Showing 45001 words to 48000 words out of 197828 words

Chapter 16 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9319

bisa takurar kuma ya cutar da ita, a dai bi komai a hankali" Mother ta girgiza kai ta ce "Uncle Haroon ka rabu da Aliyu, tunda ya amince dana Zahrah zai amince da wannan ɗin ma sai ya tattara su tafi can Madina su ƙarata" Yaya Halima ta kalle su baki ɗaya kafin ta ce "duk ba Wannan ba, na tambayi Zahrah a sigar wasa cewa wannan ƙanwarta ce? Sai ta ce mini wai ƴar aiki aka samu mata, That's the position of a maid in Aliyu's house" Dr A'isha tai murmushi ta ce "Matar gida ko ƴar aiki? dama a ɗauke ni aikin gidan Aliyu naga yadda zaman zai kasance" Yaa Sheikh ya ɗaga kansa a hankali kamar zai kalli Dr A'isha sai kuma ya fasa ya mai da kan ƙasa.
Sai a lokacin Uncle Bashir ya ce "Ya kamata kada ita Zahrah tasan cewa itama yarinyar matar Yaa Sheikh, a barta ta tafi da ita a matsayin ƴar aikin kamar yadda tazo da ita da manufar hakan"
"I also agree with this decision, she took it as her worker" cewar Dr A'isha. Abba Hakimi ya sauke numfashi yana duba lokaci,bayan nazartar maganganun sauran ya ce. "Na amince baka son ƴar fillo, suma sun yarda da hakan, zaka tafi da ita can gidanka dake Madina matsayin matar ka kuma ƴar aikin matar ka, zaka iya zuba idanu matar ka ta zama baiwa a cikin gidan aurenta, ra'ayinka ne,
Ni bance kaji tausayin ta ba, kawai ina son ka riƙe mini ita a wajanka na tsayin shekara ɗaya ciff, ka sata makaranta, ni bance ko sau ɗaya kayiwa Halisa Danejo kallon matar ka ba, ita ɗin kamar ajjiya ce na baka, ka dawo mini da ita shekara guda, kada naga wani sauyi a tare da ita, ka tabbatar yadda take budurwa a haka ka dawo mini da ita, nayi maka al'ƙawarin shekara nayi zan raba auren naku rabawa ta har abada" gaba ɗaya mutanan parlourn suka zubawa Abba Hakimi idanu, su basu ga dabarar haka ba, sun san ko shekarar biyar aka bawa Yaa Sheikh there is nothing he will do, there will never be any change from him, balle ya furta da bakin shi ya ce yana son ta,That will never happen.
Abba Hakimi ya gyara zama sosai idanunsa akan Yaa Sheikh ya ce "Amma Wallahi Wallahi Allah kenan Aliyu ban taɓa rantsuwa akan ka kamar haka ba, shekara guda tayi ka dawo mini da yarinyar nan saɓanin yadda nai tunani zaka sha mamakina, kai ba yaro bane ka fahimci mai nake son faɗa maka, babu dalilin da zai sanya ka lalata budurcin yarinya kuma ba son ta kake ba, This is a deal" Uncle Bashir ya ce "Amma Abba Hakimi wannan deal ɗin bai tsauri ga Malam ba?" Abba Hakimi ya ce "Ba kaji kai ma kace Malam ba? Yaa Sheikh zai iya ɗaukan wannan game ɗin" Murmushi Uncle Haroon ya yi kai tsaye ya yarda da abin da Abba Hakimi ya zartar cikin fara'a ya ce "To idan haka ne ina tsagin uwar gidan Halisa, za muje matsayin masu aikin gida kawai" Uncle Bashir ma ya ce "Ni ma dai ina team ɗin uwar gida" yaya Halima tai murmushi ta ce "Ikon Allah, to ina team ɗin Aliyu koma mai zai faru ya faru she is his wife matar shi ce babu laifi" Dr A'isha ta ce "Ni dai ba zan zaɓi team tun yanzu ba, sai naje Madina naga yadda zaman zai kasance" Idanun Yaa Sheikh ya yi jajir shi kam a rayuwa mai Abba Hakimi ya mai da shi? Ina ruwan shi da wata ƴar fillo balle har yaje gareta matsayin miji mai buƙatar hakƙin shi wajan matarsa? Zai bawa kowa mamaki. Miƙewa ya yi a hankali zai bar wajan Abba Hakimi ya ce "No tayaya ka taɓa ganin anyi deal ba saka hannu, maza saka hannu a wannan dairy ɗin" Yaa Sheikh ya kalli Abba Hakimi da kyau, shi kam Abba Hakimi ya ɗauke kan shi alamar bai gane meke nufi ba. Cikin sauri ya saka hannu tare da saka suna da date da kuma time. Yana gamawa ya juya jiri na ɗaukan shi sbd ciwon kai ya nufi Part ɗin shi.
