Showing 93001 words to 96000 words out of 197828 words

Chapter 32 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9330

ƙara Halisa ta fasa jikinta ya saki baki ɗaya tana neman zubewa ƙasa Yaa Sheikh ya yi saurin taro ta tare da saka hannu ya ɗauke ta cak ya mannata da jikinsa.
A nan kuma ya nemi Prince Bilal ya rasa sai wani hayaƙi dake fita daga bakin Halisa, ta dinga jijjiga tana kaiwa Yaa Sheikh doka ta ko'ina tana neman ƙwacewa amma ya riƙeta sosai tare da ɗora bakinsa a kunnanta yaci gaba da karatu.
"Wallahi zan tafi ka barni haka da raina, yanzu haka ka ƙona mini rabin jikina, zan bar maka mata amma kada ka kusanceta kada ka sadu da matata Danejo"
Yaa Sheikh yaja numfashi sbd yadda take son fin ƙarfinsa ya ce.
"Ikon Allah ne kawai zai hanani mallakar matata cikin watan Ramadana" tun Halisa ƙara ta dawo kuka sosai a hankali kukan ya fara raguwa can kuma tai hamma tare da yin atishawa ta kwanta jikin Yaa Sheikh barci ya ɗauketa..
Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya shima Yaa Sheikh ya sauke daga ita harshi zufa ke yanko musu ta ko'ina duk da kasancewarsu a saman dutsen Jabal an-Nour ɗin.
A hankali ya fara tafiya yana sakkowa ƙasa har ya gama sakkowa da idanu yake bin Umar-khan ba tare da ya ce komai ba.
"Mai martaba ya gama zirayar da zai a madina yana son ɗaukan azumi a Makka, yanzu haka yana masaukin da aka bashi, shi da El-bashir, Ummul ta shaida mini zatai aikin hajjin tama biye kuɗin an gama komai" Yaa Sheikh ya jinjina kai tare da shiga bayan motar ya zauna har lokacin yana rungome da ita.
Umar-khan ya shiga motar kai tsaye ya nufi wani babban masaukin da aka bawa Yaa Sheikh wanda bashi da nisa da masallacin ka'abah.
Sai da sukai nisa Umar-khan ya ce.
"Father ya kira, da alama magana ce mai muhimmanci kuma ta shafi Zahrah ya ce dai ka kira shi immediately idan ka dawo"
Yaa Sheikh yaja idanunsa ya rufe shi kansa a gajiye yake kuma ya wahala, amma zuciyarsa yanzu ta samu nutsuwa dan dan ba a tantance farin cikin Yaa Sheikh da baƙin cikin Yaa Sheikh shi ya sa ba a iya gane sauyin yanayinsa.
Zubin halittar da Ubangiji ya yi masa daban ne dana sauran dukkan Ahhalin gidan nasu. Ya buɗe idanu yana faɗaɗa fuskarsa kamar anyi masa bushara da gidan Aljanna ya kalli fuskar Halisa a hankali ya riƙe tafin hannunta ya haɗa tana shi ya riƙe sosai cikin ƙasa da murya ya ce. "Matar malam mai gayyar aljanu shikenan an gane mini matasan ƙirjin da nake kiwo"
"Magana kake?" Cewar Umar-khan Yaa Sheikh ya yi masa banza.
A haka suka kawo gidan tun daga nesa yake ɗauke da jami'an tsaro ta ko wacce kusurwa. Umar-khan ya tsaya sbd wani Security daya tsayar da shi cikin harshen larabci ya ce.
"I.d card" kafin Umar-khan ya yi magana Yaa Sheikh ya zuge Glasses ɗin ɓangaren da yake zaune ya ɗan leƙo kaɗan, ganin Yaa Sheikh yasa gabaɗaya suka rusuna tare da bashi girma.
"Kayi haƙuri daman an shaida mana idan ba kai ba kada mubar kowa ya shigo duk zaman jiran zuwanka muke" Ya jinjina musu tare da komawa ya jingina da jikin kujerar yana zuge Glasses ɗin sama.
Aka buɗe musu gate suka shiga har gaban ƙofar da zata kai mutum zuwa parlourn daya ya raba parts ɗin gidan Umar-khan ya tsaya, bai ƙoƙarin fitowa ba ya fara danna wayarsa.
