Showing 90001 words to 93000 words out of 197828 words
Chapter 31 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
WA KHAIRI MA JABALTAHA ALAYYA.WA A'UZU BIKA MIN SHARRIHA WA SHARRI MA JABALTAHA ALAYYA, Ya Allah ka kula mini da ita, ka sanya albarka a iyalina" ya ƙara sumbatar goshinta bisa sunna ya ce "Rabbi ya yi miki Albarka Ƴar Aljanna" ta kallesa da kyau bakinta na rawa ta ce "Abba kaga me na gani kowa?" Ya rufe bakin ya ce.
"Shahh, Al'amarin aure ne" ya zame jikinsa har lokacin bai dawo daidai ba, tabi shi da idanu. Ya ɗauki lokacin kafin ya fito fuska a ɗan kame gudun surutun nata amma duk da haka sai ta miƙe zaune ta ce "Wankan Janaba kayi Abba?........
*Idan kana buƙatar posting har weekend wani time ɗin sau biyu a rana. Zaka biya 1k... Idan ka riga ka biya 500 zaka ƙara adding 500 a saka ka cikin Special grp 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616."Ga Yaa Lee muna tare da shi, yaushe yazo ya ɗauki Halisa?" Headmaster ya goge zufar dake bin fuskarsa al'amarin ya fara bashi tsoro ya ce. "Wallahi ina faɗa maka, yanzu ka shigo ka tafi da ita, har kana ce mini ya karatun nata, kuma sai ka dawo kace tana ina?" Yaa Sheikh ya yi shiru.
"Wani irin murɗaɗɗen abune, ba dai Yaa Sheikh yazo ba, sai dai wani kai kuma baka duba ba" "Ta ya ya za kai mini musu? bayan muna da cct.v Camera yanzu sai na duba maka"
Umar-khan ya ce "Muje, amma da sake" Yaa Sheikh ya ɗaga kansa sama a hankali cikin sauyawar murya ya ce.
"Na fahimta,muje" Umar-khan zai magana Yaa Sheikh ya ɗaga masa hannu alamar ya yi shiru. Tunda suka ɗauki hanya Yaa Sheikh ya kasa samu damar yin cikakken tunani.
"Waye?" Ya furta a zuciyarsa ya ɗauka tuntuni ya magance wannan matsalar ashe ya kashe maciji bai sare kansa bane. Yanzu kuma ya yi girman da idan ya ce zai raba shi da ita babbar matsala ce. Duk da bashi da cikakken hujja akan abin da ƙwaƙwalwarsa take faɗa,amma zuciyarsa na son gaskata hakan.
Har suka iso gida Yaa Sheikh bai san sun ƙarasu ba. Sai da Umar-khan ya ce.
"Lafiya kake dai?" Ya kame fuska tare da saukowa sai da ya yi nisa ya tsaya ya ce.
"Ka nemi abin faɗa"
Umar-khan ya ce "Kada ka damu da hakan" bai bari ya shiga ta asalin ƙofar gidan ba, ya ratsa da bayan gidan ya shiga sashinsa.
Umar-khan na shiga ya samu El-bashir da Mai martaba Ahmad Sarki zaune suna hira sama-sama Ummul ta cika musu gabansu da kayan cima kala-kala.
"Ina Aliyun fa?" Umar-khan ya zauna cikin matartabawa ya ce "Yana ɓangaren shi,baya jin daɗi" Ummul ta ajjiye plate na hannuna ta ce.
"Halisa fa?" Ya ce "Tana makaranta" Ta kallesa alamar bata fahimta ba ya ce.
"Tana ɗaya daga cikin yaran da aka zama masu ƙwazo, wanda za ai quiz dasu, an riƙe ta zuwa kwana biyu dan bata huro" Ummul ta ce "Something fishy" maganar ta tsaya iya ranta, ta san babu hujjar da zata sanya Yaa Sheikh yabar Halisa a wani wajan har tsayin kwana biyu, dole akwai abin da yake ba daidai ba. Ko yini ya yi bai ji motsinta ba, ba zai tambayi ina take ba, amma daya fito Main parlour tasan neman lafiyarta yake son ji, da rashin jin motsinta.
Tai murmushi kawai ta ce. "Ah ba shakka, Allah ya bada sa a" Umar-khan ya ce "Amin"
"Umar-khan ya batun Companyn Sarrafa shinkafa na Aliyu?" Umar ya ɗan kalli El-bashir da yake danna waya hannunsa riƙe da Apple yana sha ya ce "Allah ya taimaki Mai martaba, komai lafiya yake cikin yarda da amincin Ubangiji" Mai martaba ya sauke numfashi yana jinjina kai kafin ya ce.
