Showing 165001 words to 168000 words out of 197828 words
Chapter 56 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
yalwataciyyace kamar wacce ya sanya mata dayin sbd rabuwa da tayi kala biyu daga tsakiya zuwa goshinsa tai baƙi sosai sai ƙyalli take, daga tsakiya zuwa wuya kuma tayi jaa yawancin jikinsa gargasa ce, ga ƙirjinsa mai faɗi kamar yana ɗaga ƙarfe kullum yana da tsayi sosai but his ears are big suna da faɗi. Ya saka hannu ya zungureta tayi saurin ɗauke kai tana sauke numfashi ya ce.
"Kin wani tisani a gaba"
Ta kwaɓe fuska ta ce "to me zan yi bayan ka cika zuciyata da farin ciki"
Sai kuma ta ƙara sakin kuka hadda na shagwaɓa da zarar zai kalli Idanunta sai ta ɗauke kai ya kamota gabaɗaya tunda har lokacin El yana can yana duba motar Halisa, ya bata side hug tare da ɗora hannunsa a kafaɗarta ya ce
"Dodo na zama?" Ta girgiza kai ta ce "Wallahi Abba haka kurum kunyarka nake ji" ya saka hannu ya dungure mata kai yana girgiza kansa a taushashe ya ce
"Allahumma yaá hadiki Zawja" tayi dariya shi kuma ya ɗaga kiran Abba Hakimi tare da nufar mota ya juya ya ganta tsaye da hannu ya nuna mata ta koma cikin gida, ta ɗaga hannu tare dayi masa bye-bye
Tana shiga El ya dawo wajan Yaa Sheikh domin bar musu wajan ya yi dama, Yaa Sheikh ya shiga mota yana bawa El car key kafin nan ya yi masa gargaɗi bai son driving na ganganci a haka suka fice daga cikin gidan. Zaune Halisa ta samu Dada da Mother a parlour suna hira, Dr A'isha na danna waya Zahrah na zaune Idanunta akan plasma Surry kuma tana kallon Halisa tana ƙara yaba kyan da Ubangiji ya yi mata, Halisa tayi murmushi ta ce "Sannu da zuwa Dada sannu da zuwa Mother" Mother ta ce "Bana so, sbd farin cikin an siya miki mota ai ko kulamu bakiyi ba" tayi dry tace
"Kai Mother wake wasa da kyautar miji? Ba ko wacce mace zata sameta bafa sai wacce ta zama kamilalliyya ta kare kima da mutumcin ta har zuwa gidan miji ba dole na manta daku ba"
Maimoon tayi caraf ta ce "Absolutely right Anty Halisa, wallahi irin motar ake yayi kin zama ƴar gaban goshin Yaa Sheikh congratulations Princess" Zahrah ta miƙe zata bar wajan Maimoon ta ƙara cewa
"Laa Anty Zahrah ba kije Kinga motar ba" tayi murmushin yaƙe ta ce "Haba mu da muke gida ɗaya ai motar kamar tawa ce ko" Maimoon ta buɗe komai da komai har receipt ɗin ta ce
"Kinga kowa iya sunan Princess ɗin sakoto na gani Halisa Sheikh Aliyu haydar Aliyu" Halisa ta gyara zama tana ɗan ya tsuna fuska sbd ciwon da cikinta ke mata ta ce
"Ke kam Maimoon idan da kara ai motar ta ce" Maimoon ta watsa hannunta sama ta ce
"Oh yeahhh"
Baƙin ciki ya cika zuciyar Zahrah duk ta inda ta ɓollo amma sai Halisa ta zame, kuma bata taɓa nuna baƙin ciki gabaɗaya ta rasa mafita, ta koma ta zauna gudun kada a gano ace baƙin ciki take. Surry ta ce "Congratulations" Halisa ta miƙe ta ce "Muna zo mana" Maimoon ta miƙe tare da bin bayan Halisa har zuwa haɗaɗɗan part ɗinta, lafiyayyan girkin da tayi ta haɗa a tray ta bawa Maimoon ta ce takai Main parlour, takai ta ƙara ɗaukan wasu ta koma ita kuma tayi Alwala tare da yin sallar Asar kana ta dawo parlourn. Ƙamshi ya dinga ratsa hancin Zahrah yawonta na tsinkewa rabonta da abinci tun jiya ko breakfast ba taci ba, Mother ta ce "Surrayerh kuzo kuci abinci" Zahrah ta girgiza kai ta ce
"No thanks" Surry ta kasa jurewa ta ɗauki Spoon ta fara cin fried rice ɗin wacce taji hanta daɗi har ratsa kunnenta yake, Zahrah cikinta ya dinga ƙugi daga ƙarshe tabar wajan tana zuwa ta shiga kiran number Yaa Sheikh amma bai ɗauka ba, sai kawai ta fashe da kuka tana riƙe cikinta ga ciwon kai dake damunta.
