Showing 180001 words to 183000 words out of 197828 words

Chapter 61 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9294

murza yatsun hannunsa yana duba lokacin tare da tunanin inda Umar-khan ya tsaya, slowly ya ɗago kan shi cikin sa a ya sauke idanunsa akan Umar-khan shi da Hafsat suna hira kamar sun jima da kamuwa da junansu, Ya girgiza kai kawai tare da komawa ya jingina da jigin motar shi. Beeherh ta taho da gudu ta ce
"Abbana shi ne tun daga ranar nan baka dawo ba, kuma Mumy bata zo ba?"
Ya durƙosa ya ɗauketa yana kallon Kyakkyawar fuskarta ta yarinyarta ga baby hijab a jikinta ta saka hannu ta fara wasa da gemun shi ta ce
"Ni yau wajan Mumy zan kwana" Yaa Sheikh ya fesar da numfashi ya ce
"Rigima Beeherh,yau za kiga Mumy" daidai lokacin Umar-khan ya ƙarasu Hafsat ta durƙusa ta ce "Ina yini Abba" ya jinjina mata kai yana buɗe bayan mota tare da saka Beeherh ciki, Umar-khan ya shafa kan shi ganin kallon da Yaa Sheikh yake masa. Cikin rawar murya ya ce "Uhm dama....dama...dam"
"Mene haɗinku?" Yaa Sheikh ya katse kunyar Umar-khan cikin inda inda ya ce "Yaa Lee ina son Hafsat ne, ina son aurenta idan ka bani dama" Yaa Sheikh ya kalli Hafsat ya ce "Kina son shi?" Ta kasa magana sbd kunya ita duk duniya ta yarda ta kuma amince Yaa Sheikh shi ne babanta domin a wajan shi ta tasu "Uhm"
Sanin halinsa tayi saurin cewa "Eh Abba" tana faɗa ta kwasa da gudu tayi ciki. Ya girgiza kai, Umar-khan ya buɗewa Yaa Sheikh mota ya shiga, daman yau gabaɗaya kamfanin shi dake kano ya zaga wanda suke wata jahar ne bai je ba....kafin su zo gida Beeherh tayi barci Halisa dake zaune a parlour da ƙaton ciki haihuwa Yau ko gobe ta miƙe da ƙyar tana riƙe kujera cikin saurinsa ya ƙarasu tare da kwantar da Beeherh ya kama Halisa ya zaunar da ita a ƙasan carpet ya ɗauki pillow ya saka mata ta ɗora ƙafarta tayi murmushi tana jan hancinsa ta ce
"Na gode Yallaɓai" Ya zauna yana danna mata ƙafar cikin tsananin so da kulawa wacce kullum take ƙara yawa a zuciyarsa ya lumshe idanunsa jin tayi masa wlcm da zazzafan kisses ɗita tun daga bakinsa har zuwa wuya suka kalli juna ta ce "Sannu da zuwa" Ya jinjina kai sbd ya gaji da gaske, gashi bashi da burin fita wata ƙasar. Ta kalle shi ta ce
"Yarinya muka samu?"
Ya kalli Beeherh dake barci a nutse ya ce
*"Beeherh Sheikh Aliyu haydar Aliyu"* ta ce
"Yaa Sheikh mai yara da yawa" Yana shafa cikinta idanunsa tuni ya juye ya ce "Ina son yara, sosai ina son nawa na kai na sama da ashirin" ta zare idanu ta ce "Ashirin tab"
Zahrah dake fitowa hannunta riƙe da Azkar ta ce "Haba Uwar gida kada ki zama raguwa mana" Halisa ta ce
"Ba wani nan, kiyi masa hanya kawai ya ƙara aure" Yaa Sheikh dai idanunsa a rufe yake ya ce "Kwana biyu na lura Fatymerh Zahrah tafi jin tausayina" Ya miƙe tsaye Halisa ta miƙe suka haura sama suna shiga ta cire masa rigar jikinsa ya jawota ya baya tare da mannata a ƙirjinsa idanunsa rufe yake sauke mata wasu lafiyayyun kisses masu wahalar fassaruwa ya saka hannu ya farke bra ɗin jikinta ya ƙara farke under wear ɗin cak ya ɗauke zuwa toilet ta ce "Mene haka kuma" ya ciji kunnenta ya ce