"Ina son Mota guda da za a rabawa jama'a na kyautar Ramadan, waye manager na Companyn?" Kan Umar a ƙasa sbd nuna girmamawa ya ce
"Yarima Khalil Ahmad Sarki shi ne Manager na Companyn Sarrafa shinkafa na Yaa Sheikh" El-bashir ya ɗago kai da sauri jin abin da Umar ya ce, wato Yaa Sheikh ba ƙaramin kai wayo bane, kamar yana da sanin cewa za a iya yi masa sharri cikin kayan da yake kawowa, shi ne ya saka Khalil matsayin Manager ya san cewa El-bashir ba zai taɓa cutar da Khalil ba, dukkan abin da ya faru za a alaƙanta shi da Khalil tunda da saka hannunsa komai ke tafiya.
"Ikon Allah, bani da labari zanwa Khalil ɗin magana" Mai martaba ya miƙe tsaye domin ziraya yake son ya fara kaiwa tun kafin watan Ramadan ɗin ya fara, zuciyarsa har yanzu ta kasa yarda da ƙaddarar data faɗa masa gani yake kamar akwai wani abu dake shirin faruwa. El-bashir ya miƙe tsaye tare da bin bayan mahaifinsa har zuwa harabar gidan Yaa Sheikh suka shiga mota.
Yaa Sheikh ne zaune gaban Alƙibila hannunsa riƙe da ƙaton Alkur'ani gaba ɗaya ya rufe fuskarsa karatu yake cikin suratul Yaásin, ɗakin baki ɗaya yai duhu sai zoben dake hannunsa ne kawai yake bada haske mai kyau.
Ya yi nisa sosai cikin karatun yaji ɗakin ya fara girgiza wata ƙaramar ƙara ta fara cika ko'ina na ɗakin. Cikin murya mara daɗin saurare aka shiga faɗin.
"Laifinka ne, laifinka ne, laifinka ne" Yaa Sheikh ya saurara da karatun da yake tare da sauke numfashi ajajjere kwana biyu abu na neman fin ƙarfinsa, Shikenan ba dama ya karanta suratul Yaásin sai su bayyana kamar dai ya kirasu, sun nace sai sun zauna tare dashi amma me yasa yanzu suke neman takura masa duk da sharuɗan daya kafa musu?. Ya buɗe fuskarsa yana ƙara gyara zaman shi ba tare daya saurari abin da suke cewa ba.
Abin da ke magana ya bayyana a suffar wata baƙar mage mai manyan idanu. Can nesa da Yaa Sheikh taja ta tsaya ta ce.
"Ba zai taɓa rabuwa da matarka ba, indai baka mayar da ita cikakkiyar mace ba, ka halakta auren dake tsakaninku, kasancewar ku tare da kuma mai da ita babbar mace kamar ko wacce matar aure shi ne zai kawo ƙarshen shi, a ranar da kuka zama ma'aurata a ranar komai nasa ya ƙare" Yaa Sheikh ya miƙe tsaye yana son barin ɗakin don yasa abin da ya daɗe bai tasar masa ba yana gab da tashi, kafin ya fita magen tai tsalle ta hau saman wuyan shi bakinta na wani irin hayaƙi ta ce.
"A shirye yake, a shirye yake, a shirye yake, kawo yanzu muma bamu san inda ya kaita ba" a fusace kamar wanda ya samu juyewar tunani haka Yaa Sheikh ya damƙi magen bakinsa ɗauke da addu'a ya bugata da jikin bango, a tare suka saki ihu ita da Yaa Sheikh sai dai nasa ihun yana da banbanci da nata, shi mai ɗauke da kiran sunan Ubangiji ne, ita kuma ji tayi kamar Yaa Sheikh ya zuba mata dalma a jiki.
Cikin gilmawar haske a cikin duhu haka magen ta ɓace ɓat, Yaa Sheikh kuma ya sulale a tsakiyar carpet ɗin bedroom ɗinsa, tare da ɗaukan hiraminsa ya naɗa wani rawani mai masifar kyau a kansa, a nutse ya harɗe ƙafafuwansa kamar wanda yake tsakiyar fada zaune akan karagar mulki. Ilahirin fuskarsa zufa ce take yankowa kansa a ƙasa ya ɗora hannunsa saman cinyoyinsa.
