Showing 156001 words to 159000 words out of 197828 words

Chapter 53 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9331

tana cire hijabin Jikinta fuskarta a sake ta nuna itama ƴar duniya ce ta ce
"Kyakkyawan tarihi shi ake tunawa har ayi maka gori akai, masu ta zubar sai dai ya zame mutu tabo na har abar baya"
Surry ta shanye maganar ta ce "Haka fa, to ya kike fatan lafiya?"
A hankali ta ce
"Lafiya ita ke ɓoya, kin dai ga yadda nake, na ɗauka zaki bari sai na haihu ai?" Surry ta cije baki ta ce.
"Babu ko kunyata ki ke maganar haihu?" Halisa ta kaɗa ƙafa tana jingina ta ce "Cikin Yaa Sheikh ne fa, na halak ɗan sunna? meye aibu a wannan zamanin ake yawo dana shege ba bare wanda igiyar aure ya baka" tana faɗin hakan ta miƙe zata shige ta ce
"Mun kawo amarya ne, naga kamar baki sani ba, ko Yaa Sheikh bai faɗa miki ba, ƙilan abubuwan sun masa yawa ya manta" Halisa takai seconds 20 kafin numfashinta ya daidai a wannan tsaiwar da tayi, ƙirjinta ya buga mararta ta ɗaure sosai.
Idanunta ya shiga rufewa jiri na neman ɗaukanta, ta dinga kiran sunan Allah har ta samu daidaito ta maze fuska ɗauke da murmushi ta ce
"Ƙaramin abu uzururruka suke sawa a manta ai, yanzu kuma na lallaɓa shi yaje zai huta" har tai gaba ta ce
"Ina amaryar ko nace uwar mata inji Jadda nikam ai Mumy zance mata" mamaki ya kusan kashe Surry take zaune, ta ƙara tabbatarwa wuta ba wajan wasan yara bace an ajjiye ƙwarya a burminta.
"Akwai event anjima so tana hutawa zuwa lokacin" Halisa ta watsa hannunta sama ta ce
"As she wishes"
Da ƙyar ta ƙarasa bedroom ɗinta, tana zuwa jiri ya kwasheta cikin sauri Dada dake zaune ita da El suna magana akan yadda zasu faɗawa Halisa baƙon al'amarin.
"Danejo, what happened to you Halisa" ina tuni ta fara kokawa da numfashinta dake neman ɗaukewa kamar wata mai Asthma. Dada ta jata Jikinta ta rungume ta zauna bakin gado tana jijjigata tare da kiran sunanta amma ina a tsorace ta ce.
"Prince go and call Mother" ya miƙe hannunsa riƙe da sanda sbd ƙafarsa da bata gama ƙwari ba, yana fita ya samu Mother ita da Maimoon tsaye suna magana ya ce "Mom, my Mom is calling you"
"Lafiya dai Mubasshir" ya ɗan kalleta ya kalli wajan ya ce "Princess ina nufin Ha..." Bai ƙarasa faɗa ba tayi saurin bawa Maimoon bowl ɗin hannunta ta nufi bedroom ɗin Halisa.
El-bashir ya nemi saman kujera zuciyarsa fal tunani akan dalilin daya sanya Yaa Sheikh zai ƙara aure, ya rasa wacce zai aura sai Zahrah yarinyar daya sha ganinta lokacin da ya je raka Mai martaba Oummara.
Ya juya ya kalli Maimoon ya ɗan kalli bayanta ya ce "Where's Fattoumah?"
Ta ce "Zazzaɓi ke damunta, tana bedroom"
A hankali ya ce "call her"
Ta juya a zuciyarta tana mmkin miskilanci na El sai wanda ya yi niyya da shi zai magana.
Yana zaune hannunsa riƙe da waya yana dannawa ta shigo parlourn bakinta ɗauke da sallama, ya amsa without looking at her
"Uncle El gani" ta faɗa a hankali tana riƙe kai, ya ɗaga kai ya kalleta ganin yadda tayi tsaye kamar ana yaƙi ya ce.
"Zan rankwashi kan ki,idan ki ka sake ya yi mini tsaye" ta tura baki ya miƙa mata hannu ya ce "Come"
Ta kama hannunsa ta zaune gefensa yaji Jikinta zafi ya shafa kanta ya ce "How long?" Ta kalle shi ya ce "the fever" ta ce
"Yau ne" ya jinjina kai yana faɗin "Sorry"
Tai shiru ba tare da tace komai ba, ya samu kan shi da son jin muryarta ya ce "Fattom ya akai?"
