Showing 120001 words to 123000 words out of 197828 words

Chapter 41 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9336

tana ƙoƙarin kunce igiyar gaba ɗaya daga jikin reshen bishiyar, kamar daga sama taji saukar wani abu mai sanyin gaske zuwa kafaɗunta. Cak ta tsaya tana sauraren yadda abin ke tafiya sululuuuu a jikinta har ya gama sauka, hannunta ta miƙa da nufin kama abin da ya sakko mata domin bata da tsoro ko kaɗan, cikin rashin sa'a hannunta ya sauka saman ƙaton kan maciji wanda yake kwance a jikinta, wani santsi-santsi ta ji a jikin macijin ga wani sanyi sosai dake ratsa fatar jikinta, bata gama yadda da abin da zuciyarta ke ayyana mata ba, a hankali ta juya wani ihu ta kurma wanda ya yi daidai da ɗaukewar numfashinta, baya tayi zata faɗi kafin ta kai zuwa ƙasa macijin ya yi wata girgiza cikin sakanni ya juye zuwa wani saurayi wanda jikinsa ya ke sanye da wasu haɗaɗɗun kayan sarauta na farin saƙi, fari ne tas amma kamar Fatar mace haka fatar hannunsa da sauran jikinsa suke gaba ɗaya gashi ya kwanta luff. Zubewa ya yi a ƙasa ta faɗo jikinsa idanunsa a kan fuskarta, ya jima yana kallonta kafin cikin izza da nutsuwa ya ce "kin tsoratani, kin tsorata kanki Danejo, banyi niyyar zuwar maki ba yanzu" Danejo sunan da ƴan rugar Rome suke faɗawa Halisa ke nan. Sai da ya gama Kallon ta sosai, kallon da ya jima bai mata ba tun tana zanin goyo matsayin Jaririya. Ɗaukanta ya yi ya nufi inda Naggen suke yana zuwa ya tarar da wannan Saniyar dake Shure Shure ta haihu, ashe daman ciwon haihuwa ke damunta. Halisa ya kalla yana sakin Murmushi kafin ya zaro harshesa waje sai ga wani zobe ya bayyana, cikin sauri ya saka mata zoben mai ɗauke da tambarin wata masarauta, kafin ya yi Girgiza sai ga shi ya sauya kama, kamarsa a fuska na nan, amma kayan jikinsa sun sauya sun koma irin kayan Fulani sak komai da komai, goya Danejo ya yi a bayansa, ya ɗauki jaririn Saniyar cikin nutsuwa ya fara kaɗa Naggen zuwa Rugar Rome. Kamar ƙifatawar idanu haka ya ƙaraso Rugar..


Domin samun cikakken Littafin sai ku dannan Bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton 👇👇


https://www.aihausanovels.com.ng/2023/01/idan-ba-ke-by-nimcy-sarauta.html


👆👆👆Cak Yaa Sheikh ya tsaya daga tafiyar da yake, tunda ake wannan abun bai taɓa jin maganar data buge shi irin yanzu ba, ya kasa juyawa gani yake kamar ba gasky bane, ji yake kamar ya nutse a wajan dan kunya, babu wacce yake jin nauyi acikin wannan al'amarin kamar Mother, Father gumi kawai ke yanko masa idan ya miƙe sai ya koma ya zauna
"Kin san me ki ke faɗa kowa? Kalamanki sunyi tsauri, tsaurin da ba ko wanne kunne zai iya ɗauka ba" Zahrah ta ce
"Abba ina son Yaa Sheikh, akan soyayyar shi na yanke shawarar faɗa maka gaskiya, wallahi Father shi ne Uban jaririn nan" da ƙarfi cikin ɗaga murya Father ya ce.
"Ƙarya ki ke, munafuka Algunguma ni zaki yaudara,ina matsayin abokin uban naki? Sbd kuka ko muryarta baya fita ta dubi Father sai ta ɗauki wayarta tare da shiga vedio ta play akan wani vedio tare da juya screen ɗin wayar zuwa ga father,
Kasancewar suna waje ɗaya da Abba Hakimi ne yasa shima yana daga zaune yanke hango vedion.
"Amma ba zaka ka manta da vedion nan ba ko? Shi kaɗai ya isa ya zama shaida a gareni?"