Zuwan Ummul huɗu sashin Yaa Sheikh tana samunsa a rufe, yanzu ma tana tsaye a zuwa na biyar tana mmkin abin da ya hana Yaa Sheikh fitowa tasan kuma azumi yake tunda yau Alhamis ne. Ta duba lokaci taga lokacin sallar Asr ta kusa kuma shi ne zai ja jam'i ta shiga bubbuga ƙofar amma taƙi buɗewa.
Cike da damuwa ta juyawa daidai lokacin kuma Mai martaba Ahmad Sarki da Umar-khan suka shigo Parlour ganin yanayin Ummul yasa Umar-khan cewa.
"Yaa Lee?" Da sauri ya ƙarasa wajan ƙofar yana tambayar Ummul "Lafiya mene ya samu Yaa Lee?" Ta girgiza kai ta ce "Kawo yanzu ban sani ba, amma nasan dole akwai abin da ke faruwa aciki" Umar-khan ya ciro key ɗin sashin na Yaa Sheikh jikinsa na rawa ya fara buɗewa, ƙofar na buɗewa Ummul ta ce.
"Tsaya a nan Umar, ganinka zai sanya yaƙi kulamu" Ya tsaya yana addu'ar Allah yasa lafiya.
A hankali Ummul ta shiga baya parlour kai tsaye ta nufi cikin bedroom ɗinsa idanunta ya sauka akan shi zaune tsakiyar parlour, hakan kaɗai ya isa ya zama hujja da zai sanya Ummul tasan yau fa ba iya Yaa Sheikh bane, hadda sarakunan da suke bibiyar rayuwar shi.
"Aliyu, Aliyu!"
Ta faɗa tana bubbuga kafaɗar shi, bai kalleta ba bai kuma motsa ba a fili ta ce.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Wanne abu ne haka Aliyu kake gani a rayuwarka daga wannan sai wannan" ta saki kuka tana juyawa. Mai martaba bai ce mata komai ba yabi gefenta ya shige bedroom ɗin Yaa Sheikh.
A rikice Umar ya ce "Ummul lafiya? Me ya samu Aliyun naki?" Ummul hawayenta yaƙi tsayawa cikin shassheƙar kuka ta ce.
"Umar-khan na gaji, wallahi na gaji ina tunanin lokaci ya yi da kowa zai san abin da ke faruwa, ba zan jure ganin halin da Aliyu ke shiga ba, kasan cewa wani lokacin ki barci bama yi idan hakan ta faru? Mene yasa duk ƙarfin ilimi da sanin da ubangiji ya bawa Aliyu Aljanu ke bibiyar shi ne?" Umar-khan ya goge zufa ya ce.
"Kiyi addu'a Ummul, ita yake buƙata daga gareki kada ki zubar da hawaye azabace a gare shi, kowa da zanan ƙaddarar shi, Yaa Sheikh kalar tasa kenan, mu gode Allah da iya abin yake tsayawa, kuma da yawan malamai zai wahala ki same su, su kaɗai"
Ta goge idanunta ta ce.
"Shikenan, amma Umar ka faɗa mini gaskiyar abin da yake faruwa, ruwa baya tsami banza" ya kalli ko'ina kafin ya ce.
"Munje makarantar su matar malam ance wani mai kama da Yaa Sheikh ya zo ya tafi da ita, na ƙaryata Headmaster ɗin ya ce muje ya nuna mini CCTV camera amma Yaa Sheikh ya ce a'a ya fahimci komai, Halisa missing" murmushi kawai Ummul tayi ta ce
"Na sani daman, ba haka kurum bane wallahi duk ranar da Aliyu ya rasa Halisa a rayuwar shi ka tabbatar za a ɗauki gawar shi ne" baki buɗe Umar-khan ya ce.
"But baya son ta ai, zuwa yanzu na fahimci da gaske Yaa Sheikh baya son Halisa" Ummul ba tai magana ba ta juya zuwa ɓangarenta, Umar-khan kuma ya shiga cikin part ɗin Yaa Sheikh amma ya tsaya iya parlour.
El-bashir ya saki murmushi yana sauke numfashi gabaɗaya conversation ɗin Ummul da Umar-khan a kunnensa. Idan har rashin Halisa zai iya ajalin Yaa Sheikh me ya sa yake wahalar da kansa, idan ya raba Halisa da duniyar ba shikenan ba?.
"Yaa Sheikh ka gama yawo" ya furta a fili. Juyawar da zai suka haɗa idanu da Zahrah wacce ta fito sanye da wasu shegun kaya, suka kalli juna.
Ganin ta nemi waje ta zauna yasa El-bashir ya sauke ɓoyayyiyar Ajjiya, sai da hantar cikin El-bashir ta kaɗa saboda tsananin tsoro daya shiga. Tunaninsa ya tsaya na wani lokaci domin zaton shi Zahrah taji abin daya faɗa sai yaga saɓanin haka.
