Showing 60001 words to 63000 words out of 197828 words

Chapter 21 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9291

baby hijab a kanta, kai ya ɗauke ta ce.
"Anti Zahrah ba ta shi ba, ni tun ɗazo na tashi ina ta kallo" shi dai bai ce komai ba ya shige part ɗinsa tabi bayan shi da kallo kafin ta juya zuwa kollon girke-girken da ta keyi.
Yana shiga part ɗin sa ya zauna saman kujera, tare da kiran number Umar-khan babu jimawa ya ɗauka a nutse ya ce "Ka yi komai, kada ya shige kwana biyu a nemi gurbin karatun" yana faɗin hakan ya kashe wayar, tare da kiran wata number mgn ɗaya ya yi ya kashe..
Halisa na zaune taji telephone line na ƙara ta miƙe sauri daman Umar-khan ya faɗa mata yadda ake amfani da ita, tana ɗagawa taji ance "Mrng maaa, the breakfast is ready Yaa Sheikh na jira" Halisa ta ce "Kika ce me?" Ta ce "Abincin Yaa Sheikh ya kammala kina magana da ɓangaren kitchen, yanzu maid zata kawo" Halisa ta taɓe baki tare da komawa ta zauna, babu jimawa wata mata mai fararen kaya ta shigo ɗauke da tray da butar shayi ta ce "Mrng Maa ga shi Yaa Sheikh na jira"
Halisa ta amsa tana miƙewa tsaye Zahrah ta fito cikin kayan barci da alama ko sallar ba tai ba, ta kalli matar ta ce "lafiya?" Tai mata bayani ta ya mutsa fuska ta ce "Ok daman ita ce mai aiki bata ta kai, ki sama mini breakfast mai kyau yanzu" matar ta juya Halisa ta riƙe tray Zahrah ta ce "Sai ki fara aikin ki tun yanzu, kije ki kai masa breakfast ɗin ki dawo ki shirya mini kayana a wardrobe" Halisa ba ta ce komai ta juyawa zuwa inda taga Yaa Sheikh ya nufa, bakinta ɗauke da sallama bata sani ba ko ya amsa ko bai amsa ba, yana zaune kan kujera ta ƙarasu har inda yake ta tsuguna ta ce "Ga shi wai" ya gyara zama yana tsiyaya tea ɗin tare da kaiwa bakinsa. "To kai iya wannan kake sha ne? Ko nayi maka abinci?" Da idanu kawai yake bin gefen fuskarta da kallo ta gyara zama ta ce "Mother ta ce kai mijina ne" ya ware idanu da sauri yana binta da idanu, ta buɗe baki zata sake magana caraf ya saka hannu tare da kame bakin.....


08119237616
Paid book
Not edited_I unite you with the greatness of God a daina fitar mini da littafin IDAN BA KE. What you want will not be difficult for you to buy. This is not appropriate at all.🫰🏿har zuwa ake a nuna mini wai an samu book ɗin Idan ba ke as free irin ga masifaffiyar nan bari nai ta ihu a media😂 I love my book lovers wherever they are. Amma don Allah a daina fitar da book ɗin... It's 500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616_




