Showing 15001 words to 18000 words out of 197828 words

Chapter 6 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9305

bashi shekara ɗaya ko wata kaza? He is thirty-three years old now, but to this day there is no thought of marriage in his mind. Ni da kai na, na fara shakku da tantama idan ba lalata yaran mutane yake" wani irin ɗaci Mother taji a ƙasan zuciyarta, wanda ya sa ta fara ladamar yarda da Mijin nata da tayi. Magana ɗaya zai yi a janye Case ɗin amma yaƙi infact bai damu da matsalar ɗan nasa ba. Miƙewa tsaye ta yi tana kallonsa idanunta na sauyawa amma ta hana kanta zubar da hawaye ta ce.
"Court zata tantance mai gaskiya, kuma zata wanke Sheikh daga sharrin da ake masa" tana faɗin hakan tai waje cikin ƙonar zuciya. Bayanta yabi da kallo yana faɗin "If you give evidence that Aliyu is innocent, zan tsaya wajan karɓar masa haƙƙinsa Maryam" sosai kalamansa suka daki kunnanta amma ta share.
Tana zuwa parlour ta samu yaranta zaune sun zabga tagumi "Maimoon zugi driving nawa, Zeefa ke da Fattoumah ku zauna, I'll be back 10:00 ki tabbatar kunyi alwala tare da sallah kun kwanta barci, kada na dawo naga kuna kallo ok" Fattoumah ta ce "Mother ina zaki? Yaa Lee har yanzu bai fito ba fa?" Mother ta ce "Kada ki takura Sheikh, idan kika takurasa sai ya shaƙeƙi tas kafin ya baki amsa, You better be careful, bye my babies"... "Bye Mother" fita sukai har lokacin wasu ƴan jaridun na ɓoye suna jiran ganin motar Sheikh ta fito. Maimoon na fita taja motar da gudu ta ɗauki hanyar da zata kaita Maiduguri road.


Tafiya kawai Danejo take babu takalmi kalbar kanta duk ta hargitse duk wanda ya ganta a wannan lokacin babu tantama zai kirata da mahaukaciya wacce ta jima cikin ciwon haukan. Tafi futu futu baya hayyacinta baki ɗaya,ita kanta ba zata taɓa tuna kwanakin data shafe tana tafiya ba, kuma abin mamaki ko gajiya ba tayi duk wanda ya ganta tambayar duniya idan zai mata ba zata taɓa kallon inda yake ba, balle kuma ta bashi amsa. Cikin ikon Allah ta samu kanta a gefen Rugar Rome inda take zuwa kiwo, tana zuwa nan ta yanke jiki ta faɗi babu numfashi. A hankali jikinta ya shiga Girgiza wani hayaƙi nafitowa ta jikinta a hankali hayaƙin ya cure waje guda, a haka ya rikiɗe zuwa suffar Prince.. idanunsa na kanta yana ƙoƙarin zuwa inda take yaji an daka masa tsawa wacce ya sanya ya tsaya da zuwa inda take, ko ba a faɗawa Prince ba ya san wane yake masa wannan tsawar domin shi kaɗai ya isa ya yi masa tsawa ya saurara.
"Ka Saurara Prince, kada ka kuskure ka taɓa Bil'adama ɗin nan" Prince ya juya idanuna ya sauka akan mahaifina wanda yake cikin suffar mutane cike da kamala. "Matata ce Abba, ina da ikon taɓa ta a lokacin da nasu kada ka hanani aikata hakan" Wanda aka kira da Abba ya kalli Prince ya ce "Ban san yaushe ka zama mai son zuciya ba, zuciyoyi nawa zaka baƙantawa? yanzu bayan wannan ƴar tayin kaje ka saka bawan Allah cikin masifa me ya yi maka?" Prince yana huci ya ce "Abba wannan bawan Allan shi ke shirin rabani da farin cikina, na jima da sanin haka shi ya sa na fara yin abin da ya dace, kashe sa naso yi ma.." Abba ya kalli Prince da mmki kafin ya ce "Shi ne daidai da rayuwarta, shi ne Bil-adam shike da ikon kasancewa da ita, ba kai ba da kake Hallitar Ubangiji ta ban ƙasa ina rabaka da son zuciya, koda muke aljanu hakan bai zama lasisin da zamu cutar da wata hallita dake duniya ba, ko me zakai ba zaka taɓa iya cutar da shi ba" A hargitse Prince jiki na rawa yana rikiɗewa zuwa suffar aljanu ya kalli Safwan ya ce "Kai ne ka faɗa masa abin da na aikata ko? Kai ke ko?" Kafin Safwan ya yi magana Prince ya ɗaga sa zuwa sama tare da buga ƙasa da jikin dutse yana ƙoƙarin sake ɗaga Safwan, Abba yai wata kururuwa hakan yasa Prince yin kururuwa shima lokaci guda suka koma aljanu...


