Showing 192001 words to 195000 words out of 197828 words

Chapter 65 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9297

bai ce komai ya lura rigima take ji.
Ta ce "Ni dai duk ƴar iskar da take kula mini miji wallahi ban yafe ba" nan ma yaƙi kulata sai kawai ta fashe da kuka sosai ta ce "Ka auri Zahrah ban sani ba, shi ne yanzu wata banza can Dr A'isha take kulaka bayan da nata miji"
Shi abin dry ya bashi ya kwantar da Hala a gefensa ya saka hannu ya damƙo Halisa tayi ƙara ya jawota da ƙarfi ya matseta a jikinsa idanunsa rufe ya fara farke wuyan rigar Jikinta ya ce "Yarinya tsiwa ki ke ji ko?" Ta girgiza kai ta ce
"Ni fa bance komai ba"
Idanunsa ya yi jajir ya rufe bakinta ta hanyar zura nasa ciki ɗif tayi kisses ɗin bakinta yake kamar zautacce kana ganinsa kasan daman ya jima haƙuri kawai yake sai daya gama huɗu mata jiki tun kafin aje babban masauki ta fara ƙoƙarin guduwa kullum ji take kamar ana ƙarawa Abban nata ƙarfi ya miƙe yana cire Jallabiya tare da ɗaukan Hala wacce ke tsotsar hannu bata san duniyar sharholiyyar da ake ba, ya kwantar da ita akan bed ɗin kana ya sunkuci Halisa har tsakiyar gadonta....
Washegari da safe suna zaune suna breakfast Jadda sai kwasar farfesu take Yaa Sheikh a hankali yake shan kunun gyaɗar dake masa daɗi wanda indai bashi ya sha da safe ba baya jin daɗi.
Halisa ta kasa haƙuri ta ce "Abba" ya ɗago gajiyayyun Idanunsa ya watsa mata ta ce
"Sau biyu ina zuwa duba Zahrah ina ganin part ɗin a rufe fatan lafiya?"
Jadda ta ce "Ban taɓa ganin yadda kishiya ke damuwa da kishiya ba sai a wannan gidan kamar wanda aka haifa ciki ɗaya" Yaa Sheikh ya yi shiru sbd ba ɗabi'ar shi bace yin magana idan yana cin abinci gabaɗaya yanzu ne ma bakin nasa ya buɗe. "Modibbo"
Ya ajjiye cup ɗin hannunsa tare da ɗaukan tissue ya goge bakinsa cikin kamala ya ce
"Zan duba" "Wanne dubawa gata nan ta fito, ke ƴar nan lafiya? Wanna akwatin fa" Halisa ta miƙe tsaye ganin Zahrah janye da manyan akwati ta dinga dubanta ta ce
"Tafiya zaki ne" tayi murmushi ta ce "Eh" ta ƙara duba akwatin ta ce
"To ina zaki har haka kayan nan sun yi yawa fa" "Tafiyar har abada"
Halisa ta kalli Yaa Sheikh da yake kallon Zahrah kenan taji me suka faɗa jiya? "Abba me yake faruwa ne, ina Zahrah zata?" Zahrah ta ce
"Zan bar miki mijinki ne Halisa" a ruɗe ta ce
"To amma ai bance wani abu ba, babu abinda ya haɗa mu" "Ƙaddara ta haɗa Halisa, kuma ita zata raba yanzu"
Hawayen da take ɓoyewa ta zube gaban Yaa ta saki wani irin kuka ta ce
"Ina son ka Aliyu, ina son Yaa Sheikh son ni kai na ban san adadin shi ba, wlh idan zan kwana na yini ban isa na faɗa abinda na keji a raina ba, duk mijin da zan aura ba zan iya yi masa biyayya ba zan zauna da igiyar auren wani amma soyayyarka ce a raina, don Allah don Annabi ka bani takardar saki,ka sakeni don Allah kamar yadda Ummul ta buƙata"
Halisa ta riƙe Yaa Sheikh tana girgiza kai cikin kuka sosai ta ce
