Showing 144001 words to 147000 words out of 197828 words
Chapter 49 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
ya nisa ya ce.
"Ba Zahrah ba, ko mother idan na yi niyya zan aura, tunda ban sha nononta ba, idan ina son mace da zuciya ɗaya to ko wacce ta shahara a karuwanci zan iya aura, da zarar ta tuba ni kuma zan Jahadi, Ina son Zahrah da gaske"
Yana faɗin haka ya juya zuwa wajan freezer ya ɗauki Apple da gorar ruwa mai sanyin gaske ya koma bedroom ɗin da yake ciki.
Yana barin wajan Halisa ta zube ta dinga kuka kamar ranta zai fita, ashe da gaske son Zahrah yake? Yanzu duk daɗin da Yaa Sheikh ke jiyar da ita Zahrah ce zata samu, su kwana tare?gado ɗaya wata kilama a manne a jikin Abban nata? Ta dinga kokawa da numfashinta tana riƙe ƙirjinta, ita kawai jin abin take kamar mafarki, amma hakan bai dameta ba, indai zai saketa taje ta gana da ƴan uwanta domin tayi al'ƙawarin idan har igiyar auren shi na kanta to babu inda zata, sai manne cinyoyi take kamar wacce hauka ya kama wani mugun son kasance da ɗa namiji ya shige ta ido rufe ta saki kuka ta ce
"Mugu" Yaa Sheikh ya ɗaga gorar ruwan duk sanyinsa haka ya zubawa cikinsa bai iya shan Apple ɗin ba ya ajjiye gefe guda, kusan abu ɗaya ke damunsu ya shiga sakarwa kansa shower mai sanyi daga ƙarshe ya fara lafilfilo yana kaiwa Ubangiji kukan shi akan ya sausauta zafin zuciyar Matar Malam ɗin.
Ummul ta buɗe ƙofar bedroom ɗin ta shigo bakinta ɗauke da sallama tsaye ta kanshi, yana gyara zaman diamond rolex watch, tai tsaye tana kallon kyakkyawan dattijo ko magidanci da Allah ya bata matsayin ɗa ɗaya tilo, babban mutum masanin addinin Musulunci tsantsa babban likita wanda ya san aikin shi, bai haƙuri da riƙo da ƙaddara a duk sanda ta zo masa, mai tausayi da imani da jinƙan na ƙasa da shi.
"Arɗona" ya juya ya kalleta ya nisa ya ce
"Sabahul khair Ummul"
Ta ce "Yawwa, wani abu ya haɗaka da Daughter?" Kasancewar baya ƙarya kai tsaye ya ce "Rikici ne, akan sakin ne" ta numfasa cike da tausayin Yaa Sheikh ta ce "Anya ba zakai mata abin da take so ba?" Ya dubeta a raunace ya ce
"Ummul na saki Zawja?"
Ta ce "Na san zafin da zuciyarka ke ciki, Halisa yarinya ce amma ina mmki taurin kai da zafin zuciyarta,bana son na fara jin zafinta wata macan sai an mata sakin take shiga hankalinta, idan sakin ne mafita ya kamata kayi ko ɗaya ne"
Ya taka har zuwa wajan Ummul ya riƙe hannunta a taushashe ya ce
"Kiyi addu'a, komai zai daidai" "To Allah ya kawo sauƙi cikin lamarin ya kuma daidaita tsakaninku" ya jinjina kai ta ce "Tafiyar ce? Kaje wajan Abba Hakimin?" Ya ce "Zuwa 11:30 zamu ta shi, yanzu zani" ya faɗa yana jin cewa zai kewar ganin koda masifar da take masa, amma ko zai sha wahala itama dole ta sha domin ya fahimci fitinar da cikin Jikinta ya sata.
