Showing 69001 words to 72000 words out of 197828 words
Chapter 24 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
ba tare da ya ce komai ba, sbd kansa dake juyawa sosai. A haka ya nufi Part ɗinsa.
Yau da murna Halisa ta dawo sbd yaba mata da Ayyan ya yi harda gift ya bata bayan ya ce tana da kyau. Wanka tayi tai sallah ya shirya cikin wasu english wears masu kyau.
Bata nufi wajan Ummul ba, kai tsaye wajan Abban nata ta nufa lokaci yana kwance akan bed ya yi rigingine. "Abba, Abbana" ta hango shi can bed kallon da ya yi mata yasa ta juya tare da dawowa ta ce "Assalamu alaika" ya amsa a ransa. Ta matsa kan gadon tare da hayewa saman gadon, kai tsaye ta yi wa kanta masauki a bayansa, ta zauna a bayan ta ce "Abba yau nayi ƙoƙari sosai, Teacher Ayyan ya ce ina da kyau kuma yana so na" ya mirgina tare da dawo da ita saman cikinsa ya riƙe hannunta ya ce "Uhm" ta shafa fuskarsa tana wasa da gemunsa ta ce.
"Amma Abbana nake so shi ne mijina" ya ƙurawa bakin indo yadda take juyawa babu sassauta zan can.
A hankali ya mirginata, ta koma ƙasan bed ɗin, shi kuma ya yi mata rumfa. "Abba" ta faɗa tana kallon idanunsa tamkar ba na Abbanta ba. Ya kame bakin surutun a hannunsa ya ce.
"Kina buƙatar darasi Matar Malam" ya shinshina wuyanta sak irin turaren daya siyawa su Maimoon da mother. Ta ce "Abba ai na san darasin" ya buɗe ido ya ce "Za dai ki sani" kamar yadda ya yi mata haka itama ta riƙe bakinsa, ya rufe ido yana janye jiki tare da jan duvet ya rufe jikinsa baki ɗaya har kansa, gaba ɗaya jikinsa rawa da karkarwa yake kamar mazari.
Ta miƙe a rikice tana faɗin "Abba, Modibbona, Abba" da sauri ta fita wajan Ummul ta amsa black tea kana tayi ɗakinta maganin wajan El-bashir ta buɗe tana zubawa a tea ɗin, ta juya shayin da sauri ta nufi bedroom ɗin, har lokacin yana kwance ta ce "Abba ga shayi kasha kaji" yai mata banza har zata janye duvet ɗin sai kuma ta tsaya a fili ta ce "Bari muji ko babu ɗaci shayin" ta ɗauki cup ɗin shayin tare da kaiwa bakin, tai karɓa ɗaya biyu har zuwa uku samun kanta tayi da shanye shayin baki ɗaya.....Zuciyar Yaa Sheikh tai kyakkyawan bugawa a duk lokacin da ya shiga wannan yanayin yasan akwai mummunan abun da zai faru da rayuwar shi. Ya akan iya gani a mafarki ko jikinsa ya shaida masa hakan ta hanyar sauyawa.
Ya zame duvet ɗin jikinsa a hankali ya mirgina zuwa gefen ya rufe ido yana sauke numfashi bakinsa ɗauke da addu'a. A hankali ya sakkowa daga kan bed ɗin zai shige bathroom idanunsa ya sauka a kanta tare da cup ɗin shayi. Kansa ya sara a nutse ya nufeta tare da durƙusawa daidai inda yake, yanayinta ya nuna sam ba lafiya ta kifa kanta a gefen gadon ta kifa kamar zata faɗi. A taushashe ya ce.
"Kee!" Shiru bata amsa ba abu ne mai wahala Halisa ta nutsu haka dole akwai wani abu. Ya riƙe numfashi ya ce "Ƴan matan Abba" nan ma shiru ya ɗora hannunsa tare da girgizata gaba ɗaya tayi baya zata faɗi ƙasa ya yi saurin taro ta zuwa cinyarsa.
Wani irin zafi yaji fatar jikinta ɗauka sosai tsoro ya kama Yaa Sheikh amma ya riƙe kansa ya riƙota tare da bubbuga kumatunta ya ce "Ƴar fillo, ƴar fillo!"
Ta buɗe idanu da ƙyar yana kallon fuskarsa amma ta kasa cewa komai sai hawaye dake fita daga gefen idanunta yana gangaruwa fuskarta. Yaa Sheikh ya juya idanunsa ya sauka akan cup ɗin shayin ya ɗauka da sauri ya jima yana kallon cup ɗin. Da sauri ya ajjiye ya riƙota gabaɗaya ya ce.
