Showing 141001 words to 144000 words out of 197828 words

Chapter 48 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9326

ce "Ummul kai na ke ciwo sosai, na ji ba zan iya cin wainar ba"
Ummul tai murmushi kawai ita ma ta nuna kamar ba komai ɗin ta ce
"Daughter baki dai na kukan ciwo ba, jeki kwanta to" ta kasa cewa komai sai naɗe ƙafa da tayi kawai Ummul ta koma ta zauna, Maimoon kuka ta ɗauke wainar ta fara ci. "Alhaji Farouk ban fahimci zan can ka ba?"
Ya numfasa ya ce
"Ina nufin ki yarjewa Yaa Sheikh ya auri ƴata Zahrah a karo na farko, ciwon zuciya ne ya kamata,kuma tana matakin ƙarshe don Allah kada soyayyar ɗanki tayi silar mutuwar tilon ƴata da nake da ita a duniya"
A wannan karan Halisa zama tayi kamar zararriyya duk sukai banza da ita, idan ta kalli Yaa Sheikh sai taga idanunsa rufe, tana ɗauke idanu yake buɗe na shi ya kafeta da jirkitattun idanunsa masu ɗauke da wutar sonta kamar rai da Ajali.
Ummul ta ce "Da zan yi taking revenge akan Zahrah da tuni nayi, kawai bata gabana bata kai na tsaya ɗaukan hukunci kan ta ba, nasha ganin cases kala-kala, bayan kasancewa police ina aiki da hukumar NASA tare da CVI, ina son ka ɗauki wannan matsayin ƙaddara, wanda kuma ance cikar imanin mutum shi ne yarda da ƙaddara, idan ni zan saka Arɗo ya auri Zahrah to har abada ba zan sahale masa ba, domin babu kyautatuwar hakan, dubi abin da ya faru tsakaninta da wanda ya raini Aliyu, amma idan har shi Aliyu ya amince zai aureta to gaka ga shi nan, ba zan hana shi aure ba, domin Ubangiji ya umarci maza da auren mace sama da ɗaya har zuwa huɗu, idan kuma ba zai iya adalci ba, ya auri ɗaya domin ita ce mafi a'ala a gare shi"
Umar-khan da Maimoon hadda ita Halisa suka kalli Yaa Sheikh suna jiran jin abin da zai ce
Alhaji Farouk ya ce
"Ka taimaki addinin Musulunci, ka auri Zahrah ka ɗauka jahadi kayi,ina iya yin komai domin ganin ka amince" ya shiga ƙoƙarin durƙosawa gaban Yaa Sheikh, Yaa Sheikh ya yi saurin kama hannayen Alhaji Farouk ya ce.
"إِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تُقْسِطُواْ فِى ٱلْيَتَٰمَىٰ
فَٱنكِحُواْ مَا طَابَ لَكُم مِّنَ ٱلنِّسَآءِ مَثْنَىٰ وَثُلَٰثَ وَرُبَٰعَ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُواْ فَوَٰحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَٰنُكُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰٓ أَلَّا تَعُولُواْ"
Yaa Sheikh ya dubi Alhaji Farouk da kyau ya ce "Dalilin da suke sakawa mutum ya ƙara aure na da yawa, akwai rashin samun mace ta gari, akwai rashin kwanciyar hankalin iyali, akwai rashin gamsuwa da iyali, sai ka ƙara aure idan kaga da cutuwa" ya yi jim kafin ya miƙe tsaye ya ce
"Wani matar shi ke buƙatar hakan, akan sake da damar ta, taji yana iƙirarin IDAN BA KE amma ai ba ita ɗaya ba ce a duniyar ko? Wani ƙazamar mace ya haɗu da ita, wani kuma ya bi kyau wajan auren daga baya fahimci kyan yana gushewa ba kuma shi ne fa'ida ba, shi ya sa Manzon Sallallahu alaihi Wasallama ya ce "Mafi cancantar aure shi ne, wacce zaku aura dan nagarta,ko nasaba mafi alheri ita ce mai addini, a wannan gaɓar na amince da auren Zahrah matsayin nagartar da ka ke da ita, ina fatan zata zama macen rufin asiri"
Maganar ba iya Halisa ba, har Ummul sai ta daka, tasan da biyun yake maganar amma batun amincewa auren fa? Halisa daɓas! Ta yi Idanunta ƙurr a gefe guda ta ka ɗaita a zuciyarta tana auna zantukan Yaa Sheikh.
