Showing 111001 words to 114000 words out of 197828 words

Chapter 38 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9351

sai na tsine masa" Zahrah tayi saurin cewa "Ina son Yaa Father kada ya barni" ya ce "kwantar da hankalin ki" Abba Hakimi ya ce "Ni kuma idan har Aliyu ya buɗe baki a yanzu ya ce yana son Halisa zai zauna da ita wlh Engineer kayi tsararo kasa ya saketa, ruwanka bai kai tsaiko ba" Ya juya kan Yaa Sheikh dake zaune ya kasa cewa komai ya ce "Nasan akwai yarjejeniya tsakaninmu, amma nasan ka riƙe amana tunda ance baka da lafiya, idan har ka faɗa mini yanzu a gaban kowa kana son Halisa a yanzu zan baka ita ka koma Madina ko ka nufi gidanka da ita, kana son Halisa kana son zama da ita matsayin mata da miji?" Waje ya yi shiru Yaa Sheikh ya kasa furta komai sai zufa dake yanko masa. Da gudu Umar-khan ya shigo ya ce. "Yaa Lee Halisa..." Mother ta Mike tana faɗin "Mai ya sameta?" Ina Yaa Sheikh tuni ya yi waje bai tsaya jiran jin komai ba, Umar-khan ya ce "El-bashir ya ya ɗauketa, yaja mota sunyi waje akwai matsala" suka ɗauki salati. Gabaɗaya sukai waje, suna fita harabar gidan motar Yaa Sheikh na fita daga gate. Cikin sa a ya hango motar El-bashir ya ƙara gudun tashi, ta cikin madubi El-bashir ya hango motar Yaa Sheikh ya yi murmushi yana sakin dariya, burinsa ko zai mutu ya kashe Halisa ya ɗauki fansar abin da Yaa Sheikh ya aikata masa shekarun baya. Ihu sosai Halisa take tana kiran sunan Dada da kuma Yaa Sheikh, da ganga El-bashir ya saki kan motar gabaɗaya ta nufi wajan wata ƙaruwar tirela sukai aran gama, motarsu Halisa ta kifa ta ƙara kifawa a hankali ta gangara ta tsakiyar titi ta daki wani ƙaton dutse....Kukan jaririn ya dakatar da Jadda daka shigewa cikin parlourn, ta tsaya cak hannu riƙe da zanin dake neman faɗuwa a jikinta ta ce.
"Yaushe A'isha ta samu ciki ni ƴar nan? Ciki tsofe-tsofe kamar a zamanin baya?" Mother ta kasa magana al'ajabi ya kamata, me zata gani haka? Cikin da aka ce cuta ce a cikinsa daga nishi sai suji kukan Jariri? Umma A'isha murmushi kawai tayi, kasancewar ta babba mace mai hangen nesa,
Ya sa kallo ɗaya da tayiwa Zahrah ta fahimci ciki gareta,
Tayi shiru ne sbd bata da ikon yin magana akan abin, babban dalilin yadda Engineer ya shaida akan idanun kowa ta ce
Yaa Sheikh bai da lafiya zama da mace, to ina cikin ya samu?
"Masifa da bala'i kowa ce ƴar banza taci kanta ina magana ko wacce tai kunnen uwar Shegu, nace yaushe ne A'isha ta yi ciki har aka haife shi yanzu? Kuma banda asara duk faɗin gidan nan sai a parlour zata baje mazaunai ta haihu?"
Daga Umma A'isha har Mother suka kasa cewa komai, bakinsu ya kulle ganin Zahrah na neman danne jaririn ya sa Umma A'isha faɗin.
"Maryama zare babyn ki yanke cibiyar" Mother ta ce "To!" A sanyaye jiki ba ƙwari. Sai a lokacin ne kuma Jadda idaniyyar ya sauka akan Zahrah ta hangame baki, idanunta ta buɗe domin ƙara tabbatarwa da gaske Zahrah ce dai ta haihu, ta miƙe tsaye tana yin mitsi mitsi da idanu kafin ta ce
"Me zan gani ɗan shege cikin gidan Hakimi, la'ilaha illallah Muhammadur Rasulullah s.a.w rabon dana ɗan shege ido da ido tun ina budurwa da tsautsayi ya rutsa da ƙawata, to wallahi ba a gidan nan ba, daman tun kallon farko nasan idanun yarinyar nan a tsakar ka yake, faɗa ne kawai ban ba, taje can ta buɗewa gantalallun masa mazauna sun sha bidiri da bushasha, sunyi hajji da umara akan shi, bawai ashe da karuwa muke zaune, ashe shararriyar ƴar hannu aka aurawa Malam to Allah ya isa" Umma A'isha ta ce.