08119237616...*🌈 IDAN BA KE 🌈*


_*Zaku samu cikakken labarin a Arewabooks, kuyi searching sunan littafin ko username Arewabooks@Nimcyluv*_


8....
Ihu da kururuwa Prince ya din ga yi, sbd tsananin azabar da Abba ya ganawa masa. Cikin wata kakkausar murya wacce take nuna cewa ko a cikin Aljanu shi ɗin nada banne, kuma taƙadiri ne. "Akan aurena dake kan Halisa banƙi na kashe kowa na illata shi ba, daga ci hadda kai Abba, ba ruwana da kasancewar ka mahaifina, kada ka rabani da Danejona zakai babban kuskure zanyi ɓarna a duniya" Bakin Abba na fitar da hayaƙi kamar zai kunna wuta a ciki ya ɗaga hannunsa sama gaba ɗaya ya naɗe Prince cikin wata sarƙa da yana bakinsa ɗauke da addu'ar neman samun nasara akan Prince ɗin.
Duk ihun da yake bai hana Abba ya sarƙafesa cikin yanar ba idanunshi ya yi wata kala. Cikin ɗaga murya mai amo! Ya ce "Na raba aurenka da Halisa, babu kai ba ita, kuma a yanzu zan cire cikin dake jikinta mara imani mai muguwar zuciya" yana faɗin haka ya yi girgiza tare da ɓatar da Prince ɗin baki ɗaya daga wajan. A hankali Abba wanda Asalin sunansa ya kasance MURWAS ya sauke numfashi, tare da juyawa ya kalli Halisa dake kwance a ƙasa tana barci, juyawa ya sakeyi ya kalli Safwan dake kwance shi ma. Cikin nutsuwa wacce ba zata addabi dabbobin dajin ba ya yi Girgiza tare da rikiɗewa ya koma suffar mutane sak. Hannuna ya ya ɗauki Halisa Dajeno Rome da sauri ya nufi cikin Rugar Rome zuciyarsa fal farin ciki ganin yau ya raba ɗansa Bilal da Bil-adam.
Babu kowa cikin rugar kamar an share hakan yasa ya fara bin bukkokin Rugar da kallo kamar daga sama Hamma Yabi ya fito daga cikin ruga zufa na yanko masa hannunsa riƙe da ƙwarya maganin gaba ɗaya tunaninsa ya yafi wani wajan bai lura da mutumin dake tsaye yana binsa da kallo ba. "Jamɓanduna" Abba ya faɗa yana kallon Hamma Yabi dake ƙoƙarin yin gaba, tsayawa ya yi yana duba mutumin da ya ce masa Ina kwana, cike da mamaki ya ce "Jamni tawon" ma'ana lafiya. Abba ya jinjina kai ba tare da ya ce komai ba, jikin Hamma Yabi na rawa ya amshi Danejo daga hannun Abba kafin ya ce "Ikon Allah, ina kasa meta? Tsayin mako guda ta ɓace mana ba ita ba labarinta, shai Allahamdulillah" Murmushi mai sanyi Abba ya yi cikin nutsuwa ya ce "Ayyah ni ma yanzu ina iyu a cikin ruwan na ganta kwance gefen ruwan" cikin nuna jin daɗi da manta halin da Dada ke ciki wanda duk rashin Danejo ya haifar da haka ya ce "Shannu, wallahi shannunka kaji" kai kawai Abba ya ɗaga yana ƙarewa yanayin rugar kallo kafin ya juya bayan sun yi Sallama da Hamma Yabi yabar wajan. Yana fita ya ɓace a wajan baki ɗaya.