Kasa ƙarasa maganar ya yi sbd gemunsa data kama tana cewa "Yasunan wannan abun? Kuma da gaske ni matar malam ce, naje na faɗawa Ummul nace kace mini matar malam?" Ya lumshe idanunsa na wani lokaci kafin ya buɗe su a kanta tare da ɗora hannunsa akan nata data riƙe gemunsa ya zare yana girgiza mata kai.
Zata sake yin magana ya miƙe tsaye yana nufar hanyar bedroom ɗinsa dole sai ya sauya kaya gaba ɗaya ta goge masa maiƙon hannunta a jiki, da sauri ta biyo bayansa ta ce "To baka faɗa mini sunan wannan dugun abin ba, kuma waye zai kaini makarantar ina son zama babbar mace" ya juya tare da kallonta a nutse yana mai mamakin surutun ta, yana da masaniyya akan yadda take amma bai ɗaukan surutun ya yi girma da tsayin haka ba. Bai ce mata komai ba ya juya yana mai sakin murmushi shirmanta a karo na farko da suka kasance tare domin sauran duk baɗini yake ganinsu. Ummul na kitchen Halisa ta dawo ta kalleta cikin kyakkyawan lafazi ta ce "Ba dai haka kika je da hannunki ba?" Ta kalli hannun kuma ta kalli Ummul ta dafe ƙirji ta ce "Wallahi na goge masa" Ummul tai shiru daman tasan za a rina, kuma sam ba tayi mamakin hakan ba. Maid Suhaima ta ce "Wa kika gogewa?" Da sauri Halisa ta ce "Malam, nikam ya sunan wannan dugun abin na fuskar shi? naji yana da laushi aradu" Ummul ta dafe kai da sauri kuma ta miƙe tsaye tana kama hannun Halisa suka nufi can part ɗin Ummul ɗin.
Bayan sun shiga Ummul ta kalli Halisa sai kawai tai murmushi kafin ta ce "jeki wanke hannun ko?" A sanyaye ta ce "To" ta nufi bathroom ta wanke tas tare da wanke bakin ta fito har lokacin Ummul na zaune tai shiru tana kallon hanyar toilet ɗin, ganin yadda Ummul tai shiru yasa Halisa faɗin "Ummul" ta buɗe idanu ta ce "Kin gama? Lokaci na tafiya zaki buƙaci abinci a can, lunch box naki yana cikin mota" suka fita Main parlour daidai nan Zahrah ta fito da kayan barci da alama ko sallah ba tayi ba, balle ashirin zancan wanka tabi Ummul da kallo ta ce.
"Wace ke? daga ina bana hana ana shigowa kai tsaye ba, ba tare da permission ba, ke kuma jeki gyara mini bed ki haɗa mini ruwan wanka" Halisa ta ce "makaranta za a kai ni, idan na dawo zan haɗa miki sai Kiyi wankan" Ummul ta danne dryar data zo mata. Da mamaki sosai Zahrah ta ce "School? Da izinin waye kuma? babu wata makaranta da zaki, baki zo gidan nan dan kije makaranta ba" ta faɗa tana fisgo hannun Halisa daga kusa da Ummul.
"Ke kuma da kika tsaya kina ƙwalala mini idanu da alama kina da masaniyya, tell me waye zai kai ta makarantar"


"Ni ne" ya faɗa a taushashe yana mai fitowa daga inda yake tsaye, yana sanye da sabbin shiga saɓanin ta ɗazo, farar dakakkiyar shadda ya sanya mai jamper da babbar riga, ya ɗora hirami ɗaya a kansa ɗaya kuma a kafaɗa..
Ta saki Halisa ta nufi inda yake ta ce "My Excellency amma daga zuwa sai batun makaranta, kuma ya kamata a faɗa mini, ni bani da ra'ayin yarinyar nan tai makaranta" Halisa ta tura baki tana mai jin haushin yadda Zahrah ta wani matsa kusa da Yaa Sheikh haka kawai taji zuciyarta ta cunkushe, amma hakan bai hanata cewa. "Amma ai Dada tana da niyya ko Anti, da izinin zani makaranta ta baki...." Cikin rawar murya Zahrah ta ce "Oh ok it's ok you can go, but waye zai kai ta?" Sai a lokacin Ummul ta ce.
"Umar-khan, kafin driver ya fara kai ta, Aliyu yana da lecture da ɗaliban shi, zai iya magana" Ummul ta faɗi haka ne domin Zahrah ta bawa Yaa Sheikh hanya. Haka kurum Zahrah taji sha'awar kasancewa da mijinta ya bijiro mata, musamman da ƙamshin Roja ke ƙara narkar da zuciyarta, Yaa Sheikh na musamman ne, idan zaka kalli cikin idanun shi yayin magana to ba zaka taɓa yi masa ƙarya ba, ɗaya daga cikin baiwar shi kenan. Babu kunya ta rungome shi a gaban Ummul tana faɗin "Am going to miss you My Excellency back soon please" gani sukai Halisa ta juya da sauri zuwa part ɗin ta, Ummul ba tai magana ba. A hankali ya zame jikinsa daga na Zahrah ta ce "Bari naje nai wanka da Sallah bye" Ummul ta kalli lokacin 7 harta gota ba dai sallar asuba ba, sai dai walaha.
Bayan shigewar Zahrah Yaa Sheikh numfasa yana mai gyara murya a kasalance ya ce.


