Showing 168001 words to 171000 words out of 197828 words

Chapter 57 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9306

daga Allah maɗaukaki gare ka, sai ka girmama ta, ka tausaya mata, duk da kuwa hakƙinka a kanta ya fi karfi, amma tana da hakki a kanka na ka tausaya mata domin ita ribacewarka ce. Kuma ka ciyar da ita, ka tufatar da ita, idan ta yi rashin sani da wauta sai ka yafe mata” ta tura ƙaramin bakinta gaba ta ce
"Salon ace Malam ya zama mijin ta ce"
Kamar ba Yaa Sheikh ba ya saka hannu ya riƙe ƙugunshi cikin son kwantar mata da hankali domin ya fahimci damuwarta ya ce
"Lallai ƴar nan, Malaminsu a waje abokinki a gida, a good friends should be helping each other" Ya kwashe kayan zuwa kitchen tana zaune taji ƙarar ruwa ta miƙe tana leƙawa.
Tsaye ta ganshi yana wanke plates ɗin tayi saurin cewa "Ka bari don Allah ban saka ba, ni wallahi Abba duk ka ɓata mini kitchen"
Ya gama jagwalo gwalon shi ya ajjiye ya kafi Idanunta ya sureta zuwa sama ya nufi kan bed da ita cikin kunnenta ya ce
"Nifa ki daina ɗauka wani malami,sbd cutata zaki kwana biyun rowar lemon tsami ake mini" ya hautsinata yana zame rigar ta zuwa ƙasa, tayi saurin riƙe ƙirjinta tana marairaice fuska ta ce
"A'a Please, bana son ka shiga fushin Allah kaje wajan matarka kuma mayyarka tana jiranka" muryarta na rawa ta ƙare maganar tana ɗauke kai, ya yarda da batunta amma ai laifinta ne waye ya ce tayi shigar Iskanci ya gani da goga abu a jiki. Ya jingina da jikin prame tare da jawota ya zaunar saman cinyarsa ya kama hannunta tare da binta da kallo kamar mara wayo ya taɓe fuska cikin ƙasa da murya ya ce "kina sane da hakƙin ɗan Ummul da ki ka ɗauka?"
"Wanne irin hakƙi kuma Yaa Sheikh?" Ya girgiza kai tare da lumshe kamar mai barci, ta saka hannu ta shiga shafa fuskarsa zuwa lips ɗinsa, ya cafke yatsun ya zura a bakinsa ta ce "Modibbo lafiya?"
Ya buɗe idanu da ƙyar ya ce "Ana maganar cuta ina lafiya? Kije Allah ya yafe miki" ya ƙare yana tsotse yatsun da yake ɗauke da zanan henna.
"Ba zaka tafi bane"
Ya yi mata banza, ya jawota ya rungometa a jikinsa da kyau, hannunsa cikin riga a hankali yake addu'a kuma yana shafa mata tare da hura mata iska a kunne, tayi luff tana riƙe shi gam!.
Numfashinta mai zafi ya fara sauka a ƙirjinsa alamar tayi barci cikin nutsuwa ya zameta ya gyara mata kwanciya, tare da ja mata duvet ya sumbaci goshinta tare da cikinta data ɗora hannu akai, bai san ya ya yake ji game da ita, ya kuma kasa fahimtar yadda zai fasalta ko bayyana al'amarin, kalmar Ina son ki tayi ƙanƙanta a gareta, sam! Ta shige hakan, kawai abu ɗaya ya sani aikatawa a bayyane kamar yadda ta zama wani sashe da sashin jikinsa.
Ya shafa kanta ganin ta tura baki tare da marairaice fuska kamar ƴar tsana she looks like takeaway. Ya fita bayan yabi kusurwar ɗakin da addu'a kana yaja mata ƙofa ya nufi part ɗin Zahrah yana riƙe kansa tare da kame fuska ya dawo Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu ya fita daga Yaa Sheikh ko kuma malamin Danejo Rome.