"Ina ki ka samu wannan? Waye baki?" Gaba ɗaya ya nemi rasa nutsuwata duk yadda yasu ya kame kansa daga shiga firgice ya kasa.
Ya jawota sosai muryata na rawa ta ce "Abbana" ya shafa kanta ya ce "Yes, Amanata. Me ya sa? Zaki kassara rayuwarki akai na?" Ta riƙe hannunsa jikinta na rawa na tsananin azabar da take ji, domin ji take kamar ana hura mata wuta a naman jikinta idanunta ya kasa tsayawa sai lumshewa take tana buɗewa ta ƙara riƙe sa ta ce.
"Kashe mini kai za ayi Abbana? Me ya sa? Me kayi don Allah kada a kashe mini kai" wani irin hawaye na zubuwa daga idanunta.
"Amanata why? Guba ki ka sha tayaya Abbanki zai jure?" Ta girgiza kai ta ce "Na san maganin mutuwa ne Abba, amma ni babu abin da zai mini, Abba ka ɗaukeni jikina bafii ciwo Abbana" ta saki numfasa, sanyi kawai take buƙatar ji zafin jikinta ya tsananta azaba da raɗaɗi kawai take ji, ta gwammace taji azabar da ace Abban nata yaji, ba zai iya ɗauka ba.
"Nothing... Nothing will happen Amanata" ta ƙara buɗe idanunta daya fara sanyawa ta ce "Modibbona" "Na'am ta Malam?" Ta kallesa da kyau ta ce "Modibbo bafii ina jin ciwo" tausayinta ya kama shi a zahiri ya yi mugun rikicewa, amma dake ya iya riƙe kansa fiye da kima ya girgiza kai kawa tare da ɗaukanta zuwa kan bed ɗin da ya kwantar.
Telephone line ɗinsa ya ɗauka ya kira wata number, babu jimawa akan ɗauka. A nutse ya yi bayani wanda aka kira ya ce. "Blood poison ne, wanda yake ƙona jinin mutum cikin ƙaramin lokacin, am on my way" Yaa Sheikh ya yi shiru tunani kala-kala a ransa yana ƙara maimaita kalmar _“Blood poison?”_ waye? Daga ina? Akan wanne dalili?. Dr ɗin ya ce "Ka bata taimakon gaggawa kafin nazo, zaka iya yin body connection da ita sbd ta samu zafin jikinta ya ragu a jikinta, ma'ana dai sanyin jikinka ya shiga nata, zafin jakinta ya shiga naka....,"
Yaa Sheikh bai tsaya jiran jin abin da Dr ɗin zai ƙarasa faɗa ba ya ajjiye wayar tare da nufar bathroom, gaba ɗaya ya zare sutturar jikinsa ya rage daga shi sai farar singlet da trouser a karo na farko wani zaiga jikinsa kuma waninma ƴar rainonsa.
Ya sakarwa kansa shower da ruwa mai mugun sanyi, bai taɓa wanka da ruwan sanyi ba sai warm water amma yau shi ne tsaye shower na dokan tsakiyar kansa, sai daya jiƙe sosai sai ko'ina na jikinsa ɗiga yake kafin ya fito daga bathroom ɗin.
Direct bed ɗin ya nufa tana kwance ba zaka taɓa ɗauka tana da rai ba, sbd ita kaɗai ta san abin da take jin bakinta wani irin ɗaci ya yi idanunta ya fara yin fari sosai, da hanzari ya hau kan gadon yana ɗaukanta tare da zaunar da ita saman cinyarsa, ta buɗe ido tare da zuba masa su alamar "Me zakai Abba?".
Ya saka hannu ya shiga ɓalle gaban rigar ta, ita dai kallonsa kawai take ya zame rigar tare da yin cilli da ita ya rage daga ita sai farar vest da White Padded bra sai under wear. Ya saka hannu zai zare vest ɗin yaji ta riƙe hannun, yana ɗago kai suka haɗa ido, ta rufe ido ta buɗe kai tsaye ya fahimci me take nufi.
