Showing 135001 words to 138000 words out of 197828 words
Chapter 46 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
masu kyau" Hajja ta ce "Zasu ja kuɗi fa" "Amma kin san kuɗi ba matsala bane, bani target na fita waje ki duba komai Expensive haka, bana son lace na ƙasa da 200k Please" Hajja ta ce "Babu damuwa" suka shiga wata maganar duk akan haɗa kayan lefen. Suna gamawa Ummul ta samu Halisa tai mata tas akan sakewa namiji jiki da take yana moreta son ran shi. Halisa ta kalli Ummul ta ce "Ummul tausayin shi nake fa" Ummul ta riƙe baki sai kawai ta juya cike da mamaki. Ta samu Yaa Sheikh tsaye a parlour ko bata faɗa masa komai ba, yasan ya yi laife ba zai shige tafiya da Halisa da ya yi ba. Yana tsaye Halisa ta fito sukai waje har suka isa gida basu ƙara magana da juna ba. A harabar gidan suka samu Mai martaba tsaye sai Abba Hakimi da Khalil, da kuma Dada sai kuma El-bashir dake wheelchair, mother da Umma A'isha. Yaa Sheikh ya fito Halisa ma ta fito ta ce "Ina zaki Dada?" Kai tsaye Abba Hakimi ya ce "Sokoto zata koma masarauta, tare dake sai sati uku zaki dawo" farin ciki ya kama Halisa zata dangin mahaifinta, Khalil ya ce "Jirgi baya jira fa" Abba Hakimi ya ce "Halisa shi ga mota, Khalil shigar da Mubasshir ciki" Yaa Sheikh ya tsaya kallon ikon Allah tafiya da matar shi ba tare da an sanar masa ba? Ya rasa me yasa Abba Hakimi yake haka ne? Shi kam yau zai nuna cewa shi ne mijinta zai nuna ƙarfin iko, duk suka shiga mota Halisa ta tsaya tana kallon Yaa Sheikh Abba Hakimi ya ɗaure fuska ya ce "Shige ki tafi, ai zaki dawo wajan shi ne" a sanyaye ta juya zata shi ga mota Yaa Sheikh ya ce "Idan har ki ka bar gidan nan zuwa Sokoto to na haƙura da ke, na cire igiyar aure dake kan ki wallahi Allah....
08119237616*_Mai son ai masa tallah a IDAN BA KE kwana 5 za a bada 1,500.... Kwana goma 3,000 kwana sha biyar 4,500 kwana ashirin 6,000 wanda yake so a saka masa har littafin ya ƙare zai bada 15k dubu goma sha biyar❤️ Littafin Idan ba ke na kuɗi ne 500 nrml grp,1k for Special posting har weekend 08119237616_*
Thank you for choosing sarautar's Library💋🫶🏼.
Halisa ta tsaya ba tare data ƙarasa motar ba, annurin dake fuskantar ya ɗauke da mmki sosai take kallon Yaa Sheikh, ba tare da ta ce komai ba jiki a sanyaye ta nufi cikin gidan idanunta na zubar da hawaye. Yaa Sheikh yabi bayanta da kallo ta gefen idanu, daman bai riga daya shige ciki ba, murmushi Abba Hakimi ya yi yana jinjina kai ya ce "Khalil ku je, Allah ya tsare ya kai ku lafiya" Mai martaba yaso a wannan karan ya zauna da Princess Halisa, ya nuna mata soyayya irin ta ƴa da uba, amma ba shi da ikon yin magana tunda yanzu ita ɗin ba ikon shi ba ce. Ita kanta Dada bata ji daɗin abin da Yaa Sheikh ya furta ba, sai dai ba kowa za aiwa abin da akewa Aliyun ba ya jure, an shirya tafiya ba tare da sanin shi ba, alhalin shi ne mijinta kuma sai da izinin shi. Mother ta ƙarasa wajan Yaa Sheikh dake shirin shigewa ciki ta ce.
