Showing 33001 words to 36000 words out of 197828 words

Chapter 12 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9317

ji da masifa, daidai nake da ko wanne ɗan iska Wallahi" Saif-wazir ya kalli Zahrah da kyau kaya ne wanda suka kama jikinta sosai hannunta duk farce taci gashin doki, juyawa ya yi ya kalli Surayyerh ba tare ce komai ba ya juya zuwa cikin emergency. Kai tsaye aka bawa Danejo gado Dr ya kalli Saif-wazir ya ce "Suna?" Saif ya shafa kansa sbd sam bai sani ba sai kawai ya wayance da faɗin "Dr ka fara yi mata taimakon gaggawa, sai mu yi magana" Dr ya ce "Dole a buɗe mata file ai" "I knw, amma kulawa da ita ba zai hana buɗe file ba, a duba ta first buɗe file second" Dr ya miƙe tsaye tare da nufar ɗakin da suka kwantar da Danejo abun mamaki ba ita ba alamarta, cikin hanzari ya fito sukaci karo da Saif-wazir ya ce "Yarinyar nan ta gudu bata cikin room ɗin?" Saif ya ce "What?" Da sauri ya juya zuwa waje amma neman duniya babu Halisa Danejo Rome babu ko inuwarta "Innalillahi yau na shiga uku ko dai aljana ce yarinyar nan? Amma babban asibitin irin wannan ina zata?" Ganin bashi da wata mafita ya nemi abin hawa wanda zai dawo da shi Kano domin ba zai iya komawa Rugar Bello ba yace bai ga yarinyar ba, haka kurum su kashe sa a banza.


Ɓangaren Halisa ana kwantar da ita a saman gado A.c ta fara ratsa ta, ta farka da sauri tana dabe kanta, tsoro ya kamata tana mamakin yaushe tazo. Ita dai ta fito tallan Kindirmo ta ce bari ta biya ta Rugar Bello a hanya yunwa da jiri suka yarda ita, kanta ya daki wani dutse bata ƙara sanin inda take ba. Miƙewa tsaye tayi jikinta na rawa ta ce "Hande en boni gidan cire kai aka kawo ni wayyo Allah Dadata na lalashe, lalashewa ta sameni" kuka take sosai har da majina fuskarta tai jaa. Leƙewa tayi ta window taga ashe bayan asibitin ne, da sauri ta kama tagar ta dira baya duk da zafin da kanta ke mata amma haka ta dinga gudu kamar barewa a haka ta isa Rugar Rome. Shiri sosai Zahrah tayi ta tarbar Sheikh amma har dare babu labarinsa baƙin cikin duniya duk ya kamata ga ƙawayenta duk ta tara zata nuna musu haɗaɗɗan mijin da zata aura amma ya kwafsa mata.


Misalin 10:23 Abba Hakimi na zaune a Main parlour dashi da Momi kamar daga sama su kaga Sheikh ya shigo hannunsa guda ɗaya dafe da kansa, Momi zatai magana Abba Hakimi ya Girgiza mata kai alamar tai shiru,babu wanda ya kula ya shige part ɗinsa dake gidan, kai tsaye bathroom ya nufa bayan ya zame kayan jikinsa abin da bai taɓa yi ba shi ne, amfani da ruwan sanyi ya tsaya a shower na sauka akansa sanyi na ratsa masa tsakiyar kansa, sai numfashi yake fitarwa dan kansa ya kashe shower ɗin ya naɗe jikinsa a cikin wata bathroom mai ɗan kauri, idanunsa na rufewa sbd azababban ciwon kai a haka ya kwanta saman gado ya daɗe kafin barci ya ɗauke sa.


"Lafiyar Sheikh ɗaya kuwa?" Abba Hakimi ya ce "Kinga alamar bai da lafiya ne?" Momi ta ce "A'a, kawai yadda na shigo gidan ne" Apple ɗin hannunta da take miƙa masa ya amsa ya ce "Kada ki damu, duk sanda ya yi haka alheri ne ke bibiyarsa" tattaunawa sukai akan gobe za a kai kayan lefen na Sheikh ita ma zata a hankali ya ce "Allah ya kaimu" sai kusan 12 na dare Sannan Saif-wazir ya shigo ganin dare ya yi kai tsaye ya nufi part ɗinsa, motar Sheikh da ya gani ya bashi tabbacin ya dawo gida. Da batun Auren Sheikh ya kwana yana tunanin ya faɗawa Abba Hakimi ko ya yi shiru? Har barci ya ɗauke shi ba samu mafita ba.