Zahrah na zaune ta riƙe Jikinta sbd magungunan data sha, gabaɗaya a sama ta sha ga wani magani goran tula mai saukar da ni'ima sai duk ta birkici, ƙamshin turaren Roja ya ruga sallamar Yaa Sheikh zuwa wacce ya yi a kamalance tana ganinsa ta miƙe tsaye fuskarta ɗauke da murmushi ta rungome shi ta ce
"Wlcm Sweetheart, har na fara tunanin zuwa gareka" Ya jinjina kai tare da zareta a jikinsa a hankali ya ce "kizo part ɗina" yana faɗin haka ya juya ya fita, sbd turaren dake hautsina kansa amma bai nuna ba, ta ce "Ok I'll be there"
Ta ƙara fesa perfume ta shan magani wanda ya sa duk ta lalata kanta, yana zaune ya sauya kaya zuwa na barci ash colour hannunsa riƙe da coffee daya samu an ajjiye masa, ta faɗo ba sallama yaƙi kulata da kanta ta miƙe ta fita ta sake shigowa ɗauke da sallama ya amsa yana miƙewa zuwa bathroom ya yi brush da alwala ta kariya, ya sameta kwance ya kwanta yana kashe hasken ɗakin.
Zahrah ta ce "Me ya kake samun Halisa har part ɗinta, amma ni sai nazo naka akwai fa'ida hakan ne?" Bai kalleta ba cikin gajiyawa ya ce
"Banda hayaniya please"
Ta jawo Jikinta zuwa nasa ta riƙe shi tare da ƙoƙarin haɗe kissing nasa, ya yi saurin zame fuska yana sakar mata murmushi tare da kissing goshinta.
Zahrah ta ce sam bata san Wannan ba, ta birkice masa, gabaɗaya gangar jikinsa ta kasa amsar saƙon da take tura masa, yana da biye da ita gudun saɓawa mahalicci da gaske tana tsananin buƙatarsa da kulawarsa gareta, ya yi yaƙi da zuciyarsa bada wasa ba yana kiran sunan Allah a haka ya samu sassauci ya fara kyautata mata, amma sam ya kasa yarda yaji bakinta a nasa. Yaa Sheikh na fita Halisa ta buɗe ido, zuciyarta na bugawa ta riƙe kawai domin wannan daren tabbas zai shiga cikin kundin lissafin ajjiye muhimman abubuwa, zai zama dare mafi tsayi da muni a tare da ita duk wani mai sonta dole ya tausayawa mata, yau Abbanta ne zai kwana tare da wata? Ɗaki ɗaya,gado ɗaya? Maybe na jiki ɗaya. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un" ta furta tana fashe da wani irin kuka mai cin zuciya ko cikakken abinci ta kasa ci yau, taji a ranta idan akwai abinda zai bata matsala acikin aurenta bai shige kishin da take dashi akan Abbanta Yaa Sheikh ba, tayi kuka sosai daga ƙarshe ta miƙe tayi Alwala tare da ɗaukan Alkur'ani sai dai sam bata ganewa kuma bata fahimta, gudun kada tayi saɓo ta ajjiye ta fita zuwa main parlour barci tuni ya ƙauracewa Idanunta, ta zauna a kujera tana kuka ƙasa-ƙasa.
Zahrah taga Yaa Sheikh ya tsaya cak bai taɓa ganin abin al'ajabi da almara haka ba, ki da can baya da yake riƙe kansa lafiyayye ne shi, amma yanzu daya nufi hanyar samawa Zahrah nutsuwa sai maɗaukan suka daina ɗaukan sati ta zama tamkar ruwan da tsumma ya jiƙa tare da kwanciya tayi barci irin barcin nan da zakai zaton namiji nakashasshe ne...






Sorry For the shortly👏🏽*Follow my Facebook page👇🏾*
https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL


Ta shi Yaa Sheikh ya yi sbd tsananin kunyar Zahrah daya lulluɓe shi, bai san yadda zata ɗauki al'amarin ba, ya nufi bathroom ɗin shi tare da sakarwa kansa shower, idanunsa lumshe yana kiran sunan Allah maɗaukakin sarki, wanda ya samar da sammai da kassai bakwai, ya wanzar da sirrai a cikinta, ya samar da ƙasa, wacce muke tafiya a kanta, ya halicci mutane da dabbobi da dukkan abin dake da rai. Ya sauke numfashi wannan abu shi ne mafi tsayuwa a ranshi, yana ganin abin al'amara amma wannan ya banbanta, ya kai duban shi ganin yadda yanzu komai ya daidaita kamar ba yanzu ne maɗaukan suke barci ba, ya ƙara sakin ruwa sosai tare da ɗaura alwala ya sanya bathrobe ya fito jikinsa na zubar da ruwa. Zahrah ta dube shi Idanunta cike da hawaye sosai ta ce "Na sani, ba zaka iya ba amma daka sani da baka fara mini abinda zai sanya na samu matsala da tunani na ba, ina jin kamar Allah ya ɗauki raina kafin cikar lokacin da Dr ya faɗa"
Ya dubeta lokacin da yake taje gemunsa mai tsafta, kaifin idanunsa a kanta ya sanya ta kasa cewa komai sai kawai ta fashe da kuka na baƙin ciki tana rufe fuskarta.