Hawaye ya shiga saukar mata ta ce "Mother nake so ta dawo wajan gidanmu, kowa babarsa na tare da su mu daga Grandma sai Father" ya lura abinda ke damunta kenan, yarinyar nada riƙo sosai cikin son kwantar da hankalinta ya ce
"Kina son daina damuwa?" Ta ɗaga masa kai ya ce "Ki biyoni nan muje na ajjiyeki har abada" ya faɗa yana nuna mata saitin zuciyar shi. Ta dinga kallon shi ta rashin fahimta ya ce
"I love You Fattom, Kinyi ƙarama but I'll manage zan kula dake" kunya ta kamata ta miƙe da gudu tabar wajan ya bita da kallo yana taɓe fuska.
Mother dake tsaye ta dinga trying number Yaa Sheikh baya going ta ce
"Meke damunta ne wai?" Yarinya rigima tai yawa, ga saurin ficewa daga hayyaci. A raunace Dada ta ce "Ban sani ba, kawai haka ta faɗo"
"Ko ta samu labarin auren Yaa Sheikh ne?" Dada ta ce "Anya? Bana jin haka" Ta dubi Halisa dake kwance jikin Dada ƙirjinta na ɗagawa hawaye na bin fuskarta, ta juya babu jimawa ta dawo da ruwa mai sanyi ta buɗe ta shiga shafa mata a fuska zuwa ƙirjinta, taja doguwar ajjiyar zuciya a hankali ta buɗe idanunta ta shiga binsu ɗaya bayan ɗaya ta ce "Da gaske Abbana Ya auri Zahrah?" Dada da Mother suka kalli juna, suka kasa bata amsa ta miƙe zaune hawaye wani na korar wani ta ce
"Kuma ya tabbata Abbana ya sakeni? Yanzu nu ba Matar Yaa Sheikh bace na daina amsa sunan Matar Malam, ya auri Zahrah" Idanunta ya ƙara rikicewa Mother ta ce "Wai injiwa? Waye ya ce ya auri Zahrah?"
A takaice ta ce "Her friend Surayyerh" Mother tai murmushi ta ce
"Yanzu maganar banzayen can ki ka ɗauka? Ko dan ranki ya ɓaci ai ta faɗa ke kuma ki ka yarda mai maimakon ki nuna mata baki damu ba, ko mata uku Yaa Sheikh zai sake aura" Ta runtse idanunta taji jamar zuciyarta ce zata faso sbd yadda take harbawa ta ce
"Don Allah Mother ki faɗa mini gasky, wlh zuciyata zata buga ni kaɗai nake son Abbana bana son ko wacce mace ta so shi" Dada ta ce "Da gaske....," Tayi saurin katse Dada da cewa
"Maganar aure babu, sun zo kawo wai Muhammad dayi miki murna zama hafiza" wata wahalalliyyar ajjiyar zuciya ta sauke mai nauyi a fili ta ce
"Allhamdulillah" Sai tausayinta ya kama Mother domin Halisa na cikin matayen nan masu bala'in kishi wanda yake kusan yin ajalinsu ta ce
"Dole ki nuna musu babu abinda ya shafeki, ki tashi yanzu ki wanka mai gyara zata zo a ƙarasa yi Kinga idan akai yau shi ne aka ɗauki wata guda anayi, za'ai miki nut make-up akwai event a gidan Ummul"
Ta miƙe tsaye, Dada ta dinga kallonta a ɓoye da yadda kullum cikin Halisar ke sake bayyana kanshi a fili, ya zauna tas wanda ya ƙara mayar da ita babbar kan ɗauka tayi shekaru 20 zuwa saka amma she's still on 17 going to 18.
Wanka tayi da wani bath perfume wanda aka kawo mata tun daga Maiduguri, tana fitowa mai gyaran wacce ta kasance matashiyar budurwa ta fara yi mata dilka a jiki nan da nan fatar ta ɗauki glowing, ana gamawa aka saka mata turaren wuta na jiki aka rufeta da wani duvet ya shiga ratsa jikinta, kana ta bata wani ta tsuguna akai ya shigeta da kyau, ta sake yin wani sabon wanka gabaɗaya bedroom ɗauki ƙamshi turaren ya zauna Jikinta, kowa ya ganta sai ya yaba kyan Jikinta, musamman data kasance mai haske.
