Showing 174001 words to 177000 words out of 197828 words
Chapter 59 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
Father ya fito daga mota shi da Maimoon, Auta sama sai Zeefa da kuma Jaddada. aka shiga kallon kallo, Father ya yi baƙi ya lalace ya fita hayyacinsa kamar ba mijin nan nata ɗan gayo ba, Jadda baki ya mutu sbd halin da ɗan ta ke ciki, babu jimawa kuma wata motar ta sake shigowa Uncle Haroon da Uncle Bashir ne a ciki. Yaa Sheikh ya juya zai shiga mota Uncle Haroon ya ce
"Malam Aliyu ai da ka tsaya ko?" Ya saki hannu motar tare da harɗe hannunsa yana rufe idanu. Mother ta kalli Maimoon da Idanunta ya yi jajir sosai, ta ce.
"Are you sick?" Maimoon ta kasa magana ta fashe da kuka tana zubewa a ƙasa tare da riƙe ƙafar Mother, Zeefa da Auta Fattoumah ma sukai elxty what Maimoon did.
Kuka suke sosai gwanin ban tausayi, a raunace Father ma ya tsuguna ya ce "Maryama na sani, wallahi na sani kuma hakkinki dana Yaa Sheikh ke bibiyar rayuwata, ban cancanci ki tausayi mini ba idan nayi kamar na haƙura dake sai naji babu wacce nake buƙata a cikin rayuwata sai ke ɗin nan, wallahi Barrister IDAN BA KE na tabbatar rayuwata zata iya salwanta, babbar isharar da Ubangiji ya nuna mini yadda ƴata ga cikina Fattoumah take cewa ta tsaneni, wacce kalar jarrabawa ce wannan" Ya fashe da kuka ganin yadda Mahaifinsu ke kuka ya sanya gabaɗaya ya ran suka sake fashewa da kuka sosai. Ya ƙara riƙe ƙafarta ya ce
"I made a mistake, a mistake I can't fix,But let's take this as the determination of the existence of Muhammad,
Destiny is the cause, be patient and forgive me for the blessings of God and our children"
Tausayi ya kama Mother irin tausayin _Mata zuwa ga mijinta_
Uwa uba yaranta da rayuwarsu ta fara lalacewa. Jadda ta matse hawaye ta ce "Harfa cewa nayi zan ɗaga mishi nono, gashi tun ban ɗaga ba rayuwarsa tana gantali tsakanin duniya da lahira, ni dai an fitar mini zakka a cikin yarana naga Nahwu naga aya akan Aliyu, amma hannunka ba zai taɓa ruɓewa ka yanke ka yar ba, kiji tausayinsa ko ɗan mitsitsi ne ki yafe masa kana ki koma gidansa ku rungumi yaranku" ta kece da kuka sosai ta ce
"Wallahi gorin duniya nake jiye musu, a dinga nuna su da baki ana babansu ya yi wa wata cikin shege harta haihuwa"
Uncle Haroon ya kada baki ya ce "Sai haƙuri fa"
"To ba ya zama dole ba? Haka fa Ubanku ya yi daman ance shi hali ɗan akene ya mutu tare da bar masa mugun gado"
Uncle Haroon ya yi shiru
Jadda ta ce "Naga duk kun tsare ni da idanu? Ku ɗin nan Ubangiji ne ya taƙaita da kuma ƙarfin addu'a kwarankwasa da a shegu za kuzo duniya, muta ta addu'a kullum ina kuka cikin dare sbd Ubangiji yafi duba zuciyarta har ya shiryu, shi ya sa duk abinda zaka aikata a duniya ka tuna cewa zaka haifa, idan baka haifa ba za'a haifa maka, gado kuma jini yake bi gashi nan Ali ya kwashe Iskancin da ubanku ya yi"
"Yanzu ai ba wannan maganar ake ba"
Ta kalli Uncle Bashir ta ce "To ita nayi niyya babu ruwanka dani" Engineer Aliyu dai yana tsugune ya ƙara cewa "Ki rungumi ƙaddara ki dawo gareni don Allah, wallahi wallahi Ina son ki IDAN BA KE I can't be..."
