Showing 75001 words to 78000 words out of 197828 words
Chapter 26 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
ta daka mata tsawa ta ce "sufa daman yaran matsiyata masu iya neman waje ba, na kusa rabuwa da masifa na huta zaki shige ko sai nayi ƙwallo dake" daga Umar-khan har Ummul suka zuba idanu. Zahrah ta kai hannu zata daki Halisa taji an riƙe hannunta cikin kakkausar murya ta ce "kada ki dakemu, ki fita sabgarmu za mu yi bankaɗar da kike ɓoyewa" Zahrah ta kalli hannun Halisa daya riƙe nata, har lokacin kan Halisa a ƙasa yake cikin ɓacin rai Zahrah ta kifawa Halisa mari, wani irin ihu Halisa ta fasa wanda kai tsaye ya sauka har kunnan Yaa Sheikh dake sauya kaya. Gaba ɗaya tai kan Zahrah kamar mahaukaciya duk girman Zahrah sai da Halisa ta kai ta ƙasa tare da hayewa kan cikinta ta dinga dukanta da ƙarfi cikin ɓacin rai. Naushin da akaiwa Zahrah a ciki yasa ta fasa ihu tana neman taimako tare da kiran sunan Yaa Sheikh. Al'amarin ya yi wa Ummul daɗi Umar-khan kam gyara zama ya yi ya ce "wannan faɗan yafi ƙarfin sa" Yaa Sheikh ya jima da fitowa amma yaƙi ƙara sawa, sosai Halisa ta birkice tana ihu tana dukan Zahrah ta yaƙoshi "Please My Excellency zata kashe ni ka taimaka mini wallahi mahaukaciya ce, ba ƙarfin ta bane" wata dry ta ƙwacewa Umar-khan ya kifa kai a armchair ya dinga dry yana buga ƙafa.
A hankali cikin nutsuwa Yaa Sheikh ya ƙarasu tare da saka hannu ya ɗauke Halisa daga kan Zahrah, nan fa ta shiga kokawa daga hannunsa zata ƙwace ya riƙeta sosai yana faɗin. "Meye haka? Ni za aiwa ƙaddama?" Ta girgiza masa kai sai kawai ta faɗa jikinsa tare da ƙanƙame shi tana sakin wani irin kuka jikinta duk rawa yake, gashi kanta harya fashe idanunta ya juye tausayinta ya kama shi. Gabaɗaya ya manta da wata Ummul a wajan bare kuma wani Umar-khan ya riƙeta sosai a jikinsa.
Zahrah ta dafe cikinta ta ce "My Excellency kalli zata kasheni amma ita kake taimakawa?" Umar-khan ya ce "Haba matar Yaa Sheikh ba kiga ita kamar ba yin kanta bane, taimako kika nema gashi nan kuma ya ɗauketa, ai Malam shi ne taimakon dani da Ummul babu mai iya tunkarar Aljanu" kasa miƙewa Zahrah tayi wani irin nishi take kamar mai naƙuda mararta na riƙewa ta ce. "Wallahi dole ta koma gidan ubanta ta tafi can Rugar su" Umar-khan ya ce "Ruga kuma? Ba ƴar uwarki bace meye haɗinta da Ruga?" Zahrah ta ce "Ruɗewa nayi, gida zan mayar da ita" Yaa Sheikh dai ya ɗauke ƴar amanar shi ya nufi Library room da ita. Umar-khan ya miƙe daman yazo akan batun zakkar da Yaa Sheikh ɗin zai raba sbd zuwan Ramadan. Ummul ma ta nufi kitchen ranta fes.
A daddafe Zahrah taja jiki zuwa part ɗinta tana shiga jini ya ɓalle mata a rikice ta kira number Deen yana ɗagawa ta fashe da kuka ta ce.