"Mun kwana lafiya,
Ummul?" Ummul ta ce "lafiya lou, kaga ƴar rigima ko? kamar kuka naga ta nayi?" Ya saki fuska daga kamewar da ya yi shima yana duba lokaci a diamond rolex watch ɗinsa.
"Aje a duba, kin san hali tun ba yau ba" tai murmushi ta ce "Wallahi fa" ta nufi part ɗin Halisa shi kuma ya goya hannunsa a baya tare da tsaiwa a tsakiyar parlourn. Kwance Ummul ta samu Halisa ta cire baby hijab ɗin jikinta sai kuka take kamar ranta zai fita. Ummul ta zauna cikin sakin fuska ta ce "Matar Malam lafiya? Wani abun ne? ko wani gurin ke miki ciwo?" Kuka kawai take taƙi magana tamkar zata shiɗe haka take kukan. "Faɗa mini mene? ke dawa" ta miƙe zaune cikin shassheƙar kuka ta ce "Ummul Dada zani, ni na fasa zaman wajan Dadata zani ki saka a bayar dani" Ummul ta ware idanu da kaɗuwa sosai ta ce.
"Yanzu Matar Malam ina ke ina zuwa gida, keda kika zo bautar Ubangiji? Maza tashi akai ki makarantar ga shi can yana zuwa kin san kuma akwai inda zashi" idanunta ya yi jajir hawaye na zuba daga cikinsu ta ce "banso, na fasa makarantar ni rugarmu zan koma" yin duniya taƙi yarda Ummul ta ce "To dai na kukan bari na faɗa masa" ta juya tana mmkin sauyin da yarinyar ta samu lokacin gudu, me akai mata me kuma ya sauya mata tunaninta daga sha'awar zuwa makarantar.
A tsaye Ummul ta same shi, bai kalleta ba amma tunaninsa da hankalinsa na kanta ta ce. "Kuka take sosai, wai bata son makarantar kuma a bayar da ita can ruga" maimakon ya fita sai ya juya zuwa part ɗin shi ba tare daya amsa maganar ta Ummul ba. Ta gane yaran kuraman nashi dan haka ta ƙarasa juyawa zuwa sashin na Halisa. kanta kife idanunta data rufe su take hango rungumar da Zahrah taiwa Yaa Sheikh, kuma bata manta maganar da Maimoon ta faɗa mata ba, idan kana son mutum da zarar wata macen ta raɓesa zaka ji kishinsa, ita a yanzu ta kasa fahimtar me ya sa taji komai ya dameta zuciyarta babu daɗi ne? Da wannan tunanin Ummul ta dawo ɗakin tare da ce mata "Ki saka hijab ɗin, kije Abban naki yana kira zai mayar dake" ta kalli Ummul sosai amma bata ce komai ba, hijabin a hannu ta nufi part ɗinsa. Ummul ta girgiza kai tana sakin murmushi kawo yanzu ta gama gane abin da ke damun Halisarta ta fahimci zallar rigima da shagwaɓa ce ke damunta akan dalili mara toshe.
Yana zaune hannunsa riƙe da azkar yana dubawa yaji saukar siririyar muryarta tayi sallama, amsata ya yi a rai, yana mai ɗago kansa tsaye ya ganta taƙi ƙarasuwa sai cukurkuɗe hijab ɗin hannunta take. Shi bai fiya son yin surutu ba kwana biyu kuma tana neman sashi, gashi kamar ciwon kanshi na neman ta shi. Ajjiye azkar ɗin hannunsa ya yi, tare da miƙa mata hannunsa alamar tazo, kanta a ƙasa ta matsa inda yake zata zame a ƙasan ƙafafuwansa ta zauna a ƙasa ya kamo hannuna tare da zaunar da ita a gefen shi yana kafeta da idanunsa. Kafin ya ce komai ta fashe da kuka sosai tana jan numfashi, ya tallafo haɓarta da hannunsa mai taushi idanunsa na yawo a fuskarta.
"Ya akai?
Ke dawa?" Ya faɗa yana mai sauke numfashi tare da jan jikinsa zuwa jikin kujerar. Muryata na rawa ta ce "Abba gida zani, ni Dadata zan koma" ya lumshe ido kana ya buɗe a sauƙaƙe cikin son dakatar da kukan dake neman fasa masa kai ya ce. "Karatun fa? Ban son rigima" ta girgiza suna haɗa ido ta tura masa baki ta ce "Shi ma banso, kuma..." Sai kuma tai shiru tana ɗauke kai.
Kallon yadda fuskarta tai jajir ya yi sosai duk ta birgita kanta sbd rigima, he's still holding her face ya fesar da iska ya ce.
"Gida kike so? Ta ɗaga masa sai kuma ta ce "Eh wajan Dada zaka kaini kaji Abba"