"Kiyi haƙuri mubi komai a sannu, babu tabbacin abin da Zahrah ta haifa bashi da uba, auren Aliyu take ba kuma a gidan shi take zaune.
"A'a kada ki fara kada ki sake, wlh rufe idanu zan naci biki mutunci muddin zaki goyi bayan iskanci ga zahiri, gabaɗaya wata nawa da bikin? Bai fi wata huɗu bane ina ji fa? Ko bakwaini bai isa a haife shi yanzu, balle ga Muryar jaririn nan yadda yake inya ko ni ba zan iya buɗe maƙogaro nayi haka ba" Umma A'isha ta jinjina kai, itama ta yarda da batun Jadda amma baza su yanke shawarar hakan ba, dole a bincika.
"Bari Hakimi yazo, sai anyi maganar komai a nutse" Jadda dai sai kaɗa ƙafa take tayi ƙwafa tare da zabga Salati ta ce.
"Ɗan shege ne wallahi"
Mother ta duba Zahrah taga bata buɗe ba ta ce "Da sauƙi bata samu ƙari ba" caraf Jadda ta ce "Ina zatai ƙari abin da ya zama kamar rariyya? Tun tuni ƴan iskar suka mayar dashi ƙofar waika" kunya ta kama Umma A'isha amma ta kasa cewa komai. Zahrah Tunda ta samu kan ta haihu taji kamar an zare mata gabaɗaya ciwon dake damunta, ta rufe idanu ta kasa motsin kirki bata taɓa jin kunya a duniya irin yau ba.
_“What should I do?”_
Ta tambayi zuciyarta abin ya zo lokacin da sam ba tayi tsammani ba, Umma A'isha ta naɗa kyakkyawan jariri fari tas dashi cikin showel, Mother ta goge wajan tas ta zuba turare ta kunna boner tare da air-con. Da taimakon Mother Zahrah ta miƙe suka nufi bedroom ɗin da take ciki, ta haɗa mata ruwa mai zafi sosai duk abin da mai jego ke buƙata akai mata.
Bayan mother ta fito daga ɗakin Zahrah ta nufi nata bedroom ɗin direct number Abba Hakimi ta kira, ta jima tana ringing kafin a yi picking call ɗin cikin kamala ya ɗaga yana faɗin.
"Maryama ya akai ne?" Ta sauke numfashi kaifi ta ce "Abba ya jikin daughter dana El?" Ya juya ya kalli Halisa wacce har lokacin bata farka ba hannunta riƙe dana Yaa Sheikh da tun ɗazo yake ɗakin yaƙi cewa kowa komai akan maganar daya furta ɗazo.
"Allhamdulillah, fatan lafiya?" Ta ce "Abba akwai matsala nan gida, idan babu damuwa abar Umar-khan wajan El-bashir, ku taho yanzu har Malam ɗin"
Ya yi jim! Na wani lokaci kafin ya furta
"Allah ya a jisshemu alheri, gamu nan" ta ce "Amin, Ishaq ya ƙara sa boutique ya siyo mana baby set na kaya, da oil, Pampers, everything na baby dress kuma baby boy" "meke faruwa Maryam?" Mother ta ce.
"Abba ka bari ka ƙarasu, idan ka gani za kafi yarda, yanzu ba lallai ka yarda ba" ya ce "To ba shakka,gamu nan" har zai kashe wayar ta ce.
"Abba" "what again Barrister?" Ta ce.
"Muna buƙatar Engineer a wajan Please" Abba Hakimi ya yi shiru kafin ya ce "Bana son fitina a Maryam" ta ɗan marairaccen masa tunda kamar uba yake a wajanta ta ce
"Ka yarda dani, just trust me" bai ƙara magana ba ya kashe wayar. Abba Hakimi ya juya ya kalli Yaa Sheikh kafin ya ce.
"Ta shi muje, zuwa anjima ka dawo ko?" Ya ɗaga kan shi ya kalli Abban nashi sai kuma ya jinjina kai ba tare da ya ce komai ba, Abba Hakimi ya fita. A sanyaye cikin nutsuwa yana jin komai na jikinsa na sauyawa ya ƙara damƙe hannun Halisa hannunsa ɗaya dafe a goshinta wanda tunde ya zauna yake mata addu'a yana tofa mata..
