Showing 177001 words to 180000 words out of 197828 words
Chapter 60 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
abinda ta ke ji ganin bai san mene ba, ya saka hannu ya ƙwace plate ɗin ya tura mata soyayyan ƙosan daya sha kayan ƙamshi da tea mai kauri wanda bai ƙarasa sha ba. Ta ce "Nifa shi na keso" Ya ware gajiyayyun Idanunsa akanta ba tare da ya ce komai ba, ta fahimci shirun nasa ta ce "Ɗan silif ne wallahi daɗi sosai Habibi" ya ajjiye bottle water yana goge bakinsa da tissue ya miƙe yana faɗin.
"Duk an gama zuba yawo ciki" kamar jira take ta ce "Wata rana sai na ɗore maka yawon cikin baki" Zahrah duk sai ta zama uncountable kamar wata maid, sosai taji yadda suke wasa da dariyar kamar wa da ƙanwa sun birgeta, she wishes ace ita Yaa Sheikh ya kewa haka. Ta goge Hawayen daya zubu mata a ɓoye.
Can ya zauna saman kujera ya ce "Jeki Library ki ɗakko ƙawa'idi guda uku" ta ce "To" tana barin wajan ya ce "Fatymerh Zahrah" ta amsa da "Na'am" da hannu ya ce ta zo. Ta miƙe ta dawo wajansa ya kama hannunta ya ce "Kina lafiya?" Ta amsa da "Allahamdulillah" ya jinjina kai yana riƙe da hannunta har Halisa ta dawo, sosai ta gani amma bata nuna ba ta koma gefensa ta zauna suka sanya shi tsakiya, ya buɗewa Zahrah babin da zai musu, yasan Halisa ta sani amma baya son nuna bambanci itama ya amsa ya buɗe mata. Cikin sanyi da taushin murya ya ce.
*Babin raɓewa wanka*
Ya yi shiru, cikin nutsuwa ya shiga bayanin kamar yadda ya yi wa Halisa lokacin da suke garin Makkah!. Ya ɗora da faɗin.
"Akwai wakan jinin haila, Janaba na jima'i, wankan jinin biƙi, wankan juma'a, wankan shiga garin Makkah, wankan mutuwa, shi ne rabe-raben wanka" sukai shiru baki ɗaya musamman Zahrah ya ɗora da faɗin.
"Janaba: Janaba ɗaya ce daga cikin abubuwan da suke wajabta wanka, wanda yake hanyoyin kasantuwa da janaba sune kamar haka; *Fitar Mani* Idan maniyyi ya fita daga mace ko namiji to wanka ya wajaba, amma kafin wankan ya wajaba sai ya zama maniyyin ya fitane ta hanyar jin daɗi, kamar kallo ko wasa ko tabe-tabe ko jingina.., amma idan ya fita ba ta hanyar jin daɗi ba ya fitane ta hanyar wahala, kamar ya taka wuta ko harbin kunama ko kuma wutar lantarki ta ja shi, to wannan wanka bai wajaba a kan shi ba sai da kawai ya yi alwala. Shi wannan fitar maniyyi da ake Magana akan shi ko dai ya fita a farke ko kuma ya fita ana barci, idan ya fita ana farke shine ake maganar an ji dadi ko ba'a ji ba, amma idan ya fita ana barci ne to ba wata maganar jin dadi wanka ya wajaba"
Yanayin yadda yake bayanin kaɗai ya isa ka fahimci magana bata dame shi ba, shi ya sa gabaɗaya ko wa'azin shi za'a tura mutum ake jinsa muryarsa mai sanyi ce cikin haiba ya ce
"Na biyu, saduwa da iyali idan har an tabbatar miji da mata sun zama turmi da taɓarya babu shakka wanka ya wajabta a gare su, inma namijin ya fitar da maniyyi ko mai fitar ma haka ma macen, idan mutum sai sadu da Iyali sau goma to wanka ɗaya ne ba goma ba.Idan mutum ya sadu da mace kuma yake so ya jinkirta wankan janaba zuwa an jima to abinda zai yi shine ya yi tsarki sai ya yi alwala, domin alwalar tana rage kaifin janaba, sannan kuma tana kara kuzari lokacin da ake so aƙara saduwar.