Abba Hakimi yabi bayan shi da kallo a zuciyarsa ya ce "let's see ko Aliyuna waliyyi ne"
Wajan ya yi shiru kowa da abin da yake tunani a ran shi, Mother na tunaninsu yadda zata cusa Halisa a zuciyar Yaa Sheikh, kallo ɗaya ta yi wa yarinyar hankalinta ya kwanta da ita, kawai dai ta fahimci bakin yarinyar babu control kamar ba a gasa mata shi ba. Yaya Halima kam gani take kamar Yaa Sheikh ba zai iya tsallake wannan gasar ba, lura da yanayin Halisa da komai sai tafi Zahrah jan hankalin ɗa namiji kowa zaman zai kaya ohhu! "Kada a bari Jadda da Engineer su san maganar auren wannan yarinyar Halisa da Yaa Sheikh, mu bari muga abin da hali zai aga yanayin zaman maybe a samu sauyin ra'ayi game da Yaa Sheikh akan yarinyar" cewar Uncle Haroon. Abba Hakimi ya miƙe tsaye haka Uncle Haroon da Uncle Bashir sukai wa Mother sallama.
Bayan tafiyar su yaya Halima ta kalli Mother ta ce "Yanzu me zaki Barrister?" Mother ta girgiza kanta idanunta akan wayarta tana neman contact ɗin wata mata ta ce "me zan yi kowa yaya? ga Abban Sheikh nan ya gama magana" ta faɗi hakan tana danna call.
"Tun ɗazo da nace ki kawo mini bottle water ina kika tsaya?" Zahrah ta tambayi Halisa tana zare mata idanu. Ta turo baki gaba ita tsakani ga Allah take son faɗawa Zahrah abin da ta fahimta wajansu Abba Hakimi. Zahrah ta ce "ba dake nake ba dan ubanki?" Da sauri Halisa ta kalli Zahrah bakinta na rawa ta ce "Baffana kika zaga? Ya mutu fa?" Wani tsaki Zahrah taja ta ce "Idan ya mutu ni na mutu? Waye shi da ba za a zage shi ba" Halisa ta jima tana kallon Zahrah idanunta ya yi jajir ga abin masifa babu halin yi sbd ka shaidin Dada a gareta.
"Matsa ki bani waje ai dama har uwar suka haɗu suka mutu Kinga baki da sauran wani gata kiyi mini aiki hankali kwance" Halisa ta juya da gudu tare da fashewa da kuka hannunta a fuskarta tana karewa. karo suka ci da Maimoon data ɗakko warmers ɗin lunch wanda akace ta kaiwa Zahrah, Maimoon ta ja baya da sauri tana faɗin "Subuhanallah ya akai kike kuka haka ke dawa?" Halisa ta kasa kuka sai shassheƙa da zata iya ita gida kawai zata gudu wallahi. Maimoon ta ce "Ok ya isa daina kukan jirani a nan wajan kinji?" Ta ɗaga kai a nutse alamar "to". Zahrah na kwance waya a hannunta suna vedio call da Deen wanda gaba ɗaya ba vedion Allah da Annabi bane, ita dai Maimoon taji wani sauti kamar gurnani da sauri Zahrah taja duguwar rigarta zuwa ƙasa tana rufe wajan data buɗe. She pretended not to notice what she had done. Tana ajjiye warmers zata juya Zahrah ta ce "Hey you" Maimoon tai banza kamar ba taji ba. "Ina magana" Maimoon ta juya kaɗan suka haɗa idanu ta ce "dani kike?" Ta ce "to waye a ɗaki?" Maimoon ta ce "Huh na ɗauka kina magana da wayar hannun ki ce" Zahrah ta sakko daga kan gadon ta ce "what the do you mean by that?" Maimoon tai shiru can Zahrah ta ce "What's your name?" "Maimoon" ta bata amsa Zahrah ta ce "Ok At least you have to respect me ni matar yayanki ce, kin shigo bedroom without my permission da muna tare Yaa Sheikh fa?" Maimoon ta ware idanu sosai ta ce "Yaa Lee a bedrooms ɗinki? Shhhh" tana faɗin hakan tai waje da sauri.
