Showing 48001 words to 51000 words out of 197828 words

Chapter 17 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9286

"No Zahrah Aliyu mijinki ne, ki koyi zama da shi kafin ki fara juya rayuwar shi tamkar waina a tanda, dole ragamar rayuwar shi ta dawo tafin hannunki" wata zuciyar ta shiga gargaɗin haka, jikinta ta kalla tsaf duk da kasancewar ciki ne jikinta amma ƙirjinta yana kwance ya manne da fata, ita kalar halittar ce ko kuma garin yawan ta zubar aka gama lalata halittar da Ubangiji ya yi mata wacce kuma iskancin kawai ta sani sam bata san tsaunin da zata hau tabi ba, zuwa tubalin da zai gyara mata garkuwar jikinta.
Ta tura ƙofar a hankali ƙamshin air-con da wani air freshener sune suka daki hancinta, shigar ta parlourn ya yi daidai da sautin karatun Yaa Sheikh dake ratsa cikin wajan har ya kawowa kunnenta farmaki.
Yana zaune saman kujera ya ɗora farar ƙafarsa akan table idanunsa rufe a haka yake motsa bakinsa yana karatun cikin baiwar da Ubangiji ya bashi ya sahale masa yin karatun ba tare da harɗewar harshe ba..
Zahrah ta bi farar Jallabiyar dake jikinsa da kyau da kyau, zuwa kansa dake rufe hirami hannunsa guda ɗaya riƙe da carbi yana ja.
Ta nemi wajan a kujerar dake kusa da shi ta zauna tana fari da idanu tare da juya jiki amma ta kasa yi masa magana balle gaisuwa.
A jikinsa yaji ana kallon shi bambancin ƙamshin turaren da bai taɓa ji a gidan yasa ya fahimci ko waye ba ɗan gidan bane.
Zahrah ta gyara murya ta ce. "My Excellency"
"Shhhh" Yaa Sheikh ya furta a ran shi gaba ɗaya murya ko a maza bai taɓa jin mai amonta ba.
Ganin ya yi shiru ta ɗauka ko bai ji mai tace bane?.
"Daman nace bari nazo muga juna muyi hirar ku mintuna biyar ne kafin mu tafi gidanmu" still shiru ya yi mata, ta miƙe tsaye cike da kwarkwasa ta ƙarasa har zuwa inda yake tare da zama kan armchair ta saka hannu ta shafi fuskar shi kaɗan zuwa dugun gemun shi ta ce.
"You're just quiet, but I know you hear what I'm saying" a wannan lokacin Yaa Sheikh ya ɗauka gangar jikinsa zata ƙaryata zuciyarsa, amma sai yaga abin ya zama diro, ya ƙara tabbatarwa lallai to da gaske bashi da cikakkiyar lafiya irin ta cikakkun maza, mace ƴar 32 tazo har inda take suyi very close da juna amma ko tsigar jikin shi bai ji ta motsa ba, balle ya yi zaton zai ji abin da Khalil ke masa surutu akai.
Zahrah ta kai hannu zata ƙara jan gemun shi ya buɗe narkakkun idanunsa na mai kama da mai jin barci. He didn't give her a full look, because looking at people is not his style. Bai sake kallonta ba ya miƙe tsaye yana goya hannunsa a baya, ya nufi bedroom ɗinsa, Zahrah ta ce "Amma dai ni matarka ce ka sani?" Ya tsaya cak ba tare daya juya zuwa gare ta ba, kamar zai magana sai kuma ya fasa ya shige cikin bedroom ɗin, Zahrah tabi bayan shi da kallo me hakan yake nufi? Ta ɗauka zuwanta gare shi zai nuna wata buƙuwa ta miji ga matar shi sai kuma taga saɓanin haka.
Ta juya ta sauri Dr A'isha dake Main parlour tabi Zahrah da kallo wato halitta kala-kala ce, ita bayan shekaru da zubin halittar jikinta har wani tumbi take dashi kamar namiji?. A fili Dr A'isha ta ce "Allah ya kyauta" tana faɗin hakan ta miƙe zuwa bedroom ɗin Mother itama a yau take son shigewa gidan mijinta.