"Aliyu!" Ya tsaya yana harɗe hannayensa a baya ba tare daya kalleta ba, ta ce "Ka ba ni mamaki da kunya sosai Malam, ba kaiwa Abba Hakimi al-kunya ba, duk da hukuncin shi ya yi tsauri na tura Halisa,amma yana da kyau kayi magana mai kyau yadda za a fahimta ba tare da zuciya ko ran wani ɗaya daga cikinmu ya ɓaci ba" ta kalle shi taka ba ita yake kallo ba, hannunsa ɗaya dafe da kansa alamar ciwo yake masa ta ce
"Ka yi haƙuri, kabar Daughter ta ziyarci dangin mahaifinta a karo na farko na rayuwarta, babu wanda ta sani, yanzu ne ya kamata ta zauna dasu, su bata Soyayyar dangin mahaifin data rasa, baka duba yadda tayi farin ciki ba ko? baka duba yadda furucinka a yanzu ya sauya mata lissafi ba? Ko dan son da take maka" Abba Hakimi ya ɗagawa su Mai martaba hannu har suka fice daga harabar gidan, ya juya zuwa inda Mother take tsaye da Yaa Sheikh, ba yabo ba fallasa ba alamun damuwa ya ce.
"Ya yi abin da ya dace ne a matsayin shi na mijinta, bada wata manufa nai maka hakan ba, ba kuma dan na takura auren ka, ko dan auren bai mini ba sam, nasan son Halisa sosai, tun ba yanzu ba, ban kuma damu daka furta gaban kowa kana son ta ba.Alal haƙiƙa nayi haka ne domin na ƙara inganta aurenku, ya kafa tarihi a duniya ba iya family ba, duk macen da mutum ya rena har zuwa matakin duniya ya kuma aureta, batun ace bai san wahalar aure ba wannan gaibu ne da tsagwaron son zuciya,yafi kama da tatsuniyar gizo da ƙoƙi, muje ciki ka ɗauki matarka, Allah ya sanya albarka cikin rayuwar aurenku ya kaɗe fitina"
Ya juya cikin gida zuciyarsa cike da mamakin Yaa Sheikh ɗin da kuma rashin ta idanu da ya yi masa.
"Baka kyauta ba Malam" ya juya ya dubi Mother a hankali cike da gajiyawa da komai dake faruwa ya girgiza kai ya ce.
"Ina son kai ta da kai na ne, shi ne burina" ya yi gaba, daman tuni Umma A'isha ta shige cikin gidan. Mother ta bi bayansu, Abba Hakimi na tsaye kamar yadda Yaa Sheikh yake tsaye ya kalli Mother ya ce.
"Kirawo mini ita" Umma A'isha ta ce "Kayi haƙuri Hakimi, kada ka biyewa zuciyar Aliyu data fara sanin mace yanzu,ai masa uzuri" "Kin Allah a yau kuma yanzu sai Aliyu ya ɗauki matar shi sun tare, kada na sake jin bakin ki Aishatul-humaira" ta ce "Allah ya baka haƙuri" lokacin da Mother ta shiga Halisa na kwance akan gado ta rungome, ta ɗauka Abban nata zai so farin cikinta, tana son iyeyenta, danginta She wants to spend some time with her father's family, taji daɗinsu tasan yadda suke amma shi ne zai sanya ƙafa ya yi fatali da farin cikinta? Duk wanda bai son Ahhalinta kamar ita ce baya so, ya nuna Jikinta yake muradi amma banda farin cikinta, a karo na farko taji zafin Yaa Sheikh mijinta, ma riƙnta, uban yaron dake cikinta fiye da kima ta ji sam ba zata iya bari ko yatsarta ya kama ba. Ta yi saurin goge hawayen dake bin fuskarta tana mayar da sautin kukanta, sbd motsin da ta ji, ta miƙe zaune tare da yin ƙasa da kanta. Mother ta nemi waje ta zauna ta ce
"I saw that you were crying" ta yi murmushi ta ce "Barci na fara"
"You supposed to do that, but not now" Halisa ta ƙara yin murmushin ƙarfin hali tare da yin ƙasa da kanta irin al-kunya nan ta Fulani
"Your grandfather is calling you, ki saka hijabi ki fito"
A sanyaye ta ce "To" ta miƙe tare da ɗaukan wani hijabi sage green ta saka Kyakkyawar fuskarta ta bayyana wacce ta ƙara haske da cika, ta zura slippers ta nufi Main parlour. Cikin ƙaramar muryarta tai sallama ta nufi tsakiyar parlourn ta zauna ƙasan carpet ta ce "Gani Jon wuro" Ya kalleta ya ce "Tashi ki bi mijinki Halisa" zuciyarta ta buga da ƙarfi tai ƙasa da kanta ta kasa cewa komai, Yaa Sheikh ya jingina da jikin ƙofa idanunsa a kanta, sai yanzu ladamar furta abin da ya ce ta lulluɓe shi, amma a yanzu ko haƙuri ya bayyanar Abba ba zai ji ba, kuma ba zai saurara ba.