"Kan uba wannan yarinyar sai na saita mata zama kalli Yadda take mayar mini da matar tani?" Waya ta ɗauka ta shiga kiran Surry.


Maimoon ta kalli Halisa wacce ke zaune a ƙasan carpet ta ce "Sister tasu muje part ɗin mu" Halisa ta girgiza kai Maimoon ta ce "Anty Zahrah ta ce mu tafi tare zuwa dare sai ki dawo" ta miƙe tana faɗin "Ita ta ce haka?" Maimoon ta ce "ita ce mana" hannunta ta kama suna zuwa Main parlour El-bashir na tashi tare da ɗaga waya ya nufi ƙofa, Halisa ta bi bayan shi da kallo ta ɗauka Balarabe ne. Maimoon taja hannunta har zuwa part ɗin su, Zeefa da auta Fattoumah suna zaune ganin Halisa yasa Auta Fattoumah faɗin "Wow yaya Moon wannan kyakkyawa ce She's very beautiful she looks like bro El" Maimoon ta ce "to sarkin surutu" ta zaunar da Halisa ta shiga ɗakko mata su ice cream da chocolate amma sam Halisa taƙi ce sbd bata saba dasu ba, ta ɗago kai a hankali ta ce "bana cin irin wannan" Nazeefa ta ce "To sai me?" A hankali kanta a ƙasa ta ce "Kindirmo nake shu" a tare suka zare idanu tare da faɗin "what?" Tai shiru tana kallon su can Maimoon ta ce "Zeefa haɗa mata ruwan wanka a bathroom bari na kawo mata kindirmon" tana faɗin hakan tai waje har lokacin Maimoon ta kasa mance abin da idanunta ya gani a bedroom ɗin Zahrah. Cikin sauri Zeefa ta haɗa mata ruwan wanka tare da nuna mata komai a toilet ɗin da yadda ake amfani da su. Suna bakin toilet ɗin suka ji ana knocking "Halisa duba kiga waye?" Kamar ba zata ba sai ta nufi ƙofar jiki a sanyaye zagin da Zahrah tayi mata har yanzu damun zuciyarta yake.
Halisa ta tsaya bakin ƙofa ta rasa me za ta ce can dai ta ce "waye?" Ta faɗa cikin ƙasa da murya. El-bashir ya gyara tsaiwa hannunsa riƙe da waya da kuma chocolate ya ce "Buɗe ki gani mana?" Halisa ta murguɗa baki tana ƙoƙarin buɗe ƙofar Zeefa ta ce "jeki kiyi wankan bari na buɗe ƙila Maimoon ce" Halisa ta juya zuwa bathroom ba tare da ta ce komai ba, Zeefa na buɗe ƙofar taga El-bashir tsaye fuska ɗaure ta ce "Yaya El" ya wurga mata harara ya ce "wace take tambayar waye?" Zeefa ta juya ta kalli ƙofar bathroom ta ce "Laa Halisa ce bata sanka bane" ya ce "I'll break her legs" chocolate ya bawa Zeefa ya juya yana faɗin "Kira mini Fattoumah" ya nufi Main parlour Mother dake zaune ta ce "Yau zaka shige ne?" Ya ce "I don't think so.. sai abin da Mai martaba ya ce" ta ce "Ohh abokin Mai martaba".