"Baki son Malam?" Ya tambaya kai tsaye domin shawo kan rigimar tata, ta riƙe hannunsa ta ce "Ina so bana, to ba naga Anti Zahrah ta rungomeka ba, shi ne naji kawai kuka yazo mini kaga gwanda na tafi gida" ya miƙe da sauri tare da shigewa bedroom ɗinsa not too long ya dawo fuska a kame, a tsaye ya sameta kallon da yake masa yasa ta saka hijab ɗin. Kana tabi bayansa babu kowa a main parlour dan haka ya nufi compound direct.
Yana zuwa Umar-khan na fitowa daga mota tare da faɗin. "Good Mrng Yaa Lee" kai ya ɗaga masa ya shiga bayan mota, itama Halisa ta shiga bayan motar gatekeeper ya buɗe musu fita.
Sun jima da tafiya amma abin mamaki Halisa bata ce komai ba, ko Umar-khan bata gaisar ba, a haka suka ƙarasa Al Aqeeq International School. Umar-khan ya yi parking a harabar makarantar tare da fita yabar musu motar, ƙoƙarin buɗe motar take ta fita taji ya kamo hannunta taƙi yarda ta kallesa alamar dai She's still angry with him. Wani sirrin baƙin zare ya ɗaura mata a hannunta, ya riƙo hannun da kyau ta yadda dole ne ta matso kusa dashi idan taji an jawota, sukai kusa da juna.
"Ƴar fillo" ya ce a hankali da sauri ta kallesa sai taga ba ita yake kallo ba, ta ce "gidan zaka bayar dani?" Sai a lokacin ya juya gaba ɗaya zuwa gareta a hankali numfashinsa ke sauka cikin murya ta yanayin gajiya da kasala ya ce.
"Anti ba zata sake ba,
Amma idan Anti bata rungome Malam ba waye zai rungome shi?" Bakinta na rawa ta ce "Ni matar malam zanyi" ya buɗe ido sosai da sosai yana mmkin ƙarfin halinta. "Da gaske ni kullum sai na rungome ka nace maka mijina" bashi da wani option wanda ya shige bin bakin mganar da kallo ya daɗe yana kallonta kafin ya ce.
"Uhm" da sauri bakinta na rawa ta ce "Ai na iya bari ka gani" kafin ya yi magana ko wani yunƙuri yaji gaba ɗaya ta zagaye hannuwanta tare da rungome shi, ta ɗora kanta a ƙirjinsa, ya buɗe idanu da sauri cikin In-inar data zo masa ya ce. "Su...su... Subuhanallah Ya Allah....Ta saki dry sosai ta ce "Abba Allah na iya kaji ai?" He was completely lost for words and just shook his head. Bayan wasu giftawar seconds ya nuna mata ƙofa da hannu ta buɗe ƙofa tare da fita, a hankali shima ya buɗe ƙofa ya fita tare da fitowa yana ƙara covering jikinsa da kyakkyawar shigar dake jikinsa. Umar-khan na ganin fitowar Yaa Sheikh ya ƙarasu wajan yana mai sakin murmushi,kai tsaye office ɗin headmaster school ɗin Yaa Sheikh ya nufa, gaba ɗaya teachers na school mmkin ganin Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu a cikin makarantarsu ya kama su, kowa sai durƙusawa yake yana miƙa gaisuwa a nutse cike da kamala nutsuwa yake ɗaga musu hannu yana ƙara kame kansa wanda yake fidda kwarjinin shi.
Cikin mutunci Headmaster ɗin mai suna Ayyan ya miƙe yana gaida Yaa Sheikh. Umar-khan ya ce "you did the interview for her, then you look at the one class that is suitable for her" Headmaster ɗin ya kalli Halisa cike da birgewa ya ce. "What's your name?" Tai ƙasa da kanta sam bata ji me yace ba, balle ta fahimci me yake cewa. Ya ɗauka bata gane english sai ya juya zuwa cewa.
"ma asmuk?
kam eumarka?" Nan ma tai shiru Ayyan ya kalli Yaa Sheikh cike da martabawa ya ce


