Showing 18001 words to 21000 words out of 197828 words

Chapter 7 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9301

a zuciyarta wacce irin larura ce haka wacce bata barin har babban mutum? Zare hannunta ya yi domin har ransa bai san lokacin daya saka hannunta a baki ba a hankali ya juya zai bar wajan da sauri mother tana goge hawaye ta ce "Aliyu" cak ya tsaya tana ƙoƙarin magana Umar-khan ya shigo wajan da sauri gaba ɗaya suka bisa da kallo Umar-khan ya ce "Sheikh na shirya mota a ƙofar baya, yanzu zamu bar gidan nan jami'ai na hanyar zuwa nan zasu kamaka" ko motsawa Sheikh bai ba shi dai ya san ba zai taɓa hana abin da Ubangiji ya tsara afkuwa ba. "Jeka Aliyu ka bisu su fitar dakai Sheikh" Mother ta faɗa tana jan hannunsu ganin haka yasa ya bita har zuwa bakin wata sabuwar mota shiga ya yi. Drivern yaja, Umar-khan shima ya shiga mota, Saif-Wazir ya shiga wata motar. Motar ƙarshe kuma Ishaq-hakim ya shiga kai tsaye suka nufi wata hanya ta daban. Sbd gujewa haɗuwa da jami'an da kuma ƴan jaridu, kasancewar duk sunyi connecting wayoyinsu dana juna yasa Umar-khan gyara bluetooth na kunansa ya ce "Saif-Wazir" Saif ya amsa da "Ina kan layi" haka Ishaq-hakim da kuma Drivern Sheikh. Cikin jin daɗi Umar-khan ya ce "Saif-Wazir idan mun isa Shatalelen gidan gwamna kabi hanyar Amado bello way" Saif-Wazir ya ce "Noted bro" Umar-khan ya ce "Ishaq-hakim kabi hanyar Asibitin nasarawa, Drivern Sheikh Kabi hanyar ƙofar nasarawa,ni kuma zanbi hanyar kasuwar tarauni, gaba ɗaya hanyoyin zasu haɗamu a titin Dawaki roud zamu sauka gidan Hakimi.." haka duk suka amince suna zuwa Shatalelen gidan gwamna ko wacce mota ta ɗauki hanyarta suka ɗauke tunanin jami'an tsaron daka hanyar da zasu bi, Sheikh na bayan mota ya zubawa ikon Allah idanu a haka suka ƙarasa Dawaki roud motocin suka haɗu waje guda kai tsaye suka ƙarasa gidan Hakimi. Sheikh na fito da ƙafarsa waje aka riƙe hannuna tare da saka masa sarƙa kamar daga sama yaji ance "You are under arrest.....


08119237616.*🌈 IDAN BA KE 🌈*


*_Nimcyluv sarauta_*
_*E.O.W*_


9...
"You're under arrest?" Umar-khan daya fito daga cikin mota ya ƙara maimaita kalmar ɗan sandan wanda ya yi ɓadda kama cikin kayan gida. Ɗan sandan ya kalli Umar-khan fuska ba walwala ya ce "As you heard" Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Shi ne kalaman da Saif-Wazir ya faɗa domin Umar-khan kasa motsawa ya yi idanunsa a ƙasa baya taɓa jin zai iya haɗa idanu da babban mutum kamar Sheikh Aliyu Haydar cikin wannan halin. "Yallaɓai kayi mana afuwa mu shiga ciki mu tattauna, ba sai an tafi da Yaa Lee police station ba please" Wanda aka kira da Yallaɓai ɗin ya ce "Stop interfering with our work, because we know our work well, kuma wane ya faɗa maka police station zamu kai Aliyu Haydar Aliyu? State C.i.d zamu" da tsoro sosai akan fuskar Saif-Wazir ya ce "C.i.d? Wajan da ake ajjiye manyan masu aikata criminals, ƴan fashi,ƴan daba, Kidnappers Sheikh bai dace da wannan wajan ba, don Allah kada ko taɓa mana martabarsa.....," Ishaq-hakim ya katse Saif-Wazir da faɗin "har yanzu ba a tabbatar da abin da ake tunanin ya yi ba, zargi ne kawai" Wani daga cikin ma'aikatan ya ce "Say whatever you want to say,We must arrest Sheikh Aliyu Haydar Aliyu" cikin zafin zuwa Ishaq-hakim ya kalli ɗan sandan yana nu nasa da hannu ya ce "Idan ta ƙamar kai uniform ne a jikinka mu kuma mune da garin, wallahi idan ya tabbata Sheikh bashi da laifi sai munyi Shari'a da kai" yana faɗin hakan ya juya da sauri ya nufi babban gate ɗin shiga gidan Hakimi, kasancewar daman a ƙofar gidan suke. Sheikh dai na tsaye tamkar ba akan sa ake wannan muƙabalar ba, ya tsorawa hannunsa dake maƙale da ankwa ido shi kaɗai zai iya fasalta halin da zuciyarsa ke ciki sai kuma Abba Hakimi dake iya fahimtar raunin zuciyar Sheikh ɗin lokaci guda. Suna ƙoƙarin saka Sheikh cikin wata baƙar mota mai kyau wacce babu wanda zai iya ganin Sheikh ɗin a ciki gyarar muryar Abba Hakimi ta karaɗe wajan. Cikin mutuntawa da tarin ladabi duk jama'ar wajan suka sunkuyar da kansu ƙasa. A hankali Sheikh ya ɗago kansa tare da sauke ganinsa akan Abban nasa Hakimi, raunin idanun Sheikh ya bayyana sakamakon zuwan Hakimi wanda shi kaɗai ya fahimci hakan, shi kansa ya kasa yiwa Sheikh ɗin gwaggwaran kallo, idan akwai abin da Hakimi ya keso a rayuwa bai shige Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ba, son da yake masa ko ƴar ƴan cininsa su Ishaq-hakim ba ya yi wa soyayya ce ta musamman tun Sheikh na zanin goyo.