Ya ɗora fuskarsa akan nata His breath fell gently on her face,Not everyone understands the situation he is in, the only one who understands is lying in a hospital bed. Idan labɓansa sun kasa furta abin da zuciyarsa ke son bayyanawa, yana da yaƙinin ita zata gane, kuma zata fahimtar da Abba Hakimi, a lokuta da dama yana yunƙurin furta wannan kalmar mai daraja a gare ta sai ya samu kan shi cikin sarƙewar harshe.
Ya goga mata tattausan gemunsa a fuskarta yana jin yadda ta sauke ajjiyar zuciya ya kalli bakinta gabaɗaya lips ɗinta sun bushe, gently kamar mai tsoro ya ɗora bakinsa akan nata ya shiga kissing nata, can ƙasar zuciyar shi addu'a yake karantawa ya tara yawu fal bakinsa na addu'ar ya juyewa mata cikin nata bakin. Ƙut! Sautin shigewar yawun ya bayar a hankali ya sumbaci goshinta kana ya ɗora bakinsa daidai wuyanta ya jima yana kissing fatar wuyan da dukkan zuciyar shi..
"Wow, I've been looking for someone who can kiss like that for a long time, irin wannan sai malamai" Khalil Ahmad Sarki ya faɗa yana ƙarasa shigowa cikin room ɗin.
Yaa Sheikh ya zame fuska yana haɗe rai sosai lot looking at his direction. Khalil ya yi dry sosai yana buga cinya kafin ya ce.
"Stop pretendinglike you didn't do anything, take your time. And enjoy, tuzuru kamar Malam Aliyu ya samu ɗanyar yarinya ƴar Fulani sai abin da muka gani"
Yaa Sheikh yaƙi cewa komai da sauri kuma ya rufe tafin ƙafar Halisa da bargon asibitin, a tsari nashi babu abin da za a gani a jikin iyalinsa sai fuska itama dan ta zama dole ne.
"Da alama an yiwa zuciyar Malam mugun kamo, naga alamar ya kusa zama jani talau" sai a lokacin Yaa Sheikh ya ware gajiyayyun Idanunsa akan Khalil ya ce. "Kamar amaryar a lalle?" Khalil ya saka dry ya ce "Ai ba kamo na aure ba, kamo na zuciyar data kamo da soyayyar wani, _Love of the opposite sex_"
"To akwai wanda na taɓa cewa ban so?" Khalil ya ce "Eh, babban misali ƴar fillon nan kace baka sonta, ƴar ce wajanka, auren dole ne fa ko ka manta" Yaa Sheikh ya kame fuska yana yin gaba ya ce "True love, between heart to heart, ka daina munafurci Khalil Ahmad Sarki, Ubangiji ya yi hani da shi"
"Ba batun munafurci, nafa ɗauka zanga ka rame ka fita hayyacinka, kasan auren dole masifa ne" Yaa Sheikh ya tsaya cak tare da juyawa suka kalli juna sai kwarjinin Yaa Sheikh ya cika idanun Khalil, kusan age mate ne tsakanin Yaa Sheikh da Khalil shi ya sa yake yawan jan Yaa Sheikh da hira,wani lokacin ya biye masa wani lokacin ya share. Ga mamakin Khalil sai yaji Yaa Sheikh ya ce.
"Wanne kalar so ka kewa Oum Juwairah? yaushe kuka haɗu" Khalil was silent trying to remember the time, day, month, and year. "I can't remembering, but a school muka haɗu, time ɗin shekarunta 20"
Al'ajabin ganin murmushi mai laushin cike da kamala a fuskar Yaa Sheikh ya kusa zautar da Khalil ya ce.
"What make you laugh?"
Suna tafiya a jere sun jima kafin Yaa Sheikh ya ce. "Shirmen Khalil, ka kwatanta da yarinya da akan idanunka aka raini cikinta, ka raɗa mata suna, ka goyata a bayanka, ka raineta da hannayenka, ka kalli Kyakkyawa fuskarta ta yarinta ka ce _IDAN BA KE_ ba zan iya rayuwa ba, ya zaka kwatanta da Oum Juwairah?"
Khalil ya ce "Tab, to ai ba zan iya haɗa son ta dana ko wacce ƴa mace ba, zan ce mata IDAN BA KE ba zan ƙara aure ba"
Yaa Sheikh ya girgiza kai ya ce "Ka ɗauka idan ba ita babu rayuwar wanda ya reneta ne, ba komai ake bayyanawa ba, wani abun sai dai gangar jiki tayi aiki" Khalil ya saki baki domin ya gama ƙaddara wa ba Yaa Sheikh ne gabansa ba, yafi masa kama da Yaa Lee. Har suka ƙarasa harabar asibitin Khalil ya kasa cewa komai.