"Kada ka saketa Abba, kada rabamu Abba ina son ta ina son zama da ita don Allah Habibi kada ka saki Zahrah I'll talk to her" Yaa Sheikh ya rasa ta ina zai fara ya saka hannu ya ɗago Zahrah idanunsa sunyi jajir Zahrah kuka Halisa kuka, Jadda na gefe tana zare idanu. A hankali ya tallafo fuskarta Zahrah yana kuma riƙe da Halisa ya ce "Ko wanne bawa akwai ƙaddarar shi, kada ki sare ina son zama dake, Ummul na son ki zauna dani amma zamu cutar da ke"
Ya yi shiru ya ce "Wani sirrin idan Allah ya ɓoye zai fi kyau a rufe babu buƙatar faɗa, ina jinki har raina wani abun ba alheri bane a rayuwarmu amma idanunmu su rufe ki koma ga Allah, zai baki miji wanda ya fini"
Tayi murmushi amma wani irin zafi zuciyarta ke mata ta ce "Na fahimta, amma a ko wanne zuciyata zata iya bugawa kawo yanzu nasan ciwo ya gama lalata zuciyata, Alfarma ɗaya nake so kayi mini" Ya riƙe fuskarta ya ce "Me kike so Fatymerh Zahrah?"
"Sau ɗaya kawai, sau ɗaya kiss me hug me as goodbye" Halisa ta runtse idanunta a hankali ta sulale tabar wajan Jadda tuni tayi waje tana bawa maids ɗin gidan labari. Ya dubeta ta ce
"Please kiss me, please Yaa Sheikh kiss me....




08119237616Kamata Yaa Sheikh ya yi ya riƙe And he gave her a nice little kiss, some minutes ya zareta jikinsa numfashinta har riƙewa yake sbd yadda ƙamshin Roja ya shiga hancinta a ƴan minutes ɗin da tayi a jikinsa ji tayi komai ya tsaya mata. Ya kama hannunta zuwa waje can compound Jadda na ganinsu tayi ƙasa da murya ta kalli mai bawa flowers ruwa cikin nutsuwa ta ce
"To ita wannan lokacin ita ce mai jawo manyan akwatinan tana cewa a saketa, ɗayar kuma zaka ganta kamar zabiya don fari mai ƴar jaririya ita ce take kukan kada ya saketa fa" Shi dai kallonta yake ta ƙara karkacewa tana ƙasa da murya ta ce
"Duk yadda akai ta fahimci baya son ta ne, shi kuma kasan miskilanci gare shi ba zai taɓa cewa komai ba, jiya fa suka dawo daga Madina ina kyautata zaton ya ƙara sakar mata wani cikin ne domin farin nata bana lafiya ne ba"
Duk abinda take faɗa kai tsaye yake shigewa kunnen Yaa Sheikh ko inda take bai kalla ba, ya nufi motar shi mai baƙin glasses ya buɗewa Zahrah ya fahimci bata hayyacinta.
Tana shiga ya saka aka zuba kayanta a bayan mota shi kuma ya shiga mazaunin driver.
Cikin nutsuwa yake driving yana jin yadda take kuka amma ya kasa cewa komai, kukan shi ne sauƙi ga zuciyarta.
Dab da gidan Abba Hakimi ya gangara gefen titi tare da yin parking ya kashe motar, ya sauke numfashi cikin kulawa da son kwantar mata da hankali ya ce
"Stop crying Fatymerh Zahrah!" Ta kalle shi ta ce "Me ya sa? Ban san ranata da daina kuka ba Yaa Sheikh naso na ƙare rayuwata ne bakiɗaya da kai kuda baka kusanci inda nake ba"
Ya kalleta da kyau baya son bayyana sirrin shi ga kowa kamar yadda ya riƙe sirrinta ga matar shi Halisa har yanzu bata san bai kusanci Zahrah ba, ya ƙudiri niyyar ba zata sani ba ɗin.
