Showing 123001 words to 126000 words out of 197828 words

Chapter 42 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9332

her down.
Yaa Sheikh ya sauke hannayensa gently ya ƙarasa inda take gabaɗaya suka zuba masa idanu, hatta Halisa kallon shi take a hankali ya miƙa hannu zai riƙe nata tai wani tsalle tare juyawa ta dire daga kan gadon tana fasa wata gigitacciyar ƙara....


Paid book
Nrml grp 500
Special 1k
08119237616Yaa Sheikh ya juya paper ɗin a hannunsa ba tare da fuskarsa ta nuna yanayin da yake ciki ba, Abba Hakimi ya kalli Yaa Sheikh ba yabo ba fallasa, ganin duk sun kasa magana ya sa Dr ɗin "Akwai matsala ne?" Mother ta miƙe tsaye tare da amsar paper ɗin tana kallo ta ce
"No babu, abin ne ya zo Unexpected ne, but ka ce 1 week and three days? Sai naga 1 Week ne kawai" dafe ya dafe kan shi alamar mantuwa ya ce "Oh! Am sorry i almost frgt tunani da ke zuciyata daban, na ɗauki wani zance na faɗa" ta ce
"No problem, Thank you Dr" ya ce "Allah ya inganta" Mother da Umma A'isha suka amsa da Amin.
Umma A'isha ta ce
"Daman ana iya gane cikin sati guda ne?" Mother tai murmushi ta ce "Sosai ma, zamanin baya dana yanzu bambancin su a fili yake, ciki har na kwana uku ana fahimtar shi, kawai is the defend da yadda akai text ɗin, wasu suna yin text at home na HCG for pregnancy test. Testing _(Strip, Cassette, Midstream)_ Typically, medical professionals measure pregnancy week 1 from the first day of a woman’s last menstrual period. Although a woman is not actually pregnant at this point, counting week 1 from the last menstrual period can help determine a woman’s estimated pregnancy due date.
However, this article will refer to pregnancy week 1 as starting a week after conception, meaning the literal first week of pregnancy.A missed menstrual period is often the primary symptom of early pregnancy" Umma A'isha tai jigum alamar bata gane ba ta ce
"Is hardly ace kai tsaye an samu cikin kwana bakwai, ko da gwajin HCG ne sai da ya nuna cikin kawai" Mother ta ɗauki wayarta ta ce
"Bari muji Dr A'isha" Ringing ɗin Farko Dr A'isha ta ɗauki wayar bayan sun gaisa Mother ta ce "At hospital ta ya ya ne za a gane cikin sati ɗaya?" Dr A'isha ta ce
"Wake da ciki kuma?" Mother ta ce "Bana son wannan tambayar taki, First answer my question" A hankali cike da gwanancewa ta ce
"Blood tests, ta cikin gwajin jini bana fitsari ba ana iya ƙayyade adadin kwanaki ciki, irin wannan gwajin na Blood tests anfi yinsa ga budurwa wacce bata taɓa haihuwa ba, ko kuma wacce akai mata medical checkup, garin duba lafiyarta sai kuma aga ciki, da yawa ba a sanin da shi irinsa koda gwajin fitsari akai kona HCG bai fiya nunawa ba sai bayan kwanaki haka"
"To ya ne Blood tests ɗin yake?" Dr A'isha dake zaune a office saman kujera ta ɗan ja kujerar baya idanunta akan system ta ce
"Blood tests can tell if you are pregnant about six to eight days after the menstruation. Doctors use two types of blood tests to check for pregnancy: Quantitative blood test (or the beta hCG test) measures the exact amount of hCG in your blood" ta sauke numfashi ta ce
"Sanin gaibu sai Allah, abin da mu likitoci muka gani a test ko scanning ba shi ke tabbata, kamar muce zaki haifi namiji sai kizo ki haifi mace, ko muce mutum ba zai rayuwa ba sauran shi kwanaki kaza ko wata musamman masu ciwon Cancer kuma sai mutum ya rayuwa,so komai nufin Ubangiji ne shi ya sa duk muka dai na faɗin irin abubuwan nan ko da mun gani" cike da gamsuwa Mother ta jinjina kai ta ce
"Thank sister, Our Dr" Dr A'isha ta ce "Ba wannan ba Please wake da ciki ne?" Mother ta juya ta kalli Halisa dake zaune tana shan orange gabaɗaya hankalinta baya kansu balle ta san bidirin da ake ta ce
"Halisa ce" Dr A'isha ta ce "You mean matar Yaa Sheikh?" "Ita nake nufi" jikin Dr A'isha ya yi sanyi, har sai da Mother ta fahimci sauyin nata, kawo yanzu tana jin ita ce bata da rabo na haihu, ta ɗauka abin girma ne sai gashi yarinyar cikinta ta samu ciki a bayanta.