Dada na kwance bakinta na fitar da wani ruwa kamar dafara Shatu na gefe tana kuka tamkar ranta zai fita. A cikin wannan halin Hamma Yabi ya shigo cikin bukkar hannunsa ɗauke da Danejo wacce har yanzu take bacci. Jikin Shatu na rawa ta miƙe fuskarta cike da hawayen halin da mahaifiyarsu ke ciki, amma hakan bai hana Fuskarta baiyyanar da farin cikin da zuciyarta ke ciki ba na ganin Yayarta Danejo. Bakinta na rawa ta ce "Hamma ina ka samu Danejo, da gaske ita ce yanzu Dada zata tashi naji daɗi sosai" bai ce komai ba ya kwantar da Danejo gefen Dada idanunsa akanta ya ce "Maza kawo mini ruwa" Shatu ta miƙe da sauri tare da nufar tulo ta tsiyayi ruwan mai ɗan sanyi, tana bashi ya shiga shafawa Danejo yana kiran sunanta. A hankali ta sauke ajjiyar zuciya tana buɗe ido a nutse. "Danejo"... "Halisa" Shatu da Hamma suka kira sunanta lokaci guda,a sanyaye cikin sanyin jikinta kamar kullum ta shiga binsu da idanu. "Kin farka?" Kalmar Hamma ta sanya ta lumshe idanunta kana ta buɗe a hankali tana sake binsa da kallo kafin ta yunƙura zuwa zaune "Naga kuna ta kallona kamar za a cini ɗaya?" Murmushi Hamma ya yi ya ce "Munji daɗin ganinki Danejo, mako guda kenan mun rasaki kin ɓace daga idanunmu" da Mmki take kallonsa ɓata? Mako guda? Taje ina? Ita gani tayi kamar barci take mai ɗauke da mafarkai kala-kala. Shiru tayi tana ƙara sauke numfashi tare da fara tunanin maganar Hamma Yabi. "Hankalinmu ya tashi, Kullum Dada cikin kiran sunanki take, gashi yanzu ko buɗe ido ba tayi jikinta ya tashi ina tsoro kada mu rasa Dada kamar yadda muka rasa Baffa" ambaton sunan Dada ya saka Danejo saurin juyawa zuwa gefenta manyan idanunta ta buɗe "Dadata" ta furta a ruɗe ganin yadda Dada ta ƙanƙame jiki, idanunta na kafewa kamar mai shirin mutuwa cikin muryar kuka ta ce "Na lalashe ni Danejo Dadata kada ki barni kada ki mutu do Allah,Kada kibi Baffana" sai girgizata take amma ina Dada ko motsi ba tayi.
Da sauri Hamma ya fita zuwa bakin hanya tare da samu abin hawa yana zuwa suka ɗauki Dada a mota zuwa asibiti, asibitin babu jama'a sosai. Dr Hamza na zaune a Office gabansa cike da kuɗi ya kalli Dr Iliya ya ce "Kawo maganin nan ya yi mana rawa sosai, na ƙara tura saƙo zuwa ɓangaren lafiya akan magungunan da suka bayar ya ƙare, sbd cututtukan da suke damun jama'ar rugar, ina saka ran cikin satin nan za a kawo maganin" Dr Iliya ya numfasa yana jinjina kai kafin ya ce "That's good. Amma da gaske maganin ya ƙare ne?".. "No ba wani ƙare wa da ya yi, har yanzu ban bawa ko mutum ɗaya ba" cikin fahimta Dr Iliya ya kalli Dr Hamza yana faɗin "huh! za a kawo maganin sauro kyauta ma a raba, sbd yawaitar Maleriya"