Yaa Sheikh ya buɗe ƙofar tare da ɗan dubawa yaga babu mutane wajan a hankali ya fito yana naɗeta baki ɗaya da Alkyabba ko fuskarta ba a gani, a wannan lokacin ya ƙwammace a kalli surar jikinsa wacce take shekara da shekaru a lullube da dai a kallin sirrinsa. Ya nufi ƙofa yana shiga direct ɓangaren da yafi kwanciya a ransa ya nufa can Upstairs yana shiga ya kulle ƙofar ya nufi bed ya zauna yana zare Alkyabbar ya rage daga ita sai ƴar rigar dake jikinta wacce Bilal yasa mata. Ya kama hannunta ya zare zoben hannunta mai ɗauke da tambarin masarauta, sai yanzu ya lura babu baƙin zaren daya ɗaura mata.
"Matar mutum da Aljani" ya faɗa a taushashe yana zaunar da ita saman cinyarsa amma har lokacin barci take,yasan tana buƙatar barcin a yanzu ya kwantar da ita tare da rufe mata jikinta har ya juya ya dawo ya ɗan ranƙwafa daidai kanta ya sumbaci goshinta kana ya juya yana gyara zaman alkyabbar jikinsa tare da ɗaukan hiraminsa.
Sakkowa yake daga saman strais ɗin benen yana gama sakkowa ya zauna saman kujera, Umar-khan ya ce.
"Na manta ban faɗa maka ba, an gama komai na aikin hajjin Hali.....," Kallon da Yaa Sheikh ya yi wa Umar-khan yasa ya haɗiye maganar can ya ce.
"Na matar malam, komai ya zama ready" Yaa Sheikh ya miƙe tsaye tare da juyawa sai da yaje ƙarshen benen ya ce.
"A shaidawa Ummul muna nan, tare da Zahrah" Umar ya ce "In shaa Allah" Umar ya fita. Wanka Yaa Sheikh ya yi ya sauya kaya masu kyau na shan iska, idanunsa har rufewa yake sbd gajiya yana buƙatar nutsuwa sosai bayan ya kunna karatun Alkur'ani ya kwanta gefe guda yana rufe jikinsa kamar wacce tasan yana wajan ta gangaro tare da shigewa jikinsa, suka sauke numfashi lokaci guda. Wata kasalalliyyar ajjiyar zuciya ya sauke yana mai matse idanunsa wanda suke a lumshe, tsananin mamaki da kuma tarin al'ajabi ya sanya Yaa Sheikh fesar da wata zazzafar iska, yayinda daya kejin wasu masifaffun abubuwa nayi masa yawo a saman jijiyoyin kansa, abin da bai taɓa tunanin faruwa kenan dashi ba.
"Shhhh" ya furta a ransa sbd yadda Halisa ta manna bakinta a daidai ƙirjinta tana murzawa duk a cikin barci hakan ya ƙara dagula lissafin Malam.
Ya riga daya Sallama akan wannan murɗaɗɗan yanayin abun gashi a lokacin da bai taɓa tunanin faruwar hakan ba, babu zato bare tsammani yaji mararsa ta ɗaure baki ɗaya, al'amarin ya kumbura tare da harbawa wanda ya kusa tafiya da nutsuwara.
Ya riƙe ta sosai kamar zai tsaga ƙirjinsa ya maida ta ciki haka yaji, a hankali yaja duvet yana rufesu baki ɗaya yana ɓoye fuskarsa a wuyanta.
Ƙara lumshe idanunsa ya yi wanda suka tashi daga launin farare suka koma jaa, saboda tsananin azabar da ciwon da kansa yake masa lokacin guda, a tare suka fitar da wani irin wahalallan numfashi, yadda gangar jikinsu da ƙirkinsu ke haɗewa waje guda, haka ma zuciyoyinsu suke manne, yayinda numfashin ko wannansu yake fita tare dana juna. A haka cikin wannan yanayin barci ya ɗauke sa.
6:45 aka fara shelar anga jaririn watan Ramadan a garin Saudiyya, hakan yasa da Saudiya da ƙasa Nigeria da sauran ƙasashe aka ɗauki niyyar fara ɗaukan azumin Ramadan.
Cikin nutsuwa yake shigowa cikin gidan bayan ya gabatar da sallar Issha cikin Masallacin harami, ya fara haurawa upstairs yana tura ƙofar ɗakin tayi saurin ɗago kanta suka haɗa idanu, ya lura kamar har yanzu a tsorace take ya rufe ƙofar tare da zame Alkyabbar jikinsa ya nufi inda take yana zuwa ya zauna yana ƙara dubanta da kyau.
"Kika tsareni da ido?"
Ta kwaɓe fuska tana marairaice fuska bakinta sai rawa yake tana son cewa wani abu amma ta kasa sai hawaye dake bin idanunta..
Ya ɗagata sama tare da ɗorata saman cinyoyinsa suka fuskanci juna ya shafa kanta ya ce.