Ya ɗora hannunsa akan ta yana shafa sumar kanta a taushashe ya ce. "Abbanki ne amanata, ki nutsu" lokacin daya zare vest ɗin ta rufe idanu a hankali ya kwanta, tare da ɗorata saman shi, wata iriyar ajjiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana ɗana zabura sbd sanyin daya ratsa fatar jikinta, wani irin daɗi ya kamata zafi da raɗaɗin na raguwa, Yaa Sheikh ya rufe ido tasbihi kawai yake a ran shi. A hankali zafin jikin Halisa ke shigewa nasa, sai da jikinsa ya ɗauki zafi sosai ya zameta a hankali tare da miƙewa ya koma bathroom ya ƙara sakarwa kansa shower ɗin. A wannan karan ƙanƙame shi tayi sosai sbd samun sassaucin da take kallo ɗaya zakai mata kasan ta jigata. Yaa Sheikh addu'a yake yana tofa mata hannunsa zagaye da bayanta ki sau ɗaya bai tsaya ya sauke idanunsa akanta ba. Ringing ɗin telephone da yaji yasa ya kwantar da ita yana miƙewa tsaye ya san Dr ne. Ya zura jallabiya da hirami tare da nufar ƙofar part ɗinsa ta baya yana zuwa ya samu Dr da Umar-khan. Yaa Sheikh ya kalli Umar-khan gane abin da yake nufi yasa kai tsaye ya nufi sashin Ummul. Yaa Sheikh ya juya zuwa ciki Dr ya biyo bayansa, cikin sauri ya shiga buɗe dukkan wasu abun gwaje-gwaje da zai tabbatar da zargin da Yaa Sheikh yake.
Gwajin farko ya nuna guba bace mai ƙarfin gaske ba wacce zata kashe mutum lokaci guda ba, a hankali zata dinga ƙona jinin mutum har ya ƙare cikin watanni biyu ko uku ya mutu.
Ya kalleta yaga kamar barci ya ɗauketa sbd yadda numfashinta ke sauka, Dr zaiwa Halisa allura ya ɗaura mata drip tare da saka mata wani abu acikin baki, Yaa Sheikh ya yi gyaran murya ya ce.
"Kada a manta am a doctor, zaka iya tafiya" Dr ya ce. "Allah ya ƙara sauƙi da afuwa" fitar Dr ya yi daidai da shigowar Ummul a rikice ta ce.
"Poison a gidan nan? Kuma wajan Halisa Aliyu? A ina aka samu guba?" Ya sauke numfashi a ɓoye yana ɗauke kansa, da kansa ya saka mata drip tare da yi mata Injection.
"Kaga abin da nake faɗa? ba za a barka ba Malam Wannan shirun naka bashi da amfani, nasan kasan masu nufinka da haka, abin tambaya ya akai Halisa ta samu guba?" Ya zauna saman kujera ya jima kafin ya ce.
"Maganar ta tsaya iya mu Ummul, a nemi abin cewa" ta ce "Shikenan amma na fara gajiya ba zan iya zuba idanu mu rasaka ba, kalli halin da yarinyar nan ta shiga" Sai a lokacin Umar-khan ya ce "Abin tambaya ne ina ta samu poison?" Yaa Sheikh ya miƙe tsam yana buƙatar hutu da nutsuwar Zuciya ko zai samu ya yi cikakken tunani mai kyau.
"Zan huta, ina buƙatar kyakkyawan lokaci Ummul, a nemi wacce tayi shayin nan" yana faɗin haka ya shige ɗakin dage gefen bedroom ɗin....
Basu da wani zaɓi wanda ya shige fita. Ummul ta nufi kitchen gaba ɗaya ta kira ma'aikatan ta ce "Waya haɗa shayin Yaa Sheikh?" Duk sukai shiru domin sun san babu wanda ya kewa Yaa Sheikh abincin bayan Ummul. Suhaima ta ce "Ummul ina tunanin ke kika haɗa fa? Ko kin manta ne?" Ummul ta ce "Ko ɗaya dole an sauya" Bara'at da tun ɗazo ba tai magana ba taja duguwar ajjiyar zuciya ta ce "Wanni abin ne?"
"A'a. Daman ya ce ya masa yadda yake so, an zuba suger ya yi yawa, wanda ya ɓata ɗanɗanon. Kuma saƙon daɗin yaje har ƙwaƙwalwar shi, wacce aka bawa kwangilar tana buƙatar a bata tukucin kai goran albishir"
Ummul ta juya rai ɓace, gabaɗaya suka bi bayanta da kallo tare tunanin ko dai wani abun ya faru ne?.
Tunda Ummul ta shiga ɓangarenta ta rasa yadda zatai da ranta, ko dai iyayen Yaa Sheikh zata kira ta faɗa musu abin da yake faruwa su sani? Kada a wayi gari da gawar Yaa Sheikh ya zatai?. Ta nemi waje ta zauna tare da faɗin.