Zame ido Abba hikima ya yi daga kan Sheikh yana mayar wa kan jami'an tsaron da suke jiran suji mai zai ce, domin su basu da wani laifi akan aikinsu suke komai, ko da basu aikata hakan ba, gwamnatin ƙasar Madina zata ɗauki mataki, matakin da zaiwa kowa ciwo da zafi a zuciya. "Zaku iya tafiya da shi" Abba Hakimi ya furta a nutse yana shafa sumar Sheikh tare da ɗaukan hiraminsa ya fara naɗa masa sabon rawani. Da sauri Ishaq-hakim ya ce "Abba ta ya ya zaka bari a tafi da Yaa Lee? Kai ne wanda nake tunanin zaka dakar dasu daha tafiya da shi?" Murmushi mai laushi Abba Hakimi ya yi yana ɓoye damuwar ransa kafin ya ce "Mulki daban, hukuma daban Ishaq-hakim a barsu suyi aikinsu muma muyi namu" Umar-khan juyawa ya yi tare da shiga mota ya kifa kansa jikin Kujera ba zai iya zuba idanu a gabansa a tafi da Sheikh ba. Saif-Wazir idanunsa ya yi jajur gaba ɗaya yanayin baya yi masa daɗi. "Aliyuna" Abba Hakimi ya kira sunan a taushashe yana kallon Abban nasa, cikin kulawa ya ce "Kayi haƙuri, ƙarya fure take bata ƴaƴa, lashakka gaskiya zatai halinta ka ɗauka kai ni kana daga cikin bayin da Ubangiji zai gwada imaninsu" ƙanƙame hannun Abba Hakimi Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ya yi, hakan ya tabbatar wa da Abba Hakimi Sheikh ya amince da zan can nasa. Sakin hannunsa ya yi gaba ɗaya jikin jami'an tsaron ya yi sanyi bisa dole suka saka Sheikh cikin mota tare da tafiya da shi.