"Kada ki damu, kina da babban rabo In sha Allah" Dr A'isha tayi murmushi ta ce "Ina jin kamar ni na samun cikin, abin da ya shafi Malam ya shafe ni" sai a lokacin Mother ta tuna Dr A'isha bata san abin da ya faru ta ce
"Haka ne, anjima za mu yi magana bye" sukai sallama. Umma A'isha ta ce "Yanzu kam na fahimta, to Allah ya raba lafiya ya inganta ya sanya mu rabu ƙalau da mai cikin" Murmushin jin daɗi kawai Mother tayi.
Yaa Sheikh ya juya a hankali zai fita yaji Abba Hakimi ya ce "Ba zan tsayar da kai ma, amma ka sani kaci amana kuma zaka saman" fuskar Yaa Sheikh ta faɗaɗa bai juya ba ya yi ficewar shi yana jin nauyin zuciyarsa na raguwa, ashe shi ma wata rana zai haifi ɗa? Ashe zai ga jininsa a doran duniya? Wani irin so da ƙaunar Halisa ya ƙara ninkuwa a zuciyar shi, bai san tayi girma da ƙarƙon ɗaukan duka ƙwayayen daya zuba mata, har kawo yanzu kallon ƴar amanar shi kuma ƴar rainon shi yake ba. Ya saka hannu tare da shafa gemunsa yana lumshe idanunsa a sanyaye ya ce
"IDAN BA KE ba Aliyu!"
Mota ya shi ga ɓangaren driver da sauri Umar-khan dake waya ya ƙarasu wajan ya ce "Can i help with drive Yaa Lee?" Yaa Sheikh ya dubi Umar-khan a nutse ya ce "ka huta Farouk"
"Idan an hana Umar-khan ai ba za a hana Prince Khalil Ahmad Sarki rakiya ba" Yaa Sheikh ya kame fuska domin bai fiya son surutun Khalil ba, ya buɗe ɗaya ɓangaren ya shi ga ya ce "Yau zan ji kalar driving ɗin Yaa Lee" bai kula shi ba, bakinsa ɗauke da addu'a tare da bisimillah ya yi wa motar key gatekeeper ya buɗe cikin nutsuwa ya harba motar kan titi. Khalil ya ce "Nikam ka shige mini gaba akan Moon mana" tamkar bada Yaa Sheikh yake ba, idanunsa kwance akan titi yana bin sautin ƙira'ar dake tashi a motar shi. "Wallahi wulaƙancinka ne bana so ina magana kayi shiru, da shekara ɗaya ka girman fa bai ma kai ba" Shi dai bai tanka ba, bakin Khalil yaƙi mutuwa ya ce
"Ko dan kaga kana da furfura?" Sai a lokacin Yaa Sheikh ya rage sautin ƙira'ar kaɗan hannunsa ɗaya a gemunsa yana shafawa kamar ba zai magana ba sai ya ce "Nagartattun mutane da ƴan baiwa ke samun furfura irin tawa"
"Ni dai mu ajjiye, wallahi ina son moon na shirya aurenta ka shige mini gaba" Yaa Sheikh yana shan quanah ta round-about ya ce "Waye Moon?" Khalil ya ce "Ƙanwarka Maimoon" Ya taɓe baki kafin ya sauke numfashi ya ce "Allah shirya, Maimunatu shi ne Moon? Kuyi ta ɓata sunan mutane" Khalil ya ce "Irin Special name ɗin nan ne, kai ma ai ba Halisa ka ke cewa ba, na kama sai yafi nawa" bai ƙara magana ba har suka isa cikin wani ƙaton waje shi ba makaranta shi ba asibiti ba, wajan ya yi kyau sosai ga yara manya da ƙana na suna ta sabgoginsu, Khalil ya fito tare da zagayo ya buɗewa Yaa Sheikh ƙofa ya ce "Yaushe rabona da zuwa Orphanage ɗin nan, yaran Yaa Lee sun girma" Yaa Sheikh ya fito yana gyara zaman hiraminsa idanunsa akan wata kyakkyawar yarinya data taho wajansa da gudu tana faɗin "Abba.. Abba.. Abba" tana zuwa Khalil ya yi sama da ita ai kowa ya saka kuka irin yaran nan ne masu wayo, ta dinga miƙawa Yaa Sheikh hannu ya ce
"Tab, yaran wasu sukai maka wannan sabon ina ga ɗan cikin ka" Ya sauke yarinya Yaa Sheikh ya durƙosa daidai tsayinta yana shafa kanta ya ce
"Beeherh" ta sakar murmushi ta ce "Abbana ina Mumyna?" Ya riƙe hannunta da take ja masa gemun ya ce
