Showing 171001 words to 174000 words out of 197828 words
Chapter 58 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
kamar zata wawulon shi mai haƙuri ɗaya ya ce
"Sallah" da sauri ta ce
"Nima sallah zan yi" mmki duk ya addabe shi ya yi mata kallon tsaf! Ya ce "La sallah Ala, ban janabati sai kinyi wankan sarki" ta ce "Mene wankan tsarki?....
Afuwa my Special kunji shiru, ku tayani da addu'a kawai Please... Kwana biyu sai a hankali.*_Arewabooks@Nimcyluv 73_*
Yaa Sheikh was speechless ya lura da Zahrah bata da ilimi na addini, everything and anything babu, Ilimin addini zero, kula da miji zero, girki zero, shagwaɓa zero, ƙirji zero that's too much to her.
Bai ƙara ce mata komai ya ɗauki hiraminsa ya naɗa as asual, kai tsaye downstairs ya nufa bakinsa ɗauke da tasbihi gabaɗaya bai lura da Halisa dake durƙoshe a main parlour ba, walking slowly cike da nutsuwa ya nufi part ɗinta, ganin ƙofar buɗe ya sanya ya shiga bakinsa ɗauke da sallama cikin murya mai tsananin taushi.
Babu ita a bedroom ɗin, he was thinking ko tana bathroom tunda daman sallah bata shigeta, daman kuma hakƙinsa zai sauke a matsayinsa na miji. Ya juya tare da buɗe ƙofar da zata fitar da shi daga Main parlour ya nufi compound zuwa masjid. Tun a yanayin tafiyar shi Halisa tasan shi ne kafin kuma ƙamshin turaren shi ya biyo bayan, da ƙyar ta iya ɗago kanta tabi bayansa da kallo zuciyarta babu daɗi Banda duhu babu abinda take gani cikin ƙwayar Idanunta, kuka ya yi mata hijira bata taɓa sanin yinsa Rahma bane sai yanzu. Ta miƙe da ƙyar tana ambaton Allah tasan wayonta bazai fitar da ita, daman kuma ance komai yayi zafi maganinsa Allah. Tana shiga bedroom ɗinta taja ta rufe tare da murza key, bata iya wankan data saba duk Subhi ba, alwala tayi ta sauya duguwar rigar Jikinta zuwa Jallabiya.
Bayan ta idar ta jima tana addu'ar samun kusanci da mijinta, duk wani abun sharri mugun ji da mugun gani ya ɗauke idanun abin daga kansu, daga ƙarshe ta nemi Ubangiji ya sassauta mata zafin kishin da take dashi akan Abbanta Yaa Sheikh.
Wani irin zafin Yaa Sheikh taji wanda bata san dalili ba, amma maganganun da Zahrah ta faɗa ya tsaya mata suna ta kokawa da ƙarya da gaskiyar dake son gasgata batun nata, tana nan zaune taji ana knocking ƙofar babu mai yin hakan sai shi, taƙi motsawa can cikin taushin murya taji ya ce
"Zawja" tayi banza da shi su take ta barshi shi da Zahrah taga inda iya al'amarin nasu zai tsaya, Yaa Sheikh dake tsaye hannunsa riƙe da Casbawa bai jima a Masjid ɗin ba, domin hankalinsa na kan Halisa da abinda yake cikinta, tun a jiya ya fahimci kamar ba daidai take ba, shi ya sa 6:00 daidai ya fito tare da dawowa zuwa duba halin da gabaɗaya matayen nasa suke, Yaa Sheikh ya gyara tsaiwa idanunsa na lumshewa ya ƙara lanƙwasa harshe ya ce
"Are you ok Zawja"
Still batai magana ba, hakan yasa ya kasa samun nutsuwa ya juya zuwa bedroom ɗin nasa yana shiga ya ɗaga fararen idanunsa suna haɗa idanu da Zahrah ta fasa ihu da sauri muryarsa na harɗewa ya ce "La'ilaha illallah Muhammadur Rasulullah s.a.w" Ya riƙe kansa daga kallonta ya nufi gaban mirrow tare da ɗaukan key ya nufi waje tabi bayansa da sauri suna sauka tayi part ɗinta shi kuma ya tsaya tare da buɗe ƙofar Halisa, yana shiga ya sameta zaune inda tayi sallah hannunta riƙe da Alkur'ani, bai ce komai ya karɓi Alkur'anin tare da ajjiyewa waje guda, kana ya dawo ya ɗauketa cak tayi saurin haɗe fuska ta ce "Meye haka?"
