Showing 63001 words to 66000 words out of 197828 words

Chapter 22 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9340

Man’s environment affect their language, dressing, food and every other thing one can think of in the society,_ _Man also interacts with two environments which are:_
Physical environment (Natural)
Social environment (Artificial)".


"Tab ni dai dama ba wannan makarantar aka sani ba, malamin ba babu abin da ya iya" Azaan ya dubi Halisa ya ce "What's your name" ta tura ƙaramin bakinta ta ce "Me kace?" Wata wacce ba zata shige age mate ɗin Halisa ba mai suna ABIR ta ce "Ya ce ya ya sunanki?" Halisa ta ƙaramin murmushi kawai cikin siririyar murya ta ce "Halisa Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu" Azaan ya buɗe idanu da kyau cike da mamakin jin sunan data alaƙanta kanta dashi, Yaa Sheikh take nufi ko wanne? Dama yana da yarinya yaushe ma ya yi aure har ya samu yarinya kamarta?. Azaan ya ce.
"Abir make her understand, explain to her" Abir ta ce "Okey Sir" mai Hali baya fasawa domin Azaan na shirin fita ta ce "Kuma na manta na faɗa maka ina da aure" Azaan ya kalleta sai kawai ya fice dan ya lura bama tasan shi kansa auren ba har take cewa haka. Ya tafi cike da sha'awar surutunta wanda ya birgesa lokaci guda. Abir taiwa Halisa bayanin komai na topic ɗin cikin harshen hausa, ta ce amma ta rage surutu da yawa a haka ta ƙare zaman makarantar wani karatun ta gane wani a'a, Umar-khan da kansa yazo ɗaukanta sbd Yaa Sheikh yana can wajan lecture ba zai samu dama ba.


Sarki Ahmad Nuran Kingdom.
Da sauri yake tafiya hannunsa zube cikin aljihu cikin yanayin kaɗuwa da kuma tashi hankali, saukarsa kenan ƙasar kullum cikin tafiye-tafiye yake, kana kallon fuskarsa kasan baya cikin nutsuwa da walwala. Ko'ina ya gilma acikin gidan sarautar bayi da kuyangi ke zubewa suna gaida shi, amma kallon arziƙi basa samu daga gare shi. Kai tsaye sashin Fulani Atine ya nufa, wata kuyanga ta sanar da Fulani Atine zuwan yarima cikin jin daɗi ta bashi izinin shigowa bayan ta sallami hadiman nata. Tsaye ya yi yana kallonta kafin ta ce. "Meke faruwa da kai El-bashir? Yaushe ka tafi da har zaka dawo?" Yaƙi magana sai huce yake tamkar zakin dake neman abinci bai samu ba. "Wannan ɓacin ran na mene What is the reason for bringing you back to this country now?" Ya ɗauke idanunsa cikin ɗaga murya ya ce "Idan ina raye sai naga bayan Yaa Sheikh hankalina zai kwanta, sai na tabbatar ya wahala a rayuwa kamar yadda ya wahalar dani, zan tirkesa na musguna masa kamar yadda ya sanya ni cikin damuwa da ƙonar zuciya na tsayin shekaru, sanyi amfani da uniform ɗin dake jikina na police na jasa zuciya hanyar da zata ɓata suna da martabar da yake iko da su, ba zan taɓa farin ciki ba muddin ina ganin gilmar Yaa Sheikh a duniya" Fulani Atine tayi murmushi tana mmkin zafin zuciyar da El-bashir yake da ita, a hankali ta ce "El-bashir duk bai kai wannan extent ɗin ba, pls i want u to calm down" cikin zafin zuciya El-bashir ya ce "Ya kai har ya shige extent ɗin da da kike faɗa, a wannan karan dole nayi gaba da gaba da Yaa Sheikh dole nai amfani da mutum mafi kusanci da shi wajan ruguza rayuwarsa data ahhalinsa" Fulani Atine ta ce "Kana da hujja kenan? kana da shaidar da zaka iya kurfanar da Yaa Sheikh a court? Kada ka manta lokacin da al'amarin nan ya faru Yaa Sheikh baya ƙasar bare ka zurfafa cewa shi ya aikata, kada ka tirke kanka maimakon Aliyu, nice shaidarka akan idanuna komai ya faru" El-bashir ya riƙe hannun Fulani Atine ya ce "Ki taimaka mini na ɗauki revenge akan Yaa Sheikh, ba zan iya ba, na kasa haƙura na kasa jurewa Fulani, ya rabani da jin daɗina" Fulani Atine ta ce "Kafin ɗaukan fansa, dole ka nemi kusanci da Yaa Sheikh, dole ka nemi gurbi a zuciyar ƴar fillon da ake magana, kasan yadda kayi ta fifitaka akan shi" El-bashir yai shiru for some minutes kafin ya ce "Mene amfanin saka ƴar fillo cikin al'amarin nan?" Fulani tai murmushi yaro yaro ne, daman ance daka na gaba ake gane zurfin ruwa, ta ce "Idan ka taɓa ƴar fillo kamar ka taɓa zuciyar dake sarrafa tunani Yaa Sheikh ne, nasan abin da kai baka sani ba, kayi hakan" ya shiga safa da marwa He was completely at a loss, unable to understand what she was saying to him. "Nayi masa da baibayi ta ko'ina ina da investigator a cikin ma'aikatan dake aiki a can gidansa na Madina" yana faɗin hakan ya fice rai ɓace.