"Ya Isa, Allah ya yafe mana baki ɗaya" cewar Mother. Ta ɗago Auta Fattoumah ta rungome Idanunta ya yi jajir, Jadda ta ce "A'a bana son mugun abu irin naku na lauyuyi cewa zaki na yafe maka Ali kuma zan koma gidanka" kai tsaye ta ce
"Zan koma Albarkacin yarana" Father ya saki Ajjiyar zuciya. Zeefa ta ce "Father ka tashi Mother ta yafe maka" ya miƙe ya dubi Yaa Sheikh ya ce "Ka yafe mini kai ma Aliyu don Allah" Yaa Sheikh ya jinjina kansa kawai yana buɗe ƙofa zai shiga mota.
Jadda ta zabga Salati ta ce "Muhammadur Rasulullah s.a.w wa nake gani haka kamar ƴar Fulani wacce aka ce ta sai da nono"
"Ni ce" Halisa ta sauke Glasses tana faɗar haka, Jadda ta ce "To baki da lafiya ne naga kin kumbura?" Tayi shiru sai kuma ta ce "Allahamdulillah"
"A'a wallahi da sauƙi, ina lafiya a wannan ƙibar kamar anyi miki fanfo, koda yake ai ga Malam nan yasin da ban gane shi ba, kalli yadda kumatu ya zazzago"Halisa ta kai da su Uncle Haroon, Maimoon ta gaida Halisa. Kana Yaa Sheikh ya shiga mota tare da yin key bakinsa ɗauke da tasbihi ya nufi hanyar zuwa wajan Ummul, yana fita motar Umar-khan na shigowa daga wajan aiki bankin Yaa Sheikh. Driving yake a nutse duk da bai wani saba da tuƙan na shi ba, amma ba zai jure ana driving matansa ba. Halisa ta juya ta kalle shi ta ce
"Kayi haƙuri Habibi ƙalbi"
Ya saka hannu ya kamo nata tare da ɗora a fuskarsa, bai ce komai ba. Ta ce "Ina da kishi bana son ko wacce ta raɓeka Habibi, amma banwa kai na adalci na amince da ƙaddara ko zan mutu don kishi kada ka damu, ina neman alfarma ka bawa Zahrah ƴan cinta na Matarka"
Ya sauke numfashi cikin nutsuwa ya ce
"Allhamdulillah" ta kalle shi tana jan gemu ta ce "For?" Ya sha corner ya ce "Zawja tayi hankali" tayi kicin-kicin da fuska tana zame hannunta ta ce "Oh da mahaukaciya ka aura" Ya juya ya kalleta sai kawai ya girgiza kai ba tare da ya ce komai ba. Gatekeeper ya buɗe masa gate ya dinga zubawa Yaa Sheikh addu'a neman zama lafiya. Ya shafa Aljanu sai bai ji kuɗi ba, ya amshi jakar hannunta ya buɗe ya ɗakko kuɗi ya bashi. Jakar ya bata ta ce "Kai Habibi ka riƙe mini mana" yana riƙe hannunta zuwa cikin gidan ya ce "Ba mijin novels bane ni"
A kusan tare muryarsu ta ratsa parlourn dattijo ya amsa shi da Hajia halisa ta gaishe su ta ce
"Wannan tsofaffin kamar tattabaru kullum kuna tare" Dattijo ya ce
"Matar Malam gidanku" tayi dariya. Yaa Sheikh ya miƙe tare da nufar part ɗin Ummul, ya yi sallama ta amsa tare da bashi izini tsaye ya sameta gaban wardrobe tana gyara clothes ɗin ta, ya nufeta ta rungume shi sbd baya girma a Idanunta. *Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu* baya jin kan nashi matsayin babba a gareta.
