Showing 117001 words to 120000 words out of 197828 words

Chapter 40 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9312

tasan ba zai jure wannan sabon al'amarin ba.
"Yanzu ya ake ciki"?
Cewar Mother Dr ya ƙara cewa "Sallama zamu bata, a kula da hannunta wanda ya karye, kada a tsauwala tunaninta wajan tuna wace ita, ku fara koya mata dukkan abin da kuka san zai zama mai amfani a gare ta" Ya yi ɗan rubuce-rubuce, kana ya miƙawa Yaa Sheikh, ya sanya hannu ya amsa yana duba abun, some of medicine ne wanda zatai using da su..
"Thank you Dr"
Yaa Sheikh ya furta cikin murya mafi sanyi rauninsa ya bayyana sosai akan fuskar shi, da muryar shi, hatta wanda baya fahimtar raunin na Yaa Sheikh yau ya fahimta kuma ya gane, sun ƙara tabbatarwa Halisa Danejo Rome ita ce duniyar Yaa Sheikh ita ce kuma raunin shi.
Abba Hakimi ya juya ya fita zuwa Room ɗin El-bashir, Mai martaba ya kama hannun Dada suka fita, haka mother.
Room ɗin ya rage daga Ummul sai Yaa Sheikh da kuma Halisa dake maƙale a bayan Ummul ɗin. "Fito daga bayana, tunda yau Abban naki ki ke gudu" ta saka hannu ta zaro ta daga bayanta tare da dawo da ita gaba.
Ummul ta tsareta da idanu ta ce.
"Ya sunanki?"
Halisa ta tsare Ummul da idanu ita ma ta ce
"Ya sunanki?"
Ummul ta dafe kai ta ce "yau naga abin da ya fi zare tsayi ni Ummul-khairy" ita dai Halisa kallon Ummul kawai take, bata san mene so ko shaƙuwa amma taji hankalinta ya kwanta da Ummul.
Ummul ta juya wajan Yaa Sheikh da yake tsaye ya harɗe hannayensa a ƙirji tare da zuba musu ido, ganin idanunsa akan Halisa ya sa Ummul faɗin "Bari na je wajan El-bashir,sai na dawo mu tafi" bai ce komai ba sai lumshe idanunsa da ya yi
Ta kama hannun Halisa zuwa bakin gadon tare da zaunar da ita ta ce
"Yanzu zan dawo,zauna nan" tai shiru tana marairaice fuska zatai kuka ta ce
"Yanzu zan dawo, idan ki kai kuka to zan barki" tayi shiru Ummul ta ce
"Ki ce to" a sanyaye ta ce
"To!" Ta nufi hanyar fita har ta je bakin ƙofa ta juya ta kalli Yaa Sheikh sai kuma ta fita tana girgiza kai. Yaa Sheikh ya sauke ajjiyar zuciya wacce ta tafi da nauyin zuciyarsa, gently ya nufi hanyar fita daga room ɗin, yana zuwa ya ja ƙofar tare da rufewa ya murɗa mata key.
Ya jingina da jikin ƙofar yana jifanfa da wani irin hargitsatsan kallo, wani irin sabon shauƙinta na fisgar shi, burinsa ya haɗa gangar jikinsa da nata ko zai samu daidaito a zuciyarsa,
Kan ta a ƙasa tana kallon fararen yatsun ƙafarta har bata san ya ƙarasu wajan ba, sai ji tayi a saka hannu tare da ɗaga ta cak zuwa tsaye.
Wani irin zaro ido tayi ƙirjinta ya buga tsoro ƙarara ya bayyana akan fuskar yarinyar ta,
bata san me zata ce ba domin sai an faɗi magana take maimaitawa ta shiga girgiza masa kai tana yarfe hannunta, a hankali ya ɗora hannayensa saman shoulders ɗin ta, ya kalli fuskarta, baki ta buɗe zata saka ihu ya ɗora yatsar shi a bakin ya ce "Shiiii" ta maƙale kafaɗa ta zare kafaɗarta zata gudu ya yi saurin kamota tare da haɗata da jikinsa, bayanta ne a jikinsa ita kuma tana kallon direction ɗin gadon, hannayensa duka biyun zagaye da cikinta ya rungometa so tight fuskar shi a wuyanta a hankali yake manna mata sajan fuskarsa mai laushi tare da goga mata tsinin hancinsa a fatar wuyanta.
