Showing 189001 words to 192000 words out of 197828 words
Chapter 64 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
babba, mun shirya sakin labarai a Social media akan cewa Yaa Sheikh bashi da Uba, mu kaga hakan bai ba, sai muka duba yarinyar da kuka fi ƙauna a cikin ahhalin wato Halisa ita matar Yaa Sheikh ɗin, mun san idan muka kamata mukai barazanar kisa gareta dole zaku saki mahaifina, manufar shi ne ana sakin shi zan bar garin da shi"
Suka saki salati, Ummul ta dinga girgiza kai.
Mother ta ce "Sai inda ƙarfinmu ya ƙare akan Ubanka dole ya baƙunci halira" Bala Tukur ya ce
"Shi kenan?" Garbati ya ce "Eh" "Batun dabar da kake kana fashi tare da kashe jama'a, ka mance yarinyar daka nuna musu vedionta tare kuke aiki"
Garbati ya Girgiza da lamarin Yaa Sheikh.
Kamar mai gani har hanji, daman yana lura da yadda zubin fuskar shi ke sauyawa lokaci zuwa lokaci.
"Amma ya naga Halisa a jiki" "kama ce kawai" inji Garbati ya ce "Nima da kamar nayi amfani, haƙiƙa idan Halisa ta ɓata za'a iya kama Fariderh sbd tsananin kama ban taɓa yarda ana iya samun masu kama da juna ki babu haɗin jini ba sai yanzu"
Aka tattara su Garbati zuwa Police station. Yaa Sheikh ya juya cikin nutsuwa amma zuciyarsa zafi take ya buɗe bayan mota ya shiga cikin sauri Umar-khan ya shiga shima. Ya dubeta ta shiru ta riƙe Hala sai kuka take gently ya saka hannu ya jawota jikinsa ya riƙeta sosai yana shafa kanta ta sauke ajjiyar zuciya da ƙarfi. For some minutes ya ɗagota suka haɗa idanu cikin kulawa yana tattara dukkan kulawarsa akan ta ya ce "Are you Okey?" Ta ce "Abba ban yi komai ba"
Ya jinjina mata kai yana jin abu mai ƙarfi yana fisgar shi akanta.
Ya ce "Nutsu, ba wata sauran damuwa, am here, and I'll always be by your side ok?"
Ta ɗaga masa kai ya rungumeta ta jinsa ya saka hannu a riga yana shafawa tayi murmushi kawai tasan me yake nufi don haka ta gyara zaman Hala ta shiga feeding nata, har lokacin yana rungume da ita tana ɗago kai yake zaro mata idanu sai ta fahimci a yanzu shi ɗin rabi da rabi ne. Wato *MUTUM DA ALJAN*
Sabuwar rigima ta ɓalle domin Umma A'isha cewa tayi gida za a dawo da Halisa shi kuma ya ce sam ba a isa ba, babu mai tafiyar masa da matan shi aure nawa ne ya mutu daga tafiya wankan jego. Halisa taso tafiya domin ta fahimci waye Yaa Sheikh tunda ya sameta ya mayar da ita abinci, ya daina azumi sai na Alhamis da Litinin daya zame masa jinin jiki...
A wannan lokacin hankalin El-bashir Ahmad Nuran Sarki dana duk wani makusan cin shi ya tashi, abinda ake ɓoyewa ya fito aka rasa daga gidan wacce jaridan aka samu labarin fyaɗen Matar El-bashir Ahmad Nuran Sarki wato Fattoumah Aliyu. Zan can kuma sai fasuwa yake wasu suna haɗa jijita akan daman can hanyar ƴar iska ce, daga kan Social media, gidan rediyo, gidan t.v
Babu wata hujja data nuna daga wajansu maganar ta fita, da abun ya yi tsamari maganar abinda Father ya aikata da Zahrah ta fito harda batun Muhammad.
