Showing 39001 words to 42000 words out of 197828 words
Chapter 14 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
shi na son shiga part ɗin nasa ba tare da kowa ya gansa ba. Yaje corner kenan yaji ance.
"Yaa Sheikh" Khalil Ahmad Sarki ya faɗa yana murmushi hannun shi riƙe da gorar ruwa. "Yanzu nake shirin zuwa can gida muji yadda al'amarin bikin zai kama, nasan dai bikin Yaa Sheikh dole ba events ba D.j" Sheikh ya ware idanu da kyau yana bin Khalil da kallo. Khalil ya ce "na ƙosa naga matar Yaa Sheikh, nasan dole ta zama Malama kamar haka, Wow! Ga Yaa Sheikh ga Malama what a beautiful couples wlh dole love yaci ƙaniyar shi"
Yaa Sheikh ya ɗauke Idanunshi tare da kama hannun Khalil Ahmad sarki suka nufi hanyar ƙofa Khalil ya ce "Ya dai kamata ka fito tun ɗazo Mai martaba ya shigo" har lokacin Yaa Sheikh bai ce komai ba, yana zuwa bakin ƙofa ya tura Khalil waje tare da rufo ƙofar ya murɗa key. Khalil ya dinga dry daman ya lura zan can damun Yaa Sheikh yake yana mmkin yadda baya ƙaunar ai masa maganar mace?. Ya juya inda yabar su Abba Hakimi yana zuwa ya ce "Abba Hakimi ai ga ɗan naka can ya gudu part ɗin shi" Abba Hakimi ya ce "Za mu yi faɗa dakai yanzu Ibrahimul-khalil" Khalil ya yi murmushi ya ce "Nikam ina ruwar gida Momi ne?" Abba Hakimi ya ce "Tana can tana kayan buɗe baki na Aliyu, ƙosai da kunun gyaɗa"... "Ah! Lallai aikin lada take kenan" Mai martaba Ahmad Sarki ya kalli Ishaq-Hakim cikin kamala ya ce "kira Sheikh" da mutumtaka ya ce "To ranka ya daɗe Allah yaja kwana" kafin Ishaq-Hakim ya miƙe El-bashir wanda tun ɗazo yake hakimce saman kujera ya miƙe cikin nutsuwa hannu cikin aljihun suit ya nufi hanyar fita Abba Hakimi ya bisa da kallo yana nazartar yanayin yaron wanda baya son haɗa inuwa da Yaa Sheikh gaba ɗaya. "El-bashir kada kai nisa" cewar Mai martaba. He just nods his head and quickly leave the parlour. Bayan sallar magrib Yaa Sheikh na zaune a ƙawataccen parlournsa gabansa ɗauke da kayan buɗe baki, inibi yaci sai ƙosan da yake mai zafi ya yi laushi sosai sbd ƙwai da aka zuba cikin haɗin, hakan yasa ya ɗan saki jiki ci ƙosan da kunun gyaɗar. Yana jin gine da jikin kujera yana kallon Aljazzera yaji Sallamar Abba Hakimi shi ne kawai ke shigowa kai tsaye cikin part ɗin na shi, ya gyara zama sosai yana mai amsa sallamar ta Abba Hakimi. Bayan Abban ya zauna ya dubi Yaa Sheikh ya ce. "Aliyu haydar" Yaa Sheikh ya ɗaga kansa gaba ɗaya tare da kallon Abba Hakimi da yake faɗin "Jibi ɗaurin auren ka, ya ya zakai da uwar gidan naka kafin amaryar tazo?"
"Uuuu...uu... Uwar gggg gida? Am am amarya?" Ya faɗa yana kallon Abba alamar rashin fahimta. Abba Hakimi ya lura da gaske Yaa Sheikh bai gane ba ya ce "Yarinyar da aka ɗaura maka aure da ita a can Yola? Ka tuna?" Tab yakan manta abubuwa amma wannan abun ya zama abu na farko da ya yi saurin mantawa da shi. "Ina jinka,ina so muje can rugar tasu ne" magana zarar bunu cikin rashin sani Yaa Sheikh ya ce "Uhm bani da labarin hakan Abba, idan akwai auren ma zan kunce shi yanzu...
*Don Allah kada a fitar😒 littafin IDAN BA KE na kuɗi it's 500 via this account 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank. Via evidence 08119237616.
