Showing 54001 words to 57000 words out of 197828 words

Chapter 19 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9289

yake da ita, fuska kame. Hannu goye abaya tare da carbi yana ja. Banda ƙamshin Roja babu abin da ke tashi a main parlour.
"Allahu Akbar Allah ya baka haƙurin zama da uwar mata Malam, ni tsoro na ɗaya kada a dinga nunaka da baki ana ka mijin sa'ar babar shi" Zahrah data ƙarasu parlourn tai tsaye a gefen Yaa Sheikh ba tare data kula Jadda ba ta ce.
"You look good My Excellency".
A can bedroom Kuka sosai Halisa take sai rigima take ita kawai wajan Dada zata, da ƙyar Mother ta rarrasheta, ta zuba mata komai na buƙata cikin torelly bag ba tare da sanin Zahrah ba.
Maimoon ta ce "Matar Yaa Lee ga gift inji Yarima Khalil" Mother ta ce "Gift?"
"Eh, shi ya bani wai na bawa matar Yaa Sheikh, ni kuma kawai zan bawa Halisa" Mother ta amshi box ɗin ta buɗe, wani gold ring ne mai kyau sai ƙyalli yake, ta ce "Zan ajjiye waje na, hannunta akwai ring har biyu ya isa, Allah ya tsare ya ki yaye sai na kira waya Daughter" Halisa ta kalli Maimoon tana mata gwalo ta ce.
"Yarinya na tafi gidan mijina, duk abin da ya faru zan ajjiye miki labari ko na dinga faɗawa Mother tana gaya miki" Mother ta ce "A'a na shiga uku bani a nan" Yaa Sheikh tuni ya shiga mota, shi kaɗai ne a baya Saif-wazir na driving..
Zahrah a motar Ishaq-Hakim ita da Halisa da Maimoon. Mother ta ce ba zai taje rakiya ba.
Kai tsaye gidan Abba Hakimi suka nufa. Yaa Sheikh ne kawai ya shiga sbd babu lokaci, ya shige jikin Abba Hakimi yana sauke numfashi, rauninsa ya bayyana kasancewar yana jikin Abban nasa, a karo na farko ya riƙe Abban da kyau murya bata fita ya ce.
"Ba zan iya ba Abba" Abba Hakimi bai fahimta dan haka ya ce "Kai mutum ne mai tsoran Allah da gudun hakƙin wani, balle matarka kada ka damu, ita Halisa ƴar riƙo ce shekara nayi zan amshi abata" ya zare jikinsa yana sauke numfashi tare da yin sallama.
Daga nan suka ɗauki Umar-khan kai tsaye suka shige Airport inda jirgi ke jira. Tunda daga jirgin hankalinta ya tashi amma bata nuna ba, ta riƙe hannunta da kyau, Umar-khan na gaba sai Zahrah Halisa na biye da ita a haka suka shiga cikin jirgin, suna shiga Halisa ta riƙe kanta sbd tsoro, Umar-khan ya kalli Zahrah ya ce "Wajenku na cikin vip" Zahrah ta kalle shi ta ce "Yana ciki ne?" Umar na zama a mazauninsa ya ce "Gaskiya ban sani ba, ku shiga ku gani" ba tare da Zahrah ta ce komai ba ta nufi vip ɗin, jin takun tafiya a bayanta yasa ta tsaya tare da kallon Halisa ta ce "Ke kuma lafiya kike boye ni? Na manta ba a saba ba, Umar nuna mata wajan zama"bai ɗago kai ba ya ce "Wajan zamanku ɗaya ne ai duk vip" Zahrah ta riƙe ƙugu ta ce "kan uba, tayaya haka ya kasance kana nufin tare zan zauna da ita ga mijina kuma?" Sai a lokacin ya ɗaga kansa tare da kallonta ya ce "To ai suna ɗaya kuka amsa, matsayi ɗaya"


"Kamar yaya suna ɗaya? Umar ya kamata kasan me zaka ce dani, ka gane" ya haɗe hannaye waje guda ya ce.