"Wanka zaki mini".... Mother na zaune a parlour hankalinta gabaɗaya baya jikinta ta ce "Maimoon bi bayan Fattoumah" Maimoon ta ce "Mother kin san halin Auta da sanyin jiki daga kai abinci sai ta zauna" Father ya ce "Haba Maimunatu jeki mana" ta miƙe tsaye tana fita Compound El na fitowa daga mota sanye da kayan police ya yi wani irin kyau ta ce "Uncle El da yamma" ya taɓe baki kamar zai shiru ya ce "Ban waje wajan Fattoumah na zo" Maimoon ta ce "Komai Fattoumah idan tayi wari za muji" El ya buɗe mata idanu ya ce "Ke kuma munafuka halinki ɗaya da mijin naki ai" ta rufe baki ta ce "Au kana Nufin Prince Khalil munafiki ne?" Ya mata banza tayi dry kawai ta nufi bakin ƙofar ɗakin gatekeeper ta ce "Baba Fattoumah data kawo maka abinci fita waje tayi ne?" Shiru ba amsa ta ƙara magana shiru, sai kawai ta tura ƙofar wata irin gigitacciyar ƙara wacce ta cika compound ɗin ta fasa hakan ya sanya El fitowa da bindiga a sukwane, da gudu Mother da Father suka fito El-bashir ya ce "Ke lafiya?" Banda rawa da ɓari babu abinda jikinta ke yi ta kasa magana, El ya shiga cikin ɗakin kai tsaye idanunsa ya sauka akan Fattoumah dake kwance an ɗaureta da igiya an rufe bakinta da wani abu, jini na zuba ta ƙasanta alamar fyaɗe akai mata......




*Masu tambayar complete book's ɗina👇🏾*
Tsintacciya 500
Uncle ne 400
Sirrin mu 500
Abu maleek 500
Sai na aureta 300
Izzar so 300
The new emir 300
👇🏾
Zain Abeed 1,23 ₦1000
Dare da duhu 1000
Idan ba ke 1000
08119237616👈🏾 kuyi magana WhatsApp.*_Arewabooks@Nimcyluv77_*
*Women Adviser*
*Elegant online Writer's leader*
*Hausa Novelist*
*Social media presenter, Ngo, human rights*
Follow the link👇🏾
https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL


El-bashir was shocked ya kasa motsawa duk da kasancewar shi Namiji, kan shi ya yi wani irin sarawa zuciyarsa na harbawa, idanunsa sukai jajir wani irin ruwa ya kwanta a cikinsu, ya ɗauke kai da sauri daga kan Fattoumah wacce take numfashin wahala. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ya furta a fili.
Cikin sauri kuma ya shiga ciki yana durƙosawa yadda Fattoumah take kallon El-bashir babu ƙifatawa ya ƙara sanyawa El wani irin tashin hankali a fuskar shi aka ajiye masa tabon da har abada ba zai taɓa gogewa ba, his whole body was shaking zufa na yanko masa all over his body.
"Fattoumah!" Mother ta kira sunanta a gigice tana ɗora hannu a ƙirji lokacin da El yake kunce igiyar jikinsa tare da zare abin da aka sanya mata a baki. Mother ta saki kuka tana cewa
"Allah ya isa, Allah ya isa, Allah ya isa Ubangiji ya saka miki Mamana ko Uban waye shi wallahi sai nayi Shari'a da shi"
Ta ƙara sakin wani kukan tana riƙe Maimoon da Zeefa gani take kamar suma haka zai faru da su yanzu. Ta ƙanƙame su a jikinta ta ce
"Ya Allah wacce irin rana nake gani yau ni Maryamu, wacce jarrabawa ce me ya sa na aikeki wajan mugu azzalumi Fattoumah, me ki kai masa ya zaɓi ya lalata gobenki da rayuwarki bakiɗaya Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ya Allah da ganin Wannan ranar gwara mutuwa ta"
"Mother ki daina faɗar haka ne ya samu Fattom, me akaiwa Fattom jini ke zuba a jikinta" Zeefa ta faɗa yarinyar ta gigice da ganin ƴar uwarta cikin wannan halin.
"Maimoon riƙe Nazeeferh ki tabbatar kin kula ku shiga cikin gidan yanzu"
"But Mother" a gigice ta ce "Maimunatu!"
Maimoon ta fashe da kuka ta rungome Zeefa suka bar wajan. Father was speechless yana ganin idan akwai wanda Mother za tayi Shari'a da shi to babu makkawa shi ne, domin daman sharri ɗan aike ne, kan me shi yake bi. Faɗin Ubangiji ne, ita zina bashi ce dole ka biya da hannunka, kama ta diìna tû danò.