Washegari da yamma wajan 5. Dr A'isha ta zabga tagumi Yaya Halima ta ce "Dr wai lafiya tun da muka dawo kike wata kala?" Dr A'isha ta ce "Wallahi Yaya tausayin Sheikh nake, ina zai kai wannan uwar matar? Na girgiza ban san rashin tarbiyyar ta ya kai haka ba, kalli da ita aka amshi kayan lefen fa?" Yaya Halima ta kalli Dr A'isha tana mmkin rashin control na bakinta da bata iya riƙe zance. "Kowa da tsarinsa fa Dr Allah dai ya sanya albarka" daga bakin ƙofa akace "Ba Amin ba, mugun ji da mugun gani ruɓaɓɓan baki ya kau daga kan Gadanga, yau ko ni ko uban Gadanga ya zaɓa" gaba ɗaya suka kalli bakin ƙofa, tana tsaye taci lace ɗauri har gaban goshi ta lafta uban Glasses a fuska wanda ya cinye rabin fuska. Cikin farin ciki Mother ta miƙe tsaye tana faɗin "Jadda" haɗe fuska tayi ta nemi waje ta zauna, Uncle Haroon ya shigo hannunsa riƙe da torelly ɗin Jadda ya zauna kusa da ita. Cikin farin ciki Mother ta ƙara cewa "Sannu da hanya Jadda ashe kina tafe" Jadda ta ɗauke kai sai da Mother tabar wajan, ta juya ta kalli Uncle Haroon murya can ƙasa ta ce. "Munafuka Algunguma duk masifa da yaƙin da ake a gidan fa bata sanar dani ba, shi ya sa na haɗe mata fuska na kame kai na, ba kaga jikinta ya yi sanyi ba, ai wlh yau sai sun bala'i ya sauka" murmushi kawai Uncle Haroon ya yi ta haɗe rai tana ƙanƙantar da idanu ta ce "Kaji masifa ko? Ba murmushi za kai ba cewa zakai nayi daidai" ya ƙara murmushi ya ce "Jadda duk abin da ki kai ai daidai ne" cikin ƙaramin lokaci Mother ta cika gaban Jadda da kaya kala-kala, Yaya Halima da Dr A'isha suka gaidata ta amsa a ciki. "Kinga ba kwaɗayi ya kawo ni ba, maza kira mini mijin naki" Mother ta haura sama yana zaune yana duba Invitation ɗin bikin Sheikh dana Zahrah Mother ta shiga a hankali ya ce "Barrister ya dai?" Kai tsaye ta ce "Jadda na kira" tana faɗin hakan ta juya, yabi bayanta da kallo da sauri kuma ya miƙe shima. A hankali yake sakkowa daga benen yana sakin fuska bayan ya zauna ya ce "Sannu da zuwa Jadda" banza Jadda tayi masa, ta zare Glasses ɗin idanunta ta miƙawa Uncle Haroon, ta cire mayafi shima ta miƙawa Uncle Haroon, fuskar Father cike da tsoro ya ce "Jadda lafiya me kike shirin yi haka?" Bata kula shi ba, ta buɗe rigarta tana nunawa father ta ce "mene wannan?" Kansa a ƙasa ya kasa cewa komai ta ce "Idan ba zaka iya ba, ai Ubangiji ya tsaga mini bakin magana nonon dana shayar da kai ne, kasan Allah tun nonon yana kwance ka lalata batun auren Gadanga da wannan gantalalliyar yarinyar, idan ba haka ba zan ɗaga maka nonon sama ka lalace kaje duk inda zaka...




*Not edited*
Masu tambayar yadda zasu biya kuɗin IDAN BA KE. Book 1, 2 ne. Mutum zai biya ₦500 har a gama littafin baki ɗaya. 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank. A tura shaidar biya ta nan 08119237616.*🌈IDAN BA KE 🌈*


*_Nimcyluv Sarauta_*


16....


