Showing 186001 words to 189000 words out of 197828 words
Chapter 63 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
ƙasa da kanta tana son taji thank you ɗin ta mece ce?
Ya riƙe hannunta cikin nasa yana ƙara shigar da ita jikinsa yaja numfashi ya ce. "So lucky to have you in my life, Zawja.
Thank you Zawja for sending this amazing present to me…. I loved it and it will always be very special to me, Of all the gifts you have given me, this surprise gift will always be the most special because it came as an unexpected surprise and it will always stay fresh in my memories and my heart"
Ya tallafo haɓarta cikin nutsuwa tare da yin copping face ɗinsu.
"Can i say you're the best wife ever? Am proud of you Ƴar fillo"
"Am also proud of you Habibi ƙalbi, you means alot to me you're the father of my children I love you so much"
Ya tsora mata idanu bai san me ya sa a lokuta da dama take karantar zuciyarsa ba, kafin ya faɗi komai ta gama karanta. Ya gode Allah, daya bashi macen rufin asiri "Yaa Sheikh"
Ya dubeta bai amsa ba.
"I love You" yaji _I love You_ ɗin har ƙasan zuciyar shi, ta ƙara kashe masa jiki tsigar jikinsa ta shiga ta shi tana zubewa. Manna mata sumbata a goshinta cikin kamala irin ta mutanan ƙwarai masu nagarta da sanin hakƙin Iyali tare da zuri'a. Ya furta.
"لو كان العتاق يثل كم أحبك، لضمتك بين ذراعي للأبد"
"I love you Abbana"
Ya fahimci so take ya furta mata wannan kalmar da tayi watanni tana jiran jinta a bakinsa amma ya kasa..
Ya ɗauke kai tare da saka hannu ya ɗauki Little da tayi barci, babu inda tabar babarta har fari da komai hakan ya sa ya ƙara jin son yarinyar na wanzuwa a zuciyarsa. Juya mata baya ya yi. Ta ce
"Habibi" yaƙi juyawa.
Ta saka hannu taja gemun dan shin da taji a gemunsa kamar an zuba masa ruwa ya sanya ta ce "Abul-khairy ku...."
Tayi shiru jin ya juya ya sake rungumeta tare da ɓoye fuskarsa a wuyanta
Ta saka hannu ta amshi Little ta ajjiye gefe guda, a ranta take jin kuka yake abin da bai taɓa yi ba, bata taɓa gani ba.
Yaƙi yarda ya saketa balle ta kalli hawayen.
"Please Habibi stop stop..!" Ya dakatar da ita
da faɗin "Princess, my wife. You have given me the biggest blessing of my life. I treasure this moment of being the father of my child. Thank you for gifting me this bundle of joy and happiness"
"Thank you, ina jin nafi ko wacce mace dace da miji mai nagarta da sanin hakƙin iyalinsa, miji ba fahimta da shiga cikin lamarina, mijin da soyayyata bata rufe mishi idanu wajan ganar dani kuskure, miskilin mijin da zai sanya ni a gaba da kalamai masu daɗi duk kame kai da miskilancin shi, Thank you Dear Lord"
Hawayen daɗi ya shiga fita daga Idanunta jin ya kama hannunta ya zura mata zobe, ta fahimci the best gift daya iya bayarwa shi ne Ring.
Wani lokacin ya ce Allah ya yi miki Albarka wacce hakan yake ƙara sanya *Halisa Danejo Rome* cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa.
So da ƙaunar mijinta *Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu* kuma *Dr Aliyu haydar* ya gama gigita rayuwar *Princess Halisa Ahmad Nuran Sarki*
Ya kasa magana ya shiga sauke mata wasu lafiyayyun kisses ta ko'ina ya mance a gadon asibiti take kuma ita ɗin ɗanya ce, jikinta ɗaya ne.
"It seems that Little Ummul will have a sister nearby, or in this hospital"
Khalil Said yana ƙarasa shigowa cikin room ɗin, daman Umma A'isha da Mother duk suna room ɗin da aka kwantar da Fattoumah. Yaa Sheikh was speechless ya kasa furta komai ya kame fuska da kyau babu alamun wasa, amma fuskar shi ɗauke take da annuri da hasken farin ciki. "Kai Hamma daka tsaya a waje ai"
"That's what i was telling him" Khalil ya juya ya kalli El dake tsaye sanye da navy blue na suit ya zuba hannu a aljihu.