"Ki ɗauka hukunci ne daga Ubangiji, kada ki yarda zuciya ta ɗebeki yarda da ƙaddara Zahrah"
Ta jinjina kai ta ce
"I believed in fate, but my destiny is too hard My heart aches and I want to die and rest in this life"
"Come here" ta ƙarasa kusa da shi very close to him. Ya riƙeta ya ce
"Repeat after me"
Ta jinjina kai, tana share Hawayen Idanunta amma kukan yaƙi tsayawa. Yaa Sheikh was speechless sun jima a haka kafin cikin nutsuwa yana riƙe kan shi ya ce
"ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﻋَﺒْﺪُﻙَ، ﺍﺑْﻦُ ﻋَﺒْﺪِﻙَ، ﺍﺑْﻦُ ﺃَﻣَﺘِﻚَ، ﻧَﺎﺻِﻴَﺘِﻲ ﺑِﻴَﺪِﻙَ، ﻣَﺎﺽٍ ﻓِﻲَّ ﺣُﻜْﻤُﻚَ، ﻋَﺪْﻝٌ ﻓِﻲَّ ﻗَﻀَﺎﺅُﻙَ، ﺃَﺳْﺄَﻟُﻚَ ﺑِﻜُﻞِّ ﺍﺳْﻢٍ ﻫُﻮَ ﻟَﻚَ ﺳَﻤَّﻴْﺖَ ﺑِﻪِ ﻧَﻔْﺴَﻚَ، ﺃَﻭْ ﺃَﻧْﺰَﻟْﺘَﻪُ ﻓِﻲ ﻛِﺘَﺎﺑِﻚَ، ﺃَﻭْ ﻋَﻠَّﻤْﺘَﻪُ ﺃَﺣَﺪًﺍ ﻣِﻦْ ﺧَﻠْﻘِﻚَ، ﺃَﻭِ ﺍﺳْﺘَﺄْﺛَﺮْﺕَ ﺑِﻪِ ﻓِﻲ ﻋِﻠْﻢِ ﺍﻟْﻐَﻴْﺐِ ﻋِﻨْﺪَﻙَ، ﺃَﻥْ ﺗَﺠْﻌَﻞَ ﺍﻟْﻘُﺮْﺁﻥَ ﺭَﺑِﻴﻊَ ﻗَﻠْﺒِﻲ، ﻭَﻧُﻮﺭَ ﺻَﺪْﺭِﻱ، ﻭَﺟَﻠَﺎﺀَ ﺣُﺰْﻧِﻲ، ﻭَﺫَﻫَﺎﺏَ ﻫَﻤِّﻲ”
Yana faɗa tana faɗa ta sauke numfashi cikin nutsuwa ta ce "Thank you" "No!" Ta dube shi cikin rashin fahimta ya ɗauke idanu ya ce
"I have to thank you, for understanding me" kamar anyi forcing nasa to talk ya ce.
"Yola?" Ta jinjina masa sai kuma ta ce "Eh gida zani, nama ji Daddy ya sai da gidan"
"Zaki amince dani? Na aurar dake?" Tayi ƙasa da kanta kafin ta ce
"Zan so na baka wannan damar, amma ba zan sake aure ba. *NA GAMA AURE* zan riƙe yarona Muhammad In sha Allah zuwa sanda Ubangiji zai amshi rayuwata" maganar ya shiga Yaa Sheikh.
Sai kawai ya yi shiru tare da yiwa motar key ya nufi gidan Abba Hakimi, Umma A'isha ta nuna Zahrah ɗaki kafin gobe ta shige Yola, Yaa Sheikh ya zauna wajan Abba Hakimi suka ɗan tattauna da har Umar-khan ya shigo shi da Hafsat dake laulayi tana ganin Abban nata Yaa Sheikh ta sunkuya ta gaishe shi kai kawai ya jinjina mata. Abba Hakimi da yake matsayin suriki ya ce "Hasfat Sheikh Aliyu fatan lafiya kuke?" Ta sunkuyar da kanta ta ce "Lafiya lou Abba" Yaa Sheikh yana gidan har sallar Issha suna ta magana da Abba Hakimi can kuma Abba Hakimi ya kira wani a waya. Zahrah ta kalli Abba Hakimi dake cewa.