Bayan sun gama cin abincin Maimoon ta kwashe kayan tas taje ta wanke mata ta gyara kitchen ɗin, Mother taja Halisa har zuwa bedroom ta kalleta ta ce
"Ina fata kin daina shirman nan naki" idanunta ya cika da hawaye ta ce "Har yanzu zuciyata zafi take idan na kalli Zahrah wai ita ce kishiyata, Shikenan taci galaba akai na kamar yadda tace zata dawo gashi ta dawo"
Mother ta ce "Bata ci ba, amma idan kin bata dama tabbas zata ci, tana mugun son Yaa Sheikh, Yaa Sheikh na mutuwar son ki namiji kuma baya so da ƙaunar mita ko yawan complain a rayuwar shi, kiyi kishi a kansa ba laifi bane, amma kada ki zama mai biyewa matarsa kuna tada masa da hankali, kada ki nuna kishinsa akan idanun Zahrah kiyi kishin daga ke sai shi, ki kyautata masa ki zama mace mai yawan gdy, ki fahimci kuma abinda mijinki yake ƙauna daga gareki......,"
"Taya zan fahimci me Abbana yake so?" Mother ta haɗe fuska ta ce
"How can I know bayan kece yake mijinki, kin gane me nake nufi ki zama mai kula da wajan da tsaftace shi yadda zaki dinga jan hankalinsa da su" Halisa tayi shiru tana tunani kafin ta ce
"Kuma zai kwanta da ita? Shi ne abinda ba zan iya jurewa ba wallahi" Mother ta ce "Kada ki zama selfish, idan lokacin kwanaki yazo ta hanaki za kiji daɗi? Ke matarsa ce itama haka, gabaɗaya kuma da hakƙi a wajansa fifita ɗaya daga cikinku zai sanya Yaa Sheikh ya shiga fushin Allah ko kina so ya tashi da shanyewar ɓarin jiki?" Ta girgiza kai Mother ta ce "then support him wajan sauke hakƙin Zahrah domin tana buƙatar shi fiye dake ɗin nan, don Allah Halisa kada kiyi amfani da son da Yaa Sheikh yake miki kice zaki tilasta masa yin wani abun kinji" tayi murmushi mai ciwo sosai ta ce "Mother nasan me nake, ki daina ɗaukana matsayin shasha" taci gaba da yi mata faɗa da nasiha kana ta fara bata wasu bayanan na musamman da perpumes kala-kala.
Dr A'isha dauriya take amma bata jin daɗi wanda tazo dominsa kuma ko inda take bai kalla ba gashi yaƙi dawowa cikin gidan, ta miƙe ba tare da sanin kowa ba tabar gidan.
Yaa Sheikh yana daga cikin motar ya dinga kallon Hotel ɗin yana mai yin Asstagafirullah acikin ran shi, El ya buɗe masa bayan mota ya sakko da ƙafafuwansa da suke cikin Black Gustavo parent italian leather Tassel Loafers cikin nutsuwa yake tafiya mutane suna binsa da kallo cike da mmkin abinda ya kawo babban malamin cikin hotel ɗin Tahir place, wasu kuma na risinawa suna gaida shi, a haka yabi tabbataccen wajan da aka bashi, ya tsaya a bakin ƙofa El ya yi knocking, not long aka buɗe ana faɗin.
"Ko wacce shegiyar ce yau koni ko ita....," Maganar ta tsaya dalilin ganin mutumin da bata taɓa tunanin zata gani ba a rayuwarta, ta murza idanu jiki na rawa ta koma ciki da sauri tare da faɗawa cikin toilet, Yaa Sheikh ya yi sallama bisa tsari na addinin Musulunci tare da saka kan shi cikin ɗakin, ya kalli Saif-wazir dake zaune hannunsa riƙe da kwalbar giya ga madarar sukudayen a ɗaya hannun idanunsa ya yi jajir, gashin kansa ya hargitse ya ɗago kai cikin maye ya ce "You? Sheikh Aliyu haydar Aliyu ko?" El-bashir zai magana Yaa Sheikh ya girgiza masa kai alamar a'a, Saif-wazir ya ce "Are you happy to see me cikin wannan halin? Na zama kamar mahaukaci ko?" Sai kuma ya girgiza kai ya ce "No! Ni ba mahaukaci bane ba zan taɓa zama mahaukaci ba, amma waye babana? Ni ne? A'a kai ne a'a wancan ne.?"