"Kace mini me? Magaji yaushe ka fara sharri"
El ya ce "Goodness, bance maka mata da miji ne ciki ba, ai naga zuwan Abba tun farar Safiyya"
Khalil ya watsawa El harara ya ce "Kai yake Abbanka not me, ja jiki"
Maimoon dake shigowa hannunta ɗauke da flast wanda Ummul tazo da shi yanzu ta ce
"Haka ranar nan ya ce wai rawar kai gareni irin halinmu ɗaya"
Khalil ya zaro idanu ya ce
"Ni ne mai rawar kai ɗin?" El ya ɗaga hannu zai make Maimoon Khalil ya ce "Kana taɓa mini mata sai jikinka ya faɗa maka dan ubanka"
Ƙwafa El-bashir ya yi
Ya ce "Wannan yarinyar ficika da ita sai gulma"
"Eh babu komai, ficika kuma gata can kwance a gado kaje kaji da kwailar daka kwasa shi ya sa kake ta zarya daga Sokoto zuwa Kano, Kano to outside country"
Maimoon taja jiki tare da haɗawa Halisa tea mai kauri sai tiriri yake, ta zuba mata farfesun kayan ciki fal plate "Abba zo muci" caraf ya ce
"Waye zai ci abincin me jego kayan ƙazanta" Maimoon ta kwashe da dariya ta ce "Wallahi ko ni ba zan iya ci ba"
Mai jiran kaɗan balle wacce aka jefa da kashin kaza, ta saki kuka wanda ya farkar da Little ta ce
"Abba wai ni ce ƙazama, kai ma ba za kaci ba"
Yaa Sheikh ya lura da gangan Khalil yake son taso masa da rigimar ƴar fillon kafin ya ce komai
Ta ce "Ai shi nawa ne, ni tasa ce kuma dan kaji yanzu kafin ku shigo ya saka bakinsa a n...."
"Don Allah" Yaa Sheikh ya furta daidai kunnenta yadda ita kaɗai zata ji shi kam ta fasa wannan zancan a gurin nan ai ya banu da Khalil, ga Mubasshir,ga Maimunatu... El ya ɗauki bbyn ya dinga kallon ciki so da ƙauna ya ce "Me za a na ce mata to?"
"HALA" cewar Yaa Sheikh yana miƙewa tsaye ganin yadda Halisa tayi kicin-kicin da rai sbd bai ci abinci ba. "Wow suna mai daɗi Hala"
Yaa Sheikh ya yi waje abinsa kai tsaye kuma Fattoumah yaje dubawa a nan ya samu labari ashe Tun asuba jirgin su Mai martaba da Dada da su Fulani ya sauka, hadda Yaya Halima.
Mai martaba yana can gidan Abba Hakimi. Shi ma daga nan harabar asibitin ya tsaya,yana nan tsaye yana waya yaga shigowar mota ganin ɗaya daga cikin motocinsa ce ya sanya ya ɗan buɗe idanunsa baya ya ajjiye wayar shi daga kiran Umar-khan.
Zahrah ta fito sanye da shigar kamala hijabi har ƙasa hannunta riƙe da basket suna haɗa idanu da Yaa Sheikh ta saki murmushi ta ce
"Good morning sweetheart" Ya jinjina mata kai har ranshi yake son yaga ya kyautata mata amma ya kasa ta ce "Ya sister Halisa da daughter?" A hankali ya ce "Allahamdulillah, wife"
Zahrah ta ce "Bari na shiga,naga kamar fita zakai ko?" Nan ma ya ƙara jinjina kai yana lumshe idanunsa, yana jin zuciyarsa babu daɗi sam da ganin halin da Zahrah take ciki, ya kasa samu kalmomin da zai amfani dasu wajan fahimtar da ita halin da yake ciki, sam wannan kariyar da wasu can Aljanu suka bashi bai ji daɗin ta ba, idan ƴar iska Ubangiji ya ɗora masa Soyayyarra da? Shi aka cutar. rayuwa kenan!.
State C.i.d
Kai tsaye nan Yaa Sheikh ya sauka Khalil da kan shi ya yi driving nasa sai El wanda yake jin kamar zuciyarsa zata faso idan yaga ɗan iskan tsohon ji yake kamar ya saka bindiga ya harbe banza.