"Allah ya tsare ya kare, ya ƙara maka haƙuri haka lamarin aure yake wani daɗi wani sai an wahala, wanda aka wahala ɗin sai kaga yafi Kwari da inganci" Shi dai kallonta yake harta gama ya juya ya nufi waje sai da ya yi nisa ta ce
"Na manta tun safe Maimoon da Daughter suka shige" nan ma ya jinjina mata kai, ya nufi part ɗin Dattijo da Hajia suka gaisa, Alkyabbar jikinsa na ɗaukan idanu yana basa ƙamshi mai daɗin shaƙa yana mai gyara zaman hiraminsa ya ƙarasa harabar gidan ya samu Umar-khan dake tsaye yana jiran shi yana zuwa ya buɗe masa ƙofa yana faɗin "Barka da safiya Yaa Lee" ya rufe idanu ya buɗe alamar ya amsa domin maganar wahala take masa, kai tsaye gidan Abba suka nufa, babu wanda ya yi magana har suka ƙarasa Ishaq-Hakim ya buɗewa Yaa Sheikh Umar-khan ya fito suka nufi ciki A parlour suka samu mother ta saka Halisa a gaba ta inda ta shiga bata nan take fita ba, gabaɗaya haushin Halisa ya kamata bata san haka take da taurin kai ba sai yanzu. Dr A'isha ta ce
"Barrister ni banga abin faɗa ba, ba a ga abin da yake mata ba sai ita za a ga laifinta, kuma ita ce mace ita zata zauna da shi tunda bata so ba sai a rabu da ita ta fito da wanda take so ta aura"
Mother ta ce "Kenan ke ce ki ke mata huɗuba?" Tai saurin cewa "A'a,nikam ina ruwana meye nawa miji kowa da nashi, bayan itama da wayonta tunda har ciki ne a Jikinta ai ta shige ai mata huɗuba"
Daga bakin ƙofa aka ce
"A'isha ta shi kibar gidan nan" ta ɗago da sauri suka haɗa idanu da Yaa Sheikh, hantar cikinta ta kaɗa ta tsare shi da kallo kwarjinin shi da cikar kamalar shi da haiba suka cika mata idanu ta ce "Me ka ce?"
Ya shigo ciki har inda take zaune da hannu ya nuna mata ƙofa ya ce
"Ki bar gurin nan tun kafin na nuna ɗaya ɓangarena, babu ke ba matata" ta ce
"Yaa Sheikh ni ka ke cewa haka kamar wata sa'arka? Ni ka ke rabawa da matarka?" Abba Hakimi ya ce "Ta shi ki ke, tunda Yaa Sheikh ya yi magana akwai abin da ki ke" tai ƙwafa tana ficewa daga parlourn.
Yaa Sheikh ya nemi waje ya zauna fuska ɗaure idanunsa a ƙasa ba tare daya ƙara kallon kowa ba
"Ya akai Aliyu?" Sai a lokacin ya sauka numfashi ya ce "Tafiya zan yi" Abba Hakimi ya ce "Tafiya da gaggawa haka? Har tsayin yaushe?" Ya miƙe yana cewa "kawai sai Allah ya dawo dani, bari na je kada na rasa jirgi" Mother ta ce "Allah ya tsare ya ki ya ye angon Zahrah, muna nan mun fara shirye-shirye yanzu Ummul take sanar mini ai yanzu zakai aure, daman wata rabuwar alheri ce ka samu kyakkyawar mata" Umma A'isha tai murmushi tasan da biyu! Wai anjefi uwar miji da rani, an jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Yaa Sheikh ya juya yana cewa "Wajanta zan fara zuwa" Ya fice abin sha da sauri Halisa ta miƙe Mother na kiranta tai banza da ita, tana zuwa ta tsaya Idanunta kaca-kaca da hawaye ta ce "Ka ce na tuna maka, ka sake ni, ko sati ba zan ƙara ba zan samu mijin aure dalilin cikin nan kawai zan jira na haihu" Yaa Sheikh bai damu da Umar-khan da Ishaq-Hakim dake tsaye ba ya riƙo hannunta tare da dawo da ita gaba.
Ya tsareta da narkakkun idanunsa ta ɗauke kai a hankali ya jawota jikinsa tare da shigar da ita cikin Alkyabbar shi zata ƙwace ya riƙeta da kyau! Ya ce
"Bake na rungome ba, jina na, ƙwan dana zuba miki har ki ka ɗauka da shi zan sallama" ta ɗago zata kalle shi gemun shi yaƙi bata damar haka ta ce "Ɗana dai, daga yau ka daina tunanin kai ne uban shi" shi dry ma ta bashi ya shafa cikinta ya ce "Shi ya sa naga ke ki kai cikin, nutsu muyi magana" tai banza ko wanne second guda sai zuciyarta ta buga na fargabar da gaske wai wajan Zahrah za shi? Ya ce "Haliyserh da gaske baki so na?" Ta ce "Wallahi bana son ka, na tsaneka, ka rabu dani" ya jinjina kai ya ce "Zan miki abin da ki ke so, zan kuma tafi tafiyar da zaki mamaki wacce ba lallai na dawo da rai ba, ki faɗawa abin da zaki haifa ba Mahaifinsa yaƙi babarsa ba, ita mahaifiyar ita taƙi uban, wannan zai zama rungoma ta ƙarshe, ki jiƙa jikin ki, ki sha Haliyserh Ahmad Nuran Sarki, zan je nai sabuwar rayuwa da Zahrah ina fatan alheri" ya jim yana ɗan matseta a ƙirjin shi kafin ya sumbaci goshinta yana zareta daga jikinsa, ya zaro farar Envelope daga jikinsa ya damƙa mata ya ce "Your Divorce paper" yana bata ya shiga mota Umar-khan yaja motar da gudu zuwa airport...
