Showing 105001 words to 108000 words out of 197828 words

Chapter 36 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9322

boko yake mafarkin samu ta samu, ba gata akaiwa Aliyu da aka haɗa shi aure da wacce zata kula da dukiyar shi ba? Shi za a wulaƙanta ta, a aura mini ƴar aikinta, to wlh bada yawuna ba, ni nake da ikon zaɓarwa Aliyu macen da tayi mini,
Kuma ita uwar ta shi data ɗaure masa gindi ina ita ɗaya ce a gidan aurenta ko nayi mata kishiya ne?"
Jadda ta fashe da kuka sosai tana kama bakin zani ta ce "Yanzu daga magana akan la'ananniyar yarinya wacce shaiɗan ya yi wa fitsari aka shi ne ka ke zagina Ali? Ni kake tsinewa ka ke cewa na fitar maka daga gidana ai ba kai kaɗai na haifa ba? Ni ce uwar banza ko ba shakka, sbd Allah ina ruwana da shiga masifar yara daga cewa Malam bai kyauta ba shi ne ka zageni ka zagin uwa da uban da suka kawo ni duniya" ta face majina tayi mitsi mitsi da idanu ta ce. "Maimunatu masa kira mimi Haruna, shi da ɗan uwan shi Ubangiji ya ƙaddara na haifi wasu ba shi kaɗai bane"
Father ya ƙarasu wajan Jadda ya ce "Don Allah Jadda kiyi haƙuri wlh ba zagi nayi ba, fushina na sauke akan muna.....,"
"Idan ka sake cewa Maryam munafuka zaka tabbatar ƴar iska ce ni, fita ka bani wake kada na sake ganin fuskarka a gabana" Mother dai na zaune a kujera kanta a ƙasa ta harɗe hannu a ƙirji sai girgiza ƙafa take, ko ba a faɗa ba kasan cewa ranta ya yi mugun ɓaci.
Maimoon ta bawa Jadda waya jin Uncle Haroon ya ɗaga ta cikin wayar ya ce "Maimunatu ƴar Engineer da Barrister ya akai ne ƙawar?" Jadda ta ce "Masifa da bala'i,to kakar Maimunatu ce" ya yi saurin cewa "Barka ansha ruwa lafiya Jadda?" Ta fashe da kuka sosai hankalin Uncle Haroon ya ta shi ta ce "Kana can gidan matanka yaƙi ya ɓarke a gidan Ali, kafin ya kashe ni maza maza na ganka a gidan kai da Bashir, amma dai Ali yaci mini mutunci ya zageni tas zagin da ba a taɓa yi mini ba" ta kashe wayar murya can ƙasa ƙasa ta ce. "Alsulhu khair! Gashi nayi magana a nutse ba faɗa ba ihu, ke kuma Maryam ki barni da shi zai gane ni ba tsohuwar banza ba ce"
Father ya kasa cewa komai, gabaɗaya kansa ya kulle kunyar Alhaji Farouk ta kama cinye shi. Maimoon da Zeefa sai kuka suke, Auta Fattoumah tai shiru tare da kafe Father da idanu tana jin zafin shi a ranta fiye da ko wanne lokaci.
A kusan tare manyan motoci guda uku sukai parking a harabar gidan, Uncle Haroon daga Zaria road, Uncle Bashir da ga unguwa uku, sai Abba Hakimi daga Dawaki road.
Uncle Bashir ya fara fitowa cikin wata dakakkiyar shadda sky blue, sai Uncle Haroon ya fito cikin farar shadda shi ma, gabaɗaya suka tsaya domin gaisawa da Abba Hakimi, Saif-wazir ya buɗewa Abba Hakimi mota, ya fito cikin kyakkyawar tufar shi shadda ruwan madara ɗinkin jamper da babbar riga, ya ɗora hirami akan shi kamar yadda Yaa Sheikh.
Suka rusuna bakiɗaya tare da haɗa baki wajan faɗin. "Barka da dare Abba Hakimi, Ya ibada?" Ya saki murmushi irin nasu na manya ya ce.
"Allahamdulillah, baƙo na shirin tafiya ya barmu da kewa" duk sukai murmushi Uncle Haroon ya ce "To Allah ya bamu lada ya wanke dattin Laifuka" ya ce.
"Amin" Abba Hakimi ya kalli Saif-wazir ya ce.
"Ka jira nan"
Suka nufi cikin gidan, a main parlour suka samu Jadda zaune, Mother ma na zaune har yanzu bata motsa ko gyara zamanta ba, sai da taji muryar Abba Hakimi ta ɗago kai cikin rauni suna haɗa ido ya girgiza mata kai.