He just staring at her face yana hango rigimar gaske ya zauna saman kujerar dake kusa da bed ya yi nishi like he so much tried. Yana sakin fuska ya ce
"Tubarkallah, Zawja kada Kiyi lukuta fa" ita da kanta mmkin yadda Jikinta ya buɗe bakiɗaya take tayi ƙiba taban mamaki musamman hips ɗinta wanda yake ƙara tabbatar da girman cikinta. Muryar na rawa gudun shiga hakƙi ta ce
"Sabahul khair" Ya kama fuskarta tare da juyo da ita amma sam taƙi yarda ta kalle shi ya yi mata shiru yana saka hannu ta baya tare da rungomota zuwa jikinsa hannunsa yana shafa cikinta daya kumburo sosai a hankali ya manna labɓansa a wuyanta yana goga mata hancinsa, tattausan gemunsa na shafar fatar wuyan nata, tsikar jikinta ya tashi sosai sai da ya gama shafar inda yake so da yake tsole masa idanu kafin yace
"Meke faruwa?" Tayi shiru ya sauke numfashi a nutse tare da miƙewa da ita ya ce "don't tell me, but ki saka Allah cikin lamarin ok?"
Ya kwantar da ita da ita tare da durƙosawa ya ɗaga rigar Jikinta duk tana binsa da idanu ya sumbaci cikin tare da yin addu'a ya shafa, kafin ya yi magana wayarta ta fara ringing ya dubi wayar haɗaɗɗan pictures ɗinsu ne shi da ita a screen wallpaper. “Hamma El”
Yaga an rubuta bai ɗaga ba ya miƙa mata tayi saurin ɗaukan wayar tana kwaɓe fuska cikin rigima da shagwaɓa ta ƴar auta ta ce "Hamma"
Ta cikin wayar ya ce
"Princess, gani nazo wannan neman rigimar ya yi yawa" ta marairaice fuska tana sakin kuka ta ce "Uhm ni dai a'a" ya kalli harabar gidan Yaa Sheikh banda ƙamshin flowers da kukan tsuntsaye babu abinda kake ji gwanin sha'awa gidan."Ina Compound" tayi saurin cewa
"Gani nan" ta goge hawayen idanunta tare da ɗaukan hijabi, ya dubeta da kyau ko'ina na jikinta sheƙi yake musamman fuskarta, a haka zata fita Compound masu aikin duk suna nan, ya miƙe fuska a kame
Ya ce "Ki cire tunanin fita Compound" yana faɗin haka ya fita, tayi shiru domin bata gane me hakan yake nufi ba, ta kira El-bashir ta ce ya shigo. Ta fita zuwa main parlour hannunta riƙe da waya a zaune ta samu Yaa Sheikh yana kallon labaran tashar Aljazira, tana nan tsaye El-bashir ya yi sallama ya shigo hannunsa zube cikin wata Marron ɗin Double Breasted suit, ya saka Derby shoe sai ƙamshin Thierry mugler yake,ya yi murmushi dimples ɗinsa irin na Halisa ya bayyana yana ƙoƙarin zubewa gaban Yaa Sheikh ya gaida shi yaji Halisa ta faɗa jikinsa tare da ƙanƙame shi da kyau tana kuka kamar ranta zai fita. A tsorace El ya rungometa yana faɗin
"What happened Princess?" Domin ji yake da wani abu ya sameta gwara shi ya same shi, ita kaɗai suke jini ɗaya uwa ɗaya uba ɗaya, banda haka bashi da kowa sai na biyunta Yaa Sheikh. "Am sorry Hamma, kayi haƙuri ba zan sake maka harara dako in kula ba, kai kaɗai zakai mini soyayyar da babu gori cikinta kuma tabbatacciya kayi haƙuri"
Shi dariya ma ta bashi, Yaa Sheikh kuma ya kwashe karatun nata tas, bai kalli inda suke ba, idanunsa dai ya yi jajir ainun kamar wanda wutar kishi ke damunsa, El ya shiga ƙoƙarin zameta sbd cikin Jikinta tana kuka ta ce
"Please Hamma El ka tafi dani kaji, bana jin daɗi wallahi ai da ba zaka so ka rasa ni ba" yaja hancinta ya ce "Ba gaki ga Abba ba?" Ta maƙale kafaɗa, ya girgiza kai ya ce "Wlh daman Mom tace ba wani abin kirki a kiran ki, rigima ce"