"سنضعها في الصف الأول حتى تتمكن من أخذ الدروس"
_“Zamu sakata a matakin farko domin ta fara darasin”_ cewar Ayyan Yaa Sheikh ya numfasa ba dai ce komai ba. Ayyan ɗin ya ce. "Zata samu gogewa cikin ƙaramin lokaci Insha Allah, kuma a nemata mai darasi a gida,that will help her study more" Umar-khan ya yi murmushi ya ce "How long do you think she can take the time before she can learn everything, and get experience" Ayyan ya ɗan kalli Halisa yana karantar how smart she's kafin ya ce "I can't say how long it will take,But she will get good academic training" Umar-khan ya ce "that's good, amma matar...." Gyaran Muryar da Yaa Sheikh ya yi ya hana Umar-khan faɗin abin da ya ke shirin faɗa ɗin. Yaa Sheikh ne ya fara miƙewa yana kallon lokaci a nutse ya ce.
"A kula, banda wasa" ta miƙe tsaye tana shirin yin magana ya yi waje abinsa domin yasan zata iya faɗin abin da ba shikenan ba, bai shirya ɗaukan abin kunyarta cikin mutane Yanzu ba. Idanunta ya cika da hawaye sosai tana neman yin kuka a haka Headmaster ɗin ya kaita Jss 1. Akan idanunta kuma motar Abban nata da Umar-khan ta fita waje. Ita ɗaya ce a table nata, gaba ɗaya class ɗin basu da yawa dukkansu farare dasu gwanin sha'awa, itama ta saje dasu sbd farin da take dashi mai tsari.
Shiru tayi tana kallon kowa da idanu kowa na ajin harkar gabansa yake a haka Headmaster ya gabatar da ita ya fita. Babu jimawa wani kyakkyawan balarabe ya shigo cikin jallabiya ash ya ɗora half ɗin hula a kansa, bai tsaya jiran gaisuwarsu ba. Ya nufi blackboard inda suke duba kamar computer haka ya shiga latsa abubuwa sai ga sunan subject ya fito


_Social studies_
A ƙasa kuma aka rubuta _MEANING, SCOPE AND NATURE OF SOCIAL STUDIES_
Matashin ya kalli students ɗin dake gabansa, har lokacin idanunsa bai kai inda Halisa take ba, cikin kamala ya ce.
"Alhmd, yau zamu fara da meaning na social studies, please who can tell me the full meaning of Social studies?" Duk sukai shiru ya ce.
"It's okay" ya ɗan duba abu kaɗan kana ya mai da attention nasa ga ɗaliban ya ce.
_“Social studies can be defined as the study of man and his environment. Social studies can also be defined as the totality of man’s physical and social environment”_ daga nan ya yi musu explanation yadda zasu fahimta ya saka english ya saka Larabci maybe they can understand very well. Yana ƙoƙarin yin magana yaji ance.


"To aradu nidai tunda ka fara magana ban san me kace ba, idan zaka faɗa da hausa kawai ka faɗa ko kayi shiru" ya juya gaba ɗaya zuwa direction ɗin da daddaɗar muryar dake tashi, yana juya a ƙaramin bakinta idanunsa ya sauka, magana take sosai ko haɗiyar yawo ba tayi. AZAAN ya ware fararen idanunsa akanta da kyau, da alama ita ɗin new student ce, yasan magana take amma baya gane me take cewa sosai, ya dai san hausa take.
Ya ɗauke bai tankata ba ya ce.
_“SCOPE OF SOCIAL STUDIES”_
_The word “man” in the definition given above connotes human beings while man’s environment has a huge influence on mankind in all spheres of life.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login