"Na zama maraya Mumy ta guji Abba" Beeherh tai narairai da idanu ta ce
"Abba ni ma bana son.." ya rufe mata baki a hankali ya ce "Kul dole ki so abin da Abba ke so Beeherh" ya miƙe tsaye da ita a jikinsa suka ƙarasa ciki gabaɗaya yaran suka fara ihu suna kiran "Abba ina Mumy" Khalil ya ce "Abba zai kawo muku Mumy gobe" Khalil da kan shi ya dinga raba musu chocolate da abubuwa suka pictures da yawa, yaran suka koma wajan wasa Beeherh taƙi yarda da kowa sai Yaa Sheikh a haka har tayi barci jikinsa, suna tsaye wata budurwa ta zo ta sunkuya har ƙasa ta ce "Ina kwana Abba?" Ya dinga kallonta yana son yaran sosai sai ya kasa shareta ya ce
"Lafiya Hafsat" ta miƙe bayan ta gaida Khalil Yaa Sheikh ya miƙa mata Beeherh ta amshe ta ce
"Kwana biyu rigima take tai ta kiran Abba, har cewa kada sunan Abbanmu ya ƙare" Ya lumshe idanunsa da hannu ya nuna mata hanyar tafiya, daga nan suka shiga mota kai tsaye Yaa Sheikh Na'ibawa ya nufa ba tare da sanin Khalil ba, sai ganinsa ya yi a haɗaɗɗan grandparents ɗin Yaa Sheikh.
Ummul na zaune ta ji ƙamshin turaren ɗan nata, ta ɗago kai a hankali ta ganshi tsaye yana tsare ta da idanu
"Me ya sa ka ɗauke komai na Mahaifinka ne Arɗo, babu ko kara ka ɗauki wani abun nawa?" Ta dube shi da kyau ganin ya faɗa kamar mai jin yunwa ta ce
"Zonan muji, fuskar ka abu biyu ta nuna, akwai damuwa amma farin cikin ya fi yawa" ya ƙarasu wajanta yana zuwa ya zube a gabanta yana ɗora kan shi a cinyoyinta. Ta zame hiramin kan shi tasha shafa sumar kan ta ce
"Ya akai Aliyu?" Ya sauke numfashi yana ɗago kan shi ya kalli Ummul ya ce
"She hated me" rauninsa duk ya gama bayyana, wanda kuma iya gaban Ummul ɗin ne yake haka
Ta riƙe fuskar shi da hannunta ta ce "Abun farin cikin fa?" Ya yi jim nauyin Ummul ya saukar masa, ita ma ta fahimci haka amma tasan dole ita ce abokiyar shekarar
"She's pregnant, na ƙara jin son ta" farin ciki ya mayaye zuciyar Ummul sosai jin Halisa nada ciki ta ce "Ma sha Allah, so zan samu granddaughter or son zan ga jinin Arɗo am so happy" ya lumshe idanu idan ba ita ta ce ya tashi ba, zai ta zama a durƙoshe ne ta ce
"Haka soyayya ta ke Aliyu, bari na baka labarin soyayyata da Mahaifinka, ban ɗauka zan so shi ba, wulaƙanci daban na gobe daban, ya yi kuka amma bana damuwa a haka har na fara tausayin shi,tausayi ya koma soyayya mai zafi, bana iya barci idan ban ji muryar shi ba, na bijirewa iyeyena ashe duk rabonka ke kira shi kuma ya hadda sa haka" tai shiru na wani lokaci ta ce
"Idan Halisa ta tsaneka yau, gobe zata so ka, idan taji haushinka yau, gobe zata tausaya maka, irin haka lamiri mai girma ke tabbatar da shi,tare da rabo bana son Malam ya gaza tun yanzu, labarin Aliyuna soyayya ce mai zafi,ina fatan shafin gobe ya sa soyayyar ta zama kaffara a gare shi"
"Ina son ki Ummul"
Ta dungure masa kai tana faɗin "Gashi nan akan mace ka bijire mini sai farkawa nayi naga ba mota ka gudu can gidan Abba Hakimi" "Ki yafe mini" ta ce "Kada ka sake, ta shi kayi breakfast idanunka duk ya faɗa da alama ko barci ba kai ba" da hannu irin yaran kuraman nan ya yi mata nunin azumi yake. Ta kalle shi sai kawai ta girgiza kai kafin ya tashi Khalil ya yi sallama, sosai ya yi mmkin ganin Yaa Sheikh zube a gaban Ummul, Yaa Sheikh ya miƙe ya dawo kusa da Ummul.