Jikin Father rawa kawai yake da ɓari. Su biyu ne a cikin vedion a ɗakin hotel Zahrah na zaune Engineer Aliyu wanda aka fi sani da Father tsaye yana riƙe da waya a hannu. Zahrah ta dube shi da kyau ta ce
"Na faɗa maka ina ɗauke ciki kuma naka baka yarda ba, ga Pregnancy Test ɗin da nayi maybe zaka fahimta daidai" Father ya kalli Zahrah kafin ya karɓi result ɗin ya duba ya ce.
"Kin tabbatar ciki na ne Zahrah?" Ta ce "Of course YES! Kada ka manta kai ne ka amshi virgin ɗina" Ya yi murmushi ya ce.
"Ni ɗin? ni ki ke kira na amshi Virgin naki?" Ta miƙe tsaye ta ce "Oh! Ka manta before hakan ya kasance nayi Virginity test?"
_The only way to know whether or not someone has had sex is to ask. There are no physical examinations or tests that can reveal whether or not a person has had sex before. No, not even so-called “virginity tests._
Ya ce "Ban manta ba, kawai nayi mmkin yadda cikin ya shiga ne, amma ya kamata a zubar da shi kafin kowa ya sani" ta ce "Tab wai ba, ciki ɗaya, ciki biyu, ciki uku duk kana sani subar dashi a wannan karan ba zan yi ganganci da rayuwata ba, kuma Dr ya tabbatar cikin ba zai fita ba ka nemi mafita" Ya sauke numfashi ya ce.
"Ok shikenan, amma waye Deen da kuke mu'amala da shi kada kiyi mini ƙarya nasan komai kina nufin shi bai isa ya ɗora miki ciki ba, ko shi ba namiji bane?" Yana sauke magana ta ɗora da faɗin.
"Ya isa har ya kai, ba gwanda shi ba, tsakani na da Deen ya sauke mini sha'awata, ta hanyar romance wani abu mai kama da sex bai taɓa shiga tsakanina da shi ba" Father ya ce.
"Ki aure shi mana" da ƙarfi ta ce "I can't, cos I don't love him anymore ba zan aure shi ba, idan kuma kana son Ubana ya san halin da ake ciki fine, Dady ne da laifi daya sahale maka shiga gidan shi sama taka da sunan wayewa, sai yanzu nake jin baƙin ciki da kuma taƙacin ilimin da nayi na shige ƙa'ida gabaɗaya wayewar gidanmu bata amfane ni da komai ba" a rikice Father ya ce.
"Calm down please Beb, yanzu me ki ke so ayi?" Ta ce. "I want to marry your son Aliyu" a firgice Father ya ce. "Kin san me ki k cewa, Aliyu fa? Kai ba zan iya ba" ta ɗauki jaka ta ce. "Ok fine, zan sanar da Dady komai" ya yi saurin riƙota ya rungome sosai ya ce.
"Is okey, na amince ki auri Aliyu kuma zan yi masa ta ƙarfi yadda dole sai ya aureki, kuma ki ɗora alhakin cikin akan shi" Zahrah tai dry ta ce
"Gaskiya kai ɗan iska ne, ka ɗorawa ɗan ka cikin ka, to ɗan shi ne ko ƙanin shi?" Father ya yi murmushi ya ce.
"I've no option, what ever yanzu muje ki ban kayan daɗi, banda ina mugun so da ƙaunar Barrister wallahi da aurenki zan, amma inawa Barrister son da ba zan iya yi mata kishiya ba" ta taɓa baki.
Cikin sauri Abba Hakimi ya ce. "Stop the video"
Ya faɗa yana runtse idanunsa ganin ana ƙoƙarin sake aikata zina ta vedion.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Uncle Haroon da Uncle Bashir suke ta maimaitawa Jadda ta kece da kuka ta ce.
"Ashe dai ɗaga nono ya tabbata akan Ali, na haifi karuwi a cikina, na haifi ɗan taure mai bin ƴan iskan mata, Allah ya saka mini Allah dai ya saka mini haihuwarka da nayi, da nonona daka sha da tarbiyyar dana baka, wacce masifa ce wannan mutum kamar wani Ayu!" Mai martaba ya yi ta jin abun banbara kwai, wai namiji da suna Hajara, ganin abin yake kamar wani wasan kwaikwayo ko labarin littafan hausa da ake faɗa..