Shima ya zauna idanunsa akan t.v kamar daga sama yaji ta ce.
"Kana da alaƙa da Halisa ne?"
"Me ya sa zan samu alaƙa da ƴar uwarki?" Zahrah tai murmushi ta ce "Ba ƴar uwata bace, kamanninku sun ɓaci" ya taɓe baki ba tare daya damu da tace ba ƴar-uwarta ba ce.
Ta miƙe tare da nufar wajan Training ko cikinta zai sace daga kumburin da ya yi mata, ita kumburin har tsoro ya bata.
Mai martaba ya kalli Yaa Sheikh daya miƙe tsaye sai kuma ya juya ya kalli Abba Hakimi dake kan screen suna vedio call ya ce "Ina ganin komai ya yi daidai" Abba Hakimi ya rufe Kur'anin gabansa shi kaɗai yake iya daidaita hargitsin na Yaa Sheikh kafin ya ce.
"Ina tunanin lokacin da Aliyu zai dawo kusa dani har abada ya yi, banga me yake a Madina ba, shi ba uwa ba, shi ba Uba ba balle ƴan uwa a can ɗin ba, na rasa me ya liƙewa a can ɗin" Mai martaba ya ce. "Abi komai a sannu, komai zai shige" Sallama sukai Mai martaba ganin babu Yaa Sheikh a bedroom ɗin ya nufi hanyar fita.
A hankali take buɗe idanunta wanda ya yi mata nauyi sosai tare da kallon inda take wani ƙaramin ɗaki ne amma mai kyau da tsari ta yunƙura kaɗan tana jin kanta na sarawa.
"Kin farka matata?" Tunaninta ya tsaya tunda take Abbanta bai taɓa cewa matata ba, kenan ya yarda yanzu ita matar shi ce. Ta juya hannunta dafe da kanta sukai idanu huɗu, yana tsaye a cikin kyakkyawar shigar shi kamar kullum sai dai a wannan karan Jallabiyar duka ta rufe masa ƙafa ta buɗe baki da ƙyar ta ce.
"Abba, ina ne nan kuma?" Prince Bilal wanda ya yi suffar Yaa Sheikh sak ya ƙara su inda take yana kama hannunta ya ce.
"Sabon gida mukai Danejo matata, yadda zan samu damar kasancewa dake muyi soyayya sosai" ta kalle shi ya akai yau Abban nata yake sakin zance ba dadin ita yau ba darasi sai soyayya ta ce.
"Zanyi wanka Abba, jinin ya tsaya" Bilal ya ce "Jini? Shikenan an gama dani" bata gane zancan nasa ba, ta nufi bathroom tai wanka duk abin da Ummul ta faɗa tayi ta fito ɗaure da towel Bilal ya dinga kallonta ya kama hannunta zai rungometa yaji kamar an buga masa guduma a kai ya saketa da sauri yana faɗin.
"Da akwai wani abu a jikin ki, maza cire" Halisa ta dinga duba jikinta amma ba taga komai ba ta ce "Abba ba komai, wai Abbana meya sameka?" Ta faɗa tana shigewa jikinsa Bilal ta birkice ko ya ya Halisa ta taɓa shi masifa ya keji.
Ya cireta yana cewa "Lafiya nake shirya kiga" tai murmushi tana cewa "Ko wanka ne baka son kayi ne?" Ya yi mata shiru tare da ɗauke kai domin ya fara riƙiɗewa kamar Aljani.
Ta shirya cikin kayan daya bata tai sallah duk a ɗakin. Dare nayi ya bata abinci taci kaɗan kamar wacce tasan meke faruwa sai bata ƙara zuwa inda yake ba, Bilal kuma ya wanzu yana bin jikinta da kallo ko zai gano abin da yake masa shamaki da ita.
Cikin dare Yaa Sheikh ya kasa barci duk inda yake tunanin zai ga matar Malam babu ita. Wajan uku na dare ya fito direct ɓangaren Ummul ya nufa kamar tasan zai zo ƙofar a buɗe take, tana zaune saman ladduma taji ƙamshin Roja ta kallesa taga ya kalleta shima ta ɗauka zai je saman kujera sai taga kai tsaye ya dawo kusa da ita ya zauna, bai ce komai ba ya ɗora kansa a cinyarta ya dinga sauke ajjiyar zuciya.