Alhaji Farouk hawayen farin ciki ya sakko masa ya riƙe hannun Yaa Sheikh ya ce "Na gode, Na gode Allah ya saka da alheri Malam, Allah ya jiƙan magabata" suka jere har waje, suna fita Yaa Sheikh ya dakata tare da fara yiwa Alhaji Farouk magana mai muhimmanci, cike da farsaba da lafazi mai daɗi. Halisa ta rarrafa da ƙyar tare da shigewa wani bedroom tana zuwa tasa key ta murza ta zube a gado tana rusa kukan rashin makama da abin yi, ta rasa abin da ya sanya take kukan kawai ta ji ba zata iya bari ya wulakanta ta ba, bayan da auren shi a kanta, inma zai auren ya tabbatar ya bata divorce paper ɗin ta.
Wayarta ta ɗauka ta shiga kiran Dr A'isha tana ɗauka ta fashe da kuka ta ce "Na shiga uku Adda A'isha zuciyata zata buga" Dr A'isha ta ce
"Kin san bugawar zuciya kowa? Meke faruwa ma tukun?" Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Abbana aure zai yi, kuma Zahrah zai aura" Dr A'isha ta rusa wata ashar ta ce
"Kut wannan zance ne, This is something that will never happen, ƴar iskar yarinyar zai haɗa muku shimfiɗa, da ita?" Kukan Halisa ya ƙaro sosai fiye da kima ta ce
"Allah ni ya bani takardar sakina na ji bana son zama da shi ɗin" Dr A'isha ta ce "Oh no dear, ba haka za ai ba, dole shi zai nemeki da kansa, kada ki taɓa yarda da cewa kin masa laifi kuma ki basa haƙuri, har abada shi zai na baki haƙuri ke macace ke ce wacace ki ke da abin bashi, ina ƙara jan kunnenki kada ki kuskura ki bashi damar da zai riƙe koda hannunki ne, ki jan shi a ƙasa ya zo har inda ki ke"
Halisa ta yi sak a lokacin tana jin kamar ba daidai bane wannan zan can na Dr A'isha ta ce "Abbana zan ja a ƙasa? Babbane fa kuma Malami" Dr A'isha ta ja tsaki ta ce
"Mtwss ji shirme ko? Shi namiji ba ruwan shi, duk girman shi, duk maluntar shi akan wannan abin dake wajan mace sai ya zama yaro ƙarami saboda da maita, da zarar abin da suke kwaɗayi ya tsofa sai su fara tunanin hanyar da zasu bi su ƙara aure domin ya yin ta gida ya kau, kuma ai laifin na shi ki nuna da gaske bakya ra'ayin shi takardar saki kawai ki ke ya baki"
Nan da nan Dr A'isha ta ƙarasa kurɓata raguwar tunanin ƙaramar kwakwalwar Halisa a sanyaye ta ce "Thank you, I'll try my best ganin nai haka" sukai Sallama daga nan Halisa ta kunna network ta shiga WhatsApp kai tsaye grp ɗin MU MA MATA NE ta shiga bayan ta yi sallama ta ce "Don Allah ƴan uwana mata ga muhawara" kasancewar yamma ce ya sa duk manyan matan suna online suka shiga faɗin.
"Muna ji"
Ta ce "Kana da miji, yana son ka, so irin na mutuwa, sai saɓani ya haɗaku akan ba zaka je kaga dangin mahaifinka ba, bayan tun da aka haifeka baka taɓa ganinsu ba, kuma su ne farin cikin ka, har ya furta cewa idan har ta je to ya yanke auren dake tsakaninsu, ita kuma bata je amma ta dage sai ya saketa, ya bata haƙuri amma taƙi gashi yanzu aure yake shirin ƙarawa, shi ɗin mabuƙaci bashi da haƙuri akan abin da ya ke, don Allah idan ke ce ya zaki?"