Tsigar jikinta ta shiga tashi, jikinta ya ɗauki wani abu ya fara yawo a jikinta, haka nan taji abin da yake mata har tsakiyar ranta kuma tana buƙatar shi, ta rufe idanunta hawaye tuni ya gama wanke mata fuska har tsoran kallon fuskar shi take sbd yadda yake mata muni acikin idanunta.
"Why?" Ya ce a hankali muryarsa bata fita sosai komai ya dai na masa daɗi. Halisa kokawar ƙwace kanta take amma ya yi mata rungumar da ba zata iya hakan ba, ya juyata suka fuskanci juna idanunsa na yawo a kanta ya kama hannunta tare da ɗorawa daidai ƙahon zuciyar shi ya ce
"Me ya sa matar malam? Ni ne Abbanki, Modibbonki, Yaa Sheikh na ki, ki daina kafin zuciyata ta buga" taƙi kallon shi tai kicin-kicin da ranta. Ya ƙara manna hannun a ƙirjin shi yana tallafo fuskarta ya ce
"Zaki bi ni ko? Nasan kina son Abbanki" kamar wacce aka raɗawa a kunne ta yi saurin faɗin.
"Na tsaneka!"
Kalmar ta daki zuciyar shi, har sai daya runtse idanunsa ya fesar da Iska, a hankali ya buɗe idanu suka haɗa ido, ba tsoro ko ladama bare fargaba cikin ƙwayar idanunta, kafin ya yi motsi ta ƙara cewa
"Na tsaneka, na tsaneka na...," Caraf ya kame bakin domin ba zai iya ɗaukan kalmar tsana daga gare ta, ko a wasa balle har ƙasan zuciyarta maganar ke fitowa.
Ta zaro idanu waje ta kuma kasa koda motsi ya yi mata rumfa da faffaɗan ƙirjin shi dake fitar da ƙamshin Roja
Hannunsa ɗaya riƙe da kanta ɗaya kuma ya riƙe ƙugunta ya haɗa da jikin shi. Wani irin hot kisses yake mata wanda shi kan shi ya san ya yi abin da zuciyarsa ke umartar shi kenan, ya yi abin da yafi ƙarfin ta da tunaninta bakiɗaya, gabaɗaya ya sauke zafin goma da ashirin ɗin da aka tara masa a bakinta, labɓanta sukai jajir maimakon tayi ƙorafi sai yaga tana lumshe idanunta alamar abin nayi mata daɗi sai numfashi da ajjiyar zuciya yake saukewa, hannunsa guda ɗaya a bayanta yana bubbugawa kaɗan kamar ƙaramar yarinya.
Knocking ɗin ƙofa ya dawo da Yaa Sheikh daga duniyar da ya tafi ya zare bakin shi daga nata a hankali, ita kuma tayi saurin ƙasa da kanta he still holding onto her.
Ya sauke numfashi ya daidaita nutsuwa da kamewar shi, ya yi over acting da yawa hannunta daya karye ya kama yana kallo, a nan ya fahimci ɗorin bai daidai ba duba da yadda fatar hannun tai laushi har ta fara kure, ya ɗora tafin hannunsa a tsakiyar nata tare da saka babbar yatsar shi ya danna, ta saki ihu saboda zafin da hannun ya ɗauka, ya yi saurin saki yana shafa sumar kanta yana faɗin
"Sorry, Sorry!"
Har lokacin knocking ƙofar ake Yaa Sheikh kuma yaƙi sakinta shi su yake ko gwarancin tayi yaji muryarta amma tayi shiru sai kuka take tana kaiwa hannun shi cizo, ya haɗata da jikinsa tare da ɗora kanta a ƙirjinsa a hankali ya sauke numfashi ya ce.
"تعالي إلي أو خذيني .و أحرص على قلبي لأنك فيه. أريدك أنت،لاسي أخرا فقط أنت".
Ya faɗa a taushashe, yasan gabaɗaya ba fahimta take ba, da ace tana cikin hankalinta to zata gane larabcin na shi,amma yanzu jin maganar ta shi take kamar ta kurame,
A zahiri kuma idan ka cire larabcin yana nufin
_“Come back to me, or take me with you. Take care of my heart, because you're in it. I want you, nothing ey, just you_”
Ya manna mata sumbata a goshinta irin ta sunna da kuma cikakkun Malamai tare da sakinta ya nufi ƙofar, yana sakinta tayi saurin kwanciya kan bed ɗin asibitin ta jawo bargo ta rufe gabaɗaya jikinta har fuskarta, abu goma da ashirin ya shiga juya mata tunani, Kiss ɗin Yaa Sheikh ya tsaya a zuciyarta daram! Kamar yadda ƙiyayyar shi ta samu gurbi mai girma a zuciyarta, kuma tana shi she needs more na kisses ɗin, tana jin kuma ba zata sake zuwa inda yake bata ta saka hannu ta ƙanƙame jikinta ta hannunta ɗaya da yake mata masifar zafi da zugi.
