Showing 66001 words to 69000 words out of 197828 words

Chapter 23 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9292

Halisa ta kalleta da sauri zuciyarta har ɗagawa yake sbd jin zata wajan Yaa Sheikh.
Ta juya idanunta fal hawaye tare da barin ɗakin. Zahrah ta nufi part ɗin Yaa Sheikh ko'ina na part ɗin gwanin sha'awa ne, ko wacce kusurwa an kafe kalmar sunan Allah, a hankali sautin ƙira'ar Alkur'ani ke tashi, amma ta nemi ƙofar bathroom ɗin nasa ta rasa. Ta juya da sauri zuwa sashin Ummul ta sameta tare da Bara'at daga tsaye ta ce "Naje part ɗin Yaa Sheikh na rasa ina ne bedroom ɗinsa, ina buƙatar sani sbd ina son kasancewa da mijina"
"Amma shi mijin na son kasancewa dake?" Cewar Ummul. Zahrah ta ce "Ni matarsa ce, dole ya buƙace ni" Ummul tai murmushi ta ce "Zahrah ki zauna muyi magana mai muhimmanci, maybe ki gane sosai" Zahrah ta ce "ki riƙe maganarki mijina nake tambaya" Ummul ta ce "Malam yana kan rabuta Alkur'ani yanzu, kafin azumi yake son kammala rubutun, ba zai iya ganin kowa ba" Zahrah ta juya rai ɓace gashi masifa ke cinta kamar taci babu.
Ummul bata da zaɓi wanda ya shige faɗin hakan, tasan ba lallai Zahrah ta samu abin da take so ba. Washegari tun da Halisa ta tashi bata da wani karsha shi ta wakana da tunanin ko Zahrah ta je wajan Abbanta? Tai sallah Asuba tare da Azkar ɗin da Ummul ta bata, 6:30 ta nufi kitchen tasan a nan zata samu Ummul ɗin, Tana zuwa Bara'at ta ce "Sannu da zuwa Halisa" Suhaima ta ce "Baki zo da wuri ba" tai murmushi kawai ta ce "Ina kwana Ummul?" Cike da farin ciki Ummul ta ce "Allhmd. Sanyi bai ka maki ba?" Ta ɗaga kai tana taya Bara'at aiki tare da ita suka kammala breakfast. Ummul ta bata shayin Yaa Sheikh ta kai masa bayan ta shirya zuwa kayan makaranta. Ta amshi shayin ta mufi part ɗinsa kai tsaye.
Fitowar sa kenan sbd barcin da bai samu ba jiya, kana kallon yanayinsa da sauyin idanunsa kasan akwai matsala. Yana zama kan kujera ta shigo bakinta ɗauke da sallama ta ajjiya tray ɗin tana zubewa wajan ƙafafuwansa ta ce. "Abba ina kwana?" Ya jinjina tare da zuba black tea ɗin ya shiga sha a hankali ta gyara zama ta ce "Abba" ya ware ido a kanta ba tare daya tanka ta ba. Ta ce "Anti Zahrah ta zo jiya?" Hawaye ya cika idanunta ganin ya kasa cewa komai, zai gumi dake tsastsafo masa ta goshinsa jijiyoyin kansa sun ta shi. Ya ajjiye mug ɗin hannunta bayan ya gama shan tea ɗin tare da miƙewa tsaye, ta miƙe da sauri ta ce "Abba baka da lafiya?" Sai a lokacin sauke numfashi yana jin kansa kamar zai rabe yana ɗan yin gaba ya ce.
"Ki kula,ba wasa" ranta bai mata daɗi ba, shi kansa ya kasa riƙe sauyin nasa gudun kada wani ya ankare baya son kuma Ummul ta san halin da ake ciki... Ta fita tana jin kamar kada taje makarantar.
Har ta yini a makaranta cir bata da wata walwala haka kurum ta tsinci kanta cikin sukuni, Abir tai ƙoƙari sosai wajan fahimtar da ita duk subjects ɗin da sukai attending. Har suka taɓa hira sai lokacin ma Halisa ta saki jikinta jin Abir itama asalinta ƴar Nigeria ce.
Yau ma Umar-khan ya dawo da ita ya lura da sauyin nata bai kulata ba, tunda ba huruminsa bane yin magana da matar malam ɗin. Tana shigowa gidan bata nufi part ɗin Ummul ɗin ba, ta nufi Main parlour zata shige part ɗin ta Zahrah ta ce.