"Ubangiji kamar yadda ka bawa Yaa tsayin shekarun daya ɗauka yana kula da Halisa tun tana ciki, har kawo haihuwar ta, Ubangiji ka ƙara masa wasu shekarun da zai tabbatar da mauradinsa ta zama cikakkiyar mata a garesa, Ya Allah Ya Rahmanu ka nufi Yaa Sheikh da mayar da wannan taɓargazar da ya yi, Yadda take ƴar raino a garesa Allah kasa ta zama mata a gare shi har abada"
Ta goge hawayen daya sakko mata, tana son komawa taji yadda jikin nata yake amma tasan taga Yaa Sheikh tasan riƙe kansa yake amma baya jin daɗi, ko zazzaɓin Halisa baya jurewa yanzu zai zo yana cewa. "Ummul ƴar fillona" balle yanzu data sha poison ason kare rayuwar Abban nata.
A daddafe Yaa Sheikh ya gabatar da Sallar Issha a masallacin da yake ɗaukan su jam'i. Bai tsaya yi musu karatu ba, ya dawo gidan ma'aikatan dake kula da dukkan wasu abubuwa daka waje ya shiga bi da idanu gabaɗaya suka sha jinin jikinsu wannan shi ne karo na farko daya kallesu har haka.
Zahrah na ganin shigowar Yaa Sheikh ta miƙe da sauri tare da rungomesa ta ce.
"My Excellency yau duk ban ganka ba, sai yaushe zamu kasance tare?" Ya zareta daga jikinsa ta ce.
"Na fara gajiya, matarka ce ni amma kana nunawa sam baka damu dani ba, ina da hakki a kanka kasan ni macace mai rai wacce jini ke gudana a jikinta kuma....," Kaifin idanunsa daya sauka cikin nata ya hanata ƙarasa maganar duk rashin kunyarta bata isa taiwa Yaa Sheikh.
"Me kike so? uhm kada ki damu shekaru biyu ne kawai na baki" maganar ta tsaya mata a zuciya, wato kada ta damu ko dan tai masa rashin kunya?! Ta tsiri kukan ƙarya idanunta rufe ta ƙara rungomesa ta ce.
"Ina buƙatar My Excellency, ina son kasancewa da mijina" Yai mata shiru ta riƙesa sosai ta shiga yi masa wani abu, amma ko gizau bai ba, al'amarin daya bawa Zahrah matuƙar mmki kenan.
Sumbatar shi zatai daidai lokacin kuma ɗan dake cikin cikinta ya yi wani kyakkyawan juyawa tare da harba ƙafa wanda ya a sanya taji mararta ta ɗaure tana da tabbacin Yaa Sheikh yaji juyawar ɗan dake cikin nata..
Ya ɗauke kai tare da shigewa abinsa. A ruɗe Zahrah ta nufi bedroom ɗinta tana kiran number Surry gaba ɗaya ta fara rasa mafita tashin hankali ya bayyana akan fuskarta.
Tun daga bakin ƙofa Yaa Sheikh ya fara jiyo numfashinta tana kwance jikinta zai rawa yake kumfa na fita daga cikin bakinta, tuni ta fisge drip ɗin hannunta. Ya ƙarasa da sauri yana zama kan bed ɗin tare da ɗagota, ko magana ya kasa jinta jikin mutum yasa ta ƙanƙame Yaa Sheikh tana ɓoye kanta kwantar da ita ya yi tare da kama hannunta ya shiga murzawa da sauri da sauri, ya daɗe yana murza hannunta kafin ta ja numfashi ta sauke jikinta ya saki sai hawaye dake bin fuskarta.
Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya shi ma sauke yana janye drip ɗin ta buɗe ido tana kallon Yaa Sheikh ta ce.
"Modibbo zan mutu kai ni Dadata" duk yadda yasu kame kansa da riƙe yanayin kasawa ya yi, ya jawota jikinsa tare da yi mata masauki da kyakkyawan ƙirjinsa ya rufeta ruf ya yi mata rungumar da rabon da ya yi mata tun tana shekara biyar a duniya.
Ta sauke numfashi tai luff a jikinsa ƙamshin Roja na ratsa zuciyarta a hankali ta ce.