Duk Wannan maganar da abinda yake faruwa Yaa Sheikh yaja baki ya yi shiru, shirun na shi na nufin abubuwa da dama. Hankalin Mai martaba Ahmad Nuran Sarki ya tashi domin ana shirin lalata masa masarauta ne jama'ar garin Sokoto sun fara surutu akai. Sati na zagayowa aka sha shagalin sunan Halisa Yarinya ta ci sunan *Ummul-khairy Sheikh Aliyu haydar* ana kiranta da *Hala* bayan sallar zhur aka ɗaura auren *Umar-khan Abba Hakimi, da Hafsat Sheikh Aliyu Haydar* sai kuma *Prince Khalil Ahmad Nuran Sarki da Maimunatu Aliyu* Tare dana *Saifuddeen Abba Hakimi* Sosai aka sha shagali farin ciki wajan angwayen ba a magana, kada ma Khalil Yaji labari he can't believe wai yau ya auri Maimoon. El burinsa daman a sallami Fattoumah domin ƙasar zai bari da ita, duk da kwaɗayin Mai martaba na son yin murabus ya dan ƙawa El kujerar mulkin amma ya rufe idanu yaƙi sam, daga ƙarshe ma ya ce baya so shi yafi ƙaunar siyasa. Shiru babban makami ne shirun da Yaa Sheikh ya yi da wanda ya sanya El ya yi ya tayar da hankalin Fulani Atine domin ita ce wacce ta fitar da bayanan komai zuwa gidan jaridar da ba a son da zaman su ba, suka fara haɗa shi a twitter ya shiga jerin news ɗin da yake trending. Sai gashi ta fito tana surutai akan ko basu ga abin bane sun ɗauka wasa ne sai abu ya tabbata ta zare ta zama zautacciyya ta dinga tunawa kanta asiri abu yaci tura Mai martaba ya ce a dangana da ita zuwa gidan mahaukata.
_*After 3 week's*_
Saukar su kenan daga airport Ummul da kanta ta zo ɗaukan su ta amshi Hala ta ce
"Ma sha Allah, takwara tafi iyayenta kyau"
Halisa ta ce "Kai Ummul kada dai ki ce yanzu ita kike so" Ummul tayi murmushi ta ce "Babu laifi idan nayi haka, a daina kwasar mata sanyi fa kusan weather ya sauya, ayi sanyi ai zafi daga haka damuna zata sauka"
Yaa Sheikh yana tsaye a tsayin satin ukun zaka ɗauka shekara ɗaya ne, domin fatar shi ya sauya ya ƙara haske saje da gemu sun ƙara ƙawata fuskar ya daina aikin komai sai na wa'azi wanda ake sakawa a gidan redio da t.v yanzu, yana ji da gidan maruyansa. Ta dube shi ta ce "Me kuke ci a Sokoto ne?"
"Laa ai satinmu ɗaya a can muka shige Makkah" Ummul ta riƙe baki ta ce "Ikon Allah ba gaya dangi" Suka shiga mota ita take jansu da kanta Halisa na baya shi kuma yana gaba rungome da Hala wacce Ubangiji ya sanya masa ƙaunarta yana jinya tana ta tsotsar hannun shi alamar nono take buƙata. "Idan zaka zauna da Zahrah to ba kayi mata adalci ba, naga tausayi na neman ya sanya ka shiga hakƙinta" Halisa tayi shiru domin a zaman da sukai ta fahimci haƙurin Zahrah daman wani lokacin akwai huɗubar ƙawaye. "Ummul..."
"Aliyu" Yadda ta kiran sunan zaka san babu sauƙi a sanyaye yana shafa kan Hala da yake cike da suma ya ce "Kiyi haƙuri"
Gani ya yi ta ɗauki hanyar gidansa mai makon na grandparents nasa, suna shiga suka samu Jadda riƙe da Apple tana ci ga jakar kayanta a gefe, Zahrah wacce ta rame sosai sbd tsananin buƙatar namiji ta miƙe ta ce "Wlcm Sweetheart" tayi ƙasa da kai ganin Ummul Jadda ta ce.
"Daɗi miji, kin bi miji kullum cikin dare ya danneki kamar ayu babu mmki yanzu ya ƙara ɗirka miki wani cikin....
08119237616
Paid book aji tsoran Allah an ga mana magana ina sane fa! Kawai duk abinda kafi ƙarfin shi babu batun tsayawa ɓata baki akai*Da wasu suka biya da wanda suke karantawa Free 🤣 aje arewabooks ayi following acct ɗina, har girma ake taɓa Allah wadai da masu fitar da book ba haka da masu karantawa matsayin free, to ina naga lokacin surutun hakan ma🤣 typing da ƙyar sbd busy, ku shiga link ɗin kai tsaye👇🏾ku danna following*
https://www.arewabooks.com/notifications
"To ai gwara nayi cikin dana zauna zaman gulma" Jadda tayi mitsi mitsi da idanu ta ce "Azaba, daga maganar alheri sai gasa magana to ai babu laifi don kin samu ciki da ki zauna hoto kamar wannan fa?" Ta nuna Zahrah kafin ta girgiza kai cikin takaici ta ce
"Ga waccar ƴan banzar mai mugun hali ita fa ta dinga zuƙa matarka can watannin baya akan ta tsaneka" Halisa ta nemi waje ta zauna, Yaa Sheikh ya haura upstairs cikin nutsuwa tun a hanya ya fara zame Alkyabbar jikinsa sbd tsananin gajiya kuma tayi masa nauyi a jiki.