Da wata number mai username ɗin: Akeela Mrs Akeem. Aka ce _Shir me kawai_
Wata babbar mace harta shige Maganar sai ta dawo ta fara typing ta ce
"Kai tsaye zan iya cewa mahaukaciya ce, kuma In sha Allah sai ya ƙara aure,mata wani lokacin basu da tunani" Akeela ta tura emoji na dry tare da yin reply akan maganar Sarah ta ce
Akeela😂🤦🏻‍♀️Sarah Mrs Abeedeen Abdul-jabbar Abas wannan ba yi ba ne gasky, idan kuma matsalar ta Halisa ce fa?" Sarah bata bada amsa ba, sai wata mai suna Julde ce ta ce
Julde: Ta yi kuskure gasky, ni ma haka na tafka wannan kuskuren har mijina Abu-maleek ya fara masturbation, shi namiji ba a hukunta shi da Wannan akwai hanyoyi na hukunta miji banda wannan, ni ma dai zan so ya ƙara auren ƴar banza taci malafar gidansu"
Sarah: ta ce "Bari kawai Julde, ita Halisa ai ba zata aikata haka ba, mijinta ba shi ne babban malamin nan ba?"
Da sauri Halisa ta fara typing ta ce.
"Laa Wallahi ba ni ba ce, kawai a wani grp na gani shi ne na yi sharing da ku" maganar tai girma aka fara tafka muhawara mai zafi wasu su tsinewa Halisa ba tare da sun sani ba, wasu kuma su goya mata baya akan ƴan uwa su ne komai, miji zai iya barinka banda ƴan uwa. Jiki ba ƙwari tai Offline tana sakin wani sabon kukan a haka har barci ya ɗauke ta.
Bayan sallar magriba Yaa Sheikh na zaune a wani haɗaɗɗan parlourn gidansu Ummul da ƙyar ya iya shanye kunun gyaɗar da tayi masa, he lost his appetite.
A karo na farko da Ummul ta ce "Yaa Sheikh wannan kasa dace, auren Zahrah?" Ya kalleta idanunsa na rufewa ya rame sosai ya ce "Ya zan Ummul?ke ma kin goya mata baya" Ummul ta ce
"Ba baya na goya mata ba, kai na haifa ba ita ba, babu yadda za ai na tilasta Halisa ta dawo wajanka za taga kamar don kai na haifa ba ita ba, zan ƙara faɗa maka kayi kuskure daka hana ta tafiya da kuma furucin da kayi shi ne ta riƙe a ranta har haka" ta jina kai yana son amsar laifin shi ko ta halin ƙaƙa kafin a raunace ya ce
"Ban hanata da wani dalili ba Ummul, ina son na zama ni ne silar zuwanta gare su, na kasa jure yadda ake mini hawan ƙawara, ita ɗin ƴar gata ce, tana da Abba, Dada, grandparents ɗinta they are still alive, tana da yaya uwa ɗaya uba ɗaya, she have a siblings kamar su Khalil Maimoon, ni fa? Ke ɗaya nake da ita, Zawja kawai nake gani a idanuna bayanke.." Ummul tai ƙasa da kanta she was trying to hide her tears
Sarai ya fahimci me take don haka ya miƙe tsaye zai fita tayi saurin miƙewa ta riƙe hannunshi ta ce "Idan auren Zahrah kana ji shi ne mafita, kuma shi ne tubalin da zai dawo maka da wacce zuciyarka ta buɗe ido a sonta kayi haka, bana son ka auri sbd ba zaka iya adalci ba, kuma kafi kowa sanin hukuncin hakan, ni ɗin dana rage maka na ɗauki nauyin Uwa, Uba, ƴan uwa a gare ka Aliyu, ka lalace sbd mace ka fita hayyacinka bana son ganinka haka, kada ka sake naji labarin ka ɗauki azumi gobe" ganin Ummul na shirin kukan da gaske muryarta na rawa sosai ya shige Jikinta ya rungometa ya ce "Ba zan ba Ummul, amma sai na fi azabtuwa idan har ban azumi ba" ta rungume shi tana shafa kan shi ta ce "Akwai Allah Arɗo, lokaci ya yi da zaka koma Rugar Bello ka amshi kujerar mahaifinka ka gana da ƴan uwanka na can" ya jinjina mata kai ya ce.
