Showing 195001 words to 197828 words out of 197828 words
Chapter 66 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
sharhi yadda kuka ji daɗin labarin da gyaran ban ɗaukewa kowa ba am ready to accept my mistakes👏🏻_
Complete Book 1 2 ga mai so dubu ɗaya 1k.
This page dedicated to my husband much much love ❤️❤️❤️❤️❤️
Ta juya da sauri domin ba ƙaramin surprising nata ya yi, idanunta cike da ƙwalla da kuma soyayyar mijinta ta riƙe Yaa Sheikh ta ce
"Yaa Allah, i so much love you Habiba you're the best husband ever Allah ya ƙara maka arziƙi da wadata ya taimake ka" ya holding nata back yana sakin murmushi mai kyau idanunsa lumshe ya ɗauki wayarsa tare jawota jikinsa sosai ya yi musu selpie.
Hala nada shekara ɗaya ciff a duniya Halisa ta kuma samun wani cikin a wannan lokacin farin cikin Yaa Sheikh har yafi na baya, Ummul ta kalli Yaa Sheikh daya fito daga ɗakin grandpa ɗin shi ta ce "Ku barni mini Hala mana, sbd yayeta dole za tayi" Ya kasa cewa komai domin ba ƙaramin nauyi ya ke ji ba, ganin yanayinsa ya sa ta ce "Ina Halisar fa?"
"Tana wajan Mubasshir waje" Ummul ta buɗe ido ta ce "Yau kuma, yaushe yazo da Fattoumah?" Yana yin waje tare da covering jikinsa da Alkyabbar jikinsa ya ce
"Uhm maybe yau ko?"
"Ok kirata muji" ya nufi waje tun daga nesa ya hango hasken fatar jikinta domin shigar sabon cikin ya sanya tayi wani irin fari kamar wacce jini ya ƙarewa.. da idanu ya kalleta ta miƙe tsaye tana kallon Fattoumah ta ce "Mijina na kira, ke kam Hamma El ya lalata miki tarbiyya" El dake jingine jikin mota Hala na riƙe gemunsa yaji maganar Halisa sama-sama ya ce
"Angela me princess take cewa?" Fattoumah tayi murmushi ta ce
"Cewa tayi yaushe zaka sama mini kamar Hala?" Ta faɗa tana kashe masa idanu ɗaya. Ya girgiza mata kai ya ce
"Bayan ajjiyar da nayi tun watan daya shige wani kuma ki ke so? Don't worry I'll give you more"
"Kasan kuna kama da Hala? Dama kawai abar mana" El ya ce
"Rufa mini asiri Angela daga Abba Sheikh har Princess babu mai iya bayar da Hala wannan yarinyar kamar gold, kuma maganar kama ai ba abin mmki bane ni da babarta kamar twins haka muke wajan kama da juna, Hala kuma kamar su ɗaya da babarta that's means mu uku muna kama da juna"
Fattoumah dariya tayi tana shigewa cikin gida wajan Ummul El Yabi bayanta yana zuwa Halisa ta ce "Prince ɗan muga Hala zan saka mata ring" bai kawo komai a ran shi ba ya miƙa mata ita ya shige ciki, yana shiga Yaa Sheikh ya kama hannu matar shi zuwa mota ya jasu har zuwa airport a hanya ya kira Umar-khan suka haɗu ya bashi key ɗin motar Umar-khan na tsaye shi da Hafsat da Jaririyarta mai suna Ajimal har jirgin su Yaa Sheikh ya lula sama zuwa gari mai albarka Madinatul-munauwara.
A vip suke _very important people_ suna shiga ya zame Alkyabbar jikinsa ya ajjiye gefe yana lumshe idanunsa tare da jan numfashi sai yanzu abin ya bashi dariya da kunya sun gudu da ƴar su sbd kasa su barta wajan Ummul. "Habibi ƙalbi naji kunyar Ummul"
"Uhm" ya ce yana kallonta kafin a hankali ya miƙa mata hannu ya ce "Zo kiji" ta kwantar da Hala a kan wata kujera ta ƙarasa wajansa suka kalli cikin idanun juna, ba zata iya cewa ga abinda Idanunta ya hango mata ba, tana karantar kallon shi, ko shirun shi amma yau abubuwan da suke gilmawa a cikin idanunsa daban suke.