Washegari Zahrah na zaune ta caɓa ado cikin wata atamfa mai kyau ruwan ƙwai ta yafa mayafi babba kamar ta Allah. A hankali ta fito zuwa Main ta samu Mother zaune ita da Jadda suna hira sai Maimoon Zeefa da Auta Fattoumah suna makaranta. Zahrah ta durƙusa ta ce "Ina yini Mother?" Mother ta ce "kina lafiya ya kwanan baƙunta?" Zahrah ta ƙara sunkuyar da kai alamar kunya ta ce "Allahamdulillah, daman cewa nayi bari nazo idan da aiki nayi" Jadda da bakinta ke rawa ta ce "Allah ya yi gutsi gutsi da maƙaryaci" Zahrah taƙi kallon Jadda. Mother ta ce "Ayyah jeki ki huta ba aiki" Zahrah dai ta kasa riƙe abin da yake ranta ta ce "Yaa Sheikh fa? daman ina son gaishe shi ne" da hannu Mother ta nuna mata wani part ta ce "zaki iya samun shi can" ta miƙe da sauri ba kunya ta nufi Part ɗin Yaa Sheikh.
Mother ta ce "Maimoon kira mini Halisa yanzu" Maimoon ta nufi part ɗin Zahrah ta samu Halisa sai zuba kayan Zahrah take cikin trolley bag tayi saurin riƙe hannunta ta ce "Kizo Mother na kiranki" Halisa ta ce "Bari na ƙarasa aikin Anty" Maimoon ta ɗaga ta tsaye ba tare da ta ce komai ba ta jata zuwa waje. Bata samu Mother a parlour ba sai suka shige bedroom ɗinta tana zaune bakin gado. Mother ta ce "shigo Halisa, Maimoon jeki ko" Maimoon ta juya Halisa ta shiga kanta a ƙasa haka kunyar Mother tai mata nauyi taji kunyarta ta ce "Saki jekin ki zo nan" ta kama hannunta tare da zaunar da ita bakin gado ta ce "Yaya sunanki ma?" A hankali ta ce "Halisa Danejo Rome" Mother ta jinjina kai ta ce "Ok Zahrah ƴar uwar ki ce?" Ta girgiza kai ta ce "A'a wai aikatau zan mata" ta faɗi haka a taƙaice. Mother ta jinjina kai sosai ta ce "Saurare ni da kyau, Zahrah matar Yaa Sheikh ce Wannan babban mutumin da kika gani fari dashi?" Halisa ta ce "Balarabe?" Mother ta ce "Yawwa shi" haka kurum idanun Halisa ya cika da ruwa Mother ta ce "Shi ne mijin Zahrah kuma kema mijinki ne, dan haka ke ba ƴar aiki bace matar shi ce ke, kamar yadda Zahrah take matar shi haka kema kike matar sa" Halisa tai ta kallon Mother har lokacin idanunta cike yake da hawaye da gaske Balarabe shi ne mijin Zahrah?. Mother ta katse mata tunani da faɗin.
"Kece uwar gida, aurenki aka fara ɗaurawa sannan na Zahrah, na kira ki muyi magana sbd Yaa Sheikh ya ce baya son ki" da sauri Halisa ta miƙe tsaye hawaye na zubu mata bakinta na rawa ta ce "Amma ni ina son shi ai.....




Ni ina team Yaa Sheikh ku fa?


08119237616
Paid book
₦500"Kin san shi ne da kike son shi?" Mother tayi tambayar idanunta akan Halisa wacce hawaye ya gama cika mata idanu. Ta kasa cewa komai amma bakinta bai bar rawa ba, ganin yanayin ta ya sanya Mother sassauta murya ta ce
"Kina da ƴan uwa a garin nan?" Ta girgiza ta ce "Aradu babu" "Ok to ki Saurare ni da kyau, listening to me..." Tsayawa tai da maganar idan ma tayi ta san a banza, Halisa does not speak English, let alone understand what is being said. Ganin bata da wani option wanda ya shige tayi magana da harshen da Halisa zata gane ya sanya Mother tattara nutsuwarta ta ce "Ki ɗauke ni matsayin uwa kafin ki koma gida, zan riƙe ƙo kamar ƴar dana tsuguna na haifa, da farko ki yarda cewa ke matar Yaa Sheikh ce Balarabenki kamar yadda kika ce ɗin, Kinga zoben hannunki shi ne sadakinki, abu na biyu kada ki kuskura koda wasa ki faɗawa Zahra kema matar Yaa Sheikh ce, duk aikin data saki kiyi zaki samu lada albarkacin igiyar auren dake kanki, duk abin da Yaa Sheikh zai ce kiyi just do it ina nufin kiyi kai tsaye, ba zai cutar dake ba, infact ai kin riga da kin san shi ko?"