Ya tsuguna ya gaidata ya nemi waje ya zauna, kallon da yake tayi mata ne ya sanya ta lura akwai wani abu ta ce
"Arɗona ya akai?" A taushashe ya ce "Ki bani labarin Abbi" tayi shiru sai kuma ta zauna ta ce
"Na faɗa maka, me kake son ji kuma" Ya kalleta ba tare daya amsa ba ta ce. "Mahaifinka samun kamar shi za a jima, kamar yadda kake cewa Matarka *IDAN BA KE* ba zan iya rayuwa ba, haka yake duban cikin idanuna ya ce "Ummul-khairy kina da haƙuri, Ubangiji ya biya ki, *IDAN BA KE* zan yi rashin wani sashe daga cikin rayuwata" tayi shiru alamar tana jin zafin abin sosai amma ta jure ta ce
"Bayan kasancewar shi Arɗon Rugar Bello, shi ɗin ma'abocin shiga jeji ne, har aka yi rashin sa a ya faɗa gidan tururuwa, tunda daga wannan lokacin yake jinya sosai, ya fara gane-gane amma bai faɗa mini ba, daga ƙarshe ko yana gida sai ace an ganshi waje kaza, na share duk ban damu ba, ashe a faɗawa gidan tururuwa da ya yi, ya samu matsala Aljanu suka ratsa jikinsa wanda lokacin daya yana iya fahimta ko jin abinda ba ko zai ji ba, idan na damu sai ya ce meye ne ƴar matana akwai wanda zai maye gurbinki gareni, yana nan zaki samu, wani lokacin cikin dare zai ta shi ya fita jeji babu jimawa sai ya dawo, da safe na sake gani ya dawo mutum biyu kenan, sai ya ce kada na wani damu, mahaifinka har magunguna yake bayarwa ya ɓoye wata laya acan Rugar Bello ya ce kada a taɓa fito da ita sai lokacin da wani jininsa ya ɓukaci jin wani abu daga cikin rayuwarsa" ta goge hawayen idanunta ta ce "Magana ta Gasky ban taɓa ganin mutum kamar mahaifinka ba, nagartar shi ta kai, yana da zafi ƙwarai amma yana da sauƙin kai baya ɗaukan duniya ta zafi, idan na kalleka sai naji kawai shi nake gani baka ɗauki komai nawa ba, baka ari wani abu daga wajena ba amma babu abinda ka bari na Mahaifinka everything"
Ya saka hannu ya goge mata hawayen idanunta ya ce "Allah ya yi masa rahama, ina son Abbi kamar yadda nake son Ummul" ta ja hancinsa ta ce "ina tunanin lokaci zuwa Rugar Bello ya yi a fito da layar a duba mene cikinta" Kafin ya yi magana suka ji muryar Halisa Ummul ta ce "Shigo" tana shigowa ta juya zata fita ganin uwa da ɗana zaune saman gado Yaa Sheikh sai narkewa Ummul yake. Ummul ta miƙe ta ce
"A'a dawo mana ni tashi zan yi" Halisa ta ce
"A'a daman kawai yunwa nake ji" Ummul ta kalli Yaa Sheikh ta ce
"Bata ci abinci ba kuka taho?" Yaa Sheikh ya kwanta gadon Ummul yana sauke numfashi ya ce "Ita take cinye abincin gidan fa, ni da Fatymerh bamu da ci" Halisa ta haɗe fuska taƙi cewa komai sbd ganin idanun Ummul, ta ce "Shige ya danna miki wannan ƙafar bari na kawo abinci" ta fita ita kuma ta shigo bedroom ɗin tana zama ya jawo ƙafar ya dinga danna mata, idan ya kalli ƙafar sai ya kalli fuskarta shi kaɗai ya saki murmushi ta ce "Wai Habibi me ka kewa dariya" ya ce "Kalli hancin ki Zawja kamar fanke, Asstagafirullah" ta ɗauki pillow ta cilla masa ya cafe ta ƙara ɗaukan wani ta cilla masa sai kawai ta fashe da kuka ta ce "To waye ya jawo mini idan ba kai ba" ya rungumeta bakiɗaya ya ce "Sorry zo nayi miki waƙa".... Misalin 9 na dare ya shiga sakkowa daga kan upstairs ya nufi part ɗin Zahrah yi mata sai da safe, ya sameta kwance Idanunta yana kallon gefe ɗaya wayarta can nesa da ita, Ya yi sallama ta amsa a hankali tana tashi zaune ya jima tsaye yana kallonta kafin ya zauna kusa da ita cikin taushin murya ya ce "Lafiya"
Tayi murmushi kanta ƙasa ta ce "Ya Ummul? jikin Halisa su Abba Hakimi" ya tsora mata idanu yana son gano meke damunta, ganin yaƙi magana ta ce
"Nayi abinci ban sani ba ko zaku iya ci" nan ma bai magana ba sai can ya ce "Ina ki ka iya?" Ta ce "Nayi searching by Google" ya jinjina kai ya ce "Come" Ta kalle shi ta ce "Halisa" bai magana ba ya saka hannu ya jawota jikinsa ya rungometa, a tsakanin nan ya lura Zahrah nada haƙuri, kuna da alama haƙurinta shi ne zai taimaketa Allah baya taɓa mutum da mugwayen abubuwa dole ya baka wani abu wanda za ai misali da shi, tabbas tana da haƙuri ya kuma ji tausayinta Halisa kuma zafi gareta ta iya masifa amma tana da saurin yafiya. Ya ƙara rungometa jin ta sauke numfashi a kunnenta ya ce "Fatymerh Zahrah" tayi murmushi sai taga bata damu ta neman komai wajansa ba, a karo na farko wani abu mai kama da SO ya gilma a zuciyarsa game da ita ɗin. Ya ɗago kanta duk ta rame amma tana da kyau sosai itama babu zato taji ya ce...*_Arewabooks@Nimcyluv75_*
Ransa ya ji ya ɓaci for no reason ya sauketa daga jikinsa yana miƙewa tsaye hannunsa zube cikin aljihu, slowly ya sauke numfashi trying to control his anger, cikin nutsuwar nan tasa mai jan hankalin mutane gare shi ya shafa kai a hankali ya ce.