*I am proud of my fans wherever they are, nayi mamakin yadda kuka amshi littafin IDAN BA KE fiye da ZAIN-ABEED. Masoya TSINTACCIYA, MOON, UNCLE NE duk ba a barku a baya ba🥰💋for the first time zanyi rubutu akan labarin zanan ƙaddarar soyayya zallah🫰🏿a shirya a gyara zama sosai yanzu aka fara...*
#TEAM SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU
#TEAM HALISA DANEJO ROME
#TEAM EL-BASHIR AHMAD SARKI
#TEAM ZAHRAH FAROUK




Jadda ta ƙara cewa "Kalle ni da kyau uwarka ce Jadda, Wallahi nono zan ɗaga maka kawai kabi duniya kaje duk inda zaka Aliyu tunda ka gagara, idan ya so ana nunaka da baki ana cewa gashi can uwar shi tai masa baki ta ɗaga masa nono shi ya sa yake ta galantuyi a duniya, duk wanda bai yarda ba, ni nai maka baki ba zaka iya kawo shi wajena na tabbatar masa" zufa ta dinga yankowa Father a hankali ya zame daga kan kujera zuwa inda take ya ce "Jadda don girman Allah kada kice haka, ki tsaya ki fahimci al'amarin nan I have a reason why I want Sheikh to get married with Zahrah." Uncle Haroon ya ce "Mene dalilin naka? Uwar yaron nan bata so, I don't agree either" Jadda dai kaɗa ƙafa take har lokacin tana riƙe da ƙirjinta cikin rarrashi Father ya ce "Jadda don ki fahimce ni Sheikh ba zai iya kula da dukkan al'amarin daya shafi kasuwancina da dukiyata ba, kullum ƙarfina ƙasa yake abubuwa na neman yi mini yawa, na bashi dama yafi sau goma akan ya kawo matar da zai aura amma yaƙi, Umar-khan yace tunda Sheikh yake magana bata taɓa haɗa shi da wata mace ba, kalli sharrin da akai masa tun daga jami'ar Madina, da ace yana da aure babu mai binsa da wannan sharrin shi ya sa na yanke hukuncin aura masa ƴar aminina tasan kan business sosai zata janye hankali Sheikh ɗin zuwa kasuwancin, Jadda ina son Sheikh Aliyu ban taɓa son wani abu kamar shi ba, kiyi mini uzuri ayi auren nan idan yarinyar ba tai miki ba sai ki ɗauki mataki" Mother ta girgiza kai cike da takaicin yadda Father yake tsara zan ce. "Aini duk bani da labarin haka, jiya jiya labari ya saman ana ta yaƙi a gidan naka, kuma yarinyar ƴar iska ce" Father ya kalli Jadda da kyau ya juya ya kalli Mother yana faɗin "ke kika faɗa mata Zahrah ƴar iska ce sbd ba ƴarki bace shi ya sa zaki ai bata musu ƴa?" Rai ɓace Mother ta ce "Ni na faɗa Engineer tunda haka zuciyarka ta shaida maka, kaga yaushe rabon da naje wajanka akan maganar Aliyu ko auren? Aje ayi aure lafiya nima zan zaɓawa Sheikh yarinyar da nayi niyya na aura masa ita" tana faɗin haka ta miƙe tare da nufar upstairs zuciyarta cike da tarin baƙin ciki. Baki buɗe Jadda ke kallon kowa kafin ta ce "Na amince ayi auren kuma na amince Maryam ta zaɓawa Gadanga yarinyar da duk tai niyya" Father ya ce "Amma Jadda daka aura masa Zahrah sai ya yi mata kishiya? Ba ai mata adalci ba" Jadda ta miƙe tsaye tana ƙanƙance idanu ta ce "Wai wacce ƙaniyar ce Zarra ko me? Ba ita ba ko uwarta ka aurawa Gadanga kwaranƙwasa sai anyi mata kishiya, Allah dai ya nuna mini ƴar banzar yarinyar da idanu naga abin da bai mini ba, maza ɓace mini da gani ko mene haɗina da kai dana tsaya shiga sabgar ka" Father ya miƙe tare da barin wajan yana faɗin "A huta lafiya Jadda" sai da yabar wajan Jadda ta sauke numfashi tana raɗawa Uncle Haroon ta ce "Ba gashi ba anyi sulhu komai ya lafa daman duk iskancin mutum ina zuwa shikenan, ai Alsulhu khair" murmushi kawai Uncle Haroon ya yi yana cewa sai Anjima zai dawo.
Sai a lokacin Jadda ta lura da Yaya Halima da kuma Dr A'isha kowa yana danna waya abinsa kasancewarsu masu ilimi da dukiya ya sanya suka kame kansu basu saka baki cikin abin da babu ruwansu ba.