Aka shiga yi mata make-up duk da tace bata so, amma Mother ta tsaya akanta kafin a gama akawo wani farin voyel na mata mai golden ɗin flowers da manyan zane, ana gamawa ta saka kayan riga da skert ne ya kama Jikinta ya yi bala'in kyau, akai mata ɗauri mai steps, Halisa bata yarda da gaske ake event ɗin ba, sai da taga an ɗakko golden ɗin Alkyabba ta mata mai farin zane an saka mata. So ma sha Allah! Ta fito a Princess Halisa Ahmad Nuran Sarki, ta fito a Halisa Danejo Rome sbd kyanta na Fulani, Ta fito a Halisa Sheikh Aliyu haydar Aliyu sbd nutsuwar ilimin data bayyana a jikinta.
Make-up artist ɗin ta dinga yi mata vedio da pictures masu a zaɓaɓɓen kyau. Mother ta ce "Ki zauna kada ki fito,sai ma kira ki" ƴar Maiduguri ta shiga bawa Halisa kyakkyawan darasi na aure tana mata bayanin abubuwan da maza suke ƙauna musamman mijinta daya kasance babban malamin addinin Muslunci.
Zahrah da mai make-up ɗinta, aka zuba wani eyelashes da eyeshadow ta saka red ɗin lace fitted gown "Wai meye kike haɗa rai?" Ta ce "Naso nasan wanne kaya yarinyar can zata saka ne wallahi" Surry taja tsaki ta ce "Kina da damuwa, yarinyar da bakya gabanta" Zahrah ta ce
"Ba zaki fahimta ba, yarinyar kamar ƴar tsana wallahi komai kyau yake mata" Surry ta ƙara jan tsaki ta ce "Madam be yourself".
Misalin biyar daidai ba tare da sanin kowa ba motar Halisa ta bar gidan zuwa gidan Ummul, Babban harabar gidan an zuba masa decoration sai ka ɗauka hall ne, yanayin decoration ɗin sai kayi mamaki domin close hall akai mayar da wajan mai maimakon open, Familyn su Ummul da suka kasance manyan mutane wayayyu duk sun zo, Aka rufewa Halisa fuska da hular Alkyabba Ummul ta kama hannunta zuwa wani bedroom ba kowa ciki, ta shiga kiran Yaa Sheikh baya ɗagawa, ta kira Umar-khan shima bai ɗaga ba, tun safe Yaa Sheikh yabar wajan sauka har biyar ina ya yi? Ko ya mance da batun event ɗin?. Tana tsaye sai ga Khalil ya shigo suka gaisa ta ce "Yarima ina Yaa Lee ɗin?"
Ya shafa kai ya ce "Yana can ɗaya part ɗin Halisa nazo kira" tai murmushi ta ce "Ok zata zo"
Ummul ta ƙara feshe Halisa da perfume wanda Yaa Sheikh yake mahaukacin so, ta jata ta ƙofar baya har zuwa part ɗin da yake ciki. Sai kunya ta kama Halisa Ummul ta harareta ta ce "Ke da Abban naki?" Tai ƙasa da kai, a hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar cikin siririyar muryarta ta ce "Assalamu alaika"
Yana tsaye a tsakiyar parlourn fitowar shi kenan daga wanka ya shirya cikin shadda fara da Alkyabba wanka ya zuba kyau sosai, saukar muryarta ya sa ya juya a hankali suka haɗa idanu, frm head to toe ya dinga kallonta a ransa ya ce
"Mace ta gari" a fili kuma ya ɗan saki fuska tare da ware mata hannu alamun ta zo, kanta a ƙasa ta shiga takawa har zuwa inda yake tana zuwa ya jawota jikinsa yan ɗora kansa a wuyanta ya ce "Amincin Allah ya tabbata ga ruhin Aliyu" ya rungometa sosai daidai lokacin suka ji ƙarara saukar camera akansu ta ko'ina, da hasken vedio, Khalil Ahmad Nuran Sarki, Umar-khan, Ishaq-Hakim, El-bashir Ahmad Nuran Sarki sai wani ɗan uwan Yaa Sheikh wanda bai san da shi ba sai yanzu Mujaheed gabaɗaya sun saka farar shadda da milk ɗin Alkyabba, sai wasu photographers wajan su biyar, Hadda Majeeda photographers mai yiwa sarkin Kano photo, Yaa Sheikh an shammace shi, baya son wanann bidi'ar bai kuma san da ita ba, yana son sakin Halisa sbd vedion da ake musu amma yana tsananin kishin pech ɗin jambakin da aka saka mata, ya ware fararen idanunsa akanta gently ya tallafo haɓarta yana ƙara ranƙwafawa daidai fuskar yana mai rufeta da Alkyabba cikin nutsuwa ya ɗora bakinsa saman nata, su duka suka lumshe idanunsu rabon da suji ɗanɗanon kiss na juna sun manta wata kyakkyawar cafka ya yi wa bakin nata ya shiga kissing nata cikin kwarewa irin ta malamai a ran shi yake jin duk gift ɗin daya ta nada sunyi kaɗan a gareta, ya ƙara janta ya matse ya rungometa sosai kamar za a ƙwace ta...