Tsammaci abin da baka tsammani, aiki da hankali yafi aiki da kwakwalwa😊Ta dinga juya Envelope ɗin a hannunta Idanunta akan gate tana kallon yadda motar Yaa Sheikh ke ficewa, ji tayi kamar yana tafiya da zuciyarta da ruhinta Jikinta ya yi sanyi wani abu mai kama da faɗuwar gaba ya risketa. Ita ce ta ɓukaci sakin amma sai taji wani baƙin ciki na sakin, kamar yadda ki wacce ƴar mace taje jin baƙin ciki idan an saketa, shikenan ta zama bazawara Yaa Sheikh zai je ya yi rayuwa da Zahrah "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Na shiga uku, wayyo Allah"
Ta faɗa tana dafe kanta tare da yin baya zata faɗi Mother tayi saurin tare ta ta ce "Ke lafiyarki ɗaya ki ke shirin suma?"
Halisa ta riƙe Mother ta ce "Wallahi ya sake ni, ya sakeni na shiga uku" ta fasa wani ihu tana riƙe Mother. Ita kanta Mother sai da ƙirjinta ya buga tsoro ya kamata,
Wanne irin hukunci Yaa Sheikh ya yankewa zuƙatansu? Ta tabbata ya haƙura da Halisa kenan? Ta ce
"Saki kuma? innalillahi....," Tama ƙarasa faɗar abin da tayi niyya ganin Halisa kamar zata data iska sbd yadda yake kuka, ya sanya ta jata zuwa cikin parlourn Abba Hakimi yana shirin barin wajan sai ya tsaya ya ce "Lafiya dai?"
"Ina fa lafiya, abin da take hauka neman ta samu" Abba Hakimi yai shiru yana nazarin maganar. "Kamarya Maryam?" Mother ta nuna mata Envelope ta ce "He divorced her, Now she is a widow"
"Lallai ran Malam ya ɓaci, tunda har ya iya rubuta saki, banso haka ta kasance ba da yabi komai a hankali"
Abba Hakimi ya koma ya zauna ya ce "Muga"
Mother ta miƙa masa Envelope ɗin, ya amsa yana gama warewa ya ci karo da rubutu kamar haka.
_“Ta ya ya ki ke tunanin ni Malam Aliyu Haydar Aliyu zan iya sakin matata Princess Halisa Ahmad Nuran Sarki? How can i spend my time ba tare da ƴar fillona ba? Taya zan jure ganin rigmar da take mini tana wa wani? Zan ci gaba da rainon ƴata, matata, gimbiyar masarautar Sokoto, Yaci gaba da son Matar Malam na tsayin rayuwa zuwa mutuwa, na barki zuwa lokacin da zaki nemeni da kan ki, ki ɗauka aurar Zahrah mu duka ƙaddararmu ne kece sanadi kuma, One thing shi ne IDAN BA KE ba Yaa Sheikh na ki, Abbanki, Modibbonki na yarje kiyi makaranta ki je garinku idan hakan zai faranta ranki.. Fatan alheri”_
Abba Hakimi ya yi murmushi a ɓoye bayan ya kammala karatun, zuciyar Mother cike da zullumi ta ce "Saki nawa ya yi mata Abba?"
"Sakin tsayin rayuwa!"
Cewar Abba Hakimi.
Ya bawa Mother takardar ta fara karantawa, ta jinjina kai tana sakin ajjiyar zuciya. Umma A'isha ta karanta itama, Dr A'isha data shigo yanzu ta miƙa hannu zata amsa Abba Hakimi ya ce "Aishatul-humaira bani nan" Umma A'isha ta miƙa masa.
"Abba mu gani,naga duk kun duba ko?"
"Eh, amma ba dole kowa ya gani ba" tai shiru ba don ranta ya so ba.