"Kiyi haƙuri amma na biye Malam ina da yaƙinin ya yi miki zaɓi na alheri ki amince, an ɗaura aurenki da Saifuddeen ga sadakin ki" Idanunta ya cika da hawaye ta ce
"Ba komai Abba, Yaa Sheikh ya yi mini komai yasa na san wace ni ya bani ilimi sanadin shi na zama mace komar kowa Allah yasa zaɓin shi ne ya zama alheri a gare ni" Abba Hakimi ya miƙe yana faɗin "Allah ya yi miki Albarka Zahrah, mun yi magana da Alhaji Farouk mahaifinki ya amince idan ba damuwa ba sai kin koma ba za a kawo miki Muhammad ɗin"
Tayi godiya Yaa Sheikh miƙe yasan kawo yanzu Halisa hankalinta ya ta shi ta ce "Na gode sosai"
Yana yin waje abin shi ya ce "Ki ɗauke ni like a brother to you komai ki ke so come to me, happy marriage life" ya yi waje abin shi ta bisa da kallo zuciyarta nayin wani zafi. Lokacin daya isa gida Jadda ta jima da yin barci, direct part ɗinsa ya nufa ya cire Jallabiya ya yi wanka ya sauya kaya zuwa white Pajamas riga da wanda sai ƙamshin Roja yake yana jin zuciyarsa ta rage nauyi sbd hakƙin Zahrah daya sauke, daman bata da iddar shi wannan dalilin ya sanya ya ɗaura mata aure da Saifuddeen wanda shi da kan shi ya amince. Steps ɗin benen yake takawa zuwa downstairs a haka ya nufi part ɗin Madam Halisa ya murɗa handle bakin shi ɗauke da sallama, bashi da tabbacin tana parlour sai ta shige bedroom ya sameta tsaye gaban wardrobe,tana ƙoƙarin sanya night gown cak taji an ɗage ta sama, ta zaro kumburarrun Idanunta waje ta ce
"Habibi kaya zan saka" yana kwantar da ita tare da rufeta da ƙirjin shi yana goga mata fuska a wuyanta yana shaƙar ƙamshi murya can ciki ya ce
"No need" ta riƙe shi ta ce "Please mana, kuma.....,"
"Zawja tsarin iyali?" Ya faɗa yana ƙara taɓa gefen hannunta. Ta ce
"Sbd Hala na saka, kuma kasan yanayinka Habibi" ya yi ta kallonta idanunsa sun yi jajir jijiyoyin kansa duk sun fito sai huci yake ya tsareta da manyan idanunsa a hankali ya saketa tare da miƙewa zai fita ta diro daga kan bed ɗin tare da shan gabansa ta ce "Ka fahimce ni Please Habibi bada wata manufa nayi haka ba" ya saka hannu tare da matsar da ita gefe, ta ƙara yin gaba zata riƙe shi ya buga mata wata kyakkyawar tsawa cikin faɗa ya ce
"Move!" Taja jikinta wanda yake ta rawa da ɓari bata taɓa jin tsawar daya shigeta irin wannan ba, sanadin haka ya tayar da Hala ta saka kuka kafin ta ƙarasa yaje ya ɗauke yarinyar shi tare da bar mata ɗakin.