Ya zameta yana durƙosawa gaban Yaa Sheikh ya ce "Good morning Abba" Ya jinjina masa kai alamar lafiya fuska kuma sake yana jin El-bashir ya zuciyarsa,sosai yake ƙaunar yaron. Ta ce
"Ka zauna mana"
Ya harareta ya ce "Ke gidanki ne, ni kuma wajan Abbana nazo" ya gyara zama daidai ƙafafuwan Yaa Sheikh ya ce "I'm starving aban breakfast" tayi wani irin murmushi ta ce "Laa Anty Zahrah ce zatai breakfast maybe ta gama" daidai lokacin Zahrah ta fito cikin kwalliya ta zuba lace Idanunta sun faɗa sunyi zuru-zuru. Ta nemi waje ta zauna tana ɗan yin murmushi tace "A'a baƙo mukai ne?" Idanun El akan plasma bai ce komai ba, Halisa ta ce
"Anty Zahrah kin gama breakfast ne?" Ta ɗan saci kallon Yaa Sheikh taga gabaɗaya basu yake kallo ba, ta ce
"Ban ba, bana jin daɗi"
Halisa ta jima tana kallonta kafin ta ɗauke kai tana faɗin "Allah ya sauwaƙa"kitchen ta nufa ta fara shirya abu mai sauƙi irin very liquid ɗin nan wanda ba zai ja lokaci ba, fried indomie tayi ta saka mata su carrots, onion, da sauran vegetables. Tana da garin kunun tsamiya ta dama kunun tsamiya, kana ta tafasa shayi da zuba ginger da barkono da na'a na'a. Kana ta soya ƙwai tasan ba lallai El ya sha kunun da tayi ba. Tana gamawa tayi wanka ta shirya cikin wata simple light blue ɗin abaya wacce ta fidda shaps ɗinta, ta fito sai ƙamshin turare take.
Yaa Sheikh ya kasa riƙe kansa ya dinga satar kallonta har ya ɗora idanunsa a kanta da kyau, wani kasala ya saukar masa musamman da suna haɗa idanu ta tura masa ƙaramin bakinta na tsiwa ya zame idanunsa yana girgiza kai a ransa yake sanya mata albarka.
Ta zauna so close to him tare da ɗora kanta a ƙafaɗar hannunta a gemunsa tana ja idanunta akan El-bashir ta ce "Prince the breakfast is ready" Ya miƙe ya ce "Ok Little Our Princess Abba's girl" ya nufi dining room ɗin dake main parlour, Halisa ta juya suka haɗa idanu da Yaa Sheikh taja gemun ta ce "Habibi ƙalbi let's go" ya riƙe hannun nata,ganin idanun Zahrah ya sanya ya saketa ya ce
"Part ɗina, cikin freezer Honey" ya yi maganar ba tare daya faɗi ainahin abinda yake so ba, ta fahimta sai ta miƙe ta ce
"Okey Yallaɓai"
Tana barin wajan Zahrah ta ce "Amma kasan kayi ba daidai ba" a taushashe ya ce "Da?"
"Daka riƙe hannunta bayan kasan ranata ce" ya ɗago ya kalleta da kyau, kamar zai shiru sai ya ce "aikin da ki ka kasa tayi,ke zaki breakfast baki ba, ita kuma tayi tazo inda nake ta gaishe ki, kefa? Ko ina kwana babu" Ta ɗauke kai ta ce "Amma ina da niyyar gaisheka" kafin ya yi magana Halisa ta ƙwalla masa kira ta ce "Ɗan babyna Abbana Yaa Sheikh banga zumar ba"
Ya miƙe tsaye tare da ajjiye wayar shi ya nufi upstairs, yana zuwa ya sameta durƙoshe gaban freezer yana zuwa ya saka ƙafa ya zungureta bata kallesa ba ta ce
"Ina take" a hankali ya ce
"Stand up" ta miƙe da ƙyar kafaɗarta ta sake tayi saurin shigewa jikinsa tana "Wayyo Abbana" ya riƙo ƙugunta tare da binta da kallo ya ce "Zaki iya haifar yara 20 anya?" Ta zare ido ta ce "Tab ai na gama daga wannan"
"Kidding" ya furta domin shi da gaske zuri'a yake son mai yawa tunda familynsa basu da yawa. Ta ce "Sakeni to" ya kalli ƙirjinta ya kalli bakinta ya ɗauketa ya ɗora saman freezer kafin tayi aune ya fara bata wani cikakken sumbata yana birkitata, yana shafa duk inda yaso baya son yi abin kunya inda yaji abu ya yi masa sai ya fara faɗin..