"Na shiga uku Deen kamar haihuwa zanyi ko bakwaini?" Ta cikin wayar ya ce "Haihuwa kuma?" Tai masa bayanin komai. "How many times zan ce ki daina shiga sabgar yarinyar nan? Kina son rusa mana plan nan ko?" Nishi Zahrah take sosai jini na fita a jikinta ta ce "ba wannan ne matsalar ba, yarinyar kamar tana da Aljanu kuma tana iƙirarin zata tona mini asiri, ga yadda Yaa Sheikh yake nuna kulawa gareta ya fara bani tsoro ina son mijina" Deen ya buga mata tsawa ya ce "Ni ki ke faɗawa kina son mijinki? Me kike nufi?" Ta ce "ina nufin abin da nace mana Deen, wallahi ina son Aliyu ba zan iya rabuwa da shi ba, duk abin da ka ke nema zan maka amma banda rabuwa da Yaa Sheikh" Deen ya furzar da Iska yama rasa me zai ce. "Kisan yadda zaki ki fito yanzu na kai ki asibiti idan ki ka haihu a gidan ko ki kai ɓari ba ruwana" yana faɗin haka ya kashe wayar, a daddafe Zahrah ta shirya bayan ta saka pads da tsumma bata tsaya jiran komai ba ta nufi wajan bisa umarnin na Deen ɗin, Address ɗin daya bata tafi ta samu motar shi a gefe guda tana zuwa ta zube a ƙasa, Deen ya ɗauketa zuwa mota suka nufi asibiti..
_2hours Left_
Deen ne zaune a gaban a gaban Dr ya ce "kana nufin kace cikin dake jikin Zahrah ya zube?" Dr ya ce "haka ne, duk yadda muka so dakatar da cikin mun kasa, sai dai hqr" Deen ya dafe kai gaba ɗaya plan ɗinsa ya ruguje ya ce "Amma Dr kwanaki munyi ƙoƙarin cikin ya zube, wani Dr ya ce ba zai taɓa zubewa ba" Dr ya gyara zama ya ce "Anya? Sai dai idan baya so ya zubar da cikin, amma cikin ƙaramin lokaci za a iya zubar da cikin" Deen ya yi shiru idan haka ne akwai wanda yake son yaga Zahrah ta sha wahala ko ya tuna mata asiri. "OK Thank you" yana fita ya ƙarasa ɗakin da Zahrah take, ita kanta Zahrah ta rasa me zatai farin ciki ko ɓacin ciki? Kuka ko dry?. Sai dare aka sallameta Deen ya kawota har ƙofar gida ta lallaɓa ta shiga. A hankali yake tafiya yana tattare Alkyabbar jikinsa dawowarsa kenan daga sallar Issha kai tsaye kuma part ɗinsa ya nufa, kwana biyu yana stressed kansa sosai, yana buƙatar yaje Nigeria kafin zuwa Ramadan shi ya sa yake ƙara takura kansa. Yana shiga bedroom yaji ta rungomesa ta baya ta ce "Abbana sannu kaji" ya jawota gabansa idanunsa akan bakinta ya ce "Sallah?" Ta ce "Nayi Abba, Darasi zaka bani" yana da ayyuka amma dole ya ware lokaci ga karatun ta. Akan table ya zauna itama ya nuna mata waje ta zauna, littafin Fiqhu ya buɗe ya ce.
"Nutsu sosai, abu mai muhimmanci ne" ta miƙe tsaye tare da dawowa wajansa ta zauna saman cinyarsa ta ce. "Abba zanfi ganewa haka" ya ɗauke idanu ya lura kwana biyu taiwa jikinsa kyakkyawan sabo, hannunsa ya zura ta ƙasan nata hannun ya ɗora kansa a wuyanta a hankali ya sauke numfashi cikin nutsuwa ya ce.
_“Babin dake bayani akan abubuwan da suke ja ayi wanka”_ zata juya ta kalle shi ya sakar mata nauyin kansa ya jima a haka kafin ya ce.
"Abubuwan dake jawo wankan Janaba, wanka ɗaya ne, amma ya kasu kashi kashi, ko wanne kuma akwai dalilin dake sawa ayi, idan nace Janaba ina nufin najasa" ya yi shiru yana lura da Yadda ta nutsu tana bin duk inda ya nuna da hannu da idanu. A hankali ya ɗora da cewa.
"Fitar maniyyi a cikin bacci, ko a farke, daga namiji ko mace, ta hanyar lafiya da jin daɗi, saboda hadisin da ya ce, “Idan ruwa ya fita a yi wanka.” Wato idan ruwan maniyyi ya fita, a yi wankan janaba" ya ƙara yin shiru na wani lokaci kafin ya ce.
"Idan mutum ya yi mafarki yana saduwa da mace, amma da ya farka babu alamar fitar maniyyi, babu wanka a kansa. Idan mutum ya yi mafarki yana saduwa da mace, bayan ya farka sai ya ga maniyyi a jikinsa, wajibi ya yi wanka. A nan ana nufin ko da kayi mafarki kayi mu'amala mace kuma baka fitar da komai ba, to wanka bai hau kan mutum ba, idan kuma akasin hakanne dole ai wanka" ya saurara da maganar ya ce.