Yana buɗe ƙofar yaga Mother da Ummul tsaye suna magana, ganin shi tsaye fuska kame ya sa suka ratsa ta gefen shi suka shige, bai koma room ɗin ba, ya nufi room ɗin da El-bashir yake ciki, a nan ya samu Mai martaba yana yi wa El-bashir faɗa kamar ƙaramin yaro, Abba Hakimi kuma na tsaye Dada na zaune saman kujera, ƙamshin Roja data ji ya sa ta ɗago kanta ta kalli inda Yaa Sheikh ya ke, ta saki murmushi tana faɗin.
"Yanzu nake shirin zuwa wajanka Besty" ya ɗan kalleta sai bai ce komai ya lura bata yi masa kallon siriki shi kuma yana mata haka da idanun tsarkakkiyar zuciyar shi.
Mai martaba ya ce
"Ka bani mamaki Mubasshir, ban ɗauka zaka iya jin ƙiyayyar wani musulmi ba, balle mutum kamar Yaa Sheikh, idan ka shiga aikin police da wannan niyyar ne, ya zama dole ka shirya barin aikin dan ba zan lamunta ba" ya yi shiru domin ya manta rabon da ya yi magana mai tsayin haka, ya sauke numfashi kafin ya kalli El-bashir ya ce
"Garin son zuciyarka ka sanya Zuciyar wani cikin zullumi da damuwa, ka ɗauke masa farin cikin shi" ya ƙara yin shiru kafin ya ce.
"Say sorry to him, ka nemi ya fiyar shi yanzu nan Mubasshir" El-bashir ya ɗago kansa tare da kallon Yaa Sheikh a hankali ya ce
"Am sorry Abba, ka yafe mini" bai san cewa har kawo yanzu Yaa Sheikh bai ji zafin shi ba, yasan duk abin da El-bashir yake akwai wanda ya ɗora shi akan hanya, ya taka a hankali zuwa bakin gadon tare da neman waje ya zauna
El-bashir ya sake kallon Yaa Sheikh ya ce
"Kayi haƙuri Abba" Yaa Sheikh ya jinjina kai tare da kama hannun da yake mai lafiya ya riƙe a na shi, nan take soyayyar Yaa Sheikh ta samu gurbi a zuciyar El-bashir ya yi ta kallon Yaa Sheikh.
Ya sauke numfashi kafin ya ce "Ya jikin?"
"Da sauƙi Abba, forgive me please, na ɗauka kai na ka kashe mini Ammi ka yafe mini" Yaa Sheikh ya ce "Shhhh! Sannu, Allah ya sauwaƙa" El ya ɗago kai ya ce
"Ya jikin Sister ɗina? Nasan bata so na" Yaa Sheikh ya girgiza kai kamar ba zai magana ba sai ya ce.
"Zaka iya gina soyayyarka a zuciyarta yanzu, idan akwai wanda bata so yanzu to ni ne" ya saki hannun El-bashir tare da miƙewa ya yi waje, Abba Hakimi yabi Yaa Sheikh da idanu cike da tausayawa, da sauri Dada ta miƙe suka jere da Yaa Sheikh magana take masa yana jinjina kan shi, a hankali yaja ya tsaya tare da juyawa ya kalleta ta ce.
"Mene kuma Besty?"
Fuska kame ya ce "Koma" ta ce "To ai mun daɗe bamu haɗu ba, akwai abin da nake son faɗa maka" ya yi mata shiru zata sake magana ya buɗe mata idanu cikin gajiyawa ya ce
"Ya Allah, surutunki Ƴar fillo ta ɗauka ashe,jeki" ya nuna mata hanya" ta juya ba tare da ta ce komai ba. A hankali Yaa Sheikh yaci karo da Ummul ta ce "Muje ko?" Ya kalleta ya kalli bayanta ta gane me yake nufi sai tayi kamar bata gane ba tace
"Ya akai kuma?" Ya marairaccen mata fuska kamar ba shi ya ce "Ummul kin gane" ta ce "Ni ban gane ba, tunda sanin gaibu sai Allah" a hankali ya ce "Matata"
Fuska haɗe ta ce
"Yaushe Arɗona ya zama haka ne? Koda yake mace na sauya halayya da ɗabi'ar namiji daman, ba shakka Halisa tayi tasiri wajan sau yaka" bai cewa mahaifiyar ta shi komai ba ta ƙara cewa
"Ba zaka samu yadda ka ke a wajanta ba yanzu, dole ka nemi haƙuri ka sakawa zuciyarka Aliyu" sai a lokacin ya kama hannun Ummul ya ce
"Yaushe haƙurin nawa zai ƙare? Nayi na kuma Ummul, I want her in my life" sai ya bata tausayi tasan duk Abin da Yaa Sheikh ya ce to har zuciyar shi ne, idan abu yafi ƙarfin shi yana faɗa mata kai tsaye ne.