"Shekarar ki nawa ne?"
Tambayar ta bata baki sosai kafin ta ɗaga Idanunta sama alamar tunani ta daki ƙirjin shi ta ce "I think 18 going to 19 what happing?"
Ya girgiza kai ya ce
"No! kin zama big Mama Zawja" tayi dry sosai tana kama gemunsa tare da kitsawa ta ce
"Ba dole ba, ina samun kwanciyar hankali, soyayyar miji kulawa ka romantic style naka kala-kala" ya zura hannunsa a ƙirjinta yana sauke wani zazzafan numfashi idanunsa ya jirkice ya tura kan shi a wuyanta tare da manna lips ɗinsa ya shiga bin fatar wajan da tongue ɗin shi. "Modibbo"
Ta zame fuskar shi da ƙyar ya watsa mata idanu ta ce "I love you Modibbona" ya runtse idanu ya buɗe yasan bata san tasirin da I love you ɗinta ke da shi a zuciyarsa shi ne a sanya kullum take narkar masa da zuciya da hakan.
"Tsoho ki ke so?"
"Bana kallon tsofan kyakkyawan saurayi nake kallo" ya jinjina mata kai tare da kafe ta da kallo.
"Wannan kallon fa?"
Ya riƙe kafaɗunta cikin nutsuwa ta sarƙewar murya ya ce
"Shekaruna 37 cif, shekarunki 19 lokacin cika she 40yrs kina 22 ba za kiga tsofana da furfurana ki juya mini bay...," Bakinta da yaji cikin nasa tayi masa wata kyakkyawar sumbata yasa ya ƙarasa haɗiye sauran maganar a zuciyarsa. Sai da tayi kisses nasa da kyau kafin ta ce "Har abada, gaban abada idan zan rayu to dakai ne"
Ya lumshe ya girgiza "I feel empty without you IDAN BA KE Just..."
Sai kawai ya rungumeta a ƙirjinsa yana shafa cikinta ɗumin cikin na ratsa hannunsa farin ciki sosai yake ciki za'a ƙara haifa masa Baby.
Sai dare jirginsu ya sauka haɗaɗɗun motoci suka zo ɗaukan shi, har gidan shi aka kai shi daren ranar basu runtsa ba gefe guda aka ajjiye Hala suka kwashi soyayya mai cike da tsafta. YAA SHEIKH bakinsa baya iya furta abubuwan da yake ji game da Halisa Danejo Rome, gangar jikinsa ita ke fansar bakinsa hakan yasa yake ƙara shigewa zuciyar Halisa a ko wanne lokaci,ko wacce daƙiƙa ko wanne harbawar seconds. Faɗan su baya ɗorewa domin Halisa ta gama gane waye mijinta duk son da yake mata ta nayin ba daidai ba zai rufe idanu ya yi mata faɗa tas, idan kuma ta ce kawai ya mayar da ita gida a lokacin zan sakko daga dokin zuciyar tare da accepting apologies ɗin ta, ta hanyar sauke mata mazantakar shi.
Ɗaliban shi na ISLAMIC UNIVERSITY OF MADINA. Sukai farin ciki sosai domin suna ƙaunar lecture ɗin shi, yana nan da kame kan shi fuska kame Kullum ya ƙara daddako cikikar kamala kwarjini ba a magana.
Rayuwa ta dinga juyawa ci-gaba ya dinga zuwa ta ko'ina, a haka har Halisa ta ƙara haihuwar kyakkyawar yarinya sak mai kama da ita, idan Yaa Sheikh ya kalli Halisa ya kalli Hala ya kalli Rohna mamaki yake gabaɗaya kamannin Zawja suka ɗauka lallai ya amince Ƴar fillo ta fishi fitina da ƙwazo. Da shi da wata bahaushiya suka dinga kulawa da Halisa har ta samu cikakken wata biyu. A wannan lokacin ne kuma aka fara azumi. Ana gobe sallah tarihi ya maimaita kan shi domin kiran gaggawa suka samu daga ƙasa Nigeria an kuma ƙi faɗa musu abinda yake faruwa. Babban tashin hankalin Yaa Sheikh bai shige yadda yake kiran Ummul wayar a kashe a haka har suka dira a Nigeria.