Zahrah ta bishi da kallo tana son shi a ko wacce daƙiƙa yana ƙaruwa a zuciyarta, balle yanzu daya ƙara sauya ya riƙe kan shi haibarsa kullum ƙara bayyana ga cikar kamala. Jadda ta gyara zama tana ƙara saka Apple bakinta ta ce "Ina baku labari babu kalar wulaƙanci da tijarar da Likitan nan A'isha take kowa bata yiwa mijinta ba, wai baya haihuwa dake shi sauna ne ya tsaya yana biyewa Iskancin mace banda abinsa ba sai kawai ya saki ƴar kazan uba ta kama gabanta ba, mata nawa ne a duniya ba suyi aure ba suke jiran mazan shiru"
Zahrah ko a jikinta, Ummul kuma tana riƙe da Hala wacce ta farka tana wurga hannu da ƙafa. Halisa ta mayar da hankalinta akan zancan Jadda amma zaka ɗauka maganar bai dameta ba, sbd yadda ta mayar da hankalinta zuwa ga plasma. Jadda ta girgiza kai irin zance na cinta ɗin nan.
Ta ce "tijara kala-kala tayi ina baku labari, ashe burinta ta kashe auren, ta auri mijinku malam kinji rashin amana shi yasa amana tayi ƙaranci duk yadda Matar Malam ta yarda da ita amma zata aure mata miji, haka ta dinga zugaki dake kema rainon fulani ce kika biye mata, Allah dai ya yi mijinta ba zai wulaƙanta ba, kuma babu rabon ku zama ku uku ashe ita ce bata haihuwa, yanzu dai tana can ta fita hayyacina mijin kuma kamar maye yana nan riƙe da ita kamar takalmi a hammata"
Cikin alhini ta ƙara girgiza kai ta ce
"To ni dai bance komai ba, yanzu ma ba wani abu nace ba, amma dai ta kusa cin amana"
Babu wanda ya kulata, Halisa kishi ya motsa Idanunta ya ya yi jajir domin gani take har yanzu Dr A'isha tana bibiyar Yaa Sheikh shi kuma ya san komai ya ɓoye. "Riƙe ta nan wannan dai ba tayi halin me suna ba, rigimarta yawa ne da ita" Jadda ta karkace ta ce "Azaba, Ƴar Fulani ce fa ta haifeta sai abinda kika gani"
"Ke wai miye damuwarki ne? Me Fulani sukai miki? Kina zaune a gidan Bafullatani kina masa rashin kirki, kada ki manta me gidan Bafullatani ne mahaifinsa haka, matarsa haka jinin fulani ke yawo a jikinmu and we're proud to be Fulani"
Jadda ta riƙe baki ta juya ta kalli Ummul wacce ta ɗauke kai kamar wacce bata san mene yake faruwa ranta fes kuma da abinda Halisa tayi.
"Zagina kike fa?" Halisa ta rungume Hala a jikinta tana jin kamar ma ta wurgar da ita sbd haushin ubanta ya shafe ta ta ce "Zagi ko Gasky, wallahi sai na haɗaki da Aljanu cikin dare suyi maganinki" kus Jadda tayi ta kasa gwaggwaran motsi.
Zahrah da magana bata dameta ba ta miƙe tsaye tare da nufar kitchen ta haɗuwa Ummul kayan motsa baki ta ce.
"Sannu da hanya Ummul" Ummul tayi murmushi ta ce "Yawwa Zahrah, ai bana jin zanci komai tafiya zan yi" "Tun yanzu Ummul" Ummul ta ce "Eh, kira mini Aliyu" Zahrah ta nufi upstairs Ummul ta bita da kallon tausayi.
