Showing 114001 words to 117000 words out of 197828 words
Chapter 39 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
numfashi ya ce.
"Aliyu ya akai Halisa ta zama ƙanwar El-bashir?" Yaa Sheikh ya yi shiru Ummul ta ce.
"Bari kaga babbar hujja sai ka gasgata da idanunka" ta miƙe tare da fita, wata iriyar zabura Mai martaba ya yi dashi da Umma A'isha lokacin da sassanyar muryarta ta ratsa cikin parlourn....
Littafin kuɗi
₦500
08119237616
Mai son posting har weekend 1kBa iya su Mai martaba ba, hatta Mother ta girgiza da ganin wacce ta shigo, wani abu yake shirin faruwa mai kama da almara banda haka yaushe zasu ganta a daidai wannan lokacin?
Abba Hakimi ya sauke numfashi yana girgiza kansa da son tabbatar da abin da idanunsa suke gane masa, da gaske ita ce. Har kawo lokacin Mai martaba bai gasgata abin da ƙwayar idanunsa ke gane masa ba, ya ƙarasa gareta yana mai gyara Alkyabbar jikinsa.
Idanu cikin idanu wato eyeballs to eyeballs.
"Fulani" Mai martaba ya furta cikin rawar murya yana riƙe hannunta, ta dai kalle shi ta kasa cewa komai amma irin kallon da take masa yafi kama da kallon wanda ka sani shekara da shekaru.
"Fulani ke nake gani, da gaske ke ce?" Farin cikinsa ya kasa ɓoyewa har bai san lokacin daya rungometa ba a gaban mutanan ya ce.
"Allhamdulillah! Lallai Ubangiji ya yi gaskiya,duk wanda ya yarda da Allah to zai isar masa, you're still alive. Zuciyata bata yaudareni ba da kullum take faɗa mini kina raye saɓanin wasu da ki ka zama matacciya a idanunsa, Shukru ilaika Ya Allah"
Ya saketa a hankali har lokacin bata ce komai ba, kamar bata gama dawowa daidai ba, duba da yanayin yadda take kallon mutane.
Umma A'isha ta ce
"Nana idanuna ke gane mini ikon Allah, da gaske ke ce Nana?" Gabaɗaya idanunta ya cika da hawaye bata taɓa tunanin zata ƙara saka ƴarta a cikin idanunta ba, Wacce ake ta magana a kanta sai binsu take da kallo zaka ɗauka bata taɓa saninsu ba sai yanzu. "Besty"
Ta ce tana nufar inda Yaa Sheikh yake zaune shi ma yana binta da idanu, tana zuwa ta zauna kusa da shi tana riƙe hannunsa ta ce.
"Besty where is my daughter, ina Danejona take?" Abba Hakimi ya yi murmushi mai sauti ya ce "Idan duniya da gaske daman bai ci a manta Besty ba"
Sai a lokacin Ummul ta saki murmushi itama tana bin su da idanu kafin ta ce "Ta ya ya zata manta wanda yake kula da ita da wanda ya reni yarinyarta?"
Uncle Haroon ya ce
"Na kasa fahimta, kuyi mini dalla-dalla, Khadijah ba cewa akai ta ɓata ba? Ina aka sameta aure ta sake har ta samu yarinya kamar Halisa? Ya akai Yaa Sheikh ya san inda take, kuma ya akai Aliyu ya auri Zahrah bayan yasan akwai cikin wani a jikinta? Meye dalilin El-bashir na son kashe jininsa, Ya akai Yaa Sheikh ya zama ɗan matar nan bayan gabaɗaya mun Shaida ɗan gidan Engineer Aliyu ne da Barrister Maryam? A fitar da zuciyata daga cikin zullumi wallahi kai na kulle kamar wani drama haka nake ganin abin" Ummul ta ce.
"You don't have to be worries, i think this is the right time daya dace gaskiya ta kuri ƙarya, kowa kuma ya san abin da yake ɓoye, duk abin da zai je ya dawo ku ɗauka tsararre ne daga Ubangiji, hukumu lillahi ya tsara komai a lokacin daya so, ya kashe wanda ya so, ya kuma raya wanda ya so, kada muyi baƙin ciki, har abada ba zan taɓa amsar Arɗo daga wajanku ba, ina son dai kuyi mini adalci akan abin da zan faɗa muku" Ummul is an educated, beautiful, intelligent woman in the community.