Zahrah na shiga bedroom ɗinta ta saka ƙafa ta murje yatsun Halisa cikin faɗa ta ce "ke kam wacce jakar yarinya ce? kina ganin mutum ba zaki matsa daga hanya ba?" Halisa da idanunta yayi jaa sbd zafin da yatsun suke mata, ta kalli Zahrah ta ce "Kiyi haƙuri" ta saka hannu ta ɗauke Halisa da mari ta ce "haƙurin uwarki? Ni dai na shiga ban ɗauka fulani mahaukatan gaske bane sai yanzu" gigicewar da Halisa tayi yasa ko gabanta bata iya gani, ba a taɓa yi mata mari da tafkeken hannu kamar na maza irin wannan ba. Ruɗewar da tayi yasa ta nufi wata ƙofa a tunaninta part ɗin su Maimoon ne, tana fita taci karo da mutum a hanyar zuwa swimming pool. El-bashir yaja baya da sauri yana kallon farar kyakkyawar yarinyar data fito hannunta a fuska tana shassheƙar kuka, ya taɓe baki yana ƙoƙarin shigewa Halisa tayi saurin kama hannunsa cikin matsanancin kuka ta ce. "Hamma fuskata zata cire wayyo Dadata fuskata ka taimaka mini" sai murza fuskar take da hannunta guda ɗaya, ɗaya kuma ta riƙe hannun El-bashir da shi. Hannunsa ya sanya zuwa hannunta dake fuskarta cikin ƙasa da murya ya ce "Sorry" ya faɗi hakan yana ɗauke hannunta.
Cikin daƙiƙo ya nemi ji da ganinsa ya rasa, tunaninsa ya tsaya cak, ya zama kamar wani stateu yana ganin tarin kamanni amma bai taɓa cin karo da zallar kama irin ta yau ba. Hannunsa na rawa ya kama fuskar Halisa da kyau yana ƙare wa hukuncin Rabbil izzati ido, ita dai kuka take sosai ba ƙaramin gigita marin ya yi ba. El-bashir ya sauke numfashi yana daidaita nutsuwarsa tare da haɗiye mamakinsa, ko ita ce yarinyar da Khalil ke bashi labari?.
Ya shiga goge mata hawayen fuska tare da faɗin "ke dawa? Wace ke? Mene sunanki?" Ya jera mata tambayoyin.
Halisa ta marairaice fuska tare da shagwaɓewa ta zama wata narkakkiyya hannunta cikin baki alamar shagwaɓarta a zahirance take bata ɓoyewa. "Uhm magana nake" tai saurin ɗaga kanta zuwa fuskar shi, baki da hanci ta saka ta kasa cewa komai El-bashir ya ƙifta mata idanu tare da ware su ya ce "Keee.
"Wallahi kama muke, kai ma kasanni ya naga fuskarmu iya ɗaya?" Ta ƙare maganar tana ƙoƙarin taɓa fuskar shi domin tabbatarwa. El-bashir ya haɗe fuska ya ce "Bani amsa? Wace ke?" Ta tura baki gaba ta ce "Sunana Halisa Danejo Rome, kuma ni matar Balarabe ce" El-bashir ya ware idanu ya ce "What are you married? Waye Balarabe?" Ta ce "Ace kada na faɗawa kowa sai lokaci ya yi amma dai ni zan dinga yiwa Matar Yaa Sheikh aiki, kuma ance jibi zamu tafi ko'ina ne, haka.....,"
"Heyyy will you shut up your mouth caaaaa haba" ta tura baki gaba fuska duk a shagwaɓe taƙi cewa komai. Ya gyara tsaiwa ya ce "Oh Halisa, dake Yaa Sheikh zai tafi ko?" Tayi saurin kallon shi ta ce "Eh" ya ce "Ok good, daman shi ya aike ni yanzu, kuma ke ya ce na bawa aikin domin ya yarda da hankalinki" tamkar wacce bata yarda da maganar El-bashir ba haka take kallon shi, wanne aike? daman yana sane da ita kenan yana son ta shi ma?..
"Riƙe wannan, ya ce ki ɓoye wajanki har sai kunje Madina, maganin shi ne, zaki zuba masa a cikin shayi ko abinci, kada ki bar kowa yasan da abin a wajanki, idan ba haka ba zai kureki daga gidan shi kinji?" Ta ɗaga kai ta ce "Amma bari na bawa Mother ajjiya ko?" Ta faɗa zata juya ya yi saurin riƙe hannunta ya ce..