"Ina jinki Zahrah"
A hankali ta ce "Tunda mukai haka da shi ya tafi ya fara neman hanyar da zai sanya Yaa Sheikh ya aure ni, cikin haka aka samu matsalar daya sanya Yaa Sheikh dawowa daga Madina ba shiri, lokacin da ya amince da aurena kafin ya faɗawa Dady ni ya fara sanarwa, nasan da komai. kullum da fargabar yadda zan kasance da Yaa Sheikh, i love him with all my heart and soul, ganin bani da mafita ya sa na nemi Deen da ƙawata Surrayerh, ita ta bani shawarar neman yarinya...." Ta faɗa musu duk yadda tsara plan na ɗaukan Halisa da yadda suka kai Dada asibiti, daɗin da ɗawa sun ƙara yi mata asiri wanda ya yi tasiri a jikinta shi ya sa bata fiye damuwa da son zuwa wajan mahaifiyar ta ta ba. Ta share hawaye ta ce
"I knw i made a mistake, but isn't my fault domin Deen ya amshi cikin da bana shi ba da hannu bibbiyu, burinsa shi ma ya ɗorawa Yaa Sheikh laifin cikin, mun su dayin auren Aliyu ya kasance dani yadda zan iya cewa bakwaini na haifa, hakan bai kasance ba nasan na cutar da Yaa Sheikh da maganin dana bashi daga baya kuma na fahimci tabbas ya je wajan Halisa be tunda matar shi ce, Sai yanzu na gane dalilin da ya sanya Aliyu baya raɓar inda nake. Ci,sha, ya bani baya takura ni"
Tunda ake wannan abun banda kuka babu abin da Mother take ƙirjinta har ɗagawa yake, baƙin cikin mugun tabon da Father ya barwa ya ranta shi ke damunta.
Abba Hakimi ya juya kan Father ya ce. "Engineer ka ɓata wayonka, ashe zaka iya yiwa ɗan daka haifa sharrin da zan gina baƙin ciki a zuciyarsa, ya kuma ɓata kyakkyawan tulabin halayyar shi da yake ciki?,
Nayi mamaki na kuma kasa fahimtar da gaske abubuwan da kake ji wani waje zai iya faruwa a inda ka ke" Father ya goge zufa ya ce.
"Na amshi laifina, amma bani ka ɗai bane a family wanda yake son ganin bayan Yaa Sheikh, sai ki faɗa musu sunan mutumin daya koma Deen" Yaa Sheikh dake tsaye har yanzu sunan Allah kawai yake ambata a cikin ranshi, idanunsa sukai jajir jijiyoyin kansa sun fito, sai huci yake fitarwa.
Zahrah tai shiru ta kasa cewa komai Father ya ce.
"Bani ki ka tunawa asiri ba?" Kai tsaye ta ce
"Duk abin da ya samu shamuwa watan bakwai me ya ja mata" Ya ce.
"Ok fine sai ki sanar da su Saif-wazir shi ne Deen stop lying to them" Abba Hakimi ya dafe kai ya ce.
"Saif-wazir? How can that be possible? Meye nashi na son cin mutumcin Malam? Me ya yi masa?" Daga bakin ƙofa Saif-wazir daya shigo yanzu ya ce.
"Saboda ka fifita ɗan wani fiye da ɗan daka haifa a cikinka Abba" Abba Hakimi ya miƙe tsaye bai tsaya jiran komai ya saka hannu ya ɗauke Saif-wazir da mari ya ƙara ɗauke shi da mari, ya jera masa guda biyar a jere da sauri Mai martaba ya riƙe hannun Abba Hakimi ya ce
"Idan rai ya ɓaci, nutsuwa ke nemu shi, marin ba mafita bane" Saif-wazir ya kalli Abba ya ce.