Mother ta riƙe hannun Ummul cikin kuka ta ce
"Don Allah ki rufa mini asiri Ummul-khairy, Wallahi ina son Aliyu kada ki rabani dashi, ina jinsa kamar ɗan dana haifa a cikina" Father baya gane karatun da ake idan hankalin shi ya yi duba to ya tashi.
Ummul ta ce.
"Kada ki damu Barrister, kawai ina son nunawa Engineer ƙarshen shi da yake son tirsasa Aliyu yin abin da bai niyya ba, nayi imani da Allah ko kai ne ka haifi Aliyu to a wannan karan ba zai iya yi maka biyayya wajan sakin Halisa ba"
Tai shiru tana sauke numfashi ita kanta zuciyarta babu daɗi a hankali ta ce.
"Ka tuna lokacin da matarka ta haihu acikin asibitin Specialist Yola dake Jimeta?" Father ya jinjina kai yana furta.
"I remember the day, we went to visit Yola"
Abba Hakimi kallon Ummul kawai yake sai yanzu ya lura gabaɗaya nutsuwarsu ɗaya da Yaa Sheikh, har yarda take juyawa hannunta da yadda take son tankwashe ƙafa lokaci zuwa lokaci kuma tana son girgiza kai musamman idan abu ya bata mmki, ko acikin wayayyun mata masu tarin ilimi da wahala a samu kamar Ummul-khairy Abdullahi Abdul-majeed.
Ummul ta miƙe tsaye sai kuma ta zauna ta ce.
"A wannan rana ni ma ina cikin Specialist Yola, lokacin ina ɗauke da cikin Aliyu rayuwa ta mini zafi, bana da kowa mijina daya kasance Arɗo cikin Rugar Bello Allah ya yi masa rasuwa, wanda kuma kashe shi akai akan wani cikar buri, iyayena sun yi nesa dani, infact bana cikin Familynmu sbd fushin da mahaifinsa ya yi, baya son Abou-Aliyu ni kuma na kafe shi nake so, ya ce naje idai auren Fulani ne zan gani, lokacin da mukai aure da Abou-Aliyu Arɗon Rugar Bello ban sha wahala ba, mun rayu cikin farin ciki walwala kwanciyar hankali da jin daɗi, ban taɓa ɓatan wata ba. Rana tsaka Arɗo ya shigo gida da ciwon ciki a ranar bai kwana da rai ba, gari na wayewa aka naɗa sabon Arɗo, a cikin satin ciki ya bayyana a jikinsa, na fara shiga wata sabuwar rayuwa, nasha wahala da taimakon Ubangiji na raini cikin nan, ranar haihuwa a daddafe naje asibitin Specialist Yola dake ina da file acan, aka amshe ni ina shiga kuma aka shigo da Barrister Maryam itama tana naƙuda, mu duka mun sha wahala mun ɗauka ba zamu kai labari ba, cikin ikon Allah Barrister Maryam ta haihu kuma namiji amma ya zo babu rai, sakamakon duguwar naƙuda da ruwan da babyn ya sha a ciki, tana Haihuwa ni ma na haihu, kyakkyawan jariri duk da wahalar rayuwar da muka sha amma girman Aliyu ya bani tsoro, sumar kanshi har rufe ido take saboda yawa, tun a lokacin sumar kan nashi kala biyu ne, nayi farin ciki amma na kasa bayyana shi a fili, a lokacin tunanin yadda zan kula da shi kawai nake, na lumshe jajayen idanuna zuciyata cike da zullumi a hankali na kalli Barrister Maryam na ce.
"Ina tunanin addu'a za mu yi da Ubangiji ya sauke mu lafiya, baƙin ciki bai kamace mu ba" cikin kuka ta ce.
"Dole nayi kuka, baki san tsayin shekarun dana ɗauka ina addu'ar Ubangiji ya bani ciki na haihu, saboda uwar mijina ta takura mini tana tunanin ni juya ce, gashi Allah ya amshi addu'a ta kuma Ubangiji ya amshi abin dana haifa" Nayi murmushi kawai ina sauke ajjiyar zuciya mai nauyi kafin na furta.