Kuka ta dinga yi hankalinta ya tashi bata taɓa hango masifar Yaa Sheikh a ƙwayar idanunsa kamar yanzu ba, ta jima tana kuka wajan ƙarfe 12 ta miƙe ta nufi upstairs ta samu ƙofar shi a rufe, ta dinga knocking yana jinta ya share. Yaa Sheikh ya daɗe bai shiga ɓacin rai irin wannan ba, yana so da ƙaunar zuri'a mai yawa da kuma albarka amma ace tun a haihuwar fari mace tayi tsarin iyali me hakan ke nufi? Ya dubi Hala Sheikh Aliyu haydar dake ta sukur-sukur a ƙirjinsa ta ƙiyin barci da alama nono take buƙata, ya shafa kan yarinyar dake cike da suma gwanin sha'awa kamar ya tsokanota ta saka kuka tana shura ƙafa, ya shiga jijjigata amma fir Hala taƙi yin shiru zam-zam ya ɗauka ya bata ta sha sosai yarinyar akwai kuka kamar mahaifiyarta.
Ya sanyata a kafaɗa ta shiga tsotsar fatar wajan murmushi mai laushi ya yi ya ce "I love you Hala, and i so much love your mother amma halinku ɗaya, mene laifi don ta sake yin ciki bani nake bata ƙwayayen ba? Ni ban gaji ba sai ita?"
Tayi masa ƙuri da manyan fararen idanunta kamar mai fahimtar mai yake cewa a haka suka raba dare da ƙyar tayi barci tana tsotsar lips ɗin shi kamar ta samu nono ya rungumeta yana ƙara jin soyayyar mahaifiyarta a ran shi ya kasa barci kamar yadda Halisa ta kasa.
Da azuba tana farkawa Idanunta ya sauka akan Hala tayi mmkin yadda aka sauya mata wajan kwanciya domin a ƙasa barci ya ɗauke ta dab da Subhi yanzu kuma ta ganta akan gado.
Sallah tayi ta goya Hala ta shiga kitchen ta haɗa breakfast, tana gamawa ta yiwa Hala wanka ta shiryata ba jimawa barci ya ɗauke ta itama tayaya wanka ta shirya tsaf cikin wani green lace mai kyau ta murza ɗauri.
Ta samu Jadda a parlour tana shan tea ta haura upstairs, tayi sallama ya amshi murya can ƙasa yana zaune saman kujera ya ɗora ƙafa idanunsa sanye cikin glasses hannunsa riƙe da azkar sai laptop a gefe da mug ɗin coffee ta tsokana ta ce
"Mrng Habibi" ya amsa a ciki ta ce "Breakfast is ready" ya yi mata banza. Abu kamar wasa har tsayin sati Yaa Sheikh ya ɗauke mata huta tsakanin shi da ita gaisuwa idan ya tabbatar lafiya take sai ya ɗauke hala. Tuni Jadda ta gudu tace ba zata iya da masifar shiru ba.
A kwana na goma ta same shi kwance ya lumshe idanunsa dawowar shi kenan daga duba banks da Companies ɗin shi da gidan marayu. Ya ƙarasa gidan Abba Hakimi ya duba Umma A'isha dake zazzaɓi ya samu Zahrah ta ɗan kwantar da hankalinta.
Yana jinta yaƙi magana ta daddage ta fasa masa ihu aka tare da birgima, bai san mene ya faru ba sai ganinsa shi ya yi riƙe da ita yana jijjigata ya ɗauka aljanu take.
"Ke lafiya Zawja?"
"Abba ka mayar dani gida tunda baka so na baka ƙaunata ka juya mini baya, na baka haƙuri nace na cire in-plan ɗin" yaja jiki ya kalleta da kyau ya ce.
"Zawja ni ne baki so, tunda baki son bani zuri'a daga gareki" tana kuka sosai ta ce "Kayi haƙuri Habibi ba zan sake ba, surutu ne bana so kada a ganni da wani cikin nayi maka al'ƙawari haihuwa har sai lokacin da Ubangiji zai tsayar da ita daga gareni"
Ya kalleta kawai daman tuni ya huce domin sunyi magana da Ummul kawai ya rabu da ita ne yaga gudun ruwanta. Ta dinga kuka ya ce
"Meye?" "Baka kuya mini baya ba ƴarka kawai ka sani" Ya sakko daga kan kujerar ya juya mata baya ya ce "Hau" ta maƙale kafaɗa ya ce "Ai baki isa ba, ga bayan nan dole ki hau" taƙi ya ɗauketa ya sata suka zagaya wajan kana ya sauketa.