Yaa Sheikh ya runtse idanunsa sosai a fili ya ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Asstagafirullah Allah na tuba" Saif-wazir ya yi dariya ya ce "You role my life kai ne ka lalata mini rayuwa ka sanya mahaifina ya kureni Well-done Aliyu"
Cikin ɓacin rai Yaa Sheikh ya ɗaga hannu ya zabgawa Saif-wazir mari ya ƙara zabgawa Saif-wazir mari ya ce.
"Ka cuci rayuwarka Saifuddeen ka ha'inci Abba Hakimi, ka lalata tarbiyyar daya baka, kai aka kora na fika jin baƙin ciki ban taɓa zama wajan Abba Hakimi da niyyar wani abu, ko dukiya ko dan na raba shi da yaran daya haifa ba..."
Ya sauke numfashi idanun Yaa Sheikh har wani ruwa suke sbd ɓacin rai ya ƙara zabgawa Saif-wazir wani marin ya ce.
"Na hango soyayyar ɗa da uba a idanun Abba Hakimi nasan baya iya barci sbd rashinka, iyaye na son yaran da suka haifa fiye da yadda yaran ke son kansu, suna son yaransu fiye da yadda suke son kansu, sai kai ɗaya zaka fita zaka a cikin zuri'a ka zama wanke ɗaya" yama kasa magana El duk ya tsorata bai taɓa ganin masifar Yaa Sheikh ba sai yau, daman duk wani Aliyu Masifaffe ne don a haka ma Yaa Sheikh yana riƙe kansa, bai fiya nuna kansa ba, sai dai ya yi ta sauke ajjiyar zuciya fuskarsa tayi jajir sbd masifa kuma babu halin yi. Saif-wazir ya ce "Ka fita ka bar mini ɗaki" Yaa Sheikh cije baki ya shiga danna waya ana ɗauka ya yi magana, kana ya ƙara kiran wata number nan ma ya yi magana ɗaya biyu ya kashe wayar. Yana tsaye a wajan ya kai ya kawo wasu polices suka shigo can kuma sai ga Shugaban ƴan hisba, ya kalli Police ya ce
"Take him, ba arresting nasa ba zuwa dawanau" ya juya kan Wani ya ce "Jeka fito da yarinyar" ya nufi toilet ɗin yana turawa ta buɗe yarinyar ta fasa ihu tana faɗin
"Don Allah ka rufa mini asiri Wallahi Allah a gida ba a san halina ba, islamiyya zani shi ne nazo nan, Wallahi ba zan sake ba don Allah don Annabi wallahi bana son a sani a gida" Yaa Sheikh don babu dokan mace a tsarin shi da sai ya yi mata doka tas, cikin huci ya ce "Kai ta zuwa Hisba ka binciko iyayenta ina son ganinsu" Da Saif-wazir da yarinyar gabaɗaya aka kame su, Yaa Sheikh ya yi waje tare da shiga mota El-bashir zai shiga ya miƙa masa hannu, jikin El na rawa ya bawa Yaa Sheikh key ɗin yana bashi ya figi motar da gudu yabar El-bashir tsaye a wajan.
