Showing 81001 words to 84000 words out of 197828 words
Chapter 28 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
yaye?*
*Ina yammata da ake shirin aure?*
*Ina matan gida masuson gyara?*
*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*
*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*
*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko uwargida ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*
BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679
IG Bintus-spa-nd-more..
*FTR* 44
Kowa ka duba yana farin ciki da wannan aure hatta Baba Usman ƙanin malam bakin sa ya kasa rufuwa sabida tsananin murna, Sabida Nazeer yayi niyyar tozarta su ne sai Allah ya nuna Ikon shi da isar shi akan lamarin auren domin wanda aka danganta shi da itan ya auri abarshi.
Haka su Ya salisu sukai ta fitowa da mutane tuwon ɗaurin aure suna ci sai dai waɗansu mutanan ma gulmace ta kawo su najin Nazeer ya fasa sai kuma su koma da Labarin Zaki ya amshi auren.
Kafin kice me magana ta cika unguwa wasu ma cewa suke bara zana Zaki yayi wa Nazeer shiyasa ya haƙura maganganu dai kala.kala tunda dama mutum ba'a raba shi da magana.
Daga cikin gida ma hakan ce ta kasance Domin Da matiƙar tsumar jiki Ya jidu ya shiga yana kiran Innah
Wadda taci adon jan lace mai uban tsada sai baza ƙamshi take sabida ƙyan jikinta baka ce ta haifesu ba.
Innah dake tsakiyar dangi suna tsokanarta akan nan da wata tara zata goya jika ita ta amsa masa tana tasowa zuwa wurin sa.
"Innah kinga mayen nan sai da ya auri Nuri"
Sam bata fahimta ba sai ta ce.
"Kai ban gane ba waye mayen Nazeer ɗinne ya koma maye?"
Da sauri ya shiga girgiza mata kai Baki na rawa sabida zaƙuwa yake shaida mata Yadda ɗaurin auren ya kaya har yana cewa shi dan tsabar takaici ma bai tsaya jiran a shafa fatiha ba yabar wajan.
Wata uwar ƙara Innah ta zunduma kamar mai shigar iskoki kana ta zube a wajan tana kuka wiwi wanda hakan yayi tsananin bawa Jidu mamaki kukan da take ne ya janyo hankalin ƴan uwanta dake ɗakin suka fito suna tambayar mene ne?
Da taimakonsu suka kaita ɗaki Jidu ya shiga gaya musu meke faruwa.
Wata yaya a wajan Innah tayo kanshi tana zagin shi.
"Munafuki kaja da yin Allah ne ai duk wata wutar kai kake kunnawa ina jiyar maka ranar da zakaji kunya, Ke kuma Binta kin zauna kina kuka kamar wata ƙaramar yarinya wannan aure ya isheki ishara da duk wani mai takara da soyayyarsu dan Allah kubar yarinyar nan ta huta haka wannan jaraba da mai tayi kama"
Cikin kuka innah tace.
"Haba yaya da zaki faɗi haka yaron fa ance ɗan daba ne kwanaki har bursun yayi akan ana zarginsa yayi kisan kai sannan na ɗauki ƴata guda ɗaya tilo na bashi haba Yaya bakwa tausayina"
Salati yayar Innah ta hauyi sai kuma tace.
"To wanda yafi kowa sonta ya bashi sai ki raba igiyoyi ukun da aka ɗaura musu yau ina zaton baki taɓa ko ganin yaron nan ba amman kin ɗauki karan tsana kin saka masa haba Binta kamar ba musulma ba duk yadda akai akwai rabon zuri'a tunda kika ga Rabo ya nace sabida haka ki taka a hankali kada kiji kunya nan gaba kaɗan"
Da ire iren waɗannan nasihohin masu kama da faɗa ƴan uwan Innah suka shawo kanta harta sami nutsuwa shikuma jidu suka masa zagin tsame nama suka kuma gargaɗe shi akan ya daina gaya mata irin waɗannan maganganun domin tana da ƙaramar ƙwaƙwalwa marar jure damuwa gudun kada ta shiga.matsala
Ita ko Baba sabuwa saboda farin ciki sai da ta taka rawa haka ma Maryam da abin yayi matiƙar birgeta dan har albarka sai da ta sakawa Babar Nazeer.
