Showing 72001 words to 75000 words out of 197828 words
Chapter 25 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
shawo kan rigimar ta ce "Abba kai ma ka iya?" Ya zauna bakin gado yana ɗorata akan cinyarsa ya ɗan kalli time yaga goma ta kusa.
"Kin taɓa ji ne?" Ta ɗaga masa kai ta ce "Kamar dai" tai shiru alamar tunani da sauri ta ce "Abba na tuna, wani na manta sunan mai rufe fuska shi ne yake yi mini a Rugar Rome" ya ɗauke kai yana mai sassauta fuska kamar wanda murmushi zai ƙwacewa. Ya gyara mata zama tare da zagaye bayanta ya ɗora kansa a wuyanta tattausan gemunsa na gogar fatar wuyanta ya ce.
"Duba can?" Ya nuna mata direction da hannu idanunta ya sauka akan wani photo a prame photon baby girl ne zata iya yin 10 mnts da haihuwa, idanunta rufe sumar kanta har gaban goshi. Anyi wani rubutu kala biyu ɗaya da hausa ɗaya da turanci.
_“Angel my world”_ shi ne abin da aka rubuta da turanci da larabci kuma aka saka _“Ƴar Aljanna Mrs Aliyu haydar Aliyu”_ yanayin yadda aka tsara photon zaka san cewa ana matuƙar ji da shi, ta juya ta ce "Abba wace?" Ya shafa kanta da hannunsa har lokacin fuskarsa na kifa a wuyanta yana murza mata sajansa mai laushi ya ce.
"Zaɓin Allah, matar ƙwarai, hasken zuciya" nan da nan yanayinta ya sauya ta ce "Abba nifa? Da gaske baka so na?" Ya ware bakinsa kamar zai magana sai kuma ya fasa Halisa tau saurin sauke numfashi jin tongue ɗinsa a skin na wuyanta yana yawo. "Baka so na Abba?" Ya buɗe ido tare da ɗagowa baki ɗaya. "Kina so a soki ne?" Ta ɗaga masa kai ya numfasa tare da kwantar da ita yana sauke mata numfashi ya ce.
"Ban son ina kwana, every morning come and Peck my cheeks, left and right, shi ne gaisuwar" ta ɗaga masa kai. Duk sukai shiru can ya miƙe ya bisa da idanu.
Kai tsaye sashin Ummul ya nufa Ummul na ganinsa ta miƙe tsaye ita kanta kwarjinin Yaa Sheikh rikita ta yake haibarsa da kamala har sun yi yawa.
"Ya jikin nata? da sauƙi dai? ta faɗa maka wanda ya bata gubar" Ya juya yana yin wace ya ce.
"Allhmd. Ba buƙata" daga nan ya nufi Library ɗinsa, yaci gaba da rubutun Alkur'anin da yake da ka, wanda yake son ya zama cikakken kafin zuwan Ramadan da shi zai amfani wajan yin tafsir. 1:00 ya tashi bayan ya tabbatar komai lafiya yake, ya watsa ruwa tare da yin alwala. Sallah ya gabatar sosai ya zauna zaman azkar sai 2:30 ya shirya cikin fararen kayan barci ya fesa turare ya nufi duguwar kujera tare da duvet ya kwanta, daga ina yanke ya hangota sai barci take numfashi na sauka a hankali gabaɗaya ta kwaɓe fuska.
"Rigimammiyata" ya furta a fili yana rufe idanu. Cikin dare sanyin zazzaɓi ya takura mata da wani irin ciwon kai sosai kuma duk yana cikin matsalar da gubar ya haddasa mata, ta yayar bargon da take ciki kai tsaye idanunta ya sauka akan Abban nata ta nufi kujerar tare da hayewa saman shi ta zagaye hannuwanta ta riƙesa sosai kanta a ƙirji nan take barci ya sake ɗauketa. Ba barci yake ba yana jinta kuma dama ya san dole zata ta shi yaja bargon ya rufesu tas sai a lokacin barci ya ɗauke shi.
Duk yadda ya makara a kwanciya hakan bai hana shi tashi tun kiran sallar farko ba. Ya buɗe bakinsa ɗauke da addu'a a hankali ya yunƙura zai tashi yaji an ƙanƙamesa, ya kai idanunsa zuwa jikinsa ya sauke numfashi tare da komawa ya kwanta gaba ɗaya ya manta a jikinsa ta kwana, gently ya miƙe da ita yana ji tana riƙesa tsoran kada ta faɗi a haka ya kwantar da ita saman bed tare da rufeta da duvet yana matsawa ta mirgina tare da cire duvet ɗin a haka taci gaba da barcin.