Daga Halisa har Zahrah an zuba wanka ana jiran dawowar Yaa Sheikh amma har akai sallar Issha bai shigo ba, Zahrah na kwance a ɗakinta Halisa kuma tana Main parlour ta kasa nutsuwa. Jikin tane ya bata kallonta ake ta ɗago kai yanayin yadda taga Yaa Sheikh ta tsorata Jikinta har rawa yake, ta miƙe tsaye ta ce "Sannu da zuwa" yaja waje ya zauna binta da idanu sai da ya gama kallon inda yake so kafin ya sauke numfashi ya ce "Kira Zahrah" tayi jim! Sai kuma cikin sanyin muryar ta ce "To"
Ta nufi part ɗin Zahrah tana ƙofa ta tsaya tare da yin sallama, bata damu data amsa ba ta ce "Habibi ƙalbi yana kira" tana faɗin hakan ta juya, ta zame kansa a ƙasa ya riƙe kan da hannu ta tsuguna har ƙasa ta kama ƙafarsa ta cire takalmin, daidai lokacin Zahrah na fitowa ta tsaya tana kallon ikon Allah sai kuma ta nemi waje kusa da Yaa Sheikh ɗin ta zauna ta cewa "Wlcm Sweetheart" bai amsa ba, Halisa ta miƙe ta ajjiye takalmin a gefe ta kama hannun Yaa Sheikh bai mata musu ba ya miƙe ta zame masa Babbar rigar jikinsa tare da cire hiramin, ta kwasa ta haura upstairs ɗin shi. Zahrah ta ce "Ina ta magana shiru ko laifi nayi?" Ta faɗa tana ɗora kanta a kafaɗar shi, bai ce mata komai ba kuma bai hana ta rungume shi ɗin ba, ya ɗaga idanunsa jin ana tafiya suka haɗa idanu da Halisa tayi saurin ɗauke Idanunta sbd kukan data tsaya tayi,ta durƙosa ta tsiyaya masa ruwa mai sanyi a glass cup ta miƙa masa, ya amsa tayi mmkin yadda ya shanye ruwan tas duk da bayan son sanyi, ta ƙara zuba masa Zahrah ta ce "Ya zaki ta bashi ruwa?" Bata kulata ba ta miƙa masa ya kuma shanye ruwan, sai a lokacin ta nemi waje kusa da ƙafafuwanta ta zauna tana zuba ruwa a cup takai bakinta zata sha taji ya ƙwace, ta juya ta kallesa taga ba ita yake kallo ba, sai daya gama tunaninsa da jan ajinsa kafin ya ce.
"Ku duka matana ne, Zahrah ke ce babba amma matsayin Matana Zawja ce gaba dake, kuji tsoran Allah ku duka ku zama matan sirri masu haɗuwa su faranta ran mijinsu, wallahi wallahi duk wacce naji ba daidai ba wajanta zan saɓa mata, ni ba mijin littafi bane da zan banbanta wata, ina son zama da ko wacce" ya yi shiru a hankali ya ce "Sai ku raba kwana" gaban Halisa ya faɗi jin batun raba kwana, Zahrah ta ce "2days 2days zaka fara dani tunda ni ce amarya idan kayi kwana biyu sai ka koma wajan Halisa kayi kwana biyu ko Uwar gida?" Halisa tayi murmushi ta ce "Eh" ya harɗe ƙafa ya ce
"Allah ya yi muku albarka ku tashi kuje" Halisa kamar jira take ta miƙe tare da shigewa part ɗinta, ya bita da kallo ta gefen idani Zahrah jiki na rawa aka tafi tare da fara shirin tarbar ango Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu. 10:23 ya shiga sakkowa zuwa downstairs cikin wata farar riga Armless mai zif a gaba, ta kama damtsen shi sumar ƙirjinsa a bayyane, sai wando three gaiter shima fari ya tsaya iya cinyarsa ya nufi part ɗin Halisa da nufin yi mata good night hannunsa zube cikin aljihu, key yasa ya buɗe ya lumshe idanunsa sbd wani ƙamshin air-con daya daki hancinsa, ga tsayin A.cn hakan yasa suka haɗu tare da haifar masa da kasala, da ƙyar ya ƙarasa cikin bedroom ɗin ya sameta tsaye a gaban mirrow tana shafa humura a Jikinta ta saka nightgown mai lace ɗin wuya ta tsaya mata iya cinya cikinta ya bayyana sosai domin ya girma ƙirjinta ya cika sun bayyana ta saman wuyan rigar, kai tsaye kuma idanun Yaa Sheikh a ƙirjin ya sauka bai san me zai ce abu ɗaya ya sani idan da abinda yafi ƙauna ga mace bai shige breast ba, suna matuƙar ɗaukan hankalinsa sai yaji kamar da gayya Halisa ta saka rigar, ta amsa masa sallama ba yabo ba fallasa ya jingina domin har ranshi tsoran ƙara sawa ciki yake zai iya yin ɓarna riƙe kanshi kawai yake, kamar ƙaramin yaro ko wani matashin saurayi ya narke murya ya ce
"Zanci abinci a sammin" sosai ya bata dariya sai ta haɗe rai ta ce "Abba ka manta wajan Zahrah zaka ita zata baka ai" ya yi ta kallonta da yadda take juya hips tana ƙara shafa humura a ƙirji tare da ɗago su sama, duk yadda ya kame kansa da yadda ya riƙe kanshi da kyau bai san lokacin daya tsinci kansa a gabanta ba, ya tsaya a bayanta tare da saka hannu a......https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL
*Follow my Facebook account sbd muhimman abubuwa👆🏾*
👇🏾 follow my account on Arewabooks please
https://arewabooks.com/u/nimcyluv
Humurar hannunta ya ƙwace tare da kaiwa hancinsa ya shaƙa ya ajjiye da sauri yana rufe idanunsa cikin nutsuwa da yin ƙasa da murya ya ce "Baki da tausayi Zawja" ta haɗe fuska tamau ta juya zuwa parlour yana zaune bai bita ba, ta ƙara dawowa ta shige kitchen lokacin data dawo ya tankwashe ƙafarsa saman gadonta daya sha bedsheet, hannunta riƙe da tray ta tsuguna har ƙasa ta ajjiye murya ba shaƙe ta ce "Ga abincin nan"
Ta faɗa tana neman waje gefe ɗaya ba kamar yadda ta saba zama so close to him ba.