Lokacin biyu ga sallah Halisa ta samu tayi Oummara a karo na biyu hajji ne Allah bai bata iko ba. Yaa Sheikh ya dubi idanun El-bashir da yazo ɗaukan su a airport, sosai ya firgita da yanayin El. Ya kasa jurewa ya ce "Mene ya faru Mubasshir?" Da sauri El-bashir ya rungume Yaa Sheikh yana sakin ajjiyar zuciya.
Maimoon wacce ita tayi namijin ƙoƙarin bayanta goye da Ajimal ta amshi Rohna Shatu ta amshi Hala wacce ta fara dabo Yarinyar gwanin sha'awa tayi ƙiba sosai sai tayi kamar haifaffiyar Makka ɗin. Halisa ta kasa fahimta tunaninta ya tsaya duk yadda taso ta fahimci abinda yake faruwa ta kasa ganewa. Da ƙyar El ya yi driving har zuwa gida tun a ƙofar gida ƙirjin Yaa Sheikh ya buga sbd cikar mutane.
Ganin Yaa Sheikh ya dawo musu da mutuwar sabuwa fil! A zuƙatan su Umar-khan, Ishaq-Hakim, Saif-wazir suka rungume Yaa bakiɗaya suna kuka sosai domin yanzu shi suke kallo matsayin Uba.
Mother, Dr A'isha da Yaya Halima duk suka zagaye shi tare da zuba masa idanu ya rasa mene ke faruwa da shi, ko a ba'a faɗa ba kai tsaye ya fahimci cewa Abba Hakimi gone, he's no more, he pasted away!
That's means Halisa's grandpa babu shi baya nan a raye a wannan duniya.
Ya zame jiki da ƙyar kai tsaye part ɗinsa na gidan Ya nufa jiri na kwasar shi luuu ya yi Ummul dake zaune daman ta san za ayi haka tayi saurin riƙe shi, gabaɗaya jikinsa rawa yake ya rungume Ummul sosai ya hanata motsi lokaci ɗaya zazzafan zazzaɓi ya rufe shi, Shi ɗaya tal a duniya ya kewa kallon Uba majin gina tun yana yaro a ƙasa matsayin rarrafe Abba Hakimi ya fifita shi fiye da yaran daya haifa.
Tsayin kwana uku babu mai zuwa wajan Yaa Sheikh ya yi tawakkali amma shirun bayin kan shi bane, jama'ar dake kan shi suka rufe masa baki baya ko tari sai kallo da idanu. Lokacin daya dawo daidai abinda ya fara tambaya shi ne mene ya faru? Aka shaida masa ciwon ciki ne farat ɗaya bayan ya ɗauki sahur da asuba kafin Assalatu rai ya yi halin shi. Yaa Sheikh ya tattara gabaɗaya dukiyar Abba Hakimi akaiwa yaran shi rabon gado. Tun daga ranar suka ɗauki Yaa Sheikh matsayin Uba yadda su kewa Abba Hakimi kallon Uba haka suke masa.
Ya tsaya tsayin daka akansu har tsayin shekaru huɗu lokacin yana da shekara 40 ciff, yaransu biyar Hala, Rohna, Huda, sai namiji Aka sanya masa sunan Abba Hakimi suna ce masa Hakimi sai ƙaramin su Taujid. Huda da Hakimi tagwaye aka haife su, kwanakina take zubawa sosai duk shekara sai ciki abin ya dameta amma fur Yaa ya rufe idanu ya ce Allah ya hore masa idan ma duk wata zata haihu dole ta dage da gyara.
Zahrah duk daga kan Muhammad bata sake samun haihuwa ba data samu cikin zai zube baya zama, haka ya riƙe Muhammad ya yi wayo sosai. Umar-khan da Hafsat a tsayin shekara shida ɗin nan yaransu biyu, haka Maimoon da Khalil, El-bashir Ahmad Nuran Sarki da Fattoumah Aliyu ɗan su ɗaya mai sunan mai martaba a yanzu kuma shi ne Sarkin Sokoto.
Arziƙin Yaa Sheikh ya ninka haka bisa jajircewa da taimako.