"Na gane, wato so yake yana kasa mini ke? Shi ne ya tafi da bakin mganar" ta nuna masa hannunta ɗaya wanda ya riƙe tare da riƙe hannunsa sosai hawaye na ƙara zuba a fuskarta ya goge hawayen ya ce.
"Daga bakin har hannun daya riƙe miki zai sake su" tai murmushi tare da shafa sajansa taja gemunsa ta hannunta ta nuna masa bakinsa sannan ta nuna wuyanta.
Ya ɗora goshinsa a nata tare da yin copping face ɗinsu numfashinsa na sauka a fuskarta.
"Ya kalleki ko?"
Ta ɗaga masa alamar _Eh_ Ya runtse sosai ta bugi kafaɗar shi tare da ɗaga hannu tai masa alama da _"Menene?_
Ya kalli ƙirjinta wanda yake so masha Allah fiye dana shakerunta.
"Tausayin matsan abun ko?" Tai wani kyakkyawan murmushi tana saka hannunsa a baki tare da sakar masa cizo a dole aka mayar da ita kurma dole.
Ya girgiza kai kawai yana kwanciya akan gado tabi jikinsa ta kwanta sosai taji tsoran yadda zuciyarsa ke harbawa sosai. ta miƙe tsaye tare da fara ƙoƙarin cire rigar jikinta taji anyi saurin kame hannunta mai lafiyar ya fesa mata numfashi ya ce.
"Ban shirya ganin zubin lemon tsami ba" ya sakar mata light kisses mai sanyin wanda yasa tai saurin yin zillo cikin ɗaga murya da ƙarfi ta ce.
"Abba!!" Ya kama hannunta tare da ɗorawa a gemunsa ya dinga shafawa kansa a wuyanta yana shan shana ko'ina ya ce.
"Na'am, ƴar kurmar Modibbo" ya shiriri ce tare da ita yasan daga yau bashi da wadataccen lokaci nayi hakan.
Wayarsa ta shiga ƙara ya saketa tare da nuna mata hanyar bathroom.
"Assalamu alaiki Ummul" a bayyane Ummul ta sauke numfashi ta ce.
"Congratulations! Halisa ta dawo naji ko a muryarka" ya tura hannunsa a suma jifa jifa yake faɗaɗa fuskarsa ta ce.
"Zata dawo nan ne? Ko wajanka zata zauna" ya yi shiru dan bai san me zai ce mata. Ta ce "Na fahimta, Zahrah fa ya zakai da ita, Umar-khan ya ce bayan azumi Father na nemanka da gaggawa" Yaa Sheikh ya yi saurin dafe kansa gabaɗaya ya manta ya sha'afa. "Ta zauna nan, ita kuma zatai aikin hajji ne" Ummul ta saki murmushin jin daɗi ta ce.
"Ah! Masha Allah za a zama Hajiya Halisa Danejo Rome banji motsinta ba?" A kasalance ya ce
"An rufe mata bakin ne, hannunma an riƙe sa" Ummi ta ce "Ikon Allah wannan mutane Allah kayi mana tsakani dasu, sharrinsu sai su, amma kana ganin babu matsala?" Ya jima kafin ya ce "Da izinin Ubangiji" sallama sukai ta kashe wayar.
Number Father ya kira yana ɗagawa ya ce "Da kyau Aliyu gwara ka nunawa duniya ban isa da kai ba, idan har nine uban dana haifeka to....," Yaa Sheikh ya yi saurin cewa "Kayi haƙuri don Allah Father, na manta ne kawai" Father ya tari numfashin Yaa Sheikh ya ce "Dole ka manta, kasan duk yadda kayi ka lallaɓa yarinyar nan Zahrah bata saba ɗaukan hayaniya a gidan ubanta ba, duk inda ka ke to ka sanya a kawota wajanka daga nan har a gama Ramadan wallahi idan kaƙi bin umarnina zan yafewa duniya kai babu kai babu ni" ya kashe wayar yana sakin huci kamar zaki.
Yaa Sheikh ya tsaya wani irin abune uban daya haife shi ya dinga iƙirarin zai tsine masa ko ya sallama shi, me ya sa daga wannan sai wannan ne? Laifin mai ya yi me ya sa hakan ke faruwa ne wai?.
Yaji tasa ƙaramin hannunta mai danshin ruwa ta taɓa shi ya kasa kallonta ta leƙa fuskar shi nan ma ya ɗauke yasan zata iya fahimtar halin da yake ciki sbd wayonta ya yi yawa kuma tayi masa sabo mai yawa. Yaji shassheƙar kukanta na tashi ya juya tana ganin ya juyo ta faɗa jikinsa tare da sakin kuka.