"Ina shirye-shiryen tafiya aikin hajji, zan fara zuwa Yola ta can sai na shi ge, bana son a sanar da Zawja zan yi tafiya ko barta karatu ne na sahale mata tayi zan yi haji daga gare ta" Ummul ta sake shi ta ce "Haji kuma?" Ya lumshe idanunsa ya ce
"Koyarwar Annabi ne, lokacin da matansa suka ɓata masa rai sai ya tattara kayan shi yabar gidan tsayin kwana 40 zuwa arba'in da wani abu"
A nan bedroom ɗin Ummul ya kwanta bayan yaje wajan dattijo kan shi a cinyarta tana shafawa tun yana magana a hankali har barci ya ɗauke shi. Ta ƙora masa idanu babu abin da ya bari na mahaifin shi,komai ya ɗauke haƙuri da sanyin hali, da kuma kafiya a soyayya
ta ajjiye kan shi saman pillow kana ta fita, cikin dare kamar haɗin baki wajan ƙarfe 3 suka buɗe ƙofa dake duk gidan Ummul ɗin suka kwana ba tare da sanin junansu ba, karon dasu ka yi ya sa Yaa Sheikh ya ɗan ja baya ita kuma ta yi baya zata faɗi sbd tsoro ya saka hannu ya riƙeta tare da dawo da ita dab da shi, suka kalli juna ya zame zai bar wajan tayi saurin shan gabansa kamar yanzu ne komai ke faru ko sunan Zahrah bata ƙaunar a ambata ta ce "Kabani takarda ta" ya harɗe hannu a ƙirji sosai yana ƙare mata kallo bai ce komai ba, bai kuma raɓi inda take ba ta fashe da kukan rainin hankalin shi gabaɗaya tayi kan shi tana zuwa ta faɗa jikinsa tare da zagaye hannayenta a ƙugun shi ta fasa wani irin ihu tana ƙanƙame shi ta ce "Wallahi babu inda zaka sai ka sakeni ba zan ƙara zaman aure da kai ba kona kwana ɗaya....






*Kada ku manta sunan Littafin IDAN BA KE masu cewa labari ya ƙare kawai ja nake you're guys are mistaken.. ni ma ɗin ai na fi na gama ko? Sbd na samu peace of mind na samu cikakken hutu kafin Allah ya a haɗamu a wani bayan Ramadan. Burina kuna karatun da idanun basira, kuna hango daidai da kuskuren dake cikinsa ba wai kawai nishaɗi ba ya haka ne zan fahimci nawa kuskuren..... Mata masu ɗaukan shawarar ko wanne mutane a kiyaye wata shawarar mugunta ce, kuma ba don Allah ake baka ita ba, sadaukarwa ga masu ƙaramin tunani irin na Halisa.https://vm.tiktok.com/ZMYeKp4XV/
Follow my account👆🏾 comment, like, share❤️🫶🏼💋


Yaa Sheikh ya riƙe kan shi daga rungumar da tayi masa, ya rufe idanu yana sauke numfashi a hankali, ji ya yi komai na shi ya sauka daga kan setting, duk yadda gangar jikinsa da zuciyar dake ɗauke da sabon son matar malam a kullum sukai kewar Jikinta, muryar, rigimarta haka ya kame kan shi ba tare da nuna cewa da gaske ya azabtu da rashinta kusa da shi, ya shirya nuna mata ita ɗin kawai ya ke so, ba wani abu data mallaka daga baya ba, zai tabbatar sai ta neme shi da kanta.
"Ba zan zauna da kai ba, bana son ka Yaa Sheikh tun da bani ka ke so ba, ba farin cikina ka ke so ba, gangar jikina ka ke muradi"
Har lokacin tana riƙe da shi tana kuka kamar ranta zai fita, abu biyu ke mata zafi da ƙona a zuciyarta, yadda ya amince da batun auren Zahrah wanda ko a mafarki bata yarda cewa zai iya ƙara wani auren ba, balle ta yi tunanin zai auri wata aba wai Zahrah? Raguwar maza da raguwar mariƙin daya riƙe Yaa Sheikh ɗin Matsayin ɗan cikin shi, shi ne yanzu ya amince ya amshi raguwar mahaifin shi.
Ya ware idanunsa akanta cikin rashin son magana mai tsayi ya ce.
"Sake ni Matar Malam!"