"Riƙe Babyna idan kina so bani naki wanda ya rasu" bisa mamakina sai naga Barrister Maryam ta tsorata komai take tunani a lokacin ohu! Kamar na shiga ranta na ce. "Kada kiyi kaddama, ki ɗauka ɗana Aliyu shi ne wanda zai kawo daidaito tsakanin ki da uwar mijinki, mu duka muna cikin damuwa bani da hali bani da ikon kula da Aliyu, bani da wadatacciyar cimar da zan samu ruwan nonon shayar da shi, wandon da zan sakawa Aliyu bani dashi, ina da zuciyar nema da tawakkali amma a wannan karan na gaza, na bar miki Aliyu duniya da lahira na bar miki shi, ki ɗauka shi ne ɗan da ki ka haifa yanzu, ni kuma Ubangiji zai bani wani a lokacin da ya so" ni kai na nasan na faɗi hakan ne, akan rashin mafitar da bani da ita, da kuma son nemawa Aliyu kyakkyawar makoma, ilimi, nagarta, kyakkyawar tofa. Farin cikin Barrister Maryam ya kasa ɓoyewa da sauri ta amshi Aliyu,ni kuma na ɗauki babynta, babu wanda yasan abin nan sai mu uku, ni, ita, da kuma wacce ta amshi haihuwarmu" Ummul tai shiru tana sauke numfashi idanunta ya yi jajir, ta ɗago kai taga kowa kallonta yake anyi shiru ana sauraranta.
Yaa Sheikh kallon Ummul ɗinsa kawai yake wacce itama take kallon shi.
Khadijah Dada tana kusa da Yaa Sheikh taƙi matsawa, ƙuruciyar shekarun sun motsa yadda take very close da Yaa Sheikh koda iyayenta Abba Hakimi Umma A'isha ba tayi, sun tasu tun suna ƙanana.
Ummul ta ɗauki ruwa ta sha kafin ta ɗora da faɗin. "Ban san cewa kuskura nayi ba wajan sadaukar da jinina ga wacce ban sani ba, kullum da soyayyar ɗana nake kwana nake tashi, gabaɗaya jama'ar Rugar Bello sun ɗauka ɗana ya jima da rasuwa, ni kuma nasan yana nan yana rayuwa a duniya, gidan da yake, da rayuwar da yake duk na sani" tai shiru kafin ta ce.
"Babban kuskuren da ki kai Barrister Maryam barin address details naki a jikin file, na amshi komai wajan Dr, ashe har photo taiwa Aliyu, ganin rayuwar da nake ciki ba sauyi na fara tunanin komawa gidan iyayena, senato Abdullahi Abdul-majeed, a lokacin ya sauka kan mulki, ban sha wahala ba, domin iyayena suna bala'in so na, na tattara komai nawa na fara neman aikin police na samu, lokacin nasan halin da Aliyu yake ciki, shekarar farko ta zaman Aliyu a Madina a shekarar nima na sauka na haɗa plan da komai, naje masa matsayin ƴar aiki ya kuma ɗauke ni, shi kaɗai yake rayuwa Umar-khan ke musu girki da komai, a zahiri plan ɗin El-bashir ne zuwana gidan Aliyu,a baɗini kuma nawa plan ɗin ne domin na samu connection da ɗana, tun kafin bayyanar komai haka kurum Aliyu zai sakani a gaba da kallo, sai nace masa yaya? Sai kawai ya miƙe yabar wajan, wata rana na ce ko kana buƙatar wani abu, sai naji ya ce.