Sarautar's Library
Paid book
#500
08119237616Latest news On IDAN BA KE.......❤️ There is a prize for the person who comments the most on TICTOK👇🏾
https://vm.tiktok.com/ZMYLLt9QX/


Dan shin da yaji a gemunsa da kuma kwantaccen zagayayyen gashin da ya yi luf saman bakinsa ya sanya ya fahimci kuka take mara sauti, ya zame fuskarsa bayan ya tabbatar ya gama shanye gabaɗaya jambakin da lipstick ɗin dake bakin nata.
Da kyawawan idanunsa wanda suka janye ya zuba mata su, ba tare daya rabata da jikinsa ba, ya tallafo haɓarta tare da sanya yatsar hannunsa ya goge mata hawayen yana ƙara ware idanunsa a kanta so yake ya buɗe baki ya furta.
"Ya kike? Mene na kuka?"
Amma bakinsa ya yi nauyi harshensa ya harɗe, ta kalle shi muryarta na rawa ta ce
"Da gaske ka sakeni Modibbo" ya buɗe ido sai kuma ya matse kafaɗarta like
"Oh!" Ya tsare ta da idanu, yana son yaga reaction ɗinta ya kuma gani ɗin. Domin gabaɗaya Jikinta ne ya fara rawa hawayen fuskarta ya ƙaro tana neman lalata make-up ɗin wacce tayi masa kyau a idanunsa, but he didn't know tayaya zai ce yaji daɗin kwalliyar ya kuma yaba.
Jikinta ya yi sanyi tai ƙasa da kanta tana shassheƙar kuka, yaja baya kaɗan yana zama saman kujera fuska kame ba can ba ya ce.
"Ibrahimul-khalil i want to be alone" Khalil ya ce
"You want to be alone, or want to be your wife?"
Umar-khan ya yi murmushi, yana da matuƙar girmama shekarun mutum, magana indai ta manya ce baya shiga, hakan yasa ya shafa kansa yana mai juyawa..
"Umar-khan ji mana"
Khalil ya kira shi yana cewa "Ina zaka? Let's celebrate together Princess jeki zauna close to your husband"
Ta tattara Alkyabbar jikinta kanta a ƙasa ta ƙarasa kujerar da yake zaune akai, gently ta zauna kanta daidai kafaɗar shi, babu wanda Yaa Sheikh ya kalla a cikinsu, turaren dake tashi jikin Halisa shi ne babban abinda ya sanya shi cikin wani hali
Ya kame tare da riƙe kansa, Khalil ya ce
"Drop your head" ta kalle shi a kunya ce ya ce "Ina nufin ki saka kanki a shoulder ɗin shi"
Ta juya tare da kallon Abbanta taga ba ita yake kallo ba, gently ta ɗora kan nata, tare da rufe Idanunta ta ɗora hannunta saman nashi, al'amarin dake fin ƙarfinsa ya sanya ya buɗe narkakkun idanunsa ya sauke a kanta yana ɗan ranƙwafa kaɗan daidai lokacin photographers ɗin suka shiga sauke musu pictures kala-kala.
Duk irin abinda sukai Yaa Sheikh bai motsa ba, ya sarautar fulanin tashi ta motsa, Halisa ake bawa styles wanda ake ɗaukan photon da shi..
El-bashir ya nufi wajan yana zuwa ya rungome Yaa Sheikh ɗaya gefen kuka ya riƙe Halisa ya ce
"One picture please"
Akai musu picture, daidai kunnen Yaa Sheikh El ya ce "Abba Tell your wife ta daina fushi da yayanta, ta ƙulla ce ni ni kuma ina son sister ɗita"
Sai a lokacin Yaa Sheikh ya yi murmushi yana girgiza kai ya ce
"Come Mubasshir" El ya durƙosa gaban Yaa Sheikh, a taushashe ya ce "Kayi rigima, amma ta ƙanwarka yawa gareta kada ka damu" Halisa ta kwaɓe fuska tana marairaice fuska tare da watsawa El wani kallo ya ce "Abba hararata take fa" Yaa Lee ya juya suna haɗa idanu da Halisa ta tura masa baki ya ɗauke kai kawai.