Mother na zaune tana waya da wata friend ɗinta kamar daga sama Father ya faɗo ɗakin cikin faɗa ya ce "Burinki ya cika kin haɗani da mahaifiyata,she insulted me in front of people data hana auren Zahrah da naki auren ma sai ya mutu" tunda ya fara magana bata kula shi ba sai ƙafa da take girgizawa tana ci-gaba da yin wayarta hakan ya ƙona ran Father yaso ta tanka masa ya wanke ta tsaf.
Saif-wazir na zaune gaban Abba Hakimi ya kasa cewa komai. Abba Hakimi ya ce "Ya kai ne Saifuddeen?" Ya sauke numfashi ya ce "Abba ban san ya zaka fahimci maganata ba" Abba Hakimi ya ɗaga kansa tare da kallon Saif-wazir ya ce "Tunda ba zan fahimta ba ta shi kaje" da sauri ya ce "No Abba I'm sorry" shiru yai can dai ya ce "Daman akan zuwa Yola da mukai da Sheikh ne, tsautsayi ya faɗa masa na auren wata ƴar Rugar Bello" Abba Hakimi ya ƙara kallon Saif-wazir da idanun na fahimta a hankali ya ce "Uhm Aure dai?" In short, Saif told Abba Hakimi about everything that happened daga zuwansu Yola har fitar Sheikh mota da zuwan Fulanin har auren da aka ɗaura da zoben Sheikh ɗin matsayin sadaki, har maganar zuwa asibiti da ɓacewar yarinyar.
"Aiki jaa" Abba Hakimi ya faɗa a ransa wannan shi ne dalilin daya sanya Sheikh ya dawo a rikice kenan? "Kace yarinyar ta gudu? Zaka gane ita Rugar?" Saif ya ce "E, ta gudu Abba Rugar ma zan gane domin akan hanya take, amma bana ganin Sheikh zai amince da auren mata biyu lokaci guda" murmushi Abba Hakimi ya yi wanda shi kaɗai yasan ma'anar shi a nutse ya ce "Auren da ai masa na haɗi ne, wannan kuma Ubangiji ya ƙulla, Allah ya nuna mana zuwa Yola ɗaurin aure zamu je can Rugar" Saif-wazir ya jinjina kai alamar gamsuwa ta gefe guda kuma ya kasa faɗawa Abba Hakimi abin da ya gani a tattare da ƴar fillon wanda ya ruɗa masa lissafi ya hana shi bacci daren jiya. "Jirginsu Mai martaba ya tasu, zuwa ƙarfe huɗu zasu sauka yace Sheikh buƙatar ya je ɗakko shi, yanzu kuma lokacin barcin Sheikh ne" Saif ya duba lokaci ya ce "Yana barci tsakanin Zhur zuwa Asr jirgin kuma 4 zai yi landing akwai time Abba" Abba Hakimi ya ce "Mafi mushkila"
Bayan fitar Saif-wazir Momi ta ce "Amma bana ganin wannan auren ya ɗauro fa?" "Me ya sa A'isha?" Momi ta ce "Naga babu wani na Sheikh a wajan sai Saif" jinjina kai kawai Abba Hakimi ya yi yana ci-gaba da rubutun shi ta ce "kayi shiru?" Bai kalleta ba ya ce "Idan kika sake cewa I'll do the same thing, aure ba shaidu da sadaki yake buƙata ba? Saifuddeen ya ce shaidu wajan 20 a wajan, Zoben da suka amsa kin san darajar shi kam?, Aure ya ɗauro kamar na ko wanne ma'aurata" Momi tai murmushin jin daɗi ta ce "To Allah ya sa albarka,ya sanya matar shi ce har aljanna sai a faɗawa Barrister" nan ma Abba Hakimi ya ce "A'a Maganar ta tsaya iya mu, bana son ko su Umar-khan da Ishaq-hakim suji, hatta Barrister Maryam da mijin nata bana son suji" hira sukaci gaba dayi.