Idan mutum ya sadu da mace sai bai fitar da maniyyi ba wanka ya wajaba akanshi kamar yadda bayani ya gabata, to bayan ya yi wankan sai kuma ya ga maniyyi ya zubo, to anan idan wata sabuwar sha'awace ta fitar da wannan maniyyin wani wankan ya kama shi, amma idan janabar da ya yi wa wankace maniyyinta ya zo yanzu to alwala kawai zai yi" Ya rufe littafin yana amsar ruwan da Zahrah ta miƙa masa ya sha kaɗan ya ajjiye ya ce. "Mu tsaya nan, sai gobe In shaa Allah, kafin nan ga yadda ake wanka"
Suka kalle shi ya kame fuska ya ce
"Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai siffatul ijza' (ta
wadatar), kuma wacce
ake kira siffatu
kamal' (ta kamala). Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da
zaka fara yi shi ne: zaka karkato bakin
mazubin ruwanka, ka
wanke hannunka sau
uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka ɗebo ka wanke gaban ka, a dai-dai lokacin da
zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko
waninsa) wanda yake
wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana
kayi tsarki kenan to
daga nan kuma sai kayi alwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah zakayi sai abu ɗaya shi ne wanke
ƙafafuwa to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shi ba, to daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka ɗebo ruwa ba
sai ka murmurza kanka saboda ko wanne gashi da
ya buɗe a lokacin da
maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya
koma yanda yake, don
gashin dan Adam yakan buɗe musammam
gashin sa na ka, idan ka zuba ruwa a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani abu daban, bayan haka sai ka ɗebi ruwa a cikin tafin hannun ka ɗaya sai ka zuba a kanka ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, ka sake kanfata na biyu ka tabbatar ya
game ko'ina a kanka,
haka na uku ka tabbatar ya game ko'ina a kanka. To idan kayi wannan sai
ka ɗebi ruwa ka game
dukkanin jikin ka da shi
kana mai farawa da
ɓangaren jikin ka na
dama kafin na hagu, sannan na hagu ka
tabbatar ruwa ya taɓa
ko'ina. To idan kayi
wannan ne ka kammala,abu na ƙarshe shi ne sai
ka wanke kafar ka ta dama sannan kafarka tahagu shine cikon alwalarda ka riga ka faro. Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan janaba. In wankan janaba ne
haka zakayi, in na haila
ne haka za'ayi inma
wanka ne na biƙi haka
mace zata yi, idan
wankan jumu'a ne ma haka za'ayi, wankan idi
ma haka zaka yi,
banbanci kawai shi ne
NIYYA" Halisa ta kama hannunsa ta ce
"Allah ya saka da alheri Yaa Sheikh, Allah ya ƙara basira da ilimi mai amfani ya sa matar malam ta ɗauki halin Malam" Ya girgiza mata kai, Zahrah ta goge hawaye a ɓoye ta ce "Thank you so much Sweetheart really appreciate" Ya miƙe tsaye yana gyara zaman alkyabbar da hiramin kan shi ya ce
"Allah ya yi muku albarka" Halisa ta miƙe tana maƙalewa gefensa ta ce "Zan raka ka mota" Bai ce komai sukai waje Zahrah ta bisu da idanu, addu'a Halisa ta dinga yi masa kala-kala harda yaji tsoran Allah akan yadda zai taraya dukiyar shi.
Kai tsaye Police station ɗin da ya kai Saif-wazir ya nufa, ya cike komai aka bashi beli damar kamar ajjiyar shi ya kai, ya nufi gidan Abba Hakimi lokacin Umar-khan ya shigo tare da iyayen yarinya da hisba suka kama, uwar yarinyar ta dinga kuka kamar ranta zai fita shi ma kan shi Saif-wazir ya yi laushi ko haɗa idanu ba ya yi da *Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu* kai tsaye kuma Yaa Sheikh ɗin ya nuna auren Saif-wazir zai haɗa da yarinyar Abba Hakimi ya amince, suka tsayar da maganar nan da sati mai zuwa ranar juma'a za a ɗaura auren. A nan Abba Hakimi yake shaidawa Yaa Sheikh an bawa Khalil Ahmad Nuran Sarki auren Maimoon domin ya gaji da sintirin da yake daga Sokoto zuwa Kano, don haka rana ɗaya za a ɗaura koda Maimoon bata tare ba.