Suna zuwa suka shiga mota, daman zuwan Khalil ƙasar kenan, Abba Hakimi da Mai martaba a mota ɗaya, Umar-khan ya jasu domin El-bashir yana barci.
Ɗaya motar kuma ta Yaa Sheikh Khalil ya shiga masanin driver Yaa Sheikh bai fiya driving ba sai dole, motar da Khalil ya shigo da ita asibitin kuma tun ɗazo Ishaq-Hakim ya tafi kai saƙon mother.
Kasancewar Khalil baya driving a hankali duk da faɗan Yaa Sheikh amma sai da ya riga su Umar-khan zuwa, cikin sa a yana sauka motar su drivern su Maimoon na sauka. "Am lucky wallahi da rabon zanga amaryar dake wahalar da zuciyata" Yaa Sheikh ya taɓe fuska ya jima da sanin Khalil na son Maimoon amma taƙi bashi dama.
Suka fito kai tsaye Yaa Sheikh ya yi cikin gida suka jera da Abba Hakimi da Mai martaba suka zama kamar wasu abokai ko sa'anni. Naomi tunda ta hango Khalil ta haɗe fuska ya ƙarasa yana cewa. "Autar Mother an girma" Auta Umar-khan ta ce "Ina yini Uncle K" ya ce "Lafiya" Zeefa ma ta gaida shi ya ce "Maza ku shiga anjima samu shopping amma banda mara gaida mutane" Maimoon ta ƙare haɗe fuska ta ce
"Ina yini Uncle?" Ya haɗe fuska ya ce.
"Yana kwano, ni ki ke bawa wahala ko Moon?" Ta tura baki ta ce "Me nayi kuma?" Ba wasa a fuskarsa ya jingina da jikin mota yana harɗe hannu ya ce.
"Saboda ina son ki? Shikenan na haƙura kije ki auri wanda ki ke so, nima zan nemi wata, be happy" maimakon tai farin ciki sai yaga ta sunkuyar da kanta ƙasa hawaye na zuba a idanunta. Ya saka hannu ya tallafo haɓarta ya ce.
"Meye kuma? Na ɗauka farin ciki zaki yi?" Ta fashe da kuka ta kasa cewa komai.
Ganin ba mutane a wajan ya miƙa mata hannu ya ce "Zonan" kanta a ƙasa ta ƙarasa wajan shi sai kuka take kamar yarinyar, ya riƙe hannunta ya ce.
"Ya akai? Meye na kuka Prince guda kince baki son shi ba dole na haƙura ba" ita dai Maimoon kuka kawai take ya riƙe hannun ya ce. "Ok tell me, do you love me? Do you want to marry me?" Ta kasa cewa komai ta yi saurin shigewa jikin shi tana kuka, ya saki dariya yana rungometa ya ce "Oh! Ina ganin halin kwailaye ni Ibrahimul-khalil"
Shiru parlourn ya ɗauka, Abba Hakimi, Mai martaba, Father wato Engineer Aliyu, Uncle Haroon, Uncle Bashir, sai Oga Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu!
Ɓangaren mata kuma, Mother, Umma A'isha, Zahrah, sai Yaya Halima, tare da Jadda wacce ta kafa ɗauri a gaban goshi kaɗan take jira.
Aka kasa samun maiwa su Abba Hakimi bayani Jadda ta miƙe ta nufi bedroom ɗin Zahrah baby boy ɗin na barci cikin kwanciyar hankali ta figaloshi tana Asstagafirullah! Na taɓa ɗan shege da tayi.
Tana zuwa ta ɗora jaririn a kan cinyar Zahrah ta ce
"Ubangiji kawai nake tsoro ba wani shege, a yau idan Malam bai saki Zura take kowa wallahi ban cika ƴar banza ba, kuma duk abin da aka kashe na aurenki sai an biya, tunda cakawa Malam akai, ashe dauɗa aka bashi raguwar masu gajeren wando" ta girgiza kai ta ce.
"Na rantse da zatin Ubangiji nafi shekaru arba'in rabon da naga ɗan shege sai yau a gidan Hakimi" Abba Hakimi ya kalli Umma A'isha ya ce.
"Meke faruwa Aishatul-humaira?" Umma A'isha ta sauke numfashi ta ce.