"Ai har Mother ba a so tasan da maganin a wajanki, ki zama mace mai sirri ki tabbatar kin zuba masa, idan ba haka mutuwa zai gaba ɗaya" ta shiga girgiza kai tsoro da fargabar abin da El-bashir ɗin ke faɗa suka firgitar da Halisa ta ce "Wallahi ba zai mutu ba, ba zan barshi ya mutu ba, ni da kai na zan zuba masa maganin" wani irin kyakkyawan murmushi mara sauti El-bashir ya yi kafin ya ce "Good girl" ganin ya yi gaba ta ce.
"Kai ya sunanka to?" "Ki ce El" ya faɗa a taƙaice tayi saurin faɗi "Ban iya faɗa ba, tunda muna kama ɗaya zan dinga cewa Hamma ka yarda?" Ya tsaya tare da juyawa wani abu nayi masa yawo akan abubuwa da yawa, kalmar kamannin data faɗa suka ƙara dagula masa lissafi. Ya jinjina mata kai tare sakar mata murmushi.
Halisa bata da riƙo lokaci guda ta mance marin da Zahrah tayi mata.
Cikin sauri ta ɓoye maganin da El-bashir ya bata tare da juyawa tabar wajan.
Barinta wajan ya sanya Yaa Sheikh sauke numfashi tare da zame idanun shi daga saitin wajan da Halisa da El-bashir suka tsaya, yana mai ɗan girgiza kai tare da ya motsa fuska.
Father ya kalli Yaa Sheikh ya ce "Kaje ka duba visa ɗin Zahrah da Yarinyar da zatai mata aikin" Yaa Sheikh ya jinjina kai alamar "to" tare da miƙewa sai da ya je bakin ƙofa Father ya ce "Ka shiga part ɗin nata, da kanka ba aike ba kace ta shirya kuje tare, matarka ce saɓa mata tamkar zaɓa mini ne, kai ne mai auren amma ni ne mai zartar da hukunci ko da wasa ka sake Zahrah ta kawo ƙararka za kaga yarda za mu yi dakai Aliyu, kaji tsoran Allah kai Malami ne kasan hakƙin aure da sauke nauyin miji ga mata, kada ka yarda saboda baka son ta kace zaka tauye hakƙinta wallahi wallahi Allah Aliyu akan aurenka da Zahrah sai nayi maka baki" Yaa Sheikh ya juya da sauri ya kalli Father kalmar shi ta ƙarshe ta daki zuciyar Yaa Sheikh, kansa a ƙasa ya nufi wajan Father yana zuwa ya zube a wajan ƙafafuwan Father, cikin ƙasa da murya mai tarin nutsuwa da Ilham yana mai ɓoye abin da yake ransa a kame ya ce.
"Kada ka aibata ni Abbi, zan riƙeta, ka saka albarka a kai na a karo na farko na rayuwata Father" Father ya kalli Yaa Sheikh kafin ya ce "Kaje Allah ya yi maka Albarka" Yaa Sheikh ya kifa kansa a ƙafar Father farin ciki ko baƙin ciki zai ji? Yau Father ya saka masa albarka dalilin Zahrah?.
"Ka tashi kaje nace, kuɗi ne kama fini shi me zan maka? Ko akwai abin da ka ke buƙata?" Yaa Sheikh ya yi shiru can kuma ya miƙe tsaye tare da yin waje. A hankali ya haɗu da Maimoon da Halisa shi sam ba zai ce yaga Halisa ba domin direct idanunsa ya sauka akan Maimoon ɗin.
Part ɗin Zahrah ya nufa lokaci wata farar riga ce a jikinta iya gwiwa waya riƙe a hannunta ta ce "No Deen ka bari muyi 1week a Madina sai ka zo ɗin? I will arrange a day when we can meet, I don't want to be recognized....," Ƙamshin Roja da hancinta ya shaƙa yasa tayi saurin ajjiye wayar tana duban door way, idanunta ya sauka akan Yaa Sheikh dake tsaye bakin ƙofar yaƙi shigowa ciki. Zahrah duk ga ruɗe bata tsammaci ganin shi a yanzu ba, ta sakko tana yin murmushi tare da girgiza jiki ta ƙarasu tana faɗin "My Excellency" Yaa Sheikh ya duba ta da kyau, har zai larabci ya tuna ba lallai tana ji ba, shi kuma he's not interested akan english.
"Ki saman waje, mota" ya faɗa a taƙaice cikin rarrabe murya.