Ɗaya bayan ɗaya suka fice daga cikin ɗakin, ya rage daga Halisa sai Yaa Sheikh, ta lura zanan fulawar hannunta yake kallo da kuma jan henna ɗin da Sss henna tayi mata, ta fahimci ya yi masa kyau amma bai san me zai ce ba. "Ya yi kyau ne Modibbo?" Ya lumshe idanu ya buɗe yana ƙara kallon hannunta kafin ya kama ya riƙe cikin nasa, a nutse kuma ya kai hannun bakinsa ya sumbata ya saka yatsun a baki bisa sunna ya tsotsa ya ce "Allhamdulillah" shi ne kawai abinda ya a furta, yana riƙe kan shi. Ya miƙe tsaye yana cewa
"Meye kike kallona haka?" Tai ƙasa da kanta nauyin Abban nata ya kamata ta ce
"Babu" da hannu ya nuna mata ƙofa ya ce "Go"
Bata ji daɗi ba, ta juya cikin sanyin jiki zata fita taji ya rungometa baki ɗaya, numfashinsa na sauka a wuyanta ya hanata juyawa baya buƙatar da kalli cikin idanunsa sun juma a haka cikin muryar da bata san yana da ita ba ya ce "For the make-up"
Ya yi kissing wuyanta ya ce "Jazakallah-bil khair Allah ya yi miki Albarka" yana faɗin haka ya juya mata baya, tayi sauri zata sha gabansa da sauri shi ma ya shige bedroom yana murza key tare da ɗaga shaddar jikinsa yana mai ɓoye abinda baya son ta gani.
Tayi tsaye tana mamakin abinda yake ɓoyewa ganin bata fahimta yasa ta fita jiki a sanyaye. Tana fita Ummul ta kamata, Halisa ta ce ita sallah zatai yin duniya aka juya tace itafa magriba tayi dole aka rabu da ita, bayan ta idar mai make-up ta ƙara yi mata wata, ta shiryata cikin wani farin lace mai kyau da tsada wannan karan ma hadda Alkyabba.
Zahrah na zaune a bayan mota, aci uwar kwalliya ana yauƙi, Surry na zaune kusa da ita, tai kwalliya itama, hannunta riƙe da waya tana duba, kamar daga sama tana shiga I.G taci karo da posting ɗin B.B.C ya buɗe ido da kyau Yaa Sheikh ta gani zaune a kujera sai Halisa dake gefenta ta marairaice fuska shi kuma yana kallon yadda take rigima su duka gabaɗaya sun sha Alkyabba sunyi wani irin kyau wanda baki bai isa ya faɗa ba. Under the posting ɗin aka ce
_“Bayan samun jita-jita akan auren Babban malamin nan da matar da bamu sani ba, yau gani ya kori ji, Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu ya auri ƴar gidan Sarkin Sokoto Princess Halisa Ahmad Nuran Sarki, yayinda suke walimar zama hafiza da tayi a makarantar Ibadur-rahman, Allah ya sanya albarka”_
Zufa ta yankowa Surry kamar ita ce Zahrah ta ce "Zahrah anya baki ɗebo ruwan dafa kanki ba?" Zahrah ta ce
"Kamarya?" Ta miƙa mata wayar, Zahrah ta dinga kallon picture ɗin zuciyarta na bugawa sai ta ce "They're lie, ƙarya ne" Surry ta ce
"BBC basa posting ba tare da sun tabbatar ba fa, amma bari na duba Twitter ai Prince Khalil nayi" tana shiga Twitter tai searching.
Prince Khalil Ahmad Sarki. Sai ga profile ɗinsa ya bayyana tana shiga taga anyi tweet 20 minutes ago, a nan taga pictures kamar hauka na Yaa Sheikh da Halisa. Ya rubuta “Finally, the day, the most most couple's in the world, Mrs....and Mr Congratulations My sister Princess Halisa Ahmad Nuran Sarki with her handsome husband Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu” A fili Surry ta ce
"Tab, ina ruwan saki na dafe" Zahrah ta kasa magana kishi ya mamaye mata zuciya, Surry ko a ƙafarta ta koma ta dinga karanta Retweet na mutane, harda masu cewa Ai Halisa tayi masa ƙarama. Ana haka taga Tweet ɗin El-bashir ya faɗo just now.
Photon Halisa da Yaa Sheikh ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login