Bai ƙoƙarin hanata ba, yasan da zaifi hakan ga ko wacce mace musamman ita da ga yadda al'amarin ya kasance, zata iya zargin wani abu, duk da zato zunubi ne.
Ya shimfiɗa prayer mat bayan ya sanya farar jallabiya tare da tayar da sallah, ya jima yana Sallah tare da addu'ar Allah ya nuna masa manufar sabon wannan al'amarin a cikin maɗaukan shi ya yin barci, kamar yadda ya saba yin gamo da sabbin al'amura cikin rayuwar shi. Har lokacin daya idar kuka take ya dubi agogo a hankali da sauri kuma ya rufe idanu ganin 2 da wani na dare, gently ya miƙe tare da nufar kan gadon ya zauna cikin laushin murya da gajiya da jin kukan nata ya ce
"Zahrah" ta ɗago kai ta kalle shi ya numfasa ya ce "Kuka? Name?"
"Kafi kowa sanin kukana Yaa Sheikh wallahi...,"
Ta kasa ƙarasa maganar tana fashewa da kuka sbd ita kaɗai tasan ciwon da mararta yake mata, ya jawota ya rungometa jikinsa ya shafa kanta ya ce
"It's okay, ki barwa Allah komai cikin lamuranki, ban san yaya ne ba, ban san matsalar ba kiyi addu'a just pray" ta riƙe shi gam! Numfashinta na fita da ƙyar raɓuwa da take a jikinsa wani tsananin a zaba take ji sbd wutar abinda ke cinta ta ce.
"Kayi mini al'ƙawarin farin ciki, ina son samun baby dakai kafin Ubangiji ya ɗauki raina" ya girgiza kai yana ɗan faɗaɗa fuskarsa wacce hakan ya sanya gemunsa motsawa yana gogar fuskarta ya ce.
"Idan kina son rahamar Ubangiji da kuma farin ciki ga rayuwarki da mijinki, You should stop lying" kukanta ya tsaya tayi saurin kallonsa ta ce
"Ƙarya?" Ya jinjina kai ya ce "Eh, idan za kayi ƙarya don ka samu wani abu, sai Ubangiji ya baka abin kuma ya barka kai da shi daga ƙarshe ya zamana abin bai amfana maka da komai ba" ya numfasa cikin gajiyawa amma ya zama dole ya fahimtar da ita abinda bata sani ba, domin ya lura Empty head ce ya gyara zama cikin tarin nutsuwar shi ya ce "Kin ya ƙarya kina da Cancer, kin manta ni likita ne?" Bakinta na rawa Zahrah ta ce
"Ni... Ni.. yaushe?" Ya tsareta da idanunsa masu kaifi wanda ya tilasta mata yin shiru ya ce "Kada Kiyi musu, kowa da baiwar da Ubangiji ya yi masa, haka kowa da naƙasun da yake da shi a rayuwa, na sani na sani, i knew everything da ki ke harding, ban aure don naji tausayinki ba, ban kuma aurenki don ina son ki ba, haka ban aureki don inci zarafin ki ba ni da kai na bani da dalilin aurenki, amma na bar hakan matsayin ƙaddara wacce take zama zanan dutse, duk wayonka, da iliminka, duk na gartar da Ubangiji ya baka sai ya jarabce ka da ƙaddarori masu zafi domin ya gwada imaninka, idan kayi haƙuri ka miƙa lamarin ga Ubangiji sai Allah ya duba ka kuma ya sanya hannu cikin al'amarinka, ke ƙaddara ta ce ke kuma soyayyar da ki ke mini ita ce ƙaddararki"
Idanunta ya cika da hawaye kunya ta kamata, Allah da kansa ya ce fazakkir fa'innàl zikkira tamfa'ul mu'uminun. Yaa Sheikh ya ƙara samun ƙarfin gwiwar fahimtar da Zahrah ya tallafo haɓarta yana bin fuskarta da shekaru ya ce "Kin san za a haifeki? Kin san zaki karatu mai zurfi? Kin san zaki haɗu da Father? Kin san zaki samu ciki har huɗu? Kin san zaki haɗu da Saif-wazir? Kin san saki aureni? Kin san zaki haifi Muhammad?" Ta girgiza kai jiki duk a mace ta ce