"Like this, irin haka sune suka sanya mini tsanar Yaa Lee, kaƙi bawa yaran daka haifa space a zuciyarka, har dukiyar dana mallaka sai dana rasata dalilin Yaa Lee, bani da masaniyya akan Zahrah zata iya auren Yaa Lee wata rana, amma nasan Babanta Best friend ɗin Father ne, na nemi connection da ita na tsara plan ɗin yadda zata jawo hankalin shi harta su kasance abu guda na ɓata masa suna, sai ya zamana bana nasara Yaa Sheikh ko sha'awar dawowa Nigeria ba ya yi, a haka har Allah ya kawo ranar da aka haɗasu aure kasa barci nayi don farin ciki burina zai cika, Abba ka mareni kasa an saka ni acinin mari, tun kafin nai wayo har boarding school nai duk dalilin Yaa Lee, mene laifina dan nayi kishi da shi,bayan nasan ko mutuwa kayi bashi da gadon ka tunda ba ɗan ka bane"
Ya ƙare maganar yana hawaye. Tunda Abba Hakimi yake ba'a taɓa masa rai irin na yau ba, ya kama hannun Saif-wazir ya ce
"Aliyu shi ne komai nawa, tunda ya so ƴar dana fi so fiye da komai, ya kareta daga mugwaye azzalumai, ya kula da ita hai ta haifi Halisa, akan yarinya ƙarama ya zaɓi aci gaba dayi masa kallon gwauro, tuzuru, wasu na jifan shi da maganganun rashin ɗa'a akan me ba zan fifita shi fiye daku ba? Me ya Umar-khan bai complain ba? Me ya sa Ishaq-Hakim bai complain ba sai kai? ba zan aibata ka ba, amma kaje na yafe ka, ka nemi wani uban!"
"Kada ayi haka Abba, don Allah a saisaita abi komai a sannu" Abba Hakimi ya ce. "Sarauta ta girmi tsofa, amma ba zan iya yin haka ba, dole Saif-wazir yabar mini gida" Umma A'isha ta ce
"Ya zama dole, tunda ya zaɓi hakan" Saif-wazir ya kalli Umma A'isha ya juya ya kalli Abba Hakimi ya kalli Yaa Sheikh dake fuskantar ƙofa, sai kawai ya yi murmushi yabar gidan bakiɗaya.
Mother ta goge idanunta tas ta ce "Allhamdulillah! Hakan ya yi mini daɗi ko ba komai nasan halin uban yarana, banyi mamakin yadda Mamana Fattoumah bata son ka, akwai abin data gani tare da kai, Aliyu ina son ka ƙarasa cike mini sakin da kayi wallahi na gama zama da kai"
Father ya girgiza ya ce
"Abin da ba zan taɓa iyawa ba kenan Maryam, ko sakin da nayi miki ban san nayi ba, wlh ina son ki ba zan iya rabuwa dake ba _*IDAN BA KE*_ am nothing absolutely nothing"
Uncle Haroon ya sauke masa wasu tagwayen maruka wanda ya sa Father saurin runtse idanu yana dafe fuska.
"Shasha ban taɓa jin kunya a rayuwa irin ta yau ba, ka kunya tamu gaban mutanan da suke da ƙima da martaba a idanunmu, tashi kabar wajan nan" Mother ta ce
"Yaje ina? idan yabar gidan nan ka tabbata ya ƙarasa ciki mini raguwar saki ɗayan" Cikin tashin hankali ƙarara Father ya ce "Wlh ba zan iya sakin ki ba, duk abin da za kiyi" yana faɗin hakan ya miƙe jiki ba kuzari, sai da yaje bakin ƙofa Mother ta ce
"Mu haɗu a Court"
Mai martaba idanunsa akan Dada wani irin sabon son ta na ƙara taso masa ya nisa ya ce.
"Allah ya kyauta, Ubangiji kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu. Ya cire masa ƙyashi da hassada" duk suka amsa da abin. Ummul ta duba agogo tare da miƙewa ta ce. "Zan tafi Allah ya ki ya ye" Sai a lokacin Umma A'isha ta ce.
"Kiyi haƙuri da abin da aka aikatawa Yaron ki Aliyu, ki yafe mana" Ummul tai murmushi ta ce "Barrister Maryam za ki bawa haƙuri ita ce uwar Malam, kawai zan nemi Alfarmar ya bini zuwa wajan ka kanin shi" Umma A'isha zatai mgn Abba Hakimi ya ɗaga mata hannu ya ce
"Allah ya tsare"
Ummul tabi bayan Yaa Sheikh suka fita, ita ke driving shi yana gefen mai zaman banza, ba tare da sanin su Abba Hakimi sun biyo bayansu ba. A haka suka shiga cikin asibitin lokaci guda motocinsu sukai parking, har kawo lokacin ba a gane halin da Yaa Sheikh ke ciki, bada kowa yake haɗa idanu ba kuma yaƙi cewa komai akan al'amarin. Kai tsaye office ɗin Dr ya nufa yana gaba Ummul na bayan shi, Dr ya miƙe yana miƙawa Yaa Sheikh cike da martabawa suka zauna Ummul ce ta samu ƙarfin gwiwar cewa
"Meke faruwa Dr?"