Maƙota nata shigowa suna Allah sanya alheri kuma ba dan komai suke zuwa ba sai don gulma Idan suka zo kuma haka Baba sabuwa zatai ta gaya musu magana a fakaice.
Dole su Ya Saudat suka tafi gidan Nazeer aka kwaso kayan da aka jera.
Haka suka dawo gida da kayan.
wanda zuwa wannan lokacin Nazeer ya faɗi an tafi kaishi asibiti yana ta sumbatu shi bai haƙura da Nuriyyah ba hankalin Umman shi ya tashi shine ta shigo gidan Su Nur A fusace tana dukan ƙyaure.
Wallahi sai Innah taje ta cire asirin da sukai wa ɗanta.
Hayaniya ce ta kaure domin Sosai su Ya saudat suka yo kan Babar Nazeer wanda hakan ne ya tashi Nuriyyah data ke ta bacci sama sama take jin muryoyi na tashi har ta gaji ta miƙe a hankali ta fita tsakar gidan duk da yadda hannunta da ƙugunta ke mata zugi.
Amman haka ta ƙarasa ta janyo hannun innah dake mayar wa da Babar Nazeer martani.
Itama Babar Nazeer ƴaƴanta ne suka fitar da ita waje.
A ɗaki Nur ta saki Hannun Innah wadda jikinta har rawa yake.
"Duk ke kika cuce ni kika nace sai wancan yaron gashi nan uwar nazeer tazo tana aibata mu abanza"
Da rashin sani Nuriyyah tace.
"Wani abun ne ya faru Innah?"
"Nazeer ya fasa auren ki a wajan ɗaurin aure sai Kakan Asad ya amsar masa auren ki"
Cewar Maryam dake shigowa ɗakin yanzu.
Luuu tai zata faɗi da sauri Innah ta janyota jikinta tana shafa bayanta.
Numfashi taja tare da sakin kuka tana cewa.
"Shine Kuma zasu bawa Asad aure na kamar an gaji dani bayan yayi auren shi ya barni sannan a kuma bashi ni"
Sai ta soma shure ƙafafu a ƙasa tana kuka kamar wata ƙaramar yarinya.
Abin sai ya bawa Innah mamaki duk zaton ta Nuriyyah zata fi kowa farin ciki ne sai ta ga akasin haka wannan yarinya kishin wa ta gado haka ita dai bata da wannan kishin.
"Shagali yau ina ganin bidiri munafuka bayan koke koken da kika gama yi sai shi shine zaki zo kina kuka"
Innah ta faɗa tana ƙoƙarin fita tsakar gida don ba zata iya da iya shegen Nuriyyah ba don ita zuciyarta tai sanyi da lamarin tunda ƴan uwanta suka Nunnuna mata gaskiya akan ta bar wannan aure domin ba'a ja dayin Ubangiji.
Da sauri Nuriyyah ta rungumota tana kuka sosai da iya gaskiyarta tana cewa.
"Innah dan Allah kicewa malam ya raba auren nan wallahi bana son shi ni yanzu Nazeer nake so"
Innah na dariya maryam na taya ta innah tace.
"Haba tattabara uwar soyayyah tunda nima nai mubaya'a da wannan aure kema sai kiyi manyanki sun nuna isarsu akai Nikam ina muku fatan alheri dan wannan aure naku ya bani tsoro ya ƙara sawa naji tsoron Ubangiji sosai Allah yasa hakan ya zame muku alheri"
"Amin Binta haka ake son mutum ya zama mai karɓar shawara muma ƴan uwanki munji daɗin yadda kika amshi shawararmu kuma ina tabbatar.miki auren nan alheri ne sha Allah, Bama son ƙiyayyarki ga surukinki tai yawa gaba kiji kunya Shiyasa amman yanzu kam tunda kin gane gaskiya Alhamdulillahi Allah ya basu zaman lafiya amin"
Cewar Yayarta wadda tai tai mata faɗa a ɗazu.