"Da kin huta, munci abinci" tayi murmushi ta ce "To babu damuwa sai a zubar, daman ba lallai ku iya ci ba" bai kalleta ba ya nufi waje yana faɗin.
"Ba kyau albazaranci, ki fito da abinci za a bayar" kai tsaye ya buɗe ƙofa ya yi waje, not too long ya dawo ya sameta a parlour hannunta riƙe da warmer ta miƙa masa ya amsa tare da sake fita, ta na nan tsaye ya ƙara dawowa ya saka key ya rufe gidan.
Tayi ta kallonsa jin kamar idanu na yawo a kansa, gently ya juya yana zuba mata idanunsa da yake rufewa sbd tsananin gajiya da son yaji ya samu kansa cikin hutu ko ya yi barci ishasshe. "Need something?" Ta yi ƙasa da kai sbd kwarjinin da ya yi mata, yau ɗin sai ta ganshi yafi kullum cikar zati ta ce
"Karatun? Ina nufin wankan da kai magana" ya ƙarasa kamar zai tsaya inda take sai ya dubeta da kyau cikin kulawa ya ce "Zuwa safe, ki kula"
"Okey good night sweetheart" tayi part ɗinta, shi kuma ya yi addu'a ya shiga tofawa a ko wanne lungu na parlourn, kafin ya kashe hasken ɗakin.
Direct wajanta ya nufa, tun tuni zuciya da gangar jikinsa ke jansa zuwa gare ta, ƙofar a buɗe take ya buɗe bata parlour ya shige bedroom bakinsa ɗauke da sallama cikin sanyin murya.
"Wasalamu Alaika Yaa Sheikh" ta faɗa tana miƙewa da ƙyar frm head to toe yake binta da kallo. "Me ciki"
Ya faɗa cikin sigar wasa ta ɓata fuska ta ce "Ai dai daga wannan Shikenan, matarka ta haifa maka" Ya saka hannu ya ɗagata yana murmushi ba sosai ba ya ɗorata a gadon ya ce "Lallai yarinya"
Ta ce "Abba"
Ya kalleta bai amsa ba ta ce "Me ya sa ka ke son ce mini yarinyar bayan kasan yanzu nima uwa zan zama"
Sunna ne zama da matarka kayi hira koda baka da ra'ayi ko baka da surutu hakan yasa ya ce "A sbd ke yarinyar ce" ta ɓata fuska sosai ganin haka ya lumshe idanunsa ta ce "Tashi ni yau na yafe kowa ya kwana a bedroom ɗin shi, wlh takura ni ka ke Abba"
Ya maƙale kafaɗa yana shafa sumar kansa tare da kwanciya saman cinyar ta ya ce
"Ni ba inda zani kawai ki barni ina nan, ina gadinki da killata kuma sannan, na baki kula idan akwai buƙata kenan" ta saki baki jin babban malami kamar Yaa Sheikh yana zage yana rera mata waƙa kafin ta ce komai ya riƙe kumatunta yana girgizawa ya ce
"Ko na tafi sai na dawo, sadakin ki sai na kawo zuciya ya nai mini zillo....," Ta tuntsire da dry sosai ta ce "Wow What a nice voice, Habibi kafi mawaƙin murya mai daɗi" bai kulata ba ta ce "Daman ka iya waƙa? Malami guda?" A taƙaice ya ce
"Malami Sahabi ne? Ba gashi kin yi dry ba"
"Don Allah sake mini kaji." Ya miƙe zaune ya ɗauki ƙafarta ya ɗora saman cinyarsa ya shiga danna mata, yana tsananin jin tausayin mace mai ciki, bare Ƴar fillonsa kuma gudan jininsa.