"A'a ranki ya daɗe, mai da wuƙar mijin naki shi ne ya bada umarnin haka" ta haɗiye yawun takaici tare da shigewa vip, daman ita Halisa ta jima da shigewa, dan haka Zahrah na shiga ta samu Halisa zaune ta sunkuyar da kanta ƙasa, wajan ya haɗu sosai akwai duguwar kujera wacce Halisa take zaune akai, sai kujera mai guda biyu, tunanin Zahrah ya bata mai guda biyun ita ce wacce zasu zauna ita da Yaa Sheikh, ta nemi waje ta zauna idanunta akan Halisa ta ce.
"Ina mijina?" Tai shiru taƙi cewa komai. "Ba magana nake miki ba, na lura kin fara ganin wajan barcina?" Ta ɗago lulu eye's ɗinta wanda suke sheƙi kamar an tara musu ruwa sbd yadda hawaye ya kwanta cikinsu. A tsiwa ta ce.
"Ina mijina?" Zahrah ta zare ido tare sakin baki da jin abin da Halisa ta ce. Ƴar fillo tai murmushi kawai tare da girgiza kai ta ce "nifa kamar haka naji kince Anti shi ne nake ƙara tambaya, to a haka naga wajan kam" Zahrah ta ɗaga hannu zata ɗauke Halisa da mari suka ji gyaran murya.
Gaba ɗaya suka ɗaga kai a tare daga Uwar gidan har amarya Zahrah, basu yake kallo ba wayarsa yake sakawa a airplane mode. Yaa Sheikh ya riƙe ya saba akan duguwar kujera yake zama, sbd yana ɗan samun hutu yayi barci kafin ya isa inda zashi, kai tsaye ba tare daya lura da Halisa ba ya nufi duguwar kujera tare da zama dab da ita. Numfashin Halisa ya kusa ɗaukewa sbd wani mugun shaƙar ƙamshin Roja da tayi, gashi Yaa Sheikh ya zama ƙato babba sosai har kafaɗar shi na rufe kanta.
A karo na farko zuciyar Zahrah ta shiga bugawa gabanta ya faɗi,ta juya ta kalli Halisa wacce ta kafe Yaa Sheikh da idanu, a hankali kuma ta kalli Yaa Sheikh wanda ya nuna kamar bai san da mutane a wajan ba. Ta kasa magana ta rasa a wanne ma'auni zata saka haka, anya bata hau tsaunin da zai kaita zuwa ga hallaka ba?. A zahiri Yaa Sheikh ya mance ya taho da matayen nasa har biyu, da uwar mata da kuma ƴar rainon shi. A hankali aka fara sanarwar a ɗaura blet, Zahrah ta ɗaura Halisa kuma ta rasa me ake cewa sbd cikin harshen turanci ake maganar, sai faɗa computer take tana ƙara sanarwa.
A nutse ya ware rawani kansa domin duk a zaton shi, shi kaɗai ne a cikin vip ɗin, kyakkyawar sumar shi ta bayyana abin mamaki ilahirin sumar kan shi daga gaba jajir take tamkar wanda ya fara furfura, daga baya kuma baƙaƙirin tai luff har wuyan shi. Ya sauke hannunsa akan Alkyabbar jikinsa ya ɗan buɗe gaban kaɗan sbd nauyi da tayi masa, yana kammalawa yaja blet, daidai lokacin aka fara sanarwar a shirya jirgi zai tashi, Halisa ta razana ta ƙanƙame jikinta, kanta ya shiga juyawa sai tayi nan luu tayi nan luu, lokacin da jirgi ya ɗaga zuwa sama Yaa Sheikh ya lumshe idanunsa ba zato ba tsammani yaji an fasa wata gigitacciyar ƙara kafin ya buɗe idanu ta faɗo kan cinyarsa babu numfashi....


Paid
It's 500
08119237616"Shiru" ya ce yana sakin bakin tare da mai da Idanunsa kan glass cup ɗin da ya tsiyaya tea aciki. Ta tura baki gaba ba tace komai ba duk da irin ƙaiƙayin da bakin yake mata, haka nan taji kamar ana mintsininta akan Halisa yi magana cikin sauri ta ce.