Innah bata iya amsawa ba sabida kunyar kukan data dinga yi ɗazu sai ma fitar datai tabar Yayarta da Maryam da Nuriyya a ɗakin.
"Ke kuma kukan me kike haka?"
Cewar Yayar Innah.
"Babu komai"
Nur ta bata amsa.
"To kinga dai bake ɗaya bace ance yana da mata"
Gaban Nuriyyah ya faɗi itafa tsoron kishiyar ma take ji.
"To ki nutsu ki kula da mijinki ladabi biyayya kinga dai yadda uwarki take da Baba bamai cewa zaman kishi suke haka zalika tunda take bata taɓa yaji ba dan Allah fatima kema ki zauna lafiya kinji ko"
Nuriyyah ta share hawaye! kana tace.
"In sha Allah Hajiya Yaya nagode"
Haka Yayar Innah taita mata nasiha kana ta fita.
Nuriyyah ta kwantar da kanta a cinyar maryam tana cewa.
"Allah mai iko maryam yau wai Asad ya zama mijina kinga lamarin Allah ko, Nifa na ɗauka Innah zata dake ni ne fa sai naga kuma ta saki kam yanzu ta daina jin haushin Asad"
Maryam ta murmusa kana tace.
"Kina ji fa Hajiya yaya tace sun mata nasiha akan auren kuma ta burgeni da ta ɗauki Nasihar su wallahi"
Nuriyya tace.
"Dama fa Rigima ce irin ta Innah ita bata ga Asad ba Amman Jidu yana ta zugata tana hawa"
Nuriyyah ta faɗa tana dariya.
Maryam ta ɗan dake ta a baya tana cewa
"Yau sai kiyi bacci mai daɗi ai buri ya cika"
Ta wani lumshe idanu Sannan tace wa Maryam.
"Ba bacci mai daɗi ai sai a jikin Ogana Na matsu yazo na ganshi duk da dai wallahi Wannan matar tashi ta shige mana hanci da ƙudundun ne"
Dariya maryam tai.
"Dama shegantaka kike wa Innah ɗazu wallahi dama tace to bari ta gayawa malam a warware auren"
Zare Ido Nur tai tana yamutsa fuska sabida zafin da hannunta ke mata.
Haka suka wanzu suna ta hirar su cike da farin ciki.
**********
Daga gidansu Asad Ummi tace bazatai wani taro ba amman ƴan Biyu sunce wallahi tayi ai yawan rai ne haka suka yanke shawarar kama Waje wanda zatai wuni anan har da su Nuriyyah da Aysha da Asad.
Wajan Biyar na yamma ya fito cikin shirinsa na ɗanyen boyel milk colour sai baza ƙamshi yake ya shiga ɗakin Ummi bayan sun gaisa yace zashi gidan su Aysha.
Ummi tace.
"Gidan su Nuriyyah fa? yakama ta itama kaje kaga yaya suke ciki"
Ya ɗan gyara zaman hularshi tare da cewa.
"Ita sai gobe naje ummi Rigimarta yawa ce da ita yanzu naje sai ta san yadda tai ta ɓatamin rai na"
Ummi tai murmushi tace.
"Kunfi kusa amman dai ya kamata ka leƙa Domin ma ka sanar mata da Wunin da zamuyi"
Ya ɓata rai kaɗan yana cewa.
"Nifa Ummi bana son wannan bidi'ar dan Allah abar wani wuni kawai akai su gidansu haka"
Ummi tai dariya tace.
"Wannan baka isa ba in sha Allah jibi asabar zamuyi wunin ko wacce tai kwalliya aje a ɗauko min su harda kai ƴan uwa da abokan arziƙi su taya mu murna"
Dariya Ummi ta bashi yadda ta hakimce tana tsara yadda za'ai yasan kuma huɗubar ƙannen shine dan haka bai ce komai ba ya miƙe ya fita.
Motarshi ya buɗe ya shiga ya tayar sai gidan Haji Isah wajan Uwar gida sarautar mata gimbiya Ayshatu...................