"Yasubuhanallah! Ya Allah Ma sha Allah" cikin ƙaramin lokaci ya ɗorata akan network duk tana cewa bata so suka hargitse juna, ƙarar da taji yasa tayi saurin dubawa ta zare idanu ganin ya kusa yaga mata gaban riga. Ta sakkowa da sauri yana shirin kamota tayi waje tana maida numfashi, a hanya sukaci karo da Zahrah da take da wayar Yaa Sheikh da ake kira, ta bita da kallo kishi ya mamaye zuciyarta fal!
Tana shiga ta samu Yaa Sheikh ya kifa kansa da jikin freezer ta ce "Ana kira" yana yin magana zai fallasa halin da yake ciki, ya miƙe tare da juya mata baya "Are you already?" Ta faɗa tana shirin dawowa gabansa ya yi saurin ɗaga Jallabiyar shi yana shigewa bathroom.... Misalin 5 na yamma motar Yaa Sheikh tayi parking a harabar gidan Abba Hakimi, ya fito yana gyara zaman babbar rigar jikinsa, Halisa ta buɗe ƙofa ta fito sanye cikin duguwar riga kamar kullum ta zumbula hijab, ga liƙab a fuska hadda safar hannu, tana fitowa ta ɗage liƙab ɗin tana haɗe fuska tare da tura baki ya yi murmushi mai sauti cikin kamala ya ce
"Yanzu ki ka amsa sunan Matar Malam" Tayi gaba sbd haushin hijabin take ji ga cikin daya fara takura ta, duk ta damu kanta ya kuma ƙara fuskarta ƙiba tayi wata ƙatuwa, ita ta fara shiga cikin gidan bakinta ɗauke da sallama, Abba Hakimi da shigowar shi kenan ya ce "A'a wa nake gani kamar matar?" Ta nemi waje kusa da shi ta zauna ta ce "Ni ce Jon wuro ina yini" ya dinga ya ce "Ma sha Allah,sannu kinji Allah ya bada lafiya" Umma A'isha ta ce
"A'a tashi daga nan kada ki danne mini miji, jibi yadda ki ka zama narkekiyya ni ƴar nan" Ta juya tana amsa sallamar Yaa Sheikh ya zauna saman kujera cikin tarin nutsuwar nan na shi ya gaida su. Umma A'isha ta ce "Me kake bata ne? Wannan ƙibar ai ta shige ta hankali" Halisa ta ce "Soyayya yake bani, ke kam matar nan mene damuwarki da ƙiba ta ne?" Abba Hakimi ya ce
"Kishi take baki da ita" Mother ta fito ita da Dr A'isha cikin farin ciki ta ce "Oyoyo ga Daughter ma sha Allah, aure ya karɓe ki" ta zauna Halisa ta gaida ita ta ce
"Mother wai baki koma gidan Father bane?" Kai tsaye ta ce "Eh, Aku"
Tayi murmushi kawai ta ce "Allah sarki Farther tausayi kuke bani ne" Dr A'isha tayi mmkin yadda Halisa taƙi ko kallonta balle ta gaisheta.
Abba Hakimi ya ce
"A'isha ta samu matsala da mijinta, harta dawo gida" Ya juya ya kalleta fuska haɗe ya ce
"Ɗauki tarkacanki ki koma" cewar Yaa Sheikh. Ta ɓata fuska amma sosai taji daɗin jin muryarsa ya buga mata wata gigitacciyar tsawa ya ce "Out immediately"
Ta fashe da kuka sosai tare da jan mayafi tayi waje. "Me ya sa?"
Yaa Sheikh ya kalli Abba Hakimi rai ɓace ya ce
"Shirme tayi, bayan ita ce bata haihuwa ya rufa mata asiri...
08119237616Duka suka bishi da kallo, Mother ta ce "Idan har haka Dr A'isha ta yaudari kanta" Abba Hakimi ya kasa magana, sbd a iya saninsu babu wata hujja data nuna cewa Dr A'isha ce bata haihuwa, a kullum mijinta take nunawa matsayin wanda ke kawo naƙasu kuma likitoci sun ƙara tabbatar da hakan. "Amma a ko wanne lokaci Likitoci sune suke bada tabbaci akan mijinta shi ne baya haihuwa, ya akai reshe ya juye zuwa mujiya?"
Umma A'isha ta ƙare tana kallon Yaa Sheikh da alama suna jiran su ji ta bakinsa ne kuma yaja baki ya rufe yaƙi cewa komai, suna da tabbacin kuma ba zai ce komai ɗin ba, na bayan ma daya furta ta kaishi ƙarshe ne.