"Magana nake ki tsaya mini, ba daman an saka muku ido ba? Yanzu an cire tashi ki je Allah ya tsare ya bada ladan aure" hawayen da take maƙalewa ya gangaro zuwa fuskarta cikin Muryar kuka ta ce
"Kayi haƙuri nai kuskure Jon wuro ba zan sake ba, ina neman alfarma a gareka ka janye batun na bi wani, ka barni na zauna tare da ku" da sauri Mother da Umma A'isha suka kalli Halisa ba wasa ko sakin layi a cikin maganarta. Abba Hakimi ya ce "Mijinki ne, bana wani ba ra'ayinki shi ne zaki ba, amma ai kina son shi meye dalilin haka?" Ta saki murmushi sosai ta ce "Bana son shi Abba, bana son zama da shi, ina son ya bani ta kardar sakina kamar yadda ya furta" Mother ta ce "Ai ba ai sakin ba, cewa ya yi idan ki ka tafi kuma ai kina nan" ta kalli Mother ta dawo ta kalli Yaa Sheikh ta ce.
"Amma ai ya yi niyya? Kuma Ubangiji da ita yake amfani Mother, Yaa Sheikh jikina ya ke so bani ba, ba kuma farin cikina ba, na ɗauka shi da kan shi zai ce naje ga dangina sai naga saɓanin haka, ban san kowa ba sai Hamma Khalil da Hamma El duk da bana jin zan amshi shi matsayin yayana, ba zan zauna da Yaa Sheikh ba, ba zan zauna da shi ba, zanta zama a wajanka Jon wuro zuwa sanda zan haihu ya sakeni nayi idda na samu miji nai aure" Yaa Sheikh ya runtse idanunsa jiri na neman ɗaukan shi, yana hasko rigima a idanunta amma bai hasko wannan tashin hankalin ba, wanda ba zai iya ɗauka ba kuma ba zai jure hakan ba.
"Daughter kin yi kuskure, kin fahimci Yaa Sheikh ba daidai ba, kada kiyi amfani da ƙaramar ƙwaƙwalwarki ki datse soyayyar dake tsakaninku, kada ki hau tubalin da zai kai ki zuwa ladama, ita *DAUƊAR GORA* ciki kan shata (Real Smasher)" Halisa ta fashe da kuka ta ce
"A lokacin na so shi,kamar bana son kai na, babu abin da nake muradi a duniya sai shi kaɗai a rai na, Mother tana bi jire bani Abbina da yanzu ni ba Matar shi ba ce, kawai yanzu naji ba zan iya zama da shi ba" Mother zatai magana Abba Hakimi ya ɗaga mata hannu ya ce
"Ba a shiga sha'anin mata da miji sai kiji kunya, ki bari tabi abin da zuciyarta ta yanke mata" _A decision of the heart,
What the heart chooses._
"Allah ya kyauta,ya kawo sauƙi cikin lamarin" cewar Umma A'isha. Abba Hakimi ya ce "Jeki Allah ya yi miki Albarka!" Ta miƙe tsaye zata koma bedroom bai san mene ya faru ba, sai ganin shi ya yi tsaye a gabanta riƙe da hannayenta ya kafeta da jirkitattun idanunsa masu laushi da nuna tsantsar buƙatar miji zuwa ga matar shi.
Ya kasa magana sai launin idanunsa daya sauya ƙwarai, zafin zuciyar shi ya fi ƙarfin ya bayyana yadda yake ji a cikinta, tamkar gobara ce ta tashi wani ke ƙara tuttula mata fetur.