*Team Nur how market*😝
*Littafin FITAR RABO na kuɗi ne akan farashi mai sauƙi domin biyan kuɗin zaki tura naira 300 ta wannan asusun bankin 0078174806 sterling bank shedar biya ta 08142105218, idan kuma card ne mtn card na 400, zuwa wannan number 08142105218**Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*
*Ina masu kananan nono?*
*Ina masu yaye?*
*Ina yammata da ake shirin aure?*
*Ina matan gida masuson gyara?*
*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*
*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*
*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko uwargida ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*
BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679
IG Bintus-spa-nd-more..
*FTR* 45
Yana tuƙi yana jinsa acikin farin ciki da nishaɗi Allah mai alheri yau shine da zuƙa zuƙan mata har guda Biyu ba tare daya yi zato ba.
Haka ya ƙarasa ƙofar gidan Haji isah wanda sai da ya kusan ɓatan kai damma yana da fasaha da baze gane gidan ba sabida yadda ya jima bai zoba.
A ƙofar gidan yayi parking ya jingina da seat ɗin kujera yana auna yadda zai ya kirata don bai da Numbern wayarta kuma da kunya ya kira Haji Isah yace yazo wajan Ƴarsa.
Haka yasha zaman shi a mota har akai magariba shi bai tafi ba miskilin kuma bai fita ya tambaya ba.
Sai da yaji masallacin dake gefen shi Ana ƙoƙarin tayar da sallah sannan ya fita ya sai pure water a wani shago ya ɗaura alwala ya shiga masallacin.
Sai da suka idar da sallah ya fito suka ci karo da Haji Isah.
Da sauri ya zube yana gaishe dashi, cikin sakin fuska Haji Isah yace.
"A'a Asad kai ne a unguwar tamu dafatan ka shiga gidan nima yanzu na dawo daga wajan aikin"
Ya shafa gemu tare da cewa.
"A'a Abba ban shiga ba, Dama bani da numberta ne da zan neme ta"
Mamaki ya kama Haji Isah na yadda Asad ya nuna kamar wani baƙo sai yace masa.
"Muje to tunda gidan ya zama baƙon ka"
Haka ya saka Asad A gaba wanda kunya ta kamashi har zuwa cikin gidan.
Wanda ya cika da ƴaƴan Haji Isah guda uku mata ƙannen Aysha dake aure duk da ƴaƴansu sai ƙanwar Umman Aysha itama da yaranta waɗanda suka zo tattaunawa akan Batun Auren Aysha wanda yazo musu ba zato don a ranar da aka ɗaura auren ma gidan sai da ya zama babu masaka tsinke sabida ƴan taya murna.
Daga Bakin ƙofar falon Asad ya tsaya Haji Isah ya shiga kiran.
"Mamata fito ga mijin ki yazo"
Daga cikin falo Aysha data idar da sallah tai cikin ɗakinta aguje duk kunya ta kamata wai yau ita keda miji lallai babu abun yabo da godiya sai Allah.
Ƙarasa shiga falon yayi yana cewa Umma.
"Kinga ɗanki da miskilanci wai tun yamma yake cikin mota ya rasa yadda zai ya kira Aisha sai da na dawo yanzu na ganshi a masallaci muka shigo"
Umma da daɗi ya kamata duk da taji zafin Auren da Su Haji Isah sukai wa Asad na biyu sabida ya gaya musu tun ɗazun amman yadda Asad ya tako yazo sai daɗi ya kamata domin ta tabbata baze wulaƙanta mata ƴarta ba.
Sai ta miƙe ta bi Haji Isah cikin ɗaki sauran ƙannen Aysha ma sukai ɗaki suna murnar zuwan Mijin yayar tasu.
Aysha kuwa tsintar kanta tayi da cancaɗa kwalliya ƴar gaske ta saka doguwar rigar atamfa ja da baƙi sai tai amfani da baƙin mayafi abin ka da farar mace sai tai matiƙar yin kyau.