"Muje mota" ya kasa motsawa ta ce "Arɗo ka gane ka fahimta, Halisa zata koma masarauta kafin komai ya daidaita sun tafi gida da Barrister Maryam, kai ma kuma zaka bi ni ne" Ya dinga kallon Ummul da rikitattun idanunsa, shi kam a yanzu a shige level ɗin da za ana gindaya masa wasu sharuɗa, ganin ran Ummul ya fara ɓaci yabi bayanta zaune ya sameta gaban mota wajan driver ya zagaya mazaunin mai zaman banza ya zauna, bakinsa ɗauke da addu'a ko zai samu sassauci daga zuciyar shi.
Sun yi nisa akan titi ta ce
"Lokaci ya yi da zaka koma Yola, ka ɗauki ragamar Rugar Bello a hannunka, ka maye gurbin mahaifinka, suna buƙatar ka a can" ya yi shiru ta juya ta kalle shi, taga ya kifa fuskarsa a tafukan hannayensa ta ce "Zamu matsala da kai idan zaka bayyanar da damuwarka a fili" ya ɗago kai idanunshi sun yi ja sun ri ne ya ce.
"'ana 'uhabuha"
Ta ce "Ni na nasan haka, amma ita fa? Iyayenta Abba Hakimi fa? Sun sani,ko ka taɓa furtawa kana son ta? Ka aureta without her permission dana iyayenta baka taɓa cewa kana son ta" ya yi shiru can ya nisa ya ce
"Kamar ba sai na faɗa ba, amma ki faɗa musu" ta kalle shi kawai ta girgiza kai ta ci-gaba da driving har zuwa Na'ibawa, gatekeeper ya buɗe mata gate ta shi ga da motar a hankali tai parking a harabar gidan tare da fitowa, Yaa Sheikh ya fito kan shi na sarawa sbd ciwon da yake masa zuciyar shi tayi nauyi.
Idanunsa ya sauka akan wani dattijo dake zaune a saman kujera, kamanin shi da Yaa Sheikh sun ɓaci komai nasu iri ɗaya, Ummul tai murmushi ta ce "Your grandfather" Yaa Sheikh ya ƙarasa Dattijon ya miƙe riƙe da sanda ya ce "Yau gani ga babban malami lale" gabaɗaya suka shige cikin gidan.
A can gida Mother ta nunawa Halisa komai, hankalinta ya kwanta ganin babu Yaa Sheikh a gidan, Zahrah tana ɗakin tana aikin kuka tuni akaiwa iyayenta waya ana buƙatar ganinsu.
Misalin ƙarfe 10:30 na dare Mother ta tura ƙofar bedroom da Halisa ke ciki, a zaune ta sameta riƙe da hannun alamar zafi yake mata, ta nemi waje ta zauna cikin kulawa ta ce.