"Ban sani ba" a taushashe yana sakin fuskarta ya ce
"Allah ya sani, tun kafin haihuwar ki ya rubuta hakan jikin allon lauhil-mahfuz, allon da baya ƙarya bawa baya shige ƙaddarar shi, baki san ina jin tsananin nauyi da kunyar kai na na auri wacce tayi hulɗa da wanda nake kallo matsayin Uba? Na kanji sauƙi idan na tuna babu haramci, ba ke ba ko Mother zan iya aura idan hakan ya zama ƙaddarar Aliyu!" Ya miƙe tsaye ganin kamar lokacin kiran sallar farko ya yi ya ce "One thing da zan faɗa miki, ki dai na yarda da mutum akwai wanda suna zaune da kai domin su samu abin faɗa akan ka acikin mutane, akwai wanda zasu ya beka bisa raɗin kansu a baya su zageka, akwai wanda su da kansu basu dalilin daya sanya suke tare da kai ba, zaka birgesu har zuciya amma zasu zageka, masu yin hakan kuma Ubangiji ya tana dar musu makoma domin laifin bawa akan bawa saɓo ne mai girma da zunubi, ki tsarkake harshenki daga cin naman mutane ko cin mutuncin su"
Ya ƙara sauke numfashi gajiya duk ta bayyana a jikinsa ya ce "Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce: lokacin da aka yi Mi'iraji dani, muka hau sama sai naga wasu mutane da baƙaƙen farata suna yage fuskokinsu da ƙirjinsu, na tsorata da hakan nace Ya ɗan uwana Jibrilu su waye wannan?" Sai ya ce mini "Su ne wanda suke cin naman mutane da cin mutuncinsu su" Anas bin Malik
(RA) . Yaa Sheikh bai gushe ba sai daya ƙara bata fatawa da faɗin Ibn Abu Shaiba
ya ruwaito shi a cikin
Musnaf ɗin sa ya ce Manzon Allah
(SAW) yana cewa:
“Wanda ya ci mutuncin
ɗan uwansa za a yi
masa suturar wuta (a
Lahira), idan mutum ya yi ba daidai ba kira shi ka sanar masa da kuskuren shi domin ya gyara”.
Zahrah Jikinta ya ƙara sanyi sosai gabaɗaya bata san Wannan ba, musamman daya kasance kaf zuri'arsu ilimin ya hudu ya yi musu gurbi a zuciya, Zahrah kuma tazo ta fisu ilimin daman kuma ace abin cikin kwan yafi kwan daɗi, kyan ɗa ya gaji ubansa, kuma ko wanne tsuntsu kukan gidansu yake. Taji ta tsani kanta,kuma ta tsani komai zafin iyayenta da basu kyakkyawan ilimin addini ba ya shigeta. Ta kalli Yaa Sheikh cikin kuka ta ce
"Da gaske baka so na?"
Bai iya ƙarya ba, kuma baya son farata ba zan faɗa mata gaibu domin taji daɗi ba, sbd yasan babu hakan a ran shi ya ce "Eh, ban san me gaba zata haifar ba kiyi addu'a" ta miƙe tare da faɗawa jikinsa ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, soyayya masifa ce, musamman Allah ya haɗaka da wanda baya son ka kuma jarrabawa ce, ita kam zata iya cewa Soyayyar Yaa Sheikh ita ce girbin abin data shuka na saɓon Ubangiji tun a duniya. Ya ɗan rarrasheta kana ya koma Bathroom ya wanke jikinsa domin a jininsa yake jin ta ɓata shi ga ɗan abin da ya yi mata.
Da sauri ta nufi steps na benen zata yi downstairs ganin Halisa zaune ta riƙe kanta tana kuka ƙasa ƙasa ya sanya Zahrah taka tawa. _"Zahrah think, Kada ki zama abar gori wajan kishiya"_
Zuciyarta ta faɗa mata haka, tayi saurin komawa da baya tare da laɓewa ta kurma ihu ta ce.
"Wayyo Allah Yaa Sheikh zan mutu, ka bari wallahi ban saba ba, zaka ka sheni na tuba nayi ladama wayyo bayana Wayyo marata I love you so much sweetheart" Halisa ta firgita tare da miƙewa ta saka hannu ta toshe kunnenta.