SARAUTAR MARUBUTAMurmushin manya Abba Hakimi ya yi yana mamakin yadda kai tsaye Yaa Sheikh yake nuna zallar ƙiyaya ga ƴa mace balle kuma ai masa batun aure, ya san dai rayuwa ba zata taɓa yin yiwuwa ga babban mutum irin Sheikh Aliyu haydar Aliyu ba aure ba. Yana sakin murmushi ya ce.
"Baka sonta? Ko auren ne baka so?" Yaa Sheikh ya yi shiru kansa a ƙasa ba tare da ya ce komai ba, hakan bai damu Abba Hakimi ba domin ya riga yasan waye Yaa Sheikh sai dai ya bawa wani labari sanin da ya yi masa baya tunanin ko Mahaifin shi Engineer ya sani. "Shi kenan, Allah ya kyauta, ka jira sakin muga ko?" Abba Hakimi ya furta hakan yana miƙewa tsaye hannun shi riƙe da sanda. Yaa Sheikh ya a miƙe tsaye shima suka jera shi da Abban na shi duk da bai so fita wajan ba.
A parlour suka samu Mai martaba Ahmad Sarki shi da Khalil suna tattaunawa a hankali lokacin guda kuma fuskar Mai martaba ɗin ta sauya launi sosai. Bayan sun zauna Khalil da bakinshi baya shiru ya ce "Abba ka fito da ango kenan, ban taɓa ganin ango kamar shi ba He doesn't want to talk about his marriage at all" Abba Hakimi ya kalli Mai martaba ya ce "Your highness mai ya sa ka taho da wannan ne? Ina ya bar matar ta shi" murmushi girma kawai Mai martaba ya yi ba tare da ya ce komai ba idanun shi akan Yaa Sheikh yana taso ya faɗa masa wata magana amma ya kasa.
"Yaushe El-bashir ya zama haka ne? Kamar wanda wani abu ke damun shi?"
Khalil cikin rashin jin daɗi ya ce "Na lura da hakan, matsalar El-bashir taurin kai, komai ya yi zafi a rayuwa maganin shi Allah yabi komai a sannu har Ubangiji ya bayyana abin da yake rufe ko?" Abba Hakimi ya ce "haka Innalillaha ma'al sabirin" a hankali Mai martaba ya duba lokaci yana mai miƙewa tsaye kafin ya kalli Yaa Sheikh ya ce "Yaa Sheikh aci gaba dayi mana addu'a, ina nan ina ta sadaƙa, kamar yadda kace" Yaa Sheikh ya buɗe ido wanda tunda suke magana idanun suke rufe, tare zubawa Mai martaba idanun cikin nutsuwa ya ɗaga kai tare da ɗan faɗaɗa fuskar shi da murmushi. Abba Hakimi ya ce "ba zaka zauna a nan ɗin ba?" Mai martaba yana gyara sandar hannun shi ya ce "Anya? Gwara naje can hotel ɗin zaifi" sai da safe ya yi musu Yaa Sheikh da Abba Hakimi suka zauna zaman karatu kamar yadda suka saba kullum.
Juyi yake saman lafiyayyan royal bed ɗin na shi ya kasa barci baki ɗaya mafarkin da yake ya hana shi runtsawa, gashi duk karatun shi bashi da masaniyya akan fassarar mafarki, ya miƙe zaune yana mai motsa bakinshi alamar addu'a cikin nutsuwa ya kunna blue light haske ya ƙara bayyana a bedroom ɗin, daga shi sai white night wears masu taushi da kyau, ya saka Hermes slippers tare da shigewa bathroom ya wanke bakin shi tas kai tsaye ƙaramin parlournsa ya koma, hannunshi riƙe da kwalin Dabino yana zama kan kujerar ya zari dabino ɗaya ɗaya tare da kaiwa bakinshi, zaƙi da garɗin dabinon suka ratsa saman harshensa tare da kaiwa jijiyoyin dake sarrafa kwakwalwar dake basa umarnin ziyara, kai tsaye dukkan wani daɗin dabinon ya gama ratsa ko'ina na bakinshi. Iska mai daɗi ta fara kaɗa shi kafin can kuma ya fara jiyo kukan mage ƙasa-ƙasa bashi da wata alaƙa da mage infact baya son mage a rayuwarshi da alama kuma so ake a firgita shi da ita. Babu tsoro a fuskarshi ya miƙe hannu goye a bayansa bakinsa ɗauke da addu'a a haka ya fara bin hanyar da kukan yake tasuwa ba tare da tunanin komai ba. A can corridor ya ga wata baƙar mage jibgegiyya wacce bai taɓa ganin irinta ba, a kallo ɗaya kuma ya fahimci ba mage bace irin jama'arsa ce masu takura masa. Girgiza kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba ya nufi hanyar bedroom ɗin kamar daga sama yaji magen ta ce.