Mai kula da sashen bincike da fyaɗe da kan shi yazo wajan Yaa Sheikh bayan sun gaisa ya ce "Kada ka damu Yaa Sheikh, zamu aika shi court daga nan kuma za a yanke masa hukuncin bayan fitar da hujjoji"
El ya ce "How long za'a ɗauka kafin zuwa court duk wani fyaɗe kuma wanda yake da aure hukuncin kisa ne fa? A bani dama na harbe ɗan taure" Ya yi murmushi
"Clam down prince, zai girbe abinda ya shuka imma irin ya fidda ƴaƴa masu kyau ko akasin haka" dole El ya haƙura.
Yaa Sheikh ya koma gida domin ya huta ya samu cikakken tunanin da zai yiwa Zahrah bayani.
A can asibiti da mamaki Zahrah ke kallon Mimi da Alhaji Farouk tare da wasu ƴan uwanta. "Zahrah" Mimi ta kira sunanta muryarta na rawa hawaye ya cika mata cikin idanunta.
Zahrah ta juya da sauri zata shiga mota, Mimi tabi bayanta cikin rashin sani ta bangaji wata budurwa, budurwar ba tayi ƙasa a gwiwa ba ta saka hannu ta ɗauke Mimi da mari cikin faɗa ta ce "How dare you ahh? Wacce irin banza dabba ce ke kina tafiya kai a sama kamar tinkiya mai yasa talakawa suke haka ne mtwss" wani zafin zuciya ya tasowa Zahrah ta ɗaga hannu zata daki budurwar Ummul ta riƙe hannun tana murmushi
"Ummul mahaifiyata da mara fa?"
Ummul ta ware idanu ta ce "Oh da gaske? Har kin manta?" Ummul ta ƙara murmushi ta ce
"Idan maye ya manta uwar ɗa ba zata mance ba, faɗin Ubangiji ne da kansa, wanda ya zagi uwar wani haka za a zagi tasa, kin mareni kin zageni ba akan idanun ɗana ba, yau gashi an mari mahaifiyarki akan idanunki an kuma ci mutuncin ta, shi ya sa a kullum kake iya bakin ka naso ɗaukan mataki sai na share domin iya son ɗana da Ubangiji ya gwada miki shi kaɗai ya isa ya zame miki ishara, sai dai ba zaki taɓa zama inuwa ɗaya da Aliyu ba, kamar yadda ki ke mafarki nasan ya kasa faɗa miki ko?" A gigice Zahrah ta ce
"Don Allah Ummul kiyi haƙuri ki rufa mini asiri kada ki ɗauki fansar abinda nayi miki ta hanyar rabani da Yaa Sheikh ki tausaya mini shi ne kaɗai inuwar da nake jin gina naji daɗi" ta saki kuka sosai.
"Babu ruwana Fatimerh, banyi lalacewar da zan raba aure ba, zanan ƙaddarar damu kanmu bamu san da shi ba, shi ne Ubangiji ya yi ikonsa akan haka zai kuma rabaki da Yaa Sheikh cikin ruwan sanyi" Halisa da Umma A'isha da suka fito domin tafiya gida an bata sallama suka tsaya suna kallon ikon Allah.
Kowa ya kasa magana,
Abin mamakin dake faruwa bai shige dukkan wanda yazo hucewa sai ya juya ya kalli Halisa wasu suna nunata da hannu suna cewa ita ce
Ƙarar jiniya suka ji ko ta ina Mother ta ce
"Wai meke faruwa ne?" Halisa ta marairaice fuska ta ce "Mother me ya sa ake kallona ne?"
Aka buɗe motocin kai tsaye wani ya nufi wajan Halisa Ummul tayi saurin shan gabansa ta ce
"What's going on?"
Ya fito daga Card ya ce
"Ɗan sanda daga hukumar C.I.D Criminal Investigation Division" Ummul ta ce "Ok then, mene ya kawo ku?" Da hannu ya nuna mata Halisa ya ce "To Arrest that young lady behind you......
08119237616
Paid book
₦500
Complete ₦1000
*_After 3yrs🫣....._*_*Sarautar marubuta 80*_
"Arrest?" Suka haɗa baki wajan faɗa Halisa ta gigice ta riƙe Ummul domin ita take gani kamar mijinta Yaa Sheikh cikin rawar murya ta ce
"Wallahi banyi komai ba, me nayi su waye ku?"