"Kin gane?" Ta girgiza kai ta ce "Wallahi Abba ji kawai nake ni wannan karatun bana ganewa, sai abu ɗaya naji kana faɗa wai Mani..." Ya jima yana kallonta yama rasa ta ina zai ɓullo mata ya numfasa kaɗan ya ce.
"Bakin ce ke matata mace? To idan nayi mu'amala dake ake nufi mu'amala ta aure" ta tuntsire da dry ta ce "Ina ji ci-gaba" ya murmusa a ɓoye ya ɗora da cewa.
"Idan mutum ya tashi daga barci sai ya ga maniyyi a jikinsa, amma bai yi mafarkin saduwa ba, wajibi ya yi wanka, saboda samuwar maniyyi a tare da shi, wanda fitarsa ne yake jawo wanka" tayi saurin kallonsa ya ware mata idanu sosai ta ce.
"Abba to kai ma ka gani dana kwana tare da kai" tambayar ta Girgiza tunaninsa bai tunanin cewa tana ganewa ba, sai kawai yai mata shiru ta juya gaba ɗaya suka fuskanci juna ta ce.
"To gsky misali zaka bani idan ba haka ba, ni bana gane karatun naka Malam" a taushashe ya ce "ban gani ba" ta ce "To sbd me? Kai mafarkinne ba kayi ko me?" Ya numfasa sosai tare da ajjiye littafin ya riƙe fuskarta a hankali ya ɗora tashi fuskar saman tata, ya kama hannunta ya ɗora saman gemunsa suka kalli juna a hankali kuma ya sauke idanunsa akan ƙaramin bakinta ya ce.
"Sbd da kwaila na kwana...
Paid book
500
08119237616"Mene kwaila?" Ya yi shiru zata sake magana Yaa Sheikh ya sanya hannu tare danne bakin a hankali ya ce "Shhhhh shiru" dole tai shiru badai ta rasa abin faɗa ba. Yaci gaba dayin karatun cikin salo da nutsuwa yadda zata fahimci komai ta kuma gane abin da yake magana akai. Ya lura kuma tana ganewa duba da yadda tayi shiru, bayan sun kammala Halisa ta kalli Yaa Sheikh dake murza hannunta ta ce "Yaa Sheikh ya zan gane wankan janaba ya hau kai na?" Da hannu ya nuna ta kawo kunnanta tayi saurin miƙa masa kunnen ya ɗora bakinsa ya faɗa mata magana tayi saurin kallonsa tana zare ido ya ɗaga mata gira ya rungometa sosai a jikinsa a taushashe ya ce "Zaki Albarka, tare da zuri'ar ki" Halisa ta kalle shi ta ce "Yaa Sheikh"
Yaƙi magana ta ce "Yaa Sheikh mun gama darasin?" Ya ɗaga mata kai tare da cewa "Sai wanda zaki ban" tai murmushi tana son ganin idanunsa amma yaƙi yarda ta gani sbd juyewar da sukai "Yaa Sheikh me ya sa ake son kashe ka? Kuma ina gani kana kuka cikin barcina kana cewa na taimaka maka ni kuma inaƙi" Ya dubeta yana nazartar maganganun nata kafin ya ce "Kina son sanin sirrin Abbanki?" Ta ɗaga masa kai alamar eh ya riƙe fuskarta yana ɗora tasa kai ya ce. "Mafarki ƙarya ne, wani lokacin gsky ke kam naki ba daidai ba ne" buɗe baki tai zatai magana ya sakar mata wani hot kisses a lips ɗinta idanunta cikin nasa al'amarin ya girmi tunaninta ji take tamkar ba Yaa Sheikh ɗinta ba, wani irin sahihin abu yake mata ta kasa jure al'amarin hawaye ya shiga gangaro mata ganin ƙirjinta na ɗagawa tana riƙe hannunsa sosai ya yi saurin sakinta tayi luu zata koma baya ya yi saurin dawo da ita zuwa jikinsa..