"Matar Yaa Sheikh ce ta haihu ɗazo, yaro namiji" Da sauri Father ya kalli Zahrah wacce take kuka sosai. Yaa Sheikh ya yi ƙasa da kan shi, Abba Hakimi ya yi ta jinjina kai. Uncle Haroon ya ce.
"Ikon Allah, haihuwa kuma bakwaini kenan?" Jadda ta ce "Wanne bakwaini? Shekararran ɗa a ciki, kalli fuskar yaron da kyau, da ƙyar bai gado iskanci a ciki ba" "This is complicated, Sheikh kasan da cikin ne?" Yaa Sheikh ya yi shiru can ya ce.
"Ku tambaye ta" Uncle Haroon ya ce "I'll do the same thing har sai ka ban amsa, kasan da cikin Zahrah" Yaa Sheikh ya ce. "Eh" gabaɗaya suka kalli Yaa Sheikh Father ya ɗaga hannu zai ɗauke Yaa Sheikh da mari daga bakin ƙofa aka ce.
"Kada ka kuskura hannunka ya sauka akan ɗana Engineer Aliyu" suka kalli bakin ƙofar zumbur Mother ta miƙe tsaye tana nuna matar da hannun ƙirjinta na ɗagawa kamar zata shiɗe ta ce
"Ummul-khairy!" Ummul tai murmushi hannunta riƙe da key ɗin mota, Abba Hakimi ya kalli Ummul da kyau kaifi ya ce. "Ɗanki kuma?" Ta ƙarasa shigowa ta nemi waje ta zauna ta ce.
"Na katse muku hanzari ko? Ku gama sai muyi magana daka baya" Father ya ce.
"Ni da ɗan dana haifa a cikina za kice ɗan ki?" Ummul ta girgiza kai kawai ta juya kan Zahrah ta ce.
"Kin tuna magana ta? The day you slapped me, you insulted Aliyu's grandfather, nace zan nuna miki ikona a lokacin da ki ka san wacece ni, In sha idan harni na haifi Arɗo a yau zan baki divorce paper ya zauna da zaɓin zuciyar shi" Father ya miƙe cikin faɗa da ɗaga murya ya ce.
"Ke awa? Ni nake da ikon saka Aliyu ya yi abin da nake so bake ba, ɗana ne mallakina ne" Ummul ta juya ta kalli Mother ta ce
"Barrister Maryam me ya sa kika ɓoyewa mijinki, while I doesn't f****** care" ta juya kan Father ta ce "Tunaninka me? Biyayya Yaa Sheikh ya yi maka, baka san cewa kafin ya amince sai daya samu yarda ta ba? Na maka uzuri"
Abba Hakimi ya gaji da jin duk wannan maganganun ya ce.
"Zahrah ɗan waye a hannunki" cikin kuka ta ce "Yaa Sheikh" Jadda ta miƙe tare da dungure kan Zahrah ta ce.
"Annamimiyya to Allah ya isan malam Alkur'an"
"Aliyu? Kin tabbatar ɗan Aliyu ne?" Ta jinjina kai ya ce "Ya akai kuma kika san Aliyu bai da lafiya? Kuma yakai ɗan ya zama na Aliyu bayan mu'amala bata taɓa haɗa ku ba" ta fashe da kuka sosai ta ce. "Don Allah Abba kayi mini alfarma idan na faɗa maka gaskiya ba zaka bar Yaa Sheikh ya sakeni ba, don Allah Abba wallahi zan iya mutuwa idan babu Aliyu nayi ladama" ya jinjina kai ya ce "Inaji" ta share idanuna ta ce.
"Ba ɗan shi bane, lokacin da mukai aure ina da cikin wata huɗu" Jadda ta hangame baki ta kasa cewa komai. Ta ɗora da faɗin. "Nayi ƙoƙarin ganin na samu mu'amala da Yaa Sheikh domin na ɗora alhakin cikin akan shi amma ya rusa duk wata ƙofa, har maganin sha'awa na zuba masa wanda na tabbatar ba zai iya jurewa ba sai ya keɓe da mace,amma bai kulani ba, Ummul ke sanar dani ai bashi da cikakkiyar lafiyar ɗa namiji sai na faɗawa Father" ta rushe da kuka sosai ta ce.
"Don Allah Ummul kada ki rabani da mijina don Allah Kiyi haƙuri" Ummul murmushi kawai take. Father kunya ta mamaye shi, ya kasa haɗa idanu da kowa tashin hankalin shi bai shige yadda Ummul ke iƙirarin Yaa Sheikh ba ɗan shi bane.
Abba Hakimi ya sauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login