"Ishaq-hakim kawo mota, zuwa wajan Aliyu da Barrister Maryam" jinjina kai kawai Ishaq-hakim ɗin ya yi, tare da buɗewa Abba Hakimi bayan mota ya shiga, Saif-Wazir da Umar-khan suka bi bayan motar su Sheikh domin suji inda zan can zai tsaya.
Mother na tsaye ta kasa zama sai number ɗaya daga cikin samarin take gwadawa amma basa ɗagawa, hankalinta ya ƙara tashi fiye da ko yaushe tunanin abin da ya samu Sheikh ya wanzu a zuciyarta. Upstairs tayi da sauri kai tsaye part ɗin Father ta nufa yana zaune a ƙawataccen parlournsa mai kyau, hannunsa riƙe da jarida cikin baƙin ciki yake karanta inda aka saki zan can Sheikh tare da photonsa,gaba Al'amarin ya wanzu a duniya dama media baki ɗaya. Shigowar mother ya sanya Father Kallonta yana jiran jin abin da zata faɗa wannan karan. "Barrister Maryam lafiya ki kai mini tsaye?" Da mmki ta dubesa sosai kafin ta ce "lafiya kake tambaya? Wai me Aliyu ya yi maka da baka kula da al'amarinsa ne?" Hannu ya ɗaga mata ya ce "Saurara Barrister Maryam ni na aiki Aliyu ya aikata hakan? ko da izinina ya ke lalata yaran jama'a yana musu fyaɗe?At Aliyu's age, I will not be surprised at all that he did, ba a shaidar ɗan yau Maryam da ace yana da mata babu mai zarginsa da aikata haka" tarin mamaki da ya gama cika Mother ya sanya ta kasa cewa komai sai kallon Father kawai da take "Aliyu ɗan ka na cikinka kake wa wannan shaidar, shaidar iyaye ita ce shaidar Allah fa, banda na san kai ne mijina kai ka samar da Aliyu da babu abin da zai sanya nace ba kai ka haife shi ba, amma kaje lokaci ne zaka fahimta idan baka son sa muna son shi" kai kawai ya girgiza mata yana faɗin "Zaki iya zuwa ki nemi Mahaifinsa a waje, tunda kina tantama" kafin Mother tayi magana Fattoumah ta shigo Parlourn kallon iyayen nata tayi ganin kamar hayaniya suke, fahimtar hakan yasa Mother yin murmushi ta ce "Mamana ya akai? Ban hanaku zuwa waje ba without permission zan fara bulala fa" marairaice fuska tayi ta ce "Am sorry mother ina ta sallama tun ɗazo" kallon yadda Fattoumah ta tsare Father da ido mother tai cikin sauri ta ce "Ya akai to?" Da sauri ta ce "Abba Hakimi yana Parlour kizo ke da Father" tana faɗin hakan ta juya da sauri tana jin Father na faɗin "Fatimah.. Zarahh..!!" Amma tai banza da shi, Fattoumah irin yaran nan ne masu riƙo da kuma kishin iyayensu mata gaba ɗaya taji abin da Father yake faɗa akan Sheikh.


Fita Mother tai tana sakkowa fuskarta ɗauke da fara'a tasan tun da taga Abba Hakimi to Sheikh yana can gida cikin kwanciyar hankali. A ƙasa ta zauna tana gaida shi ya amsa a nutse kafin ya yi magana Father ya fito shi ma ya zauna saman Kujera ya ce "Sannu da hanya Abba Hakimi" kai kawai ya jinjina idanunsa akan Fattoumah yana faɗin "Matar zo nan mana ke dawa haka?" Turo baki tayi idanunta na sauyawa ta ce "Mijin me ya sa Father baya son Yaa Lee?" Sa mamaki Hakimi ya kalli Father yana faɗin "Aliyu ya akai haka? Me ya sa kake barin raya su san abin da ke zuciyarka ne?" Father ya ce "Abba Hakimi ta ya ya zan ƙi ɗana? Shirman Fatimah ne" da sauri Fattoumah ta ce "Da gaske nake Mijin,ina jin yana faɗawa mother wai a nemo mahaifin Yaa Lee kuma ai ba kyau ƙarya" surutun Fattoumah ya jijjiga Mother bata taɓa haifar yarinyar mai kaifin bakin Fattoumah ba. "shige ki bamu waje Mamana kafin ranki ya ɓaci laɓe kike mana kenan?" Turo baki Fattoumah tayi tace "Mother kawai ki nemowa Yaa Lee Abbansa wanda zai so shi tunda father baya son sa" Abba Hakimi da Mother suka kalli juna da sauri kuma suka janye idanunsu ko wanne tunani fal ransa. Tsawa Mother ta yiwa Fattoumah ta tafi ɗakinu Maimoon tana sakin kuka ta fara bori a ƙasan carpet.