Suka zauna bayan sun gaida Jadda ta amsa ba yabo ba fallasa.
Mother ta gaida Abba Hakimi dasu Uncle Bashir.
"Fatan lafiya ne, wannan kiran gaggawa dare har ya fara" Jadda ta fara matse ƙwalla ta ce.
"Lafiyar kenan, ku kira ɗan uwanka kuji dalilin sakin Maryam har saki biyu" Suka saki salati Abba Hakimi ya yi murmushi kawai he's speechless.
"Wanne irin saki ana zaune lafiya,saki kuma cikin azumi?" Jadda ta ce "Idan mutum ya fara shan wiwi da tiramol sai abin da aka gani" Uncle Bashir ya miƙe zuwa upstairs ya samu Father na waya daka gani mai muhimmaci ce, yadda yake ta begen.
"Ka fito muna jiranka" ya miƙe tsaye tare dabin bayan Yayan na shi.
"Wani irin shirme ne haka Aliyu? mai Barrister ta aikata a gareka har haka?" Ka tsaye Father ya ce.
"Ta yi wa Sheikh aure ba tare dana sani ba, kuma ta aura masa yarinya mafi ƙasƙanci a idanun Zahrah, daɗin da ɗawa ba aiwa Familynsu Zahrah kishiya na shaida mata hakan, shi ya sa na yanke hukuncin laifukan da tayi mini, kafin Aliyun ya sauka ƙasar"
Uncle Haroon ya ce.
"Mu kuma sai ka ɗaure mu, tunda mune muka bada shawarar kada ka sani ɗin, mun san da auren tun kafin Aliyu yabar ƙasa zuwa wajan aikin shi, auren Halisa aka fara ɗaurawa kafin na ƴar gaban goshin taka".
"Ni dai bada yawuna ba, Aliyuna ɗa na ne" Uncle Bashir ya ce "Sannu mai ɗa, ka faɗa mana wanda bai da zuri'a a nan balle kayi mana gori, ko ɗan kana ne to yanzu ƙarfin ikonmu ya ƙwace Malam daga wajanka"
Jadda ta ce "Gwara ya zage ku kamar yadda ya yi mini, abin duka ya ɗauka zai dake ni fa? Uhm uhm Allah kada ka nuna mini masifar dana gani ɗazo"
Uncle Haroon ya ce "kaga let by gone be by gone, mu duka ba sa'aninka sa'insarka bane, ba zamu ce komai daga nan har Sheikh ya sauka ƙasar nan, kuma Barrister tana gidan nan ina tabbatar maka za kai ladamar sakin da kayi mata" sai a lokacin Abba Hakimi ya ce.
"A'a Inn shaa Allah da Maryamu zan tafi, ya riƙe yaran shi na tafi da ƴar ɗan-uwana" ya juya kan Mother ya ce.
"Ta shi ki shirya" Uncle Haroon ya ce "Baza ai haka ba Abba Hakimi, ko sbd su Fattoumah" Abba Hakimi ya miƙe ya jima da sanin Father ba ɗan ƙwarai bane son rai dana zuciyar shi kawai yake bi.
Mother ta kwantar da Auta Fattoumah saman kujera, ta nufi bedroom ta ɗauki mayafi waya da hand bag sai kayanta dake torelly bag.
Maimoon ta dinga kuka tana rungome Mother.
Mother ta kasa cewa komai idanunta ya yi jaa ta nufi Main parlour.
Abba Hakimi ya kama hannun Mother suka fice daga gidan zuciyoyin ko wannensu babu daɗi.
Da ƙyar aka samu jinin dake zuba a hannun Yaa Sheikh ya tsaya, akai masa Allura baya son magani shi kuma sai dole, Zuciyar Halisa ta ɗauki zafi haka kurum taji har Abban nata zafin shi take ji, don mai zai bari wata banza tana faɗa masa magana kuma ta gaji ta ɓoye batun auren su.
Ta shige ɗaki ta kwanta sai kuka take, cikin dare ta kasa barci ta dinga juyi ta saba da jikin Yaa Sheikh. Ta dubi lokaci taga ƙarfe 2:30 na dare, ta miƙe a hankali jikinta sanye da farar night gown kanta ba kitso, ta saka slippers har ta fita sai ta dawo ta ɗauki perpumes ta fesa, ta shiga fitowa a hankali.
Ta samu Ummul zaune saman kujera a main parlour hannunta riƙe da casbawa. Suka kalli juna ta ce "Lafiya ki ka fito a daren nan?" Ta ce.