"Yawwa ke nake jira dama, ki shirya zamu asibiti" Halisa ta kalleta tana mmkin waye babu lfy kuma? Sai kuma gabanta ya faɗi ko dai Abbanta ne bashi da lfy, ta rikice rikicewar da Zahrah taso ta ɗaure mata kai ta ce.
"Bana son shirme mene haka kuma? Kije kafin mu tafi ki gyara mini ɗaki kizo ki ɗan danna mini ƙafata" Halisa ta tsurawa cikin Zahrah idanu har bata ji abin da Zahran ta faɗa ba, tayi saurin jan riga ta rufe cikin da ya ƙara girma fiye da ko yaushe.
Ta juya tare da shigewa part ɗin nata, duk ta gigice tana shiga kuma ta fara duba maganin da El-bashir ya bata, ƙila shi ne maganin da Abban nata yake sha bata sani ba. "Kayi haƙuri Abba, laifi na ne" ta faɗa a sanyaye idanunta na cika da hawaye.
Zahrah ta miƙe tare da shigewa ɓangarenta, kai tsaye wayarta ta ɗauka tare da kiran number Deen, kamar wanda yake jiran kiran nata yai picking call ɗin ta ce "Akwai matsala Deen" ta cikin wayar ya ce.
"Yanzu muka fara samun matsala idan har ba zaki abin da ya dace ba, yanzu mene?" Ta ce "Cikin nan girma yake, yau ƴar fillon nan ta gani amma kamar bata gane ba, kasan kamar shirme ya yi mata yawa, shi ya sa na zaɓi nayi aikin nan da ita" Deen dake zaune idanunsa sauke akan wata Balarabiyya dake ɗakinsa ya ce.
"Kada ki damu da wannan ƴar fillon na yanke shawarar abin da za mu yi mata, kawai ki tabbatar Yaa Sheikh ya samu kusanci da Halisa, ki daure ko a tea ne ki zuba maganin feeling ɗin, yana da ƙarfi sosai" Zahrah ta sauke numfashi ta ce "Amma kada a raunata ƴar mutane, nice daidai da Yaa Sheikh mai zai hana ni naje gareja bana tunanin zai gane bani da budurci" Deen yaja tsaki sosai ya ce "Kina da matsala Zahrah,ki fito kice bana gamsar dake mijinki kike buƙata tunda naga alamar ba sanya a wannan ɓangaren ba, listing to me Zahrah nasan waye Yaa Sheikh, nasan shi sanin da zaki mamaki, duk yadda kike tunanin basirarsa ya shige nan, duk abin da zai same shi yana ji a jikinsa, ki tura yarinyar kawai babu damu da duk irin abin da zai mata ba" ɓoyayyan numfashi ta sauke tare da shafa cikinta wanda ya fara motsawa alamar yana cikin ƙosashiyar lafiya ta ce "Deen what's your plan?" Ya ce "ban gane ba? Ina tare dake muke tsara plan ɗin? Are you doubting me?" Ta kasa cewa komai sai kashe wayar da tayi. Ta shiga zirga-zirga a bedroom ɗin duk ranar da Yaa Sheikh ya kusanci Halisa maybe ita kuma zuciyarta ta buga, a ƴan kwanakin nan wata sabuwar Soyayyar Yaa Sheikh ta wanzu a zuciyarta, duk da bai bata wata dama ta Kasancewa dashi ba, amma kullum da soyayyar shi take kwana a rai.