Cikakken wanka ya yi tare da ɗaura alwala ya shirya cikin embrodiery Islamic jallabiya jikinsa sai fidda ƙamshin Nivea Men Active Clean Shower Gel, ƙafarsa sanye cikin Scuff faux-shearling slippers ya nufi fita daga gidan zuwa Masjid sai baza ƙamshi Roja yake. Sai da ya gabatar da raka'atul fjr kana yaja jam'i cikin daddaɗar muryarsa cikin makarijul huruf da fidda hakƙin tajwid yake karatun. Ana idarwa ya fara gabatar da karatu wanda ya kasance da mutane da yawa, ya ɗago kai tare da kallon mutanan kana ya bayar zuwa ga littafin dake gabansa a taushashe ya ce.
_“ Babin da yake bayani akan tilasta mace zuwa ga shimfiɗa bada yarda ta ba, a turance kuma Sexual violence”_ ya gyara zama sosai gaba ɗaya larabawan wajan sukai shiru suna sauraran abin da zai ce. A hankali ya ce.
7:00 ya shigo gidan bayan ya biya ta wajan tsuntsayensa, daman yasan ba zai samu kowa a main parlour ba. Kai tsaye part ɗinsa ya nufa da mmki yake dubanta tana kwance saman prayer kar sai gyangyaɗi take. Ya nufeta bai ce komai ba taji an ɗagata sama tayi saurin buɗe idanu suka kalli juna sai kawai tai murmushi mai kyau tana kwantar da kanta. Bayan ya sauketa saman bed ya ce.
"Sanyi sai kama ki, a daina kwanciya ƙasa" ta ɗaga masa kai tare da faɗin "To Abba makaranta fa?" Ya tsare ta da idanu kafin yai magana wayar shi ta gida ta fara ringing ya miƙe tsaye a hankali ya manna wayar a kunnansa. Umar-khan dake kan layi ya ce.
"Barka da safiya Yaa Lee, ya mai jiki? Ummul na neman iso na shigowa sashin naka" "Uhm" ya ce yana ajjiye wayar. Babu jimawa Ummul ta shigo hannunta ɗauke da babban tray.
"Barka da safiya, ya jikin nata?" Yana zama kan kujera tare da naɗe ƙafarsa ya ce.
"Mun tashi lafiya?" Ta ce "Allahamdulillah, Ya jikin ƴar Abba" Halisa tana daga kwancan ta ce "Naji sauƙi Ummul, tambayi Abba kiji shi ne ya ɗaukeni yanzu kuma a jikinsa na kwana" kamar ƙasa ta tsage ta shiga haka Ummul taji kunyar Yaa Sheikh ta kamata Halisa ta ƙara cewa.
"Ummul Abbana ɗan gayo ne ba kiji bakinsa ba..."
"Ya isa haka, yau naga takai ne ni Ummul" Halisa ta juya za taiwa Yaa Sheikh magana amma ko inuwarsa babu a bedroom da alama ya daɗe ta ficewa tun da yaji abin kunyar da take neman haɗa shi da ita. Ummul sam batai wani mmki ba, ita juriya da haƙurin Yaa Sheikh kawai take gani.
"Ƴar Abba ba komai ake faɗa ba, shi aure sirri ne, duk abin ya faru ki barshi a ranki, kinji?" Ta ɗaga mata ta ce "maza sha tea kinji?" Ta maƙale kafaɗa ta ce "Modibbona zai ban kije kawai Ummul, kuma me ya sa ki ka daina cewa matar malam?" Ummul ta ce.
"Because he's no longer your husband" tana faɗin haka ta fita. Ita kuma Halisa sam bata gane ba. Tana fita Yaa Sheikh ya fito daga bathroom suna haɗa ido da Halisa ya watsa mata harara ita dry ya bata ma.
Zahrah na tsaye ta kafe Ummul da idanu tana tirketa da manyan tambayoyi. "Ina ƴar aikina take, ya zama last question da zan miki" Ummul ta ce. "Bata jin daɗi, a part ɗina ta kwana" Zahrah tai shiru sai kuma ta ce "Muje akwai aikin da za tayi mini yanzu?" Ummul ta ce "Bata lafiya fa?" A fusace Zahrah ta ce "And so what? Ke rashin lafiyarta ya dama" Ummul ta ɗauke ta ce.