*20 year's later*
Gidan cike yake Hala da Rohna sai kuka suke kamar ransu zai fita Hala ta ƙanƙame mahaifinta tana cewa "Abbi ban so, ban son auren kada a rabani daku na fasa auren" kuka take sosai Yaa Sheikh yana ƙaunar yarinyar shi ƙwarai komai nata na Halisa ne shi yasa yake jinta daban a zuciyarsa. Ya rungumeta yana bubbuga bayanta shekarun shi 60 cif ya zama babba mutum wanda ake kwatance da shi a hankali ya ce "Sorry Mamana, sorry" ta girgiza kai tana riƙe shi Rohna kuma Halisa ta riƙe tana cewa "Mami ki ce Abbi kada ya basu mu" school mate ɗinsu sai vedio suke musu haka photographers abin ya zama wani extraordinary. Mother da Dr A'isha suna kallon ikon Allah basu taɓa sanin haka Yaa Sheikh yake ƙaunar yaransa ba sai yanzu. Daga gefe guda aka saki tsaki mai kyau Hakimi ya juya zuwa ga ɗan yaron da ba zai shige 16yrs ba, baƙi ne shi sosai har sheƙi yake gabaɗaya shi ne ya banbanta a cikinsu ba zaka taɓa cewa daga cikin Halisa ya fito ba, shi ne last born nata.
Labɓansa jajaye ne tas haka idanunsa farare ne gabaɗaya jikinsa zanan tattoo ne ra'ayin shi ya bambanta da duka sauran yaran. Ya ƙara jan tsaki yana saka hannu tare da har gitsa sumar kan shi wacce ta zama irinta Yaa Sheikh kala biyu. Hakimi ya ce
"Abraham what exactly wrong with you?" Ya ɗaga manyan idanunsa yana miƙewa tsaye tare da bada faɗi idanunsa na lumshewa kamar mai jin barci a hankali speaking calmly ya ce
"I don't know what exactly wrong with me, wannan ihun yana gab da fasa mini kai Please Hakimi do something i need to rest duk an cika mana gida da ihu kamar gidan mutuwa"
Hakimi ya ce "Yaron nan baka da hankali, Big sister's naka suna kukan rabuwa da Mami da Abbi damu kanmu amma kana zancan iska"
Abraham ya watsa hannu tare da buɗe ido sai ka ɗauka shi ne babba ya ce
"And so what? Na faɗawa Abbi yaran nan ba zasu iya zaman aure ba, dani ya yi wa ta gidan ubanwa zan zauna ina kuka" Hakimi yabi ƙaramin ƙanin nasu da idanu yana mmkin faɗin ran yaron har tsoro yake bashi. Abraham rai ɓace ya saka hannu ya fisge Hala daga jikin Yaa Sheikh daidai lokacin angwayen suka shigo jin abinda ke faruwa. Idanun Abraham har wani ruwa ruwa ne yake kwanciya cikinsu ya kalli Junaid-Ali ya ce "Brother take your wife ta dame mu" Junaid-Ali ya yi murmushi ya ɗauke Hala cak tana zunduma ihu ya yi waje da abar shi.
Haka ya ƙara fisgo Rohna ya damƙawa Abuturab ya ce "And you too take your wife" shi ma ya riƙe Rohna yaran sunyi mugun shaƙuwa da iyayensu sosai. Huda kuka take sosai na rabuwa da ƴan uwanta haka Hakimi idanunsa ya yi jajir banda uban tafiya Abraham ko a jikinsa sai ma riƙe kan shi da ya yi da hannu bibbiyu sbd juyawa yake baya ƙaunar hayaniya. Halisa ta juya zuwa bedroom ta dinga kukan rabuwa da yaranta tausayinsu ya kamata.
Yaa Sheikh ya haura upstairs. Sauran ƴan bikin suka shiga mota zuwa rakiyar amare. Yana daga kwance ya miƙe zumbur yana jan lafiyayyan tsaki ya ce
"Ni meye nawa laifin da ba za a yi mini aure ba?" "Kai yanzu idan akai maka auren kayi me?" Ya girgiza kai kawai yana jin tambayar rainin hankalin da Hakimi yake masa.
Ya haura upstairs zuwa part ɗinsa har ya juya ya ce "And don't forget wallahi babbar mace nake so In sha Allah irin 40 to above ɗin nan ko 50" yana faɗin haka ya shige part ɗinsa yana taune lips.