"Nima ina jin yunwa na sha shayin naka?" Cak ya ajjiye tea ɗin daga hannunsa yana ɗaukan tissue tare da goge bakinsa, ta ɗauki shayin daya rage zata kai bakinta ta ji ance "A'a" ta ajjiye cup tana miƙewa tare da bin bayansa, sahun tafiya da yaji a bayansa yasa ya tsaya, tayi saurin dawowa gabansa suna haɗa ido ya ware mata manyan idanunsa masu kaifi ta tura baki ta ce "Na sake magana banga ka riƙe bakin ba ai" Yaa Sheikh ya girgiza kai kawai tare da shigewa bedroom ɗinsa yana ɓoye yanayin fuskar shi. Ta kalli inda ya shiga sai kuma ta juya tana kwashe tray ɗin. A main parlour ta samu Zahrah zaune tana breakfast ga wata maid nayi mata tausa a ƙafa. "Ke zonan" cewar Zahrah Halisa ta dawo ta zauna tana ɗauke kai gefe guda, saboda har yanzu bata mance mari da zagin da Zahran tai mata ba, Zahrah ta ajjiye spoon ɗin hannunta wanda take shan tea da shi ta ce.
"Kai breakfast ɗin sai yanzu? Ko bai ta shi bane" Halisa ta kalle ta sai kuma ta ɗauke kai tana faɗin. "Shi ya ce na tsaya" Zahrah ta ce "Shi Yaa Sheikh ɗin?" Tai shiru ba tare da ta ce komai, tasan indai zatai magana to zata saki layi ne, Maid ɗin ta kalli Halisa da sauri, ai ko ita da tayi shekara da shekaru tana aiki a gidan Yaa Sheikh magana bata taɓa haɗa su ba, infact ko parlourn shi bata san ya yake ba, Ummul ce kawai take kai masa breakfast ita ma iya dining room, sai ya gama yabar wajan take zuwa ta kwashe, idan kuma yini gida zai yi a ranar basa taɓa zuwa part ɗin, Umar-khan ne ke kai masa dinner, bai fiya cin lunch ba sai dinner, anytime yana tare da butar shayi kamar buzu. Mamaki ya cika Maid ɗin jin abin da Halisa ta faɗa wai shi ya ce ta jira? Who is she to him?.... "Whatever, Ke yama kika ce sunanki?" Maid ɗin ta ce "Bara'at" Zahrah ta ce "Ok, duk wani aiki na part ɗin nan, zuwa part ɗin Yaa Sheikh ya dawo hannun wannan yarinyar, idan kun kammala abinci na Yaa Sheikh ita zata dinga kai masa, bana son na dinga ganin wani abu na ba daidai ba, bana son surutu da hayaniya yana saka mini ciwon kai, ko a gidan ubana ban taɓa sanin hanyar kitchen ba, to a nan ba zan fara saninsa ba, kuna gama girki ki bata ta kawo mini nawa" daga Halisa har Bara'at kallon Zahrah suke, suna mamakin ƙarfin ikon nata, duk da cewa Bara'at bata san matsayin Zahrah ba, amma tasan dole da akwai abin da ta taka a gidan... Zahrah ta kaɗa ƙafa tana faɗin "Ku ɗauke idanunku daga kan mijina, daga nesa kuka ganshi ku sauya hanya, duk abin da kuke nema ni zaku faɗawa, koda abin cin gidan ne ya ƙare" Bara'at ta ce "Ok, amma kula da abincin gidan yana wajan Ummul" It's your problem, I just finished planning what I want" ta juya kan Halisa tana faɗin.. "Jeki breakfast ki saman a bedroom" tana faɗin hakan ta shige part ɗinta, Halisa ta bita da kallo a zuciyarta tana mmkin halin Zahrah. Miƙewa Bara'at tayi Halisa ma haka, tabi bayanta har zuwa sashen kitchen, ma'aikata ta gani mata da yawa ko wanne da abin da suke a kitchen ɗin. Da sauri Bara'at ta nufi wajan Ummul tana ce wa "Yau naga abin mamaki Ummul" kyakkyawar matashiyar matar wacce zata iya shekaru 50 zuwa sama ta kalli Bara'at ta ce. "Da akai me Ukkuti Bara'at?" Bara'at ta sauke numfashi ta ce "Wata mata na gani, mai iko da isa, wallahi na tsorata da yanayinta" Ummul tai murmushi tana ajjiye abin hannunta ta ce "Faɗimatul-zahrah bin Umar Farouk, matar Yaa Sheikh" a tare duk suka ce "Matar Yaa Sheikh?" Ummul ta kallesu ta ce "Na manta ban shaida muku bane, sai a haƙuri da juna ko?" Idanunta ya sauka akan Halisa wacce take dube dube duk abin da suke faɗa tana ji amma hirar bata gabanta, Ummul ta girgiza kai kawai, tana mai jin wani abu a ranta, yarinyar tana nan dai babu sauyi a tare da ita kamar yadda yake nuna mata ita a waya. Hawaye ya sakkowa Ummul ko yanzu ta mutu ta yi farin ciki, Aliyu ya samu gefen rayuwar shi kamar yadda yake faɗa mata a koda yaushe.