"Zahrah da zaka aura tana da ciki, tana ciki, tana da ciki" ya tsaya daga tafiyar da yake tare da juyowa baki ɗaya yana harɗe hannu a ƙirji, duk kusan wani abu da zai faru da shi a rayuwa yana mafarki da shi, inma mai kyau ko mara kyau, ya yarda cewa kuma mafarki ba gaskiya bane bai taɓa yarda da abubuwan da yake gani ɗin ba. Wani lokaci jama'arsa da suke bibiye da shi sune suke faɗa masa wani abun.
Ya sauke numfashi cikin laushin murya ya ce.
"Ta nan aka ɓullo, raba aure zaku koma?" Ya faɗa a taushashe yana zubawa magen idanun ta ce "musan abin da baka sani ba, tana da ciki, tana da ciki" Yaa Sheikh ya jawo aya mai zafi cikin kamilalliyyar muryarsa gumi na tsastsafo masa ya ce "Ubangiji shi ya san komai" ya sauke numfashi yana mai ƙara cewa "matsa nan, kafin raina ya ɓaci" kasancewa ko a malamai suna shakkar Yaa Sheikh cikin ƙaramin lokaci ta ɓacewa ganinsa, da ya san sune ma babu abin da zai tsanya ya fito Maganar Zahrah da cikin ya tattara ya sanya su a mala.
Washegari ya kama juma'a Yaa Sheikh ya fito cikin wata dakakkiyar shadda gezner fara tas sai ɗaukan idanu take, bai saka Alkyabba ba kasancewar jamper da babbar riga ya sanya sai rawani kawai da ya yi ya ɗora hirami saman ƙafaɗarsa. 1:30 daidai motarsa tai parking a babban masallacin juma'a dake nan Kano. Cikin sauri gudu harɗewar harshensa ya fara huɗu ba akan muhimmancin sadaƙa da kariyar da take bayarwa dan gane da asara. 2:00 ya data iƙima na sallah ana idarwa kamar yadda ya saba ya nufi gidan marayu da naƙasassu yana basu taimako. 3:30 ya dawo gida kiran Father ne ya ƙara sanyawa ya yo gidan kai tsaye ba tare da tunanin komai ba, yana gaba Khalil na gefen shi a haka suka shigo cikin parlourn mai ɗauke da some of relatives nasa, idanunsa akan Fattoumah wacce akai wa henna a hannu da ƙafa tana ganin shi ta miƙe da sauri tana faɗin "Yaa Lee, Yaa Lee" da sauri yaja baya domin baya son abar hannunta infact he doesn't know menene ba, ya zauna saman kujera yana harɗe hannu a ƙirji ba tare daya kula Auta Fattoumah ba. Dr A'isha ta ce "Ango kasha ƙamshi, wata tsiyar ma sai jibi amarya ta zo can wait to see this day" Yaya Halima ta ce "ke dai Dr bakya kalan girma Wallahi ta ya ya ɗan naki zai girmama ki?" Kafin kowa ya yi magana Jadda ta fito zani na faɗuwa ta ce "Ga Malam ga Malam, huhu azabar duniya ya naga duk an sa shi gaba kamar wata tattabara sabuwar ƙinƙisa? Nifa masifar Sa'idu ce bana son uban kowa kuma ya san babu kyau ai" Khalil ya saki baki yana kallon Jadda. "To dan mun gaisa da shi ai bai zama laifi ba ko?" A fusace Jadda ta ce "Alkur'an ya zama? Ki faɗi inda kuka haɗa jini da Malam? Ba dangin iya balle na baba, sai ihun cewa ke ƙanwar uwar shi ce, gaba kuma kice ke uwar shi bayan ko ƙaton kashi baki taɓa ba, balle haihuwa tirrr da iri na irin naki, ke dai baki yo gadon haihuwa ba, Insha Allah duk inda wata tara tayi matar Malam ta sauke cikin fari ke dai kiyi ta zama" nan da nan idanun Dr A'isha ya cika da