"Nasan ba gasky bane Zawja" ya faɗa a taushashe cikin wata kalar muryar shi kan shi bai san ya faɗi hakan ba. Ta kalli cikin idanun shi ta ce "Babu ƙarya a irin riƙon da kayi mini, babu kuma wasa a irin darussan daka bani, dan haka ban taɓa ƙarya ba kuma ba zan fara akan ka ba Malam Yaa Sheikh"
Ya fesar da numfashi ya kasa magana ya yi ƙoƙarin jawota ya rungome ko zai ji nutsuwa tayi saurin bige hannunsa ta ce.
"Ina jin al-kunya sbd shekaru da furfurar dake tare da kai, baka duba halin da zan shiga ba da ace ka sakeni, ka manta da kai ɗaya nayi sabo, dan haka wannan ya zama First and last da zaka ƙara kai hannunka jikina, domin na haramta a gareka, kyautatawa ɗaya zan maka shi ne ɗan ka da zan raina a cikina na kuma shayar da shi nonon da ka ke kwaɗayi" cikin harshen larabci ya ce
"Zawja ki fahimta *_IDAN BA KE_* kamar babu Aliyu ne" ta kalle shi sosai ta ce.
"Sai wata rana" ta juya da sauri zuwa bedroom ɗinta, kuka na ƙwace mata, Allah ya ji ya gani tana son Abbanta amma dole ya barta ko yasan zafin so da kuma raɗaɗin da take ji na abin da ya yi mata. Yaa Sheikh ya sulale ya zauna saman kujera ya dafe kai da hannu bibbiyu, daman tuni su Mother suka bar wajan. _When all is gone_
A wanann rana da kuma daren zuƙatansu da zuciyoyinsu basu zauna lafiya fa, _The night was long for them, a dark night and the heart was filled with sorrow_ sun rasa ya ya za su yi, _The night that prevented them from sleeping, the love and passion for each other entered their hearts more and more_
Da asuba Yaa Sheikh bai iya jan jam'i ba, sbd zazzaɓin daya rufe shi da wani wahalallan ciwon kai, da ƙyar ya iya zuwa masjid ɗin.
Da azumi ya tashi har wajan ƙarfe 12 bai ta shi ba. Misalin 2:45 ya shigo cikin parlourn sanye da shadda cream colour babbar riga da ƴar ciki, ƙafarsa sanye cikin Black Gustavo parent italian leather Tassel Loafers sai ɗaukan idanu takalmin ya ke, hannunsa maƙale da Rolex na Companyn Daytona. Ƙamshin Roja ya sanya Ummul ta ɗago kanta, suka haɗa idanu tayi saurin janye nata, domin ƙarara tashin hankali ya bayyana a fuskar shi, Dattijo da Hajia suka kalli Yaa Sheikh ta ce.
"Mai gidana shigo mana kai tsaye" ya dai tsaya ta ƙara cewa "Lafiya dai?" Ya ƙara yin shiru ta gyara zama ta ce "To kaci kan ka, wallahi nafi ƙarfinka sai dai uwarka gata nan" Ummul dai tayi murmushi kuma bata kula Yaa Sheikh ba, alrdy Mother ta sanar mata komai, hakan ya yi mata daɗi duk da abune mai wahala Halisa ta ce dole sai ya rabu da ita, ya ƙarasu ciki ɗauke da Sallama kan akan cinyar Ummul ya gaida kakannin na shi.
Shi bai magana ba Ummul ba tai ba, can ta ce "Ɗaga ne da na kawo maka lunch" ya girgiza kai ya ce "Azumi" ta ce "To Allah ya bada lada" a hankali taji gabaɗaya kan shi ya ɗauki zafi sosai ta taɓa kan ta ɗauke hannu ta ce "Baka da lafiya?" Ya ce "Lafiya lou" tai ta kallon shi. Ta cire hiramin ta dinga shafa sumar kan shi tana masa addu'a, a haka taji saukar numfashi shi ta leƙa taga ashe barci yake.
Wasa wasa sati guda ya shuɗe, na biyu ya shafe, na uku ya shige sati huɗu cif bai sanya Halisa cikin idanunsa ba, ko gilmawar ta baya gani.