Halisa ta kalli Mother ta ce "Ni dai wallahi yunwa na keji" sai a lokacin Yaa Sheikh ya ɗaga fararen idanunsa tare da kallonta, abincin da taci kafin su taho har mamaki yake, amma yanzu har tana neman wani?.
Mother ta ce "Shi yasa gaki nan kamar an zuba yis tubarkallah, me zaki ci" Halisa ta sakko ƙasan carpet tana miƙar da ƙafarta wacce ta kumbura, a nutse ba tare da kowa ya lura ba ya dinga kallon ƙafar dole akwai dalilin kumburin. Ta buɗe baki cikin takurawa irin ta masu juna biyu ta ce
"Kawai ni duk abinda kuke da shi a bani zanci"
Umma A'isha ta kada baki cikin zulaya ta ce
"Bafa Abbanki Yaa Sheikh ke bamu kuɗin cefane ba" kamar jira take ta bata martani da
"Mijina bashi da rowa, idan ku kai mini rowa na haifi ɗana haka zaku haɗu da shi"
"Da waye zamu haɗu?" Umma A'isha ta sake faɗa, domin Halisa jikar ta ce shi ya sa bata damuwa da sakin zan can nata. "Gwarzon mijina ba irin tsohu na kujera" Sai a lokacin Mother ta sake cewa
"Yanzu kuma kan Ubana kika dawo" Ta juya kan Yaa Sheikh ta ce
"Malam ka ɗauke matarka duk ta Ishemu" Yaa Sheikh ya ɗan faɗaɗa fuskarsa yana mai yin baya kaɗan ya ce
"Wajan Ummul zamu, taci a can" Mother ta riƙe baki ta ce "Kana son faɗa mana Ummul tafi kula maka da Matarka ko?" Ya miƙe tsaye yana shafa fuska zuwa gemunsa, Halisa ta kama jikin kujera ta miƙe tana faɗin "Ai wallahi tafi so na, shi ya sa nake son ɗanta kamar hauka I love you Abbana so much love" tuni ya yi waje ta zura hijabi tana cewa
"Kuma ba zan dawo ba sai na haihu" Umma A'isha ta kada baki ta ce
"Allah ya raba lafiya, mu ai haka muke so" Abba Hakimi da addu'ar fatan alheri da samun farin ciki na har abada ya bisu, Halisa macace tana son Abbanta bayan kallon miji da take masa, tana masa kallon komai nata shi ya sanya bata riƙe kanta akan soyayyar shi, tana da kaifin baki kamar reza tunaninta kullum kaifafa yak. Yaa Sheikh yana riƙe kansa sbd bai saba ba, kuma halinsa ne haka baya iya bayyana yadda yake ji sai dai ya nuna shi a aikace, jajir tacce ne, ya gode Allah da son da ya kewa Halisa bai rufe masa idanu ya kasa nuna mata kuskurenta a duk sanda tayi ba daidai ba.
Yaa Sheikh na fita ya tsaya jingine da jikin motar shi yana shaƙar iskar dake wajan, tafiya yake son yi mai muhimmanci amma baya son barin baya da ƙura, Halisa nada ciki tana tsananin buƙatarsa Zahrah na cikin damuwa da muradin jinsa a jikinta, ya kuma abinda ke faruwa babu wata cikakkiyar fahimta da fuskantar juna tsakanin matan nashi guda biyu! Laifin waye? Nasa? Ko Halisa da take ƙarama kuma uwar gida? Ko kuma Zahrah mai zuwan yanzu data kasance Amarya kuma gaba da Halisa a shekaru.
Horn ɗin mota ya dawo da shi cikin tunaninsa ya ware idanun yaci karo da motar Father dake shigowa cikin gidan lokacin kuma Halisa ta fito hannunta riƙe da jakar da Mother ta bata, Yaa Sheikh ya ɗauke idanu yana daidaita kansa da kyau tare da juyawa ya miƙawa Halisa hannu ta kama ya dawo da ita kusa da shi yana amsar liƙab ɗin hannunta zai saka mata ta ce
"Modibbo ka barni kamar zan faɗi nake ji" ya riƙeta da sosai ya ɗaura mata daidai kunnenta cikin lallashi ya ce
"Dole ki saba Zawja"
Mother ta ce "Kinga na manta na baki wannan....," Maganarta ya tsaya lokacin da sukai idanu biyu da