"Wajan Abbana zani" maganar ta girmi Ummul ta ce "Ina jin ya yi barci fa?" Halisa ta kalli Ummul ta ce "Bana jin Abbana ya yi barci tun da ni ma na kasa" kunya ta kama Ummul ita kam oganniyyar ko a jikinta.
"Koma to, tunda baki san yadda zaki riƙe Abban naki ba" Halisa bata gane ba, bada son ranta ba ta juya Ummul ta bita da idanu, dole ta gyara mata zama shi namiji a rayuwa bashi da tabbas idan kullum zaka sakar masa jikinka haka yake buƙata, amma dole ta koyi yadda zata dinga juya Yaa Sheikh duk da bata da haufi a kan shi.
Babu jimawa da tafiyar Halisa Yaa Sheikh ya fito cikin ash ɗin Jallabiya mai ƙaramin hannu a wannan karan bai ɗora hirami ba, sumar kansa mai kala biyu ta bayyana.
Mamaki ya kama Ummul ta ɗauka tuni ya yi barci ya dawo kusa da ita ya zauna.
"Bakai barci ba Arɗo?"
Ya jinjina kai ya ce "Bana ji Ummul" ta ƙara gasgata zancan Halisa ashe da gaske duk ba za su iya barci ba juna ba?
Yaushe sukai wannan mugun sabon har haka? Ta share shi tana kallo yana duba ɓangaren Halisa amma baya da ikon zuwa sbd zaman Ummul ɗin,ai kam kamar daga sama su kaga ta sake fitowa.
Da sauri ta ƙarasu ta ce.
"Ummul daman nace ba zai iya barci ba" ta faɗi hakan tana nufar Yaa Sheikh ya yi saurin rufe idanunsa sbd nauyin Ummul yake ji. Halisa ta zauna saman cinyar shi tare da kwanciya jikinsa ta rungome shi ta ce.
"I miss You Modibbo"
Ummul ta miƙe domin tuni salatin ya ƙwace mata ta ce.
"Allah ya kyauta" tana barin wajan Yaa Sheikh ya sunkuceta yana mannata da ƙirjinsa duk da ciwon hannunsa ya ciji fatar kunnenta kaɗan ya ce.
"Kankanata, yau ban sha ruwa ba" ta lumshe idanunsa tana jin soyayyar shi na ƙara haɓawa tare da tunɓasa a zuciyarta tana yaɗo ta ko wacce ƙofa dake zuciyarta..
Washegari tun Subhi ya farka ita kam kasa motsi tayi har yanzu ta kasa sabawa da yanayin Abban nata kullum da salon da yake zuwar mata. Yau take sallah, an sallame azumi mutane Al'ummar Annabi kowa yana haramar tafiya masallaci, ranar da ko yake jiran zuwanta farin ciki a fuskar musulmai ba a magana..
A hankali yake sakkowa cikin wata dakakkiyar shadda fara tas sai ɗaukan idanu yake, ya ɗora Alkyabba jikinsa wani irin sahihin kyau ya yi na musamman, bakinsa ɗauke da tasbihi na tafiya masallaci.
"Allahu Akbar, Allahu Akbar, la'ilaha illallah! Allahu Akbar khabira, Walahamdulillah kasira, Wasubuhanallahi bukuratan wa'asila" a fili yake faɗa har ya sakko ƙasa. Ya samu Umar-khan cikin sabbin tufafi, sai Mai martaba Ahmad Sarki da El-bashir tare da Ummul.
Kafin kowa ya yi magana idanunsa ya sauka akanta ta fito cikin duguwar riga fara sol da ita ta yi rolling kanta da veil ba wani make up tai ba, amma tai wani kyau mai ɗaukan hankali bakinta sai kyallin lips lamp yake, ta ƙara girma da kyau da haske ko'ina na jikinta ya buɗe.
Idanunta rufe ba tare data lura da su Mai martaba ba ta nufi wajan Yaa Sheikh.
A hankali ya furta..
"No kankana bar Abba" shi kaɗai ya yi maganar shi kaɗai kuma yaji tana zuwa ta faɗa jikinsa ta rungome shi tana riƙe hannun ta ce.
"Kafi mazan duniya kyau Abbana, ina son ka da yawa" Suka ji saukar maganar Mai martaba ya ce. "Abbanki dai ki ka sani, amma ko ni ai nafi shi kyau" Yaa Sheikh dai ya kasa cewa komai ita daman Ummul tasan za a rina. "Da gaske Abbana mai kyau ne Mai martaba, banda abinka ai kai ka tsofa"
Umar-khan ya ce.