Halisa ta kalli Abba Hakimi ta ce "Da gaske Abbana ya sakeni Jon wuro?" Ta faɗa da ƙyar.
"Na ɗauka haka ki ke so?" Ta ɗaga masa kai zuciyarta na zafi da soya.
Ya ce "To meye na damuwar?" Ta fashe da kuka mai cin rai sai da tayi mai Isarta babu wanda ya tankata ta ce
"Kuma sai ta sakeni da ciki, daman da gaske baya so na? Zai je ya auri karuwa" mother tai murmushi a ɓoye
kafin ta ce "me zai sa ya zauna inda aka tsane shi? gashi can wata zata mutu akan son shi, aini naji daɗin haka kina haihuwa sai ki fito da miji musha biki" ta ƙara fashewa da kuka tare da miƙewa ta nufi bedroom ɗinta ta faɗa gado ta mance da cikin Jikinta birgima kawai take akan bed ɗin tana ihu tana tsinewa Zahrah albarka.
daga ƙarshe ta fara cilli da komai na bedroom ɗin ta rasa wa zata faɗawa damuwarta waye zai bata shawara mai kyau, Dr A'isha ce mai sonta kawai, kuma ya rabata da ita ta zauna tana ta kuka.
Ƙarar wayarta ya tsayar da ita daga kukan da take ganin sunan Dada ya sanya taji zuciyarta ta karaya ta ɗaga wayar murya a dashe ta ce
"Hello!" Dada ta ce
"Kin kyauta Danejo, Allah ya yi miki Albarka, ko da wasa naga ƙafarki gidan sarauta sai ranki ya ɓaci, idan har sbd haka ki ka aikata abin da ki kai"
Cikin kuka ta ce
"Hande en boni na lalashe me na yi kuma?"
Dada ta ce "Ba ke ba, hatta ni Besty nada iko dani balle ƴar dana haifa, ke ko nauyin furfurar shi ba kiji ba? Shekarunsa? Darajar ilimin addinin shi,ki zubawa idanunki toka sbd baki data ido ki ce wai ya sake ki? Kin san hukuncin macan dake neman saki wajan mijinta? Kin san azaba da tanadin da Allah ya yi musu? Wallahi ba ruwana wannan ba tarbiyyar dana baki ba, akwai wacce ke son lalata mini ke, ko kuma wata ɗabi'a ki ka sauya wacce ban sani ba, ki tuba ki bi Allah"
Tunda ta fara magana Halisa ke kuka ta ce
"Ya zan yi Dada? Ban taɓa ganin mahaifata ba, ban zauna tare da mahaifina ba ko sau ɗaya ba, ban san ƴan-uwana ba, shi ya fara ɗorani a hanya har naji zan iya masa komai ya gaji ya kai ni" ta saki kuka ta ce "kuma fa baya so na, wai Zahrah zai aura ina laifin ya nemi auren wacce ban sani ba ya san na tsaneta ba, kuma ya yi mini al'ƙawarin ba zai auri kowa ba.....,"
Dada ta katse ta da faɗin
"Tunda shi bashi da hankali kamar ki ko? Besty ni ya yiwa biyayya, ni na shaida masa bana buƙatar zuwanki masarauta, sbd ban manta wahalar dana sha ba, na ce sai naga yadda zamana ya kasance da sauyawar al'amarin zan bashi damar ya kawo ki, umarni na ya bi, ni zaki tsana Danejo ba Abban naki ba, batun Zahrah kuma ke ki ka bawa mijinki lasisin damar kula wata har ya aureta, ni na ji daɗin haka gobe wata mai irin halinki ta kuma, Zahrah kuma daman son shi yake yana aurenta ki kaɗe har ganye sai a fara lissafa miki aure tun yanzu"
"Dada don Allah zan zo wajan Mai martaba wallahi zuciyata babu daɗi" Dada dake kan layi ta ce "Kin san Allah babu inda zaki zo, ko kinzo sai na saka Khalil ya dawo dake ko El-bashir"
Ta haɗe rai ta ce "Ni ki daina haɗani da wani El-bashir" ran Dada ya sosu da halin Halisa ta ce "Ɗan uwan naki ki ka tsana? Akan wanne dalili" tai shiru domin da kunya ta ce akan Yaa Sheikh ta tsani El-bashir
"Zan zo kai lefen Besty ne zaki bayani" kafin tai magana ta kashe kiran
"Lefe?" Ta furta a fili kenan aure ya tabbata Yaa Sheikh ya kasa jure fushin zai auri Zahrah mai yasa zai hukunta ta da hakan? Ta ce
"Na tsaneka, bana son ka" A can parlour bayan tafiyar Dr A'isha Abba Hakimi ya ce "Koda wasa kada wani ya kuskura ya shaida mata ba saki bane, zuwa lokacin da za ta gaji da kanta"
"Ya batun auren Zahrah gasky ne?" Ya ce
"Ba wanda zai iya tsayar da Malam, zuciyar shi ba irinta kowa bace, baya son Zahrah amma ba zai iya bari ranta ya salwanta ba, kuma ta rantse idan bai aureta ba zata iya kashe kanta, ya ɗauki kasadar zai yi Jahadi kuma zai riƙe Muhammad ya dawo wajan shi, ya yi masa riƙo da zuciya ɗaya saɓanin yadda Engineer Aliyu ya riƙe shi, zai ramawa kura anniyyarta"
"Amma ban ji daɗi ba, bai dace Yaa Sheikh ya auri wacce Engineer ya sani ba" Murmushi kawai Abba Hakimi ya yi ya ce
"Me ya sa zaki haramta masa abin da Allah ya a halarta masa? Mata tunaninku da ban yake" ya miƙe tare da ficewa.
