wannan deal kai da Abbanka, amma ka zama garkuwa a gare ta don Allah don Annabi ba danni ba Aliyu" ta haɗe hannaye biyu alamar roƙo a gare shi, a taushashe ya kama hannun Mother duk biyun, ya jima kafin ya ce.
"Fiye da yadda kike zato, al'ƙawari ne" tai murmushi ta ce "Allah ya yi maka Albarka Malam, tare da matanka, kayi ƙoƙarin sauke hakƙin ko wacce mace a cikinsu, kada ka tauye na wani ko fifitawa" ya jinjina mata kai yana miƙewa tsaye.
Kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa tare da ɗaukan system ya shige Library ɗinsa, wasu muhimman ayyuka ne dashi gashi yana son tattara komai wajan Saif-wazir tunda da Umar-khan zasu koma, ɗalibai na can suna jiran shi da gidan marayunsa.
Misalin 10 kowa yana zaune akan dinning ana dinner Father ya ajjiye Spoon ɗin hannunsa ya kalli Zahrah ya ce "Aliyu ya faɗa miki 12 jirginku zai tashi ko?" Ganin Idanun Mother yasa Zahrah faɗin "Eh Father, nama gama shirya kayana" Jadda ta fashe da kuka tana share majina da gefen zani ta ce "Ubangiji ya bawa Malam haƙuri, an haɗa shi da wacce tafi ƙarfin shi, na rantse uwata ta haifan ban taɓa ganin ƙatuwa budurwa irinta ba, an bashi sa'ar babar shi da kaɗan fa na girme mata, gaskiya dole Malam ya ƙara aure zan nemi Hakimi da kai na ai shela a sama masa mata ko cikin masarauta ne" gaban Zahrah ya faɗi sosai kishiya za ayi mata? To ai Yaa Sheikh shi da wata mace har abada,da ita zai ta rayuwa da daɗi ba daɗi,idan har tana raye babu wacce ta isa ta shigo cikin gidanta, ba zata taɓa haɗa Mijinta da wata ƴa mace ba.
Father ya ce "Bayan auren da yake dashi?" Jadda ta ce "A'a zan maka Allah ya isa Aliyu, tun nazo gidanka kaji na kulaka? Nifa ba zan yarda Malam ya zauna da ɗirkekiyyar mace kamar durunar ruwa ba, ko ni bata ban sha'awa ba balle namiji, kana kallon ƙirjin kamar an zuba kwalta a titin gwammaja, dole ya auri ƴar ƙarama wacce zai mure ƙuruciyarta ai Alsulhu khair" bakin Halisa na rawa ta ce "To ai nima matar shi ce kuma ƴar ƙarama ce ni....," Kafin ta ƙarasa maganar Mother tayi saurin rufe mata baki, faɗan da Jadda kewa Father yasa babu wanda yaji maganar sai Maimoon.
Baƙin ciki ya cika Zahrah jin daɗinta ɗaya babu Yaa Sheikh a wajan. Cikin makirci Zahrah ta fashe da kuka tana zubewa gaban Jadda ta ce "Don Allah kiyi haƙuri Jadda, kada ki rabani da mijina yana so na, ina son shi" Jadda tai mitsi mitsi da idanu tana riƙe haɓa ta ce "Mai ƙarya aƙona shi a wuta, nifa na rarrashi Malam na bashi baki akan ya aureki da ƙyar sai dana zubar da hawaye, nace zanbi duniya kawai idan bai yarda da aurenki ba, shi ne zaki ce yana son ki?" Da sauri Zahrah ta nufi part ɗin ta, sbd gab take da yiwa Jadda rashin mutuncin wallahi.
Jadda ta ce "To ai kaga nayi mata bayani cikin sauƙi,ta fahimta da faɗa nai mata sai ta ƙulla ce ni, ai Alsulhu khair"
"Ai kam dai munga Sulhu, bamu sani ba ko zai zama alheri" cewar Auta Fattoumah. Jadda ta ce "A'a kowa ya yi ta kansa, bana shiga abin da bai shafan ba, amma fa na girgiza a bawa mutum auren sa'ar uwar shi?"