*_3 weeks ago_*
Har kawo lokacin babu abinda ya haɗa Zahrah da *Yaa Sheikh* haƙurinta ya ƙara bayyana, bata sake masa maganar komai Halisa cikinta ya girma sosai domin kusan wata na takwas yake ta kusa shiga na tara ta zama babbar mace. Abu ɗaya ke damun Zahrah yadda take yawan mafarkai da jarirai guda uku suna binta suna kuka duk inda tayi suna maƙale da ita ɗaya hannunsa riƙe da almakashi, ɗaya safa, ɗaya kuma da magani duk ta firgita kuma ta kasa faɗawa Yaa Sheikh. Wani lokacin suna zaune zata sabura tana "Don Allah kuyi haƙuri ban sanku ba, ba yara na bane" al'amarin kamar wacce zata zauce. Satin daya kama Yaa Sheikh yaso kai Halisa Sokoto can masarauta amma girman cikinta ya hana shi, ya ɗauketa ya kaita wajan Umma A'isha, Zahrah kuma ya ce ta shirya su je Yola ta nuna bata so ko kamar iyayenta bata ƙaunar ya yi, sai da ya yi mata jan idanu ta amince. Yaa Sheikh da Ummul da kuma Zahrah suka nufi Yola, gaisuwa kawai ke haɗa Ummul da Zahrah suna zuwa suka sauketa a Jimeta. Suka shige Rugar Bello, har inda Layar take Ummul taje ana haƙowa ta buɗe tas taci karo da rubutu kamar haka.
*_Kariya ne daga dukkan jinin mai wannan layar, babu shi babu aikata zina, duk inda zina take mu aljanun Arɗon Rugar Bello mun haramtawa jinin Arɗo raɓar inda take, ko ya haɗu da makira wacce ta aikata hakan to mazantakar shi ba zatai aiki ba, matarsa wacce take tsarkakkiya a gare shi ita ce zata same shi, babu mai iya lalata wannan aikin domin wanann layar bata gaskiya ba ce, ta gaskiyar na wajanmu Wannan shaida ce domin ku sani, idan wanda ya mutu zai dawo to lallai mazantakar shi wata rana zatai aiki, idan wanda ya mutu ba zai dawo ba babu shakka shi da wanda ya ke zina ko ya taɓa har abada......
*Note*
_Masu magana akan auren Yaa Sheikh da zata ba zai taɓa faruwa a zahiri ba,to wallahi wallahi za kuyi ladama kuma za kuyi kaffara ku saisaita rantsuwarku ni ke da labari na fiku sanin mene zai faru, babu hujjar da zata saka littafi ya ƙare na dinga jansa bisa jin daɗina rubutun nan da wahala ba, komai ma rubuta daman a tsare a yake sai abinda aka cire..... Nayi magana akan wanka na tsagaita bayanin nawa sbd nauyin wata maganar amma ku bincika littafan Fiqhu, ko Umdatul ahhakam_*_Arewabooks@Na'ima Sulaiman Sarauta76_*
"So that's the reason?" Ummul ta faɗa a ranta tana ƙara kallon rubutun, Yaa Sheikh ya kalleta kawai, sai kuma ya miƙa mata hannu ta bashi shi ma ya karanta kamar yadda tayi. Sai taga sam bai damu ba, ko dan ba a gane damuwar shi ne ya sanya haka? shi ɗin kaifi ɗaya ne kuma mai wahalar fahimta, wannan magana ce mai matuƙar nauyi Yaa Sheikh kuma ya kasance namiji ba mace ba, bare ta tsaya su tattauna makomar Zahrah take tunani, bata jin yarinyar a ranta amma tana girmama auren dake tsakaninta da Yaa Sheikh ɗin, infact Ummul bata ɗauki Zahrah matsayin,Daughter-in-law ɗin ta ba. Ummul tabi bayan Yaa Sheikh zuwa cikin Rugar Bello domin daga baya ne inda aka ɓoye layar take tana zuwa ta samu Yaa Sheikh shi da Labo suna magana wanda ya wancin maganar Labo ke yinta Yaa Sheikh jinjina kai kawai yake sbd tsananin gajiya, akwai tarin abubuwa a gabansa baya jin zai zauna a Rugar Bello zuwa wani lokaci. Wata Bukka Labo ya nunawa Yaa Sheikh ya durƙosa tare da shiga ciki bakinsa ɗauke da Tasbihi. Ya zauna saman wata tabarmar kaba yana tankwashe ƙafarsa, Ummul ta shigo ta zauna ba jimawa aka kawo musu Kindirmo fal cikin ƙwaya da zafinsa, tsananin daɗin Kindirmon ya sanya Yaa Sheikh rufe idanu ya sha son ran shi a lokacin kewar mahaifinsa da matarsa ne suka lulluɓe zuciyarsa.