Abin da ya shuka yake girba, kashin kajin daya shafuwa kansa ya shafi yarinyar da bata ji bata gani ba, yarinyar da babu wani kyakkyawan kusanci tsakaninta da shi, tana ƙyamatar duk abin da zai, tayi masa tsana ainun tun akan Yaa Lee, da ƙyar ya samu ya lallaɓa ta dawo yadda suke. Ya saki kuka.
"Laifi na ne, it's all my fault kiyi haƙuri Fattoumah" El ya ɗauki Fattoumah ganin yadda take ta razana ta kuma kafe shi da idanu kamar wacce take jira ya taimaketa, bai ji nauyin Mother ko Father ba ya shiga mota tare da ita a jininsa cikin sauri Mother ta nufi gida tana ɗaukan mayafi da key car.
Tasan yadda El yake a fusace da wahala ta same shi, Father ya ce
"Jirani mu tafi tare"
Tayi masa wata muguwar harara tare da yin ƙwafa ta shiga mota tana danna horn ta mance babu gatekeeper babu alamun shi.
Bai taɓa jin ladamar abinda ya aikatawa Zahrah ba sai yanzu, kunyar haɗa idanu da duk wani na shi yake uwa uba kuma Mother wacce yake jin babu wacce zai kaita jin zafin abinda ya faru idan akwai bai shige *Prince El-bashir Ahmad Nuran Sarki* ba.
Ya jima da fahimtar shaƙuwar dake tsakaninsu ba wai iya haɗuwar jini bane, hadda abin nan da ake kira da _Blind love, first love between heart and heart_.
Bai san ya akai ba, kawai ya ganshi ya yi parking a harabar Aminu Kano teaching hospital! Ya buɗe mota muryarsa was shaking ya ce
"Nurse, Nurse, Dr"
Cikin sauri wasu Nurse's suka zo suna janye da gadon marasa lafiya ganin shi ɗauke da kyakkyawar budurwa or under age baby, Fattoumah. She's 14 yrs old going to 15 amma tana da jikin girma so ma sha Allah, kaf cikinsu tafi kowa fuskar kamala tana da idanu masu sanyi bata son hayaniya, but she's so cute damn cute irin shhhhh ɗin nan..
Tana da kafiya da zuciya hakan yasa suke zaune da El lafiya komai ta ce Uncle ɗina ko tana kuka Mother ta ce ke da waye?
Sai ta ce " *UNCLE NE*"
Suka amshi Fattoumah daga wajan El wata ta ce
"Sir You have to change your clothe ya ɓaci da jini" A dame ya ce "Owk" was what she's sayed to him. Ganin El da police uniform ya sa basu tsaya tambayar police cikin Raped case ɗin ba.
In few minutes El ya kira Sergeant ya shaida masa, Sergeant ya kira C.F.P Commissioner of Police. Daga nan ya kira Human rights, wanda suke da haɗin gwiwa da Ahip tare da Ngo.
Yana nan tsaye Mother ta ƙarasu a gigice ta ce
"Mubasshir Ina Mamana"
"Clam down, she'll be fine" ta dafe kai tana kuka ta ce "Mubasshir ina cikin tashin hankali, ace mai gadin gidana the old man ya yi rapping ƴar cikina, mai yasa har yanzu ba a maganin masu fyaɗe ne? Zan tabbatar daga kan Fattom babu wanda ya ƙara aikata fyaɗe a jihar Kano" Ta rushe da kuka ta ce "Ya lalata rayuwar Fattom gobenta nake ji wacce irin jarrabawa ce, mai yasa baƙin halin Ubanta zai sauka kanta?"
Ya kama hannunta har zuwa emergency ɗin ya zaunar da ita, ya kasa cewa komai zuciyarsa ta tsaya da aiki ya zama kamar wani statue..... Yaa Sheikh ne ke tafiya cikin kamfanin sarrafa shinkafar shi yana mai lura da komai, cikin nutsuwa yake jinjina kan shi yana sauraran abin da Umar-khan yake faɗa masa. "An kammala komai gobe za a fitar da container goma, kafin zuwan azumi dai zamu fitar da containers kusan 200" he just nodded his head. Silent ringtone ne ke tashi ya zura hannunsa cikin aljihu ya ɗauki wayarsa Samsung ganin sunan wanda ke yawo saman wayar ya sanya ya yi jim yana tunani gently kuma ya yi answering call ɗin yana lumshe gajiyayyun Idanunsa tamkar mai jin barci. Ya kara a kunne.