Surry har yanzu babu mijin aure, Jadda nan tsofa ya gama cin ƙarfinta Ummul daman bata zo bikin ba sbd bata ƙasar bakiɗaya.
Shigowa ya yi ƙamshin Roja ya shiga hancinta ta ɗago suka kalli juna idanunta a kumbure ya yi murmushi yana zare Glasses ɗin idanunsa ya ce "Mene ya samu Mami ne?" Ta kwaɓe fuska ta ce "Are questing me? Bayan an rabani da yarana" ya jawota jikinsa ya ce "Oh! Sangartar Abraham ya yi yawa zo muje na baki wasu ƙwayayen haihuwar yanzu ki ƙinƙishi"
Ya bugi ƙirjinsa ta ce "Ina tausayin Rohna" "Ni Hala" ta kalle shi ta ce
"Hala gaba take da Rohna fa?" Ya rungumeta yana zame hannunta daga riƙe fuskar shi ya ɗauketa yana cewa
"Mamana halinki ta ɗauka, mijinta zai sha barbaɗa da surutun ba a tambayeta ba amma bata da juriya kamar ki that's why" ta lumshe idanu ta ce "Thank you Abba, ka gama yi mini komai I love you"
Ya yi mata rumfa sosai ya ce "Ni ne da godiya, kin bani Mamana, Kin bani Khadijah, kin bani Mother Maryama (Huda) da Abba Hakimi, ga auta Ibrahimul-khalil Abraham, kin zame mini komai kin mamaye mini gida da zuri'a masu Albarka, *IDAN BA KE* that's means babu YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU" ya rufe idanu ta ce "Allahamdulillah, Allah na gode daka bani miji kamar Yaa Sheikh i love You Habibi ƙalbi"
Idanun Yaa Sheikh ya yi jajir bakinsa ya shiga rawa ya faɗa buga kan shi, Halisa ta tsaya kallon ikon Allah cikin sarƙewar harshe da wata In-ina ya ce
"I.... I... I...." Wasu irin hawaye Masu zafi suka sakko daga cikin idanunsa yana matseta kamar zai rabata gida biyu cikin In-ina ya ce
"I.... I.... Lov...love... I love You" dam! Zuciyarta ta bada sauti sbd tasirin kalmar tunda suke sai yau ya ce mata I love you, ya yi murmushi itama tayi murmushi ta gama fahimtar a yanzu ba Yaa Sheikh ɗinta bane kawai ya juye zuwa MUTUM DA ALJAN tana ganin yadda jikinsa ke murɗewa kamar wani maciji ya ƙara ɗaga murya ya ce "I love you Zawja" yana faɗa yana rungumeta sosai ta ce "Allahamdulillah" tana faɗa ya ce "I love you Haliyserh Sheikh Aliyu haydar Aliyu I love ƴar fillo,I love you Danejo I so much love you princess Queen of my heart IDAN BA KE ba Sheikh Aliyu haydar Aliyu Allahamdulillah"
"Abraham laɓe ka kewa su Abbi" ya kame fuska hannunsa riƙe da iphone system zai kaiwa Yaa Sheikh ya duba masa wani abu shi ne ya kai bakin ƙofa yaji ana I love you. Ya juyawa har ya je bakin ƙofa ya ce
"Yaa Hakimi can i ask you?" Hakimi ya ce "Sure, go ahead I'm listening"
Abraham ya ce "A cikin mata wace tafi iya soyayya irin romantic love ɗin nan" Hakimi ya ce "Wannan sai dai Malamai ai sune suka san kan soyayya" Abraham ya ce "Ohh! I'll catch you MALAMA malama zan aura" Hakimi ya juya yana cewa "Sannu *MIJIN MALAMA* (Upcoming book).
_Allahamdulillah. Nan na kawo ƙarshen littafin IDAN BA KE Book 1&2 Ya Allah ka sanya littafin ya zama hujja gareni ba hujja akai na ba, Ya ka datar damu duniya da lahira Ubangiji kaga manufarmu ka sanya mu gane gasky ka kuma shiryemu kada ka barmu da iyawarmu, dabararmu wayonmu ka sanya mu amsa tambayoyin da duk za'ayi mana😭👏🏻_
MEENA VIP GROUP HAUSA NOVEL DOCUMENT for more information contact on
+234 7014979567 WhatsApp ONLY