Halisa kuma sai ta fahimci baya gidan take fitowa parlourn suyi hira, da zarar taji motsi ko ƙamshin turaren shi take barin wajan. Tana shan wahala amma haka take jurewa cikin dare tayi ta kuka tana riƙe ƙafa, ta faɗa sbd buƙatar mijinta da take, Yaa Sheikh baya bambance Alhamis da Litinin kullum cikin azumi yake,ya rame sai fararen idanunsa da suka ƙara fitowa. Zahrah ce kwance gadon asibiti Jikinta na rawa, na'urar room ɗin sai ƙara take, Surry ta riƙe ta riƙe Muhammad sosai, cikin sauri Mimi da Dr suka shigo ganin ba zai iya ba, ya ƙara kiran wasu likitocin aka nufi emergency da ita, da ƙyar suka shawo kan matsalar. Alhaji Farouk da Mimi suka kalli Dr ta ce "Ban fahimta ba Dr mene ya samu yarinyata?" Ya gyara zama yana zame Glasses ya ce "Bayan hawan jinin da take da shi, ciwon zuciya ya shige ta da ƙarfi, bai kai matakin aiki ba, amma irin shi da wuri yake kisa, domin ganin yarinyar ku ta ci-gaba da rayuwa a duniya ya zama dole ki bata abin da zuciyarta ke so" Kuka ya ƙwacewa Mimi Alhaji Farouk ya ce "Me take so har haka? Idan kuɗi ne akwai komai take so za a siya mata" Mimi tana kuka sosai ta ce "Abin da Zahrah ke so, kuɗi bai isa ya siye shi ba, ko da zaka ƙarar da gabaɗaya dukiyarka ne, ba zaka sama mata Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu ba" Alhaji Farouk ya miƙe ya ce "Dole naje na samu mahaifiyar Yaa Sheikh da Abba Hakimi tun da mahaifin shi baya duniya ya zama dole"
Cikin dare wajan ƙarfe 3 Halisa na zaune a saman kujera hannunta riƙe da ice cream wanda Maimoon ta siyo mata a Havilla, ta saka a freezer ya ƙara sanyi tare da ƙanƙara. Ta lumshe idanu tare da siɗe ƙaramin cokalin da baki sanyi na ratsa ta sosai, yana ƙara sanyata cikin wani hali feelings mai tsanani na ta so mata, ta ajjiye ice cream tare da miƙewa tsaye daga ita sai Riga da wando na Pajamas white colour Yaa Sheikh's favorite colour ta sanya Scuff faux-shearling slippers sai ƙamshi take ƙirjinta ya ƙara cika, ta miƙe zata juya zuwa cikin bedroom kenan ta ji an ɗaga ta cak tare da fara tafiya da ita...https://vm.tiktok.com/ZMYJCVDeF/
Ka shiga link ɗin ka faɗi kalma ɗaya mai kyau akan littafin idan ba ke👆🏾08119237616
Ko ba a faɗa ba, tasan shi kaɗai ne zai iya yi mata haka, ta shiga kokawa zata ƙwace kanta amma ta kasa, ta daddage ta fasa ihu ta ce
"Wallahi zan maka ihun kwarto idan baka sauke ni ba" bai shirya tunan asirin da take shirin yi masa ba, ya yi saurin dire ta ƙasa yana riƙe da hannayenta, kalmomin da zai mata bayani yake ta harhaɗowa a bakinsa amma ya kasa samun cikakkiyar kalma ko ɗaya, ganinta kusa da shi ba ƙaramin barazana bace ga zuciyar shi da kuma abin da ke addabar shi tsayin satittika.
Ya numfasa yana riƙe kan shi gudun kada ya yi abin kunya a gaban ƴar ƙaramar Yarinyar dake neman jan shi a ƙasa ya ce "Zawja ni ne kwarto?"
Ta kame fuska tare da ɗauke kai can, ganin yadda muryarta ke tasiri a zuciyar Yaa Sheikh take saukar masa da nutsuwa yasa ta ƙara tsuke ɗan ƙaramin bakinta.
A raunace cikin wani sabon yanayi mai wahalar fassaruwa YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU ya furta.
"Zawja ƴar fillona come to your husband, why are you doing this to me, am I stranger?" Cikin ƙarfin hali, da rashin nutsuwar Zuciya data gangar jiki ya furta hakan.
Halisa ta ƙwace hannunta tana yin nesa da shi taƙi cewa komai, babu alamar tausayi akan fuskarta... Taurin kan yarinyar ya bashi mamaki bai san lokacin data sauya ta zama mai kafiya da naci haɗi da zafin zuciya ba. "Anya kina son