"Na samu Information ɗin hakan, amma idan an kawo gidan sauron, asibitin nan za a Ajjiye mu zamu raba, so za a bawa Kowa akan 1500 each one" waro ido waje Dr Iliya ya yi kafin ya ce "baka ganin zamu iya samun matsala, tunda kyauta gwamnati ta bayar?" Ɗaga hannu Dr Hamza ya yi yana dakatar da Dr Iliya da faɗin "Hakan shi ne ribarmu, ba za mu yi musu bauta ba kamar wasu bayi, they have to pay"
Kafin Iliya ya yi magana Hamma Yabi ya faɗo office ɗin da sauri cikin tsawa Dr Hamza ya ce "Malam ya haka zaka faɗo kamar wani mahaukaci? Me ya sa duk fulanin nan baku da ilimin zaman rayuwa ne, baku san yadda ake mu'amala ba?" Hamma baya gane zancan nasu ya ce "Don Allah ka taimaki Dadarmu, kada ta mutu cikin wannan halin ita kaɗai ta rage mana, sau wajan goma ina zuwa" "Idan munje kanta lafiya zamu bata kenan? Ko zamu hanata mutuwa? Zan maka last warning Kada na sake ganin ƙafarka cikin asibitin nan, na faɗa maka bamu da maganin ko ɗaya me kake so nayi maka? Haba kuna yi mana adalci mu likitoci sai an bimu a hankali mai ya sa zan zuciyarku ya yi yawa ne?" kasa magana Hamma yai sbd Hawayen daya cika masa idanu me ya sa su Fulani ake musu kallon mahaukata wanda basu san me suke ba? Akwai wani bambanci a jikinsu wanda ya bambanta su da sauran jama'a ne? Juyawa ya yi yana zuriyarsa babu daɗi. Danejo na ganinsa ta ce "Hamma ya naga ka daɗe, numfashi Dadata zai gudu ka taimaka, ina masu bada lafiya ɗin?" A hankali ya kama hannunta ya riƙe yana shafa kanta dake ɗauke da suma mai kyau can ƙasa ya ce "Muje gida, ba zamu ƙara zuwa asibitin nan ba, Allah ya a bamu Kuɗi mu kaita asibitin burni" shiru kawai tayi tana kallonsa tare da son fahimtar abin da yake nufi a haka suka koma gida jiki babu daɗi, kwana sukai ba su yi bacci ba, Shatu kawai ta runsta sbd ƙarancin shekarunta. A daren Danejo ta sanyawa ranta zata sai da nono iya iyawarta ta tara kuɗi masu yawa akai Dada asibiti. Hakan yasa ta tashi da asuba ta tatsi kindirmo a ƙwayar gari na fara haske ta nufi cikin burni wajan Abti America.