"Mubasshir Ahmad Nuran Sarki" Yaa Sheikh said. Sbd jin El ya yi shiru sai ajjiyar zuciya yake saukewa, a hankali kamar zaiwa Yaa Sheikh kuka ya ce "Abba"
"Speak,Son." Cewar Yaa Sheikh yana mai da hankalinsa zuwa ga wayar sbd raunin El daya bayyana ta ciki.
"Amma zuciyata babu daɗi, anci mutuncin wacce a keso nake burin aura Abba"
Yaa Sheikh ya yi shiru yana jin maganganun ya kasa fahimta. Halin Yaa Sheikh daya sani ya sa El ya ce "My girlfriend was raped" ya ƙara da faɗin
"I mean Fattoumah"
Ya runtse idanu, yana kiran sunan Allah a zuciyarsa cikin kamala ya ce "Where are you now?" "At hospital, Aminu Kano teaching hospital" ƙit, ya kashe kiran yana juya zuwa harabar kamfanin nasa hannunsa ɗaya riƙe da Alkyabbar jikinsa ɗaya kuma yana shafa gemunsa, Umar-khan ya biyo bayansa da sauri tare da buɗewa Yaa Sheikh bayan mota, shi kuma ya nufi gaban mota tare da yi mata key suka nufi hospital. Cikin ƙaramin lokaci Family suka san abin da yake faruwa, hatta Dada ta bata garin kano al'amarin ya risketa, Abba Hakimi ya dubi Mother ya ce
"Ina ne garin su Mai gadin?" Idanunta ya yi jajir ta ce "A Ɗan-batta yake" Ya dubi Ishaq-Hakim ya ce "Amshi Address da komai, na yi magana da police kaje ayi arresting nasa" "To, Abba."
Ya fita waje, Yaa Sheikh da kansa ya ƙara duba Fattoumah tare da yi mata ɗinki yadda yake girgiza kai da yadda idanunsa sukai jajir zaka san cewa zuciyar Maza Aliyu ta motsa.
"Uhm ba kullum ina faɗa ba ana mini kallon ƴar hau, ƴar guguwa? Kawai ka ɗauki ƙaton banza a gidanka kace wai mai gadi bayan kana da zataran ƴan mata balagaggu a gidan" ba wanda ya kula Jadda ta ƙara cewa "Ga irinta nan, kayi mugun gado ita daman zina rance ce ka fara biya duk akan Zara'u Allah yaga son da na kewa yarinyar nan wallahi da Munari ce ba zan damu ba" Ta fashe da kuka sosai tana matse ƙwalla ta ce
"Masifa yanzu Haruna idan babu damuwa kawai ka tattara yaran nan ka riƙe wajanka ina tsoran a ɗirkawa wata ciki a gidan nan, shi ya sa ake son mutum ya aikata abu mai kyau ba komai yake zama ƙaddarar bawa ba, hadda son zuciya, kayiwa ƴar wasu anyiwa taka"
"Jadda ki daina wannan maganar" ta miƙe tana kallon Uncle Bashir ta ce
"Algungumi gaskiya ce baka son na faɗa ko? ai dama ƙawata Didi na nan tabbas da mun haɗu munci mutunci ko wanne ɗan banza, ai duk tare mukai ƙuruciya tasan halin uban baku club club ba wanda bai sani ba a faɗin jihar Kanon dabon lijeriya"
"To Allah ya kyau"
"Ya kyauta abin da ya fi haka ai, kawai ya cuci yarinya ni wanda zai aureta nake tunani, mazan yanzu daba kunya gare su ba"
"Ko yanzu aka ɗaura mini aure da Faɗimerh na shirya" Jadda ta kalli El ta ce "Allahu Akbar, kun wanda bai damu da duniya ba ko? To ubanwa zai hanaka auren Zara'u"
Fitowar Yaa Sheikh daga cikin wani emergency room ya sanya Jadda yin shiru tana kallon Yaa Sheikh wanda ya ƙara cika idanu fiye da baya, bai kula kowa ba ya nufi wani office kai tsaye yana dafe kansa yadda yaga jikin Fattom ya yi ya sanya shi shiga cikin tashin hankali, baya son depression and stress su kama shi, Ya rufe idanu da kyau da sauri ya buɗe ganin yadda yake hasko cin mutuncin da tsohon ya yiwa Fattoumah. Zuciyoyin kowa babu daɗi babu kamar Barrister Maryam da IGP kuma Prince El-bashir Ahmad Nuran Sarki. Tana ganin an gama lalata rayuwa da goben ƴarta, abu ne wanda kan iya zama tabo a zuciyar Fattoumah za