Zahrah na kwance hannunta ɗaya manne da drip ɗayan kuma jini ke shiga a hankali, ta rame tai baƙi ta fita daga cikin hayyacinta bakinta ya bushe ba kowa ake bari ya shiga inda take ba,
Kallo ɗaya zakai mata ka zubar mata da hawayen tausayi, ko nono Muhammad baya samun shi kullum cikin shan madara yake.
Dr ya gama duba ta ya juya yana fitowa Mimi ta ce "Dr ya ake ciki?" Ya sauke numfashi ya ce
"Kuyi mata addu'a, zuwa lokacin da Allah ya nufa zata tashi idan mai tsayin rai ce"
Ta juya ta kalli Alhaji Farouk cikin kuka ta ce
"Alhaji kwanakin ka biyu da zuwa Kano, amma babu Yaa Sheikh ba alamar shi, don Allah kayi wani abu kada Zahrah ta mutu akan Soyayya wacce irin Masifaffiyar soyayya ce wannan? Wlh ko a film da labarai na littafai ban taɓa ji ba, Allah ka dubi idanuna kada ka hukunta mini Zahrah da soyayya"
"Allah zai shiga lamarin In sha Allah" Mimi na ƙoƙarin magana suka ji ƙamshin turaren Roja ya mamaye wlrd ɗin da suke zaune. Ta ɗago da sauri Idanunta ya sauka akan Yaa Sheikh da Umar-khan sai wani kyakkyawan Bafullatani da kuma Surry.
Wai, dole Zahrah ta so Yaa Sheikh mutum bai nagarta da tsantsan addini da nutsuwa da kamewa har haka
Sai bazan ƙamshi yake idanunsa cikin white Sunglass wanda ya ɓoye faɗawar na shi Idanun,
Farar shadda ce a jikinsa sai ɗaukan idanu take babu Alkyabba dai hirami kafaɗa da kan shi, alamun har ya yi wanka ya sauya kaya a hotel ɗin daya sauka.
Mimi da Alhaji Farouk suka miƙe, Alhaji Farouk ya miƙawa Yaa Sheikh sukai subawa a hankali cikin nutsuwa ya ce
"Ya mai jiki?"
"Jiki sai addu'a Yaa Sheikh" Ya jinjina kai yana duba lokaci kafin ya ce "Allah ya bada lafiya"
Umar-khan ya ce
"Za mu iya ganinta?"
Da sauri Alhaji Farouk ya ce "Eh, In sha Allah muje muje" gabaɗaya ya ruɗe sbd nutsuwar Yaa Sheikh da kwarjinin da ya yi masa a idanu.
Jagora sukaiwa Yaa Sheikh har zuwa ƙofar shi kaɗai Dr ya bawa damar shiga. Tana kwace amma sai da zuciyarta tai kyakkyawan bugawa sbd ƙamshin turaren shi wanda ba zata taɓa mancewa da shi ba, ta rufe idanu hawaye na silalowa daga gefen idanunta, sai yaushe zata daina mafarkin shi? Komai na shi gizau yake mata ta kasa jurewa ta amsar ƙaddara. Yana tsaye kanta yana mmkin yadda ta faɗa ƙwarai duk ta lalace,