Bai aune ba yaji Zahrah ta shige jikinsa tare da rungome shi. Bakinsa na rawa cikin rashin ya ce "Asstagafirullah, Allah na tuba" ya faɗa yana zame jikinsa tare da barin part ɗin da sauri.
Yana zaune a bayan mota idanun shi rufe yana ta Asstagafirullah akan rungumar da zara tai masa, ba wani sauyi a jikinsa amma that is forbidden.
Umar-khan ya ɓoyewa Zahrah bayan mota har zata shiga sai kuma ta tsaya ganin kamar maca ce a gaban motar, ta tsaya tana faɗin "Umar-khan wace wannan a gaban motar mijina?" Umar-khan ya kalli Halisa wacce take sanye da wata Marron ɗin turkish Abaya wacce Mother ta bata, Maimoon kuma tai mata rolling vail ɗin abaya a fuskarta, ƙaramar round face ta fito sosai farinta ya ƙara bayyana, gashin idanun nan lub zara-zara dasu idan ba magana tai ba, ba zaka taɓa cewa ƴat fillon Rugar Rome bace, ta kame kanta sosai bisa gargaɗin Mother. Umar-khan ya danne dariyar dake cin sa ya ce "Motar mijinku dai" "me kace?" Cewar Zahrah ya ce "cewa nayi baki gane wace ba?" Ta girgiza ta ce "Idan na gane wace mene amfanin tambayar?" Yaa Sheikh dai duk abin da suke cewa yana jinsu bai magana ba. Umar-khan ya ce "Ikon Allah, Ƴar fillo ce fa? Mai aikinki ina nufin Halisa ce a gaban motar garkuwarta" wani irin bugawa ƙirjin Zahrah tayi ta ƙara leƙa motar Halisa ta sakar mata wani cute smile ta ce "Laa Anti ni ce fa, mai aikin ki Halisa Danejo Rome" wani jiri ya ɗebi Zahrah tayi saurin riƙe motar a cikin ranta ta ce "Da sake wallahi ba zai yiwu ba....


_IDAN BA KE it's paid book... ₦500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616. If you read for free😂🤷🏾‍♀️_Umar-khan ya katse mata tunani da faɗin "Ki shiga muje" Zahrah ta ɗan basar tare da faɗin "Dake ban kula da kyau bane, amma ita me za ta je yi?" Ta tambaya idanunta akan Halisa wacce wayar Umar-khan ke hannunta sai latsa ko'ina take ba tare data san ta kanta ba. Umar-khan ya ce "Ayya ko kin manta Glasses ɗin naki ne, ita za ai mata visa ne" baƙin cikin maganar da umar-khan ya yarfa mata ya sanya ta kasa cewa komai ta shiga cikin motar tana sauke numfashi sbd ƙamshin Roja data shaƙa ga daddaɗan freshener dake tashi a motar.
Tana shiga Umar-khan shi ma ya shiga a hankali ya yi wa motar key sbd Yaa Sheikh baya son gudu da yawa, gatekeeper ya buɗe gate suka nufi wajan da za ai photo a haɗa musu visa. Bayan sun yi nisa akan titi Umar-khan ya juya ya kalli Halisa ya ce "Madam idan kika latata mini waya mijinki zai biya" Zahrah ta ɗago kai tare da duban saitin Umar-khan, bata fahimcin zancen ba domin ita ta ɗauka waya yake. Halisa ta buɗe fararen daidaiton haƙoranta masu kyau ta ce "To ai baya da kuɗi"
"Injiwa?" Umar-khan ya tambaya idanunsa akan titi, ta ɗan turo baki tare da watsa hannu alamar bata sani ba, ya girgiza kai ya ce "Shi ke da kuɗi, hakan ne ma ya sa ban ƙwace wayata ba, albarkacin ki sai a siya mini iphone 13max pro Matar Malam na makka da madina" taja lulu eye's ɗinta lumshe wanda hakan ya zama jiki a gareta, magana zarar bunu cikin rashin sani da kuma sabo da surutu yasa Halisa faɗin.
"Kai ma kasan ayi mini aure ne? Ko na faɗa maka yanzu" Umar-khan ya tuntsire da dariya sosai yana faɗin "Ina zan sani ƴar fillo? Kuma......,"


Yaa Sheikh da tun ɗazo idanunsa yake a rufe ya buɗe su a hankali kai tsaye ganinsa ya sauka akan ƙaramin bakinta wanda yake motsawa a hankali ta cikin madubin motar. Yaa Sheikh ya ɗauke idanunsa da sauri yana mai ɗan dafe kai cikin nutsuwa da kamewa wacce ta zauna a jikinsa ya buɗe baki da ƙyar ya ce.