Zahrah na kwance cikin dare tana barci taji cikinta ya juya an daki mararta ta farka a firgice sbd fitsarin daya zubo mata, ta tashi tare da nufar bathroom tai fitsari ta fito me take ji haka kamar motsin ɗa? ɗan ma irin wanda yake cikin ƙoshin lafiyar nan, shiyasa yau gabaɗaya bata fito ba sbd yadda cikinta ya ƙara fitowa sosai like 7mnt ɗin nan. Tana wannan tunanin taji cikin yaji gaba da zillo daga ya yi nan gefen sai ya yi nan. Aka fara bubbuga ƙofar ɗakinta ta miƙe tare da buɗewa Bara'at ta gani tsaye da tray ta ce.
"Ya akai da wannan daren?" Bara'at ta ce "lokacin sahur ya yi ne, anga wata yau za a fara azumi" a fili Zahrah ta ce "Tab" Bara'at zata shiga bedroom tayi saurin cewa "Bani nan" ta miƙa mata kana ta rufe ƙofar, Zahrah ta kasa tunanin mene gaskiya shin da gaske cikin yana nan ko ya ya?.
Dubban jama'a musulmai suka tashi da azumi daga ciki hadda matar malam cikin Ikon Allah bakin ya buɗe bayan ruwan zam-zam da Yaa Sheikh ya bata. Ita kaɗai ce a gidan domin tun 3:50 yabar gidan. A hankali kwanakin azumi ya dinga gangarawa har aka gabatar da guda Ashirin sha shida yau ana daren na Ashirin da bakwai daren da ake saka ran ganin Lailatul-ƙadr. Halisa Azumin sai addu'a idan yau an kai lafiya yau kuma da kuka musamman idan taga idanunta Yaa Sheikh wani lokacin kuma tsakaninta dashi sai dai a t.v idan yana tafsir ko an hasko yadda Sallar Taraweeh da Tahajjud take wakana dake shi ne limamin... Yaa Sheikh yana tsaye gaban ka'abah yana karatun mu'ujizal Alkur'ani ta sauka akansa harshensa ya harɗe ya kasa gaba ya kasa baya, ga ayar sosai a kansa amma bakinsa ya gaza furta komai wani hawaye ya shiga sauka daga cikin idanunsa. Shiru masallacin ya yi na wani lokaci a hankali ya ƙara dawowa baya amma faɗin ayar ya gagara sai kawai ya fashe da kuka. Sheikh Hafix ya janye Yaa Sheikh tare da komawa mazauninsa yaci gaba da karatu.
Cikin lokacin ciwon kansa ya motsa a daddafe ya fito tare da bin ƙofar baya ta wajan ƙofar Sarki Abdul'aziz-Bab Abdul'aziz ya shiga mota kai tsaye aka kaisa gida, Halisa na zaune tana karatun Alkur'ani domin yau bata fita Ka'abah ba, taji an shigo ana bin bango tayi saurin miƙewa ta ce.
"Malam?" Ta nufesa da sauri tana zuwa ta riƙe hannu a ta ce "Kan ka ne ko Modibbo?" Ya buɗe da ƙyar ya akai tasan kansa ke masa ciwo? Ta kama hannunsa har zuwa bakin gado ta zaunar dashi ta nufi kitchen ta haɗo tea mai zafi ta saka honey ciki.
"Abba zaka samu lafiya kaji Abbana" ta bashi shayin ya saka hannu ya ture tare da fisgota suka faɗa gado ta ce "Abba baka da lafiya fa, bana son komai ya sameka" ya mirginata zuwa ƙasa tare dayi mata rufa yana zame Alkyabbar jikinsa muryarsa bata fita ya ce.
"Azumi nawa akai yau?" Ta juya idanu ta ce "Ashirin da shida" ya shafa gefen cikinta ya ce "Muna dare na nawa?" Ta riƙe numfashinta ta ce "Daren ashirin da bakwai, daren ganin Lailatul-ƙadr" Ya yi cilli da Alkyabbar yana kama maɓallin gaban ruwa rigarta ya shiga ɓallewa kama ana jona masa shucking haka yake tura kansa a wuyanta yana murza gefen cikinta gabaɗaya ya sake mata nauyin jikinsa a hankali ya zame ya dawo da kansa daidai ramin cibiyarta ya yi mata wani kyakkyawan zuƙa Halisa tayi zillo ta ce "Wayyo Abba zaka cinye mini cibiyata" riƙe kansa kawai yake ha ciwon kai ga kuma abin da ya kejin yau ikon Ubangiji ne kawai zai hana faruwarsa ya tallafo fuskarta baki ɗaya ya ce "Mu ribaci wannan daren mai albarka matar malam" bai bata damar magana ba ya cafke bakinta ya riga ya manta ita ɗin ƴar raino ce, ya manta da deal ɗin Abba Hakimi neman maida Amanarsa yake zuwa cikakkiyar mace...Numfashin Halisa ya tsaya sbd nauyin da ƙirjinta ya yi mata muryarta na rawa ta ce.