hawaye babu abin data tsana irin ai mata gorin haihuwa. Yaya Halima itama da ranta ya ɓaci ta ce "Jadda amma dai kin san haihuwa lokaci ce ko? Duk wanda ya haihu Allah ne ya bashi ai" Jadda tai mitsi mitsi da idanu ta ce "Ai baki cika ƴar halak ba Halima indai baki zo kin dake ni ba, na faɗa ta haihu ne? Naga shekara guda akai bikin ita A'isha take kowa da kuma siyan Akuyar da nayi, gashi nan sai haihuwa take kamar almara ko yanzu ciki gareta ina ta rabawa jama'a domin su sami irin albarka" Dr A'isha ta fashe da kuka sosai tana ciwo sosai a ranta. Yaa Sheikh dai yana zaune tare da sauraran komai ba, jin ihun Jadda ya yi yawa ya sanya ya miƙe tsaye tare da saurin barin wajan, yana zuwa dab da Dr A'isha ya kama gefen rigarta ya jata can part ɗin mother. Bai ce mata komai ba, amma ya lura da irin zafin da take ji a zuciyar ta. Sai data gama kukan ta fara shassheƙa ya lumfasa kaɗan ya ce.
"ka yi bushara ga masu hakuri (155) su ne waɗan da idan wata musiba ta same su, sai su ce: mu daga gare shi muke kuma gare shi za mu koma, Baqara (!56)" ya yi shiru saboda In-inar data zo masa, shirun daya sanya Dr A'isha ɗago jajayen idanunta tare zuba masa su, sai taga ba ita yake kallo ba, gaba ɗaya ya tattara gaban babbar rigarsa ya riƙe ƙam hannunsa na rawa, alamar da gaske magana yake son yi, jikinsa ya bashi kallon shi take da sauri ya juya zai bar wajan kamar fitar gashi daga cikin nono haka maganarsa ta fito ya ce.
"Wannan ayar ta kur’ani ana kiranta da ayar maidowa kuma tana karantar da mu darasin cewa kada mu yi baƙin ciki da faduwar falala, domin duk wannan baiwar Allah ce. Wata rana ya yafe, washegari kuma ya ga dama ya dawo mana da ita, su biyun su ne maslahar mu. Ki yi haƙuri"
Yana faɗin hakan yabar wajan kamar walƙiyya Dr A'isha ta saki Ajjiyar zuciya tana jin sanyi a ranta, yau Yaa Sheikh da kansa ya jata har ya yi mata wa'azi lallai ta zama ta musamman ko a cikin ƴan uwa.
Jadda kuma ta inda ta shiga bata nan take fita ba. "Ko wanne ɗan hau idan ba zai iya zama bai yai gaba, idan mutum yaja baki yai gum sai ace ya yi wulaƙanci, ya yi magana kuma ace shi ɗan iska bai iya magana ba, huuuu wannan azabar Alkur'an ba dani ba Alsulhu khair" tana ganin Yaa Sheikh yaja baki tai shiru akan idanunta ya haura upstairs part ɗin father, kamar yadda yai tunani yana parlourn shi zaune sai haɗa gift yake wanda zai bawa bride's family. Yaa Sheikh zai sallama Father ya ɗaga hannu ya ce "shigo kawai, riƙe sallamar ka" hakan bai damu Yaa Sheikh ba, ya nemi waje ƙasan carpet ya zauna.
"Akwai events da Zahrah zatai, kuma tana buƙatar kaje iya friends ɗinta ne, kai ma kaje da friends naka, 12 na dare zasu fara event ɗin gobe, You can check by yourself" Yaa Sheikh bai ce komai ba, kuma bai amsa ba, domin ya san ba za shi ba.
Ya miƙe tsaye yana gyara zaman hiramin jikinsa. Sai da ya ɗan jima a tsaye ya ce "Allah ya taimaka" yana faɗin hakan ya juya cikin sauri tare da barin gidan baki ɗaya shi da Khalil.