A hankali Halisa ke tafiya cikin wasu kayan shan iska sbd sanyin garin ya lafa, ta sauke numfashi ganin Zahrah bata parlour kai tsaye ta nufi part ɗin Yaa Sheikh, ta shiga bakinta ɗauke da sallama Umar-khan dake yiwa Yaa Sheikh bayani ya ɗago kansa tare da kallon Halisa, da sauri ya ɗauke kai ganin kayan dake jikinta, Yaa Sheikh dake jingine jikin kujera sanye da Jallabiya sabuwa kamar ko yaushe ya miƙe tsaye tare da amsar ducoment ɗin da Umar ke basa, Umar ya ce "Ban gama yi maka bayani ba" Yaa Sheikh shiru da Umar ganin haka yasa Umar miƙewa yana ɗauke idanunsa daga kan Halisa, Ta ce "Umar-khan teacher ya ce gobe ka same shi a officer" ganin kamar bai jita ba yasa ta sake cewa "Umar-khan, Umar-khan" ta faɗa tana ƙoƙarin bin bayansa cak taji anyi sama da ita tare da nufar bedroom da ita.....Ya direta gabansa yana binta da gajiyayyun Idanunsa masu kaifi, ya shiga ƙarewa kayan jikinta kallo can dai ya juya zuwa wani ƙaramin bedroom dake jikin wanda suke ciki, ya dawo hannunsa riƙe da hawaya bai ce mata komai ba, sai hannunta daya kama zuwa bakin gado ya nemi waje ya zauna tare da zaunar da ita a gefensa. "Kina son Allah ya kama ki ne matar malam?" Ta marairaice tana narke fuska ta ce "Abba me na yi? Kuma wai baka da lfy naji Anti ta ce wai na shirya zamu asibiti" ya dubeta da kyau tare da kawar da batun Antin ya ce. "Baki san me ki kai ba? Ki nutsu ƴar fillo" ta tura baki zata ta shi ya tsare ta da idanu sosai kafin ya yi magana wayarsa ta fara ringing ganin sunan Abba Hakimi yasa Yaa Sheikh ya danna wayar a handsfree.
"Malam, ina ajjiyata ne?" Halisa tai murmushi jin muryar Abba Hakimi, kafin Yaa Sheikh ya ce wani abu ta ce "Jon wuro" Abba Hakimi ya saki murmushi ta waya ya ce "To matar ni dai ban iya yaran nan ba, dama dai Abban naki ne" ta juya tare da kallon Yaa Sheikh taga idanunsa a rufe amma kamar mai jin zafi duk zufa ta gama rufe masa fuska sai gemunsa yake shafawa.
"Jon wuro Abba ya iya fillatanci ne?" Abba Hakimi ya ce "Eh sosai, fiye da ke ɗin, baki taɓa ji ya yi bane?" Ta ce "Jon wuro ai baya nunawa yaji me nace ko da fulde nai magana, to Bafullatani ne Abban nawa?" Abba Hakimi ya ce "Matar baga ki kusa dashi ba? Ki tambaye shi, ni dai nasan duk wani motsi na Fulani a idanunsa yake" tai murmushi kawai har lokacin kallon Yaa Sheikh take shi kuma yaƙi yarda ya buɗe idanu, amma yana jin idanunta na yawo a jikinsa.
Abba Hakimi da yaji shiru ya ce "Abban naki yana kula dake? kuma yana kusa yanzu" da sauri ta ce "Ai shi ya ɗauke....." Tattausan hannunsa da taji a bakinta yasa tayi saurin zaro ido suna haɗa idanu ya ware mata ido yana ya mutsa fuska gaba ɗaya yanayinsa ya sauya jin tunan asirin da take shirin yi masa. Ya miƙe baki ɗaya yana daidaita zamansa ya zagaya hannunsa ɗaya ɓangaren nata.


"Shhhh" ya ce yana tare da yi mata alamar tai shiru. Abba Hakimi ya saki murmushi daga wayar kafin ya ce "Da alama kinyi nisan kiwo, ki bawa Abban naki" ta sauke numfashi bayan Yaa Sheikh ya zare hannunsa daga bakinta cikin ƙasa da murya ta ce.
"Jon wuro Abba ya ce nai shiru kada nace ya ɗauke ni" tamkar Yaa Sheikh ya ce ya shiga uku haka yaji shi kam tayaya zai fara nuna mata illar surutun nan? Abba Hakimi ya yi kamar bai ji ba ya ce.
"Me kika ce, ntwrk na rawa" Yaa Sheikh ya zare wayar tare da kashe handsfree ɗin a hankali ya manna wayar a kunnansa ya ce.
"Abba" ya faɗa tamkar baya son maganar. "Aliyu" Abba Hakimi ya kira sunan cike da girmama kamar yadda yawancin lokaci yake ambatar sunan kai tsaye. Yaa Sheikh ya ce "Uhm".