Dr ya zare Glasses ɗin idanunsa ya ce.
"Ta farka, ba wani ciwo dake damunta sai babban ciwon daya gama lalata kwakwalwarta" da sauri Ummul ta ce.
"Meke faruwa? Kayi magana kai tsaye" Ya zaro File ɗin Halisa da wani X-ray ya miƙawa Yaa Sheikh
"Nasan zaka fahimta"
Zuciyar Yaa Sheikh ta buga file ɗin ya nemi kwace masa, Ummul tayi saurin riƙe hannun shi tana faɗin "Be careful Arɗo" a fili cikin muryar fargaba ya ce.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Losing memory?"
Dr ya ce "Haka binciken ya nuna" Ummul wacce ta lura da rikicewar Yaa Sheikh ta matsa kusa da shi tana bashi side hug ta ce "Memory? Like how" Dr ya danna system ɗin gabansa tare da juyawa Ummul ya ce
"Memory loss is unusual forgetfulness. You may not be able to remember new events, recall one or more memories of the past, or both. The memory loss may be for a short time and then resolve (transient). Or, it may not go away, and, depending on the cause, it can get worse over time" Ya ƙara danno waje tare da nuna mata wani waje, kafin ya ce.
"Ta samu Short-term memory loss. Short-term memory loss is when you forget things that have happened recently, such as an event or something you did, saw, or heard. It can be caused by a number of factors, including a nutritional deficiency, sleep deprivation, depression, side effects of some medications, or dementia"
Ummul ta ce
"What causes short time memory loss? Dr" ta faɗa she's still holding onto him, ganin har yanzu Yaa Sheikh ɗin ya kasa cewa komai, Dr ya ce.
"Possible causes of reversible memory loss include:
Medications. Certain medications or a combination of medications can cause forgetfulness or confusion.
Minor head trauma or injury.
Emotional disorders.
Alcoholism.
Vitamin B-12 deficiency.
Hypothyroidism.
Brain diseases.
Sleep Apnea. Ita ta samu dalilin Trauma"
Yanayin Ummul duk ya sauya ta ce
"Zamu iya ganinta?" Ya ce "Sure" Yaa Sheikh ya juya tare da zare jikinsa daga na Ummul ya fita.
Dr ya bi bayan shi, haka Ummul ma.
A ƙofar Room ɗin suka samu Dada da Mai martaba sai Mother duk suna tsaye, Yaa Sheikh bai ce komai ba ya buɗe ƙofar Room ya shiga.
Tana zaune ta jingina jikin gadon idanunta rufe, da sauri ta buɗe idanunta jin motsi kamar mai tsoron ganin wanda ya shigo haka ta dinga ɗaga lashes ɗin idanunta slowly slowly.
Idanunta ya sauka akan Yaa Sheikh ta ƙura masa idanu, shi ma ita ɗin yake kallo ita kuma kallon sabon mutum take masa a sabuwar duniyar data tsinci kanta.
Ummul ta shigo ita ma
"Sannu Daughter"
Tana sauke maganarta Halisa ta ce
"Sannu Daughter"
Ummul ta kalli Dr ta kalli Yaa Sheikh wanda yake ta kallon Matar Malam.
"Ya jikin naki?" Cewar Ummul da sauri ita ma Halisa ta ce
"Ya jikin naki?" Kan Ummul ya ɗaure sosai ta juya zuwa waje ba jimawa ta dawo ita da Dada ta ce "Daughter kin gane wannan?" Ta ƙara faɗar the same words ɗin da Ummul ta ce.
Tuni idanun Dada ya cika da hawaye ta ce
"Danejo baki gane Dadarki ba?" With Emotional kamar yadda Dada tai magana Halisa ta ce "Danejo baki gane Dadarki ba?" Ummul ta dafe kai ta ce
"What are the symptoms of short-term memory loss?" A take ya ce
"asking the same questions repeatedly.
forgetting where you just put something.
forgetting recent events.
forgetting something you saw or read recently"
Mai martaba ya ce
"Ya Salam, ƙaddara data samu Princess kenan?" Dada ta fashe da kuka tana faɗin.
"Your highness Halisa ta mantani" Ya riƙe ta yana bubbuga bayanta trying to calm

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login