Ta fesa turare mai jan hankali ta ɗauki wayarta ta fita kai tsaye kicin ta nufa ta haɗa mai frut,tare da ruwa da lemo ta haɗa a ƙaton try ta nufi falon.
Ta aje a ƙasan carfet sannan ta nufi wajan sa don tai masa iso.
Da taji nauyin auren amman lecture ɗin da Ummanta da Ƙannenta sukai mata yasa taji ta aje kunyar agefe tana jin zata kula dashi don kulawa ita ke janyo namiji ga mace don namiji kamar yaro yake mai kula dashi yake liƙewa bata tabbatar da zata iya bashi dukkan kulawarta bama sai da taji Abban ta ɗazu yana gayawa Ummanta sun ƙara nemar masa auren wannan yarinyar harma an ɗaura auren tunda taji ba ita kaɗai gare shiba ta ƙara jin ita ma mace zata Bashi dukkan kulawarta.
Tun kan ta ƙarasa wajan da yake tsaye ƙamshin turarenta ya masa maraba.
"Subuhanallahi"
Yace a ƙasan maƙoshi sabida ƙamshin shu'umin ƙamshin ne.
Da sassanyar murya tai masa sallama.
Tare da yi masa iso zuwa falo.
Yabi ta abaya yana kallon yadda take juya jikinta cikin nutsuwa.
Saman kujera ya zauna sai ta zauna a daidai ƙafarsa a ƙasan carftet, Dab dashi sosai ta tsiyaya ruwa a cup ta miƙa masa babu musu ya amsa yana mata godiya.
Cikin kulawa yace.
"Ya kamata ki dawo nan sabida magana nazo muyi kina ƙasa ina sama tayaya zamu ga juna kamar wasu surukai"
Sai tayi dariya kaɗan tare da dawowa kujerar dake saitinta tana cewa.
"Na haɗa maka frut?"
Ta faɗa kanta a ƙasa.
"A'a na ƙoshi ki ɗaga kanki mana kya sunkuyar da kai ƙasa"
Ya faɗa yana ɗan leƙenta.
Gaskiya bata da makusa kuma baya ce yana ƙinta ba tunda matar shi ce ta sunna.
Maganar ƙannenta ce ta hanata bashi amsa suka shigo dukkan su suka zube suna gaidashi.
Ba yabo ba fallasa yake amsawa suka miƙe aransu suna yaba mijin yayar tasu suna kuma yi mata fatan alheri.
"Duka fa ƙanne na ne waccan gajerar ita ke bina yaranta huɗu, mai binta uku ƴar auta biyu"
Duk da yayi mamaki lallai tana da kyan jiki amman bai nuna mamakin ba sabida kada taga kamar yayi mata cin fuska don aure lokaci ne sai yace.
"Kema huɗun zamu haifa next year da izinin Allah"
Sai tai ƙasa da fuska tana dariya.
"To Meemah ga dai ni kin ganni"
Wani sanyi taji yau ɗaya ya ɓoye mata suna zuwa wani da ban.
"Sunan Ummina kenan sunan ki nada daraja wajena gaku ma matata duka dole bazan iya faɗi kai tsaye ba"
Tayi murmushi bata ce komai ba.
"Haka Allah ya tsara auren namu ta dalilin kotu zamu haɗu fatana dai Allah ya bamu zaman lafiya, kuma bake ɗaya bace Akwai Nur Mun jima muna tare kuma Allah ya ƙaddara kece uwar gida na ita amarya Nur yarinya ce don Allah ku zauna lafiya danni bana son tashin hankali"
Tabi bakin sa da kallo wannan ƙatuwar budurwar ce yarinya lallai ma, taji wani dutse ya tsaye mata a zuci amman sai ta danne tana cewa
"In sha Allah baka da matsala dani"
Namiji shike nuna ai kishin sa ada ta ɗauka zai wulaƙanta ta ya nuna auren dole akai masa, amman sai ya bata mamaki ya karrama ta ya bata martabarta bai nuna waccan ta fita ba tunda in wani ne cewa ze sun jima suna soyayyah da Nur amman shi sai yace sun jima suna tare baiyi kalaman