"Well-done El-bashir Ahmad Nuran Sarki, kana yin komai bisa tsari kamar yadda aka shirya" Fulani Atine ta faɗa tana bin bayansa da kallo. Ma martaba Ahmad Sarki ne ke tafiya shi da Khalil yana yi masa bayanin sauyawar da El-bashir ya yi cikin kwana biyu. Mai martaba na ƙoƙarin yin magana El-bashir yazo ya shige ta gabansu tamkar zai ta shi sama, meke damun El? Kamar wanda ya zauce ko wani abu ya taɓa tunaninsa? "That's what am going to tell you, El ya sauya ko dai akwai abin da yake faruwa ne?" Mai martaba ya numfasa bai ce komai ba ya shige babban sashinsa, Khalil kuma ya nufi wajan Oum Juwairah.


Halisa na zaune tana duba Assignment ɗin da aka bata juya littafin kawai take amma ta rasa ta ina zata fara. Tunda ta dawo gida bata ji motsin Yaa Sheikh ba, ko taji Ummul ta ce akai masa abinci. Ta miƙe tsaye jikinta sanye da wata riga mai kyau wacce tazo mata iya gwiwa wandon jikinta 3gauter ne. Zahrah data fito daga ɗakinta zuwa parlour hannunta riƙe da plate ɗin da aka soya masa ƙwai ta kalli Halisa ta ce. "Ke ubanwa ya ce kina saka wannan kayan a cikin gidan nan?" Halisa ta kalleta ta ɗauke kai ita bata ita take ba "Kan uba? Ke dan ƙaniyarki ni sa'ar ta ruga ce ina magana kina jina?" Halisa ta murguɗa baki cikin tsiwa ta ce "Ban ɗauka magana ki ke ba" hannu ta ɗaga zata wanka mata mari taji an riƙe hannu, ƙamshin Roja daya cika parlourn ya gama shaida mata wanda ya riƙe ta. Ta juya da sauri har lokacin yana riƙe da hannunta ta ce.
"My Excellency yarinyar ta fara raina ni ne, ka barni naci.." wata kyakkyawar tsawa ya daka mata wacce bata taɓa jin irinta ba, Halisa ta firgita da tsawar ga Yaa Sheikh ta kwasa da gudu zuwa part ɗin Ummul tana haki.
Zahrah ta ce "Tsawa kai mini akan wannan mara gata da ƴancin ƴar aiki na ce ita ga Yaa Sheikh?" Ya saki hannunta fuska kame yana gyara yanayinsa ya ce.