Tayi saurin sakin shi domin tama manta ta riƙe shin. Ta ce "Ai dan ban sani ba, kasan ba zan taɓa riƙe jikin ka ba"
Ya jinjina mata kai kawai tare da juyawa a zuciyar shi ya ce "Matar da duk ita ta lalata dani, da ban ɗanɗani zaƙin ba ina zan damu, ina ganin shaiɗan cin mace ni Aliyu"
"Don Allah ka sake ni, zuciyata bugawa zatai muddin naci gaba da sanya ka cikin idanuna matsayin mijin dake aurena, kaje can ka auri raguwar uban riƙon ka"
A wannan karan ya kasa shanye maganganun Halisa, yadda take fidda zance kamar wacce aka zaunar tare da yi mata huɗuba. Ya juya bakiɗaya zuwa inda take fuskar shi tayi jajir alamar wannan shi ne karan farko da ranshi ya ɓaci da maganganunta, tai tsaye zuciyarta na bugawa tare da harbawa ganin yadda ya yo kanta babu wasa akan fuskar shi, sai tsoro ya kamata.
Yana zuwa ya yi mata rumfa zata ja baya ya saka hannu ya damƙo ƙugunta tare da jawota ya mannata da na shi ƙugun, ta lumshe ido tana fidda numfashi, sbd wani abu daya shiga yi mata yawo mai kama da feelings. Ta nemi ƙwace kanta domin iya turaren rojan daya kama cika ɗakin kaɗai ya isa ya sauya mata lissafi balle kuma yanzu da ƙugunsu dake manne, kwantaccen gemun shi mai laushi kwance a wuyanta yana shafa mata, yanayinta ya sauya ta kasa motsi a hankali cikin nutsuwa yana mai ƙara fahimtar yanayin nata saɓanin ita da bata ga sauyi ko guda tattare da shi ba,
Ya goga mata tsinin hancinsa a fatar wuyanta yana nai fesa mata zazzafan numfashi mai ɗauke ƙamshin mouth mint chocolate freshener, ta buɗe ido da ƙyar wanda suka jirkita ta sanya cikin nasa idon kamar yadda yake kallonta. Ya zura hannunsa ta ƙasan ƴar rigar barcin dake cikinta, ya ɗora tafin hannun a saman cikinta ta wajan mara, a hankali yaja ido tare da rufewa numfashinsa ya ɗauke na wani lokaci sbd ɗumin cikinta daya ratsa hannunsa, wata Soyayyar uba da ɗan shi ta bijirowa Yaa Sheikh, ƙaunar abin da ke cikin Halisa ya mamaye dukkan ƙofofin dake zuciyar shi, ɗiya maca ce? Ɗa namiji ne bai sani ba, amma son ko wanne jikinsa ya kama Yaa Sheikh, tare da son uwar Unborn ɗin na shi.
Nan da nan Halisa ta birkice ta nemi nutsuwarta ta rasa, bakin neman sakin ya yi shiru ji take tamkar ya jata ya rungome, a zame jikinsa ka ɗan tare da zamewa ya tsuguna akan qwiwoyin shi nutse cikin wani mataccen yanayi duk da yana riƙe kan shi ya ɗora bakinsa a mararta tare da sumbata, wajan zame bakinsa ya sakar mata wani kyakkyawan kisses wanda ya sanya tai saurin kama sumar kan shi, ya dinga addu'a yana tofawa a cikin kafin ya miƙe tsaye, yana miƙewa tayo jikinsa zata rungome ya ja baya yana faɗin "Ki ke cewa me?" Ya faɗa a gajiye yana jan gemunsa, Baƙin ciki da takaicin ya cika ta ya kunna ta da ashana tare da sanya fetur ciki, amma ya barta ita ɗaya tana ƙona kanta.
Zafi biyu! Ya ƙaro da ƙyar take buɗe ido ta ce
"Nace bana son ka Aliyu!"
"Aliyu?" Ya maimaita a zuciyar shi. Is that true ƴar fillon shi ke kiran shi da sunan da ko Abba Hakimi baya faɗa sbd girmama ilimin Ubangiji? Amma ƴar cikin shi ta faɗa gatsal! Hankali kwance. Ta ƙara cewa
"Kaje ka auri karuwar uban riƙon naka, ka ɗora daga inda ya tsaya"
Da ace Yaa Sheikh na cikin tsarin maza masu dokan matayensu, da babu shakka sai ya lakaɗawa Halisa mugun doka wanda zai dawo da ita daga haukan daya sameta, ya juya yana sauke numfashi har zuciyar shi ta samu nutsuwa daga zafin da tayi dalilin ambaton sunan Allah.
Murya can ƙasa irin ta marasa lafiya ɗin nan ya ce "Zan baki, ki tuna mini zuwa safiya" yai shiru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login