"Kina son sanin sunanki ko?" Ta ɗaga mata kai ta ce "Sunanki matar malam, kin gane?" Ta ce "Matar Malam?" Mother ta ce "Eh, sunanki kenan yanzu ki kwanta ki huta" ta nuna mother hannunta ta ce "Zafi" ta faɗa a hankali, hannun ya kumbura sosai ta ce "Ina zuwa" ta miƙe tare da fita waya ta ɗauka ta kira number Yaa Sheikh tana ta ringing not answering, dole ta ajjiye ta ɗauki maganin rage zugi ta bawa Halisa tana nan zaune har barci ya ɗauke ta. Abin da bata sani ba tun 9 Yaa Sheikh yake cikin gidan a part ɗin shi ba wanda ya sani, haka can ma Ummul bata san fitar shi ba, yana kwance Sa juyi yake rana ɗaya tal amma ya faɗa idanunsa ya fito, ya miƙe tsaye yana ɗaukan jallabiya ya zura a jikinsa tare da saka slippers ya buɗe ƙofa ya fito, parlourn ba kowa alamun kowa ya kwanta, direct bedroom ɗinta ya nufa ya tura tare da shiga yana sallama a ran shi, duhu ne ya mamaye bedroom ɗin amma yana hango yadda take zaune a tsakiyar gadon riƙe da hannunta tana shassheƙar kuka zafin da hannun ke mata yasa ko ƙarar ƙofar bata ji ba, a hankali ya zare Jallabiyar jikinsa ya rage daga shi sai trousers ko riga babu, surar jikin shi ta bayyana idanunsa ya juyewa bakiɗaya, hannunsa riƙe da kwalbar man zafi ɗaya kuma na gyaran karaya ya nufi bed ɗin, a hankali ya zauna ba tare data sani ba ya tsaya daidai bayanta murya can ƙasa ya ce. "Matar malam" ta yi saurin ɗago kanta tunda ta sakawa ranta sunanta kenan kamar yadda Mother ta ce, bata ɗauki murya ba, cikin sauri murya na rawa ta ce "Hannu, zafi ban so" ya ajjiye abin hannunsa tare da saka hannu ya jawota jikinsa ya shiga balle gaban rigarta yana gamawa ya yi cilli da rigar ta sauke numfashi ta ƙara cewa "Zafi" ya ɗora kan shi a wuyanta ya zura hannunsa ta ƙasan hannayenta ya riƙe hannunta mai ciwo, ɗaya hannunsa kuma yana cikinta yana shafa ramin cibiyarta a hankali ya shiga hura mata iska a kunne tai luff jikin shi barci na fisgarta, da sauri kuma ta ce
"Waye" ya ciji fatar kunnenta in a romantic style ya ce "Malam ya zo wajan Matar Malam yara sunna.....Idan Ba Ke By NimcyLuv


Jimeta/Yola
Njoɓoli Rugar Rome


Gudu Saniyar take tana bin ta a baya itama, hannunta riƙe da sanda na korar Nagge, tamkar wanda suke wasan tsere haka Saniyar ke gudu a cikin jejin ita ma bata fasa bin ta ba, sauran Naggen suna gefe guda ko wacce na cin ciyayi wanda bisa kuskure tana can tana bin Saniya ɗaya tilo, sauran Naggen suka faɗa cikin gonar wani manomi, a yunwace suka rufarwa albarkatun gonar. Cikin siririyar muryarta mai nuni da Yarintar ta, da kuma nuna cewa ita ɗin zallar bafullatanar Yola ce ƴar Usul. "Waru! Waru! Waru" shi ne abin da yarinyar ke ta nanatawa cikin hausarta ta Fulani, yayinda Saniyar tuni tai mata nisa cikin gajiya wa da bin Saniyar ta tsaya a wajan wata gaɓar ruwa tana riƙe ƙugunta ta ce "Bone, lalashewa ta samu Nagge Aradu" da sauri kuma ta ɗauki sandar tana ƙara yin kan Saniyar ganin ta tsaya da gudun da take, cikin sa'a ta cimmata tana zuwa ta kama ƙahonta tare da ƙifƙifta idanunta alamar zallar fitsarar dake tattare da ita "d'ume ngid'd'a?" Ma'ana "me kake so?" Kallon ta Saniyar ta yi sai kuma ta kaɗa jela tare da zubewa a wajan ta shiga shura ƙafafuwa kamar zata mutu, cikin tsoro haɗi da razani HALISA ta ce "Jomirawo ka taimakeni" ta faɗa tana kallon Saniyar wacce tai male-male a ƙasa ga wani ruwa mai kama da jini na fitowa ta ƙasanta, kuka Halisa ta sanya domin idan Saniyar ta mutu a nan wajan ta shiga uku, itama watan mutuwarta ya kama. Tsayar da kukan tai kafin ta fara duba cikin jeji babu kowa sai ita, ga wani kwantaccen baƙin hadari dake ƙasa wanda a koda yaushe zai iya tashi.


Juyawa tayi ta nufi wajan wata bishiya inda ta hangi ƙaramar igiya a jiki, tana zuwa jikin bishiyar ta zame hular Fulanin dake kanta, nan da nan sumar kanta ta sauka wacce take jajir babu alamar baƙi ko ɗaya, gashin ba wani cika ne dashi ba, kawai tsayin gashi gareta, domin har fatar tsakiyar kanta ana iya ganowa. cikin sayin jikinta ta fara jan igiyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login