"Ba a kanta ba,
Akan zagin da ki ke mana, idan zaki ki bari kije waje" ya faɗa a taƙaice kwarjininsa yasa Zahrah kasa tanka masa a ranta kuma ta ɗauki niyyar cin uban Halisa. Cike da kissa da buƙatar mijinta kusa da ita, cikin dake jikinta ya ƙara sanya mata son kasancewa da namiji ƙwarai da gaske. Ta rungome Yaa Sheikh tana shassheƙar kuka ta ce "Amma kasan ni ba sa'ar ta bace, kawai zan mayar da ita, tunda akwai masu aiki a gidan" ya yi mata shiru shi dai bai kuma hanata rungome shi ba, kallo ɗayan da ya yi mata ya karanci yanayinta. Ganin abin da take ƙoƙarin yin yasa Yaa Sheikh faɗin. "Asstagafirullah Allah" Zahrah ta tsaya tana kallon shi kafin ta ce "what do you mean by that? Am your wife exit?" Ya zameta daga jikinsa tare da juyawa zuwa part ɗinsa sai da ya kusa shigewa ya ce
"Lokacin Sallah, akwai alwala tare dani" tai murmushin jin daɗin ganin ya juya da alama alwalar da yake riritawa ta lalace dalilin rungumar shi da tayi. "Shikenan, anjima zan zo" ta juya zuwa nata part ɗin.
Ummul ta kalli Halisa dana cewa "Wannan hakin fa? yana da kyau ki nutsu sosai matar malam" Halisa ta dafe ƙirji ta ce "Wallahi na tsorata sosai Ummul, Allah yasa ba dokan Anti Zahrah ba" Ummul ta dubeta ta ce "Doka wanne iri, ni wannan Assignment ɗin naki ba Abin da na gane, kije wajan Abban naki" ta kwanta cinyar Ummul tunanin Dadarta ya faɗo mata a rai. Tai shiru can kuma ta ce "Ummul Abba mijina ne ko?"
"Me ya sa kike tambaya matar malam?" Cewar Ummul. Halisa ta miƙe zaune zance na cinta ta ce "Ummul naji baya ce mini matar shi, kuma ni bana son naga Anti Zahrah..." Wayar Ummul tai ƙara hakan ya hana Halisa ƙarasa maganar. Bayan kammala wayar Ummul ta ce "kije ya duba littafin naki,ko a buge ki a makaranta" Halisa ta ɓata fuska ta ce "haka kurum ya dakeni, zaro ido naga ya yi fa?"


"Ko zai daki kowa,
Ai banda matar malam, kawai baya son taurin kai ne, kuma na lura kina da shi tun ba yau ba" Halisa zata sake magana Ummul ta ce "Tashi kije, sai ki dawo kici dinner muyi karatu" ta miƙe tana ɗora hula akanta tana tafe tana waƙa da fillatanci. A hanya taci karo da Bara'at tai mata murmushi.
A hankali ta shiga parlourn dake part ɗinsa, gaba ɗaya baya cikin parlourn sai kyakkyawan ƙamshin daya bari wanda yake tashi a hankali, tabi ƙofofin dake parlourn da kallo ta rasa wanne Kofar bedroom ɗinsa, a hankali take tafiya kamar mara gasky tana raɓewa jikin bango ta shiga leƙa wani ɗaki tsarin bedroom kaɗai ya tabbatar mata shi ne. Ji tayi an tsaya a bayanta ta juya da sauri taci karo dashi tsaye towel a hannunsa yana tsane gashin kansa daya kwanto, ganin ruwa na zuba a jikinsa tasan wanka yayi, maimakon taji kunya a matsayinta cikakkiyar bafullatana sai ta zubawa wani waje a jikinsa ido. Ya tsare ta da idanu.
"Abba" ta faɗa dimple ɗinta na lomawa ya ɗauke kai ya ce. "Me kike leƙe? Kin yi ajjiya ne?" Ya tambaya yana bata hanya ta tura baki fuska a narke sai juya bakinta take ta ce "Ummul ta ce ka koyan karatu, ni ba kai nake nema ba" ya dubi bakin maganar da kyau, ya ɗauke kai wato fushi take har yanzu.
Ganin yaƙi bata amsa ta saki kuka tana juyawa zata bar wajan, ya damƙi hannunta ya dawo da ita gabansa. Cikin kula da tausasa harshe ƙamshin shower gel yana fita daga cikinsa ya saka hannu tare da tallafo haɓarta ɗaya hannun ya dafa kanta dashi, tayi saurin riƙe ƙugunsa da duk hannunta biyu.
"Abba" ta ƙara faɗa idanun na cika da hawaye wanda suka ƙarawa idanunta sheƙi. "Rigima dai matar malam, nayi busy banje makaranta ba" ta tsora masa idanu masa idanu tana ƙara riƙe ƙugunsa ta ce "To darasi zaka duba mini, Abba kuma me ya sa Anti Zahrah take riƙe ka" ya saki fuskar yana dafe kai ta saki kuka zata juya ta fita ya saka hannu ya ɗaga ta cak tare da yin bedroom ɗinsa da ita...