"Ina fatan baka mance deal namu ba, ka watsa mini ƙasa a idanu, kai tsaye na nuna buƙatar ka zauna da yarinyar nan, amma ka ce baka sonta? acikin shekara munci sati ko sama da haka, kamar yau Ubangiji zai nuna mini cikar shekarar. Wallahi Aliyu naga saɓanin yadda muka ajjiye yarjejeniyar zaka san bani da kirki zaka san waye Ostman-zannur" Yaa Sheikh ya juya tare da kallon ƴar rainon da ake kafa masa sharuɗa akanta cikin lafazi mai kyau ya ce. "Abba zan dawo da ita"
"Alfarmar riƙon nata ne ba zaka iya ba?" Yaa Sheikh ya ɗan ya mutsa fuska kaɗan ya ce "Ramadan zai zo Abba, ba lokaci ba zan iya ba" sautin murmushin Abba Hakimi ya ratsa kunnan Yaa Sheikh ya ce "Kai kaɗai ne a gidan? da wasa ka bari Matarka taci zalin Halisa wallahi sai nayi maganinku duk" kafin Yaa Sheikh ya sake cewa komai Halisa ta miƙe tare da zama kan ƙafafuwansa tare da zagaya hannunta ta riƙesa da kyau ta ce.
"Ina son ka Abbana, kuma...." Ƙitt Yaa Sheikh ya kashe wayar baki ɗaya yana rufe idanu tare da dafe kansa da hannu.
Tuni Abba Hakimi yaji abin da Halisa ta faɗa kafin Yaa Sheikh ya kashe wayar.
Halisa ita bata ɗauka wani abu tai ba ta ce "Abbana, ni ma kace kana so na" ya sanya hannu ya share zufar dake binsa kafin ya buɗe ido ya kalleta a hankali ya ɗagata da kyau ya zaunar da ita saman cinyarsa ya kifa fuskarsa daidai nata numfashinsa na sauka a hankali saman nata ya jima yana sauke Afra kafin ya ce.
"Me... Me.. me..." Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! In-ina ta dawo sabuwa a lokacin da bai zato ba, kuma daman tuni tuni jikinsa ya bashi hakan zai iya faruwa. Ta zuba masa idanu ganin yadda yake ɗan karkatar da kai yana damƙe hannunsa.
"Abba kayi haƙuri ban sakewa ka yafe mini" ya girgiza idanunsa sukai jajir cikin son nuna mata kuskuren kaifin bakinta ya tallafo haɓarta sai kuma ya saka ya riƙe hannuwanta da kyau ya ƙanƙame, yana buga ƙafa duk don maganarsa tazo amma abu ya gagara. Ta zuba masa idanunta wanda ya cika da ƙwalla sosai tsoron da tausayin Abban nata ya ɗarsu a zuciyarta. A hankali ya zame hannunsa zuwa rigarta ya riƙe gaban rigar da kyau yana cukurkuɗata ba tare da sanin cewa gaba ɗaya rigar ya tattare ba, ya jawota kusa da shi sosai ba tare daya haɗe jininsu ba, wasu hawaye suka kwanta a idanunsa na zallar asabar fitar maganar. Tamkar wanda zai shaƙeta haka ya rirriƙe gaban rigarta ƙwayar idanunsa kwance cikin nata, cikin Muryar In-inar ya buga ya ce.
"Ma...mama.... Mata ma matar maaa ma malam...." Ya faɗa yana buga ƙafa Halisa ta saki kuka bana shaƙar da ya yi mata, na tausayin Abban nata na, da yanayin da taga ya shiga ta ɗauka duk rashin lafiyar ce. A hankali ya saketa tayi sauri ta zame jikinta tare da shigewa cikin jikinta ta rungomesa cikin kuka ta ce. "Abbana" ya dubeta kana ya ɗauke yana shafa kanta a nutse. Ganin kuka take da gaske ya ƙara tallafo fuskarta tare da kama hannunta ya ɗora a ƙirjinsa, wani irin bugawa sosai taji saitin zuciyar shi nayi kamar zata tsago ƙirjin shi ta fito.
"Shhhhh" kalmar ta ƙwace masa yana mai lumshe idanunsa tare da buɗewa ya zareta a jikinsa ta ƙwace ta koma tana ƙara riƙesa. "Abbana ka barni" ta faɗa a tsorace shi kifa kansa kawai ya yi a wuyanta sbd tsananin yanayin dake hura wutar abin da yake ji, ya jiƙe sharkaf da gumi. Ya goga hancinsa a wuyanta tayi saurin kallonsa ta ce "Modibbo" ma'ana Malam ko malami, ya cireta a jikinsa yana miƙewa tsaye itama ta miƙe da sauri wata Jotter ya ɗauka da pen ya shiga yin rubutu cikin good handwriting. Yana jin hakan da ya yi shi ne mafita, idan akwai divorced tsakanin su dole Abba Hakimi ya daina tunanin wani ba. Bayan ya gama rubutun ya naɗe tare da sakawa cikin envelope.