"Hakan ya ƙara saka mini shakku akan ki"Ya faɗa yana ƙara jinjina kai ba tare da tsoro ko fargaba ba. Ummul ta ce
"Excuse me Officer, kasan matar wace da za kayi arresting nata?
Akan wanne dalili, me tayi" Ya duba lokaci ya ce
"Sorry Madam, kina wasting time ɗina, idan muka ke office ɗinmu zaki ji komai wajan tuhumar mata laifin daya sanya mukai arresting nata" Halisa ta fashe da matsanancin kuka
"Ummul, Abba, Mother I don't wanna go to prison"
Gabaɗaya ta gigice ta saka kuka, ga jikinta babu ƙwari abinka da ɗanyan jiki irin na masu jego. Mother ta bawa Umma A'isha Hala ita kuma ta riƙe Halisa dake neman fita hayyacinta daman ita bata iya firgita ba yanzu zata zauce.
"Babu inda zata ba tare da faɗin dalilin arresting nata ba" Mutumin ya kalleta ya ce.
"Ki saurara da maganganunki, ko mutuwa tayi sai mun tafi da gawarta" a ruɗe Mother ta ce "What! Are you at of your sense?"
Mothers na gama magana Ummul ta fito da card ɗinta wanda take shirin kai wa.
Ta nuna mishi ta ce
"I am police officer, nasan kana da matsayi mai girma ba rukuninmu ɗaya ba, amma zan baka mmkin ƙarfin ikon daga sama" "And am ready to be her lawyer" cewar Mother! Cikin tsawa ya ce "Arrest her!"
Ya faɗa a tsawa ce cikin zafin rai. hankalin Familyn ya ta shi, Ummul taja gefe tana waya mai matuƙar muhimmanci yadda take wayar zaka san ranta zai ya ɓaci.
Mother ta riƙe Halisa, Dada daman kasa cewa komai tayi taja gefe Idanunta cike da hawaye.
Cikin sauri Zahrah ta shiga tsakani ta ce
"Arrest me first before her, ko tausayi baka da shi mace ta haihu a sallamata yanzu shi ne kake tunanin tafiya da ita Oh My Goodness"
"Officer" "Yes Sir!" Wani ya faɗa yana ƙamewa ya miƙa masa hannu ya bashi wayar gallery ya shiga ya fito da photo tare da juya screen ɗin wayar ya nunawa Zahrah ya ce "Yanzu sai ki fahimta" Zahrah ta zare idanu tare da dafe ƙirji cikin sauri ta matsa daga kusa da Halisa tana amsar wayar tare da duba photon da kyau.
*Halisa* ce tsaye hannunta riƙe da wuƙa ta cakawa wani mutum. Daga nan ya nuna mata vedion cc.t.v camera.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Halisa wa kika kashe" a ruɗe Dada ta ce
"Kisa?" Halisa wacce numfashinta ya fara gardama ta riƙe Mother da ƙarfi tana girgiza kai idanunta na rufewa sosai cikin kaɗuwa da fitar hayyaci ta ce
"Ban kashe kowa, wallahi bani bace banyi kisa ba na shiga uku Ku kira mini Abbana shi yasan ba zan kashe kowa ba"
"You're lie. Liar"
Zahrah Said tana sakin kuka ta kasa yarda Halisa zata iya kisan kai, amma photon ya nunata komai da komai.
Dada ta amshi wayar cikin tsananin tashin hankali tayi baya tana salati ya akai Halisa tayi kisa? Ya akai ta shiga cikin har ta kashe rai mene alaƙarta da wanda ta kashe. Jikinsu ya yi sanyi suka kasa magana banda Ummul dake can tana waya. Ya watsa hannu baya ya ce
"So allow me to arrest her" Halisa ta riƙe Mother tana girgiza amma Mother ta kasa komai, ta koma kan Umma ta ce "Wallahi ƙarya suke bani bace ban kashe kowa ba kada su rabani da ƴata kada su rabani da mijina"
Wani murmushi Officer ɗin ya yi ya ce.
"So that's true daman ance kina da ɗaure gindi a duk wani iskanci da kike, yanzu zamu ga wanda ya tsaya miki zamu kawo ƙarshen barikin ki ƴar ta'adda kawai" Ya miƙa hannu tare da kama nata zai sanya mata handcuff ya ji an fisge hannunsa tare da murɗe shi baya, ya bada sauti. Ya saki ƙara "How dare you torch my sister's body, wanne ɗan iska ne kai waye ya baka damar kama matar *Yaa Sheikh, Ƴar sakin Sokoto* ?"