"To Umar-khan ya tafi kai ta asibiti" yaja tsaki tare da juyawa ta ce "Bari naje wajan Yaa Sheikh ɗin naji wanda ya bada lasisin yiwa ƴar fillo abu ba tare da izinina ba" Ummul tai bedroom ɗinta da sauri ta kira Umar-khan ta ce.
"Ka kira Yaa Sheikh yanzu ga matarsa Zahrah nan zuwa, kasan Halisa na wajansa" tana faɗin hakan ta kashe kiran.
Kiran telephone line ya tsayar da Zahrah daga tafiya part ɗin Yaa Sheikh, ta ɗaga kiran tare da cewa "Hello" Jadda dake bisa layi ta ce "Waye ne za a fasa mini kunne kamar yaƙi?" Zahrah taja tsaki a ranta ta ce "Matar Aliyu mana?" Jadda ta zabga Salati ta ce "Yaushe Gadanga ya yi aure kuma?" Zahrah ranta ya ɓaci ta ce "matarsa Zahrah" Jadda ta ce "Uban meye kuma Zahra? A to Allah ya isa ban yafe ba maganar da nayi dake, maza maza mutum nake nema bake ba don Allah, kije kiji da Iyaye abu a kwance kamar tawul ɗin wankan mai jego" wani kyakkyawan tsaki Zahrah ta ja. Tamkar Jadda ta fasa wayar haka tayi ta ce "Uwarki ki kaiwa tsaki, ai sai yanzu na tabbatar Gadanga bai aure mace ba, mai siffa irin ta fir'auna da ƙaruna, baki kamar maliya tayi ambaliya" kashe wayar Zahrah tayi baki ɗaya tsanar mata ya ƙara zama daram a zuciyarta.
Ko sallama ba tayi ba a haka ta shiga part ɗin Yaa Sheikh, a tsaye ta gansa ya baza Alkyabba sai ƙamshi yake zabgawa wani irin kyau ya yi mata wanda bata taɓa ganinsa ba, ya ƙara girma da faɗi.
Ta sauya tafiya tana kaɗa jiki cike da kissa ta nufesa tana zuwa ta ce.
"My Excellency, you look good kayi kyau sosai" ta rungumesa ta ce "I love you husband" ya buɗe ido yasan daman babu gaisuwa a tsarinta. "Yaushe zaka bani damar zuwa sashinka na tayaka barci? Na fara gajiya kawaici na ya ƙare ina buƙatar mijina" sai a lokacin ya kalleta sosai a hankali ya ce "Sanda ki ka shirya" zata sumbaci bakinsa taji kamar wani abu yana yi mata yawo a jiki ta ɗan motsa ta ce "Uhm daman nace a daina fita da ƴar aikina ba tare dana sani ba, kuma idan da hali ta kwashe kayan zuwa sashen masu aikin gidan nan" ta zabura sbd abin da yake ƙara bin jikinta gudun kada ta bata kanta a gaban Yaa Sheikh tayi saurin cewa "I'll be back" ya lumshe idanun tare da buɗewa tai saurin ficewa.
Wani irin fisgar numfashi ya yi jin yadda ta riƙesa sosai ta baya, gaba ɗaya ta jiƙa masa bayan riga ta bakinta. Ya saka tattausan hannunsa tare da fito da ita waje daga cikin Alkyabbar jikinsa.
Ya dubeta ya kalli hannunta brush ne wanda ta wanke baki ta tura baki ta ce.
"Ji nayi tana cewa zata kwana dakai fa Abba shi ya sa" wato ita ta kuri Zahrah?.
Ya juya zuwa bedroom har lokacin jikinta baƙwari sosai suna zuwa taga ya jawo Injection yana zuƙar ruwa gabanta ya faɗi sosai. "Allah sarki Abbana waye babu lafiya kuma?" Da ace dry halinsa ne babu abin da zai hana shi yi ya juya ya ce. "Ƴar fillo" ta haɗiye yawo ta ce "A'a wallahi lafiya nake,don girman Allah Abba kada kayi mini don soyayyarka da Annabi wlh banso" ganin ta gaske yi mata zai ta kwasa zata gudu ya damƙota tare da zama da ita akan cinyarsa ya ce.