"Ribata? Me zamu ribata Yaa Sheikh?" Shi kansa idan ya ce zai iya magana a wannan lokacin ya yi ƙarya kalamansa bakinsa gabaɗaya suka tsaya idanunsa rufe ta cikin zuciyarsa yake tasbihi ga Allah da kuma neman dacewa da rai mafi girma da tarin albarka.
Daren da miliyoyin mutane suke neman tabarraki a tattare dashi, a hana idaniyya barci kowa na neman gamawa da duniya lafiya, a takura zuciya da kirari haɗi da karatun Alqur'ani, daren wuya! Ga wanda ya sanyawa ransa ba zai iya ribatar lokacin ba, daren ladama ga wanda ya yi hasara yana mai yin barci a lokacin.
Daren alheri ga muminin daya damu dacewa da ganinsa. Wannan daren na Lailatul-ƙadr shi ne mafarin buɗe zanan ƙaddarorin ɓangaren zuƙata guda biyu, shi ne ya zama fitila wajan haska abin da yake ɓoye tsayin shekaru, shi ne ya zame raba kaddama tsakanin igiyoyin auren dake saman gajimare suna yawo.
The night became the reason for the separation of Humanity and the demon. Ya zama hasken daya haska zuciyar Halisa Danejo Rome ta gano wacece ita, hakan ya zama barazana ga rayuwar Yaa Sheikh Aliyu haydar. _(Now is the beginning of the manifestation of everything)._
Yaa Sheikh ya sauke numfashi mai zafi yana ƙara shigar da fuskarsa tsakanin wuyanta tare da goga mata tsinin hancinsa a fatar wuyan nata idanunsa rufe ruf! While yana murza hannunsa guda ɗaya a waist ɗinta tare da murza blet ɗin data riƙe trousers ɗin data sanya.
"Abbana sallah ake, kace kada ga shige...,"
Fuskarsa da taji tsakanin ƙirjinta da saukar tattausan labɓansa a fatar wajan ya sanya maganar ta tsaya a fili a wahale ya ce.
"Yasubuhanallah"
Ya riƙe numfashinsa da kyau wanda ke neman ƙwacewa sosai kuma ya jarumtar kame kansa da hana bakinsa abubuwan da suke masa yawo a zuciya.
He followed her body and kissed her with a certain style, ta zabura jikinta na rawa sosai tare da ɓari idanunta ya raina fata duk da har yanzu bata san me yake ƙoƙarin yi ba, kuma bata san meke faruwa Cikin aure ba.
Amma ta firgita da sauyawar Abban nata baya sauƙi a zafafe yake cikin salo mai narkar da zuciyoyin manyan mata balle ta ga da take jaririya mai sauƙin kama tarko.
"Abba wani abu yana bin ƙafata wayo kamar tsotsa Abba ka duban" baya gane yaran maganganun nata yake ji can saman kansa yana masa amsa kuuwa! A cikin kunne.
"Shhhh Li....li..liserh"
Ya faɗa cikin rawar murya shi kansa al'amarin kunya yake bashi, idan ya tuna how hot he's da tazarar dake tsakaninsa da ita.
Bai da tabbacin zata iya ɗauke girman abun da yake shirin tunkararta da ita. Ya zame fuska a hankali daga kan ƙirjinta wanda ya bashi mmkin zubinsa a daidai kunnanta ya sauke bakin yana fesar da huci in a romantic voice ya ce.
"Kin ce kina son sanin sirrin Abbanki?"
"E, ina so Abba. Amma ka ƙi faɗa mini" Halisa ta faɗa tana riƙe fuskar shi kamar yadda ya riƙe nata. Yadda zuciyarsa ke rawa haka gangar jikinsa ke rawa ya yi kiss neck skin ɗinta ya ce.
"Ina jin tsoran bakin nan" ta girgiza kai tana turo bakin Yaa Sheikh ya kasa ɗauke bai ƙasa a gwiwa ba wajan kame ƙaramin bakin tsoran da take ji sam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login