Ummul ta ce "To ɗan na gada, sai yanzu ka ƙara fitowa matsayin Fulanin Yola Usul kuma cikakke, Fulanin ma ɓangaren makiyaya masu dukiya"
Ya dubi Ummul ɗin tasa yana janye ƙwayar ya ce
"Fulani da Barebari ba a zama lafiya fa naji"
"Wani ya ce maka ni barebari ce?" Ummul ta faɗa tana watsa masa harara ya yi murmushi kawai yana lumshe idanunsa, a wannan daren Yaa Sheikh ya zauna da ƴan uwansa Fulani ya shaida musu baya buƙatar maye gurbin mahaifinsa kawai su kasance masu adalci wa juna, banda ƙyashi da hassada, Yola ita ce mahaifar shi duk da ba a nan aka binne cibiyar shi ba. Washegari suka ƙarasa Rugar Rome, yaso da ƴar fillonsa ya zo idan akwai abin da ba zata manta ba, shi ne rayuwar da tayi a cikin wannan Rugar, da dukkan wanda yake cikinta ba zata manta da su ba. Shatu ta ƙara girma da wayo, Ummul ta tambayi umarnin tafiya da ita aka bata, zo kaga murna wajan Shatu.
Zahrah ta share hawayen idanunta ta kalli Mimi ta ce "Baki taɓa zaunar dani kince abin da nake ba daidai ba ne, kina cewa na maida hankali a karatu amma me ya sa ki banbanta mini karatun boko dana addini, baki nuna mini yadda zan samu lahira ba sai ki ka nuna mini yadda zan san duniya, ita ma ta sanni"
Ta fashe da kuka sosai numfashinta na riƙewa Idanunta ya yi jajir cikin zaucewa ta ce
"Nayi rayuwa irinta dabbobi, na zama jahila na kuma zauna cikin jahilanci, kun cutar da rayuwata tun ina ƙarama da wando da riga na buɗe idanu da sunan sune kaya na, ina 4yrs kuka sani play grp, na san kun sani islamiyya ban san yaushe na daina ba, ban kuma san dalilin daya sanya na daina ba, ina shigar da bata dace ba, ina fita inda nake so kina ganin sauyi a jikina amma baki taɓa cewa fitar da nake bai dace ba....," Yaa Sheikh dake bakin ƙofa shi da mahaifin Zahrah Alhaji Farouk ya ce "Kee!!"
Ya faɗa cikin ɗaga sauti, hakan ya sanya ta tsaya da maganarta fuskarta tayi caɓa-caɓa da hawaye ga majina ta ce
"Sweetheart ranar wanka ba a ɓoye cibi, duk halin dana shiga she's the reason behind"
"Ki fahimta Zahrah, bayin kai na ba ne soyayyar da muke miki ya sanya idanunmu ya rufe bama son damuwarki, bama son duk wani abu da zai baki matsala a rayuwa, tunanina kullum zamu rasaki" Zahrah ta fashe da dariya while kuma hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Gaskiyar bahaushe, daman ance ka ƙi naka duniya ta so shi, kaso naka duniya ta ƙi shi, tun banje ko'ina ba ina ganin ishara kala-kala a duniya, Ubangiji ya fara hukuntani da soyayyar wanda bana ran shi, kullum ji nake zuciyata kamar zata fashe naji kamar na bar gidan Yaa Sheikh" Ta girgiza kai ta ce "Soyayyar da nake masa ta rinjayi duk abinda zuciyata ke raya mini, motsin Yaa Sheikh kawai idan naji yana sauƙaƙa mini ƙuncin da kuka jefani da halaka na tsayin shekaru, balle nayi tuzali da fuskarsa sai naji iya hakan kawai ya wadatar dani"
Ta miƙe tsaye tare da dawowa wajan Yaa Sheikh ta ce "Ba miji na ɗauke shi ba, ina masa kallon Yayana ne, wanda zai iya tsare mutuncina, ya fito dani daga ranar da kuka sanya ni zuwa inuwa, na gane bambanci mai ilimi da jahili na gode Allah da bai barni na dauwama haka ba, balle na zo duniya a banza na koma a iska"
Tas ta goge hawayen idanunta ta ɗauki mayafi ta yafa ta ce "Muje Sweetheart"
"Fatymerh Zahrah!"