A'a, ina ji kamar ke nake cikin barcina, nasan ƙwayar idanunki, kai tsaye na shaida masa ni ce really mother ɗin shi biological. Ya kasa yarda ya ce mother ita ce babar shi, nasan shi Dr ne a ɓoye a zahiri kuma Malami kuma lecture kuma kai D.N.A test komai ya nuna ni ce babar shi, tun a lokacin Aliyu ya ɗauki ma'adanin ajjiye sirrin shi saɓanin baya da yake da zuciyar shi, ni na bawa Aliyu shawarar kai Dada Rugar Rome, a lokacin da akai mata kurciyya, Dada ta zauna wajan Abokin mijina, yana da ɗa Yabi, suna zaune da matar shi Shatu, fitar Dada daga masarauta ya yi daidai da bayyanar cikin jikinta, nan take aka Shaida mini ni kuma na faɗawa Aliyu, duk sati sai yaje Rugar Rome, kaya kala-kala yake kaiwa Dada, lokacin da ya jima bai ce ba, shi ne suka shiga mayuyacin hali, Aliyu da kan shi amshi haihuwar Danejo ya gogeta da zaitun ya rungometa ya kuma raɗa mata suna Halisa ya ɗora da Danejo, duk sanda zashi yana ɓoye kan shi baya bari aga fuskar shi, sunyi sabo da Halisa ya goyata a bayan shi, yana mata waƙa wani lokacin ya ce _IDAN BA KE ba Aliyu_ har takai shekaru biyar lokaci kuma Aliyu ya kwanta ciwo na tsayin shekaru, daga nan ne bai ƙara waiwayar Rugar Rome ba, sai lokacin da za ai masa aure da Zahrah, rigima sosai ya yi mini akan baya so, shi fa Halisa kawai zai rayu, na rasa soyayyar da Aliyu ke mata,amma hakan baya rasa nasaba da soyayyar da ya kewa Khadijah, ba iya Halisa ba son da Aliyu ya kewa El-bashir ya ɓaci, duk abin da El-bashir ke masa ya sani, amma ya ce ba zai taɓa cin mutuncin jinin Besty ba"
Tai shiru tana ƙara ɗaukan ruwa ta sha kafin ta ce. "Auren Halisa da Yaa Sheikh ba tsautsayi bane, everything that happens is a plan, Aliyu planned how to marry his adopted daughter. I also supported him, na koma Rugar Bello da Aliyu kafin lokacin nai musu bayani suka fahimta, nan take kuma ya maye gurbin Mahaifinsu na shugaban Rugar, shi ne yasa a karɓe Naggen su Halisa daga wajan shugaban Rugar Rome, wannan shi ne" jikin kowa ya yi sanyi ana zaton wuta a maƙera sai gata a masaƙa.
Abba Hakimi ya kalli Yaa Sheikh ya ce.
"Malam ya akai kasan Inda Khadijah take bayan mun wayi gari ba ita cikin Masarauta?" Kamar Yaa Sheikh ba zai magana ba sai ya gyara rawanin kansa yana miƙewa tare da sauya waje, so yake ya yaki ce Dada daga gare shi tunda sirika take wajan shi, ƴarta yake aure, bayan ya zauna ya ce.
"Abba na buɗe idanu a wajan Mother, Soyayya ta gaskiya ta nuna mini, ban san ya akai na kasance wajanka ba, amma mother ta shaida yaye aka kawo ni wajan Umma A'isha, lokacin shekarar Besty ɗaya a duniya, mun shaƙu sosai mun taso tare komai tare, babu abin da nake sha'awa irin yadda Abba ke karatu tare da mutane tun ina shekara goma na sauke Alkur'ani na shaddace Hadisai, a makaranta ɓangaren Islamic nayi na samu abin da nake so, ina gamawa na juya fannin likitanci, lokacin da Mai martaba ya nemi auren Besty ban damu ba, lokacin data bar gidan nan a Matsayin Matar shi, dukkan wata walwala tawa ta ɗauke sai kuma a lokacin na gane ba Soyayya ce ya shaƙuwa ba, abin yafi kama da wanda ka ke so ka rayu da shi irin ta har abada ɗin nan, tun a satin farko na aurenta nake yawan mafarkinta tana kuka, bata cikin kwanciyar hankali, kai tsaye na fahimci Aljani ne a jikinta wanda da bai bayyana kan shi ba sai yanzu, baya ƙaunar kuma ta kasance a gidan mijinta, a wannan lokacin kuma ta samu cikin El-bashir wanda ya ɗagawa wasu jama'ar dake cikin masarauta hankali, bayan haihuwar El-bashir aka sakawa Besty idanu, Aljanin jikinta ya takura mata, bayan shekaru huɗu da haihuwar El-bashir na saka Almajirai na saukar Alkur'ani suka kwana suna yi, 10 a Sakoto tayi mini nasha wahala kafin Aljanin yabar jikinta ta samu barci, sai dai tashin da tayi ta tashi da babbar ƙaddara ta baza tare da fita daga cikin masarautar, komai take akan idanuna cikin sauri nabi bayanta, da ƙyar na kamata zuwa mota na samu wani gida na ajjiyeta,naci gaba da kula da ita tsayin shekaru 3 lokacin El-bashir yana sa shekaru 7. A lokacin kuma na mayar da ita Rugar Rome, a shekara ta 8 da haihuwar El-bashir ta haifi Halisa, wacce take shekaru 17 yanzu El-bashir kuma 25 suna da tazarar shekara 8, nasan El-bashir yana mini kallon wanda na kashe masa mahaifiya ko na salwanta da rayuwarta, wanda kuma bashi da wayo hakan ta faru akwai wanda ya zauna gina shi akan tubalin ƙiyayya dani, Auren Zahrah kuma babu shi akai na domin ba a aure da ciki, na amince zan aureta ne sbd hankalin Father ya kwanta dani kuma nayi masa biyayya kamar yadda Ummul ta ce, na kuma rufa mata asiri, ya akai ta samu cikin ɗan waye ban sani ba, amma nasan tana da dalilin aure na, na kuma san duk wanda ke farautar rayuwata"
"Ikon Allah, Al-hakkumu bowayi gagara misali!" Cewar Uncle Bashir.