"Kuma ke ki ke kiɗanki ki ke rawar ki, Yaa Lee bai ce kinyi kyau ba" Yaa Sheikh ya fahimci kowa shi dai bai isa an saka ya faɗi abin da bai niyya ba..
"Kafin nace ya yi kyau shi ya fara faɗa ai"
"Mu bamu ji ba, yaushe akai haka?" Ta ce "Idanunsa sune suka faɗan, Modibbo ka faɗa yanzu kowa yaji kaga suna tsokanata Please kace nai kyau" gabaɗaya suka gyara zama, sun san da Kamar wuya gurguwa da auren ne sa.
"Abba ka ce, ka faɗa musu na yi kyau zan yi fushi idan ka ƙi" nan da nan zufa ta fara yanko masa harshensa ya harɗe ya shiga ƙoƙarin yin magana ya kasa, cikin ƙarfin hali ya ɗan buga ƙafarsa a ƙasa ya riƙe kafaɗunta da kyau kamar zai kuka cikin In-ina ya ce...


*Allah ya nuna mana Monday lafiya, mai son posting har* *weekend zai ƙara adding 500 a saka shi a Special grp*
*08119237616*Kamar zakin dake neman kalace tsayin shekaru haka Zahrah ta ƙara damƙar Halisa cikin tashin hankali kiɗima da gigita kamar mahaukaciya sabon kamu, kafin ta kamata Yaa Sheikh ya yi saurin miƙewa tare da riƙe hannun Zahrah yana tsareta da idanu ya ce.
"Lafiya? Me tai miki?"
"Kan ubancan! Ni ka ke tambaya ko lafiya Aliyu? Ban sani ba amma idan na nakasata sai ka gane manufata tayin hakan" ta faɗa tana cire ɗan kwalin kanta gabaɗaya idanunta ya rufe ta mance batun cikin dake jikinta wanda ya gama bayyana kansa a zahirance.
Ta ƙara kai wa Halisa damƙa Yaa Sheikh ya ƙara tarewa idanunta ya jirkice masifa da wutar ɗaukan fansar cin amanar da Halisa tai mata sune kaɗai abin da ake hangowa cikin Idanun nata.
"Wallahi sai na kasheta, na ga uban wanda ya tsaya mata da har ta nemi cin amanata, yarinya ƙarama ta zama karuwarka?"
Halisa ta leƙo ta bayan Yaa Sheikh idanunta ya yi jaa sosai sbd bugewar da tayi amma taƙi kuka sbd tsabar dauriya da ƙarfin zuciya! Cikin rawar murya ta ce.
"Ni ba karuwa ba ce, kuma tambayi Abbana kinji" tana faɗin haka ta koma bayan Yaa Sheikh da sauri tana riƙe ƙugunsa sbd kukan kurar da Zahrah tayi ta ce.
"Ni ce ajalinki ko uwarki tayi kaɗan ta shiga sabgar mijina balle ke, daman talaka bai iya neman zama ba, taimako ya zame mini masifa yanzu Aliyu ka rasa dawa zakai iskanci sai da ƴar aikina? Ni zaka wulaƙanta a idanunta? Daman da yawan malamai duk ƴan iska ne" Halisa ta ƙara leƙowa ta ce.
"Abbana ba ɗan iska bane, ke ce dai" Da ƙarfi Yaa Sheikh ya bugawa Halisa tsawa ya ce.
"Haliyserh!"
Cikin sauri ta shiga nutsuwarta ta koma bayansa ta ce "Kayi haƙuri Modibbo" Zahrah ta lailayo wani ashar ta ƙunduma gabaɗaya kanta ya ɗaure ta kasa fahimtar abin da yake faruwa ko yake shirin faruwa, tunaninta ya tsaya zuciyarta na ɗagawa Allah ya gani tana son mijinta akan Yaa Sheikh zata iya komai.
"Kai cuceni daka bawa wannan tsinanniyar yarinyar abin da nake fata da burin samunsa daga gare ka, sai na zama ajalinta kuma sai na faɗawa duniya irin zaman da ka ke da ƴar aikin ka, ka mayar da ita karuwar ka, ka fake da addini kana aikata zini aban ƙasa" kamar da ga sama suka ji Ummul ta ce.
"Matar ƙwarai bata taɓa faɗar sirrin mijinta" kafin kowa ya yi magana Halisa ta ƙara leƙowa ta bayan Yaa Sheikh ta ce.
"Shi ya sa ban faɗin darasin auren da mukai da Abba ba, har ya ce sunana kankana" Yaa Sheikh ya dafe kansa abin da yake ta gudu kenan gashi ta kasa sarrafa bakin nata.