kuma taji zafin mahaifinta Father da gaske idan ta san cewa shi ne sila, El yana ganin kamar shi aka ruguzawa rayuwa anci mutunci his fiance, an lalata kima da darajar uwar yaran shi... Halisa na zaune gabaɗaya yau bata jin daɗi ko sallah a zaune take cikinta ya sakko ƙasa sosai tun safen kuma ruwa ke fita a jikinta gudun kada ta tayar da hankalin Yaa Sheikh ya sanya bata gaya masa ba, shima ya lura sai ya kawo rikici ne kawai irin nata domin tun jiya faɗa take ji da shi abu kaɗan zata ce ita ba haka kai ni ka fita ma daga ɗakin kawai, ya kan lallaɓata a samu zama lafiya. A lokutan ya dawo dayin azumi cikin kullum yana lazumtar ko wacce rana gudun faɗawa halaka, baya iya kusantar Halisa sbd condition ɗin ta, Ga Zahrah zero take gare shi baya iya komai. Zahrah dake kallo ta dubi Halisa data ɗan ja tsaki ta ce "Lafiya kike dai ko?" "Uhm lafiya" was abinda ta ce. Wayarta ta ɗauka ta kira Mother tana ta ringing ba a amsa ba, can ta kira ta Maimoon babu jimawa ta ɗaga jin muryarta babu daɗi ya sa cikin dauriya Halisa ta ce
"Moon lafiya?" Maimoon ta fashe da kuka ta ce
"Mai gadin Gidanmu ne ya yiwa Fattom fyaɗe" Halisa ta miƙe tsaye sai kuma ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!"
Wani irin murɗewa mararta tayi, lokacin guda bayanta ya riƙe ta kasa motsawa cikin tashin hankali ta yarda wayar sbd tasowar wani irin masifaffan ciwo mai kama dana mutuwa a firgice ta ce.
"La'ilaha illallah Muhammadur Rasulullah S.a.w wayo bayana wayyo Abbana zan mutu" zufa ta shiga yanko mata cikinta ya shiga rawa da ɓari na tsananin ciwo.
"Subuhanallah ba dai naƙuda ba Halisa" "Kira mini Abbana mutuwa" Zahrah ta gigice tausayin Halisa ya kamata domin bata mance wahalar data sha lokacin haihuwar Muhammad ba, Halisa na kuka Zahrah na kuka suka rasa yadda za suyi, cikin sa a Zahrah tunani ya faɗo mata har zata kira shi da number sai tayi tunanin idan da number Halisa ta kira zai fi ɗagawa, tana ɗauka ta shiga ɓangaren calls babu wasu kira sai number ɗaya wacce a rana sai ayi waya goma da number babu suna sai Double kisses a jikin number tayi kiran number ba jimawa ya ɗauka, cikin nutsuwa daman kiran nata yake jira jin shiru ya sanya Yaa Sheikh sauke numfashi yana rufe idanunsu tare da lafewa jikin kujera ya ce "Kankanaty"
"Ba ita ba ce" Ya zaro idanu sai kuma ya basar ya riƙe kansa da kyau ya ce "Sorry Wife"
"It's okay, Halisa wanted to speak with you"
"Oh!" Ya ce yana rufe idanu jikinsa ya saki. Ihun! Halisa ya sanya Yaa Sheikh buɗe ido yana furta "Yaa Rasulullah!" Cikin kuka da ciwon dake cinta ta ce
"Abbana zan mutu, cikina, marata, bayana babyn zai fito ta baki wayyo Allah na mutuwa zan yi" Ya runtse idanunsa ya miƙe cikin nutsuwa duk da a rikice zuciyarsa take ya ce.
"Yi addu'a, Zahrah karɓi waya" Halisa ta ƙara wani kukan da gaske ji take ba zata rayuwa ba.
"Wife" Zahrah ta ce
"Na'am" ya ce
"Can you drive?" "Sure"
Ta ce tana riƙe Halisa wacce jikinta ke rawa ta durƙoshe tana yarfe hannunta, kukan Halisa duk ya dagula masa lissafi ya ce "Fito da Zawja ina tunanin motar ta akwai mai maza zuwa Aminu Kano, kiyi driving a nutse"
"In sha Allah sweetheart ka kwantar da hankali" ta miƙe zuwa part ɗin Halisa ta ɗakko mata ƙaramin hijab wanda ba zai takura ta ba, itama ta saka hijab da ƙyar ta iya miƙar da Halisa zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login