"Me ka ke so?" Ya girgiza mata kai ta ce "Kana nufin babu? Abba kwana goma bama tare fa?" Ya buɗe baki zai magana tayi saurin haɗe bakinsu ta shiga bashi wani kyakkyawan kisses a wannan lokaci sai da Halisa ta goge gabaɗaya fushin Yaa Sheikh ta ƙara bashi mmki domin ta gama gane lagwan shi.
*2 months later*
Mai gadin su Fattoumah aka yanke masa hukuncin jifa kamar yadda addini ya faɗa, ɗan shi kuma aka yanke masa hukumcin zaman kaso akan amfani da kayan soja da tuhumar shi kan siyar da miyagun kwayoyi. Ɓangaren Fulani Atine hauka sai abinda ya ƙaro babu sauƙi cikin lamarin.
Dada na fama cikin wata huɗu, Maimoon da Hafsat duk cike gare su haka matar Saifuddeen.. a lokacin Zeefa ta samu miji itama aka sanya aurenta. Rayuwa taiwa kowa daɗi banda Surayyerh dake faman neman miji idanu rufe amma bata samu ba, gabaɗaya samarin sun gudu taƙi amfani da damar da Ubangiji ya bata tun tana da lokaci taƙi amfani da shawarar mahaifiyarta.
Ummul ta riƙe Shatu wajanta tana kula da komai nata taƙi yin aure duk har zuciyar Yaa Sheikh yana son yaga mahaifiyar ta shi da aure amma ya kasa furta mata. El tunda ya ɗauke Fattoumah Angela ba'a ƙara jin motsin shi ba.
Ta dubi cikin gerden ɗin da ya ya yi mata kyau sosai a hankali ta ɗaga kanta zuwa gefe wajan wani ruwa taga an saka.
*_Happy 1 year Anniversary_*
Ta ƙara juyawa zuwa wani wajan da aka saka _*To My wife Zawja*_ ta dubi ƙaton zanan heart ɗin gently ta taka zuwa ƴar rumfa mai kujeru guda biyu an saka cake a tsakiya da ƙaton frame na picture nasu su biyu an rubuta.
_*"OUMU-HALA*_ Marrying you was the smartest thing I ever did, happy 1 year Anniversary Zawja"_*IDAN BA KE 83 End*_
O Allah, I have greatly wronged myself and no one forgives sins but You. So, grant me forgiveness and have mercy on me. Surely, you are Forgiving, Merciful. My biggest Fans i no words to thank you, ban sani ba amma kullum masoya ƙaruwa suke, Ba zan saka *IDAN BA KE* cikin tops popular book's ba, but i can say zai iya zama The best book among the other's, godiya ga *Paid grp 1* godiya ga *Paid grp 2* special thanks to *My special grp* girmamawa ta musamman ga *Arewabooks* Nimcyluv sarauta loves you always forever ever.


_Special thanks to these people who are important to me_ NASIR NID, FAUZIYYA D SULAIMAN BRIGHT PENS, Sauran marubutan da suka bibiyeni a wannan littafin kuna da yawa i can't list them thank you all.


Thank you my parents thanks for support and care rabbi ya saka muku da alheri. 🤣 Ƴan wasa na ina godiya Uncle Sheikh Aliyu ina tsoran haɗuwa da kai serious, Brother Bashir Mubasshir, Ummul🥰 and the rest Sorry Khalil🏃🏼‍♀️. _Oh! I almost frgt to thank my people those who read my book as free nasan soyayya ce ba zance ban yafe ba amma littafin kuɗi ne ga duk wanda ya yi niyyar biya contact me 08119237616. Ƙofa a buɗe take ga abinda aka yi kuskure, yabawa, jinjinawa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login