If you read for free🤷🏾‍♀️ it's 500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616.Kokawar ƙwace kanta take amma ta kasa ya sauke ta saman kujerar dake kusa da bed ɗin ɗakin nasa, bai kula ta ba ya nufi deep freezer ya ɗauki Apple guda ɗaya wacce tai sanyi. Cikin nutsuwarsa da son kame kansa daga yanayin da yake ciki ya nemi waje saman gado ya zauna, kyakkyawan numfashi ya sauke yana ƙara daidaita kansa a karo na babu adadi. Ya ɗago kai yana duban direction ɗin da take, dole sai ta sanya ma gantu ya miƙa hannu cikin taushin murya ya ce..
"Zonan naji, rigimar me ce?" kanta a ƙasa ta ƙarasa inda yake domin bata iya bijirewa umarninsa. Ya dubeta da kyau amma taƙi yarda ta kallesa cikin son jin meke faruwa ya kamo hannunta zuwa inda yake zaune muryarsa har kullum a taushashe ya ce. "Ya akai matar malam? waye?" Hawaye na sakko mata ta ce "Abba kai ne, Mother ta ce kai miji na ne, me ya sa kake bari Anti Zahrah take taɓa ka" ya dafe kansa cike da mmkin kaifin bakin Halisa ya ce "Ba zaki bar mganar mijin nan ba? You're too young to understand that"
"Abba ina son ka ai" Ya girgiza kai ya lura rigima take ji kuma ta shirya bashi kunya a Idanun kowa. Yana mamakin yadda maganar miji ta zauna a bakinta raɗau kamar wacce akewa bita akan hakan. Ya dubeta yana dawo da ita gefensa tare da riƙe hannunta ya ce "Matar Malam ki bar mganar mijin nan, ba zaki gane ba, ki dai bar Anti ta faɗa ok?" Ta maƙale ka faɗa alamar bata amince da zancan ba kaifin ta ce "Abba...." Sai kuma tai shiru ya ɗago kanta tare da tallafo haɓarta yana duba cikin idanunta da hawaye ya kwanta. "Matar malam" ta marairaice fuska tare da faɗin "Abba yaushe zan zama matar malam ɗin? Kuma yaushe zan zama kamar Anti Zahrah nima na dinga rungomeka?" Ya kau da fuska tare da lumshe idanunsa a hankali ya ce "Baki son Antin naki tana haka? Ni kuma fa" ya ƙare maganar yana ƙara riƙe fuskarta a hannunsa da kyau, gaba ɗaya ta marairaice fuska ita a dole bata son abin da Zahrah ke masa, haka kurum ranta ke ɓaci taji kuka yazo mata ta ce "Abba zanna yi maka, da safe da rana, da daddare" ya shafa kanta cikin nutsuwa ya ce.
"Kada mu fara haka, ki tsaya a ƴar rainonki" ta langwaɓe kai ta ce "Abba ni ban son rainon Ummul ta ce kayi mini karatu" bai biyewa surutun nata ba, ya amshi littafin nata duk dan a rabu lafiya, burinsa kuma bai shige ta tafi part ɗinsa ba, ko zata barshi ya samu salama daga surutun nata mara dalili da toshe.
Cikin sauƙin harshen yake mata bayani akan Social studies ɗin, da kuma muhimmancinsa. Ya kama hannunta ya ɗora saman littafin a hankali ya ɗora nasa hannun akan nata ya fara nuna mata yadda zatai rubutu, yana lura da ƙwazonta ko dan akwai son karatun a ranta duk abin da ya nuna mata ɗauke shi take.
Ta ɗago kai ta kallesa taga hankalinsa baya kanta gaba ɗaya ya tattara nutsuwarsa zuwa ga abin da yake nuna mata.