Mother ce ke sakkowa daga upstairs kunnanta maƙale da waya idanunta sanye cikin farin glasses ta fito a Barrister Maryam ɗinta sak. A hankali ta ce "Na riga nayi reporting case ɗin, idan ba a samu good evedance ba akan wanda suka kawo ƙarar Aliyuna, kai tsaye zan maka ko wacce ƴar banza a court dama kawai nake jira" daga cikin wayar aka ja numfashi tace "Barrister Maryam kasa aje court,idan akaje to kin bawa duniya damar zata fahimci halin da ake ciki,abi komai a sannu" ɓayayyiyar ajjiyar zuciya Mother ta sauke idanunta na sauka akan Zeefa da Fattoumah "Ok za mu yi magana bari naje wajansa Allah ya sa ya yi magana, al'amarin Sheikh na bani tsoro yana bani mamaki" ƙara tattaunawa sukai kafin sukai sallama. "sannu da sakkowa mother" idanunta akan Plasma ɗin da suke kallo ta ce "Fattoumah sau nawa zan ce bana son kuna kallon zee world ne? Ashe ban isa daku ba ko?" A sanyaye Fattoumah ta ce "We're sorry Mother ba zamu sake ba" zama tayi ta ce "Change the channel immediately Mamana" Sauya channel Fattoumah ta yi zuwa Aljazeera tana faɗin "Ok Mother" kallonsu ta yi sosai ta ce "Where's Maimoon and Auta?" Zeefa ta bata amsa da "She's inside the kitchen, Auta barci take" Mother ta ce "Bana son barcin yamma taso mini ita" tana faɗin ta miƙe tare da nufar kitchen daga bakin ƙofa ta tsaya tana kallon Maimoon dake haɗa coffee ta ce "Ina Lunch ɗin Sheikh?"... "Gashi a tray mother bari na kai masa" tsareta tayi da idanu ta ce "Bani nan" tray ɗin lunch ta bawa Mother tana ci-gaba da aikin gabanta.
Haɗaɗɗan part ɗinsa ta nufa tun daga nesa ƙirar arar Sheikh Muhammad didat ta ratsa cikin kunnuwanta da Mmkin fal fuskar Mother ganin ƙofar shiga parlournsa a buɗe. Ƙamshin air-cod ya ratsa cikin hancinta. Tana shiga idanunta ya sauka akan Umar-khan dake zaune gabansa ɗauke da system yana duba wani abu, ganin Mother ya sa Umar-khan saurin miƙewa tsaye ya ce "Sannu da zuwa Mother" "Yawwa Umar-khan ina Aliyun?" Hanyar da zata sadaka da bedroom ɗin Sheikh ya kalla yana faɗin "a Parlour na samesa lokacin da nazo, ina fara yi masa magana akan wannan case ɗin ya tashi ya shige bedroom har yanzu bai fito ba" jinjina kai tayi ta nufi bedroom ɗin, babu abin da bedroom ɗin yake sai ƙamshin turarensa ROJA wanda ya a jima da kama ɗakin duk da cewa bai fiye rayuwa a cikin gidan iyayen nasa ba, yafi rayuwa a Madina idan yana ƙasa Nigeria kuma yafi rayuwa a gidan Hakimi. ba kowa nan ma a bedroom ɗin sai tsarin ɗakin da Mother tabi da kallo wanda a kullum yake Sauya mata, komai na ɗakin fari ne tas, ɓangaren clothes, shoes, perfumes. Komai daban yake. Juyawa tayi zuwa parlourn tana faɗin "Umar-khan Aliyu baya nan fa? Ko dai ya tafi gidan Hakimi?" Umar-khan yai shiru ya ce "Bashi da ikon fita, kamar kullum ƴan jaridu na waje ta ko'ina maybe yana Library ɗinsa" sai a lokacin ta tuna da Library tana zuwa ciki ta samesa zaune akan wata ƙyakkyawar kujera wacce take juya kanta da kanta ya rufe idanunsa, sumar kansa ta ɗan bayyana sbd yanayin naɗin rawanin nasa wanda ya yi da farin hirami. Hannunsa harɗe a ƙirji. Zama tayi kujerar dake kusa dashi tana kama hannunsa ta ce "Abbana Babana" ajjiyar zuciya Sheikh Aliyu Haydar ya sauke sbd jin sunan da Mother's ta kirasa da shi amma ya kasa buɗe idanunshi domin baya son ta fahimci halin da idanunsa ke ciki wanda sune kaɗai suke fallasa raunin zuciyarsa. "Buɗe idanunka mu yi magana Babana, ba zan taɓa bari kayi gidan yari ba, zan tabbatar da kai a matsayin mai gsky ba zaka wulaƙanta ba" nan ma shiru ya yi mata bai ce komai ba kamar yadda ta tsammata. Hawayen da take maƙalewa ne ya kwance mata wanda ya zuba a tafin hannun Sheikh. Da sauri ya ƙankame hannunsu dake riƙe da nata yana buɗe idanunsa a hankali wanda suka sauya daka rinewar da sukai. Fararen idanun nasa ya ɗora akanta ganin hawaye a Fuskarta ya ƙara sashi cikin damuwa amma sam hakan bai bayyana a garesa ba. "Kayi magana Babana rashin maganarka shike sawa a dinga tunanin baka da gasky, zuciyata ba zata jure ganinka haka ba" Kallonta yake har lokacin bai ce komai ba. Ganin bashi da niyyar magana yasa Mother fashewa da kuka sosai tana miƙe tsaye da sauri ya riƙe hannunta gam! Yana miƙewa tsaye jallabiya ce jikinsa mai kyau da tsada ga laushi da tsantsi. Kai ya fara Girgiza mata yana matse hannunta sosai babu abin da Sheikh yake ƙauna sama da mahaifiyarsa sai Father daga su Hakimi sune duniyarsa. Hannunsa mother ta riƙe ta ce "Try to speak Sheikh ban damu ba nasan zan fahimce ka, zamu Court bani da wani proof da zan kareka, mene gasky?" Riƙe hannun Mother Sheikh ya yi tare da fara buga ƙafa yana ƙoƙarin buɗe bakinsa. Ganin haka yasa Mother taimaka masa wajan riƙe hannunsa tana faɗin "Ahha say something, speak Babana, say it" hannunta duk biyun ya kama ya riƙe yana runtse idanunsa sai buga ƙafa yake tuni hawaye ya fara cika idanunsa. "Yee... Ƙaƙƙƙaaa... M...mmm" kai ta ɗaga masa tana shafa kansa a fisge bayan ya buga ƙafarsa da ƙasa yana saka hannun Mother a bakinsa ya ce "Babbbban akaita ba, bbbb ba zan taɓa yin yin yin haka ba mother" yana faɗin hakan yana ƙara saka hannun Mother a bakinsa duk ya jiƙa mata hannu da yawunsa mai ƙamshi a ƙoƙarinsa na ganin ya yi magana daidai waya baiwa ta Sheikh idan koyarwa zai yana samu maganarsa ta fita yake fara karatu cikin sauri baya tsayawa sai ya gama yana gamawa baya ƙara cewa komai yake fita daga hall. Wani irin rauni ya kama zuciyar Mother tausayi da ƙaunar Sheikh ya ƙara wanzuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login