Surayyerh ta zame jikinta daga cikin friends ɗin Zahrah tana duba agogo dake nuna 10:15 na safiyar ranar asabar. Cikin sauri ta nufi compound na gidan tare da shiga mota, tana yi tana dubawa gudun kada wani ya kanta, driving motar dake da gudu har tabar Commissioners Quarter's kai tsaye ta nufi wani babban mall parking tayi, kasancewar mall ɗin na manyan mutanai ne ya sanya aka fara yi mata Wlcm tun daga bakin gate. Tana shiga ciki wata mata ta ce "Wlcm Maaah" ta ɗaga mata kai, kai tsaye ta nufi ɓangaren kayan mata ta saka wata maid ta zo. Tana zaune saman kujera lemo a hannunta maid ɗin ta ce "Yes Maaah, how can I help you?" Surry ta ya motsa fuska tana kallon maid ɗin ta ce "Ina buƙatar, Abaya's, perpumes, body spray, body lotion, shower gel, everything na mace masu kyau na ƴar 17yrs ki haɗu ki kawo mini yanzu" Maid ɗin ta rusuna ta ce "Insha Allah Maaah, enjoy your time" ta juya da nufin tafiya Surry ta ce "hiii nace ba" Maid ta ce "Yes" Surry ta miƙe tsaye tana ƙare wa wajan kallo ta ce "Ki tabbatar body lotion ɗin sai sauya fata cikin kwana biyu" Maid ɗin tai murmushi cikin hausar ta ta ce "kada ki damu kinji" kaya masu mahaukacin kyau aka haɗawa Surry ga tsada ka cika aiki, komai na babban company aka zaɓo, ta biya kuɗi aka loda mata kayan aleda daga mall ɗin Specialist Yola ta nufa, tana zuwa ta samu Danejo zaune a gaban room ɗin da aka kwantar da Dada, ta miƙe tsaye fuskarta ɗauke da fara'a ta ce "Sannu da hanya Adda" Surry ta haɗe rai ta ce "Ba nace bana son Addar nan ba, kice Anty" tai ƙasa da kanta tana wasa da hannu "Ya na ganku a nan?" Danejo taƙi cewa komai sai Shatu da ta ce "Ana duba Dada ne" ta jinjina kai tare da neman wajan zama, sai duba lokaci take tasan anytime Zahrah zata iya nemanta sbd shirye-shiryen zuwa event anjima. Likitocin suka fito Danejo na ganin haka ta shiga room da sauri Shatu ta mara mata baya, Surry tabi bayansu A zaune ta samu Dada cikin ranta ta ce "Wow, ashe Halisa gado tayi" Kyakkyawa ce sosai Dada ajin ƙarshe, ta faɗaɗa fuska idanunta akan Surry wacce ke mata sannu cikin sanyin muryar ta ce "Allahamdulillah, ke ɗaya yau?" Surry ta ce "Wallahi, hanya ta biyo dani bama sai an faɗa mata nazo ba, anjima likita zai sallame ki" Dada ta ƙara sakin murmushi ta ce "To ba damuwa, Allah ya saka muku da alkairi, Halisa ta faɗa mini aiki sai dai ban gane ba" Surry tai murmushi ta ce "Oh! Daman ƙawata zatai aure shi ne za a ɗauke ta aiki sbd mun yaba da hankalinta, kuma duk shekara ko wata za a dinga biyan ta kuɗin aikin, kuma sa a sakata a makaranta akan wannan sharaɗin da tace zata cika muka kawo ki asibitin" da sauri Danejo ta kalli Surry domin tasan ba haka akai ba, bakinta na rawa kasancewar bata barin magana a ciki ta buɗe baki ta ce "Lalashewa ta sameki Anty Aradu ƙarya ne ba haka akai ba, shewa sukai zan..." cikin sauri Surry ta tare Danejo da faɗin "wannan daban ne kinji ƙanwata Halisa, zo kiga kayan da na siyo miki" tai shiru tana ware idanunta itafa haka kurum ba za a dinga rainata mata hankali ba. Surry ta buɗe ƙatuwar shopping bag ɗin ta shiga zaro dugwayen riguna kala-kala, masu kyau da tsari.
"Wannan kayan duk na mene?" Cewar Dada domin ganin kayan ya sanya kanta sarawa ta rufe idanu