"Abbana" ya dubeta bai ce komai ta ce "Abbana me ya sa zasu kashe mini kai? Su waye mai kayi musu zan basu haƙuri ni su kashe ni kaji?" Ya ɗora hannunsa a bakin nata "Shhhhh" ya ce yana ƙara matseta a jikinsa. "Modibbo, Abbana kada ka mutu kaji?" Idanunsa da suka gama juyawa ya buɗe tare da kwanto da ita saman hannayensa ya kifa kansa a fuskarta suka kalli juna muryarsa bata bita sosai ya ce..
"Rayuwa, mutuwa na hannun lillahi wahidul ƙahhar, ban son hawayen" A hankali Halisa ta fara tunanin vedion data gani a wayar Anti Zahrah komai ya dawo cikin tunaninta ita kanta Zahrah bata san Halisa taga wannan vedion ba. Yaa Sheikh yana ƙoƙarin zame fuskarsa daga kan ta Halisa kamar a mafarki, kamar gilmar tunani cikin ƙwaƙwalwar mutum haka yaji saukar bakinta cikin nasa.....
Paid book
It's 500
08119237616"Ya subuhanallah, wa...wa wa'auzubillah" sune kalmomin da suka samu fita daga cikin bakin Yaa Sheikh wanda suka kasance iya zuwa. Ya riƙe kanta da kyau yana ƙara ware idanunsa akan ta, mmkin ya cika shi yaushe matar malam ƴar amanar shi tasan duk wannan? ya ɗauke numfashi yana ƙoƙarin sauya yanayin yaji ta ƙara riƙe bakinsa da kyau idanunta rufe, al'amarin da bai taɓa ji ba shi yake neman bijiro masa.
Ilahirin jiyoyin kansa sun fito tare da yin kwance a saman goshinsa. Ya zare bakinsa da ƙyar ba dan ta daina abin da take ba, Halisa ta marairaice fuska idanunta na cikowa da hawaye ta ce "Abbana" ya goga fuskarsa a wuyanta yana tura dukkan hannunsa cikin sumar kanta ta sauke numfashi tana bin fuskar shi da kallo tare da kama gemunsa tana ja..
Cikin wata kalar raunatacciyyar murya wacce shi kaɗai yasan ma'anar ta ya ce _"Ta fuɗɗu ko a wawata famtugo nder majuum"_ karo na farko da taji fillatanci a bakinsa wanda ya zauna raɗau kai kace harshen shi ne na Iyaye. Ta ce "Abba zan iya gane darasin da gaske" "Uhm" ya ce kawai dan bakinsa ya yi nauyi sosai, yarinyar ta shayar da shi mmki.
"Sallah zaki" ta ce "Abba ba zan iya tashi ba, kuma zanyi fitsari" ya miƙe da ita tsaye tare da nufar bathroom. Suna zuwa ya sauketa tare da ƙoƙarin juyawa tayi saurin maƙale kafaɗa ta ce.
"Ka tsayani, tsoro ina" ya kalleta sai kawai ya tsaya tare da juyawa mata baya. Bayan ta kammala ya yi mata alwala da kansa a taushashe ya ce.
"Walk" bata gane zaran zancan nasa ba da hannu ya nuna mata ƙofa ta shagwaɓe fuska sosai kamar yadda take masa a shekarun baya amma duk ta mance. "Ni ka ɗaukeni ba zan iya tafiya ba" ya girgiza kai tare da sunkuya ya ɗauketa ta saƙalo wuyansa. A jingine a jikinsa a haka ta gabatar da Sallar duk yana kallon ta, saura kaɗan gabar ya kassara mata jiki gabaɗaya bata da kuzari duk babu kazar kazar ɗin. ganin tana lumshe idanu ya ce "Gajiya? Jikin? Yunwa?" Ya faɗa a taƙaice ta girgiza kai ta ce.
"Abba Dadata yaushe zan ganta? Ni goyani take idan bani da lafiya" ya ware manyan idanunsa yana hango zallar rigima dake kwance a nata idanun. "Abba ka goyani" ya dubeta a dole sai ta saka ya magantu ya ce.
"Ki rufa mini asiri, goyo tun shekarun baya baki mance ba?" ta saki kuka da gaske domin ita har zuciyarta take son a goyatan ƴar rigima ce, idan abin ya motsa bata ji bata gani.
Ta saka kuka sosai ya ɗauketa gabaɗaya tare da jijjigata ya ce "Kina son rikitani Amanata, ki tauyasawa Abbanki" ta maƙale kafaɗa daidai kunnanta ya shiga yin wasu baitotoci na waƙar larabci na addini. Tai shiru tana tunani kamar tasan waƙar, Yaa Sheikh yasan dole ta haka zai