"Shhhhh, ina gaisuwata?" Ya faɗa yana ajjiye allurar gefe ɗaya. Ta sauke numfashi ta ce "Naji tsoro ashe bani za aiwa ba" ya dai bita da idanu a hankali ta saƙalo wuyansa tare da ɗora bakinsa a kumatunsa, ta sakar masa kiss ya saka hannunsa a bayanta tare da yin ƙasa da trousers ɗin jikinta, idanunsa cikin nata a haka ya ɗauki Injection. Halisa tai murmushi tana ƙara yi masa kiss a kumatu shi kuma ya saita Injection ɗin a jikinta. A hankali ta dawo bakinsa sai kuma ta fasa ta ɗaga idanu tare da kallon Yaa Sheikh ta ce "Abbana ina son ka" a karo na farko ya sakar mata murmushi wanda yasa ta zuba masa idanu kamar bata taɓa ganinsa ba, ya sumbaci goshinta ya ce.
"I na... Ina.." tai dry ta ce "Yawwa Modibbona ni ma kace kana so na" ya ɗora tsinin allurar sosai a jikinta ya ce "Ina.. ina son" bai ƙarasa ba ta ce "Ina son k....," wani ihu ta fasa daidai lokacin daya tsira mata tana ƙoƙarin sakin kuka ya kame bakin kukan da nasa bakin ya rungometa sosai a jikinsa...
Paid book
500
08119237616
Allah ya nuna mana Monday ai weekend lfy🥱*_A jiya da France sunci ƙwallo tabbas da littafin IDAN BA KE free book zai dawo. Wannan yaron Mbappe ajin tsoran gabansa, ko yanzu ya jijjiga zuciyar Messi. Wlh ban taɓa zaton Argentina zasu ɗauki cup ba👉🏾🏆.Mufa har gobe CR7 shine real GOAT kuma kowa yabi idan Ma ba kabi ba anbima eheeennnn...dama tun farkon wasan Saudi Arabia dA Argentina muka gano FIFA Messi suke so yaci world cup, then lokacin dA muka bata na kallan world cup ɗin nan bamu yafeba wuta bal bal😏_*
Haɗiye kukan nata tayi, Yaa Sheikh yabi duk wata hanya da yasan zata iya yi masa rigima ya toshe ta. Tai shiru tana sauraran sabon lesson ɗinsa gently ta buɗe ido kai tsaye suka haɗa idanu ya zame fuskarsa baki ɗaya still holding onto her "Abba kayi mini wayo" ya girgiza kai hannunsa cikin sumar kanta yana shafawa ta ƙara tura baki ta ce "Munyi faɗa, Allah sai na faɗawa Ummul kuma fa Allurar bafii wayyo Dadata" sai a lokacin ya dubeta murya bata fita sosai ya ce "Zaki samu zunufi, a daina kiran faɗa" ta kwaɓe fuska ta ce "Abba bakai bane? nace banso banso kayi mini" ya riƙe fuskarta yana gyara mata zama a cinyarsa ya ce.
"Idan baki so me kike so?" Ta riƙe dugun gemun shi tana ya motsawa idan ta kitsa sai ta ware ko ta murmuɗe, duk da zafin da yake ji amma bai kulata ba ta ce "Modibbona nake so, Abba ka siya mini nagge kaji?" Ya buɗe ido sosai ta langwaɓe kai tana shafa lips ɗin shi ta ce "Don Allah Modibbona, an ƙwace mana Naggenmu wanda Baffa ya bar mana, wai ana bin Baffa kuɗi shi ne Sarkin ruga ya ƙwace, kuma ma ai kayi mini al'ƙawari ko?" Shi dai bakin maganar yake kallo yana mmkin yadda bata gajiya da surutu, banda ya riga ya tsara yadda karatun ta zai kasance a zuciyarsa da bbu abin da zai hana ya juya akalar karatun zuwa Mass communication.
"Ni ka siya mini nagge irin na Rugar Rome kaji Abba" ya riƙe hannunta daga kan gemunsa idanunsa cikin nata ya ce.. "surutun ya ƙaro fiye da baya, ki sassauta mini" ta ce "To kace zaka siya mini mana" ya juya kai tare da ɗaukan cup ɗin shayin da Ummul ta kawo ya kai bakinsa zaƙi da garɗin zumar dake ciki ya ratsa cikin kunnensa sai da ya gama shanye na bakinsa ya ce.