Halisa ta ɗaga kai da sauri kuma ta ce "Kuma ina son shi ai, ina ganin shi idanuna idan ina barci" Mouth ta ce "Good, a kullum yana tashi tun ƙarfe 4 na dare baya komawa barci sai ƙarfe 12 sbd ƙarfe 8 yake zuwa wajan ɗaliban shi, duk inda 12 tayi ya dawo gida, bai damu da abinci ba sosai ba zai taɓa cewa yana jin yunwa ba, tsakanin azahar da asr yana barci idan bai ba, ciwon kai yake sosai, sannan baya rabo da black tea da zuma a ciki, duk ranar Alhamis da Litinin azumi yake, yana son ƙosai sosai" Halisa ta saki murmushi tare da riƙe hannun Mother ta ce "Innalillahi ƙoshai aradu daɗi akwai burudi to? Wayyo Allah zanci ƙoshai na mure" dariya Mother zatai ko takaici bata son duk wannan shirman a wajan Halisa..
"Zaki samu abin da yafi ƙosai ba, amma can idan kina shirme gidan yankan kai suke kai mutum, ki zama a nutse, bayan haka yana son abincin gargajiya tuwo, dambu da sauran su dai, ki tabbata kina wanka sau biyu zuwa uku a rana, idan ba haka ba Yaa Sheikh kurarki zai yi daga gidan shi, kuma kishiyarki ta rabaki da mijinki har abada" Idanun Halisa ya sauya kala jin abin da Mother ta ce. Bayani Mother taci gaba dayi mata cike da ƙwarewa ta ɗora da faɗin.
"Kina jin alamun ya dawo, ko babu abin da zai miki kije wajan shi kice kanki ke ciwo ko ya koya miki karatu, zan zuba miki kayan amfani masu kyau ki tabbatar kina using dasu amfani kinji?"
"Zan yi ai, amma dai ba zata ƙwace mijina ba ko?" Mother ta haɗiye dryar data zo mata ta ce "Akan me? Idan kina yin abin da nace bata isa ta ƙwace miji ba, amma idan bakya yi uhm ko ganin shi kin dai na yi, yawwa sai gaisuwa kullum da safe kije ki gaishe sa, da yamma haka da kuma daddare, akwai lokacin da yake ciwon kai bai azabar zafi ganin shi har ɗauke yake ya zama kamar makaho, zan faɗa miki abin da za ki yi idan ciwon ya tashi, yanzu maza jeki gama aikin ki za kuje a gyara miki wannan gashin kan" Halisa ta miƙe tsaye kanta a ƙasa ta ce.
"Na gode" "is nothing jeki daughter" sai da taje bakin ƙofa ta juya a hankali ta kalli Mother idanunta ya yi raurau da hawaye ta ce.
"To yaushe zan faɗawa ina da miji? kuma yaushe zan fara dama masa fura" a ranta Mother ta ce "na shiga uku, wannan za ayi sirri da ita kam?" A file ta ce "zan faɗa miki ranar jeki" ta juya ta fita tana ayyana cewa da gaske dai Balarabe mijinta ne.
Kai tsaye ɗakin Zahrah ta koma taci gaba da shirya mata kayan da zata tafi Madina dasu, zuciyarta cike da tunanin maganganun da Mother ta faɗa mata. Ta sauke ajjiyar zuciya a fili ta ce "Wallahi kyakkyawa da shi, Allah ya sa na zama kamar shi" ta faɗa tana taɓa fuskarta sai kuma ta miƙe da sauri tana nufar inda mirror yake, a hankali ta shiga ƙarewa kanta kallo, bata hango nata kyan zallar kyan da Rabbil izzati ya yi wa Yaa Sheikh idanunta ke hangowa.
Tsaye tayi a bakin ƙofar da zata kaita parlourn Yaa Sheikh tun a nan kuma ta gane Yaa Sheikh daban yake a gidan, tsarin shi da yadda yake tafiyar da rayuwar shi, bata taɓa shakkar tsayawa gaban namiji ba, amma a yanzu tsoro da fargabar tsayawa gaban Yaa Sheikh da yadda kaifin idanun shi ke tasiri a zuciyarta sun gama cika Zahrah.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login