Engineer kunya ta kama shi, tsoro da fargaba suka wanzu a zuciyar shi, tashin hankalin shi ɗaya kada gasky tayi halinta akan shi.
"Sannu Aliyu, Sannunka kai da mahaifiyarka bamu da baki ko kalmar gode muku, kin cancanci ki zama uwa ta gari" Abba Hakimi ya juya kan Zahrah ya ce.
"Ina da ikon da Malam, kuma nasan mahaifiyar shi zatai mini karar haka, nayi miki al'ƙawarin da zarar ki ka faɗa mini gasky akan wannan jaririn to lashakka Malam zai aureki a karo na biyu" kafin Zahrah ta ce komai wayar Yaa Sheikh ta ɗauki ƙara ganin sunan Dr ya sanya ya ɗaga kiran.
"Hello Dr Ibrahim ke magana" Yaa Sheikh ya jinjina kai Dr ya ce.
"Mrs Yaa Sheikh Aliyu haydar ta farka daga suman da tayi, akwai babbar matsala muna nemanka yanzu" Yaa Sheikh ya miƙe tsaye yana faɗin
"Gani nan" Ummul ta kalle shi sai ba tayi magana ba, Mother ce a sanyaye ta ce "Aliyu ya dai?" Ba tare daya kalli kowa ba ya ce.
"Matar malam" duk suka kalle shi da rashin fahimta "Wace haka?" Cewar Mother sai a lokacin ya fahimci mai ya yi ya ce "Ta farka kuma da matsala cewar Dr i think am going.."
Abba Hakimi ya ce.
"Ɗan da kata, ina jinki Zahrah" Cikin kuka Zahrah kamar ranta zai fita ta ɗaga hannu tare da nuna direction ɗin da Father yake zaune ta kasa cewa komai sai kuka take tari na sarƙe numfashinta.
"Ɗan Father ne, shi ne ya yi mini cikin na rantse da Allah Abba.....
IDAN BA KE
Isn't free book is for sale, nrml grp 500 for Special grp 1k posting har weekend. 08119237616*_IDAN BA KE_*
BOOK2 PAID BOOK
₦500 Via this number 08119237616
إِنَّ اللّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ
Ilahirin jikinta rawa yake ganin Yaa Sheikh take kamar sabon halitta a cikin idanunta, ta koma jikin bango ta maƙale tana mai da numfashi ƙirjinta na ɗagawa numfashinta na sama, ta rufe idanunta ruf bata san ko ganin inda yake. Yaa Sheikh ya ware jajayen idanunsa wanda suka fara janyewa ya miƙe a hankali tare da nufar ta tun kafin ya ƙarasa ta buga tsalle ta koma bayan Ummul ta riƙe Ummul sosai tana ɓoye fuskarta a bayanta. Dr ya ce "Ka rabu da ita" sai a lokacin Abba Hakimi ya ce "Mijinta ne ai" murmushi Dr ya yi ya ce "Matar da bata san wace ita ba, ta ya zata fahimci cewa mijinta ne?" Abba Hakimi ya ce "Hakan na nufin ba zata amince da shi ba?" Dr ya kalli Halisa tare da juyawa ya kalli Yaa Sheikh ya ce "Ita ai kallon abin tsoro taka masa, sakamakon shi ne namiji na farko data fara gani bayan farkawar ta" Ummul ta ce "Akwai matsala idan haka ne, amma mene mafita?" Dr ya ce "Idan har zai rabe ta anta tashin hankali da ita kenan, ita a yadda take ji ko zai shekara bai kulata ba she doesn't care, a ko wanne lokaci zata iya recovering" Ummul ta jinjina kai alamar gamsuwa ba wanda take jin tausayi irin Yaa Sheikh