"Kada ki damu, Abbanki nada garken nagge masu yawa" tai murmushi ta ce "Abba ina suke zaka kai ni na gansu?" Ya numfasa ya ce "Je Rugar Bello ki tambaya, ban son surutu karatu za ai ok?" Ta ce "To Abba" domin ta lura da sauyin fuskarsa ya kame ta sosai babu wasa, ya lura tsaf zata sanya ya faɗi abin da bashi kenan ba, tana son ya yi ta surutu kamar yadda bakinta bai gajiya. Miƙewa ya yi ta biyo bayansa a hankali sai da yaje bakin ƙofa ya tsaya tare da juya yaga ta sunkuyar da kai ƙasa taƙi kallonsa.
Ya ɗauke nasa kan tayi saurin cewa "Abbana cikina ciwo" cak ya tsaya kana ya janyo ta zuwa gabansa a taushashe ya ce "ba nace ba surutu ba?" Ta ce "To gasky a ɗinke bakin kawai Abba, wlh ban san ina yi ba" bata san mene ya samu Yaa Sheikh ba sai gani tayi a durƙosa dai tsayinta tare da rungometa a jikinsa yana shafa bayanta wani irin kyakkyawar murmushi mai tsananin kyau da tsari ya suɓuce masa, wanda kuma ya rungometa ne sbd baya son taga murmushin nasa. "Kada ki damu, zan ɗinke shi kamar yadda ake ɗinke ƙwarya" ta ƙanƙame shi ta ce "Abbana zai rufe mini baki" ya cirota daga jikinsa yanayin kallon da yake mata yasa ta nutsu sosai a hankali ya ɗora bakinsa a goshinta ya sauke mata wata kyakkyawan sumbata forehead kiss ma'anar shi, shi ne _“I Care About You”_ a daidai kunnanta ya ƙara ɗora bakinsa cikin Jamila muryarsa ya shiga karantu wasu adduo'i yana tofa mata a cikin kunnen tai shiru tana jinsa sai ajjiyar zuciya da take saukewa.
_"Allah ya yi miki Albarka, Ubangiji ya kare ki daga sharrin mutum, Allah ya shirya mini ke"_ ya faɗa yana miƙewa tsaye tai murmushi tana riƙe hannunsa ta ce "Ina son ka Abbana" bai kulata ba ya fice abinsa tana biye da shi. A main parlour yaci karo da Umar-khan na shigowa ganin Yaa Sheikh yasa Umar-khan durƙosawa ya ce "Barka da safiya Sheikh" ya jinjina kai. "My Excellency ka fito?" Suka ji saukar maganar nan da nan annurin fuskarta Halisa ya ɗauke ta tsaya kawai tana kallon fuskar Abban nata. Zahrah ta ƙarasu tana cewa "Yanzu nace bari nazo na faɗa maka bana jin daɗi ne, ko zaka iya kai ni asibiti"
Ba tai tunanin zai magana ba amma sai taji ya ce "kuje da Umar-khan" ta ce "Kamarya Umar-khan? Da mijina nake son zuwa bada wani ba, matsayina ya shige kana haɗani da masu aikin ka" Umar-khan ya nemi waje ya zauna idanunsa akan Halisa wacce tai tsaye jikinta na rawa kamar an buga gangar biki.. Ummul ma data shigo ta lura da yanayin na Halisa. "Babu lokaci" Zahrah ta ce "to kayi dropping nawa a hospital ɗin daman Dr na son ganinka ai, hold on meya faru da gemunka" Umar-khan ya saki murmushi domin tuntuni yaga kitson da gemun na Yaa Sheikh yasha. Ummul wata kunya ta kamata ganin yadda gabaɗaya aka kitse gemun na Yaa Sheikh tasan babu mai aikata haka sai oganniyya Halisa..
Yaa Sheikh bai gane ba amma jikinsa ya bashi wani abun ne, duba da yadda Ummul taƙi kallonsa a hankali ya kai hannu ya shafi gemun nasa. Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ya furta a ransa da sauri irin saurin da bai san yana da shi ba ya juya zuwa part ɗinsa babu wanda yake jin kunya sama da Ummul. Dry ta ƙwacewa Umar-khan ya ce "Ummul ya mai jiki?" Ta girgiza tana faɗin "Da alama yau akwai daro duba ka gani?" Ya juya zuwa inda Halisa take har yanzu tana tsaye idanunta ya kakkafe. Zahrah couldn't understand what's happening ta ƙarasa wajan Halisa ta ce "muje kiyi mini tsifa" Halisa tai shiru Zahrah