"Ƴar sarkin Sokoto? A information ɗin da aka bayar ance yarinyar a gidan karuwai take da zama" Manyan motoci ne suka shigo cikin asibitin a guje har da ta wasu polices nada ban.
Yaa Sheikh ya fito da sauri hankali ta she yana sanye da Jallabiya idanunsa ya yi jajir da alama fitowar ba zata ce wacce ba'a shirya yinta ba. Halisa na ganinsa da raguwar ƙarfinta ta nufe shi ta faɗa jikinsa kamar yarinya taba rufe kuka.
Ya rungumeta yana bubbuga bayanta cikin sigar rarrashi.
Yadda jiniyar kan shi tayi zai baka mamaki haka tabbatar yana cikin fushi mai zafi, zuciyar ƴan maza Aliyu na kusa, babu batun malunta.
"Abba banyi komai ba, kada su tafi dani kada su rabani da kai da Hala ban musu komai ba"
Ya runtse idanunsa wanda ruwa ya kwanta cikinsu tsabar zuciya takaicin yadda suka gigita masa mata yafi komai bashi haushi, ya ƙara sanyata jikinsa yana rungumeta da kyau ya kasa magana sun jima haka kafin ya kama hannunta zuwa dalleliyar motar shi ya sanyata a baya, zai juya ta riƙe shi ta ce "Habibi kada ka barni nan" ya watsa jajayen idanunsa akanta ita kanta ta firgita sai taga idanun tamkar bana mutum ba ya yi wani kala-kala yana sauyawa.
Ya riƙe hannunta alamar
"Relax" yana zame jikinsa tare da juyawa.
Kai tsaye wajan Umma A'isha ya nufa ba tare da ya ce komai ba, ita ma ta miƙa masa *HALA SHEIKH ALIYU HAYDAR*
Ya amsheta yana jin yadda take wurga ƙafa tare da tsotsar hannu.
Motar ya koma ya sanya mata Hala a cinya ta rungumeta sosai tana ganin kamar wani zai rabasu idanunta cike da hawaye ta ce
"Modibbo kazo mu gudu Please rabamu za suyi" ya juya mata idanu kai tsaye ta fahimta shi ne *IDAN BA KE*
El-bashir Ahmad Nuran Sarki ya riƙe wuyan Officer ɗin ya ce
"Akan me zaka yanke hukunci ba bincike" Garbati ya ɗimauce wani ya zo da sauri ya ce
"Officer munyi kuskure ashe kama ce kawai suke da juna ba ita bace"
Wanda aka kira da Officer kuma shi ne Garbatin cikin In-ina ya ce "Oh! to to ya yi, kuyi haƙuri kamanni ne ba ita ba ce" Ɗaya daga cikin jami'an da suka shigo tare da El ya ce
"Babu sunanka cikin list ɗin Officers namu daga ina aka turo ka?"
"Sunan shi Garbati Nuhu, ɗan gidan Mai gadin da aka kai Court" gabaɗaya suka kalli Garbati kenan yayi haka ne da nufin su sake mishi Uba? Ta hanyar basaja da kayan ƴan sanda da kuma cin amanar hukuma..
"Fake news ne kenan? What about the vedio mene shirinka?" Yaƙi magana Yaa Sheikh ya kasa jurewa ya kuma kasa lamunta daya rufe idanunsa yadda Garbati ya damƙi Halisa yake gani, cikin zafin nama ya ɗauke shi da kyakkyawan maruka. Ya ce.
"Za mu yi masa hukunci irin na addinin musulunci, za a kashe shi ta hanyar jifa ya aikata fyaɗe da auren shi" El wanda zuciyarsa ke kusa ya saka hannu ya naushi Garbati gani yake kamar ubansa yake doka. Garbati ya galabaita ya ce "Wannan shi ne karo na biyar da mahaifina yake fyaɗe, kuma a duk wanda ya aikata a matsayin me gadi ne, da ya yi sai ya gudu imma an kama shi zan saka kayan ƴan sanda na yiwa iyalan yarinyar kashe di a haka har magana ta mutu, hankalina ya tashi lokacin da naji ya yi fyaɗe ga zuri'ar babban Malamin nan da ake faɗa Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu. Bana da ikon yi musu bara zana, domin ahhali ne