A nutse Abba Hakimi ya kalli Mother ya ce "Aliyu yana state c.i.d Barrister Maryam" a ruɗe Mother ta Kalli Hakimi hankali tashe take faɗin "An kama Babana? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wallahi sharri ne ba gaskiya ba, kuma zan tabbata da hakan" Hakimi ya ce "Samu nutsuwa Barrister Maryam, mu duka ba zamu ja da ikon Allah ba, kuma da hujjar kare Aliyu, shi ya sa nazo naji ko ya faɗa muku wani abun?" Father ya yi dariyar baƙin ciki ya ce "Wannan ne zai magana? Ko ya yi bata da wani amfani me zamu fahimta banda, A...Aaaa...ƙikkkk... Yeee gaba ɗaya Aliyu bashi da amfani a rayuwarmu, naji baƙin cikin samunsa Matsayin ɗa namiji" wani baƙin ciki ya tukare zuciyar Mother idanunta na cika da hawaye ta ce "Sai yanzu na fahimta larurar Aliyu ta sanya kake ƙinsa? Ubangiji ya ɗora masa shi nake roƙa kuma ya ye masa" Abba Hakimi ya numfasa kalam Father sun bashi mmki a haka ya share ya ce "kayi babban kuskure Aliyu, kuma Sheikh abin Alfaharin duk wani ɗan Kano dama Najeriya ne, muhimmancin bai tsaya iya ƙasar shi ba, har ƙasa mai tsarki.. Allah ya kyauta wata rana zaka gane gaskiya lokacin da za kaji kunya" juyawa kan Mother yai ya ce "Akwai abin da ya faɗa miki ne, ina son shigar da maganar zuwa court ne" Mother ta ce "Yana cikin ƙoƙarin fahimtar dani suka taho wajanka ya faɗa mini bashi ya aikata ba, kuma ni ma na shigar da ƙara ni zan tsaya masa tare da Barrister Zainab" wayar Mother ce ta fara ringing ganin sunan Umar-khan ya sanya ta ɗauka cikin sauri ta miƙe tana faɗin "Ohhh ok on our way" kashe wayar tayi idanunta akan Abba Hakimi ta ce "Umar-khan ya ce muzo yanzu al'amarin ya shige tunani" da sauri ta nufi ɗaki tare da ɗakko mayafi da key car.


Abba Hakimi da Mother suka nufi state c.i.d hankali a tashe Maimoon da Zeefa da Fattoumah sai kuka suke a rayuwa suna ƙaunar yayan nasu duk da babu wata jituwa a tsakaninsu. Ko abinci suka kasa ci sai sallah kawai da suke suna addu'ar Allah ya kuɓutar da Sheikh ɗin. Hankali kwance Father yake zaune yana waya da babban amininsa ko da wasa bai masa magana akan matsalar da suke ciki ba, duk da cewa al'amarin ya gama zaga ko'ina a faɗin Nigeria.
A kiɗime Mother take bin su Saif-Wazir da kallo ganin yadda idanunshi ya yi jajur alamar kuka suka sha. "Ina Babana ina Aliyu mai ya faru da shi?" Shiru Saif-Wazir ya yi mata, ta juya kan Umar-khan ta riƙe wuyansa sosai cikin faɗa ta ce "Where's my son Umar-khan? Ina Aliyuna?" Umar-khan ya yi ƙasa da idanun shi ba tare da ya ce komai ba. Sakin Umar-khan tayi ta nufi wajan Ishaq-hakim ta ce "Ishaq-hakim faɗa mini gsky ina Aliyu me akace yana da gsky ko? Ba aikata abin da ake zarginsa ba?" Hannunsa ya ɗaga tare da nuna mata wani waje da sauri ta juya Idanunta ya sauka akan Sheikh Aliyu Haydar Aliyu wanda aka cire masa Jallabiyar jikinsa aka ɗauresa da Sarƙa tun daga wuyansa hannunsa zuwa ƙafarsa farar fatar jikinsa tayi jajir bakin Ishaq-hakim na rawa ya ce "Mother Sheikh ya amsa laifin da ake zarginsa ya tabbatar shi ne ya lalata ƴan matan hadda ciki.....




_*IDAN BA KE...* labari ne da kuka daɗe ba kuci karo da irinsa ba, ƙaddarar labarin akan soyayya ne mai tsayawa a zuciya da saka shauƙi a zuƙatan masu karatu..... Tsammaci abin da baka tsammani salo na musamman🫣💋 08119237616._*🌈 IDAN BA KE 🌈*