El-bashir ne tsaye a gaban motarsa idanunsa sanye cikin Sunglass ya zuba hannun a cikin aljihu, farar t.shirt ce a jikinsa sai wandon uniform na ƴan sanda. Ya daɗe tsaye a inda yake kafin wani saurayi ya ƙarasu wajan yana sarawa El-bashir ya ce "Mun gama dukkan wani binciken da muke a Company amma babu wata hujja dake nuna an zuba haramtattun kaya a kamfanin sarrafa shinkafa na Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu" El-bashir ya jinjina kansa ya ce "Okey, kaci gaba da saka idanunka" Yasir ya ce "Amma sir ga shawara, mai hana kabi ta wata hanyar kai ka zuba hudar iblis cikin kayan nasu, tunda na samu labarin kayan nasu yana gab da shigowa, idan har aka kama kayan kamfanin sarrafa shinkafar dole sai an nemi shugaban kamfanin kaga a nan ka jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, ka kai Yaa Sheikh gidan yari, kuma ka ɓata masa suna tare da lalata kamfanin baki ɗaya" El-bashir yai shiru a hankali kuma ya juya ya shiga mota yana cewa "I'll think about it" El-bashir yana son privacy life shi ya sa bai fiya fita da wasu securities ba, infact ba kowa yasan abin da ke zuciyarsa ba. Burinsa bai shige yaga bayan Yaa Sheikh har ƙarshen rayuwa ba. Direct masarauta ya nufa, yana buɗe ƙofa yaci karo da Khalil wanda ya fito daga ɓangaren Mai martaba. "Am glad you are here, yanzu nake shirin kiranka Mai martaba na son ganinka" El-bashir ya ce "Ok tom" har ya yi gaba Khalil ya ce "hold on, nayi maka magana baka ɗauki abin serious ba ko El?" El-bashir ya jingina da jikin mota yana kaɗa key ya ce "Maganar me kenan Yarima? Na manta fa" Khalil ya ce "Maganar yarinyar da nace kuna kama sosai, kamar ya ɓaci fiye da tunanin mutum shi ya sa abin ya tsaya mini rai" El-bashir ya kalli yayan nasa da kyau yana sakin murmushi ya ce "Na kasa fahimtar me kake nufi Yarima, i don't even have a wife balle nace ita ta haifa mini yarinyar har muke kama, kuma dai nasan kaf cikin masarauta ba wanda ya haihu ɗan ya ɓata right? Infact banga wata kama ba"
"Amma mu ai munga kamar ko? Da Fulani Atine za taga yarinyar ina da yaƙinin zata tai tunanin abin da nake tunani" El-bashir yai gaba abin sa ya ce "Ai shikenan, ni wannan kamar bata gabana" Khalid yai murmushi yana ganin gabaɗaya akwai sauyi a rayuwar El-bashir ɗin. Daga nan ɓangaren Mai martaba El-bashir ya nufa, kasancewar baya cikin fada yasa damai bai tunanin zuwa can ba. Yai tsaye har sai da akai masa iso kafin ya shiga ƙawataccen parlourn wanda ya sha ado da kayan sarauta kala-kala. Da mmki El-bashir yake kallon Abba Hakimi yana tunanin mene ya kawo shi garin a wannan lokacin? Ko abin da yake tunani ya faru ne?. Ya nemi waje ya zauna yana faɗin "Barka da hutawa Daddy, Allah ya ƙara girma" Mai martaba Ahmad Sarki ya sauke numfashi kafin ya kalli Autan ɗan nasa ya ce "Mubasshir ka shirya dai?" El-bashir ya ce "Dady ina? Akwai aiki habaka" Mai martaba ya yi shiru na wani lokaci kafin ya ce "Aikin hajji, ina son ziyara tare da miƙawa Ubangiji buƙata tuna, Khalil ya kammala komai jirgi zai ta shi gobe" El-bashir bashi da ra'ayin zuwa aikin hajji wannan shekarar baki ɗaya amma hakan kamar wata dama ce a gare shi. Abba Hakimi daman yasan ba lallai El-bashir ya kulasa ba, kamar yadda baya kula Yaa Sheikh ga mmkinsa sai yaji ya ce. "Barka da hanya Abba Hakimi" Abba Hakimi ya yi murmushi irin nasu na manya kafin ya ce "Allhmd Mubasshir" El-bashir ya ce "Yaa Sheikh lafiya yake dai ko?" Ba Abba Hakimi ba hatta Mai martaba sai da ya kalli El-bashir. "Kaji ance bashi da lafiya ne?" Ya girgiza kai Mai martaba ya ce "A gidan shi zamu sauka kafin fara aikin hajji, naji ance shi ne zai jagorancin sallar Taraweeh da Tahajjud a masallacin ka'abah" El-bashir ya miƙe ba tare daya ƙara cewa komai ba, gabaɗaya suka bi bayan shi da idanu.