"Ka kula, Umar-khan"
"Ok Yaa Lee" cewar Umar-khan with so much respect. Zahrah ta matsa kaɗan kusa da Yaa Sheikh tare da ɗora hannunta a saman na shi. "Asstagafirullah, Allah na tuba" ya furta cikin ranshi a zahiri bai motsa ba, sai ma rufe idanunsa da ya yi kamar mai barci. Zahrah taja gemunsa wanda yake matuƙar ɗaukan hankalinta ta ce "I love you My Excellency" baki ta miƙa zata sumbaci gefen fuskar shi, tari ya turnuƙe Halisa a kiɗime Umar-khan ya ƙara slow da driving ɗin ya ce.
"Sannu mene ya sameki, are you sick? Baki da lafiya ne?" Ganin tarin ya kasa tsayawa yasa Umar-khan faɗin "Yaa Sheikh ko zaka taimaka mata da ruwan wajanka, babu raguwar a motar" bai ɗago ba, ba kuma zakai tunanin da shi ake maganar ba..
"Sannu, sannu" ya ƙara jerawa Halisa cike da tausayi. Yana driving ya kalli Yaa Sheikh ta madubi da kuma Zahrah wacce takaicin Halisa ya cika ta duk ta hana su sakat tasu a lokaci na farko ta bawa Yaa Sheikh ɗin kyakkyawar sumbata wacce zata ruguza shi tun yanzu, tasan ba lallai ya iya riƙe kansa ba, dole ya zo gareta.
Umar ya ɗauke idanunsa yana faɗin "Yaa Sheikh Please ta wahala da yawa" ya ajjiye carbin hannunsa tare da ɗago kansa kamar mai nazari ya shiga kallon Umar-khan, not looking at her place ya kame kansa murya kamar anyi forcing nasa na magana ya ce..
"Stop the car" Yasan idan har Yaa Sheikh ya buɗe baki ya yi magana to yana nufin abin da ya faɗa ne har cikin ran shi a hankali ya yi parking motar zuwa gefen titi. Zahrah ta kalli Yaa Sheikh ta ce "Daman bai kamata mu shiga mota ɗaya dasu ba, ga wannan shegiyar yarinyar ƴar fillo, kawai su nemi abin hawa i can drive us kaji My Excellency" ya ɗan kalleta kaɗan ta wani kashe masa idanu tana shirin kama hannun shi ya fita daga cikin motar, yana fitowa ya shiga takawa a gefen titin hannunsa goye a bayansa, ganin yadda ya tsaya waje guda kansa a ƙasa yada Umar-khan fita yana tunanin ko lafiya? Ya nufi wajan shi tare da faɗin "Yaa Lee lafiya?" Ya ɗago kai ya kalli Umar-khan, mamaki ya kama Umar ganin yadda goshin Yaa Sheikh yake fitar da zufa ya jiƙe sosai da gumi.
Bai magana ba ya miƙa hannunsa tare da amsar key car ɗin hannun Umar-khan, da hannu ya nunawa Umar-khan bayan motar alamar ya shiga ciki ya zauna, mamaki ya kashe Umar a tsaye yau Yaa Sheikh zai yi driving ɗin mutane a mota bana shi ɗaya ba? Me hakan yake nufi.
Zahrah dake bayan mota tana jiran ace Halisa ta fita ita kuma ta dawo gaba ita da mijinta su tafi iya su biyu sai gani tayi Umar-khan ya buɗe bayan motar ya shigo, mamakin sauyin al'amarin cikin ƙaramin lokaci ya hanata magana.
Yaa Sheikh ya sanya tattausan farin hannunsa mai ɗauke da suma lub ya buɗe murfin gaban motar, ƙafarsa ta hannun dama ya fara shigarwa kana ya shiga ya zauna baki ɗaya.
"Ban gane wani ƙaton namijin ya zauna dani ba, bayan ina matarka?" Babu wanda ya bata amsa sai ji tayi ya yi wa motar key. Murmushi kawai Umar ya yi yana ayyana wani abu a ran shi..
Yaa Sheikh ya yi tunanin zata cika shi da surutu kamar yadda ta cika Umar-khan da hayaniya mara tushe, amma sai yaga saɓanin haka bawai kallonta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login