Ƙarfe 4:5 daidai Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ya fito sanye cikin dark blue ɗin shadda jamper da babbar riga, sai ƙamshin Roja yake wanda ya a cika parlourn. Ƙafarsa cikin Leather shoe sumar kansa wacce ya rufe da hirami ta sha Ginger Geminal Oil-hair daga sajansa zuwa gemu sai kyallin Luxury Beard oil yake. Bakinsa sai ƙamshin LB Breathe herbal sugar breath freshener spray. Fitowar shi cikin parlourn ya yi daidai da shigowar Abba Hakimi, Umar-khan da Ishaq-Hakim na binsa a baya. "Daman yanzu nake shirin zuwa sashin naka sai gaka" zama ya yi Sheikh yana gyara Babbar rigarsa yau ba saika Alkyabba ba, a nutse cikin kamala murya mai ɗauke da kwarjini ya buɗe baki ya ce "Barka da yamma Abba" kallon kallo akai tsakanin Umar-khan da Ishaq-Hakim jin yau Sheikh bai In-ina ba, Abba Hakimi kam murmushi kawai ya yi hakan bai wani dame shi ba ya ce "Yawwa Sheikh Dadynka Mai martaba ya sauka yanzu kai suke jira" Sheikh ya duba agogo ya riga yasan sai biyar jirgin zai sauka yana komai bisa tsari. Bai ce komai ba ya miƙe tsaye Abba Hakimi ya bisa da kallo yana mmkin sauyawar Sheikh da yawan lokaci kamar mai cin naman wahainiya yanzu zaka ɗauka yana da yara kusan biyar sbd yana yin kamalar shi, amma fuskarsa bata nuna shekarunsa ba kullum cikin kame ta yake.
Yana fita aka buɗe masa bayan mota, Umar-khan yaja Ishaq-Hakim da Saif-wazir suka shiga mota ɗaya sai airport. Zuwansu airport ɗin ya yi daidai da saukar jirgin har lokacin Sheikh na mota bai fito ba. Khalil Ahmad Sarki ne ya fara ɗakko daga cikin jirgin sai Mai martaba Ahmad sarki na uku ya shiga ɗakko cikin nutsuwa hannunsu riƙe da sanda, fari kyakkyawa da shi wanda zai iya yin shekaru wajan 65 da haihuwa. bayan sakkowar Mai martaba wani saurayi ya shiga sakkowa ganin saurayi ya sanya hantar cikin Saif-wazir juyawa, nan take kuma ya tuna da abin da idanun shi ke maza gizau. Zai iya yin shekaru 25 da haihuwa fari kamar mahaifinsa mai martaba har yari Mai martaba kyau da haske, Three-piece dinner suit a jinkinsa saɓanin Khalil Ahmad Sarki dake cikin shiga ta sarauta. Gaba ɗaya suka zube tare da gaida Mai martaba Ahmad Sarki. Khalil nata ware idanun ganin Sheikh can ya leƙa bayan mota ya ganshi zaune ya rufe idanun shi. "I expected to see you right here" Sheikh ya buɗe idanu ba tare da ya ce komai ba, cikin tsokana duk da Sheikh ɗin gaba yake da Khalil ya buɗe masa ƙofa yana faɗin "Ango kasha ƙamshi, Finally the Sheikh will get married, praise the couple's line" har lokacin dai Sheikh bai kula Khalil ba sai fitowa da ya yi daga cikin motar a hankali ya ƙarasa Wajan Mai martaba ya ɗan sunkuyar da kansa Mai martaba ya ce "Yau gani ga Sheikh tunda yaƙi zuwa inda muke" ya lumshe idanunshi tare da buɗewa ya saki murmushi wanda ya sanya kyansa fitowa sosai.
Sheikh da Mai martaba suka shiga mota ɗaya, Khalil ya shiga bayan motar su Saif-wazir Mai martaba ya kalli matashin saurayin ɗan na shi ya ce "El-bashir..." Wanda aka kira da El-bashir ya ware ido murya a sake ya ce "Mai martaba zan zo" yana faɗin hakan ya juya yana tsayar da mai texsi...


Abu kamar wasa ɗaurin auren Sheikh ya rage saura kwana uku cif. Har lokacin da Sheikh da El-bashir ba a haɗu ba, Sheikh ba manta da wata Yola baki ɗaya balle Auren da yake kansa na ƴar fillo. A ranar aka kammala gina Bankunan Sheikh na Lagos da Abuja, tare kamfanin sarrafa shinkafa an zuba komai da komai ranar buɗewa kawai ake jiran Sheikh ya saka sai kuma ɗaukan ma'aikata.
Yana kwance a bedroom ɗinsa dake gidan father ya miƙe da sauri kamar wanda aka tsikara yana sanye da embrodiery Islamic jallabiya a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login