Fitowar shi daga wanka kenan ya zura Jallabiya mai sauƙin nauyi sbd garin ya ɗan yi ɗumi ga heater data ƙara gasa bedroom ɗin. Ruwa na zuba daga sumar gashinsa ya zube a gefen lafiyayyan gadon shi yana lumshe gajiyayyun Idanunsa masu nauyin gaske. Da sallama ta shigo ya amsa cikin murya mara sauti. Tsayawa tayi tana kallon shi ya cika mata idanu ainun tama kasa ƙara sawa. Idanunsa a rufe amma yana jin idanu na yawo a jikinsa alamun ana kallon shi, speaking calmly ya ce.
"Baki sanni bane"
Tayi murmushi tana ɗauke kai ta ce "Farin sani na, kawai You have changed"
Ya miƙa mata hannu alamar ta zo, ta ƙarasa zata zauna nesa da shi ya jawota sukai kusa ta ce "Sannu da zuwa ya hanya?" Ya yi shiru.
"Ya kuka baro mutanan sakkwatawan Shehu?" Calmly ya ce "Fatymerh Zahrah" ta amsa da "Na'am Abul-khairy" "Am sorry" ta ware idanu ta ce
"For?" Ya saketa yana miƙewa tsaye ta bisa da kallo haka kurum ƙirjinta ya shiga bugawa da ƙarfi
"Mene ya faru?"
"Babu" ya bata amsa a taƙaice yana zura D&G couples slippers ta ce
"Amma ban haƙurin na mene?" He just nods his head and quickly leave the room. Ta dinga bin bayansa da kallo.
It's been 7mnts but till now nothing change, she loves him so much but all these times he rejected her love because he didn't like her.
So what exactly he meant by saying sorry to her and har yanzu yana tare da ita something fishy! Ta zube akan ƙafafuwanta kuka na fargaba ta kufce mata, tana so da ƙaunar shi tana masifar jin shi a ranta amma Soyayyar *Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu* ƙaddara ce kuma jarrabawa! Ta ƙara yarda ba komai mutum yake so ba, azaba da soyayya babban abu ne Allah ya haɗata da soyayyar *Yaa Sheikh* sbd tarin laifukan data akaita.
Bata iya barci kullum da ciwon mara take kwana kuma take tashi tun sha'awa na damunta har ta kawo lokacin da zata iya cewa bata ma jin sha'awar ta ɗauke ta kuma tafi bakiɗaya.
A zaune ya samu Ummul ita da Halisa da tayi wanka ta yiwa Hala ta sauya musu shiga sukai kyau sosai daga Hala har babarta ya ɗan saci kallonta ganin ta haɗe fuska. Ya nemi waje ya zauna cikin nutsuwa yaja idanunsa ya lumshe yana ɗan jan gemunsa.
"Aliyu!" Ya ware idanu gabansa har faɗuwa yake duk sanda Ummul ta kira shi da sunan da yake mancewa shi ne asalin sunansa.
"Na'am" ya amsa ganin kamar akwai abinda zasu tattauna yasa Halisa ɗaukan Hala ta nufi bedroom ɗin da Jadda ta shiga. "Nasan kasan me kake kana da tsoran Allah, so ka ƙara sanya tsoran Allah cikin lamarinka, tuni zan maka Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce: Fazakkir fa'innàl zikkira tamfa'ul mu'uminun"
Tayi jim ta ce
"Ku tunatar domin tunatarwa tana amfanar mumini, na ɗauka kana son Zahrah shi ya sanya na zuba maka idanu naga kudun ruwanka, koda kana sonta zama kai da ita cutarwa ne, babbar soyayyar da zaka nunawa Zahrah shi ne ka haɗata da wani mai nagarta ka bashi aurenta, ita macace bata da kowa taci abinci ta kwanta dole akwai matsala saɓanin kai da kke namiji shekaru. Ko wacce daƙiƙa da mintuna idan suka shige basa dawowa, rashin dawowar na nufin abubuwa da dama ciki hadda lokaci,idan kayi amfani da lokaci a gurbin daya dace ba, idan ƙarin auren ka ke buƙata babu mai hanaka idan ma huɗu zaka zuba Aliyu"
Ya dubeta da sauri ta ce
"Ai Allah ya baka aron rai da damar yin mata huɗu ku? Amma kada ka zauna da matar da ba zaka amfana mata da komai ba, itama haka.