Abu kamar wasa har ana igobe ɗaukan azumi babu Halisa, babu wanda yasan halin da ake ciki na rigimar Yaa Sheikh sai Ummul, Zahrah ko a jikinta. Da sassafe Yaa Sheikh ya fita Zahrah kuma ta shiga ɗakin Ummul tana zuwa ta ce "Ki faɗa mini abin da yake faruwa da mijina da baya son raɓar inda nake" Ummul tai shiru Zahrah ta ce "Wallahi munafuka ce ke kin san komai ki faɗa mini abin da zan yi mijina ya raɓeni" Ummul tai murmushi ta ce "Tausayi ki ke bani, naga har yanzu kin kasa fahimtar waye Aliyu kin kasa gane cewa shi ba cikakken namiji bane, shiyasa aka auren haɗi tsakanin ke da Aliyu" gaban Zahrah ya faɗi ta ce "Kina nufin Yaa Sheikh bashi da lafiya?" Ummul ta ce "Ba a faɗa miki bane daman? Aliyu ai ba zai taɓa iya tarayya da mace ba, likitoci sun tabbatar da haka, zaman ibada zaki da kulawa da shi" Zahrah ta ƙunduma wani zagi tare da yin waje wayarta ta ɗauka ta shiga kiran number Father ringing ɗin farko aka ɗauka Father ya ce.
"My daughter ya ki ke?" Cikin rashin ladabi Zahrah ta ce "Ban san ya nake ba, ashe kasan cewa ɗanka Aliyu nakashasshe ne bashi da lafiyar tarayya da mace shine kasa mukai aure?....
Paid book
500
08119237616*"Kada ka kusantar mini mata, zan illataka na illata Ahhalinka Malam" Yaa Sheikh bai saurari maganar da Bilal yake ba, idanunsa akan fuskar Halisa wacce jikinta ke rawa tsoro ya kamata kallo ɗaya zakai mata kasan cewa ta gama firgita da abin da yake faruwa. Ƙirjinta na ɗagawa sosai numfashinta nayin sama hakan yasa Yaa Sheikh ƙara shigar da ita jikinsa da kyau yana mai zame bakinsa daga nata sbd ganin Bilal ya gama haukacewa ihu yake da kururuwa wanda Yaa Sheikh da Halisa ne kawai ke jin haka.
"Ban son cutar da wata halitta ta ubangiji,, meyasa ka zaɓi cutar dani?" Bilal ya buɗe tangamemen bakinsa ya ce "Kai ne ka fara cutar dani, me ya sa zaka rabani da wacce na saba da ita? na wanzu ina rayuwa a jikinta, rana tsaka kayi mini kutse ka rabani ruhi da gangar jikina dana sahibar zuciyata" Ya faɗa yana ƙara sautin kukansa yana cewa.
"Matata, matata yake matata kizo gareni, na wanzu ina son uwa yanzu na dawo kan ƴa shi ne za a rabamu, zan rasa jin daɗi kwanciyar hankali idan bake Danejo, kada ki bari ya yi ajalina"
Ta ɗago kanta tana son fitowa daga cikin Alkyabbar Yaa Sheikh ya yi saurin mayar da kan ya haɗa da ƙirjinsa wanda gaban Jallabiyar ya ɗan buɗe kaɗan sai kwantacciyyar sumar wajan da tayi luf.
"Abba me ya sa muryarka ke rabuwa gida biyu? Me ya sa kake kuka?"
Ya matseta a jikinsa sosai hannunsa guda ɗaya yana shafa kanta.
Cikin nutsuwa ba tare daya kalli Bilal ba ya ce.
"Dani kai wanda ya fasa, yanzu zan nuna maka ƙarfin ikon Allah, zan ƙonaka da manyan ayoyin Alkur'ani mai girma" yana faɗin hakan ya fara karatu cikin nutsuwa ayoyi masu zafin gaske yake karantawa, Bilal ya birkice cikin ƙaramin lokaci guduwa ta mamaye wajan tare da ƙara da kururuwa.
Ƙam! Yaa Sheikh ya rungome matarsa itama ta zagaye hannuwanta ta riƙe ƙugunsa ta ɓoye fuskarta a tsakiyar ƙirjinsa yana jin yadda take sauke masa numfashi mai zafi.
"Shikenan naji zan fita, zan tafi zan barta amma kai ma ya zama dole ka rasata kamar yadda na rasata" Yaa Sheikh bai saurara da karatun ba cikin kuka Bilal ya ce.
"Ashe zaki iya bari a rabamu? Ni ne mijinki abin son ki nace zaki bani ƴa ƴa da yawa ki tausaya mini"
Wani ihu da