Ta amsawa Khalil tana sakin murmushi sai yanzu kuma Khalil ya lura da wacece Ummul, Kyakkyawar mace mai nagarta kuma wayayyiya mai ilimi addini da boka, macan data ɗauki ɗan ta kamar abokinta friendly to her family. Ta haɗuwa Khalil breakfast, Suna zaune Granddaughter ɗin Yaa Sheikh ya fita da matar shi Zulaiher suna ce mata Hajiya.
Halisa zaune tsakiyar parlour Mother ta riƙeta, Abba Hakimi na zaune gabanta hannunsa riƙe da Alkur'ani da kuma ruwan rubutu. Yaa Sheikh daya shigo ya tsaya yana kallonsu da son jin abin da ke faruwa, A wahale Halisa ta buɗe ido ta kalli Yaa Sheikh wata murya ta ce "Modibbo ka ce kada su rabamu ina son ka, ina son ka zasu rabamu" zuciyar Yaa Sheikh ta buga sai yanzu ya gane kuma ya fahimta daidai, ya ƙarasu a karo na farko ya zube gaban Abba Hakimi ya ce
"Kada kayi haka Abba, kalli abin da tayi mini da tai losing memory idan ka cire mutanan jikinta ya zan?" Mother ta kalli Yaa Sheikh ta ce "Tayi recovering ɗa zo, tana dawowa daidai kai ta fara tambaya ta ɗaga hankalinta, daman kuma Dr ya ce short-term memory 10-15 seconds ya ke ɗauka, dalilin ruwan daya kwanta a kanta ya sa ta jima, ban san me Abba Hakimi ke nufi ba amma ya ce dole ya raba Halisa da abin da ke kanta" Halisa ta miƙa hannu tana kiran "Abbana ka taimake ni, ka faɗa masa ban hanaka mu'amala ta matarka ba kada su rabani da jikinta" Abba Hakimi ya ɗauki ruwan rubutun ya watsa mata a fuska tai ƙara, da sauri Yaa Sheikh ya riƙe hannun Abba Hakimi idanunsa ya yi jajir jijiyoyin kansa sun fito ya ce "Ka tausaya mini Abba,kada kai haka" Abba Hakimi ya kalli Yaa Sheikh ya ce "Kasan da cewa Aljanu basa tabbata a jikin mutum? Kasan nasan ba Halisa ke son ka aljanar jikinta ce, dole na raba su idan har kana son ta ka tsaya ka gina soyayyarka a zuciyarta...




Kamar saka number ta ba shi da amfani, kun hana masu siyan special su siya sbd fitarwa, na kasa sani hakan Soyayya ce ko ƙiyayya?*_Ƴan Youtube masu tambaya nawa zan siyar musu da IDAN BA KE su saurara, akwai wanda suke buƙata sai na duba farashi mai yawa tukun😂🫣 TSINTACCIYA,SIRRIN MU, ABU MALEEK Duk Available ne, ZAIN ABEED ma na siyar 08119237616_*


Yaa Sheikh ya ware idanunsa sosai akan Abba Hakimi yana son fahimtar da gaske yake masa? Koda yake iya zamansu ai Abba Hakimi bai taɓa yi masa wasa da abu mai muhimmanci ba, dukkan wani ilimin addini mai nagarta da tsafta a wajan Abba Hakimin ya samu, sai wanda ya ƙaro a makaranta da kuma masana manyan malamai,ya haɗa da wanda Yake da shi hakan ya sa ya zama babban malamin addinin na gaban kwatance.