*_Arewabooks@Nimcyluv_*


10....
Kasa magana Mother tayi sai Ishaq-hakim da tabi da kallo tana son gasgata abin da yake faɗa. "Ta ya ya Sheikh zai amsa laifi fyaɗe? Laifin da duk duniya ta san ba zai iya aikatawa ba?" Ta faɗa a fili tana sakin wani raunataccen kuka mai tsayawa a zuciya ba zata iya kallon Sheikh cikin sarƙa a ɗaure ba, kamar wani ɗan fashi ko Kidnapper. Umar-khan ne ya kama Mother wacce take ƙoƙarin zubewa a wajan sbd kukan da take idanunsu ya yi jajur ya ce "Ki daina kuka Mother, wata kila Sheikh ya amsa laifin ne sbd rashin mafita, mu duka abin ya zo mana cikin wani sabon yanayi wanda bamu taɓa riskar kanmu ciki ba, Ubangiji ka ɗai ya san gaskiya kuma shi muke roƙa ya fidda Sheikh Aliyu daga cikin wannan jarrabawar" gaba ɗaya zuciyar Mother ta karaya tunaninta ya tsaya cak duk inda take neman wata hujja ta kare ɗan nata babu.
Da hannu bibbiyu ta riƙe Umar-khan ta ce "Kai ne kake tare da Babana Umar-khan, ka taimaka mini nasan kasan Aliyu ba zai iya aikata hakan ba, yana tsare imaninsa yana amsar rayuwa a duk yadda ta zo masa" Umar-khan ya mayar da hawayen dake cika idanunsa kafin ya zaunar da Mother ya ce "Be patient Mother, muyi addu'a kawai amma da ace zan iya bada shaida, da iya abin da zan faɗa ya isa ya wanke Sheikh daga cikin zargi"


"That's enough, this is not a place to make noise" Wani daga cikin jami'an tsaron ya faɗa yana daka musu tsawa.
Sai a lokacin Abba Hakimi ya yi ajjiyar zuciya domin shi ma Al'amarin ya girgiza shi fiye da tunanin kowa, zuciyarsa shi zafi take masa sosai. A nutse ya juya ya kalli Ishaq-hakim ya ce "Ka mayar da Barrister Maryam gida yanzu, ka ce ina buƙatar ganin Aliyu immediately" da girmamawa Ishaq-hakim ya amsawa mahaifin nasa, idanunshi akan Mother yana jiran ta miƙe.
Cikin kuka ta kalli Abba Hakimi ta ce "Ina son nayi magana da Aliyu Please Hakimi" Kafin Abba Hakimi ya bata amsa wani daga cikin Jami'an tsaron ya ce.
"No way Madam" tana share hawaye ta ce "Don girman ka bani 2 minutes nayi magana da ɗa na, ina son tambayarsa, tare da kwantar da hankalin shi" cutting nata out ya yi da faɗin. "Isn't necessary Maaah..." A ƙagauce Abba Hakimi ya ce "take her out Ishaq-hakim" Mother na kuka sosai tana kiran sunan Sheikh Aliyu aka fitar da ita waje, Aliyu shi ne rauninta ka kaf cikin yaranta tafi ƙaunarsa duk abin da Mother ta mallaka daga cikin dukiyar iyayenta Aliyu ta bawa, She owned all her property for him, Lands, houses, companies, all signed in the name of Aliyu's property.
Su Mother na fita Abba Hakimi ya kalli jami'an tsaron cikin murya mai taushi ya ce "Kun samu hujja mai ƙarfi da kuka kama mini ɗa na?" Ɗaya ya sunkuyar da kai cikin girmamawa ya ce "Har yanzu bamu da hujja, amma a duk bin ciken da mukai Sheikh ƙara shiga ciki yake, yaƙi buɗe baki ya yi magana, gwamnatin Madina da universityn ƙasar sun matsa akan kwana biyu suka bayar idan ƙasa Nigeria bata ɗauki mataki ba, zasu ɗauka da kansu domin su irin wannan cases ɗin kai tsaye suke bincike kuma hukuncin kisa ne" runtse idanu Abba Hakimi hukuncin kisan ya daki zuciyarsa ainun. Umar-khan da bakinsa ke rawa tun ɗazo sbd masifa ya ce "Ita kanta gwamnatin Madinan idan bata da hujja dole ta haƙura, ina masu kawo ƙarar? Daga ina wannan zan can ya fito? Ina ƴan matan da akaiwa fyaɗen suke?"
"Stop raising your voice, we are working on our system, nan ba Court bace" Umar-khan zai sake magana Abba Hakimi ya yi gyara murya kafin ya ce "Ka bari abu komai a nutse, shi ya sa na mai da Barrister Maryam gida" Saif-Wazir dai na tsaye duk yadda suka so a basu Sheikh su yi magana hanawa akai. Kuma a gobe za a kaisa court domin fara gabatar da Shari'a tun da case ɗin ya zo da hargitsi. Haka suka komai gida zuciyoyin kowa babu daɗi.
Sheikh na zaune daga shi sai single da wani farin trousers mai laushi tunda yake a duniya babu wanda ya taɓa ganin tsari da zubin halittarsa sai yanzu, an tuzarta shi tuzarcim daya har zuƙa kuturwar zuciyarsa, shi kaɗai sai tsuma yake shi da ko sauro baya so baya ƙaunar yaga baiwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login