"Tab Yaa Sheikh da waƙa!" Ya kame kansa da kyau ya ce "Ki kula, kada a barbaɗi baki mara saiti"
"An gama jarumin, gwarzona mijina aljannata kuma ubana duniyata, I love you so much Modibbona" ya girgiza kai kawai. Ta ƙara cewa
"Ina son ka" yaji kalmar har ƙasan zuciyar shi, tsigar jikinsa ta tashi wani abu na fisgar shi musamman da cikin Jikinta ya ƙara sanyawa ta dawo kamar ba ita ba, jikinsa ya saki ya yi baya ya kwanta itama ta kwanta tana ɗora kanta a ƙirjinsa ta danne masa ƙafa da ƙafarta ta ce "Yau ba darasi ne?" A hankali ya ce "Ayu ki ka maidani?" Taja hancinsa ta ce "Kawai na san ɗan Ummul da zalama akan darasin auren, baka da haƙuri" neman magana take da abinda za a fara yi masa surutu akai har ya yi shiru sai ya ce
"To nace ki huta yau" Ta ce "Ni kuma ina buƙatar ka yau ɗin nan yanzu ma" Mamakin ƴar rainonsa ya gama cika shi ba ko wacce mace ke tarar mijinta kai tsaye ta ce tana buƙatar shi ba, sbd jan aji da iyayi irin na mata, bayan aure zama ne na dindindin, a koda yaushe miji yana cewa yana buƙatar matarsa rana ɗaya zaki iya warewa ki nemasa koda shi ɗin bai nema ba, hakan zai sanya ya ƙara jin son matarsa ƙwarai da gaske a ran shi.
"Baki jin kunya?" Tayi fari da fararen idanunta ta ce "Mene abin kunya, kai da ka ke nema kunya kaji? Kullum kazo da ƴar murya, sai ni zanji nauyi? Kenan na cutar da kai na ko bayan kai mijina ne ni kuma matarka ce" ya fahimci dai shi ɗin take buƙata, daman shima tausayinta ya keji nan da nan ya farke rigar barci tare da cilli da ita, wannan lokacin Halisa ta nunawa *Yana Sheikh* Abbanta ita ma macace ta san kan duniya, ta shayar da shi mamaki yana riƙe kansa amma sai da taso sashi yin abin kunya da zarar yaji bakinsa ya buɗe zai ce "Yasubuhanallah Allahu Akbar". Bayan komai ya daidaita ya rungumeta ya ce "Allah ya yi miki Albarka".
Da Subhi kusan tare suka tashi ya yi alwala ya sanya Arabian jallabiya da farar hula kansa, abin mamaki yana zuwa ya samu Zahrah zaune saman ladduma tana kallon sama, suna haɗa idanu ya jinjina mata kai tare da rufe ƙofar ya nufi masjid.
Misalin 11:00 Zahrah ta fito kusan a tare kuma suka fito da Halisa wacce take jera breakfast a dining room, suka kalli juna Halisa ta ɗauke tana faɗin "Ina kwana?"
"Lafiya lou" ta faɗa tana murmushi ta ƙara da cewa "Sannu da aiki, ya jikin naki da kin kira na tayaki aiki ai" Halisa ta ce "Don my me, zan iya" ƙamshin turaren shi ya bayyanar musu da sakkowar shi, Suka juya kusan a tare wani irin kallon ya kewa Halisa da sauri ya ɗauke kai yana gyara zaman alkyabbar shi, Halisa ta daure bata je gare shi ta rungume shi kamar yadda ta saba ba, duk da cewa girkin ta ne amma babu daɗin yin haka gaban Zahrah.
Ya ja kujera tare da zama Zahrah ta ce "Ina kwana?" Ya yi mmki domin bata taɓa gaida shi ba bisa ra'ayin kanta. Ya jinjina mata kai Halisa ta zuba masa breakfast kana ta zubawa kanta, Zahrah ma babu kunya taja plast ta haɗa tea. Shiru wajan ya ɗauka Yaa Sheikh yana lura da yadda Halisa ke gumi sbd azabar yaji, ya dubi