Kada wannan tausayin ya yi gabala akan gasky ka saketa ka saki Zahrah Aliyu domin ta samu ƴancinta na cikakkiyar mace" ras! Gaban Zahrah ya faɗi komai suke faɗa a kunnenta. Tama kasa kuka sai a lokacin ta fahimci kuka rahama ne, zuciyarta ta dinga ɗagawa tasa hannu ta dafe ƙirjinta dake bugawa, sunan Allah kawai take ambata wanda yanzu har a zame mata abin ambato a kullum. "Kaji me na ce?"
"In sha Allah" ya ce a sanyaye ta miƙe tsaye shima ya miƙe yana ɗaukan key car ta bisa da kallo domin tasan waye Yaa Sheikh ta kuma san ɗanta farin sani.
"Kayi fushi dani ne Arɗo?" Ya ɗan marairaice fuska wanda ya saba yi a gabanta ta ce "Sannu fa"
Ya gane me take nufi ya nufeta tare da shigewa jikinta Ummul ta sauke numfashi a yanzu a rayuwa ita babu abinda take so da ƙauna kamar Yaa Sheikh shi ne komai nata, shi yasa baya girma a Idanunta akan shi kuma taƙi amincewa da tayi aure. Babu wanda yake iya Fuskantar Yaa Sheikh da niyyar yi masa faɗa sbd ana ganin yasan kome bayan a rayuwar nan babu wanda baya buƙatar Mentoring.
Ta shafa kan shi ta ce
"Allah ya yi maka Albarka da zuri'ar ka" ta rufe idanu tana jin ƙaunar Ummul har ran shi.
"Best mother ever, my best friend" ta dungure masa kai kamar yadda ya kewa Halisa ta ce
"Ni ce Best friend ɗin?"
Ya ɗan yi murmushi sukai waje ta ce
"No thank you, ni da nake a mota zan je gida yanzu In sha Allah" "Allah ya tsare" ta ce "Amin".
A nutse take driving har ta fice daga cikin makeken gidan na Yaa Sheikh. Ya yi shiru yana bin green flowers ɗin da suke wajan, bai shiga cikin gidan ba ya nufi gidan gonar shi wanda yake ɓangare guda a cikin gidan shi, tattabarun shi na ganinsa suka fara sakkowa ya nemi waje ya zauna ya zura ƙafar shi cikin ruwa yana watsa abinci kifaye suka taso sama. Baya ɗaya daga cikin wanda suke son ƙarin aure, matar shi ta wadatar da shi da komai, ba raga masa ba, abinci, kulawa, biyayya tana ɗauke buƙatar shi a koda yaushe tana bashi farin cikin da shi kan shi yake mamaki.
Halisa ta dubi Jadda dake cewa "Ai Danta A'isha ba tayi ba, babu mamaki shi Malam ɗin ya san komai yaƙi faɗa miki, ke kuma daɗi miji kina baje masa ƙafa yana allan dungure a ciki sai fa ya kai ki ya baro ya ɗirka miki ciki, ki tashi mai kwanika ga goyo ga ciki, yo shi meye ruwan shi? Namiji ai sam bai da kunya daman tunda naga yana azumi kullum nasan babu lafiya"
Tayi ƙasa da murya ta ce "Don ma ya haɗu da fitinanniyya irin shi duk sun zama ƴan iska suna sharholiyya a gaban jariri" sosai Halisa ta jita amma tai burus.
Daga Zahrah har Halisa babu wanda ya sake ganin Yaa Sheikh.
Ta samu Hala ba tayi rigimar data saba ba, dinner ta haɗa mai kyau tayi Alwala da sallah kana ta shirya ta baza turare. Tana zaune a parlourn dake part ɗinta tana feeding Hala ƙamshin turaren Roja ya bayyanar da zuwan shi kafin kamilalliyyar muryarsa ta bayyana cikin nutsuwa ya shigo ta amsa sallamar babu yabo babu fallasa.
Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai kawai ya yi mmki domin ko Hala na bayanta tana barci yana shigowa take tashi ta nufesa shi kuma ya rungumesu bakiɗaya.
Ya zauna kusa da ita speaking calmly ya ce
"Madam yunwa na keji"
Tayi shiru ya kalleta da kyau Idanun Hala ya sauka akan mahaifinta ta dinga bin duk inda yabi da fuskar shi daya tabbatar shi take kallo ya saka hannu ya ɗauketa.
"Malam ba kaga nono nake bata ba?" Not looking at her ya ce
"Ni sai na sha"
Ta haɗe fuska ta ce
"Ko Dr A'isha ba" maganar ta dake shi ya kalleta sai