Ya daidaita nutsuwarsa tare da kame kansa waje guda a taushashe ya ce
"Ka da kayi haka Abba"
Abba Hakimi ya kalli Yaa Sheikh yana son karantar yanayin shi sai bai ga komai ba illa Ilhama da tarin nutsuwar dake shimfiɗe a fuskar ta shi
A karo na babu adadi ya ce "Yaa Sheikh ba son matarka ka ke ba da gaske, kuma baka nemi hanyar da zata soka da gaskiya da amana ba"
Ya yi jim kaɗan na wani lokaci ya ɗora da
"Ka nemi soyayya ta Gasky wacce take kasancewa har bayan rai, idan kace a haka zaku tafi to abun ba zai haifar da ɗa mai ido ba"
Halisa ta ƙwace riƙon da Mother tayi mata jikinta na rawa taja gefe zuciyarta na ɗagawa da sauri Yaa Sheikh ya runtse idanunsa,
Wani abu mai kama da zullumi na ratsa masa zuciya ya daidaita lamarin da yake addabar zuciyarsa ya numfasa kaɗan idanunsa a narke ya ce "Ba aljana jikinta"
"Na sani" cewar Abba Hakimi. Ya kalli Halisa kafin ya ce "Nayi hakan ne domin nasan wacce alƙibila zuciyarka take fuskanta, bayan kaci amanata ka yaudareni ka rusa yarjejeniyar da mukai, bayan kafi kowa sanin muhimmancin al'ƙawari da riƙon amana" Yaa Sheikh kan shi a ƙasa domin ya manta wanne amana yaci wacce kuma yarjejeniya Abba Hakimi yake magana akai,
Ya yi murmushi mmkin ƙarfin halin Yaa Sheikh a karo na farko kafin ya ce "Zan nemeka ne, zaka san kuma da ni ka ke magana, zan nuna maka waye ni, batun aljana kuma ai kasan akwaita banyi ƙarya ba, kuma kasan dalilin daya sanya ta rabu da jikin matar taka, Aljanu ke ɗawainiyya daku, ka rabata da Aljanin dake son ta, sai ka ƙi rabata da aljanar jikinta wacce ke son ka da gaske kamar rai, hakan mugunta ce ko mene? Aljanin dake son ta shi ne ya nemeka da sharri Aliyu, Aljanar dake son ka kuma ita ce ta kare ka daga sharrin aljanin, ita kuma ta sanar dakai cikin jikin Zahrah, kuma ita take hanaka kallon Zahrah da idanun rahama" ya sauke numfashi yana jin dole ya hora Yaa Sheikh ta yarda zai furta kalmar so da Halisa, ya kuma karɓeta da hannu bibbiyu, aman da ya yi agaban kowa ya lashe abin shi ya ce "Ka ɗauka ban san komai ba? Banyi mamaki ba, abu ɗaya ya sanya naji cewa ko wanne namiji zai iya sauya halayyar shi da ɗabi'a da nagartar ƙwarai da yake da ita akan mace, sufa mata shaiɗanun maza ne, idan ka iya kallonka kuma sai ka wanke, yanzu kuka fara rayuwa baka san abin da gobe zata haifar ba, yanzu nayi imani cewa Halisa ita ɗaya ce, ba wasu aljanu amma kai sai da ka mutu tare da naka" babu wanda ya yi magana. Ya juya kan Halisa yana faɗin
"Matar kina son Yaa Sheikh? Kina son zama da shi?" Sai a lokacin ta ɗago kanta da rinannun idanunta numfashinta na fita da ƙyar ta juya ta kalli Yaa Sheikh, bai kalleta ba amma ƙirjinsa bugawa na tsoran abin da zata furta "Ina son Abbana"
Ya sauke ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya mai ƙarfi na hamdala ga Ubangiji Abba Hakimi ya sake cewa "Me ya sa ki ke son shi?" Ta marairaice fuska tana juya ƙaramin bakin nan wanda yake a shirye wajan fidda zayyana ta ce "To ai mijina ne, gashi zan haifa masa baby ko Yaa Sheikh"
Kunya ta sarƙafe Yaa Sheikh a Wajan bai ɗago ba, bare ya ce mata wani abun data kalli ƙwayar idanunsa ko ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login