"Abba" Halisa ta faɗa tana ƙarewa fuskar shi kallon yaƙi kulata ta leƙa fuskar shi ta ƙara cewa "Abba kana da kyau sosai, kaga gobe idan naje makaranta zance mijina ne ya yi mini aikin ko?" Nan ma bai kulata ba amma tsat yake ɗauke zancan nata a zuciyarsa tasbihi kawai yake. Taja gemunsa cikin sauri ya miƙe tsaye yana damƙa mata littafin tare da janta zuwa bakin ƙofa kamar an masa dole ya ce. "Ki kula, akwai sanyi" ta ɗaga kai tana faɗin "To Abba" har ta juya zata fita ta dawo da sauri zuwa bedroom ɗin Yaa Sheikh kuma a lokacin ya juya hannunsa ɗauke da azkar na dare yana dubawa..
Kyakkyawar rungumar data bashi da baya ya sanya Azkar ɗin suɓuce masa cikin In-inar data zo masa a lokacin zufa na yanko daga goshinsa ya ce.
"Yaaa....yaaaa... Allahu ya ya... Ya Rahman, Yasubuhanallah" ta saki dry tana riƙesa ta ce "Abba kaga nayi maka ta dare sai da safe" kasa magana ya yi tana sakinsa ya buɗe ƙofar bathroom ya shige ciki... Cikin farin ciki da murna yau itama tayi abin da Anti Zahrah keyi ta nufi part ɗin Ummul. Ummul ta kalleta ta ce "Kin dai gane karatun ko?" Ta ɗaga mata kai kawai tana jan plate ɗin da Ummul ke mata, tana cikin cin abincin ta ce "Ummul kin same?" Ummul ta girgiza kai ta ce "Sai kin faɗa matar malam" Halisa ta ture abincin dan ba wata yunwa ta keji ba ta ce.
"Me ya sa gumi ke fitowa a goshin Abba? Kuma naga wani abu a jikinsa ba, duk sanda na gani kaina juyawa yake" Ummul a zuciyarta addu'a take Allah ya sa ba wata maganar da zata bata Kunya zatai ba, ko wani abu ne ya faru tsakaninta da Yaa Sheikh ɗin take son faɗa, duk tai mamakin haƙurinsa, daya kawo har yanzu, ta riga tasan waye Yaa Sheikh da kuma yadda ya ɗauki al'amarin Halisa da girma ko yana jin tsoran yanayin rigima da ƙuruciyarta ne?.
Halisa ta dawo da Ummul daga tunanin data tafi ta hanyar faɗin "Ummul ni ina son Abbana" Ummul ta ce "Kina iya bakinki, ba dan abinci kawai Ubangiji ya bamu ciki ba, hadda ɓoye maganar da bata da ikon a faɗa da riƙe sirri, ki nutsu idan kina wannan shirman Abban naki ba zai so ki ba" Halisa ta kwanta tana juyawa Ummul baya ta ce "to naga mijina ne, kuma ina son sa" kamar wacce aka tsikara ta miƙe da sauri domin abu biyu ne ya faɗo mata a wannan lokacin, da maganin da El-bashir ya bata, wanda take tunanin shi ne ya sanya Abban nata Yaa Sheikh yake fitar da zufar goshinsa, sai kuma tuna Dada da tayi.
Ummul tabi bayanta da kallo sai kawai ta girgiza kai ta ce "Ubangiji ga Danejo ka shirya mana ita, Allah ka kawo zama na har abada tsakaninta da Aliyu, ita ce farin ciki Aliyu, Aliyu shi ne garkuwarta"


Halisa na fita ta nufi part ɗin Zahrah lokacin tana tsaye gaban madubi sai turare take fesawa ajikinta, ta sanya wasu kaya kamar zata gasar rawa a club Halisa ta ce "Anti" ta juya ta kalleta ta ce "wai ke wacce daƙiƙiya ce ne? Ko acikin ƴan fulani ke daban kike, kawai ki faɗo ɗaki kamar wata dabba?" Halisa taji zagin har ƙasan zuciyarta ta kalli Zahrah ta ce "me ya sa kike haɗani da dabba? Bayan ni mutum ce kamar ke?" Zahrah ta tsaki ta ce "baki da wani suna da ya shige haka, and you'll never be like me never" ta goge hawayen idanunta ta ce "Yaushe zan miki aikin ki? Ina son ki mayar dani rugarmu, ban san haka kike ba kinyi al'ƙawarin kula dani da kuma Dadata" Zahrah tai wata dry ta ce "Aikin kin kusa gabatar da shi, dan kin gama zan mayar dake nima zamanki bai mini ba, yanzu bani da lokacin zani wajan mijina"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login