Yaa Sheikh ya furta iya gareta, ta kalle shi sai tayi murmushi ta ce
"Wallahi ba zan ƙara kwana a gidan nan ba, kuma daga yau su ɗauka basu taɓa haihuwa ba balle su tuna suna da yarinya kamata, wannan shi ne girban abin da suka shuka"
Mimi ta fashe da kuka ta kasa magana ta zube a wajanta ta ce
"Ni ɗin wacce irin uwa ce mara lura da tarbiyya me zan faɗawa Ubangiji"
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Alhaji Farouk ya furta, yana cikin masifa goma da ashirin.
Ta kama hannun Yaa Sheikh dake tsaye bai tanka musu ba, ya juya ya bita zuwa compound Ummul na zaune cikin mota domin daga nan Airport za su shige, ta dinga kallon Yaa Sheikh da mmki ya shaida mata a nan gida zai bar Zahrah amma ya akai suka fito tare. Zahrah ta saki Yaa Sheikh ya dubeta cikin nutsuwa da tarin kulawa yana ɓoye yanayin da yake ciki ya ce
"Iyaye fa?" "Na yafe musu, nima yafiyar Ubangiji nake nema ko zaka dubeni da idanun Rahama ka tuna nima matarka ce ka bani kulawar da nake so"
"Ina son barinki nan" ta kalle shi da mmki sai ta ce "Zaka iya barina, amma kana fita zan fita zanje duk inda Allah ya nufa na san ba zan wulaƙanta ba, amma yanzu kai Allah zai tambaya tunda ina ƙarƙashin ka"
Ya rasa bakin yi mata bayani ta fashe da kuka sosai ta tsuguna daidai ƙafarsa ta ce
"Ni ɗin daman ai ƙaddarar ka ce, amma don Allah kaji tausayina ko zauna dani kulawarka kawai na keso ba wani abu ba" ta ƙara sakin wani raunataccen kuka mai ciwo da cin zuciya ta ce "Tun ina jin haushin Matarka har na dai na, ganin son da ka ke mata na fara son ta ko za kaji tausayina" ya numfasa yana riƙe kansa dake sara masa.
"Stand up" ya faɗa a taƙaice. Ta ƙasa miƙewa sbd kukan da yaci ƙarfinta ya saka hannu ya miƙar da ita, tana tashi ta faɗa jikinsa ta ce
"Rayuwata bata da amfani Yaa Sheikh nayi ladama, soyayyarka zaka kashe ni" jin numfashinta na fita da ƙyar yana ɗan bata side hug yana bubbuga bayanta alamar rarrashi. Ta shiga sauke ajjiyar zuciya a hankali ya zareta suka nufi mota ya nuna mata gaban mota, shi kuma ya shiga baya kusa da Ummul suka nufi airport.
Alhaji Farouk yana tsaye ya zama kamar statue yaji ƙarar notifications yana dubawa yaga an zare kuɗi daga acct ɗinsa kuɗi masu yawan gaske. Kafin ya motsa bank sun kira shi sun bashi tabbacin ya samu hackers sun kwashe masa kuɗi, gumi ya dinga yanko masa yana zubewa wajan. Kafin ya ƙara wani tunani manger kamfanin shi ya masa waya yanzu haka kamfanin ya kama da wuta. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un wayo Allah Allah na tuba Allah ka tausaya mini Allah ka dubi idanuna ka yafe mini" ya dinga faɗa yana fashewa da kuka. Karayar arziƙi ta dimfaro shi..... A hankali yake ware idanunsa akan harabar Orphanage ɗin na shi cikin nutsuwa da tarin kamala ya