"Abbana mene wannan" ya dubeta tare da tsugunawa daidai da ita a hankali ya ɗaga ta ya ɗora saman ƙafarsa ɗaya a taushashe ba tare da rauni ko yanayinsa ya sauya ba.
Cikin sakin harshe saɓanin ɗazo ya ce "Matsayinki ne a nan Matar Malam, ki yafe mini kinji?" Bata gane ba dan haka tai murmushi ta ce "Abba nima ka yafe mini naji tsoro" ya shafa kanta kana yaja ƙaramin sirrin hancin ya ce.
"Ga Malaminki ba tsoro, kina ji ni ba mijinki bane zanci gaba da riƙeƙi matsayin ƴa" ya ɗan yi shiru yana sauke numfashi ya ce.
"Ba zaki gane karatun ba yanzu, ki riƙe wannan a wajanki zuwa shekara guda, yanzu ke ƙawata ce ki cire miji a bakin ki" tai murmushi bata fahimta amma haka kurum jikinta ya yi sanyi, duk wata mace da aka saka dole ta samu wannan raunin. Ya miƙe yana cewa "Muje muyi darasi"


Zahrah ce gaban likita tana jin abin da yake faɗa ta ce "Da zan baki shawara ku bar cikin jikinki yana cikin ƙoshin lafiya sosai" Zahrah ta kalli Deen dake kusa da ita ta ce "Dr akwai matsala ne, ko nawa ne zan iya baka, ayi duk yadda za ai cikin nan ya kwanta zuwa wasu watanni" Dr ya ce "Ki fahimta wannan ganganci ne" Deen ya gyara zama fuskarsa da face mars ya ce "Daga miliyan 5 zuwa sama ka faɗi abin da kake so, ka yi mata scanning da sai nuna cuta ce a cikinta harta kumbura, za ai mata aiki zuwa watanni huɗu ko biyar" likitan ya yi murmushi ya ce "Wannan ba damuwa bane, ka bada kuɗin duk sanda kuka shirya sai kuzo" Deen ya ce "Your Account number, zan kiraka idan zata zo, ya zama sirri bana lamuntar ha'inci da cin amana, zan iya ɓatar da mutum" Zahrah ta ce "Dr macan da bata fara al'ada ba, zata iya ɗaukan ciki?" Ya girgiza mata kai ya ce.
"Al'ada Ita ce hanyar dake nuna cewa mace ta shirya amsar namiji, kuma zata iya amsar dukkan wasu ƙwayaye da zai zuba mata, sai dai bisa tsari ƙwan ɗaya ke nasarar samu shiga cikin wani gurbi na mahaifa, idan ƙwan namiji guda biyu ya samu damar shiga cikin mahaifar mace lokaci guda, shi ne ake iya samun twins, twins ɗin da suke a mahaifa guda sune ake kira da identical twins, masu tsananin kama da juna, wanda suka zo a mahaifa daban daban suna iya kama amma ba can ba, mahaifa na buɗewa ne lokacin da mace ta fara al'ada magana ya gaskiya babu yadda za ai mace ta samu ciki ba tare data fara al'ada ba, wannan shi ne" Zahrah ta sauke nauyin jin daɗi kana ta miƙe daga nan Hotel ta nufa, tana murna plan ɗinta zai cika cikin ƙaramin lokaci.
Daman dai fargaba kada ace Halisa ta samu ciki a mu'amalar da zatai da mijinta, amma yanzu ta samu nutsuwar zuciya.


Washegari bayan Halisa ta tafi makarantar Yaa Sheikh na gida sbd baƙin da zai masu ɗaukan tafsir da ake sakawa a Channel. Ummul ta kallesa ta ce. "Ka tafka babban kuskure Aliyu, mene amfanin abin da kayi? Idan zaka rabu da ita mene yasa ka aureta tun farko?" Kansa a ƙasa domin yana martaba Ummul ƙwarai da gaske. Ya kalleta yana miƙewa tsaye ya ce "Ƙaddara Ummul, ƙila ba rabon zama Inuwa ɗaya, mganar ya tsaya iya mu" Ummul ta goge hawayen idanunta ta ce "Malam kada ka manta kai da kanka ka zaɓa mata suna Halisa, kai ne kayi mata huɗu ba, kai me ka reneta meye duk wannan wanne irin abu ne? Zaka yanke hukunci ba shawara" ya juya kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login