Halisa ta ajjiye Spoon ɗin hannunta idanunta ya yi jajir kalmar..
_“Yana so na, ina son shi”_ ya shiga yi mata yawo a cikin kunne. Ta miƙe a hankali tare da nufar ɗakin su Maimoon. Tana zuwa Mother ta biyu bayanta..
Ta kasa kallon Mother bakinta kuma ya ƙiyin shiru ta ce. "To yaushe zan faɗawa kowa ina da aure kuma Malam ne mijina?"
Mother ta girgiza kai ta ce "Ba yanzu ba, inda kika faɗawa wani to mun ɓata kuma zance Yaa Sheikh kada ya saki makaranta"
Da sauri tana zare ido ta ce "A'a ba zan faɗa ba, amma zan dinga ce masa mijina ko? ko Baffa?" Mother ta rasa me zata ce, surutun yarinyar baya sarrafuwa idan har ya fito to dole ta furta.. "duk yadda kika gani, amma idan kika ce miji ai Zahrah zata gane, kice Abba Sheikh" bayani ta ƙara yi mata cike da hikima na zaman rayuwa, da kuma wasu muhimman abubuwa akan Yaa Sheikh ɗin.
"Maza ta shi kije Maimoon ta ƙara yi miki saloon" ta miƙe tana cewa "To" sai da taje bakin ƙofa zata fita ta tsaya tare da kallon Mother ta ce.
"Amma idan naje can Madina zan iya faɗawa kowa ayi mini aure ina da miji?" Mother ta tafe kai tare da faɗin "Na shiga uku"..
Zahrah ce ke waya da Surry ta ce "Wallahi Surry ko da wasa aka bawa Yaa Sheikh auren wata sai na kasheta, ina da tsananin kishi akan abin da nake so, balle mutum kamar Yaa Sheikh wanda banyi tunanin zan same shi matsayin miji ba" Surry ta ce "Tab, sai ki san yadda ki kai kika tare da mijinki idan kuka tara zuri'a babu mai rabaki da shi ai" Zahrah ta ce "You're right jirginmu zai tashi, yama sunan maganin dake saka mutum feelings in 5 minutes?" Surry ta faɗa mata sunan maganin ta ɗora da faɗin "Amma dole Yaa Sheikh ya gane bake bace" murmushin mugunta Zahrah tayi tana girgiza kai ta ce "Idan kuma yana cikin maye fa?" Surry ta zare ido ta cikin wayar ta ce "Bugar dashi zaki? Kada ki cutar da ƴar mutane yafi ƙarfin ta ba"


"Surayyerh kenan, na shige duk tunaninki, kada ki manta Zahrah Farouk nake, ita kuwa Zahrah ba mahaukaciya bace ta san me take, Ƴar fillo data gama aikinta zan aiwatar da burina a kanta gudun matsala" Zahrah tai wa Surry ba zata, gashi bata da hanyar da zata taiwa Halisa magana. "Do you want to just leave me alone now? these past few days have been a bother" "Okay bey" cewar Zahrah. Tana gama wayar Halisa ta shigo tai tsaye fuska a haɗe.
"Oh su ƴar fillo an samu duniya, bari muje wannan farin na jikin ki sai na ɓatar da shi" ta tura baki gaba cikin surutu ta ce.
"Ai farin daga Allah ne" Zahrah ta ce "magana ki kai?" Tai shiru ta kalleta da kyau ta ce..
"Ki gane baki da haɗi da dangin mijina, ke ƴar aikina ce, ki daina cusa kanki inda baki da mazauni ba zaki taɓa samun karɓuwa ba, saura ki faɗawa wani ke ba ƴar uwata bace kamar yadda nace"
"Sai dai kishiya ba ƴar uwa ba" da sauri Zahrah ta ce "kika ce me?" Ta girgiza kai ta ce "Salati nayi"
Ta ja tsaki tare da cewa "Get out jakar kawai"
11:00 Yaa Sheikh ya fito cikin wata haɗaɗɗiyar Alkyabba mai kyau da tsari, ya naɗa rawani wanda ya ƙara fidda haibarsa da cikar kamalar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login