Ɗan cikinta ya juya ya daki mararta ta fara gani dishi dishi zuciyarta kuma tayi wani kyakkyawan bugawa. Zahrah ta leƙo ganin Halisa cikin wannan yanayin ya sanya ta ƙara sakin wani ihu ta ce.
"Yaa Sheikh da gaske kake faɗa mini Halisa bata daɗi? Bata iya komai ba, ka daina faɗa kada taji babu daɗi" ta ƙara yin shiru ta ce
"Na gode sosai ban taɓa sanin cewa kafi so na fiye da yadda ka ke son Halisa ba sai yanzu, na gode da kyautar fili da kuma kamfani wayyo i love You so much" Halisa ta gigice ta dinga kiran sunan Allah da karfi tana dafe cikinta, iya tsorata da firgita tayi sosai tun tana kiran sunan Allah daya kawo mata ɗauki har tari yaci ƙarfinta ta kifa tare da buga kanta da jikin kujera.
Zahrah was happy ganin Halisa cikin wannan yanayin, and she don't feel anything data aikata, ta juya zuwa bedroom ɗin Yaa Sheikh ta same shi tsaye a gaban mirror ya kafe waje guda tare da riƙe kansa da hannu ɗaya, she hope ace bai ji abinda ta faɗa ba. Ta ƙarasa tare da tafa kafaɗar shi ta ce.
"Sweetheart" Ya juya ya kalleta taga idanunsa jajir tayi murmushi sai shi shima ya yi murmushi, gabanta ya faɗi ganin haƙuri guda ɗaya dal a tsakiyar bakinsa, ta juya ta kalli mirrow bata san lokacin da fitsari ya fara zuba daga Jikinta ba, ta cikin madubin taga Rabi jikin aljani rabi jikin Yaa Sheikh ya koma wata suffa mai munin gaske, taji ya taɓa ta ya ce
"Fitsari a nan Zahrah?"
Ta kasa kallon shi domin ba fitsari ba, wallahi hatta kashi zata iya a wajan ta ƙara kallo cikin madubin, wani razannan ihu! Ta fasa ganin wani narkeken maciji yana yawo, babu addu'a ta fara ihu tana faɗin.
"Asstagafirullah no no, what's is that..." Dum! Aka kashe hasken ɗakin ya zama baƙiƙƙirin sululuu kuma taji abu yana ratsawa ta cikin rigarta tare da shigewa cikin wandon jikinta ta ƙara yin wani ihun tana faɗin "Dad, Mimi help wayyo Ya zama Aljani wallahi aljani someone please help me"
Sai kuma hasken ɗakin ya dawo ta haɗa zufa Jikinta banda ɓari babu abinda yake. Ta juya taga Yaa Sheikh tsaye a kanta ta girgiza kai sai ya wangale mata haƙuri ɗaya ta miƙewa tana layi zata kifa kafin ta faɗi sai taga babu komai a wajan ganinta ya ɗauke. Yaa Sheikh dake bathroom ya kifa kansa a sick kamar an dasa shi Jikinsa ya jiƙe sosai da zufa sai karkarwa naman jikinsa yake, kamar a mafarki yaji Zahrah ta fasa ihu ya ɗago kansa dake sara masa sosai ya dafe da hannu ɗaya tare da murɗa handle ya bita daga bathroom ɗin, Ya she ya samu Zahrah kanta ya bugu sosai ya ɗagota yana ɗan bubbuga kumatunta domin jin jikinsa yake kamar an masa dokan tsiya, ya ce "Fatymerh?" Ya daɗe kafin ta saki numfashi ta buɗe idanu tana arba da shi ta saka ihu zata gudu ya riƙeta da kyau ya fara mata addu'a ya lura kamar tsoran shi take ko an firgita ta ohhu!?
Da taimakon addu'ar ta ɗan dawo hayyacinta sai ta fashe da kuka ta ce
"Wallahi gidanmu zani, kashe ni za'ai" da mmki ya ce "kisa? Akan me" tana kuka sosai ta ce
"Kawai zani, amma akwai Aljanu a gidanka" ya ɗan yi jim! Sai kuma ya yi ɓoyayyen murmushi ya ce "Gidan Malam guda da Aljanu? Sai dai idan Malam ɗin ne Aljani da kan shi, Kinga tashi muhimmancin addu'a kenan" ta miƙe tana riƙe da shi amma ta kasa kallonsa gani take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login