"Ina tunanin amsar Halisa daga hannun Yaa Sheikh, ba zan iya bari tai shekara guda ba" mmkinsa maganar Abba Hakimi ya kasa ɓoyewa daga kan fuskar Mai martaba sai daya ja numfashi cikin tarin martabawa da bawa Abba Hakimi girman na shi ya ce "Don me ya sa?" Abba Hakimi ya ce "Don ya magantu, ina sanin ina alƙibilar Aliyu take akan aure dama mace baki ɗaya, ka sani na sani Aliyu kaifi ɗaya ne, ba a taɓa sauya masa tunanin dama shi ne a kwakwalwar shi ba. Lokaci yana shigewa shekaru na ƙara girma a tare da Yaa Sheikh, ban san ina tunaninsa yake ba, ban san mene tsarin shi ba, amma a wannan karan ba zan zuba masa idanu ba, ina da yaƙini da kuma tabbacin Yaa Sheikh ba zai saurari Zahrah Farouk ba, ina son saka masa soyayyar Halisa ko ta halin yaya" Mai martaba ya jinjina kai yana mai jin cewa gasky Abba Hakimin ya faɗa. "Hakan yana da kyau" Abba Hakimi ya ce "Da zarar an kammala aikin hajji ka tawo mini da ita, nasan ba zai ce komai ba" tattaunawa sukaci gaba dayi.
El-bashir na fita ya nufi sashin Fulani Atine ya sameta ita da tarin kuyanginta bayan sun fita ta kalle shi ta ce "Sarkin gobe na Wannan masarauta ya akai ne?" Ya tura hannunsa cikin sumar kansa tare da fesar da Iska mai zafi sai kawai ya juya kamar wanda mayan ƙarfe ke janshi.
"Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba aje ba. Ko yanzu goma ta faɗi tafi biyar albarka, sahun giwa kuma ya zarce na raƙumi, ƙadangaren bakin tulo ban fito ba sai dana shirya ja muje zuwa El-bashir Ahmad Sarki" Fulani Atine ta faɗa tana sakin wata dariya ita kaɗai. Kafin ta sanya ai mata iso da Jakadiyya. Fulani Balaraba tana ɓangarenta babu mai jin kanta daga ita sai ɗan ta Khalil Ahmad sarki suke mu'amala.
Iska mai ƙarfi ce ta mamaye cikin dokar dajin da suke, kafin wani kuka da ihu mara daɗin saurare ya maye gurbin iskar. Wata kururuwa Prince Bilal ya saka bakinsa na fitar da hayaƙi cikin jin daɗi da farin ciki, murya mara daɗin Amo! Ya ce.
"Sandu kayi ƙoƙari ban taɓa zaton matata zata kasance a Madina, ka tabbatar ita ce?" Sandu ya ɗaga fikafiki yana shawagi a sama ya ce.
"Naga zoben a hannunta, na ganshi ta fito daga makaranta ita ce" Prince Bilal ya ƙara sakin dariya ya ce "Lokacin ya yi da zan nunawa wancan Bil'adama ɗin bai isa ba, bashi da ƙarfin ikon da zai rabani da matata a karo na biyu, idan a lokacin baki da iko yanzu ina da ikon da bai isa yaja dani ba" Sandu ya yi dry sosai har lokacin shawagi yake a sama ya ce "Da tuni na ɗakkota zaren dake hannunta yasa bani da ikon tunkararta" Prince Bilal ya ƙara kwarara ihu wanda ya ƙara hargitsa dajin da suke ciki farin ciki mara misaltuwa yake ji a ran shi ya ce "Zani, zani lallai zani idan har Ramadan ya zo bana da iko ko kaɗan dole naje yanzu" yana faɗin hakan yabi iska ya ɓace.
Wajan sati biyu kenan da shan poison ɗin da tayi, taji sauƙi sosai ta koma makaranta, sosai take fahimtar karatun da har malamai take bawa mmki ɓangaren Yaa Sheikh bai saurara wajan bata karatun addini ba, musamman karatun Alkur'ani. Al'amarin da yake bashi mmki duk yawan karatun Alkur'ani da zai mata ba, nan take