"Kankana?" Zahrah ta faɗa a bayyane cikin ɗaure kai!
"Eh kankana Anti Abbana ya ce ina da zaƙi" a wannan karan Yaa Sheikh ya kasa jurewa sbd tsananin kunyar Ummul dake binsu da idanu tayi mutuwar tsaye, yawun bakinta ya ƙafe.
"Zan naka saki kuma zama a gidan mijina ya ƙare ki koma can wajan muguwar uwarki wacce bata iya haihuwa ba, daman ko sisi ban taɓa aika mata mata ba"
Jikin Halisa ya yi sanyi idanunta ya cika da hawaye ta ce.
"Kada ki sake zagin Dadata" a hargitse Idanun Zahrah har rufewa yake sbd masifar dake cinta ta ce.
"Naci uwar data haifeta bama ita ba, dan kaza-kazanta" Halisa ta fito daga bayan Yaa Sheikh ta ce.
"Idan ki sake ni ma zan rama, ke ki ka ɗakkoni har Rugar Rome, bada son raina ba, mene laifina da zaki dinga jifana akan abin da bani da laifi? Idan kishi ne ya saki hakan, wannan ba kishi bane hauka ne, kuma duk kishinki baki kama ƙafata ba, ina son mijina fiye da yadda ki ke son sa, ina son Abbana, ina son Modibbona kada ki sake zagin wanda ya zame mini garkuwa akan idanuna"
Ummul ta girgiza da jin maganganun Halisa masu cike da hikima kuma a nutse Yaa Sheikh tsaye ya yi ya kasa cewa komai, ban yi tunanin ranar zata zo nan kusa ba, duk da ya kwana da sanin cewa dole Zahran zata san gasky soona or later.
Zahrah ta rasa a wanne tubali zata saka zancan na Halisa wanda da tunaninta ya kasa fahimtar da ita komai. Cikin rashin fahimta ta ce. "Waye mijin naki? A gidan uban ki kai auren? Ko maza ki ka fara bi shi ne ki ka biyo ta kan mijina? Ko dai takari ki ka zama?"
"Ai ko giwa ta faɗi,ta fi ƙarfin Allah sarki, ko yanzu goma ta zube tafi biyar albarka" Halisa ta juya kan Yaa Sheikh tare da riƙe ƙugunsa cikin ƙasa da murya wacce shi kansa bai santa da ita ba ta ce.
"Abbana ka shaida mata ni matarka ce, ta daina cin zarafin biyayyar da Dada ta bani, ka faɗa mata ba zaman haramci muke ba, ta daina lalata maka sunanka, _I love You so much Sweetheart Abbana_"
Yaa Sheikh yaja numfashi ya kasa riƙe mmkin da take shayar da shi ya yi saurin riƙe hannunta. Kafin ya yi magana Ummul ta fasa ƙara ta ce.
"Aliyu, Halisa!"
Ta faɗa cikin fargabar yadda taga Zahrah ta zari plate ɗin glasses wanda yake shaƙe da fruits ta yo kan Halisa.
Yaa Sheikh ya yi saurin juyar da Halisa ta koma cikinsa ya rungometa sosai.
Tass! Sautin saukar Glasses ɗin akan Yaa Sheikh ya runtse idanunsa sbd sosai ya shigesa jini ya fara zuba.
"Ka faɗa mini wace ita, ka faɗa mini matsayinta kada ka sake bakinka ya ambace ta matsayin matar ka" Yaa Sheikh bai iya hayaniya ba, bai san ya ake ba, amma dole ya nuna mata shi namiji ne tsayayye a gidansa..
Kansa na zubar da jini ya juya zuwa gare ta ya ce.
"Matata ce, halaliyata, abu mai daraja na bayar na sameta ki sassauta maganganun naki akan ta" jiri ya kwashi Zahrah tayi baya luuu! Ummul tai saurin tare ta, domin ta lura abin da abin da yake jikinta. A zafafe ta kai hannu ta ɗauke Ummul da marin.
Kafin ta sauke hannunta taji saukar maruka a jere har sau uku, marin daya sanya tayi zaman ƴan bori a ƙasa, ɗan cikinta ya motsa sbd faɗuwar da tayi. Idanunta ya cika da hawaye ta nuna Ummul da hannu ta ce.
"Akan wannan ƴar aikin taka ka mareni Aliyu? Wannan matar wacce bata isa na haɗa inuwa da ita ba?" Yaa Sheikh yanayinsa ya sauya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login