Bara'at ta ce "Ummul wace ita kuma wannan?" Ummul ta ce "Masu gidan ce" "Masu gidan kuma?" Cewar Suhaima Ummul ta ce "Ina nufin mai aikin Zahrah ce" ta kalli Halisa da kyau tana mai sakin murmushi ta ce "Sunanta Halisa, ƴar uwar Zahrah ce an bawa Yaa Sheikh riƙon ta amana ne, zatai amfani da sunan Halisa bin Sheikh Aliyu haydar Aliyu" Halisa ta ƙarasu wajan Ummul da sauri fuskarta ɗauke da kyakkyawan murmushi ta kama hannun Ummul ta ce "Laa kema kin sanni ashe, kuma kin san anyi...." Ummul tayi saurin rufe bakin nata tana cewa "Ba'a yin surutu a ɗakin girki, Bara'at akwai tray tana shirya breakfast ki bawa halisa" Bara'at ta ɗakko tray ta bawa Halisa ita kuma ta ce a kitchen ɗin zata zauna ta ci.
Bayan ta gama cin abincin Ummul ta miƙa mata farar madara mai ɗauke da zuma a ciki, batai musu ba ta amsa "Nima ina son na iya girki sosai, ina son yi wa Yaa Sheikh girki mai daɗi" Ummul tayi kamar bata ji zancen na Halisa ba, taci gaba dayin aikin gabanta tana son a akai gidan ciyarwa Yaa Sheikh abincin akan lokaci.
Zahrah na tsaye a gaban mirrow anci uwar kwalliya sai ƙarinin mai take, wayarta dake ringing ta ɗauka ganin sunan Deen ta ce "Uhm maye daman nasan babu mai kirana sai kai" daga cikin wayar ya ce "Ba wannan zaki tambaya ba, fara duba number" da sauri Zahrah ta duba number da mmkin take kallon number ta Saudiya ce,what does that means? Ya katse mata tunani da faɗin "Ki daina mamaki na riga ki sauka a Madina, ke kawai nake jira, don't make any mistakes nazo da maganin da ki ke buƙata, ina son ganinki" The surprise of his behavior prevented Zahrah from speaking. "Wallahi ki san yadda akai ki ka zo, ko ki ganni a gidanki" yana faɗin haka ya kashe wayar babu jimawa ya tura mata address ɗin inda yake, Zahrah ta dafa kai da sauri kuma ta juyawa zuwa ɗaya bedroom ɗin nata a nan ta samu Halisa tana shirya mata kaya a wardrobe, zama tayi ta ce "Ke kin fara menstrual?" Halisa ta ɗauka gyaran kayan take nufi kai tsaye ta ɗaga mata kai alamar eh. Juyawa tayi ta nufi part ɗin Yaa Sheikh.
Fitowar shi kenan daga Library room ɗinsa, ya zauna sanye da wata tattausar Jallabiya a jikinsa hannunsa cikin sumar kansa, cikin nutsuwa ya gyara zama akan duguwar kujerar da yake kai hannunsa riƙe da Cup yana shan green tea wanda Ummul ta kawo masa da kanta, speaking calmly ya ce da Khalil.
"Uhm surutu dai" Ta cikin waya Khalil ya saki dariya ya ce "Ya muke da matarka? Allah ya nuna mini ranar da zata barbabaɗa tana ɗauke da cikin Yaa Sheikh, koda yake kace baka son ta ai, auren dole akai maka" Yaa Sheikh yaja idanu ya rufe yana jinsa fresh sbd barcin da ya yi, cikin son dakatar da Khalil ya ce.
"Wallahi ba auren dole bane, ni na zaɓi matata It was completely my plan..." Katse wayar ya yi jin yana faɗin abin da mai shirya ba, tare da rufe kansa. Tsaye ya ganta a kansa babu sallama ya ɗauke kai kawai yana ci-gaba da danna waya tare da duba abubuwan da Umar-khan ya tura masa.