Ya ɗauki mintuna bai ce komai ba can ya numfasa yana shafa cikinsa domin da gaske yunwar yake ji, ya jima bai ci wani abu mai nauyi ba ya ce "sbd za a sammin abinci ake kame fuska?" Tayi saurin faɗin
"Ranka a ɓace ka shigo ɗazo" ya ware fararen idanunsa masu haske da launi yana nuna ƙirjinsa da yatsar shi ya ce
"Ni ɗin? Injiwa"
Ta girgiza kai ta ce "Nafa gani, na gani a cikin ƙwayar idanunka Malam"
Ya ƙura mata idanu shi gani yake kamar ba ƴar fillon shi ba, Zawja matar nan ta shi rigimammiya gabaɗaya sai yaga kamar an sauya masa ita, ya jinjina mata kai yana sakkowa ƙasan carpet ya ce "To, ba haka bane" bata ce komai ba, ta buɗe warmer tare da fito da tuwon samun mita fari tas ta buɗe shi daga cikin leda ta ɗora saman plate, ta ƙara saka masa wani sai da ta saka masa guda uku a plate sai tiriri suke sbd warmer ɗin mai riƙe zafi ce, ta ɗauki wani plate ta zuba masa miyar bushasshiyar kuɓewa wacce taji nama sosai, baya wani cin tuwo sosai amma yadda ƙamshin ke ratsa hancinsa yaji gabaɗaya son cin tuwon ya kama shi.
Yana ta kallonta ganin ko inda yake bata gani ta matso da bowl da ruwa, gane nufinta yasa ya wanke hannunsa ciki. Tare dayin bisimillah ya saka yatsun shi huɗu ya gutsiri tuwon ya kai bakinsa, daɗi da ɗonɗanon ya ratsa kunnenshi, Halisa ta koma gefe hannunta riƙe da Hislul Muslim amma sam hankalinta baya kai.
Lokaci zuwa lokaci yana juya ya kalleta baya magana idan yana cin abinci ƙa'ida amma yanzu kasa riƙe kansa ya yi cikin kamala ya ce
"Haliyserh ce? Ko kowa zonan" ta juya da Idanunta da ya yi ja ta kalle shi ya girgiza kai tare da tsame hannunsa daga abincin ya wanke tas zai kwashe kwanokan ta ce.
"Kaje kawai, zan kawai it's my responsibility"
Ya dubeta da kyau ya ce
"Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce: matanku gonakinku, abin alfaharinku, ababen ɗebe kewa da sanya su nishaɗi, ku taimaka musu, da aikin gida domin ƙara soyayya da wanzar da farin ciki" Ya sauke numfashi yana shafa sumar kansa wacce furfura ta fara fitowa kaɗan kaɗan cikin kamala da sanin ya kamata da tsantsar addinin daya gama ratsa shi ya ce
Imam Zainul-abidin (a.s) ya yi nuni da kiyaye hakkin mata da fadinsa: “Kuma hakƙin mata shi ne ka san cewa Allah maɗaukaki ya sanya ta mazauni kuma wurin nutsuwa gare ka, kuma ka san cewa wannan ni’ima ce