Ta zauna kusa da shi tana cewa "My Excellency baka fito ba har yanzu hope lafiya?" Kai kawai ya jinjina mata ba tare daya kalleta ba, ta haɗe jikinta da nashi tana cewa "Daman nace ina neman permission zamu shopping da ƴar fillo" har lokacin idanunsa yana kan waya bai ce komai ba. Ta shafi fuskar shi tare da cewa "Ba jimawa za mu yi ba kaji My Excellency" Jotter ya ɗauka da pen ya yi rubutu kana ya ajjiye mata a gefenta haka kurum yaji harshensa ya harɗe baya jin yin maganar. Ganin ƙoƙarin rungome shi take son yi ya ɗan miƙe tsaye, yasan cewa hakƙinta take nema, kuma yasan girma da ƙarfin hakƙi amma ya zai? He's not interested at all, baya son Ubangiji ya kama shi da wannan laifin.
Tabi bayan shi da kallo, tana ji a ranta dole ne ma tayi gaggawar aiwatar da burin dake ranta, Yaa Sheikh ya dawo hannunta sai yadda tai da shi tayi imani da Allah idan ya zo hannunta shi da wata ƴar mace kuma har abada, ba zai iya kallon kowa a matsayin mace ba dole sai ita, What is the solution? where will she start and what will she do now.


"You can go,
Ina buƙatar gyaran part,
With food" shi ne abin da ya rubuta mata a jikin Jotter ɗin, ta duba kenan dole mutum ɗaya ya tsaya, ita gasky ba wani gyaran ɗaki da zata iya, bayanta ciwo yake idan ta yi,kuma bata saba ba. Fita tayi ta samu Halisa a main parlour a kwance barci ya ɗauke ta tunda ta farka da asuba bata koma ba, gashi tai aiki ta gaji sosai bata san barcin ya ɗauketa bama sbd kallo take. Tana zuwa ta fisgo ƙafar Halisa zuwa ƙasa ta faɗo daga kan kujerar, a tsorace ta ce "Hande en boni me na yi Anti?" Zahrah ta ce "Ai hutu kika samu kenan? Ai babu ranar da zaki huta, zaki ta wahala har abada, kije ki gyara part ɗin Yaa Sheikh, ki kai masa lunch zan fita unguwa" kanta a ƙasa ta kasa cewa komai, tana zaune a parlourn Zahrah ta fito cikin wata duguwar riga ta yana mayafi hannunta riƙe da hand bag, kamar yadda Zahrah bata kulata ba itama bata kula ta ba. A compound ta ci karo da Umar-khan yana fitowa daga mota hannunsa riƙe da takarda. Ya ce "Evening" ta share sa, ta nufi wajan wani da alama shi ne drivern gidan.
Kai tsaye Umar-khan gidan ya shige ya samu Halisa zaune kanta a ƙasa tana gyangyaɗi ya ce "Matar Malam" tai saurin jan mayafin abayar ta ɗora a kanta tana yi masa murmushi ta ce "Ina yini?"
"Lafiya, barci a nan kuma? Yaa Sheikh ɗin yana ciki?" Ta ce "Ban sani ba" ya jinjina kai ya ce "Ok bari na duba, kije ki kwanta mana" ita dai ba tace komai ba ya nufi Part ɗin Yaa Sheikh barci yaci ƙarfinta, ta kwanta nan ƙasan carpet.
Umar-khan ya zauna bayan ya gaida Yaa Sheikh ya ce "Na cike komai na makarantar, gobe aka bada izinin ta fara zuwa, Mother ta ce komai cikin gaggawa take buƙata" ya miƙawa Yaa Sheikh file ɗin takardun Halisa bai amsa ba, sai tsare Umar ɗin da idanu da ya yi, Umar yana fahimtar shirun na Yaa Sheikh hakan ya sa ya ce.
"Al Aqeeq International School for Girls, Safiya Opens 7:30 ita ce makarantar" Yaa Sheikh ya jinjina kansa tare da miƙewa ya shigewa ɗaki. Wajan mintuna goma suka fito tare da Umar-khan wata Milk ɗin jallabiya ce a jikinsa, sai golden ɗin Alkyabba daya ɗora a kan jallabiyar, ya fito a babban malaminsa sai ƙamshin Roja yake bazawa, yana fitowa idanunsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login